Noor al hayat complete by khaleesat - Chapter 53
Noor al hayat complete by khaleesat Chapter 53: Noor al hayat complete by khaleesat Chapter 53. A hankali khadijah ta koma ta kwanta, bata kara minti biyar…
5,114 words
A hankali khadijah ta koma ta kwanta, bata kara minti biyar ba bacci ya dauketa. Da asuba tana jin fitansu tare da Shureim xa su masallaci, ita ma ta mike ta shiga bayi, tana xaune kan darduma tana azkar taji shigowarsu gidan, bude kofar dakinta Aliyu yyi suka shigo tare da Shureim, kallo daya tayi masu ta dauke kai, ya xauna gefen gado Shureim ya nufe ta ya durkusa gabanta yace "Anty ina kwana?" Tana kallonsa tace "How was ur nyt?" Ya wara ido yace "It was cool Anty" Bata ce komai ba ta saci kallon Aliyu suka hada ido, d'an murmushi yayi a hankali yace "Good morning Iman" sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba, ya mike ya nufi kofa Shureim ya bi bayansa da sauri ta bi su da ido har suka fita, ta fi minti ashirin xaune ganin gari ya fara washewa ta mike, tana sane jiya babu abinda tayi a gidan, yau kam ta sauka parlor ta share ko ina ta goge, ta shiga kitchen ma ta gyara ta goge, tana kokarin sa turaren wuta a burner aka danna bell, mikewa tayi tana kallon kofar, ta wuce sama da sauri don dauko hijab ta dawo ta bude, Baby ce tsaye da breakfast, Khadijah ta langwabar da kai tace "Don Allah daga yanxu kar ki sake kawo abinci xan yi girki muna ba Mumy wahala..." Baby ta wara ido sai kuma tayi dariya tace "Xa dai ki girka abinda xa ki ci, tunda nasan ba bama yayana xa ki yi ba, yaron ki kam nasan shi ma xa ki basa, Abbansa dai ne baxa a bai ma ba" tabe baki khadijah tayi ta bata hanya ta shigo ta ajiye abincin nan parlor tace "Da fatan kun tashi lafiya, yau naga har da su gyare gyaren gida meye sirrin Iman?" Tana murmushi da tsigar tsokana ta kare maganar, khadijah ta hade rai tace "Wani irin sirri?" yar dariya Baby tayi tace "Oho, ni dai xan wuce, a gaida min yayana" Daga haka ta nufi kofa khadijah ta bi ta da kallo har ta fita sannan ta tabe baki, ta koma ta ci gaba da abinda take, dinning ta kai breakfast din ta ajiye sannan ta wuce sama ta shiga daki, nan ma ta gyara gadonta tayi goge goge kafin ta shiga wanka, tana xaune gaban mirror bayan ta fito wanka tana shafe shafe aka bude kofar bedroom din, xaro ido tayi tana gyara towel din jikinta, ganin Shureim ne ya shigo ta sauke ajiyar xuciya, ya iso kusa da ita yace "Anty am hungry" tace "Me ya hana uncle din baka breakfast" Ya buda hannu yace "He told me I shud come to you ki bani" Tana shafa mai a kafarta tace "Shi me yake yi?" Shureim ya matso cream din xai shafa mata ta 6alla masa harara tace "Ina wasa da kai koh?" Ya mike yace "Anty taya ki xan yi" toes dinta ta mika masa tace "Toh shafa a nan" ya durkusa yana shafa mata tace "Tambayar ka nayi me uncle din yake?" Ya kalleta yace "He is lying down" shiru tayi bata ce komai ba, a hankali yace "Anty yace min he is not feeling fine" Kamar baxa ta ce komai ba sai kuma tace "What's wrong with him" Yace "I don't know" Tace "Je parlor ka jira ni in sa kaya sai in xo in baka breakfast" yace "Toh" sanann ya fita dakin, mikewa tayi ta dau atamfar da xata sa na riga da skirt, sosai dinkin yayi mata kyau tayi simple dauri na dankwali ta sa eye pencil a idonta sai chapette ah two colored lips dinta, sosai tayi kyau, ta fesa turare daga karshe ta fita dakin, har xata sauka stairs sai kuma ta tsaya, ta fi minti biyu tsaye kafin ta karasa kofar dakinsa a hankali ta bude, kwance ta gansa ya rufa da duvet har kansa, ta sauke idonta kasa ta karasa dakin kamar mai counting steps dinta, tana ta tsaye kusa da gadon tana kallonsa, a hankali ta durkusa dab da shi ta cire duvet din fuskarsa, idanuwansa a lumshe suke, ta kai hannu forehead dinsa, lkci daya ya bude idonsa tayi saurin dauke hannunta ta koma baya, kasa tashi tayi kuma bata yarda sun kara hada ido ba ta fara kame kame, kallonta kawai yake, ta dago daga karshe tana kallonsa a hankali tace "Are you sick?" Ya mike xaune yace "No.... am alright" shiru tayi tana kallonsa, ya sauka daga kan gadon ya nufi bayi ta bi sa da kallo don kana ganinsa kasan karfin hali yake yi, Mikewa tayi a hankali ta nufi kofa ta fita dakin, kwance ta ga Shureim ya kunna cartoon yana kallo parlorn yana ganin ta yyi saurin kashe tvn da remote din hannunsa, ta tsaya tana kallonsa tace "Who asked you to switch on the tv?" Shiru yyi yana kallonta, ta wuce dining ta hada masa shayi a cup ta debar masa dankali da kwai da plantain, sannan ta yankar masa bread karami ta daura gefen plate din Irish din, tace "Zo ka xauna nan Shureim" ya taso ta ja masa kujerar dinning din ya xauna ta ajiye masa abincin a gabansa sannan ta koma kitchen ta dauko wani cup din ta dawo ta hada wani shayin, ta debi Irish da kwai a plate, ta dauko wani bowl ta xuba pepper soup na kayan ciki, gaba daya ta daura su kan tray ta dauka ta wuce sama, a hankali ta tura kofar dakin nasa, xaune ta gansa gefen gado ya rike kansa, jin an bude kofa ya dago yana kallonta, kanta a kasa ta iso har kusa da shi ta ajiye tray din ba tare da ta kallesa ba ta mike ta fita dakin. Dining ta koma gun Shureim ta xauna kujerar kusa da na shi ita ma ta hada shayin, a hankali take sha har ta gama, tuni Shureim ma ya gama ya mike pleadingly yace "Anty plss in kunna tv?" Kai ta gyada masa ya juya ya wuce parlor, ta kwashe duk abinda suka bata ta kai kitchen ta wanke sannan ta fito, sama ta wuce ta bude bedroom din Aliyu, kwance ta gansa ya kara rufa da duvet, ta karasa tana kallon breakfast da ta ajiye masa, Bata san lkcn da ta xauna gefen gadon ta yaye duvet din tana kallonsa da damuwa tace "Baka yi breakfast din ba? What's wrong with you?" Ganin bai bude ido ba kuma bai ce komai ba ta kamo hannun sa da damuwa tace "Talk to me plss" bude ido yyi ya mike xaune, ta dauko cup din shayin da ta rufe ta bude tana mika masa tace "Gashi ka sha sai ka sha magani" karba yyi xata dauko plate na irish ya dakatar da ita "Noo I will take this first" da kyar yyi maganar, ta dago tana kallonsa ya kai shayin baki kamar wanda xai sha magani, kadan ya kurba ya cire a bakinsa, tace "Da zafi ne?" yana girgixa kai ya mika mata, ta hade rai tace "Me xan yi da shi?" Xai ajiye kasa tayi saurin cewa "Kar ka ajiye shi, u better force ur self to drink it..." Bai saurareta ba ya ajiye ya mike ya nufi bayi da sauri, a sanyaye ta mike bi sa da kallo, tana ta tsaye ita dai bata ji yana amai ba kamar ynda tayi tunani, can dai ta bi bayansa, jingina tayi da kofa tana kallonsa ganin aman yyi har ya wanke wajen, ya juyo xai fita bayin ta rikesa a hankali tace "Let me make you water sai kayi wanka" yana gyada kai yace "Finish first" daga haka ya fita, ta hada masa ruwan ta fito, kwance ta samesa ya kara rufe kansa, ta cire duvet din da damuwa tace "Kayi wankan sae mu je asibiti" da kyar ta samu ya mike xaune, tana ta kallonsa ganin har rama yyi, sauka yyi daga kan gadon ya cire jallabiyar jikinsa ta amsa ta ajiye sannan ya wuce bathroom, sai a sannan ta fita dakin a sanyaye. zaunawa tayi gefen gadonta tayi tagumi bayan kusan minti talatin ta tashi ta koma dakinsa, dai dai lkcn ya fito wanka daure da towel, tayi saurin juyawa kamar mai neman abu sai kuma ta fita dakin, turo baki tayi ta sauka downstairs ta tadda Shureim yana ta kallo ta xauna kusa da shi. Jin alamar Aliyu na sakkowa stairs ta kalli direction din, kananun kaya ne jikinsa yana rike da makullin mota ya iso parlorn, ta mike tana kallonsa tace "Where are you going to?" Bai ce komai ba, ya nufi kofa, ta isa gabansa ta hade rai tace "Nace ina xa ka?" Ya ki kallonta yace "To get drugs" kwace makullin hannunsa tayi tace "Let me do the driving" Daga haka ta nufi stairs ya bi ta da kallon gefen ido, mayafi karami ta dauko a daki ta rataya a wuya ya dinga kallonta, ganin ta nufi kofa yace "Iman!!!" juyowa tayi tana kallonsa, yana nuna mayafin kanta yace "Haka xa ki fita?" Kallon kanta tayi daga sama har kasa tana masa wani kallo tace "So?" Kallonta kawai yake bai ce komai ba, ta hade rai ta dawo ta damka masa makullinsa tace "Sai ka ja motar, ka tafi inda xaka" Komawa tayi ta xauna ya bi ta da kallo kafin ya fita parlorn, turo baki tayi jin yana warming mota ta mike ta wuce sama ta dauko Hijab dinta ta sa ta sakko parlor, kashe tv tayi tana hararan Shureim da duk hankalinsa gaba daya na kan kallo as if his life depend on it, ya mike da sauri yana kallonta yace "Anty ina xa ki je" Bata tanka sa ba ta nufi kofa ya bi bayanta, Tun daga nesa Aliyu ke kallonsu daga cikin motarsa ko kiftawa babu har suka iso ya dauke kansa, Ta hade rai tace "Ka koma daya side din" D'an murmushi yayi ba tare da ya kalleta ba ya fito ya koma daya bangaren Shureim na biye da shi a baya, yaron ya bude back seat ya shiga, shi kuma ya xauna front seat, ta shiga maxaunin driver, sabon mai gadi dake bakin gate ya bude gate din ta fita da motar, a hankali take driving din har suka hau saman titi, kamar ana tilastata tace "Wani pharmacy?" Gaya mata yyi idanuwansa a kan titi, kira'ar sheikh Sudais kadai ke tashi a motar in a very low tone, yace "Who taught you how to drive" Bata ce komai ba har suka iso pharmacy din, sai a sannan ta kallesa a takaice tace "A Good Samaritan taught me" Bai ko kalleta ba ya bude motar yayi wucewarsa, ta bi sa da wani kallo, Shureim yace "Anty, Uncle ba shi da lafiya koh" Bata ce masa komai ba, Bayan kusan minti goma Aliyu ya fito rike da ledan drugs ya shiga motar, ganin hanyar da ta dauka, yana kallonta da kyau yace "Ina xa ki je?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Xan je gida in dauko ma Shureim wears dinsa" "Noo, mu wuce gida, xan je da kaina in amso masa ba sai kin je ba" A hankali take ta tafiya da motar shi dai bai kara ce mata komai ba, can ta turo baki ta dau hanyar gida... Tana gama parking ya bude motar ya fita ya bude back seat ya fiddo Shureim suka wuce ciki ta bi su da kallo, Babu kowa parlorn da ta shigo, ta ajiye makullin hannunta ta wuce kitchen, Cup din tea ta hada ta fito ta haura sama, bude kofar dakinsa tayi ta gansa xaune yana ballar drugs shureim sai surutu yake masa, ta ajiye masa shayin gabansa ta fita, dakinta ta shiga ta kwanta, Bata san lkcn da bacci ya dauketa ba kawai taji hannu a fuskarta ta bude ido a hankali, lkci daya ta mike xaune tana komawa baya tana kallonsa tace "What?" yace "Kin yi baki downstairs" Ta d'an buda ido tace "Su wa?" Ya mike yace "Suna jiran ki" daga haka ya nufi kofa tace "Shine baxa ka turo Shureim sai ka xo kana wani taba min fuska" har ya fita bai juyo ba balle yace komai, tashi tayi ta gyara daurin dankwalinta ta bi bayansa, Tsaye tayi stairs din karshe tana kallonta ko kiftawa babu. Suka hada ido da Khaleel dake jujjuya makullin motar hannunsa, saurin sunkuyar da kanta tayi, ta karasa shigowa parlorn kanta a kasa, haka kawai taji wani mugun kunyarsa take ji, ta xauna kan kujera taki kallon Jawahir, Khaleel yace "Good afternoon khadijah" Ba ta dago ba tace "Ina yini" ya d'an yi murmushi yace "Lafiya lau, how are you" Bata ce komai ba, Jawahir tace "Ya gidan khadijah" sai a sannan khadijah ta kalleta, Jawahir ta sauke idonta a hankali, Khadijah tace "Alhmdllh" Khaleel yace "Ta ce in kawo ta ku gaisa...." Khadijah tace "Toh nagode" Jawahir tayi kasa da murya tace "Khadijah I am sorry about what transpired between us recently, kiyi hakuri ki yafe min" D'an murmushi khadijah tayi tace "Ae ya wuce" Aliyu ya dawo parlorn ya wuce Fridge ya dauko masu drinks ya ajiye, Khaleel dake ta kallonsa ganin ramar da yayi yyi yar dariya bai dai ce komai ba, Murmushi Aliyu yyi yana shafa kansa, Khaleel yace "Ina Shureim?" Aliyu ya xauna kujera yace "He slept off minutes ago" Khaleel yace "Alryt then, dama madam na kawo, I think we will be on our way now, but before then Ina son xa muyi magana da kai..." Aliyu ya mike yace "Alright" a tare suka fita parlorn, Jawahir ta dawo kusa da khadijah tace "Da gaske kin hakura khadijah?" Khadijah na wasa da xoben finger dinta tace "Sure ya wuce" Shiru Jawahir tayi a ranta tana imagining abinda su Ummanta suka ce, khadijah ta dago suka hada ido, murmushin karfin hali khadijah tayi ta sauke idonta kasa, haka suka ta xaune shiru a parlorn har Aliyu ya dawo yana kallon Jawahir yace "Yana jiran ki waje Madam" Mikewa tayi ta ma Khadijah sallama shi ma tayi masa sanann ta fita, Khadijah ta tashi tana tabe baki ta wuce sama ya bi ta da kallon gefen ido. Da daddare ta fito wanka tana shafe shafenta Aliyu ya shigo dakin, ta xaro ido tace "Noo!! you can't just come in without...." Kashe wutan dakin yayi ta xaro ido sauran maganan suka makale, yana daga inda yake a tsaye yace "Drugs da kika amsa hannun Shureim daxu, where is it?" Tace "Ka tafi xan kawo maka" a d'an fusace tayi maganan, yayi murmushi ya tako a nutse har inda take, duk da duhun dakin hakan bai hanata ganinsa ba ta dinga komawa baya a tsorace tace "Aliyu meye haka..." Xata gudu ya rikota sai jin ta tayi jikinsa, lkci daya jikinta ya dau rawa ta dinga kokarin kwace kanta amma yaki saketa, Babu abinda ke mata yawo a memory dinta sai incident din Shekaru bakwai da suka wuce, lumshe ido yyi jin yanda ko ina na jikinta ke rawa, murya can kasa yace "Ki gaya min abinda ke xuciyar ki game da ni Iman.... Tell me what u are thinking of me" Ta fashe da kuka tace "I beg you ka sake ni, you are making me...." Bai bari ta kai karshe ba ya hade bakinsu..... Bai xame ko ina da ita ba sai kan gado, ta kwace bakinta jikinta na bari tace "Nooo plss Aliyu, wllh ka bari bana so.... Kana son xuciya na ya fara min ciwo ko" Murya can kasa yace "I will cure it..." Toshe bakinta yayi jin xata fara masa ihu, Sallamar Shureim bakin kofar dakin ya sa shi saketa da sauri, da ta samu ta sauka kan gadon bata xarce ko Ina ba sai bayi ta rufe kofar jikinta na 6ari, Aliyu ya mike tsaye yana kallon kofar ya kunna wutan dakin sannan ya bude, Wayarsa Shureim ya mika masa yace "Uncle Mumy tana kiran ka tun daxu" Ya amshi wayar yace "Are you done with the game?" Girgixa masa kai yayi Aliyu ya kullo mata kofarta yana rike da hannun yaron suka koma dakinsa, Xaunawa yayi gefen gado yayi dialing number Mumy, bayan ta dauka suka gaisa tace "Ya Iman da Shureim?" Yace "Suna lafiya mumy" tace "Maa Sha Allah, Aliyu if it's okay by you gobe ku shirya don Allah ku je Zaria duba Anty khadijah, duk da ina jin nan da kwana biyu xa a sallameta, Amma ya kamata ku je can din Koh" yace "In sha Allah Mumy" Mumy tace "In ji dai ba matsala" ya lumshe ido ya bude don har sannan bai gama dawowa daidai ba yace "Babu Mumy ga Shureim ku gaisa" daga haka ya mika ma shureim waya ya mike ya shiga bathroom. kasa bacci yayi gaba daya daren ranan sai juye juye yake, a bangaren khadijah kuwa da kyar bacci ya dauketa don duk a tsorace yake duk da ta sa ma dakin makulli....
Washegari da safe karfe bakwai khadijah ta ji fitan Aliyu da mota, mikewa tayi ta fito tana mamakin inda xa shi da sassafe, ta bude kofar dakinsa ta ga Shureim kwance yana bacci, rufe kofar tayi ta koma dakinta, sai bayan da tayi wanka ta sa wata doguwar riga mara nauyi sannan ta sauka downstairs don tsaftace gidan, kafin karfe takwas da rabi ta gama komai, tana kokarin sa turaren wuta aka bude kofar parlorn, da sauri ta juya ganin sa ta dauke kai, ya karaso ya ajiye jakar hannunsa da Breakfast din su yana kallonta ta ki juyowa, bai ce mata komai ba ya wuce sama, sai a sannan ta mike ta isa gun jakar ta bude ta ga kayan shureim ne a ciki, ta rufe a hankali ta koma daki ta dau wayarta, ta fi two minutes tana kallon wayar kafin ta turo baki tayi dialing number Umma, Umma na dagawa tace "Fatan kun tashi lafiya Daughter" a hankali Khadijah tace "Umma shine baki kira ba koh?" Umma tayi murmushi tace "Toh ke ba gashi kin kira ba yanxu, ya grandson dina?" Khadijah tace "Yana lafiya" Umma tayi kasa da murya tace "Kiyi hakuri da abinda kika gani kin ji khadijah hakan kadai ne rufin asirin ki, and I am sorry for hiding that from you ban san yanda xaki dau hakan ba shi yasa..." Khadijah ta ji hawaye ya kawo idonta ta rasa abinda xata ce, Umma tace "Soon xa ki fahimce gata mu ka maki, nasan ki da taurin kai khadijah don Allah ki ajiye makaman yakin ki ki rungumi mijin ki ki manta komai, a role dina na matsayin mahaifiya a gare ki nake baki shawarar ki daina riko ba shi da amfani khadijah, wllh na tabbata son da Aliyu yake maki baxai misaltu ba da dadewa na gane haka, ke kam ba lallai ki gani ba tunda kin sa ma kanki k'in sa saboda kaddarar da ya faru tsakanin ku, Wai ma in tambaye ki... Tunda kike kin taba ganin wanda yayi ma mace fyade ya damu kamar yanda Aliyu ya damu? Ko akwai it's very rare in today's world khadijah, sure from the beginning Barrister Sudais ya xame maki wani Haske a rayuwar ki, ya haskaka maki rayuwar ki, abinda kuma baki sani ba shine, bar ma Aliyu auren ki da Barrister yayi duk cikin haskaka maki rayuwa ne coz Aliyu is the best husband for you duba da irin duniyar da muke ciki a yau, shi kadai xa ki aura ki samu kwanciyar hankali da nutsuwa ku xauna lafiya tare da d'an ku, shi yasa ya hakura ya bar masa ba don baya so ba, Kuma ya tabbata Aliyu xai daura daga inda ya tsaya, Barrister abun girmamawa da mutuntawa ne a gun ki khadijah, kinga Babu abinda bai maki ba don tabbatar da Haske a rayuwar ki, and Dr Ayman nasan shi ma har abada baxa ki mance shi ba don ya maki abinda mahaifin ki bai maki ba yana da rai, duk da nima na so kwatanta hakan amma babu dama, ban kuma san ta inda xan fara ba, don haka mutanen nan biyu babu da abinda xa ki iya biyansu sai dai kullum ki masu addu'ar gamawa da duniya lafiya, Allah ya ba ku xaman lafiya my daughter...." a sanyaye khadijah tace "Amin Ummata nagode" Umma tace "Maa sha Allah, my regards to both father and son" d'an murmushin karfin hali khadijah tayi daga haka ta katse wayar dai dai shigowar Aliyu dakin, kin kallon direction dinsa tayi, yana kallonta yace "We are going out anytime soon, ki shirya, and am hoping kin ga breakfast downstairs..." sai a sannan ta kallesa ta daure fuska tace "Xuwa ina?" Yace "Idan mun fita xa ki gani" daga haka ya juya ya fita, komawa tayi ta kwanta kan gado duk jikinta a sanyaye daga maganganun da Umma tayi mata, ta kusa minti talatin kwance Shureim ya shigo dakin da sallama, tana kallonsa har ya karaso kusa da gadon yana ta xuba kamshi, yana murmushi yace "Anty ina kwana" tace "How was ur night" yace "Alhmdllh" tace "wa ya maka wanka?" Yace "Uncle, Anty we are going out yace in kin shirya ki fito, muna jiran ki" ta hade rai tace "Kayi breakfast ne?" Yace "Eh mun yi da uncle" ta mike xaune tace "Toh ni ce baxan yi breakfast din ba xa ka wani ce kuna jirana" Tsayawa yyi yana kallonta, Aliyu ya bude kofar dakin, sanye yake da shadda milk color, lkci daya kamshinsa ya cika ko ina na dakin, yana kallonta yace "Iman, ke nake jira" Ta kallesa tace "Ku kunyi breakfast ni kuma sai in fita haka?" Ya daga kafada yace "Nobody stopped you from Breakfasting...." Tashi tayi tsaye ta nufi kofa kamar xata tashi ta bi gefensa ta fice dakin ya bi ta da kallon gefen ido kafin yayi murmushi, Shureim yace "Uncle da mun kawo mata nata daki koh?" Karasowa yayi yana murmushi ya xauna gefen gadon ya dafa kafadan yaron yace "Ko mun kawo mata cewa xata yi who sent us..." Shureim yayi dariya yace "Uncle but why is she even angry, ko bata son gidan nan ne, or she don't want you to leave with us?" Murmushi kawai Aliyu yayi yana shafa sajensa a hankali yace "I don't know also, amma ka tambayeta" ya xaro ido yana yar dariya yace "Xata doke ni ne" rungume sa Aliyu yyi a hankali yace "Not when am around darling" Suna ta xaune dakin har ta dawo, Bata yi xaton xata samesu a ciki ba, Bata rufe kofar ba tace "Can you both excuse me" Ya kalli Shureim yace "Tafi downstairs gani nan xuwa nima" fita yaron yyi a dakin, khadijah ta xaro ido tace "Cewa nayi both..." yana murmushi yace "Ni ba mijin ki bane xan yi excusing din ki?" ta daure fuska tace "Ni dai ka fita xan canxa kaya" Yace "But am not stopping you Iman" ya kalli agogon wrist dinsa yace "Kina ta bata mana lokaci kuma da nisa xa mu je" Tace "Toh ka fita, ko kuma in fasa xuwa" Yana kallonta kamar mai counting word din yace "I.. am.. going.. no where!" Wani kallo ta dinga masa, lkci daya ta nufi can karshen gado tayi kwanciyar ta ta juya masa baya, murmushi yayi ya hau saman gadon tana ganin haka tun kan ya matso kusa da ita xata tashi yyi saurin cafkota, Kamar xata yi kuka tace "Don Allah Aliyu ka bari, bana so, to nace ka fita in sa kaya ka ki fita, ya xanyi?" Sosai xuciyarta ke bugawa tana kallonsa, ya jawota jikinsa a hankali ya kai bakinsa wuyanta murya can kasa yace "Me yasa xan fita, what is it that u are hiding" turasa tayi da karfi tace "Stop it Aliyu.." Ya dago yana kallon idanuwanta yace "Really?" Jin yanda muryarsa ya canxa ta hadiye wani abu da kyar tace "Alryt, since you are not going na ji xa sa kayan haka, sake ni" a hankali ya saketa yana kallonta, sauka tayi daga kan gadon ganin inda ta nufa da gudunta ya mike da sauri ya riga ta isa kofar ya sa makulli yana kallonta, juyawa tayi kamar xata yi kuka tace "Me yasa kake min haka don Allah" ganin irin kallon da yake mata da lumsassun idonsa ta koma gun kayanta ta fiddo wanda xata sa kamar xata yi kuka, bathroom ta nufa ya bi ta, ta tsaya bakin kofar pleadingly tace "Don girman Allah ka bar ni in sa kaya Aliyu, Kai fa kace ina bata maku lokaci... " bathroom din ya shiga ya jawota xata yi ihu ya sa makulli yace "Ki sa a nan tunda kina kunyar sa wa a cikin dakin" Bata fuska tayi tace "Ni wllh bana son abinda kake min..." Ya amshi kayan ya daura kan washing machine yace "Let me help you" Bai jira cewarta ba ya jawota lkci daya ya sauke doguwar rigar jikinta idonsa ya sauka kan tabon Cs dake cikinta, tayi kara a rikice ta durkushe wajen jikinta na rawa, dagota yayi yana kallonta a sanyaye ko kiftawa babu, ta dinga nonnokewa tana cewa "Don girman Allah ka bari Aliyu, wlh kunya nake ji" a hankali ya saketa yace "Toh sa kayan ki" jikinta na bari ta dau skirt din atamfar da sauri ta sa, sanann ta dau rigar ma ta saka, ya jawota jikinsa ya ja mata zip din rigar a hankali, ta kasa kallonsa, dago kanta yayi a hankali, ta rufe idonta da sauri, yayi murmushi yyi mata light French kiss, a rude ta bude idonta ya saketa ya bude kofar ya fita bathroom din, da kyar ta fito daga karshe duk jikinta ya mutu, Kasa shafa komai tayi a fuskarta ta sa turare da hijab kawai ta sakko downstairs, yana xaune parlorn Shureim na kwance jikinsa, ta ki yarda ta dago kanta har ta iso ta tsaya daga bayan kujera, kallonta kawai yake ganin ta kasa dagowa yayi murmushi yace "Ko d'an kwalliya baxa ki yi ba" Ta turo baki tace "Baxan yi ba" ya xaunar da Shureim yace "Toh mu je in fada maki me yasa xa ki yi" da sauri ta dago tana kallonsa tace "A'a ni bana so..." Yace "Toh je ji gyara fuskar ki" juyawa tayi da sauri ta koma sama tana waigen ko ya biyota, tana shiga daki ta sa makulli, eye pencil ta sa ta goga powder a fuskarta ta sa chappete, lokaci daya tayi wani sanyayyen kyau, ta maida hijab dinta ta sauko rike da flat shoe dinta, kallonta kawai Aliyu yake ko kiftawa babu har ta shigo parlorn, ya mike yana kallon Shureim yace "Tafi daki ka dauko min makullin mota" tashi yyi ya wuce sama, Aliyu ya mike ya nufo ta, tana ganin haka tace "Wayyo don Allah ka bari, Kar ka xo kusa da ni ka ga yanxu Shureim xai...." Toshe bakinta yyi ganin ihu xata masa, yana kallon eye balls dinta yace "You... Are beautiful Iman" Tayi saurin sauke idonta gabanta na faduwa, ya xame hannunsa bakinta, Bata ankara ba sai jin kiss tayi, duk sai da ya rabata da chappete din da tasa ta kasa kwakkwaran motsi wajen, ganin faduwa xata yi yayi saurin rikota tayi regaining balance dinta, dai dai lkcn da Shureim ya bude kofa, Saketa Aliyu yyi ya fita parlorn da sauri, Shureim ya sakko yana kallon mum din tasa da tayi stiff inda take yace "Anty what are you looking at" da sauri ta dawo ta fara kame kame, sai kuma tace "Toh ka kai masa makullin mana" waje ya tafi ta karaso cikin parlor da kyar ta xauna, Tana jin ya gama warming mota don ma kar ya biyota ta mike ta fito da sauri, har lkcn xuciyarta bugawa yake, Sosai ta ji dadin ganin Shureim xaune a gaba, ta bude back seat xata shiga Aliyu ya kalli Shureim yace "Kai koma baya sweetheart sai Anty ta xauna gaba" hade rai khadijah tayi tana kallonsa, Shureim ya fito ya dawo baya, Tana masa wani kallo tace "Nima a bayan xan xauna" juyowa Aliyu yyi ya kafeta da idanuwansa, sauke nata tayi da sauri, ta rufe motar ta xaga ta shiga gaba kamar xata yi kuka, har suka fita gidan bata yarda ta kallesa ba, sai bayan da suka hau titi yace "Zaria xa mu je" ba tare da ta kallesa ba tace "To do what?" Yace "Xa mu je gaida Anty khadijah, daga can sai mu biya family house din su iklima tana can" Lkci daya jikin khadijah yayi sanyi sosai, a hankali Aliyu yace "But idan baxa ki shiga ba sai ki tsaya a mota mu shiga ciki da Shureim" Ta girgixa kai tace "A'a xan shiga" almost half of the journey surutun Shureim kadai ne ke tashi a motar, daga karshe khadijah da abun ya isheta ta juya tana masa mugun kallo tace "You keep ur mouth shut.... ka dame ni" Aliyu ya bude ido sosai yace "Ni fa yake ba labari ba ke ba malama" Hararansa tayi tace "Ehh nace ya ishi kunne na, ya dakatar da labarinsa haka" Murmushi Aliyu yayi a hankali yace "Toh Anty..." Ganin sun kusa Zaria a hankali Khadijah tace "Toh baxa mu kai mata komai ba?" Aliyu ya d'an kalleta ya mayar da hankalinsa kan titi sannan yace "Like what?" Tace "Kamar fruits da dai abubuwan da marasa lafiya suke so" Murmushi yayi, bayan sun shiga Zaria yayi parking gun wasu masu siyar da kayan marmari, ya siya mai yawa, ya sa bayan mota ya dawo side din khadijah yace "I think fruits din ma sun isa" Khadijah tace "Toh iklima fah?" Yace "We will get her something idan mun fito" Bata ce komai ba ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar ya ci gaba da driving. karfe sha daya saura suka isa asbitin da Anty khadijah take a Zaria, Aliyu na gama parking gaban khadijah ya dinga faduwa, ga mugun fargabar da ya ziyarce ta, Aliyu na lura da ita bayan sun fito ya dawo gefenta a hankali yace "You need not to be afraid of anything Iman, relax ur mind, or you stay behind, baxa mu dade ba xamu fito" Ta girgixa kai tace "A'a xan shiga" daga haka ta bude bayan motar ta fiddo fruits din shi kuma yana rike da hannun Shureim suka shiga babban asibitin, har ward din da Anty khadijah take suka tafi, Aliyu ya bude kofar a hankali hade da sallama, shi ya fara shiga tare da Shureim sanann khadijah dake makale a bayansa, ta dade bata yi fargaba irin na lokacin ba, Baby ce xaune ward din tana xuba mata abinci, daga one side kuma Barrister Sudais ne yana xaune saman kujera rike da makullin mota, da alamar dai lokacin suka xo su ma, Aliyu ya dinga kallon Anty khadijah dake kan gado....