Nida patient dina book two by mrs isham - Chapter 21
Nida patient dina book two by mrs isham Chapter 21: Nida patient dina book two by mrs isham Chapter 21. Tun bayan tafiyar fanan basu sake tsinkayar kansu…
4,314 words
Tun bayan tafiyar fanan basu sake tsinkayar kansu acikin farin ciki ba se zuwan twinkle ita kadaima insuka gani ransu nayi musu sanyi domin suna kallon fanan atattare da ita, har yau daya kasance gobe suna baba da mama basu sa twinkle a ido ba sede a hoto ne suhaima da ya usman suke nuna musu ita , su umma rahina da amira da ya al ameen sunzo saboda suna da za'ayi.
INDIA NARAYANA SUPERSPECIALITY HOSPITAL
Yau tunda suka tashi doctor yazo ɗan ganin ya yanayin condition din Mr azaad yake saboda yanzu ne yacika wata uku da sati biyu inhar de be samu lafiya a wannan lokacin ba to fa sede afara mishi shirye shiryen treatment din wata shida, yaseer da Fawwaz suna zaune akan kujera suna ganin yanda doctor din yake kokarin yin conversation da Mr azaad amma yakiyin magana ,yau haka suka tashi dashi ko irin dan sambatun da yake yi ma beyi ba yana zaune yabasu baya yana kallon waje daya, doctor Shankhar ya ce " Mr azaad don't you want to speak to me today?" Ko kallon inda yake Mr azaad beyiba doctor Shankhar yasake cewa " alright is okay, but do you know that you're a father now ?" kamar daga sama batare da sun taba tsammanin hakan ba kokuma tunanin haka ze faru ba , sukaji Mr azaad yabawa doctor Shankhar amsa da" Yes i know " shikanshi doctor Shankhar seda yaji kamar kunnen shine ya mishi gizo yasashi sake cewa " okay do you know you're a father right?" murya adaƙile kamar wanda ake takurawa cikin rashin sonyin magana ya ce" Yes i know and please don't disturb me " atare Fawwaz da yaseer suka ɗaga hannu sama suna godewa Allah matsanancin farin ciki suka shiga wanda baƙi baze iya faɗa ba zama sukayi kusa da Mr azaad fuskokinsu dana doctor duk na dauke da murmushi, congratulations doctor yayi musu sannan ya ce nanda One week za'a sallameshi , kafin doctor Shankhar ya rufe baki Mr azaad ya ce ko kwana ɗaya baze ƙara a asibitin ba , yanayin yanda yake magana kaɗai ma mutum yaji yasan ya canza sosai domin inyana magana ko ɗago kai ba yayi balle ya kalli me mishi magana miskilanci yaƙaru fiye da na da . Sallama doctor yayi musu yafita, yaseer ya ce " dude nayi farin ciki sosai da Allah yabaka lafiya" banza yayi dashi kamar be jishi ba se bayan minti goma ya ce " ina twinkle?" Fawwaz ya ce " an karbota a asibiti,gobe za'ayi sunanta" tundaga nan besake ce musu komai ba ya mike yashiga toilet bin bayanshi sukayi da kallo , ganin a ƙashi ɗari na halinshi nada yanzu ƙashi 90% yadawo, saboda dama shigowar fanan rayuwarsa ne yasa yarage amma yanzu sundawo fiye dana da dinma , suna magana yafito daure da towel a kugunshi kallonsu yayi be ce musu komai ba dan maganar ma wahala yake bashi , fahimtar abinda yake nufi da sukayi ne yasa Fawwaz mikewa yabude wardrobe a bangaren da kayanshi yaje ya fito mishi da jallabiya fa ra , karba yayi ya koma toilet din yasaka yafito fuskan nan adaure kamar wanda besan menene kalmar dariya ba arayuwarsa. Sude se aikin binshi da sukeyi da ido , Dan sunsan ko sunyi mishi magana ma ba kulasu zeyi ba hakan yasa suka zuba mishi ido kawai, kira ne yashigo wayar yaseer number Abba ne dagawa yayi suka gaisa sannan ya tambaye shi Mr azaad , girgiza mishi kai Mr azaad yayi alamar kar ya ce musu komai. Kamar yanda ya buƙata haka yaseer yayi yace mishi yana nan lafiya haka suka gama magana sannan ya katse kiran.
" Fawwaz kayi mana booking flight ayau din nan zamu koma Nigeria". " okay " Fawwaz ya amsa sannan yayi musu booking flight s online karfe 6:00mp jirginsu ze tashi. https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8
🧑⚕️🧑⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺
Story & written by ✍️ MRS 🌹 ISHAM 🌹 ( Yar lelen Jarumai)
*🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚📚*
⚜️📚J. A. W🖋️📚
THE END .
*Wato Hausawa sunyi gaskiya dasukace komai yayi farko zeyi karshe haka zalika laifin daɗi karewa,ya Allah ka yafemin kura kuran da nayi acikin wannan littafin😭🙏 duk wanda na batawa rai yayimin afuwa ya yafemin dan ɗan Adam ajizine . Masu min addu'a da fatan alkhari ina godiya bazan taba mantawa daku ba, masu karfafamin guiwa Kuma ina godiya bazan taba mantawa daku ba domin kun ban babban gudunmawa nagode sosai Allah yabar zumunci*
PAGE 6️⃣3️⃣
Batare da yan Nigeria sun san da zuwan nasu ba karfe shida nayi suka wuce airport jirginsu yatashi zuwa gida Nigeria, karfe hudu na asuba jirginsu yayi landing a gombe lawanti international airport, taxi suka shiga zuwa gida tunda suka taho a cikin jirgin babu wanda Mr azaad yayiwa magana acikin su har suka shiga taxi zuwa gida se hiransu sukeyi uffan be ce musu ba daga karshema surutun nasu ma ya fara damunshi yaja dogon tsaki suna jin haka sukayi shuru da bakinsu .
*Horn me taxi yayi , fitowa baba me gadi yayi dan ganin su waye , ganin Mr azaad ne dasu Fawwaz yasa ya wangale musu gate yaname murnan ganin Mr azaad*
Fitowa yayi yabarsu suna sallamar me taxi , shigowa cikin part din yayi jin motsi a kitchen yasashi ya tsaya daga bakin kofa ya ce " ƴata na wajen waye ?" Dasauri abu ta juyo jin muryan da batayi zato ba , cikin farin ciki ta washe baƙi " yallabai Azaad kaine alhamdulillah sannu da hanya , tunkwal na wajan ummi" yar harara ya watsa mata jin yanda takira sunan twinkle da tunkwal barin kitchen din yayi ya shige part din ummi dake bathroom taje dauro alwala zatayi nafila. Hawa kan gadon yayi yadauki twinkle dake baccinta peacefully yana kallon fuskanta da bashida maraba dana fanan yanajin tsananin kaunar twinkle aranshi ,ahankali yafurta " sleeping beauty" ya mannata ajikinshi tashi yayi dauke da ita ahannunshi yafice a bedroom din ummi ya nufi nashi bedroom din, kwantar da ita yayi akan makeken gadonshi yasake rufeta da blanket sannan ya shiga toilet yayi wanka da alwala yazo yafara nafilfilu yana addu'a Allah ya kare mishi fanan yakuma sa tadawo rayuwarsu be tashi na har seda aka kira asuba yayi Sallah sannan yahau gadon yashiga blanket din yajawo jaririyar shi kusa da shi yana kallon fuskanta,ahaka bacci yayi awon gaba da shi .
Fitowar ummi daga toilet tadauro alwala kenan ta kalli kan gadonta fuskantar dauke da murmushi, gabanta ne yafadi lokacin dataga babu twinkle akai dasauri ta karasa izuwa gadon kamar wasa bataga twinkle ba hankalinta yayi matuƙar tashi ba shiri ta fice a part dinta saukowa downstairs tayi taga abu , abirkice ta ce " abu dan Allah akwai wanda kika gani yashiga part dina ne?" Murmushi abu tayi ta ce " eh ummi! Yallabai Azaad ne yashiga kuma naga fitowar shi da tunkwal a hannu " shuru ummi tayi jin abu ta ambaci sunan Mr azaad tunani tafara yaushe suka dawo to kenan hakan na nufin yasamu lafiya murna ne yakamata da sauri_sauri ta nufi part din nashi, bedroom tasamesu suna bacci zama tayi akan gadon tana shafa kanshi tanajin matsanancin farin ciki yana ratsata , ahankali yafurta " ummiii" batare da yabude idanunsa ba , " na'am son , fatan kundawo lafiya ?" tashi yayi yazauna ya ce " uhmmm" tundaga jin amsar daya bata ummi tasan he has changed completely ganin gaba daya fuskar shi ba walwala, riko hannunshi tayi ta ce " son kaga our little feena ko , babu abinda yarabasu da my feena, aduk sanda na kalli fuskar ta inaga ganin my feena atattare da ita, son yakamata yanzu kayi move on ko dan amanar twinkle da feena tabaka kazama uba na kwarai inkana cikin wannan yanayin taya ne zaka kula da twinkle? Hakuri shine Yakamata muyi ,mudauki dangana da juriyar rashin feena nasan is not easy for you my son, but you have to for the seak of twinkle ka ji " gyada mata kai yayi kawai batare da ya iya cewa komai ba yaname kwantar da kanshi akan kafadarta slowly ya ce" thanks ummi " ummi ta ce " son yaune sunan twinkle wani suna Yakamata asa mata " ajiyar zuciya Mr azaad yayi ya ce " Fatima za'a samata sunan wifey tun ranar da aka haifeta nayi mata huduba da Fatima " murmushi kawai ummi tayi tanajin dadi aranta a part din tayi Sallah. Karfe 7:00am aka raɗawa twinkle suna da sunan mahaifiyarta fanan, kafin gari yagama wayewa duk family kowa yasan Mr azaad yadawo cikin koshin lafiya , anty shayida tazo da yaranta yan biyu mata ta haihu satin da yawuce sukayi arba'in sunansu adeema da adeena ,haka anty zainab tazo tare da yaronta daya dawo daga egypt ya kammala karatu , yan uwa duk anzo suna su hairah da auta da amira tun karfe 8 suka zo gidan , haka mahaifiyar yaseer ma tazo , shigowa gidan baba da Abba sukayi suna part din Abba da wasu abokan abba suna hira Mr azaad yashigo da twinkle ahannunshi tana sanye da kayan jarirai me matukar tsada , zama yayi akan kujera rike da ita ya gaidasu suka amsa fuska asake Abba ne ya ce " to kabamu ita mu ganta mana" kamar baze bada twinkle din ba se kuma ya miƙawa baba ita , murmushi baba yayi yace " Fatima na biyu kenan , Allahu Akbar Fatima ta tafi Fatima ta dawo Allah yarayaki ya albarkaci rayuwarki" haka baba yadinga mata addu'a sannan yamikawa Abba ita shima karbanta yayi yana yi mata addu'a, yana zaune yana jiran su gama su bashi yarshi yayi tafiyarsa , karbanta yayi a hannun Abba . yafice abinshi ya nufi part dinshi afalo ya tsaya yana kallon katon hoton enlargement din hotonshi shi da fanan fuskantar dauke da ƙayitatciyar murmushi ta riƙe hannunshi tana kallon fuskanshi , shikuma yazagayo da hannunshi yana rike da kugunta fuskanshi asake dayan hannun kuma yakama kumatunta . Murmushi yayi lokacin daya tuna sanda akayi hoton , ranar da suka dawo daga shopping ne suka tsaya a garden suna hiransu gwanin sha'awa tashi sukayi zasu tafi yajawota jikinshi yayi yadaura hannunshi akan waist dinta dayan kuma kuma yariƙe kumatunta itakuma tana sakar mishi tsadadden murmushinta dake kara mata kyau , suna ahaka basu sani ba Fawwaz dabesan suna cikin garden din ba yashigo burgeshi sukayi sosai yasa yafito da wayarshi yafara daukansu hotuna,yayi musu hoto yafi guda goma ankara dashi Mr azaad yayi yagalla mishi harara ganin inda yake kallo ne yasa fanan juyawa tana ganin Fawwaz ne awajen dasauri taraba jikinta da na Mr azaad cike da jin kunya tabar garden din da gudu, da karfi Fawwaz ya ce " haba antynmu kiyi hakuri kidawo bari in baku guri " damkar kunnenshi Mr azaad yayi ya ce " wato labe kakeyi mana nida matata ko ? " Kara Fawwaz yasa yana " sorry Babban ya'ya wallahi kun burgeni ne yasa nake muku hoto" hararanshi Mr azaad yayi ya ce " kafin awa daya kazo min da enlargement din hoton in kuma beyi kyau ba zakayi bayani " yasakeshi yabi bayan fanan. Dariya fawwaz yayi ya ce " salon soyayyar ku na daban ne ya azaad da anty fanan Allah yabarku tare " ya ida maganar yaciro waya yakira layin wani photographer yatura mishi hotunan ya ce yanaso ya mishi katon enlargement nan da anjuma akawo. Haka yazauna a garden har aka kawo enlargement din da akayi rapping dinshi shiga part din Mr azaad sukayi da shi basa falo suna cikin bedroom dinshi , manna enlargement din akayi ajikin bangon falo yazauna sosai yanda suka fito sukayi kyau ajikin hoton Kamar a kirasu su amsa. Fitowa Mr azaad yayi yaga harsun manna enlargement din ya ce " Allah yataimake ka " murmushi Fawwaz yayi suka fita shida wanda yakawo hoton , jin sunfice ne yasa ta fito " habiby kazo ka nunamin wanne zansa" tayi maganar batare da ta lura da enlargement din jikin bangon ba , nuna mata yayi da hannu zaro manyan fararen idonta waje tayi sosai ta rufe baƙinta ta karaso gaban hoton tasa hannu ta shafa ta ce " yaushe akayi wannan hoton , wallahi yayi matukar kyau sosai" tafada tana rungumeshi.
Murmushi yayi bayan ya gama tunawa yasa hannu yashafa hoton dede fuskar ta ya ce " i missed you so much baby rayuwa yamin zafi sosai da babuke aciki, ki kalli our little twinkle , na miki takwara sunanta Fatima ina fatan itama tazama jajirtacciya irinki me kyawawan halaye. Bazan taba cire rai da dawuwar ki ba ina nan ina zaman jiranki " Kuka twinkle tafarayi jijjigata yayi yana murmushi ya ce" karfa kidauko min rigimar mommynki " kamar tasan me yafada tayi shuru yana tsaye agaban hotonsu zeenat tashigo kallo daya tayiwa hoton bata sake kallo ba saboda tasan intaci gaba da kallo tasan yanzu zata fara kuka ɗan ji takeyi tafi kowa missing din fanan " ya azaad ummi ta ce kabada twinkle " ya ce" kifice ki bani waje bazan bada ita din ba" da sauri tafita mishi a part din shi tsaki yaja yashiga bedroom yazauna abakin gado har time din yana rike da ita, fadawa ummi yanda sukayi da Mr azaad zeenat tayi,ummi dama tasan zaarina mikewa tayi dakanta ta tafi part din nashi tace yabata twinkle be mu sa ba ya mika mata ita takoma falo tabawa umma rahina da sukazo da mama, mama ta dade bata shiga farin ciki irin na yau ba jitakeyi kamar tana rike da fanan ne , haka akayi suna nagani nafada baby twinkle tasamu kyaututtuka me tarin yawa ,an yanka manyan shanaye guda biyar da raguna anyi sadaka dasu komai anyi awadace karfe hudu na yamma aka watse kowa ya koma gidajensu, dare yayi yagama komai yazo ze kwanta zasuyi bacci twinkle tafara kuka rarrashin duniya yayi mata amma takiyin shuru daukarta yayi yanufi part din ummi tunkafin ya karaso ummi tajiyo kukan twinkle dama abinda take jira kenan saboda bataci abincin dare ba haɗa mata madaranta tayi a feda yana shigowa ta ce " dama nasan zaku dawo ai ta fada tana karban ta tafara bata madaran shuru tayi tanasha , gama sha tayi yakarbeta sannan yasa hannu ya kwashi kayan madaran nata ummi de binshi da ido tayi harya fice .
Tunda twinkle tayi arba'in yafara fita da ita duk inda zashi yana rike da ita ummi da Abba sunyi mishi magana harsun gaji akan yadena fita da twinkle amma hakan be hanashi daukar yarshi ba duk inda zashi a gida ma sosai twinkle take samun kulawa kullum tana tare da ummi ko Abba ko suhaima da sauran yan gidan haka zeenat da yaseer suma suke zuwa gida akai_akai ɗan ganin twinkle haka su ya usman ma suna zuwa , haka duk sanda Mr azaad yatashi daga office yana biyawa gida da twinkle yakaiwa su mama ziyara . irin kulawar da take samu awajen familyn ta guda biyu na musamman ne takara girma kowa sonta yakeyi duk abinda suka gani na jarirai zasu siya mata shi musamman me gayya me aiki daddynta duk sati se yayi mata shopping din lafiyayyun kayan madaranta da kayan sawa daduk wani abinda yaro yake bukata ga dakin da aka ware mata anzuba mata kayayyakin wasa aciki , sau daya twinkle takesa kaya bata sake maimaitawa duk kayan data saka baa kara samata shi komai nata special ne kuma masu mugun tsada ,hatta kayan da zatasaka komai dinta. gata iya gata twinkle na ganinshi . Sosai ummi tayiwa Mr azaad fada kafin nan suka samu yadena fita tare da twinkle, tana da wayo sosai gashi bata da ƙiwiya saboda kowa tasan fuskarsu musamman yanzu da tafara zama daga zaran taga daddynta yadawo zata fara bude baki tana dariya hade da miko hannu yadauketa haka zedauketa yana dariya haka take tabasu nishadi agidan , safiyar yau zeenat ta tashi da naƙuda aka kaita asibiti ta haifi namiji kyakkyawa me kama da babanshi yaseer, seda suka dawo gida tukun suka kira family suka sanar dasu aikuwa sunyi farin ciki da jin labarin haka sukaje yi mata barka , bayan sati daya akayi suna aka yiwa baban yaseer takwara yakubu suka mishi inkiya da ashraff. bayan ta haihu da sati biyu hairah ta haihu amma bata iya haihuwa da kanta ba seda aka mata operation ta haifi ya mace taci sunan mama wato sumayya akayi mata inkiya da samha gida aka dawo da hairah saboda kulawa da ita kuma mama na iya kokarinta wajen kulawa da ita yanda Yakamata su ya usman anzama baba , Amira ce take ta ja da nata tsohon cikin haihuwa ko yau ko gobe , suhaima haryanzu shuru kuma daga ita har Fawwaz din hakan be damesu ba . Duk sanda Mr azaad yatafi da twinkle Company ma'aikata sun dinga yi mata wasa kenan saboda tana da farin jini ga rashin ƙiwiya , duk da Mr azaad baya basu ita saboda be yarda da kowa ba se Faisal, shi kadai ne duk sanda Mr azaad yazo da ita suke tare dama tun faɗan da ummi tayi mishi akan fita da ita yadena se de duk ranar Friday yana fita da ita .
Amira ma ta haihu ta haifi na miji anyiwa baba takwara suna ce mishi musin duk anje suna Bauchi bayan angama suna kuma suka dawo . haka rayuwa yaci gaba da tafiya abubuwa nata faruwa aciki me dadi da akasin haka Mr azaad de yana bawa twinkle datayi wayo sosai kulawa shida yan gidan suna nuna mata gata , areef yafara zuwa aiki a kamfanin Abba , hafiz kuma ya zana papper anfara nema mishi addimission a gombe state University , kuma yasamu yafara zuwa.
Allah yayiwa Alh Ibrahim tijjani rasuwa kuma yayi ta tonawa kanshi asiri daga karshe ya haukace sannan ya mutu , ga aneesa da ciwo yafara cin jikinta tadawo gida ta nutsu duk irin rashin kunya da wulakancin data dingayiwa mahaifiyarta Hajiya Zainab daga karshe ita ce, take kula da ita saboda uwa ce ita bazata iya kauda kai akan yarta ba dukda kuwa abubuwan datayi mata haka taci gaba da kulawa da ita sukaje asibiti aka daurata akan magani , alhamdulillah maganin yanadanyi mata aiki amma ba sosai ba saboda HIV yarigada yayi tsanani ajikinta yafara kashe duk wani garkuwar jikinta.
Abangaren nusaiba da lukman suma suna nan suna rayuwar farin ciki da yaronsu namiji da ta haifa wata biyu dasuka wuce .
__________________________________________ NASMINAYA.
" Sarauniya kar muce zamu biyewa zuciya, kar ayi wannan yakin yanzu koda kuwa za'ayi muma mu rama irin abinda sukayi mana mu farmakesu a lokacin da basu sani ba nan ne zamu iyacin galaba akansu amma wannan sakon dasuka turo yanuna kancewa sun rigada sun shiryawa yakin kafin suka turo mana da saƙo" cewar wazirin nasminaya .daka mishi razanannen tsawa sarauniya tayi, a harzuke ta ce " yanda suka bukaci ayi wannan yakin dole za'ayi shi mudin ba matsorata bane , ai wannan nuna tsorone bamu cika ainihin jarumai ba inhar de bamu taresu gaba da gaba ba dole ne ayi kare jini biri jini , amma maganar kai musu hari batare da sun sani ba duk shirme ne "tafada tana kallon fuskokin ko wannensu kafin taci gaba da fadin " muma zamu nuna musu mudin masu nasara ne , hankalina baze taba kwanciya ba senaga bayan wa'yannan azzaluman dan haka kufara shirin yaƙi, sannan ku maida musu da saƙon cewa na amince da wannan gwabzawar da za'ayi , abashiyya ke kuma kitafi masarautar kusfah ki fadawa sarki habar muna bukatar dakaru saboda yaƙin dazamuyi . Dole wannan ƙaron ayi dayan biyu ko mu ko su " gimbiya afroza ce ta ce " yake sarauniyata tabbas iname goyon bayanki dari bisa dari amma muna bukatar dakaru masu matukar yawa, saboda wa'yanda zamu fuskanta kungiyoyi biyu ne kuma shu'umai ne marasa tsoron Allah " yarima ahil yace " nayarda da Maganar ki gimbiya amma fa kisani, masarautar nasminaya yafi karfin duk wasu kungiyoyi munada karfi dakuma kwarjini , kar ɗan sun kasance kungiya biyu ne su daga mana hankali da yardar Ubangiji munfi karfinsu" murmushi sarauniya tayi wanda tunda tazo masarautar ba ta tabayi ba ta ce " wannan gaskiya ne yarima ahil " suna cikin wannan tattaunawa wani tsohon dattijo yashigo fa da hannunshi rike da wasu abubuwa masu tsayi yarufesu da farin tufafi , dakatar da shi fadawa sukayi suka hanashi shiga yayi yayi subarshi domin yanada magana da sarauniya amma suka hanashi da karfi yayi magana " yake shugaba me adalci zasu kibawa wannan bawan naki daman yin muhimmiyar magana dake dan Allah dan Annabi" daga musu hannu sarauniya tayi suka barshi yashigo nuna mishi wajan zama jakadiya tayi , yazauna ya ce " shugabata zanso abamu waje" kallon su tayi suka ɓace yarage daga ita se gimbiya afroza da yarima ahil se jakadiya, galadima abdud Shakur,se waziri iya sune sukayi saura a fa da. Sarauniya ta ce " dattijo zanso kafadamin dalilin dayasa kakeson yin magana dani" mikewa dattijon yayi ya ajiye abun hannun nashi akasa yabude tufafin da ya rufe su dashi nan take wukake guda biyu suka bayyana, wukane da akayi domin yaƙi anyi shine da baƙin narƙekken dalma se yalki da daukar ido sukeyi, duk kallonshi sukeyi suna jiran ƙarin bayani daga wajan shi . " Ya shugabana wannan wukar ni na hadashi da hannuna domin bada nawa gudunmawan , a iya karfafa bincike na danayi shubumbum da tanzarzar zallar wuka babu abinda zeyi musu , shisa naje har birnin sin wajan uban gidana shine yafadamin abinda ze kashesu , bayan nadawo ne nahada wa'yannan makaman domin baki su nasan ze taimaka dan Allah shugabata ki karbi nawa gudunmawan " yafada yana zubewa akan guiwansa jinjina kai sarauniya tayi itada su jakadiya ta ce" na karbi wannan kyautar taka amma kafadamin amfaninsa me kyau , saura mara kyau din " zama yayi ya ce" shugaba ko min yaya kar ki bari wannan wukar ya yankeki domin yanda zeyi miki illa haka suma zeyi musu illa " murmushi tayi ta ce" Masha Allah " galadima abdud Shakur ya ce" tabbas sarauniya da yan fa da sunyi matukar godiya da kuma jinjinawa wannan gudunmawan naka " sosai dattijon yayi murna yayi musu sallama yatafi.
Sarki habar yaturo musu da dakaru masu matukar yawan gaske haka masarautar nasminaya sungama shirya duk dakarun su domin fita yaƙi, masu kai saƙo wa kungiyar SATANIC da BAPHOMET duk sunje sunkai.
Fitowa sarauniya tayi cikin azabebben shiga na yaƙi ga khairaty na hannun daman ta dakuma dakaru mata dasuke biye da ita, haka gimbiya afroza tafito itama cikin shigar yaki da yarima ahil ga shufan da shufaina yaran jakadiya da ita kanta jakadiyar duk sunyi shiga cikin kayan yaƙi. tsofaffi dakuma yara na masarautar sunatayi musu adduo'in samun nasara dakuma dawuwa lafiya . Hawa kan dawakai sukayi suka fara firewa akan dokunansu har suka dira a babban filin dazaa gabatar da yaƙin .
Tanzarzar yazo da mugayen aljanun dakarun shi haka shima shubumbum yazo da nashi dakarun masu yawan gaske , yaƙi aka fara yi baji ba gani kowa burinsa yaga yayi nasara yakashe makiyinshi , anyi kashe_kashen da bazasu san adadin su ba , inka duba bangaren sarauniya kisa kawai takeyi idonta yarufe burinta kawai takawo bayan wa'yannan azzaluman dasuka addafi ƙasa, jikinta duk yayi gaja_gaja da jini duk wanda ya shiga hannunta kisan wulakanci takeyi musu ga drygon dinta dake feso musu aman wuta , haka abangaren gimbiya afroza itama kisa takeyi bana wasa ba , harta khairaty ba'a barta abaya ba duk da ankashe musu mutane dayawan gaske amma hakan besa sun sare ba acikin faɗane aka kashe yaron jakadiya abashiyya wato shufan, sannan ankashe galadima abdud Shakur sauran kuma anji musu mugun raunin da bazasu iyayin yaƙi ba duk sun jigata musamman abashiyya da khairaty sunji rauni sosai, sarauniya ganin haka ne yasa ta kara kaimi , isowa gabanta tanzarzar yayi yana fadin " sarauniya karkiyi zaton keda mutanen ki zaku bar nan araye , kiduba munci galaba akanku , dake da jaaazana duk nawane hhhhhhhhhhh" yakarasa maganar nashi yana muguwar dariya ,dirowa shubumbum yayi gabansu ya ce " karya kuke yi nine kadai zan mallaki jaaazana dan haka inkun isa mu gwabza mugani " yafada yana zaro sharɓebiyar wuka, duk su biyun sun mata kewaye ga ta yar karama agaban su , gwabzawa suka farayi suna kaiwa junansu hari cikin zafin nama sarauniya tafito da wa'yannan wukaken da aka bata , tayi wani irin tsalle da seda tayi sama tana ihu me karfin sannan tadawo ƙasa tana caka musu dukkansu biyu lokaci daya nan take shubumbum yazube awajan babu rai duk wasu mutanen shi nan suka fara marmashewa izuwa toka suna mutuwa , karfin hali tanzarzar yayi yazaro wukar acikinshi kafin sarauniya ta ankara ya caka mata acikin ta ya ce " dole sede dukkanmu mu mutu , tunda kikayi nasarar ka war dani abangon duniya dole kema ki mutu " yana karishe maganarsa yazube ƙasa jikinshi yakama da wuta ya marmashe yazama toka yabi iska , haka duk wasu mutanen shi haka suka dinga marmashewa suna komawa toka duk seda suka mutu yayi saura iya yan masarautar nasminaya kadai afilin dagan , ganin halin da sarauniyarsu take cikine yasa yarima ahil da gimbiya afroza da sauran dakaru suka nufota da gudu kamin su iso tafadi aƙasa babu rai atattare da ita zare mata wukar cikinta yarima ahil yayi kafin yadauketa yasabata a kafadarshi suka ɓace , duk wa'yanda suka jigata suma ɓacewa sukayi zuwa masarauta , duk wanda suka gansu sunsan cewa sunyi matukar shan gwagwarmaya a yaƙin da akayi suna shigowa aka fara buga kararrawar nasara nan take kuma lokaci daya masarautar nasminaya ta tashi da labarai guda biyu daya na farin ciki daya na bakin ciki, wato na kashe musu mutane da akayi gakuma sarauniyarsu da aka dawo da ita itama babu rai sekuma na nasarar dasuka samu .
AFTER THREE YEARS ( bayan shekara uku)