Kenza eBookz

Raina kama book 1, 2, & 3 - Chapter 51

Raina kama book 1, 2, & 3 - Chapter 51

Raina kama book 1, 2, & 3 Chapter 51: Raina kama book 1, 2, & 3 Chapter 51. Bayan Munaya da aunty Mimi sun zauna a k'asan lallausar darduma can gefe suka…

4,349 words

Bayan Munaya da aunty Mimi sun zauna a k'asan lallausar darduma can gefe suka kwashi gaisuwa, dogarai suka amsa da yawun Sarki, sannan suka kuma gaisheda fadawa. Daga nanan aka amshi su Abdurrahman, y'an majalissar Sarki sukaita d'auka d'ai-d'ai suna saka musu albarka, da addu'ar fatan alkairi. Bayan fitowarsu sai sashin iyalan mai martaba, yau ma dai gimbiya zulfa bata fasa nunama Munaya da yaranta soyayyaba, daga Munaya har aunty Mimi basu San komaiba, dan haka sukaji dad'i da sakin jikinsu fiye da sauran matan sarki. Daga nanan sai sashen Mama Fulani, (kaga manya, Sarautar gagara badau a hannunku take, mama fulaninmu ta mutunci🤸🏻‍♀😂, ga irin naku manyan mata👍🏻)

To kunsan dai mutuniyar taku, yauma dai cikin izzar mulkinta suka isketa, ita dama Aunty Mimi babu ruwanta, tana mata yanda takeso, shiyyasa babu y'ar habaici ko bak'ar magana tsakaninsu kamar Galadima, hakanne yasaka munaya samun tsira daga samun nata rabon, amma mama Fulani bata d'auki yaro ko d'aya ba, a hannun kuyangin ta gansu tana ta6e baki. Daga Munaya dai har aunty Mimi babu Wanda yay ko tari, to balle kuyangi dasuka zama takalmin takawarta, basu jimaba suka fito, haka sukaita zuwa sashe-sashe, basu sami Kansu ba saida suka Shiga ko ina . Sun dawo kusanda awanni biyu aka gama loda kayansu a mota Samha da Sauban suka shige gaba aka kai gidansu Munaya. Ita kuma sai zuwa yamma za'a mata rakiya.

**** https://2gnblog.blogspot.com/ Gidansu Munaya dai tunda kaya suka isa aka tsaya kallon-kallo, daga Sauban kam har Samha babu Wanda yamusu kallon arzik'i, yo sunaji da hayak'in girma dana mulki, innarsu Munaya da Munubiya da tuni tana gida kawai suka kula, harda sakin jiki dasu sukaita hira, sunmayi zamansu anan sai ankawo Munaya zasu koma. Nanfa matan gidan suka fara k'ananun magana, saidai babu mai yunk'urin d'aga murya saboda tsaro🤣. Oho innarsu Munu ma batasan sunayiba, balle Munubiya da yanzu saita ma gadama suke ganinta, ko yaushe tana d'akinsu, da anyi magana tace jego, dukda gasu Fiddausi a gidan duk suna wankan suma, Fauziyyace kan shigo susha hirarsu ta zuminci, amma sauran saidai idan an had'u a gaisa, kowa uwarsa Na kitsa masa munafurci a d'aki (🤦🏻‍♀gaskiya iyaye mata munada gyara babba ta wannan fannin, inhar zaka rayu gidan yawa sai kayi gamo da irin wad'annan matsalolin kuwa, ALLAH ya ganar damu baki d'aya dai).

******

Su gadima Na shigowa masarauta ana kiran salla, hakanne ya sakasu yada zango a massalaci, saida aka idar sannan suka k'arasa sashensa, Duk agajiye yake, d'akinsa daret ya nufa, yashiga zame kayansa tun a falonsa, yana shiga ciki k'arasawa kawai yayi yashige bayi. Ya dad'e aciki kafin ya fito, baiko cire rigar wankanba yasha wani Magani ya kwanta, dan kansa ciwo yake masa. Cikin mintuna k'alilan barci yay gaba dashi. Munaya batasan ya dawoba, d'okin zuwa gida ya hanata barcin ranarma ita, sai yawan duba lokaci takeyi😂👍🏻.

3:35pm Galadima ya tashi, saboda kiran wayarsa da akayi, idonsa a lumahe ya d'aga, a haka suka gaisa da Momma, ya tambayi Abie tace barci yakeyi, sunyi wayar kusan mintuna 15 haryaso makara fita sallar la'asar. Bayan yadawoma papi ya kira suka tattauna, sannan yakuma sabon shiri cikin Orange d'in yadi anmasa kwalliyar bak'i kad'an, yayi k'yau sosai, sai tashin k'amshi yakeyi, saidai fusakar kam babu alamun yasan miye dariya. A haka ya iso sashen Munaya, babu kowa daga ita sai yaranta da Khaleel dake barci a gefensu, itako wayama take latsawa, da alama game takeyi Kodai wani Abu. Sallamarsa ciki-ciki da k'amshin turarensa ya sakata d'ago ido suka kalli juna, yawani Basar yana shan k'amshi, hakanne yasaka Munaya sake kama kanta, ta gaisheshi, sau d'aya ya amsa ya zauna a bakin gadon yana shafa kan yaran d'ai-d'ai harda Khaleel. Handbag d'inta da mayafi dake ajiye alamar lokaci take jira kawai ya kalla, baki ya ta6e ya d'auke kai. Key d'in mota guda biyu ya fiddo a aljihu ya jefa min akan cinya. Ni harma Na tsorata na kalli keys d'in sannan Na d'ago na kallesa. d'auke Kansa yay daga inda nake, cike da k'asaitarnan tasa yace, bak'in kibama Abba, d'ayan kuma ki ajiye a wajenki, motar tana can, saboda ko wani abu yataso musamman kai yara asibiti sai wani ya kaiki cikin yayyenki, ki kulamin da yara, kuskure d'aya kikayi a kansu zand'au mataki mai tsaurine, duk abinda zuciyarki batayi na'am dashiba ki gaggauta kirana na sani, ki kula da Abdurraheem sosai, banda barinsa yana dogon kuka saboda doctor ya sanar mana yana d'auke da ciwon......”. Saikuma yay shiru yana furzar da iskar bakinsa. Masifar tsura masa ido nayi zuciyata Na bugu tamkar zata fad'o dan tsoro, sai tsuma nakeyi, babu shiri na taso na dawo inda yake, durk'ushewa nayi gabansa tamkar mai neman gafara, “Yalla6ai ciwon mi? Please ka k'arasa fad'an dan ALLAH”. lumshe idanunsa yayi yana cizar lips, “Ba abin tada hankali baneba ai, domin ALLAH daya d'ora mana yafimu sanin hikimar hakan, bagashi ni nakai lokacin da Magauta basuyi tunaniba”. Maganganunsa ya nuna minta cewar Abduraheem Na d'auke da Ciwon zuciya? kenan shima yayo gadon mahaifinsa?”. Matsowa nayi na fad'a jikinsa na sanya kuka, bashida za6i saina kar6ata shima ya rungumeni cikin yima Ubangiji tasbihin Neman dauriya da kar6ar jarabawa a duk yanda tazo. Bai hanani kukanba saida nayi mai isarta sannan na share hawayenna. d'agowa nayi daga jikinsa zan tashi amma saiya hanani hakan, cikin kunnenna yace, “Baki da kunya gaskiya, ban ta6a ganin uwa mara kawaici akan y'ay'an fariba saike”. Kunyace ta kamani, na 6oye kaina a jikinsa ina murmushi. Galadima ma murmushin yake yana shafa bayanta. Sun dad'e a haka sannan na tashi daga jikin nasa gudun kar khalel ya farka ya ganmu a haka, shima ya fahimceni, dan haka bai hanani ba. Yace, “Addu'arki yake buk'ata da taka tsantsan, dukda ba wayonmune zai hana Ubangiji ikonsa ba idan yaso, sai yakai watanni 6 zai fara ganin doctor insha ALLAH, ya mik'a mamin ATM d'insa, ga wannan dukdai abinda yataso saiki cira, amma a bimin kud'i a sannu ni talakane mai yawan buk'atu, ga Abdurraheem ya k'aru shima, to idan bawa bai nema kud'iba ai yagama shiga uku a wannan zamanin daba kowa ya damu da damuwarka ba, inadai kuma gargad'inki ki kula min da yara, yau zamu koma India, amma kwanaki uku zanyi insha ALLAH na dawo”. Nace, “ALLAH yabashi lafiya da dukkan al'ummar ANNABI, nagode sosai, saidai kuma inason kawai idan na tafi shi.......” Hannu ya d'aga min, “karki damu nasan maganar Aurenmu ne, kamar yanda na alk'awarin inhar komai ya fito kan shekara zamu rabu, inkuma ba a samu yanda akesoba shekara biyu inakan Sani, sauran bayani kibani lokaci zuwa kammala abinda ke gabana OK?”. ‘yay maganar yana kallonna’. Kaina kawai na d'aga masa ina had'iye abinda ya tokare mak'oshinna. Bai sake cewa komaiba ya mik'e yana kallon agogon hannunsa bak'i, “ku fito”. yafad'a yana ficewarsa. Da kallo kawai nabisa idonna yana cika da k'wallan dabasan na minene ba.

******

Munaya tasamu rakkiyar wasu daga masarautar, bisaga jagorancin Galadima da suke zaune a mota d'aya, daga ita har shi babu Wanda ya tankama wani koya kalli wani, shi tundama suka fito latse-latsen System yakeyi hankalinsa kwance, itama ta basar gefe tana kallon waje dukda glass d'in mai duhune. Sun Isa k'ofar gidan k'arfe 5:24pm, bayan su Aunty Mimi sun fita duk suka shige cikin gidan tareda Kuyangi. Munaya tayi yunk'urin fita amma sai taji motar a kulle, Sarkin Mota ta kalla sai taga harya fice, ta dawo da kallonta ga Galadima daketa aikinsa tamkar ya manta a mota yake. Shareshi nayi kamar nima bazanyi magana ba kamar yanda ya basar, amma saina kasa, na kuma kallonsa murya a sanyaye nace, “ka bud'emin mana, miye ma'anar zaman namu? Wanima saiya zargi wani Abu ai?”. Banza yay mani tamkar bazai tankaba, kusan mintuna biyu sannan yace, “idan sun zarga laifine? Naga Sadaki na biya”. “Hummm”. Munaya ta fad'a kawai tana d'auke kai. Saida ya gama shan k'amshinsa sannan ya ajiye lap-top d'in gaban motar yana matsoni. da mamaki na kallesa, “yalla6ai lafiya?”. “ita ta kawo haka”. ‘yafad'a yana wani ciccijewa da jawoni jikinsa’. Tamkar zan tsala kuka haka naji, dan naji zafi, mukaima juna kallon ido cikin ido, idona da kwalla tafara taruwa sai wani marmar yakeyi, matso da fuskarta yay sosai, cikin magana rad'a yace, “kin fara kewata ne?”. Baya naja da kaina ina tura baki da yamutse fuska, amma sai hannunsa daya sa ya tokareni ya dakatar dani daga matsawar, yakuma matsowa gaf, numfashin junanslmu na sauka a fusakar juna, a hankali yafara hura min iskar bakinsa saman ido, babu shiri na lumshesu, hawayen da suka taru suka zubo, sai kawai ya shiga sumbata ta. Tuni nabashi had'inkai babu wani gardama, saida yay yanda yakeso da ni sannan kowa yakoma gefe, wata y'ar k'aramar souvenir bag ya d'ora mani a cinya, sannan ya cire luck d'in motar, saida naja wasu Seconds nasamu dai-daita sannan ta bud'e na fice rik'eda bag d'in daya bani, ban yarda nasake koda kallonsa ba. Shima harta fice bai kuma kallon nata ba.

Jiki a sanyaye nashiga gidan, matan gidanmu duk suna falon innarmu gaida bak'i, ina shiga muka rungume juna nida Munubiya muna hawayen da ita Munubiya tana tayani ne, nikuma bansan dalilin yinsuba🤣. Kowa dai da kallon mamaki ya bimu kawai.

Su Aunty Mimi basu dad'eba sosai suka tafi, anbar laraba anan zata zauna damu. Samha da khaleel harda kukansu.

******

Bayan komawar su Galadima masarautane yakejin wai ba'aga Harun ba, k'ala bai tofa ba balle nuna alamun damuwa ko jimama. Saima shirinsa Na tafiya ya fara hankali kwance, yaje yayma mai martaba sallama. Suka wuce airport abinsu, dan jirgin 7:30pm zasubi.............✍🏻 ALLAH ya gafartama iyayenmu😭👏🏻

BOOK 3 👉🏻9⃣➖🔟

..............Kwana biyu Galadima ya k'ara suka dawo Nigeria shi da Sauban, burinsa a yanzu ya fuskanci abinda ke gabansa da iyakar k'arfinsa da basirarsa, bai shiga masarauta ba saida ya had'u da baffi yabashi wasu takardu. Dole yay barcin wasu awoyi domin samun nutsuwar gajiyar tafiya, sannan yay shirin fitowa, ya lek'a sashen mai martaba dansu gaisa saiya tarar yanada bak'o, jakadiya sarkin gulma ta gutsiri goronta tana kallon Galadima, “Ranka ya dad'e ai takawa yana tare da bak'one, bak'on kuma Na lura Wanda ba'ason sanin dami yazone, dan kullum ganawar sema k'unshe yakeyi da takawa”. Shiru yamata tamkar bai jiba, danshi mutumne da baya shiga abinda bai shafeshiba, kowa yasan haka a masarautar, shiyyasa Duk makircin masarauta bazaki ta6a samun wani ya sakoshiba, kokuma kawo masa gulmar wani. Ganin haka itama jakadiya sai taja bakinta tayi shiru. Galadima ya mik'e yana kallon agogon hannunsa, “Bara naje, zan dawo anjima”. ba tare da ya kalleta ba yay maganar yay kuma ficewarsa. Da kallon ta bishi tana cigaba da 6allar goronta, tace, “wannan murd'ad'd'en da ace zai saurara dana bashi sirrika da yawa wlhy, amma ina, maganama ta kud'ice a garesa, ka huta wlhy, wai gurgu ya za6i zaman waje d'aya😏”.

😂😂🤭 _________★

Kwance yake jikin seat d'in mota idonsa a lumshe, duk yanda yaso ture zancen jakadiya a ransa karyay tasiri ya gaza hakan, sai kaikawo zancen ke masa, tabbas bak'o mai muhimmanci ne kawai zai iya ganawa da mai martaba har cikin turakarsa, to mike faruwa ne haka?, bashida amsa dan haka ya cije lips d'insa, tafiyar tasu yau dagashi sai sarkin mota, ya hana dogaransa binsa, gidan da su Nuren suke ya isa, dukda shi Nuren ma baya nan yaje gida saboda kiran gaggawa da papi yamasa, Muftahu kam dole kullum a Masarauta yake kwana, saida taka tsantsan ma yake zuwa gidan da rana, saboda rashin ganin Harun yanzu motsin kowa lura akeyi dashi. Su Ameer ne suka bud'e musu k'ofa Sarkin mota ya shiga, yanayin parking suka bud'ema Galadima ya fito, cike da girmamawa suka gaisheshi, ya amsa musu da d'an sakin fuska, sannan ya tambayesu Yaya aiki?. Da Alhmdllh suka amsa. Har cikin falon sukai masa rakkiya, babu kowa cikinsa, amma ko ina k'al yake a gyare, ga k'amshi mai dad'i yana tashi. Yayi zama yakai Na 10minutes saiga baba Rabilu shida wani dattijo da zai iya girmarsa kad'an, kokuma wahalace ta girmamawa tsufan nashi oho. shidai Galadima kallon mutumin yake tamkar ya sanshi, amma ya manta a ina. Zama sukayi, cikin girmama juna suka gaisa, sukaima Galadima barka da dawowa, da d'an guntun murmushi ya amsa, har yanzu dai idonsa akan dattijonnan. Lura da hakan da baba Rabilu yayi saiya murmusa, yace, “Ranka ya dad'e ka shaidashi ne?”. Galadima ya hard'e k'afafunsa yana murmushi, yace, “baba rabilu inadai masa kallon Sani kam”. Baba Rabilu yay k'aramar dariya yana kallon dattijon dake durk'ushe a k'asa shima yana Murmushi, sannan ya dawo da kallonsa kan Galadima yace, “Zaka sansa Ranka ya dad'e, amma gaskiya kana tare da k'uruciya lokacin, Sunansa Badi, mahaifinsa shine mai kula da dawakan Sarki a wancan lokacin”. Da sauri Galadima ya sauke k'afafunsa daya hard'e, cikin tsantsar mamaki yace, “Baba Rabilu kana nufin wannan Badi ne?”. Dattijo ya risinar da kansa k'asa alamar girmamawa ga Galadima. Yace, “Nine ranka ya dad'e”. Rasama abinda Galadima zaice yayi. Sai bakinsane ke motsawa alamun yanason maganar amma ya kasa. Sai ido daya tsurama Badi cikeda tunosa a lokacin da shi yake d'an shekara 5 kacal a duniya, dukda bazai yuwu ya iya tuna komaiba, amma tabbas yasan fuskarsa, yasan kuma shine mai kulawa da barga ta dokunan masarautarsu shi da iyayensa, a lokacin inhar baiyi k'aryaba Badi bazai wuce shekaru 33 ko 35 ba. Amma yau gashi zaune gabansa furfura da girman tsufa duk sun bayyana a garesa...... Sallamar Muftahu ce ta katse tunanin galadima, Muftahu ya zauna suka gaisawa da Baba Rabilu, sannan ya gaida galadima, idonsa dai nakan Badi shima. da k'yar Galadima ya amsama Muftahu gaisuwarsa. Badi dakema muftahu kallon sani ya gaisheshi cike da girmamawa (Dan ALLAH yayisa mutum mai yawan rik'o). Muftahu dai kasa hak'uri yayi, ya kalli baba Rabilu yana neman amsa. Murmushi baba Rabilu yayi, ya gyara zamansa yana fad'in, “Yalla6ai baka ganesa bane?”. Muftahu yace, “Banma ta6a ganinsa ba alhaji”. Badi ya kalli Muftahu sannan yay k'asa da kai. Yace, “Nikuwa kaga Na ganeka yalla6ai, dan bazan manta sanda kukan rako Yarima ba idan za'a fita da shi bakin ruwa shan iska, ka kan nace sai a doki d'aya zaku tafi kai da sauran abokan nashi”. Murmushi Muftahu yayi, ya kalli Galadima dayay shiru yana kallon Badi kawai, yasan yana tuna bayane, kuma akwai tambayoyi fal ransa sai dai ya kasa furtawa, janye idonsa yayi ya maida ga Badi, yace, “Amma Badi minene ya faru da kai harka bar masarauta? dan bazan iya tuna wani abuba a wad'ancan shekarun namu, yanzu kuma daga ina kake?”. Zama Badi ya gyara. Yace, “lallai labarine mai tsawo da Nisan zango, amma a tak'aice dai abinda zan iya cewa shine.....”.

“Bayan kwanciyar mai martaba adalin sarkinmu jinyar da ba'asan mafarinta ba da wata biyu kacal ranar wata lahadi da tashin hantsi munje kasuwa ni da mahaifina mun sayo abincin dokuna mun dawo, muna tsaka da sauke kaya a barga saiga wani mutum a tsakkiyar harawar dokunan cikin a kori kurar da muke zubo kayan kenan, dagani har mahaifiyata da mahaifina mun razana matuk'a, harma k'anwata taso tayi ihu amma mahaifiyarmu ta toshe bakinta saboda rok'on da mutumin kema babanmu akan muyi shiru Dan ALLAH, a razane matuk'a mutumin yake dan ko ina Na jikinsa mazari yake, yace a taimaka masa da ruwa yasha zaimana bayani, iya mahaifiyarmu ta nufi d'akunanmu dake cikin bargar dagacan gefe ta d'ebo masa ruwa a randa cikin kwanon sha ta kawo masa, babana ya taimaka masa ya fito daga akori kurar, ya zauna bisa buhun harawar da muka fara saukewa, ruwan ya kar6a ya kafa kai saida ya shanye kusan rabi sannan ya ajiye yana musu godiya, wani Abu irinna d'aukar hoto (camera) ya fiddo a cikin aljihunsa ya mik'ama mahaifina cikin yin magana da k'yar. yace_”. “Sarkin Barga ga wannan abun, nasan zakayi mamakin miyasa Na bakashi, to banida wajen daya dace Na damk'ashi sai wajenka a kaf masarautarnan, Dan kaine hanyata mai sauk'i, akan wannan abun aka biyoni za'a kashe, shine ALLAH yabani ikon shiga motarku, dan nashigo tacikin kasuwa domin tsira da raina shine Na ganku, karka bama kowa camera d'innan sai d'an Sarki, Yarima Sameer, kokuma d'iyarsa, gimbiya Haneefa, ko matarsa uwargidansa wadda ta haifi su Yarima d'in, harda wad'annan takardunma, nasan ni tawa ta k'are Dan babu makawa saisun kasheni, Dan ALLAH ka tabbatar cikin mutane ukunnan ka bama wani, nasan yarima bashida wayon dazai fahimci minene, amma idan ka nuna masa yabama mahaifiyarsa zai bata, dukkan abinda ya faru da mai martaba yana acikin wannan Camera d'in, ni zan koma, Dan banason wani ya fahimci nama shigo masarautar nan balle har asan Na gana daku”. “duk yanda mahaifana sukaso tsaida mutuminnan sun gaza, dan ya tabbatar mana dolene yabar masarautar a lokacin, saboda akwai munafukan da sukasan abinda yafaru da Mai martaba. Sai dai kuma abinda bamu saniba shine, Ashe dukkan abinda ya faru akan idon waziri ne, dan haka a wannan dare yabiyo sahun abinda mutumin yabada, mahaifana Na barci ya tashesu akan su bashi, sukace basusan mi zasu bashiba, shine ya kashe mahaifiyarmu wai dan baba yaji tsoro yabashi, dukda baba ya razana hakan baisa ya bashiba, ya yarda d'in gwamma a kasheshi shima da dai yabada , daga k'arshe shima ya kasheshi, k'arar da mahaifina yayi sai dukkan dokuna suma suka d'au haniniya. Hakanne ya sakani farkawa a rud'e Na fito daga d'akina, ina sako k'afata a d'akin mahaifana, Waziri Na cakama baba k'arfe a mak'oshi,, babana ya rik'e mak'ogwaronsa da hannu, yaringa min nuni da d'ayan hannun alamar Na gudu karnayi magana kuma, Na fahimci haka saboda ni baba yabama ajiyar abin d'aukar hoton da takardun, inhar iyayena zasu iya jurar mutuwa akan su bashi ni mezai hana na bi umarnin baba na gudu da abun, ko takan iyalaina banbiba na gudu ta hanya mafi sirri dana Sani, lokacin dana fito zan gudu waziri ya farga dani, hakanne ya sakashi biyo bayana, ganin bazai cinmini ba saiya saka dogarai masu tsaron k'ofa akan su bini wai na kashe iyayena zan gudu. Na rasa Inda zan dosa da wad'annan kaya saboda na tabbata ana bina a baya, saboda mun had'a ido da waziri, na shiga cikin jeji sosai, dan a wancan lokacin gari bai gama dunk'ulewa waje d'ayaba irin haka, Masarautar gagara badau ba tsakkiyar gari takeba kamar yanzu, dabarar hawa bishiyace tazomin dan haka na hau itaciyar wani Kalgo dake kusada k'oramar da mukan raka Yarima hutawa, har dogarannan da waziri ya saka su biyoni suka iso wajen domin nemana, ALLAH bai basu ikon ganinaba, saima suka wuce ni, lokacin sanyine sannan, nasha sanyi dan na wahala, sosai na fita hayyacina, abin mamaki da asubahi sainaji hayaniya a kusa dani, ido na bud'e da k'yar saboda tsantsar jigatar da nayi da muku-mukun sanyin wannan lokacin, wannan bawan ALLAHn nagani tare da Wanda yazo masarauta ya bamu abin d'aukar hoto (ya nuna baba Rabilu), hakanne ya sakani jin dad'i na sakko a nufin maida masa abinsa, nakuma sanar masa dalilin abin d'aukar hoton an kashemin iyayena, sai dai ina sakkowa wasu mutane na isowa wajen a mota guda biyu, yunk'urin guduwa mukayi mu duka ukun dukda su saima lokacin suka farga da ni a wajen, sun sami damar kama Wanda ya bama mahaifana abin d'aukar hoton, saboda kamar yaji ciwo a k'afa bazai iya guduwa ba, shine ya ringa fad'a mana mu gudu karmu sake mu basu abinnan. Iya k'arfinmu muka ringa gudu a lokacin Ranka ya dad'e, nashiga tashin hankali ganin rana tsaka masifa tazo ta haye mini ba tare dana san farkonta ba, gashi na rasa iyayena, na baro iyalina da k'anwata, bansan halin da suke cikiba, na samu damar shiga wani k'auye, Anan ne nasamu taimakon wani tsoho makaho, dan shine yabani mafaka ta tsawon shekaru 4, makahon tsohonnan yana zaune ne da matarsa amma ita tana gani, lokacin da jama'ar gari suka farga dani a gidan sai sukaje suka sanarma mai unguwar yankin, shikuma ya sanarma dagaci, har gida akazo aka tafi dani wani babban k'auyen dake kusa dasu inda dagacin yake akamin tambayoyi nida tsohonnan makaho, koda aka tambayi baba makaho saiya sanar musu ni d'an y'ar uwarsane, nazo ne na koyi sana'a na koma garinmu, dagaci yarigada ya yarda da baba makaho shiyyasa ya amince, aka kuma barni nacigaba da zama a k'auyen, tundaga wannan lokacin nasamu saken zama k'auyen gamji, ban sake waiwayar masarauta ba har tsawon shekaru hud'un nan. Saida ALLAH yayma baba makaho rasuwa sannan, matarsa gudun kar naci gadonsa shine tace yakamata na koma gida hakanan, ban mata musuba na had'o y'an kayana da abinda na samu a k'auyen da wad'annan takardu da abin d'aukar hoto nabaro k'auyen ina kuka saboda sabo. Sai dai abinda ban saniba Ashe anata bibiyata har lokacin, tun a hanyata ta shigowa gari wasu mutane suka farmin, na zubda komai nawa amma banda akwatin dana zubo abin d'aukar hoto d'innan da takarda, a cikin wannan gudu sai Ubangiji ya had'ani da wani bawan ALLAH akan besfa, ya bigeni, naji mummunan ciwo dan alamomin fitar rai sun bayyana agareni, cikin magana da k'yar, na mik'a masa akwatin ina rok'onsa dan ALLAH ya kar6i akwatinnan, ya Isar da shi masarauta amma yarima Sameer ko gimbiya Haneefa zai bamawa, ko mahaifiyarsu, bayansu karya bama kowa, idan bai samu damar badawa a yanzuba yabari sainan gaba inhar Yarima Sameer yay girman mallakar hankalinsa, zai iya kwatama kansa y'anci saiya bashi, na rok'esa karya ci amanata dan ALLAH, na aminta da shine shiyyasa na bashi....., da Sauri ya amsamin da insha ALLAH bazaici amanataba dan shima yana aikin jaridane, iya abinda naji kenan Daganan na suma a wajen, ban sake sanin komiba kuma, sai farkawa nai na ganni tare da wani maharbi jikinsa duk ciwuka, shine yaci gaba da kulawa dani tsawon lokacin ina jiyya, ban ta6a fad'amai ni waneneba, baikuma ta6a tambayata ba har shekaru sukaja, ganin girma ya kamashi sosai ya rok'eni na sanar masa daga ina na fito?, dan karya bar duniya da kokwanto a ransa, banyi nauyin bakiba na sanar masa komai. Yasha mamaki kwarai da gaske, dan suma labarin ciwon Sarki yaje musu, harma da nad'a k'aninsa da akayi ya maye gurbinsa. Shine yabani shawarar fara bibiyar masarauta kozan samu wani labari akan ahalina da jikin mai martaba, daga lokacinne nafara 6adda bamin shiga masarauta, na fahimci k'anwata ta auri wani bawa, matata ALLAH yamata rasuwa wajen haihuwar cikin dana barta dashi, d'an yayata data rasu itama ta bari shine k'anwata tacigaba da rik'o, a yanzu haka shine Wanda yazama direbanka Ranka ya dad'e, wannan shine abinda nasani ALLAH ya k'yautata rayuwarka, ya d'aukaki darajarka da mulkin masarautar gagara badau.”

Daga Muftahu har Galadima ajiyar zuciya suka sauke, kowanne yana jinjina lamarin a zuciyarsa, shi dama baba Rabilu ya fad'a masa kafinsuzo, kafin Galadima ko Muftahu su sami damar magana baba Rabilu ya fara fad'in “Lallai kamar yanda na sanarmaka randa nazo gareka ranka yadad'e d'an uwanane shi wannan daya bada camera d'in, da ni da shi duk aikinmu d'ayane, bayan yakai wannan camera ga mahaifin Badi, gidana ya zarto, amma saiya iske ban dawoba sai iyalina kawai, yabar musu sak'on wasik'a da address d'in inda zan sameshi, wato k'oramar bakin gari inda shi Badi ya gammu, inayin sallar asubahi kuwa na nufi wannan wajen dan ya rubutamin Cewar yana cikin mawuyacin hali, yana tsaka da fad'amin abinda ke faruwa saiga wad'annan mugaye sun biyomu, bansan a ina sukaji muna canba, na gudu ne a tunanina shima Habu ya gudu, Ashe sun kamashi, saida na fara jiyo sautin muryarsa dake amsa kuwwar karmu tsaya mu gudu, badan nasoba na gudu nabar Habu a hannunsu, wasu a cikinsu sun cigaba da bina, amma wani mai lambu ya taimakeni ya 6oyeni, kwanana biyu a cikin lambun, saida mukaga komai ya d'an natsa sannan na fito Na koma gida, duk tunanina ai basu ganniba, shiyyasa nacigaba da y'an hidindimuna domin 6adda kama, a 6oye kuma na shiga binciken wanda Habu ya bama Camera d'in, dan ya gayamin tana masarauta wajen mai kula da barga, Labarin mutuwarsu tazomin shida matarsa a bisa bincikena, saidai a masarauta ance d'ansu Badi shine ya kashesu, Sam ban aminceba, wannan ya sakani Neman Badi domin na kar6i camera d'in hannunsa, inada tabbacin shine Habu ya sanarmin cewa gashi can alokacin da mutanen nan suka iso, saidai kallo d'aya namasa muka fara gudun tsira, daga nan kowa ya kama tsaginsa. Dole na ajiye aikina saboda tsaro, na kawo rigar siyasa na sanya dan nema ma kaina girma, shekarata 6 a rigar siyasa akayi yunk'urin kasheni, ba kowa bane da wannan aikin face Alhaji Shehu Adamu Darma, har gidana ya saka aka satoni, nayi mamakin ganinsa, dan jam'iyyarmu d'aya, wani sa6ani bai ta6a shiga tsakaninmu ba, dan haka na nemi dalilin sanin miyasa zaisa a d'akkoni cikin iyalina? bayan mu y'an jam'iyya d'ayane. Ya kwashe da dariya yana nunani da fad'in lallai Alhaji Rabilu fanisau bakada hankaki, a tunaninka dukkan 6addamin da zakayi bazamu ganoka ba? yanzu dai dukma ba wannanba, ina camera?. Nace wace camera kuma? Wani wawan duka yaronsa yamin, na dafe wajen saboda azaba, Darma yakuma cemin ina camera d'in da Habu idris ya bani? nanma na sanarmasa ban saniba, wannan ne yasakashi kar6ar k'arfe ya kwad'amin a kai saboda haushi, daga nan na fad'i a wajen, ashesu duk sun d'auka a lokacin dukna mutu, shiyyasa suka jefar dani gefen hanya suka tafi, wani bawan ALLAH ne ya d'aukeni yakai asibiti, abinda yasa su Darma basuji labarina ba wanann mutum ba d'an nan yankinmu baneba, fataucine ya kawoshi, daya d'aukeni kuma saiya bar nahiyar wannan yanki dani gaba d'aya, nayi jiyyar shekaru biyu, kafin na dawo dai-dai, duniya sukta d'auka na mutu, saida na d'au shekaru bakwai banzo wannan yankinba, dan bawan ALLAHn nan yazo har nan ya kwashe iyalaina ya kaimin, bayan yamusu bayanin dazasu fahimta, bayan shekaru bakwai nakanzo nad'anyi bincikena na koma cikin 6adda kamanni, a wannan yanayinne na farga da Badi, ban sanshiba gaskiya, amma ganin yanayinsa tamkar mai lek'en asiri shine na fara bibiyarsa harna fahimci wanene shi, hakama waziri da d'ansa, na lura kullum cikin bin diddigin yalla6ai Galadima suke suma, nima wannan abun shine abinda na sani, kunji dalilin Darma na kirana Fatalwa”.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull