Nida patient dina book two by mrs isham - Chapter 20
Nida patient dina book two by mrs isham Chapter 20: Nida patient dina book two by mrs isham Chapter 20. Tanzarzar yabawa yan kungiyar shi umarni dasu fara…
4,439 words
Tanzarzar yabawa yan kungiyar shi umarni dasu fara aiwatar da abinda yasa su na kashe duk wani jarirai dasuke asibiti dakuma mata masu ciki da masu jego acikin dare kuwa misalin ƙarfe goma sha daya suka fara kashe mutane acikin asibitoci sunyi shiga cikin bakaken kaya.
Karfe sha biyun dare fanan na bacci ajikin Mr azaad naƙuda yatashi mata ranga_ranga hankali atashe yatashi yaje ya bugawa ummi yasanar da ita abinda ke faruwa dasauri tabiyo bayanshi aikuwa tana duba fanan taga naƙuda ne jinjina ikon Allah tayi wato bakwaini itama zata haifa , ita bakwaini sannan zata haifi bakwaini , tasanar da Mr azaad haihuwa ne,dauko motar yayi yazo yadauketa Fawwaz jin an tada motar ne cikin dare yasashi lekawa ta window yaga Mr azaad dauke da fanan dake murkususun azabar naƙuda ga ummi da ta fito da kayan haihuwa acikin jaka suka shiga motar aka bude musu gate , da sauri Fawwaz ya tashi suhaima ta shirya suka bi bayansu suma , da gaggawa aka karbi fanan aka shiga da ita labour room tare suka shiga da Mr azaad yana rike da hannunta se faman nishi takeyi ga gumin datakeyi , Mr azaad is very speechless ganin irin azaban da mata suke sha wajan haihuwa jiyayi kamar yamayar da ciwon kanshi tana kuka hade da addu'a shima yana hawaye tun sha biyu ake fama amma har karfe hudu na asuba bata haihu ba har karfinta ya kare tama gagara yin nishin se wasiyya take barwa Mr azaad sosai yake kuka gani yakeyi kamar tafiya zatayi tabarshi , su ummi duk suna waje suna mata addu'ar sauka lafiya duk yan uwan sun hallara a asibitin harta su mama sunzo da abba su ya usman duka sunzo . duk se safa da marwa sukeyi abakin dakin labour din ganin har shida tayi babu labarin ta haihu.
Yau garin Gombe an tashi da munanan labarai na kashe kashen da akayi kuma ake kanyi ansa tsaro ba shiga ba fita sojoji da polisawa se dirƙa sukeyi acikin duk wani asibitin dake jahar gombe saboda kisan gilan da akeyiwa masu ciki da yara jarirai ankashe mutane sun fi ɗari lamarin ba kyan gani kowa a tsorace suke ko ina labaren ne ke tashi , gashi masu aikata kisan ba'a ganinsu , wannan shine tashin hankalin da aka wayi gari dashi a jahar gombe kenan.
Shigowa sukayi cikin asibitin medical center suka fara ɓarna sunshiga dakin da ake ajiye jarirai suka fara kashe su .
Shirye shiryen yiwa fanan operation sukeyi saboda ta ƙasa haihuwa da kanta har Mr azaad da baba sunyi sign za'a shiga da ita , karfinta yadawo tafara nishi da karfi ahaka harta haihu . Ta haifi ya mace kyakkyawar gaske me matukar kama da ita kamar tayi kaki ta tofar sede farin fatan Mr azaad tadauko fara ce sol gyarasu akayi ita da babyn sannan aka bata ita tana kallonta tana murmushi hade da hawaye manna mata kiss tayi ta ce " am sorry my angel zaki taso bazakiga mahaifiyarki akusa dake ba Allah ya miki albarka nasan babanki ze kula dake sosai " sude doctors binta suke da kallo dukda basu san ina zancen nata ya dosa ba amma tabasu tausayi , bude kofar labour room din sukayi suka fito hannunsu nadauke da baby girl din dasauri suka taso suna alhamdulillah mikawa mr azaad jaririyar sukayi karbanta yayi , nan take yaji wasu irin zafafan hawaye sun sauko daga idanunshi jiyayi kamar ayau din nan ze rasa wani barin bangare na jikinshi mannata yayi ajikinshi ya manna mata kiss a goshi, yayi mata huduba a kunne, karbanta doctor yayi yace " congratulations Mr azaad tasauka lafiya kuma itama Madam na lafiya yanzu ita babyn zamu sa ta acikin kwalba ne" sunaji suna gani aka tafi da ita suna jira suga an fito da fanan kenan sukaji ihun jama'a a asibitin suna neman taimako , mutane mata da maza se guduwa sukeyi suna ɓuya sude suna zaune kansu yadaure basu san abinda yake faruwa ba , ganin fanan sukayi tafito da gudu daga ita se rigar asibiti hannunta na zubar da jini saboda fincike calular da tayi , dasauri Mr azaad yarikota ganin bata cikin hankalinta yarikota ya na " wifey meyafaru Ina zakije ?" abirkice ta ce " yata zasu kashemin yata habiby " duk ta rudar dasu suna kokarin yin magana sukaga doctor dayatafi da babyn ya shawo kwana da mugun gudu hannunshi dauke da jaririyar gudu yakeyi kamar ranshi zefita ga jikinshi dake zubda jini duk anji mishi rauni , dasauri Mr azaad yasake fanan anty amina tariketa yaje yakarbi jaririyar ahannun doctor din yana tambayar shi meyake faruwa , doctor dake kokarin mutuwa ya ce" wasu azzalumai ne suka shigo wannan asibitin suna kashe mana mutane daga mata masu ciki zuwa kan jarirai dakuma masu shayarwa " yana gama fadin haka yafadi awajan rai yayi halinshi .
Iya tashin hankali sun shiga sunma rasa ɓuya zasuyi ne kokuma komawa gida zasuyi ga shi jama'a ne shaƙee abakin gate din asibitin jami'an tsaron sun hana kowa fita , suma da sauri suka fito compound din asibitin Mr azaad na rike da jaririyar Anty amina tarike fanan baba nadauke da auta akan kafadarshi haka Abba ma yadauki aslam, Fawwaz narike da hannun suhaima da Islam, babu yanda basuyi ba amma jami'an tsaron sunce bazeyu subar kowa yafita ba saboda awajenma ana fuskantar tashin hankalin da yafi na cikin asibitin ko ina se zubar da jini akeyi.
Kuka takeyi kamar ranta ze fita se kallon ahalin nata takeyi ita tasan yau ne ranar tafiyarta domin ayanzu ne zata fara tunkaran wa'yannan azzaluman , Mr azaad ya ce " kuzo muje mu ɓuya awani awajan" dugunzuma sukayi suka fara binshi juyawa yayi yaga fanan na tsaye , abayan su batako daga ƙafarta ba dakatawa yayi ya ce "wifey kizo muje hurry up" duk juyowa sukayi suna kallon fanan da itama su take kallo tana kuka , Abba ma sake mata magana yayi girgiza musu kai tayi tana kuka me tsuma zuciya ta ce " am sorry amma bazan biku ba ni yau ne ranar tawa tafiyar " duk jan burki sukayi lokaci daya zuciyoyinsu yafara bugawa da karfin gaske musamman ma Mr azaad da mama , se yanzu suka tuna da cewa akwai wani babban zaluncin da za'ayi da aranar fanan zata tafi , da gudu Mr azaad yaje gabanta yatsaya ya ce " common on wifey don't be so childish kizo mutafi kinji " girgiza mishi kai tayi ta ce " am sorry habiby amma yau bazaku koma gida tare dani ba " da karfi Mr azaad ya ce " noooo! hakan bazeyuba baby please karki min haka dan Allah karki tafi look at our daughter please kitsaya mu kula da ita tare dan Allah rayuwa zatayi mana zafi dani da ita in bake " yagama magana yana zubewa akan guiwansa agabanta yana kuka ga baby a hannunshi " riko hannunshi tayi ta mikar dashi ta ce" habiby inada full confidence akanka nasan zaka bawa twinkle dinmu dukkan kulawa daya kamata kayafemin inna tabayi maka wani abu sannan in twinkle ta girma ka ce mata ta yafewa mommynta, ta dinga min addu'a" girgiza kai Mr azaad kawai yake yi yana kuka shida ita ta rungume shi.
Kuka su mama sukeyi mama ji tayi zuciyarta na mata zafi sosai kamar ze fito waje ummi na kuka kowa na wajen kuka yakeyi musamman suhaima da zeenat Anty amina mazan ne kawai sukayi dauriya suna me matukar tausayawa Mr azaad, baba kam idonshi yayi ja yakasa cewa komai domin shi kullum dama da haka yake kwana aranshi saboda yasan ko ba jima ko ba ɗa ɗi yasan wannan lokacin na zuwa , Abba hawaye yataru a idonshi.
Fuskantar su fanan tayi tana share hawaye tayi folding hannayenta waje daya ta ce " mamana inasonki sosai amma haka zan tafi in barki kiyafemin sannan kitamin addu'a zantafi yaƙin da bazan dawo ba har abada , baba dan Allah kaima ka yafemin inasanka sosai, ummi kiyafemin kinji ? Abba ka yafemin zanyi kewar kyakkyawar ahalinku kudinga sani a addu'a, ya usman kaima kayafemin zeenat forgive, suhaima kiyafemin sannan ga twinkle nan karki barta tayi kukan maraicin uwa , Anty amina nagode sosai, " haka tadinga bin su tana nemar yafiyar su sannan ta koma kan yaseer ta ce" ya yaseer dan Allah karka bar habiby yashiga wani hali dan Allah ku kulamin dashi sosai karku barshi yayi kewa na sannan ku aura mishi mace ta gari wacce zata mayar mishi da gurbina sannan tazamowa twinkle uwa " dakyar take iya magana saboda kukan da yaci karfinta, sukkansu yanzu mazan sun kasa jurewa kuka kawai suke yi hatta jama'ar cikin asibitin da suka fito domin ceton rayuwarsu hankalinsu yakoma kansu sosai suka basu tausayi .
Mr azaad da ido kawai yake binta ji yayi dama Allah yadauki ranshi ayanzu ko zefi ji raradin dayakeji ya ragu .
Komawa tsakiyar asibitin tayi tana kallonsu suma suna kallonta suna kuka tana kuka , idonta na cikin na Mr azaad da yake kallonta yana girgiza mata kai alamar karta tafi lumshe idanunta tayi hawaye suka biyo baya , bude hannayenta tayi du ka biyu nan take garin yafara hada gagarumin haɗari bana wasa ba, ruwa yafara zubowa a iya inda take tsaye , sabon kuka ne Yakamata dagudu ta nufi Mr azaad dake tsaye hawaye nafita a idonshi dasuka rine tsabar kukan da yayi yakoma kamar Mutum mutumi ƙwakwaran motsi ma yakasa zuciyarshi na mishi tururin zafi, tsayawa tayi agabanshi jikinta na digar ruwa , ɗage ƙafarta tayi ta isoshi a tsaye tasa hannunta duka biyu ta riƙe kanshi idonsu na sarke acikin na juna suna zubar da hawaye bata damu da yawan jama'ar dake wajan ba bata da mu da iyayensu da idonsu ke kansu ba tahaɗe bakinsu waje daya ta fara bashi unforgettable kisses masu zafi , duk wani wanda yake wajen sunkuyar da kansu ƙasa sukayi ganin fanan na mishi kissed din ban kwana , seda tadau minti 20 tana kissing dinshi kafin tasake shi, suna kallon idon juna murya a dashe Mr azaad ya ce " kin tafi kinbar min abu biyu arana daya wanda duk sanda nagani kuma natuna zan tuna ki , kinbar min twinkle dakuma kiss dinki ! baby zan iya mutuwa idan kika tafi daga nan kuma twinkle zata taso a marainiya mara uwa da uba " hawaye na kwarara a idonta ta ce " inka tafi kabar twinkle kuma zafin zemata biyu ka kula mana da ita idan ta girma ta tambaya ina mamarta kace mata ta tafi yakar azzalumai, kafada mata mahaifiyarta jaruma ce data sadaukar da rayuwarta wajan ceton al'ummar Musulmai sannan kullum kafin tayi bacci ka sanar da ita da ina matukar kaunar ta tadingamin addu'a " tana gama fadin haka bata jira abinda ze fada ba ta manna wa twinkle kiss agoshi sannan tasake komawa inda ta haɗa hadarin ruwa yaci gaba da dukanta , daga musu hannu tayi tana musu bye-bye du ka suma hannun suka daga mata suna mata bankwana suna kuka banda Mr azaad da mama da sude kallonta kawai suke iyayi basa iya motsa jikinsu .
Wani irin walkiya akayi me hasken gaske da tsawa nan take ta koma asalin sarauniyarta cikin shiga na yaƙi fuskan nan babu annuri ko rahama ko kadan aciki. Hannunta na rike da bulalar wuta tana jujjuyashi nan take taba ce yazama babu wanda yake ganinta tashiga cikin asibitin ta kashe duk wa'yanda sukazo suna aikata kashe _kashen seda ta kashe su sannan ta bar asibitin ta je sauran asibitocin tana ka kashesu , seda takashe duk wa'yanda tanzarzar ya aiko takuma gyara duk abinda suka bata wadanda suka raunata tayi musu magani suka warke sunayi mata godiya domin bayyanar ta yayi dede domin ta dakatar da zaluncin dasuke aikatawa, komawa medical center tayi sannan tayiwa wa'yanda suka raunata magani , suna nan a tsaye a inda ta barsu ko da ta dawo taimakon mutane tayi bata ko kalli inda suke ba , drygon ne ya sauko ƙasa acikin asibitin nan take jakadiya abashiyya da abdud Shakur suka bayyana suma wajan su mama sukaje suna basu hakuri sannan sukaje wajan sarauniyarsu suka dibi gaisuwa hawa kan drygon ( jegare ) sarauniya tayi yafara firewa da ita akai, duk daga kansu sukayi suna ganin yanda suke tafiya a sararin samaniya tun suna iya hango su har suka ɓacewa ganinsu nan take su jakadiya ma suka ɓace . sake fashewa sukayi da kuka lokacin da suka tabbatar eh dagaske fanan ta tafi tabarsu na har abada yanke jiki mama tayi tafadi cikin tashin hankali suka dagata nurses suka shiga da ita shiga dan dubata .
Mr azaad yana nan awajen da fanan tabarshi beko ƙara koda taku daya ba kanshi na kallon sama kamar wanda yake kallon fanan din Abba ne yazo ya ce " son muje ciki " shuru ba amsa Abba yayi magana yafi baƙi biyar amma ba amsa du ka damuwa sukayi kusa dashi suna mishi magana amma ba wanda yabawa amsa sake fashewa da kuka ummi da zeenat sukayi . " Wifey karki tafi kinga twinkle ma na miki dariya ko tana cewa ina sanki sosai mommyna kalleta kigani " yayi maganar Kamar wani yaro karami yana kallon sama yana kuma kallon twinkle dake hannunshi, Abba ne yasake mishi magana amma amaimakon yabashi amsar maganar dayayi mishi seya sake maimaita " wifey karki tafi kinga twinkle ma na miki dariya ko tana cewa ina sanki sosai mommyna kalleta kigani" tashin hankali suka shiga ganin abinda yake shirin faruwa duk wanda yamishi magana awajan abinda yake maimaita musu kenan , ya nanata wannan maganar yafi sau goma . Dakyar suka iya kwace twinkle ah hannunshi, suka rirrikeshi suka shiga dashi cikin asibitin doctor ƙwaƙwalwa ne yayi mishi hoton kwakwalwar shi nan take result yafito dayake nunawa kancewa yasamu brain problem wato ( Broca's aphasia ) shi wannan matsalar kwakwalwar duk sanda mutum yakamu dashi nanata kalma daya kawai zedingayi ......
🥺😭😭😭 Am typing and also shading tears in pain , nakasa jurewa.
Please 🥺 comments and share fisabilillahi wannan pages din was very heart touching. 🧑⚕️🧑⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺
Story & written by ✍️ MRS 🌹 ISHAM 🌹 (Yar lelen Jarumai)
🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚📚
⚜️📚J. A. W📚🖋️
Gargadi Ban amince wata ko wani yayi amfani da wani sashe daga cikin book din nan ba ta kowani siga ko a karanta a youtube batare da an nemi izini awurina ba ko a hadamun document ko amin edit idan kunne yaji jiki ya tsira koda Allah nabar mutum ze sakamin yabimin hakkina.
PAGE 6️⃣2️⃣
Abba cire hular kanshi yayi dan ji yakeyi komai zafi yake mai suna cikin tashin hankalin da Allah ne kaɗai ze kawo musu mafita dakuma sa musu hakuri azuciyoyinsu amma kuwa sunyi Babban rashi arayuwarsu basaji da akwai wata yarinya dazata iya maida musu gurbin fanan.
Yaseer ne ya ce " doctor yanzu menene mafita ? Kuma tsawon wani lokaci zedauka kafin ya warke?" Doctor ya ce " ya danganta daga yanayin treatment din da majinyacin yasamu ne , mutum ze iya warkewa daga wata uku zuwa wata shidda , amma shi Broca's aphasia cikin biyu ne inhar yadade ajikin mutum be warke ba so , wannan majinyacin ze iya rasa ranshi , yanzu de inhar ana bukatar abashi kulawa na musamman sede kufitar dashi abroad acan ne suke da manyan psychologist cikin yardar Allah Mr azaad ze warke " jinjina kai sukayi cikin gamsuwa da bayanin da doctor ya musu Abba ya ce" mun gode sosai doctor " murmushi yayi ya ce" bakomai akwai doctor dazan hadaku dashi a India babban psychologist ne sunanshi doctor Shankhar " Kiran number doctor Shankhar doctor yayi ya mishi bayanin komai sannan yabawa Abba number nashi , yaseer na rike da little twinkle se kallonta yakeyi wata doctor ce ta shigo tace " yallabai kabani ita angama preparing NICU ( neonatal intensive care unit" din " miƙa mata twinkle yayi yanajin wani irin abu na sukanshi aranshi, haka doctor tashiga da twinkle akasata acikin NICU.
Fawwaz areef dasu ummi na zaune da Mr azaad da kanshi ke kallon ƙasa yayi shuru yazubawa waje daya ido kamar me nazartan wani abu, shigowa Abba da yaseer sukayi tare da doctor din Abba yazauna kusa da Mr azaad ya ce " son katashi mu tafi gida ko " " duk fa maganar da zakuyi bajinku yakeyi ba balle yamaido muku da amsa " cewar doctor,duk zubawa Mr azaad ido sukayi cikin tausayawa ummi ta ce " barin inje wajan mamansu " tafada tana mikewa ɗan bazata iya cigaba da kallon halin da Mr azaad yake ciki ba , bin bayanta zeenat da anty amina sukayi izuwa dakin da aka kwantar da mama, tana zaune akan gadon ta farfaɗo baba,ya usman, hairah, auta, suhaima,hafiz duk suna dakin sunyi ta gumi babu wanda yake iya magana acikin su , shigowa sukayi ummi ta zauna kusa da mama , rike hannun mama ummi tayi ta ce " mamansu hakuri zamuyi saboda me faruwa yarigada yafaru , babu abinda feena take bukata agurinmu sama da addu'a, duk da rabuwa babu dadi amma mu abin alfaharinmu ne yau a ce yarmu tazama jarumar datayi nasara akan azzalumai harkuma takawo ƙarshensu , kuma koda wannan tafiyar nata be rabamu ba to tabbas mutuwa zata rabamu hakuri da tawakƙali shine abinda yakamacemu , itakuma muyi mata addu'ar nasara in kuma munada rabo da sake ganin ta Allah yatabbatar da ikon sa" maganganun Ummu sun ratsa mama sosai ajiyar zuciya tayi kafin ta ce" ina Azaad ?" ummi ta ce" son yasamu matsalar kwakwalwa yanzu haka anfara shirye shiryen fita dashi India twinkle kuma ansata acikin kwalba " wani hawayene me zafi yazubo a idon mama jin Mr azaad yasamu matsala a brain dinshi, jikarta kuma tana cikin kwalba.
Haka wa'yannan ahali biyun suka tashi daga happy family izuwa sad and broken family, haka gidaje biyun nan suka rasa duk wani walwalarsu da farin cikin su , cikin kwana biyu aka gama shirya tafiyar Mr azaad , Abba da Fawwaz se yaseer ne zasu tafi dashi mama ma an sallameta sun koma gida , kusan kullum ummi da zeenat suna zuwa gidan . Suhaima kuma ta roki Fawwaz akan yabarta tadanyi kwana biyu agida tare da su mama , kuma ya amince da hakan.
Suna zaune a falo kowa yayi shuru ko wannensu da abinda yake saƙawa a zuciyarshi , Mr azaad na kwance akan kujera kanshi akan cinyar ummi , da gudu Hafiz yasauko downstairs Abba ya ce " Hafiz lafiya kuwa" sa hannu yayi ya dauki remote kafin ya ce " bakuga labaran yau ba? Ko ina maganar anty fanan akeyi " ya karishe maganar yana kamo tashar BBC Hausa duk mayar da hankalinsu kan tv sukayi banda Mr azaad dabemasan meye sukeyi ba balle yasan me suke fada.
Video ne da CCTV Camera yadauketa na duka asibitocin da taje ta taimaka musu da kuma short video lokacin da suka rungume juna itada Mr azaad ga kuma twinkle dake hannun Mr azaad, se playing din videos din akeyi again and again aƙasa a rubuta 'the warrior ' wani journalist yafara kwararo bayanai " wannan dakuke gani ita ce Jarumar da ta cece rayuka bila adadi, kwana biyu dasuka wuce wanda a wannan ranar ne muka tashi da tashin hankali mara misiltuwa , kamar yanda kuka gani a wannan dauka na CCTv camera ita ce ta cece jarirai da ake kokarin kashewa da kuma mata masu ciki da masu jego, dama ako ina Allah baya taba goyon bayan zalunci shisa yaturo mana da wannan baiwar Allah. Allah yashiga tsakanin mu da mugaye azzalumai yayi mana tsari dasu itakuma Allah yabiya mata bukatunta na alheri yabata Sa'a akan abinda tasa gaba, ya Allah ya kare ta aduk inda take , ƙasa Nijeriya dakuma ƙetare we're very proud of her she's our superstar warrior. Yanzu zakuji daga bakin wa'yanda suka kasance sheda na gani da ido, sune wa'yanda suke cikin asibiti abin yafaru " magana wani magidanci yafara " sunana Abubakar lawan . wato abinda yafaru shekaranjiya tabbas ni ganau ne ba jiyau ba domin nakai matata haihuwa ne wannan lamarin ya rufta damu a asibitin wannan baiwar Allah ita ta cece jaririnmu dakuma matata bazan taba mantawa da ita ba kuma , itadin matace ga azaad the billionaire sannan sirka ga ahalin mainasara, yanda ta taimaka mana Allah ya taimaka mata ya shige mata gaba aduk lamuranta " haka sauran da aka gayyato suka dinga fadar irin aiyukan da fanan tayi da taimakonsu datayi, haka aka dinga hasko hotunan fanan ta ko Ina yazamana labarinta akeyi , ko ina aka waiga jama'a se addu'a sukeyiwa fanan manya da yara, kowa se bashi dama akeyi yana fadan ra'ayinsa dangane da fanan kowa alkharinta kawai suke magana . Duk jikinsu yayi sanyi ganin irin yanda al'umma tun yanzu sunfara alfahari da fanan ko ina yabonta akeyi , guntun hawayen da yazubowa ummi ne tasa hannu ta share , Abba ya ce " Allah mungode maka " tashi yake kokarin yi idonshi yasauka akan video fanan da ake nunawa a tv asukwane yakarasa tashi yanufi tv da gudu yasa hannu yana shafa " wifey kalleni , ki kalleni wifey kizo mu tafi gida kinji " dasauri suka bi bayanshi zuwa wajan tv ganin yanason birkicewa lokaci daya, dukan tv yakeyi da iya karfinshi wai anashi tunanin yanason yafito da fanan din ne dake cikin tv ,dunkule hannunshi yayi ya bugawa tv wanda seda yayi sanadiyar wargajewarsa raga_raga rikoshi Abba da Fawwaz sukayi yanata sambatu yana kiran sunan fanan, su biyu suke rike dashi amma sun gagara mishi rikon da baze kubce ba ,fisgewa yayi yahaura upstairs da gudu yashiga part dinshi yarufe yasa key .
Yaseer ko magana ya kasayi yana zaune yayi tagumi abin duniya yadameshi ganin yanda babban amininsa da bayida kamarshi yana cikin wani hali, hawaye yataru a idonshi. Ummi kam izuwa yanzu bata iya controlling din hawayenta idonta sunyi ja sosai, daga ranar da fanan ta tafi izuwa yanzu kullum a cikin kuka suke da damuwa.
Haka abangaren su mama duk suna kallon labarai da suke yawo a gidajen rediyo da kuma social media, murmushin takaici kawai mama tayi aranta tanayiwa fanan addu'a.
Yau Flight dinsu Mr azaad yatashi zuwa kaishi India suka sauka a asibitin Narayana superspeciality hospital babban asibitine a India da babu kamarshi komai nasu na musamman ne , babban part aka bawa Mr azaad acikin asibitin aranar da sukazo a ranar doctor Shankhar yafara dubashi . Bayan kwana uku Abba ya koma Nigeria, Fawwaz da yaseer ne zasu zauna tare dashi.
Acikin wata daya duk sun rame amma damuwar dasuke ciki yadan ragu dukda bawai yafita azuciyoyinsu bane kawai suna dannewa ne domin sunyi tawakƙali. Duk bayan sati daya se sunkaiwa little twinkle visit a asibiti suna kallonta acikin kwalba haka ma suna kaiwa Mr azaad visit duk sanda sukaje sesunyi kuka , acikin dakin dayake ko ina yayi bi bangon yazana hoton fuskan fanan da yana kallo shi kadai za'a ga yana magana, amma yanzu abun da sauki.
NASMINAYA.
Tafiya takeyi cikin izza da mulki hade da jarumta, tana sanye da doguwar riga yellow color kanta dauke da crown ( hular sarauta) din sarauta, rigar yanaja abaya kuƴangu suna rike mata da bayan rigar domin yana da tsayi sosai , jikinta tako ina tasha ado da zinari, fatar jikinta se yalki yakeyi da idanunta , gashin kanta yana abaje shima an mishi kwalliya da gold sosai tayi kyau , fuskanta babu ko da alamar murmushi. Tunda suka nufo hanyar fa da ake mata bushen sarewa duk inda ta wuce se an sunkuya an gaisheta sannan bazasu tashi ba seta wuce tukun zasu iya mikewa , tana shigowa fa da duk suka zube akan guiwowinsu suna ɗiɓan gaisuwa agun babban sarauniya, zama tayi akan kujeran mulkin da aka ƙawa tashi da lu'ulu'u ta ɗaura ƙafarta daya kan daya daga musu hannu tayi alamar ta karbi gaisuwar sannan suka koma suka zauna , manyan sarakunan aljanu ne takowa ni bangare sunzo ne domin yi mata barka da zuwa , agefenta kuwa akwai kujeran gimbiya afroza da na yarima ahil se kuma na manya masu muƙami a nasminaya irinsu galadima abdud Shakur da jakadiya da sauransu , tashi sukayi suna gabatar mata da kansu , haka ranar sukayi shagali sosai domin farin cikin dawuwar sarauniyarsu abin sonsu.
AFTER THREE MONTHS
Gangarowa zeenat tayi daga upstairs tadan rame ga cikinta da yafara fitowa tana " ya areef wai kai da Hafiz baku gama bane nifa nashirya dan Allah kuzo mu tafi kunga su Abba sun riga da sun tafi " tayi maganar tana saukowa daga staircase din , areef ya ce " muje mungama muma" fitowa sukayi zuwa packing lot suka shiga motar areef yayi driving dinsu zuwa medical center. Ciki suka shiga ɗan karasawa inda su ummi suke , samunsu sukayi suna rike da baby a hannunsu se wasa sukeyi mata tasha hadaddun kayan baby Pink color , suna cikin farin ciki da sauri zeenat ta isa inda suke tsaye din ta ba ta fuska ta ce " amma ai bahaka mukayi ba , Ni ce fa nace aduk sanda akazo daukan twinkle I will be the first person to carry her amma yanzu kun bata min Abinda nake matukar jira" du ka dariya sukayi jin maganar da zeenat tayi Abba ya ce " to zee yanzu ma ai gata nan " miƙa mata twinkle ummi tayi ta karbeta tana washe fuska se kallonta takeyi, fuskar fanan sakk take gani ana twinkle tsabar yanda kamanninsu yaɓaci sede fatar Mr azaad ne da ita , idonta arufe hannunta na cikin bakinta tana tsotsa hawayen da yazubo daga idon zeenat ne yasauka akan kumatun twinkle mutsu_mutsu tafarayi kamar zatayi kuka taname bude idonta kadan sannan ta rufe , zaro ido waje zeenat tayi lokacin dataga kalar idon twinkle da karfi ta ce " laaah kuga ikon Allah idonta brown color ne irin na kaka me martaba " zubawa twinkle ido sukayi suna jiran suga ta bude idon nata aikuwa tasake budesu , tabbas idonta iri daya dana me martaba shi ta gado a kwayar halittar ido kenan sannan natama yafi nashi nata brown ne sosai , haka suka koma gida cike da farin ciki bayan awa daya zuwa biyu su suhaima sukazo ganin baby amma banda mama da baba . Baby girl gata nan yar lukuta da ita ga farin fata se karbanta sukeyi suna santin jaririyar sunayi mata photos suna turawa Fawwaz da yaseer da suke India su kansu sunyi farin ciki , adaren ranar me martaba da Fulani sukazo ganin jaririya aka tsayar da ranar suna nan da sati daya.