Raina kama book 1, 2, & 3 - Chapter 66
Raina kama book 1, 2, & 3 Chapter 66: Raina kama book 1, 2, & 3 Chapter 66. Barcin yaran baiyi wani nisaba suka kuma farkawa da kuka, Dan yunwa ta hanasu…
4,435 words
Barcin yaran baiyi wani nisaba suka kuma farkawa da kuka, Dan yunwa ta hanasu barcinma. Momma tace Samha tahau saman taga idan sun tashi. Da to ta amsa tana hawa saman. Amma saita iske ko ina tsitt, babu alamar motsin mutum. Dawowa tayi ta sanarma Momma basu tashiba, ga Abdurraheem harwata shid'ewa yake saboda kuka, shi dama baida jimirin yunwa, sauran y'an uwansa sunfiahi hak'iri, ga matsalar ciwonsa da ba'aso ya yawaita kuka. Babu shiri Momma ta jawo waya, zata kira Munaya saita tuna ai wayartama Na d'akinta, Dan haka ta maida akalar kiran ga Galadima.
Cikin barci yaji wayarsa Na ring, da k'yar ya iya mik'a hannu ya d'auka yana guntun tsaki, shi baima San a Yaya yay picking call d'inba, yadai saka a kunne kawai cikin yanayin barci yace, “waye?”. Mamaki ya kama Momma, wato bama su tashiba?. Tace, “Kabarmin yarinyata tazo ta shayar da yara kaji malam”. Babu shiri ya watsakke, saidai kafin yace wani Abu wayar ta yanke, kansa ya dafe danjin Momma Ce Ashe, ya kalli Munaya dake barcinta har yanzu, harga ALLAH tana buk'atar hutu, baison tashinta, saiyaji inama yabari yaran sunashan madara tun farko, aikam yanzu dolene ya nemota, Dan can zasu dinga kwana wajen Momma.
🤣yanzu kuma.
Aunty Mimi tace, “Momma kibata kawai takaisu, Dan wad'annan sakkowarsu aikice kam yau, yarannan kuma yinwa sukeji, ai maganinsa ma, bashine ya hana abasu madara ba, ai da yanzu sai a basu susha su k'oshi”. Momma tai kwafa tana fad'in, “Ai dolensa ya nemota yanzu, Dan bazan iya wannan shelarba kullum nikam, indai yaran nada abinda zasuci sukam su shekara basu fitoba ina ruwan wani, yunwama ta ishesu”. Aunty Mimi dai da jakadiya dariya suketa sha. Samha ta d'auki Abdurraheem ta Goya, sannan ta rike Amaturrahman da Abdurrahman a hannu tahau saman. Knocking tamusu dukda tanajin tsoron fad'an Uncle Sam, amma yazatayi dana Momma kuma. Tasowa Galadima yayi da k'yar, ya d'auka jallabiya ya saka sannan yazo ya bud'e k'ofar. Rissinawa Samha tayi ta gaisheshi, ya amsa fuska babu walwa, itadai duk a d'arare take, kar6ar biyun yayi yafara zuwa ya kwantar sannan yadawo ya kar6a d'ayan. Gudu-gudu sauri-sauri Samha ta sauka tana murnar an rabu lafiya🤣.
Kukan Amaturrahman ya sanya Munaya farkawa, tayi mik'a addu'a d'auke a bakinta ta bud'e ido. Da Galadima ta fara tozali, ya sakarmata wani sassanyan Murmushi yana wani lumshe ido. Itama murtani ta mayar masa da sinne kai saboda kunya. Yace, “Ayi hak'u atashi yunwa mukeji”. Munaya tad'an 6ata fuska tana kuma jan bargo, “ALLAH barcin nan bai isheniba nidai”. “Haba my Queen yi hak'uri please ”. Kamar Munaya bazata tashiba, tadai daure ta tashi zaune tana yamutse fuska, sauka tayi ta shiga bayi tayo brush sannan tadawo. Ya d'ora mata Abdurraheem daya kafa sabon kuka a cinya. “Wlhy rigimarka tayi yawa Abdurraheem, ko kad'an bakada hak'uri”. Galadima yayi Murmushi kawai amma baice komaiba, sai ido daya zuba mata itada yaron. 'Dai-d'ai taringa shayar dasu, yayinda Galadima ke can gefe saman kujera yana waya da latsa lap-top, da alama kiran mai muhimmancine. Nidai nagama shayar dasu natashi, duk saman sofa Na maidasu Na gyara gadon tsaf, harna kammala bai gamaba, koda nazo shara da Morphing ma yanata wayarsa, nagama kimtsa d'akin fes na shiga bathroom shima Na tsaftace sannan nakoma falon, dukda babu datti shima saida Na kuma gyarawa, ina jiyo hirarsu Momma a k'asa amma banyi yunk'urin saukaba, danni yau bammasan ya za'ayi Na sauka k'asaba, kunyar kowa nakeji wlhy.
A tsaye Na iskeshi yana k'ok'arin d'aura towel idonsa akan yaransa daketa kalle-kalle. Muka had'a ido ya d'agemin gira da fad'in “zanyi wanka”. Da to Na amsa masa na shige bayin danna had'a masa ruwan wankan. Ko kad'an banji shigowarsa ba, saida na d'ago da nufin fita naci karo da mutum, baya nayi zan fad'i yay saurin taroni na dawo jikinsa. “Nikam kabani tsoro”. Nai maganar a shagwa6e. “Sorry”. Shima ya fad'a yana k'ok'arin saka idonsa cikin nawa amma nak'i. Nace, “Ga ruwan, bara naje karsuyi kuka”.. Hannu yasa ya rufe k'ofar yana jana cikin bayin sosai, “Bawani kuka da zasuyi, yau duk zame-zamenki tare zamuyi wanka Matar Sameer”. Cikin waro ido nace, “Tarefa?”. Saukar ruwa naji ajikina. Yace, “ga tabbaci ma”. Inaji ina gani doledai akayi wankannan, Wanda shiriritar da muka tsaya tajamu tsawon lokaci.
Aunty Mimi ta had'a breakfast a babban tire tabama Samha takai musu, taita knocking ba'a bud'eba, saita d'an tura k'ofar ta lek'a, babu kowa a d'akin sai yara a kan gado, saikuma ta jiyo motsin ruwa a bathroom, hakanne yasata fahimtar wanka suke kenan, d'aukar tiren tayi ta shige cikin ta ajiye, a ranta tana fad'in soyyaya ruwan Zuma, duk d'aurewar Uncle Sam da k'asaitar nan tasa Ashe zai iya soyayya, Ashe mu aka raina aita mana mazurai da harara.😂
Bayan mun gama shiriritarmu muka fito fuskar kowannen mu d'auke da farincikin kasancewa da juna, yaran duk sunyi barci, ya zauna gaban mirror yana fad'in “Kashmir fa zamu wuce yanzunan”. Da mamaki na kallesa ina fad'in, “Kashmir fa?”. Hannuna ya kamo ya d'orani saman cinyarsa, yawani k'ank'ance idanu yana kallona, “To bakece kika Sani dawowar doleba my Queen, tunda nasamu kin sauka ai saimu koma tare”. Hannuna na d'ora saman kwantaccen sajensa dake jik'e da laimar ruwa ina fad'in “Kai dai ka koma abinka, ALLAH inajin kunyarsu Momma”. Murmushi yayi ya kama hannuna yad'an ciza. Kukan shagwa6a na sanya masa ina yarfe hannun. “O, my Heartbeat ingani yayi jini?”. “Ai saina rama”. Na fad'a ina lalubo nasa hannun nima. Dariya ya sanya da k'ok'arin 6oyewa, kad'an garage mu fad'i daga saman stool d'in, Dan yamana kad'an. yakuma cizona a kunne kad'an. Kukan shagwa6a na kuma sanya masa da fad'in bazan yardaba. Biyemin yay mukai tayi yana dariya da zagaye sofa akan saina kamashi na rama, amma yak'i tsayawa, gashi dagamu sai towel, saida ya tabbatar nayi laushi sannan ya fad'a saman Sofa yana dariya da sauke numfashi, jawoni yay na fad'o jikinsa nima ya rungumeni. “Sorry Yalla6iyana bazan sakeba kinji, inga kunnen shima koya huda”. Na turo baki gaba da mik'a masa kunen, “Bagashi harda jiniba”. Nanma dariya ya sanya, “Yaushe kika koyi sharri kuma?, saikace wani mai hak'orin zaki”. Dariya nayi inad'an dukan k'irjinsa kad'an. Nace, “wama yasani ko irinsa gareka, ALLAH akwai zafi”. “Rakinki yayi yawa my Queen, nidai tashi kibani abinci naci, fita zanyi Akash na jirana, kinsan d'an matsalarnan bikinsa yataho”. “A lallai kace munada shan shagali”. Hancina yaja cikin tsokana yace, “idan baki fara laulayiba sannan ko?”. “Laulayi kuma? Nami?”. “Na abin cikin kwan mana, kina tunanin banyi ajiya bane jiya?”. Sauka nayi daga jikinsa ina fad'in “Ka rufan asiri my King, ina zani da wad'annan ma dake gabana?”. “Duk ki had'a mana babie na”. ALLAH ya kiyaye na fad'a a zuciyata, a fili kam bance uffanba. Tsaf muka shirya kanmu, sannan mukayi breakfast a makare. Yayi k'yau cikin fararen suit, sai zabga k'amshi yakeyi, nikam sket da Riga na lass na sanya, kusa dani ya zauna, ya sanyani jikinsa yay mana photo, sannan ya sumbaci la66ana. Nad'an murmusa da maida masa murtani, cikin lumshe ido yace, “Thanks my Everything”. Far nayi da idanu cikin kissa nace, “ALLAH ya tsaremin kai”. “Amin” ya fad'a yana mik'ewa. Ya matsa ga yaransa dake barci duk ya sumbaci kumatunsu sannan muka fito.. Iya falon saman na tsaya ina masa adawo lafina. Harya fara taka steps d'in ya tsaya, juyowa yay yana kallona, “Wai kina nufin iya nan zaki tsaya?”.. “Nidai wlhy kunyar su Momma nakeji”. Dariya tabashi, amma sai baiyiba, yay murmushi yana cigaba da sauka abinsa.
Shi kansa dai daya sakko k'asan sai kunya ta kamashi, ganin Momma da Aunty Mimi duk suna falon, saiya samu kansa dak'in yarda su had'a ido. Aunty Mimi Ce kawai tayi k'aramar dariya, amma Momma yitai tamkarma batasan inda ya dosaba, saima ta shiga yaba kwalliyarsa da tambayarsa sai ina kuma?. Ganin Momma ta share shima saiya fuske yay mata tamkar yanda ya saba, yasamu ya fice abinsa.
*****
Ni dai kam nakasa sauka kasa, ganin kad'aici da kewar Galadima zata fara addabata saina d'auki waya na kira innarmu, hayaniyar danaji a gidan yasani tambayar mike faruwa?. Innarmu tace, “To sarkin son gulma basai kinjiba, ya kuke?”. Dariya nayi, nace, “Kai innarmu Dan ALLAH kid'an gumtsamin”. “O ni Ai'sha ALLAH ya shiryeki Munaya, wato dai bazaki canjaba kekam?”. Nanma dariyar nayi harda k'yalk'yatawa, “Kai Innarmu na canja mana, kinsan gidan namune sai a slow, nasan dai yanzu duk kin wuce da iskancinsu d'innan?”. Itama dariya tayi daga can. Tace, “Ai tsakanina da kowa yanzu sai girmamawa, ni dariyama suke bani, Safara'u ce wai mijinta zai k'ara aure, shinefa inaga ta tada hankalinta taita zuba masa rashin kunya ya shashshek'a mata mari, to jiya dai a gida ta kwana, kinsansu da gutsiri tsomar tsiya, wai Jamila tashiga gaida Hadiza ta iske suna gulma itada Mero, shine taje tasanarma uwar tasu, wannan yakawo wanan fad'an da kikeji, Maman safara'u babu hak'uri tafito tanata zaginsu da fad'in ai ko auren Safara'u mutuwa yayi ba kanta farauba, tunda ga Siyama da Zarah nan a gida tun kafin ita. Shinefa suka kaure fad'a da cin zarafin juna”. “Tofa, ALLAH ya k'yauta to, tosu su mom indai banda take laifinka ka hango na wani ai baikamata su zauna yida waniba ganasu y'ay'an zaune, anriga an koyama yaran gidanan d'aukar gulma wlhy, yanzu kamar jamila tasan ta d'auki zance takaima mamansu, to su Abba duk basa nan innarmu?”. “Wlhy suna nan, kuma duk sunajinsu, shiyyasama danaje nabad'a hak'uri sau d'aya naga sunk'i saurarena nai dawowata d'aki, Aryaan na kwance yana fama da zazza6i gara Nazo natattali yarona yafimin”. “hhh innarmu kinaji da autaras d'innan nakifa, ALLAH yabashi lafiya, sukuma ALLAH ya dai-daita komai. Hajiya Innaro fa?”. “Tana gidanta mana, bama tajin dad'i kwana biyunnan wlhy, tana fama da ciwon k'afa, ki kirata ki gaisheta, dan jiya gwaggonku Safiyya ma tazo itama”. “To su Innaro kodai gangarawa za'ayine? ALLAH yabata lafiya”. “Ja'ira saidai tsohonki ya gangara, amindai to, ai dama sauk'i”. Dariya nayi kawai. Daganan muka cigaba da hirarmu wadda ta shafemu, nan ma innarmu ke sanarmin Aunty Salamah tazo gidan ansaka aurenta. Cikin tsantsar farin ciki nace, “Innarmu dan ALLAH da gaske?”. “To Munaya ana wasa da maganar aurene? Nasanma zata kiraki ai”. Farin cikine sosai ya mamaye zuciyata, nace, “ALLAH sarki Aunty Salamah komai nada lokaci, anata surutun ta tsufa agida batayi aureba, gashi ALLAH yakawo iyakar, lallai aure da Haihuwa duk lokacine dasu, duk saurin mutum saiya jira ALLAH, ALLAH yabama sauran y'an matanmu mazajen aure nagari masu addini da nagarta, suma mazan haka”. “Amin dai Munaya”. Inna ta amsa itama cikin farin ciki.. Nace, “Innarmu zancen Ayusher fa itama?”. “Itama kwanannan sukace min zasuzo akan maganar, dan kawu Mani ma munyi waya dashi d'azunnan, tsohuwar nan ce tarasu mai ciwon hannun nan, shinema ya dakatar dasu”. “ALLAH sarki Innarmu, badai wadda tabama yara maganin ciwon kai ba?”. “Aiko dai ita, ashe kin ganeta, ALLAH ya d'auke kayansa shekaran jiya wlhy, Abbanku ma zasuje gaisuwa su dukansu harda Baba mai kanwa ”. “Wayyo, to ALLAH ya gafarta mata, amma shi baba mai kanwa ina yaga k'arfin wannan doguwar tafiyar innarmu?”. “Ai ba'anan takeba Munaya, dayake ALLAH yabashi lafiya, yace insha ALLAH saiyaje yaga tushena”. “ALLAH Sarki baba mai kanwa, ALLAH yak'ara lafiya da tsawon kwana”. Inna ta amsa da amin. Munsha hira sannan mukai sallama.
Itama Innaro na kirata namata ya jiki, daganan muka gaisa da gwaggo Safiyya da aunty Habiba. Na kuma kira Munubiya, sosai mukasha hira, take kuma bani labarin auren Aunty Salamah dayazo kamar ha6o. Tace, “Alhajinan dai dayayta naci wanda muke cema Cingom Alhaji dai shine mijin”. “Oni rayuwa, Sweetheart kinga hikimar Ubangiji ko, idan yazo muyita masa iskanci har ita aunty salamah d'in Ashe dai shine mijin, gaskiya ya cancanci ta auresa, wajen shekaru biyarfa bawan ALLAH nan baita6a gajiyawaba”. “Wlhy kuwa Sweetheart, son gaskiya kenan ai, ga Ayusher nan anata soyewa itada Hamma Youseeff, duk wannan shan k'amshin nasa ya mace mata, Yaa Fadeel ma in fad'a miki shida Badeerah Ashe sun k'ulle”. “Dan ALLAH da gaske ko wasa?”. Cikin Dariya Munu tace, “Wlhy kuwa, waike bak'ya waya da kowama kenan?”. “Wlhy ba haka bane kemakinsan d'an tsakaninan damuwar data hanani sukuni, amma yau dolene na kirasu nasha kanu, shegiya Ayusher bara itama na kirata, dukda kud'ina sun kusa k'arewa, a gaidamin da Sweetness babies d'ina da Yaa Marwan inya dawo”. “Zasuji insh ALLAH, asha amarci lafiya, aidai kulamin da yara kar soyayya tasa abarminsu su rame”. Kafim nayi magana ta yanke kiran. Dariya kawai nayi ina girgiza kai, alokacinne Samha ta shigo. “Ah lallai aunty gimbiya yau Uncle Sam ya 6oye mana ke, Momma Ce tace yau bazaki sakko bane?”. “Dan ALLAH da gaske?”. Nai maganar cikin waro idanu. Dariya ta sanya, “Wlhy kuwa da gaske nake”. “Ni munaya naga idi, ALLAH kunya nakeji”. “Kam kunyafa aunty gimbiya, to miye najin kunyar? Wlhy ALLAH yabani miji irin Uncle Sam a gabanki zan mak'alk'ale abina”. Duka nakai mata ta kauce tana dariya.
******
Cikeda jin kunyar su Momma na sakko k'asan, amma saisukayi tamkar basusan minike mawaba, tun ina sunne-sunnen kai hardai na warware nasaki jikina kamar yanda nasaba. Momma da Aunty Mimi sunji dad'in haka, a zukatansu suna mana addu'ar d'orewar zaman lafiya nahar Abadan.................✍🏻
Inaga sai Monday zakujini, kuyi fatan nama kammala gaba d'aya😅🤝🏻👌
ALLAH ya gafartama iyayenmu😭👏🏻
♦RAINA KAMA...!!♦ (Kaga gayya)
Bilyn Abdull ce🤙🏻
BOOK 3 👉🏻2⃣8⃣
.................Har yamma Galadima bai dawo gidanba, abincin ranama da aka ajiye masa sai d'aukeshi akayi, sainaji inajin tausayinsa, dan nasan yanacan ba zaune waje d'ayaba, yawan harkoki dayakeyi kansa kullum yake yawo tamkar wata motar haya, shidai kullum burinsa ya iya d'aukar nauyin ahalinsa, bai yarda zama rago ko jira daga waniba koda ace papi ne, ya yarda yasha wahalar nema amma ta gumin halak, sa6anin matasanmu da kullum burinsu nakan gwamnati ko alhajin anguwarsu ko d'an siyasa, ko alhajin da yafi kowa arzik'i a danginsu. Akwai wata kalma da Galadima yata6a fad'ama sauban Wanda akulum Na tunata tana k'ayatar dani. Lokacin inada tsohon cikinsu Amaturrahman, da yawan cin abincinnan Na masifa, aranar jikin Abie yad'an motsa, sai yakasance nikad'ai aka bari a gida sai hadiman gidan, cikin barci yunwa ta addabeni, hakan yasani farkawar dole Na sakko k'asa da k'yar, kitchen Na shiga nasami madara Na d'umama kafin kuku yad'an girkamin wani Abu, fitowata daga kitchen d'in keda wuya sai Galadima da Sauban suka shigo, da alama ya tuk'osane, dan idan yana cikin damuwar tashin ciwon Abie Momma hanashi driving takeyi. Da mamaki Sauban ya kalleni da cup a hannu yana fad'in “Yanzu nan Aunty duk hadiman gidannan saikin shiga kitchen da kanki a wannan halin? Aiko yau saisun gane kuransu”. Ya tafi fuuuu cikin fushi saina dakatar dashi ina murmushi. Nace, “A'a Yaa Sauban, kabarsu please, nice ban sasunba nayi da kaina, amma aiga shican nasaka kuku wani aikin”. Galadima dake zaune saman kujera ya d'aura k'afa d'aya kan d'aya idonsa a lumshe tamkar baisan mi mukeyibama ya bud'e baki cikeda k'asaitar nan tasa yana fad'in, “Ai duk Wanda ya dogara da k'arfin wani to lallai nasa na cikin jerin k'arewa a sahun marasa amfani, dan zai dawwama cikin bibiyar samu daga waninsa shikuma bai amfanu datasa fik'irarba, kazama mai k'arfin zuciyar gina kai ba zaman jingina da bangon waniba”. Yana gama fad'ar haka ya tashi ya haye sama, dagani har Sauban da kallo kawai muka bishi, kowa na fassara zancensa dalla-dalla, ni abinda na fahimta kai tsaye bada Sauban d'in yakeba, akwai abinda yafaru daga can inda suka fito, amma saiya za6i mu yamana sharhi bisa dalilin dashi yabarma kansa Sani. (ALLAH dai ya ganar da matasanmu domin tashi su nemi na Kansu ta hanya mai k'yau basu cigaba da dogaro a bangon wasuba.👏🏻😢).
Tun d'azun yake tsaye akanta amma bata saniba, ta Lula duniyar tunani mai zurfi, ga Abdurrahman dake gefenta yanata mutsu-mutsu da k'ananun kuka amma batama jishiba. Agabanta yay wani durk'uso mai birgewa, yakai fuskarsa daf da tata yana hura mata iska a saman ido zuwa hanci. Wata sassanyar ajiyar zuciya na sauke tareda dawowa hayyacina cikin zabura, yay azamar damk'e hannuna da fad'in “My Mata!?”. Ajiyar zuciya na sauke tareda dai-daita dan fahimtar shine, na zuba masa idanu cikin mamaki nace, “Yaushe ka shigo?”. Murmusawa yayi sannan yamik'e daga durk'uson dayay agabana, batareda ya bani amsaba ya fara k'ok'arin cire farar rigar suit d'insa. Mik'ewa nayi na taimaka masa, sannan nadawo gabansa na warware tia.. 'Din da bottoms d'in pink d'in rigarsa ta ciki. Sai wani faman lumshe idanu yake da bud'esu akaina, bansan miyake tunaniba. Ina cire bottom d'in k'arshe na rigar ya rik'e hannuna, idanu na d'ago na kallesa, ya sakarmin wani k'asaitaccen murmushi yana matsoni jikinsa sosai, a saman la66a ya furta “Kinyi k'yau sosai, amma mikike tunani haka?”. Da mamaki na kalli kaina, sanye nake doguwar rigar shadda milk color, anmata simple aiki da brown d'in zare, an k'awatashi da stones, Wanda sune suka fidda ainahin k'yawun d'inkin, sai siririyar sark'a data kwanta a wuyana d'as, nayi d'aurin Maryam babangida daya kuma fidda ainahin suffata ta bahaushiyar asali mai rik'o da al'ada. Yanda nake bin jikina da kallo haka Galadima kebi shima da idanunsa, na maida kallona ga face d'inshi dake kadaran kadahan, bai d'aureba kuma babu walwala sosai tare dashi. Gira d'aya ya d'agemin sai kuma yad'an ta6e baki yanajan hancina da had'e yatsunsa biyu na k'arshe👌🏻alamar komai yaji. Nad'an murmusa ina k'ok'arin barin wajen dan naga alamar miskilawan suna kusa. Ruwa naje na had'a masa, na fito ina goge hannuna da towel. Durk'ushe na iskeshi gaban Abdurraheem da cup d'in ruwan dana ajiye danshi a hannunsa. Ya d'ago yana kallona dad'an murmushi a face d'insa, “kinsan minake gani a jikin Abdurraheem kuwa?”. Kaina na girgiza masa alamar a'a. Kallonsa ya maida ga yaran yana cigaba da murmushinsa. Yace, “Kamannin Abie”. Takowa nayi Inda suke Nima Ina murmushi mai sauti da fad'in, “Nadad'e da wannan tunanin a raina, saidai nabarma zuciyatane har sai randa zan gansu a waje d'aya, Ashe kaima kana lura?”. Wata y'ar dariya yayi, wadda tafi kud'i tsada awajensa. Yace, “My Heartbeat ALLAH kin iya haihuwa”. Ba k'aramar dariya maganarsa tabaniba, aiko nashiga k'yalk'yalawa. Shiko ya shagala da kallonta saboda birgeshi da dariyar tata tayi, burinsa dama yaganta cikin farinciki. Bayan na tsagaita da dariyar na kallesa Ina d'aga kai da kashe masa ido alamar kallonfa?. Mik'ewa yay tsaye ya dawo inda nake tareda rank'wafowa kaina yana dafa hannayensa biyu asaman gadon gefe da gefena. Kusancin namu yasakani d'anyin baya kad'an ina kallon cikin idonsa, yakuma matsowa, na matsa, yakuma again, Nina still na matsa, saida na haye gadon sosai shima yay balance yanda yake buk'ata sannan ya kwanto gefena kusan Rabin jikinsa a nawa, har lokacin idonsa na sark'e da nawa. Galadima yay bala'in Sanin sirrin kallo, inhar ya sark'e idanunsa da nawa duk wani hope d'ina nemansa nakeyi na rasa, yatsansa kawai naji saman la66ana yana zagayawa ahankali, santsin hannunsa Dana lips gloss d'in Dana sanya sunayin kamar susa, kasa jurewa nayi na lumshe idanuna a hankali. Galadima ya murmusa da bud'e baki da k'yar yana fad'in, “Kin cancanta, kin cancanta zama matar Muhammad Sameer Munaya, ked'inki da dukkan halayyarki irinta Muhammad Sameer ke buk'ata ga matarsa, ko ayarda ko kar ayarda nasan nama sauran maza zarra, dan matata tafi ta kowa, kinzama fitila mai hake gabana da bayana, kinzamarmin bango abin jingina lokacin danawa yanemi rushewa, shigowarki rayuwata na dai-dai da farkawata daga nannauyan barci mai cikeda rud'ani, nabaki dukkan zuciyata ki jani a sannu danna cigaba da ribantuwa da ni'imomin da ALLAH ya azurtaki dasu, I love you so much Munaya, I love you har a aljanna matsayin uwargidan matana”. Bansan lokacinda hawayen farinciki suka fara zirarominba, na bud'e idanuna dakai hannu saman kwantaccen sajensa ina shafawa a hankali, cikin wani yanayi nace, “Ka cancanci fiye da haka mijina, dan kanada zinariyar zuciya, kaimai tarin tsoron ALLAH ne dabin dokokinsa, a wannan zamanin samin matashin saurayi mai kud'ad'e da mulki a hannunsa dabaya wata masha'a abune mai wahala, baka kasance mazinaci ba, baka kasance mai shaye-shaye ba, ko sigari wannan bakasha, kulum cikin Neman halalinka kake Dason k'yautatama iyayenka dana k'asa da kai, kaimai ibadane, salla bata wuceka, mai yawan tsayuwar dare, mai yawan bitar littafi mai girma dake d'auke da zancen ALLAH ne, mai yawan sadaka da taimakon mutanen da bakuma had'a addiniba, bakada wata majalissa ta abokai daza'ace gaka cikin jerin masu cin naman wani ko zind'en wani, abinda ke gabanka da Wanda ALLAH ya halatta maka kawai kakeyi, mijina tayaya bazaka samu nasaroriba a rayuwarka? Ubangiji mai ni'imane ga dukkan Wanda ya ra6u samun ni'imar, babu wani Bawa dazai tsinci kansa a ta6ewa inhar yabi dokokin Ubangiji da koyi da manzon tsira, babu cuta mafi rad'ad'i da ciwo kamar bijirema Umarnin ALLAH Wanda ayanzu shike wahal da matasan duniya irinka, burunsu kawai su hole su mori k'uruciyarsu, sun manta babu tagomashi mafi k'yak'yk'yawan farashi irin morar k'uruciya bisa ga Umarnin ALLAH, yadda da k'addara, samu ko rashi, tsayawa matsayin da ALLAH ya ajiyeka, kaucema dukkan wata bad'ala, matasa sune k'ashin bayan al'umma, lalacewarmu ta saka al'ummar tafiya a karkace a halin yanzu, da'ace zamu gyara da kowa ya mik'e, dolene Momma da Abie suyi alfaharin samun d'a irinka, dolene Aunty Mimi da Yaa Sauban suyi alfaharin samun d'an uwa irinka, dolene su Samha dasu Amaturrahman suyi alfaharin samun Uba irinka, dolene k'asarka da addininka yayi alfaharin samunka, saidai duk nice nafisu sa'a da alfaharin samunka a matsayin miji uban y'ay'ana, inaji inama y'ay'yana su gaji k'yawawan hallaya da d'abi'u irinna mahaifinsu, saidai kash ina cike da fargabar tsoron kalmarnan ta bahaushe dakance Bakowanne tauntsu bane ke raira kukan gidansu wani tun a koyan tashi yake canja salo. Mijina ka more, ka matuk'ar morewa da k'yawawan hallaya, irinku kunada tsadar samu a cikin al'umma, da mutane zasu gane dasun fuskanci ba k'yawun fuska dana jiki bane abin alfahari, zinariyar zuciya da hallaya shine abin alfahari da d'agawa, saidai kash, burin samarin yanzu da y'ammata k'yawun fuska dana halitta, nauyin aljihun wayewa, basa tunanin mika tara mizaka taras, sannan mika barma bayanka da ahalinka Wanda ko bayan shekaru aru-aru tarihi bai Isa mantawa da kai ba, da inada dama sainabi matasan mata da maza dukna musu allura sunzama kamarka mijina, inasonka, ina sonka, zan fad'a a hankali, nafad'a da k'arfi, na fad'a da kuwwa, na fad'a da ihu agaban kowa kuma, Kaine duniyar Munaya, Kaine farincikin Munaya, zanta k'aunarka har randa nufashina zaibar gangar jikina, nakumayi fatan ganina a cikin matanka dake aljanna Muhammad Sameer”. Kasa magana Galadima yayi, sai bakinsa ke motsi alamar buk'ar firta wani Abu amma yakasa, idonsa yacika taf da kwalla, lallai hikimar zancema baiwace ga mace tagari, dashi kawai zata iya mallakar mijita babu boka babu Malam, dan gashi Munaya tasamu dukkan nasarori, ya rungumeni tsam a jikinsa tareda d'ora bakinsa saman la66ana, hawayen dayake rik'ewa suka gangaro saman fuskata. Banyi yunk'urin ko motsawa ba nabashi wuk'a da nama yayi yanda yakeso ni halalinsace..........😘👍🏻
Hummmm, lallai matar kwarai rabin addini, ya ALLAH kabamu damar zama matan kwarai ga mazajenmu😢🙏🏼.
***
Bayan shud'ewar wani lokaci muka dawo daga duniyar da muka tafi, kunya duk sai ta kamani, nakasa had'a ido dashi. Galadima ya murmusa yana kama hannuna zuwa hanyar bayi, banida za6in daya wuce na bisa kawai. Yauma dai tare mukayi wankan, nad'an sake dashi fiyeda d'azun da safe. Muka fito na taimaka masa da shafa mai, yasaka kaya marasa nauyi. Nima da taimakonsa na kimtsa sannan na sauka nemo masa abinda zaici dukda magrib ta gabato. Babu kowa a falon sai Khaleel dake homework. Sannu namasa shikuma ya gaisheni, nace, “Ina Samha my boy?”. Yace, “Aunty yanzu aunty Dhibiya tazo suka fita”. Agogon falon na kalla da mamakin fita a yanzun? Halan batasan Uncle d'inta ya dawoba?. Bance komaiba na wuce kitchen. Da taimakon kuku na shirya masa Abu mara nauyi, na had'o saman tire ina fitowa. Samha data shigo tad'an kalleni a firgice, nima kallon mamaki nake mata da tuhuma. Nace, “Daga ina haka?”. Kame-kame tafara na lalubo amsar dazata bani, wadda alamunta ke nuna k'aryace kawai zata fad'a. Girgiza kai nayi kawai nai gaba abina ina fad'in “Zanso sanin mike tsakaninki da Dhibya Samha? wannan abotar taku k'arfinta yafara tsoratani”. Banjira amsarta ba na haye saman benen. Gudun karya fahimci wani Abu na daidaita kaina tunkan na shiga, nasan inhar yasan raina ya6aci akan Samha ne sai taci k'aniyarta, nikam ba buk'atata ba kenan, nafison sanin tsakaninsu da k'awartata kafin na rabasu. Tsaye na iskeshi rik'e da abin salla, na ajiye tiren saman table d'in gaban sofa sannan na kalli agogo. Yanda banyi magana ba shima baiyiba, na nufi bayi nayo alwala nima, tsaye na kuma iskeshi yana jirana.
Bayan mun idar da sallah na kallesa ina fad'in “Abinci yalla6ai”. Harara ya zubamin da rankwashi, na dafe wajen ina kwa6e fuska zanyi kuka. Yace, “Yalla6ai d'inan bazai bar bakinkiba ko?”. Dariya namasa da gwalo inaja baya, “Yo ba sunanka baneba”. “Da kika rad'amin ko? Zan kamakine ai”. Sanin halinsa yasani fad'in, “Toyi hak'uri bazan sakeba”. “Harkin karaya kenan?”. “Ba doleba, kamun nakane ai bamai sauk'iba”. Dariya sosai tabashi, amma ya had'iye abunsa kawai yayi murmushi yana cizar lips. Munaya tace, “Wato a rayuwa duk d'an Adam zaka sameshi dawata d'abi'a data zame masa jiki”. Kallona yayi da alamar tambaya, amma baice komaiba. Mik'ewa nayi tsaye ina cire hijjab da fad'in, “Cizon lips yazama maka jiki, harya zama d'abi'ar dake yawan birgeni agareka”. Lips d'in nasa ya ciza sannan ya saki wani k'asaitaccen murmushi da girgiza kai, Munaya kenan sarkin k'uruciya. Yafad'a a zuciyarsa yana mik'ewa shima.
Saman sofa ya zauna yana d'aukar system ya d'ora a cinyarsa, ganin haka saina sauke tiren Dana ajiye a saman table na tura masa gabansa, nasansa akwai son d'ora k'afa, abinka da jinin mulki. Aiko saiya maida k'afafunsa duk biyu akai yana fad'in “thanks”. Bance komaiba sai murmushi dana d'anyi, na zuba abincin ina zama kusa dashi, tunda ya d'auki lap-top d'inan hanyar zamewa cin abincin yake Neman k'irk'ira, kuma saiya cishi. Nace, “to yanzu ya za'ayi? Ga abinci”. Batareda ya kalleniba yace, “Kici da nawa kawai ya wadatar”. Ni dariyama ya bani, amma na daure banyiba, “Nikam ina mamakin yanda kake k'in abinci saikace wani Khaleel”. Murmusawa yayi hankalinsa nakan aikinsa. Yace, bazaki ganebane, nifa wlhy abinci takuramin yakeyi, shiyyasa ko sau d'aya nacisa a rana ya watar dani”. Nace, “Nikam dai ban wadatuba, bud'e baki wannan bashida nauyi, nasandai gudun k'aton ciki kake kawai”. Dariya ya sanya kawai. Nima nad'an dara ina kai abincin bakinsa. ALLAH yanzu saikaga mutun nata hora kansa da yunwa wai karyayi k'iba, shikuma ALLAH ba ruwansa, idan haka yayoka ko ruwane kawai abincinka sai kayita”. Abincin ya shiga taunawa da murmushi saman fuskarsa hankalinsa nakan system d'in.