Kenza eBookz

Raina kama book 1, 2, & 3 - Chapter 52

Raina kama book 1, 2, & 3 - Chapter 52

Raina kama book 1, 2, & 3 Chapter 52: Raina kama book 1, 2, & 3 Chapter 52. Galadima da Muftahu sunyi shiru cike da tsabagen rud'ani da al'ajabi, da k'yar…

4,248 words

Galadima da Muftahu sunyi shiru cike da tsabagen rud'ani da al'ajabi, da k'yar Galadima ya iya bud'e baki cikin muryar tsananin damuwa yace, “waishin minene a cikin camera d'in nan? Yanzu kuma wanene ke rik'e da ita?”. Baba Rabilu yace, “Duk wannan muke son sani ranka ya dad'e, yanzu haka muna kan neman wanda badi yabama wannan Camera, dan na sanar masa har yanzu batazo gareka ba”. Galadima ya sauke ajiyar zuciya yana cije lips, idonsa yayi jazur, ya kalli Muftahu sannan ya kalli Badi dake zaune kansa a duk'e, “Badi yanzu idan ka gansa zaka iya ganesa kenan?”. “insha ALLAH ranka ya dad'e zan iya, saidai idan har ya mutune, bakuma ma fatan hakan”. Shiru dukansu sukayi kowa na nazari, Galadima sai ajiyar zuciya kawai yake saukewa, shi kad'ai yasan mi yakeji, ya kalli Muftahu yana fad'in “Sarkin mota ya shigo, dan nasan baisan matsayin Badi a wajensa ba”. Muftahu ya amsa da “to ranka ya dad'e”.

Cikin y'an mintuna saiga Sarkin mota tare da Muftahu sun shigo, a k'asa ya durk'usa yana musu sannu, Galadima ya kallesa yana nuna masa Badi, “kasan wannan?”. Badi da Sarkin mota suka kalli juna, a lokacin ne Muftahu da Galadima sukaga kamannin su, saidai shi Badi tsufa ya 6oyesa kad'an. Ganin sun shagala da kallon juna kowa yakasa magana sai baba Rabilu ya katsesu da fad'in “Badi kamasa bayani mana”. Dattijo badi ya kamo hannun Sarkin mota kusa da shi, yana zubda hawaye yace, “matso gareni Yunusa, nine babanka yayan mahaifiyarka, Badi ya rungume Sarkin mota suka fashe da kuka, a haka yake bashi labarin alak'arsu. Saida kwalla ta cika idon Galadima, hakanne ya sakashi tashi ya fice daga falon, Muftahu da tausayinsu ya kamashi shima ya bi Galadima da hanzari. A tsaye ya iskeshi ya tsurama flowers d'in da akama gidan ado dasu ido, hannayensa biyu duk cikin aljihu, gaba d'aya bugun zuciyarsa ya fara canjawa, sai had'iye yawu yake da k'yar, wayarsa ya zaro daga aljihu, rasa wanda zai kira yayi, sai bin numbers d'in yake da idanu yana canki canka, ya tsansa dai ya sauka kan number Munaya.........

**********

Fitowata daga wankan yamma kenan Munubiya ta shiga, yau kwana biyu duk zuciyata babu dad'i, hakannan na tsinci kaina cikin 6acin rai, harzan fara shafa mai Aryaan ya shigo d'auke da Abdurrahman yana kuka, dole na ajiye man na kar6esa, na ta6a jikinsa da har yanzu zafin zazza6in daya yini da shi bai saukaba, saboda tunda asuba ya farka da kuka cibiyarsa na ciwo, kashinsa harya canja kala, saida innaro tazo tabashi magani sannan muka samu nutsuwa, daga nan kuma sai zazza6i, shine har yanzu nake d'an jin jikin nasa da zafi kad'an, nono na saka masa a baki kozai kama, dan duk yinin yau bai shaba, na sauke ajiyar zuciya ganin ya kar6a, ina shafa kansa idona na kallon fuskarsa data fara rikid'ewa zuwa kamannin mahaifinsa wayata ta shiga Ring, d'auke idona nayi daga kan Abdurrahman na maida ga wayar, nayi mamakin ganin yalla6ai, danna canja sunan tun a waccan ranar, na daiyi picking a d'arare na saka a kunne. yau dai banjira k'orafinsa ba nace, “Ina yini”. A yanda ya amsa min sallamar da gaisuwar saida gabana ya fad'i har na cire ma Abdurrahman nono ban saniba, aikam ya fashe da kuka. Hakkane yakuma rikita Galadima daga can, yace, “miya faru? Waye ke kuka?”. K'aramin tsaki naja, nace, “Abdurrahman ne, wai dama ka dawo?”. Bai amsa min na k'arshen ba saina farkon, yace, “mi'akai masa?”. “Babu komai, bayajin dad'ine kawai”. Lips d'insa ya cije yana fad'in “yanzu zanzo gidan”. Bai jira cewar Munaya ba ya yanke kiran.

Sororo nayi ina kallon wayar, kai kace zan ganosa a wajen ne, Munubiya data fito ta katseni da fad'in “mikike kallo haka? ga ruwan nono kin bari yana zuba a jikin yaro”. Ajiyar zuciya na sauke, sannan na gyara ina kwantar da Abdurrahman d'in dayay shiru. Munubiya dai takuma tambayata, fad'a mata zuwan Galadima nayi, tace, “oh shine kikema wannan mamakin ko miye?”. 'Dan hararta nayi, amma bance komaiba, itama ta ta6e baki tana kamo hannuna ta zauna a stool d'in Mirror. Wai sai tamin kwalliya. Da faro k'in yarda nayi, saida naga ta 6ata rai sannan na hak'ura dai tamin inata tura baki gaba.....................✍🏻

ALLAH Sarki, wlhy harna fara missing d'inku, waya tamana tsiya😢, yanzuma da wayar Oga nayi typing, koba komai Comments naku na sakani nishad'i, I Miss you so much all😔😘😘😘❤❤

Insha ALLAH vary soon zan dawo gareku😂.

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK 3 👉🏻1⃣1⃣➖1⃣2⃣

.............Mintuna basufi 20 da gama kwalliyar ba saigasu Aiyaan sun shigo dad'an gudunsu, Munaya na cikin d'aki tak'i fitowa, wai kunyar su inna suganta da kwalliya takeyi. Inna ta dakama su Aryaan tsawa saboda batason wannan gudun. Nutsuwa duk sukayi. Tace, “Gudun mi kukeyine?”. Y'ar rige-rigen fad'a suka fara, kowa yana ture d'an uwansa akan shine zai fara fad'a, ana cikin haka Yaa Anas yay sallama. Hayaniyar su Aiyaan ta hana aji, sai laraba ce ta farga dashi, shine Yakuma yimasu Aiyaan tsawa suka nutsu, kowa ya zauna gefe yana tura baki. Yaa Anas ya gaishe da laraba da innarsu munaya, Munubiya ma ta gaisheshi, ya Amshi Ameen dake hannun inna yana fad'in “inna Yalla6ai Galadima ne fa agidan namu, gashi kuma duk su Abba basa nan, shine nace ko'a kawoshi nan ne”. Inna tace, “A'a Anas, ai ba'ayi hakaba, bara na d'akko makullin d'akin Abbanku saika bud'e masa nan ya shiga”. Anas yace, “to inna”. Laraba dake taya Munubiya shirya su Amaturrahman tayi murmushi, a ranta tana yaba yawan karamci na ahalin Munaya, mutanene masu dattako da sanin darajar d'an Adam, shiyyasa kullum take kuma taya Galadima murna da samun tsatson wannan mutane....... Tunaninta ya katse lokacin da inna tadawo da key ta bama Anas, Ameen ta kar6a a hannunsa shikuma ya fice. Munubiya tace, “innarmu ajiye wannan ki k'arasa sama Abdurraheem kayan Dan ALLAH, sainaje na had'ama Abbansu abincin, nasan yanzu yayi”. Inna ta harareta, “kai nifa kunma maidani Nanny d'inku, nizan ke muku hidimar y'ay'ane?”. “please mana innarmu, basune masu kawo miki kaza kina ciba sannan kin tsufa”. Laraba tayi dariya tana fad'in “Gaskiyarki kuwa Maman 2, ALLAH dai yaja da rai”. Inna tace, “iya kema biyema shirmennan nata zakiyi?”. Laraba takuma darawa tanama Abbdurrahman rawa. Itadai Munubiya ta fice tabarsu, laraba na bama inna amsa.

Duk ina jiyosu daga d'aki, haka kawai sainakejin wani iri, yanzu dole ta gaban su Innarmu zanbi natafi wajensa? Na kalli kaina a mirror kunya ta kuma kamani, dukda Simple kwalliya Munubiya tamin nayi k'yau, dan d'aurin kaina ya zauna dak'yau, fuskata ta kuma nutsuwa, har rantsuwa tamin inhar na canja wani Abu saitayi 2weeks batamin maganaba, nasan kad'an kenan daga abinda Munu... Zata iya, shiyyasa dole na hak'ura na bari..... Shigowar Munubiya yasani waigawa na kalleta, ta harareni tana matsowa tamin kallon tsaf, nasan sotake taga mina goge kona canja, ganin komai yana yanda tayishi saita kuma d'aukar soson hoda ta gyara, ta d'akko turare tana kuma fesamin, hannunta nai saurin rik'ewa ina 6ata fuska, “Wai Sweetheart bazaki barshi haka bane? Turaren nan har hawa kaifa yake, Ni wlhy kunyarma fita nakeyi”. Munubiya ta fisge hannunta tana dariya da fad'in “to kibi ta k'ark'ashin k'asa kawai mana, kuma wlhy ki nutsu, idan yauma tsiwar zaki masa saiki bada himma, anacewa mutum Idan ya haihu yana hankali kedai bakiyiba, saima rashinsa kika k'aro, malama muje yana jiranki”. Yanda kukasan na make Munubiya haka naji, amma saina k'yaleta, nima nasan ta hanyar da zanbi na rama, gyalen data samin a kafad'a nabi da kallo. nace, “haba Munu, amma wannan d'an gyalen Dan ALLAH?”. “Okay, wajen surukinki zakine? ALLAH ki kiyayeni”. Baki na murgud'a mata. Tace, “oho dai, kije kimasa kidawo ta cinyayyen lips, danba barinki zaiyiba”. Juyawa nayi na kalleta, amma saita d'auke kai tamkar bama itace tayi maganarba. Nayi kwafa kawai muka fito. ALLAH ya soni babu kowa a falo sai su Aiyaan, hakkane ya sakani sauke ajiyar zuciya nad'an saki jikina.

Gwaggon Haleematu dake kaikawo a kitchen da tsakar gida saboda itace ta kar6i girki tabimu da kallo, gulma nacin ranta, daga ni har Munubiya d'auke kai mukayi tamkar bamu gantaba, muka shige falon Abba da takalman Galadima heif cover milk ke a k'ofar. K'amshin turarensa yafara amsa mana sallama, na shak'a na lumshe ido. Hankalinsa nakan yaransa da duk suke jikinsa, yana sanye cikin milk d'in shadda harda hular zanna bukar itama milk da d'an kwalliyar Brown kad'an, sosai yamin k'yau amma saina d'auke kai tamkar banma gansa ba. Munubiya tace, “To Abban 3 gatanan nakawo maka”. Murmushi yayi, idonsa sanye cikin farin eyeglasses, cikin muryarnan tasa mai kama da anmasa dole yace, “Thanks you Auntynmu”. Murmushi itama Munubiya tayi, ta jinjina masa kai ta juya zata fita, har takai k'ofa ya katseta da fad'in “Su twins rowarsu akemin?”. Hannu ta saka ta dafe bakinta, saikuma ta janye tana cewa, “A'a Abban 3 zasuzo su gaida abbansu insha ALLAH”. Baice komaiba sai murmushi daya sakeyi. Ta harareni sannan ta fice, Nina ramawa nayi.

Koda Munubiya ta fice saiya kuma maida hankalinsa ga yaran ya shareni, abin yabani haushi, jinaima kamar na fice abina, amma na danne zuciyata na matsa gabansa. Wajen tiren abincin na durk'usa, na d'auki jug d'in zo6on na zuba a k'aramin cup, d'agowar da zanyi na kamashi yana kallona, amma saiya basar, baki na tura kad'an, na mik'a masa cup d'in. Bai kar6aba, sai wani bina da kallo yake tundaga sama har k'asa, a raina nace rainin wayo. Idonsa ya janye daga kaina, ya fara kwantar da yaran d'ai-d'ai a gefensa, saboda a doguwan kujera yake. Saida ya gama nakuma mik'a masa cup d'in, hannuna ya had'a da kofin ya rik'e, na d'ago ido muka kalli juna, duksai na daburce, danya cire eyeglasses d'in, kamar mai koyan magana na had'o kalmomin gaisuwar da gyar. Nace, “i...na..yini”. Wani Munafukin murmushi yayi yana lumshe idanu, ya kuma bud'esu a kaina yana d'age girarsa d'aya da cizar lips, a hankali ya furta “ke matsoraciya Ce, miye na rikitar daga kallo uhmyim?”. Idanuna nad'an juya nace, “Tab badai niba”. Ya ta6e baki kad'an, idonsa akan hannunmu dake had'e waje d'aya akan kofin. Nima saina kalli hannun, cikin sanyin muryar dabansan nayiba nace, “da sanyi fa”. “Really?”. Shiru nayi ban amsashiba, ya zame kofin a hankali, sannan ya koma jikin kujerar ya kwanta yana hard'e k'afafu. 6oyayyar ajiyar zuciya na sauke, bansan miyasa inhar Galadima zai kasance kusa dani daf irin haka koya kafeni da ido nake rikicewa ba, haka kawai sainaji jikina yana tsuma... Yay wani luuu da idanu saboda ajiyar zuciyar da tayi, zo6on ya kai bakinsa ya kur6a kad'an, dad'insa ya sakashi lumshe idanu ya had'iye. Da hannu yamin nuni da kujera, tamkar kazar da kwai ya fashema a ciki na mik'e, harzan bar wajen naje ta nesa dashi saiya rik'o hannuna. Juyawa nai na kallesa, ya nunamin kujerar kusa dashi da ido cikin tsare gida. Banida za6in daya wuce bin umarninsa, na zauna tamkar mai shirin guduwa da ance ar. Zo6on yakuma sha yana kallona, kamar zaiyi magana saikuma yayi shiru. Ganin haka sai nace, “yaya jikin Abie? dasu Momma?”. Yaji dad'in ganin ta damu da ahalinsa, ya ajiye kofin yana gyara zama, yace, “jikin Abie Alhmdllh munata k'ara ganin haske, duk since na gaidaki dak'yau”. Nace, “ina amsawa”. Daganan mukai shiru, kowa yana tattaunawa da zuciyarsa, Idan ka gammu saika d'auka wasu saurayi da budurwane, irin had'uwar farko d'innan😂. Abimda na fahimta dai kamar yana tattare da damuwa ma, nad'an kallesa ta gefen ido, idonsa nakan yaransa, nace, “Abinci fa?”. Maido da kallonsa yay gareni, yad'an yamutsa fuska yana girgiza kai. Kallonsa nayi, cikin marairaicewar da bansan nayiba nace, “please mana yalla6ai, yanzu haka bakaci komaiba ka fito gida”. Wani Abu dabaisan miyeba yaji ya tsarga cikin kansa har zuwa tafin k'afa, idonsa k'yam akan Munaya ko k'yaftawa bayayi, itama gareta hakanne, ta zuba masa ido batare da ta shirya hakanba, sai tsantsar tausayinsa dayake hangowa cikin idanunta, hannunta ya kamo cikin nasa, yana fad'in “kinaso naci?”. A sanyaye na jinjina masa kai alamar eh. Murmushin gefen baki yayi, ya matsa hannunta kad'an, “indai kinason naci akwai sharad'i”. Batareda nasan mi bakina ya fad'aba nace, “kafad'a kona miye na amince”. Kansa ya jinjina yana janye hannunsa, ya gyara zamansa yana fuskantata sosai, akan la66a ya furta, “saidai idan zaki bani da kanki”. Babu shiri na waro manyan idanuna ina dafe baki alamar mamaki, ya had'e fuska yana ta6e baki da kwantar da kansa jikin kujerar. Yace, “Ashe ba sokike nacinba, kuma yunwa nakeji”. Harga ALLAH inason yaci, dan na fahimci yanada buk'atar abincin, amma yana azabtar da kansa saboda bai yarda yaci na kowaba amasarautarsu, idan kuma ya fito inhar ba birnin gayu yajeba bazai ta6a cin komaiba inba ruwa ba harya koma gida kuwa... Na sauke ajiyar zuciya, idona cikeda kwalla nace “to amma...” Idonsa ya bud'e ya d'agamin hannu, amma baice komaiba. Nima ban sake yunk'urin cewa wani abunba, na sakko daga kujerar na durk'usa a k'asa ina bud'e kulolin. Mamaki ya kamani, dan ganin masa, a ina Munubiya ta samo masa haka? A lokacin da tasan zaizo yayi k'arancin da har za'ayi Masa. ganin babu mai amsamin tambayar na zuba hud'u a plate d'in, na d'ago ido na kallesa, Ashe shima ni yake kallo, idanu ya lumshe alamun ya Isa. Nima saina jinjina kai, kwanon da zansa miya na d'akko, amma saiya rik'e hannuna yana girgiza kai, na kalli plate d'in masar sannan na d'ago Na kallesa, ya kad'amin kai. Fahimtar mi yake nufi da nayi saina zuba miyar gefen masar, sannan na mik'e da nufin komawa inda na taso, tiren abincin ya janye gefe, ya jawo center teble d'in a gabansa sosai. Kallon teble d'in nayi shima na kallesa, saiya d'auke idonsa, a yanda ya janyo teble d'in inhar na zauna dolene k'afafunmu suke gogar juna, amma ya zanyi tunda na d'auki alk'awari. Zama nayi, na d'ora plate d'in saman cinyata, na d'ebo masar da spoon na nufi bakinsa, baki ya ta6e yana girgiza kai. Na dafe kaina irin naga ta kaina d'innan, na kallesa a marairaice, “yalla6ai to ya kakeso nayi please?, kaifa kace zakaci”. Da d'an yatsa ya nuna hannuna. Cikin mamaki nace, “da hannu?”. Yanda tai maganar tana zaro ido saiya so bashi dariya, amma ya had'iye kayarsa. “O ni Munaya naga ta kaina”. Nafad'a a hankali. A ransa yace zadai ki gani yarinya. Dole na mik'e nakuma wanko hannuna a bayin falon Abba, na dawo, gyalena na zame dole na shinfid'a masa saman cinya gudun karna 6ata masa kaya, na fara d'ibar masar kamar yanda yake buk'ata na nufi bakinsa, saida ya kama hannuna sannan ya k'arasa dashi cikin bakin, ALLAH sai da tsigar jikina ta tashi, amma na daure nakuma d'ibowa, haka naita bashi har ya cinye, na bashi nama ya girgiza kai, alama namasa a k'ara?. Da d'an yatsa ya nunamin wai d'aya, bud'e kular nayi na d'auka, sauran miyar plate d'in ta isa, zan gutsura ya rik'e hannuna, a mamakina sainaga ya d'an ja hannun rigarsa sama ya saka hannu a plate d'in, idanu na waro da bud'e baki Dan mamaki, sai kawai naji hannunsa cikin bakina ya sakamin masa, ya d'agamin gira d'aya damin alamar inci, tamkar sokuwa haka na shiga taunawa, harna had'iye idonsa nakan bakina, saida ya rage saura lauma d'aya ya dakata da bani, na ida d'aukar laumar k'arshen na saka masa nima, ina niyyar tashi na wanke hannu ya maidani zaune, hannun dana bashi ya kamo yana sud'ewa, salon dayake lashe miyar saiya haifarmin da kasala, na rumtse idona harya gama sannan ya sakarmin hannu. Nima saina kama nasan na tsotse sannan na mik'e, ina toilet zan wanke hannuna zan d'ibo shima nakawo ya wanke sai na jishi a bayana, juyowa nayi na kallesa, ya mik'amin hannunsa. Bance komaiba na kama na wanke masa, na zuba masa ruwa ya kuskure bakinsa. Nidai gaba d'aya mamaki dukya nemi halakani. Koda muka fito ina niyyar komawa inda na fara zama sai naji an fisgoni, jikinsa na fad'a, bance komaiba dukda naji zafi. Shima baice uffanba. Lallai akwai abinda ke damunsa da gaske, hannuna na d'ora a kan k'irjinsa saitin zuciyarsa, ya bud'e ido sosai yana kallon hannun nawa, cikin aro jarumta nace, “Autan Momma mike damunka wai?”. Murmushin dabai shiryaba ya saki, ya kalleni ido cikin ido yana fad'in, “kin rainani ALLAH kuwa, wannan autan bazai bar bakinkiba dai ko?”. Murmushi nayi mai sauti, har hak'orana na bayyana, na had'e hannayena a waje d'aya alamar ban hak'uri, cikin langa6e kai nace, “tuba nake to na tsakkiya nefa kai ashe”. Rankwashi yamin a kai, na dafe wajen dukda d'ankwali yasa banji zafiba sosai, amma na 6ata fuska ina k'ak'alo hawayen k'arya. Gira d'aya ya d'age yana kallona alamar yadai?. Na tura baki gaba ina fad'in, “da zafifa”. Murmushi yayi yana kauda idonsa yana kallon yaransa. Na yunk'ura da nufin sauka a jikina amma ya rik'eni, ba tare da ya kalleniba yace, “yakamata kisan kin girma”. Bakin na kuma tunzurawa nace, “hu'im ina nan a babyna wlhy”. Shi kansa baisan k'aramar dariya ta kufce masaba, ya d'an dara yana girgiza kai da kallona. Ganin ya fara sakin jikinsa saina kuma cewa “Please yalla6ai bakada lafiya ne?”. Tafin Hannunsa ya sanya saman kumatuna, a hankali tamkar mai rad'a yace, “mikika gani?”. Na d'an kuma kwantar da murya ina janye idona daga cikin nasa, “Ba komai, kawai yanayinka ne ya nuna”. Baice komaiba ya matso da fuskarsa gab da tawa ya had'e bakinmu, dukda na tsorata kar wani ya shigo ya gammu haka na barsa, yayi yanda yake so inhar hakan zai kauda damuwar dake ransa, nidai fatana na cika alk'awarin dana d'aukarma Momma a duk sanda na gansa cikin damuwa. Saida ya gaji da kansa sannan ya bari tareda rungumeni yana sauke ajiyar zuciya, muryarsa can k'asan mak'oshi yace, “haka kike son ganina”. Kaina na girgiza masa, ya d'agoni da sauri yana kallona, yace, “to yaya?”. Murmushi nayi nafad'a k'irjinsa ina 6oye fuskata saboda kunya, shima saiya saka hannuwansa ya zagayeni yana murmushin, a hakanla ya furta “Thanks”. Bance komaiba, amma naji dad'i daya godemin. Kiran wayarsa da akayi ya sakani tashi daga jikinsa, zan tashi gaba d'aya ya rik'eni, a haka yay picking call d'in, na fahimci da papi yake waya, dukda kakansa ne yanda yake magana cikeda tsantsar girmamawa saiya birgeni, Mai dawakai danaji yana ambata da bayanin d'ansa mai suna Badi ne yaja hankali na, tsaf na fahinci zancen dukda bansan mafariba, yakuma yanke maganar bai k'arasaba yana fad'ama papi sai yazo zasu k'arasa zancen. Yanke wayar yayi yana huremin ido saboda kallonsa dana keyi, tunda ya fara wayar. K'asa nayi da kaina dan naji kunya ya kamani ina kallonsa, ya ajiye wayar yana fad'in “Zamukai Abdurrahman asibiti ne?”. Kaina na girgiza masa. nace, “A'a aiya warke bama sai an kaisa ba”. Yace, “Okay”. Idonsa akan yaran, Abdurraheem ya fara motse-motsen tashi, sauka nayi a jikinsa nakoma gaban kujerar na durk'usa ina d'an bubbuga bayansa, dan banason ya tashi, inhar ya tashi saiyasha nono, sauran kuma suma duk tashi zasuyi, bada nono a gaban Galadima shine abinda nake gudu ni kuma. Shikam tsura musu ido yayi cikeda sha'awa daga ita har yaran, ya d'auki wayarsa yamusu hoto batare da ta saniba.

Saida naga ya koma barci sannan Na dawo kujerar dana fara zama, shima zamansa yagyara yana kallona, magana yakeson yi amma yanata juyata a zuciya, nidai bance dashi komaiba, saida ya gama k'asaitarsa da basarwa sannan yace, “Abba fa?”. Nace, “yayi tafiya yau kwana biyu”. “zuwa ina kenan?”. “wlhy ban saniba, amma miya faru?”. Kansa ya girgizamin alamar babu komai, yad'an furzar da huci yana kallona agogon hannunsa. “Shikenan ni zan wuce, zan iya dawowa a kowane lokaci inhar Abba ya dawo”. Kaina na jinjina masa, ya mik'e, nima saina mik'e ina fad'in “yaa Sauban fa?”. Bai tankaminba saida ya duk'a yayma yaransa kisses a kumatu sannan ya d'an kalleni ya d'auke kansa, “Tare muka dawo, amma zai wuce masarautar su papi gobe, dan a can zai zauna harya gama”. “ALLAH ya bada nasara”. Nafad'a ina sauke ajiyar zuciya. A kan la66a ya amsa da amin. Harya kusa nufar k'ofa nace, “bakace komai game da maganarmu bafa”. Cak ya tsaya amma bai juyoba, a haka yace “wace magar?”. Wani yawu na had'iye da k'yar ina fad'in, “Maganar rabuwa, nifa gaskiya bazan komaba”. Saida yaja kusan seconds 20 kafin ya juyo yana fuskantata, kallon da yakemin yasani janye idona daga kallonsa, cikeda k'asaitarsa yatako ya dawo inda nake tsaye, hannayensa ya cusa cikin aljihu yay matuk'ar d'aure fuska, cikin izzarsa yace, “wai nikam miyasa kikeda naci?”. Nima fuskar na tamke. Nace, “Neman y'ancina nake, tun farko a wannan tubalin ka gina auren, mizaisa kuma lokacin rugujeshi yayi bazakayi hakanba?”. Lips d'insa ya ciza yana kallona da k'ank'ance idanu, cikin salon Basarwar tasa yace, “So what idan nine na gina a haka d'in? Kinsan dai bazaki ajiyemin yara ba koda abinda kikeson ya kasance, dan yarana bazasu sha madaraba bayan sunada abinci”. “Humm” na fad'a cikin takaici. na gyara tsayuwa idona na cikowa da kwalla, “Yalla6ai karka manta a randa na kwana biyu gidanka da bakiknka ka tabbatar min baka zalunci? daga ni har kai mun amince cikin yarannan ya zone cikin k'addarar dabamu shiryama zuwanta ba, to mizaisa kuma zuwansu duniya yazama salon tauye hak'k'ina? Na amintane da aurenka domin warware k'ullun da akaimin da wanda yake kan mahaifina, bawai dan bansan y'ancin kainaba ko darajata, idan har nice a matsayin Amaturrahman zakaso wani ya aureni a matsayin auren shekara d'aya ko biyu domin cikar wani burinsa ya rabu dani?, addininmu da al'adarmu duk basu koyar damu hakaba, anayin aurene domin ibada, saboda bautar ALLAH ne, sannan ana ginashine bisa tausayi da rahama, inhar zuciyarka bazatayi dad'iba a matsayinka na mahaifin Amaturrahman idan hakan ace akanta ta kasance, to ya kake tunanin randa nawa mahaifin yasan gaskiyar matsayin nawa auren zaiji?, tunda nataso nake d'and'anar zafi da d'aci na zamantakewar rayuwar gidan yawa, taya zanso saka rayuwata a walagigin kila wa kala, na shigo wannan yak'inne domin neman y'ancin kai badan ribantuwa da ganima ba, amma lokacin dana wayi gari da abinda ban shiryamawa ba a cikin jikina haka na hak'ura na kar6a da hannu biyu saboda k'ok'arin cinye jarabawa, miyasa kakeson yin wasa da rayuwatane wai? Duk motsi dai yaranka! Yaranka! Karka manta nimafa y'ar wasuce, kamar yanda kakeji haka suma sukeji akaina, inason nima nayi aure na zauna tamkar kowacce mace a gidan mijinta, na fidda hak'insa da ALLAH ya wajabta min, shima ya fidda min nawa da ALLAH ya wajabta masa......”. Hannu ya d'agamin alamar ya isheshi haka, yakuma matsowa gabana cikeda izza yace, “mikikeso yanzun?”. Nace, “sanin matsayin aurena, inhar yaranka ne zan muku sadakar shayarwa na wata shida na yayesu nayi aurena da mijin dazai soni ya k'aunaceni domin ALLAH”. Bakinsa ya ta6e yana cije lips, jijiyoyin kansa duksun mimmk'e saboda 6acin rai, cikin takaici yace, “Yarinya har abada babu shegen namijin daya Isa na k'etara gona shima ya k'etarata, koda kuwa wannan gonar ta jinginace, ko ayanzu nabar duniya wani yayi hakan ban yafeba, duk gonar dana ra6a tawace ni kad'ai koda banyi noma a cikinta ba, wannan yazama first and last da zaki kuma kawomin irin wannan maganar, kodan kinga ina k'yaleki ne shiyyasa kike d'aukata wani sauna kiringa min zancen wani banza can daban, Munaya karki yarda na nuna miki a salin true color d'ina wlhy, ina kuma gargad'arki a karo na k'arshe”. ‘ya k'are maganar da bugamin yatsunsa biyu saitin fuska ya fice abinsa’.

Baki na ta6e ina bin inda yabi da harara, sannan na saka gyalena na goge hawayen dake zarya a kumatuna nai kwafa na fice abina nima nabar yaran.

**********

Tunda ya fito Muftahu ke binsa da kallo, harya bud'e mota ya shiga baiko kalli Muftahun ba shi. Dama shine ya kawoshi, amma yana ajiyeshi ya koma saboda wani aiki daya bashi, dawowarsa kenan yana k'ok'arin kiransa yace zai shigo su gaisa da Munaya shine yafito a fusace. Baice dashi uffanba ya bud'e motar shima ya shiga ya tada suka tafi, saida sukayi nisa da tafiya sannan Muftahu yace, “Ranka ya dad'e wai mike faruwane?”. Shiru yamasa yak'i tankawa, shima Muftahu sai yaja bakinsa ya kulle ya cigaba tuk'insa. Sai jera tagwayen tsaki yakeyi, Muftahu ya kuma kallonsa sannan ya maida hankali ga tuk'insa, ya kuma rik'e sitiyarin yana fad'in “ALLAH ya huci zuciyarka ranka ya dad'e, idan kana ganin bazaka juri zuwanba kace ta dawo mana kawai”. Cikin jan wani tsakin yace, “inhar taci gaba damin zancen wani wawa lallai zan datse harshenta wataran”. 6oyayyan murmushi Muftahu yayi, a zuciyarsa yana jero hamdala wa ubangiji, dan babu abinda yake hange tattare da galadima sai tsantsar kishin matarsa, dukda baisan miya had'asuba yaji dad'in hakan, koba komai yanzu ya fita daga damuwa da fargabar rabuwar wannan auren. cikin son kuma fahimtar wani Abu yace, “to amma ranka ya dad'e yazamuyi idan lokacin rabuwarku yayi kenan? Kasanfa alk'awarin da mukai mata”. “Oho! Maka”. Galadima ya fad'a cikin tsananin fusata. Da k'yar Muftahu ya iya had'iye dariyarsa, bai sake cewa komaiba har suka isa gidan baffi, dan karya mazgeshi a banza. Muftahu ya fita domin nema masa ison shiga ciki, a lokacinne yasamu yay dariyarsa mai isarsa, lallai Galadima akwai kishi, tashin hankali, irin wannan ajiyar zuciya haka.

*********

Tunda na shiga Munubiya take bina da kallo, ta ce, “ina yaran?”. “Suna can”. ‘nafad'a ina shigewata ciki’. K'ala bata sake cewaba tafita abinta.

Har dare ina fushi, nak'i kula kowa, innarmu yitai kamarma batasan inayiba, dukda batasan mike damunaba, Munubiya ma shareni tayi, sai laraba Ce ke tambayata kodai banajin dad'ine?, nace a'a.

__________

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull