Raina kama book 1, 2, & 3 - Chapter 67
Raina kama book 1, 2, & 3 Chapter 67: Raina kama book 1, 2, & 3 Chapter 67. Haka nacigaba da bashi abincin da janye hankalinsa da hira, yayinda yake…
4,447 words
Haka nacigaba da bashi abincin da janye hankalinsa da hira, yayinda yake aikinsa da saurarena, idan na murmushine ya murmusa, Wanda zaiyi magana ya amsamin a tak'aice, Wanda tuni na fahimci al'adarsace tak'aita magana yabaka a dunk'ule kawai ka fassara sauran. 'Dagowa yay fuska a marairaice, “My mata ki tausayamin hakanan cikina karya fashe”. Dariya nayi da nuna masa plate d'in daya koma empty. Ya waro idonsa waje yana shafa ciki, “Dan ALLAH da gaske kike dukni na cinye?”. Nakuma tuntsurewa da dariyar danake dannewa, “Yo dawa kukaci? Wlhy duk kai kacinye harma d'an k'arawa nayi”. “Chiii yarinyarnan kin gama dani, amma gama dariyar muguntar ai kanki zata k'are wlhy, ke zakiji nak'ara miki nauyi”. Dukda na fahimci inda ya dosa saina shareshi ina cigaba da dariyata, nama mik'e daga kusa dashi. “Humyim zaki gane kuranki ne”. Yay maganar yana cije lips.
Da lokacin isha'i ma yayi shine ya jamana jam'i, ya kuma komawa kan aikinsa, ganin aikin ya d'auke dukkan hankalinsa saina d'auka wayarsa Na kira su Zuhuriyya y'an Niger, muka gaisa dad'an ta6a hirar zuminci cikeda nishad'i. Sannan Na kira aunty Salamah itama nasha labari. Ganin harna gama wayoyina yana aikin still saina d'auka Novel d'insa d'aya nai zaman karatu. Sai wajen 10 ya dafe kai yana sauke ajiyar zuciya. Kallonsa nayi da tausayawa. Nace, “Ka huta haka nan mana my king”. Huci yakuma furzarwa yana k'aramin tsaki, ya taso daga gaban tebir d'in ya dawo bakin gadon ya zauna. Hannunsa Na kamo, Na kwanto kansa bisa cinyata inad'an shata goshinsa, idonsa a lumshe yace, “wlhy sonake naga na had'a kud'in jirgi da abubuwan buk'atar mu idan zamu wuce Nigeria, Dan Dr Erfan Fahad yamin albishir da k'arshen watannan insha ALLAH zai sallami Abie, gashi ina cikin matsalar kud'i Munaya, narasa yanda zanyi, bazai yuwu Na kwashe kud'in kasuwa Na narkarba kuma”. Ajiyar zuciya Nima nayi cikin damuwa, ganin ya bud'e idonsa saina murmusa ina d'an matsa masa kafad'unsa. Nace “ga shawara to”. “Ina saurarenki”. Yafad'a cikin maida hankali gareni tareda hard'e hannayensa a k'irji. Yatsana d'aya Na d'ora saman girarsa ina kwantar da gashin a hankali, “My King mizai hana gifts d'in dana samu Na aure da haihuwar yarannan kayi amfani da kud'ad'en ciki, abinda ya kasance Na kud'i a siyar dashi Dan banga amfanin ajiyesuba ai”. 'Dan Murmushin gefen baki yayi yana lumshe ido, sannan ya bud'e a kaina, “Munaya duk abinda aka baki ko yarana halalinkine, idan Na kar6a nazama mai handama kenan, ta wani faninma zaluncine, nine yakamata Na baki domin sauke wasu nauye-nauyenki Na y'an uwa da makamantansu, saikuma Na amsa Dan nine baba rodo sarkin babakere”. Na 6ata fuska ina janye hannuna daga saman girarsa dukda dariyar da furucinsa Na k'arshe ya bani, “Shikenan tunda baka d'aukeni yanda Na d'aukeka ba, yanzu tsakani da ALLAH idan kabarni dasu mizanyi dasud'in? Ashe abuna ba naka baneba?”. Nai maganar cikin matso hawaye. Da Sauri ya tashai zaune yana rik'oni amma saina kwace ina niyyar sauka ma gaba d'aya daga gadon. Gaba d'aya yasani a jikinsa yana fad'in, “Sorry tsaya muyi magana to kinji my sweetness, ya kikeso ayi yanzun?”. Hawayen nakuma sharewa nace, “Ka kar6a kawai”. Shiru yay yana kallona da nazarin maganar, saikuma yad'an numfasa yana gyara zama. Yace, “to ai naga suna Nigeria? ”. “A'a suna nan, Dan dukna had'osu Na taho dasu wannan karon”. “Ok babu damuwa, da safe zamuyi magana, shirya yara nakaisu wajen Momma dare nayi nafara jin barci”. Naji dad'i daya amince zai kar6a, Dan haka Na rungumeshi ina dariya. Bayana yad'an bubbuga kawai yana cewa “jeki shiryasu”. 'Dagowa nayi ina kallonsa, “Amma my King zamuke takura mata itama ai, ka barsu kawai”. “Babu wani takurawa, bazaki gane bane y'ammatana”. Babu yanda Na iya, dan babu jayayya a tsakaninmu, shiryasu nayi Na shayar dasu kowanne yay d'if, ya d'auka biyu yakai yadawo ya d'auki d'ayan shima. Nikamdai wannan Abu ya girmeni, amma babu damar magana.
Ya dawo yana dariya da bani labarin gargad'in da momma tamasa akan wlhy mu tashi da wuri, kokuma da anyi sallar asuba yazo ya d'aukesu, Dan bazai yuwu ake barinsu da yunwaba. Sai Na k'arajin duk kunya ta lullu6eni, amma shi ko'a kwalar rigarsa, saima wata tashar daya kamo.
A gurguje please😊.
********
Washe gari ya koma Kashmir, yaso mu tafi tare amma Na nuna masa Momma yakamata ta fara zuwa, Dan tunda aka kai Abie babu Wanda yaje saishi kad'ai. Daga baya dai sai muka tsaida shawara akan zaije yafara ganin halin da ake ciki a yanzu, da wannan shawarar yatafi. Ba k'aramin abin mamaki Dr Erfan ya shiryama Galadima ba, shiyyasa gaba d'aya ya hanashi ganin Abie. Da yamma lik'is Galadima ya isa Kashmir, saboda bai tafi da wuriba, kai tsaye asibiti ya nufa dukda yana tunanin mawuyacine ya samu Dr Erfan Fahad a can, saboda lokacin tashinsa aiki yayi, saidai idan wani muhimmin aiki ya tsaidashi ko Emergency ya riskeshi. Ilai kuwa a harabar asibitin Galadima yaci karo da Dr Erfan Fahad ya fito zai wuce gida, sosai Dr Erfan Fahad yay mamakin ganin Galadima, Dan basuyi waya yana hanyaba. Ya bashi hannu sukayi musabaha da rungume juna, “wai my friend dama kana hanya?”. Galadima ya murmusa da shafa kansa, “Kabari kawai, ya aikin?”. “Alhmdllh”. “To inaga kawai muwuce gida. Dan wlhy nagaji sosai, yau nayi aikin daya wuce kima”. Galadima yay d'an jim alamar tunani. Murmushi Dr Erfan Fahad yayi yana dafa kafad'ar Galadima, “Sameer nasan kana tsananin buk'atar son ganin Abie ko? Karka damu, kaidai muje gida kawai abokina”. Galadima baice komaiba ya bisa suka wuce, Dr Erfan Fahad nata jansa da hira, amma shi iyakarsa murmushi ko eh da a'a. Ko kad'an Dr Erfan Fahad bai damuba, danya fahimci halin Galadima Na rashin son hayaniya tsaf, dama tun a baya bashida yawan magana, Ashe halin Na nan bai canjaba, saima k'aruwa dayay. Shikam Dr Erfan Fahad mutum ne faran-faran, ko jama'ar dake jiyya namasa wannan shaidar ta yawan tsokana. Ahaka dai suka isa gida, shidai Dr Erfan Fahad yanata murmushinsa. A k'ofar falo ya tsaida Galadima, tareda fidda handkerchief a aljihunsa yace Galadima ya rufe idonsa. Da mamaki Galadima ke kallonsa, amma yagaza furta komai. Dr Erfan Fahad ya jinjina masa kai da had'e hannayensa alamar rok'o. Ruf Galadima ya rife idonsa, Dr Erfan Fahad ya saka handkerchief d'insa ya d'aure masa ido, sannan ya kama hannunsa suka shiga ciki. A tsakkiyar falon ya tsaidashi, ahankali yace, “my friend are you ready?”. Cikin sauke numfashi Galadima ya d'aga masa kai. Dr Erfan Fahad ya murmusa yana kwance masa handkerchief d'in sannan yace, “Bud'e idonka”. A hankali Galadima ya shiga bud'e idanu, harya bud'esu gaba d'aya akan k'yak'yk'yawan dattijo zaune bisa kujera, fuskarsa ta k'awatu da murmushi, yasha gyaran fuska mai k'ayatarwa, sai gashi kad'an mai adon furfura da aka bari ya zagaye fuskarsa. Wata zabura Galadima yay mai kama da firgita, Dr Erfan Fahad yay saurin tarosa, Dan kad'an yarage ya zube a k'asa. Cikin rawar baki data jiki yake kallon dattijon, dak'yar ya iya fusgo numfashi da magana mai cike da in'ina daga bakinsa “A..b..ie k..ai.ne?”. Abie ya share hawayen da shima suke ziraro masa, cikin tsantsar so da k'aunar d'an nasa yabashi amsa da fad'in “Tabbas nine Muhammad Sameer sanyin idaniya, Abie d'inka ne zaune yau agabanka, Wanda ya tashi cike da hukuncin Ubangiji gagara misali”. Galadima ya maida kallonsa ga Dr Erfan Fahad. Murmushi Dr Erfan Fahad yayi, “Karkayi kokwanto da ikon ALLAH Sameer, shike kwantar da Wanda yaso, Yakuma tasheshi a lokacin da yaso, dama ba'a yankema rayuwa hukunci, mai jiyya saiyayi rayuwa mai tsayi amma mai lafiya a wayi gari yazama gawa, ciwo bashi bane mutuwa, kwanaki 10 kacal Na d'auka ina treatment d'in Abie ga66ansa suka fara aiki, a sauran sati uku danayi tare dashi muna koya masa yanda zaiyi tafiyane, da zama, d'aukar Abu, da sauransu, Dan duk ga66ansa sun manta, kamar yanda ka sanarmin addu'ar da kukaita masa lallai itace babban magani daya zama mai tasiri a garesa, domin nikam abinda ba'a rasaba Na k'arasa, duk Wanda yabar addu'a lallai dole matsala tazama ma'abociyar rayuwarsa, a yanzu haka ina mai tabbatar maka Abie zai iya tafiya dayima kansa wasu abubuwa, amma bamasu yawaba, tafiyarma bamai tsaho ba, Dan yawanyin ne zai bama ga66ansa kwari da sabo, shekara 26 mutun Na kwance sai na'urori ke sarrafashi ba k'aramin Abu bane Sameer, Dan dolene akira Abie d'an baiwa, masu irin nasarorinsa kad'anne a cikin al'umma wlhy, kaje ga Abie, domin kuna buk'atar juna”. Tamkar Dr Erfan Fahad yama Galadima allura ne, cikeda sasaarfa ya k'arasa ga Abie, a gabansa ya zube yana sakin wani kuka maiban tausayi tamkar mace”. Abie ya sakko daga kujerar ya rungume jarumin d'ansa shima yana hawaye, sun dad'e a haka, jisuke tamkar karsu saki juna, a tunaninsu Kodai mafarki sukeyi, suna tsoron rabuwa su farka suga ba haka baneba. Shi kansa Dr Erfan Fahad hawayen tausayinsu yake sharewa.
Ni kaina masu karatu wannan lamari yasani hawaye Na gaske😭, da zaka k'iyasta hakan a kanka wane farinciki kake hangowa yayinda waraka ta riskeka?.😭
Wad'annan bayin ALLAH yau lallai suna cikin tsantsar farin ciki, ko kad'an Galadima ya kasa gusawa daga jikin Abie, Yakuma k'i kiran kowa, burinsa shima yabasu mamaki tamkar yanda Dr Erfan Fahad yabashi. A yau yay niyyar su juya amma Dr Erfan Fahad ya hana hakan saidai gobe, Dan dare yayi kam a yau. A gado d'aya Galadima da Abie suka kwana, dukda sunma cinye rabin daren da fira😁.
****
Hankalin Munaya duk a tashe yake, saboda tanata kiran Galadima yak'iyin picking, tun tana daurewa harta gaza tafara kuka da shiga tsantsar tashin hankali. Momma Ce ta lura da canjawarta, ta tambayeta lafiya?. Kasa magana tayi saboda kunya, saida Momma ta kuma maimaitawa sannan tace, “Momma inata kiran Number Abbansu ne yak'i yin picking tun d'azun”. Ita kanta Momma ta kirashi baiyi picking ba, amma ta d'auka ko wani uzirine yasha kansa, sai yanzumefa hankalinta ya fara tashi itama, waya ta d'auka tashiga kiransa amma babu amsa, kusan kira 10. Cikin firgici ta kalli Munaya da aunty Mimi da itama take kan gwada kiran nasa, amma itama ba'ayi picking. “Kinga Munaya tura masa massage mu gani”. Jiki a sanyaye Munaya ta tura massege, amma kusan 30minutes babu reply. Hankalinsu fa yakai k'ololuwar tashi, amma sun rasa mafita.
***
Shikam Galadima baima San sunaiba, wayarma kanta baisan inane ya jefar da itaba, gabaki d'aya hankalinsa ya tattarane ga Abie, harkuma suka kwanta barci bai nemi wayarba.
*****
Yau kam inhar wani yay barci a cikinsu to bana kwanciyar hankali baneba, dan kowa damuwa tamasa katutu, dai-dai da Hadiman gidan suma duk a damuwa suke, sai dai tamkar yanda suka saba yauma sun mik'a lamarinsu ga Ubangijin talikai.
Washe gari
Tunda safe Momma ta nemi Number Dr Akash da Dr Ajey akan rashin jin Galadima, duk sun amsa mata da zasu bincika.
Can kuma su Galadima sun wayi garine da shirin dawowa New Dhalhi, cikin tsantsar farin ciki irin Wanda misaltashi ma 6ata lokacine.................✍🏻
ALLAH ya gafartama iyayenmu😭👏🏻 [7:09 PM, 8/21/2019] +234 813 508 4146: Typing📲
https://2gnblog.blogspot.com/
💡HASKE WRITERS ASSO....
♦RAINA KAMA...!!♦ (Kaga gayya)
Bilyn Abdull ce🤙🏻
BOOK 3 👉🏻2⃣9⃣
https://2gnblog.blogspot.com/ .................Gaba d'aya sun kasa yin breakfast, suna cikin zaman jigum-jigum suka jiyo bud'e gate da shigowar mota. Samha ta fita da hanzarinta danson ganin wanene, fitowar tata tayi dai-dai da fitowar Galadima daga cikin mota fuskarsa d'auke da wani irin k'ayataccen murmushi daya fidda sirrin k'yawunsa. Da gudu ta taho garesa, yakan mata fad'a akan son rungumarsa ko Sauban amma yau saigashi ya bud'e mata hannu dakansa tazo ta shige jikinsa. Ihun murnartace tasaka su Momma fitowa da hanzari suma Ganin Galadima ai sai duk sukayo kansa itada aunty Mimi, itadai munaya gefe ta tsaya tana sharar hawayen farin ciki. Abie dake kallonsu daga cikin mota ya saki murmushi yana share hawaye, yana k'asa d'aya da iyalansa amma bai ta6a sanin muhallinsu ba sai yau, dukda bai shigaba gidan yamasa k'yau. Galadima ya ture Samha daga jikinsa ya rungume Momma da aunty Mimi yana sakin wani irin kuka daya matuk'ar tada hankalinsu. Da sauri suka d'agosa hankali tashe suna tambayarsa mike faruwa? Kodai ALLAH yayima Abie rasuwane?. Cikin kuka da dariya yace kowa ya rufe idonsa . Babu musu sukabi Umarninsa, har Munaya dake gefe. Yace, “kun tabbatar kowa ya rufe?”. A tare suka amsa masa da eh. Ya murmusa da goge sauran hawayensa sannan ya juya ga motar ya bud'e, hannun Abie ya kama da taimakonsa ya fito rik'eda sandarsa mai k'yau dazata dinga taimaka masa wajen tafiya, Dan har yanzu tafiyar batai kwariba. Saida Abie ya jingina jikin Mota ya tsaya da k'yau sannan Galadima yace, “Kowa ya bud'e idonsa”. Har rige-rigen bud'ewa suke. Akusan tare Aunty Mimi da Munaya da Samba suka kwalla k'ara, Momma kam sai tayi luuu sai gata a k'asa kawai ta sume. Abie da Galadima dasu Munaya duk kanta sukai suna kiran sunanta, shima Abie ya tuzgud'e zai fad'i, Dr Ajay daya kawosu yay hanzari rik'esa yana fad'in “A sannu dai Sir, k'afafunka basukai k'warin wannan hanzarinba”.
Da gudu Munaya takoma ciki sai gata da ruwa, ta zuba a hannu tana shafama Momma, da k'arfi takawo Numfashi. Bin yaran nata tayi da kallo tana fad'in “mafarki nakeyi ko yarana? Nasan irin mafarkin dana sabane dama, ba takawa Na bane ba”. Cikin dariya da kuka Aunty Mimi tace, “Wlhy shine Momma, shine agabanki ba mafarki kikeba, Momma Abie d'inmune wlhy tallahi kinji Na rantse”. Zumbur Momma ta tashi daga jikin Aunty Mimi, Abie dake tsaye har yanzu bisa taimakon su Galadima ya murmusa yana fad'in “Zeenah ki cire kokwanto, da gaske wannan Saifudden d'inkine ba Wanda yasaba zuwa miki a mafarkiba kinji”. Tasowa Momma tayi garesa, ta shafa fuskarsa domin tabbatarwa, takuma binsa da kallo tundaga sama har k'asa, lallai da gaske wannan Saifudden d'intane bana mafarkiba, Ai sai kawai ta rungumeshi babu kunya ko tunawa dasu Galadima a wajen. Sai duk'ar da Kansu duk sukai suna Murmushi.
Gaba d'ayansu kowanne soyake ya nuna ajintarsa ga Abie domin nuna masa gamsuwa da farincikin samun lafiyarsa, aka kawo masa y'an Uku ya had'a duka ya rungume yana maijin k'aunarsu har cikin jininsa, Khaleel ma yana nanik'e dashi. Munaya dai nadaga gefe bata zak'eba. Idon Abie ya sauka akanta, Murmushi yamata yana fad'in “'Diyata zo mana”. Takowa tai cikeda jin kunya tazo gabansa ta durk'usa, cikin girmamawa ta gaisheshi da masa addu'ar k'arin samun lafiya mai d'orewa. Ya amsa yana mai k'ara jin farin cikin kadancewarta suruka agaresa uwa ga jikokinsa. Galadima ma yakasa d'auke ido daga gareta, sai yaga tamasa y'ar rama tsakanin jiya da yau. Breakfast d'in dabai samu shigaba d'azun aka baje domin ci, amma shi Abie kasancewar an hanashi cin wasu Abubuwan Kuku yay azamar tanada masa Wanda yake buk'ata. Daka gansu kasan suna tareda matsanancin farin ciki . Koda suka kammala Galadima ya taimakawa Abie shiga d'akin Momma, shima ya haye sama shida matarsa. Tun'a falo ya d'auketa cak yana juyi da ita cikin hajijiya, babu shiri Munaya tahau k'yalk'yata dariya da k'an k'ame wuyansa da hannayensa tana cusa kanta cikin k'irjinsa. A haka suka k'arasa cikin bedroom, ya jefa abarsa saman gado yabita tareda jan bargo yay musu runfa.
An hanani ganin abinda akeyi🤨, sauk'inma inada mijin Nima😏🙄.
Farin cikin da wannan ahali suka tsinci Kansu wlhy 6ata lokacine, Momma kam sai ko ganinta bama ayi🤭🙈.
A gurguke please🥺😔.
Walwala da farin cikin wannan gida tadawo kam, ga nutsuwa mai saka zukata samun damar yawan ibada, ko yaushe suna manne da Abie, sai idan time d'in hutunsa ne yayi, Galadima yayma kowa gargad'i akan sanarda tashin Abie, burinsa kowa yaga abin mamaki, 100% Momma ta yarda da shawararsa, hakama Abie. Yanzu dai kam sun yanke shawarar Isa k'asarsu ta haihuwa ranar salla k'arama, zasu azumi na kwanaki 20 a india, su biya Saudiyya suyi Umrah ta kwana goma su isa Nigeria a ranar salla ayi idi dasu. Gaba d'aya azumi saura kwanaki 6 a farashi.
******
AZUMI
Alhmdllh kowanne musulmi yau ya tashi da azumin watan Ramadan mai mai albarka, saidai irin masu ak'idar saimun gani da suka kasance k'alilan acikin wasu k'asashe irin namu Na yankin Africa. Duk da shayarwa hakan bai hana ni zama cikin jerin masuyiba, dan raino dai bani nakeba, tsakanina da yarannan idan sunji yunwa, koyaushe suna tare dasu Momma, sunyi 6ul-6ul dasu tamkar y'an watanni 6, amma har yanzu suna cikin wata Na hud'une ma kacal. Tunda safe Galadima ya fice, Na d'an tashi nai gyaran saman sannan Na sakko, yau babu maganar shiga kitchen, Dan tunda Abie ya dawo nakoma nike mishi girkin abinda zaici, wataranma nakan had'a da namu muma, babu abinda zan cema wad'annan mutane sai godiya, soyayya dai mai cike da k'auna ina samunta a garesu, ni da mijina kam ai sai hamdala, yana tattalina da tarairayata, saidai d'an sa6ani Na yau da gobe Wanda baka Isa raba ma'autara da Shiba, shima kuwa bai wuce wasu awanni muke shiryawa ba, inko Momma ta lura ma takan kiramu tamana Nasiha, hakama Aunty Mimi. A falo Na iske Abie daga can gefen falon inda wasu kujeru biyu suke da kanta mai d'aukeda buks Na karatu, tundaga kan Na addini har zuwa Na makaranta dadai sauransu, zaune yake yana nazarin wani littafi da banga sunansa ba saboda tazarar dake a tsakaninmu. Sai Samha dake falon kwance a kujera tana kallon film, zaman gyalena Na gyara, Na taka a nutse zuwa garesa, saida Na durk'usa a gabansa sanann nace “Barka da safiya Abie”. 'Dago k'yawawan idanunsa da Galadima ya gado yay yana kallona, ya zare medical eyeglasses d'in idonsa yana Murmushi, “'Diyata barka dai, kin tashi lafiya?”. Kaina a k'asa ina murnushi nace, “Lafiya lau Abie, ya ibada da k'arin k'arfin jiki?”. “Alhmdllh d'iyata, ai jiki kam sai godiyar Ubangiji, Muhammad fa?”. “Ya fita tunda safe”. Na fad'a cikin kuma duk'ar dakai. Murmushi Abie yayi, ya maida eyeglasses d'insa yana fad'in “ALLAH ya dawo dashi lafiya to”. A saman la66a Na amsa, sannan Na mik'e da k'yar zuwa d'akin Momma. Abie ya bita kallo zuciyarsa cikeda k'aunar wannan yarinya, irinta yaytama y'ay'ansa addu'ar samu amatsayin abokiyar rayuwa, Alhmdlh Ubangiji ya amsa masa, saura Sauban kuma.
Nidai nashiga Na gaida Momma, Na iske tanama su Amaturrahman shiri, da alama wanka tamusu, Na gaisheta cikeda girmamawa kamar yanda Na saba, itama ta amsamin da kulawa tareda d'an jana da hira tamkar yanda ta saba, nad'an jima a d'akin, harta fito tabarni Na gyarashi tsaf kamar yanda nakeyi tun bayan dawowarmu, Dan tuni Na dakatar da Samha ni nakeyi. Na fito da nufin shiga Na gaida aunty Mimi saina isketa tama fito falo, anan muka gaisa Na zauna muka d'ora da hira tamkar yanda muka saba, mafi yawama firar ta Sauban Ce, Dan kowa yayi missing d'insa, yace azumi da kwana 3 zai zo sai salla zai koma, Galadima bai hanashiba, dukda yana tareda tattalar kud'i a tsakaninnan saboda sun masa k'aranci, to saima papi ya d'auki nauyin zuwan Na Sauban da komawarsa. Mund'an ja lokaci Muna hira barci yafara rinjayata, mik'ewa nayi Na gudu sama, nad'an rage kayan jikina Na haye gado sai barci.
Kusan 10am saiga Galadima ya dawo, bai iske kowa a falonba, da alama barci suke kokuma suna harkokin gabansu a ciki, kai tsaye d'akin su Momma ya nufa, yay knocking aka bashi izinin shiga. Abie Na zaune saman abin salla ya idar da sallar walha, yayinda Momma ke zaune bakin gado tana bama Abdurraheem Magani saboda zazza6in dake jikinsa. Galadima ya zauna a saman sofa yana gaidata da tambayar miya sami Abdurraheem d'in?. Cikeda kulawa ta amsa masa tana gogema yaron inda maganin ya 6ata masa a wuya da fuska. “Tunda muka tashi yau Na kula bayajin dad'i yaronnan, inagafa yakamata ka kaishi a bincikasa, basai mun zauna wata 6 ta cikaba, tunda kasan ciwon yana zama iri daban-daban, karmuyi tunanin ko irin nakane azo ba hakaba, Dan Na kula yafika yawan laulayi shikam, Abdurraheem baya had'a sati biyu da isashsshiyar lafiya”. Jin jina kai Galadima yayi, tausayin d'an nasa Na ratsashi, ya had'iye abinda ya tsaya masa a mak'oshi da k'yar yana amsar Abdurraheem d'in daga hannunta. Abie daya shafa addu'a ya maido hankali garesu. Mik'ewa Galadima yay yakoma inda yake yana gaisheshi, Abie ya shafa kansa hakama Abdurraheem, cikeda tsokana yace, “Like Father like son”. Dariya Momma tayi, yayinda Galadima yay Murmushi mai k'ayatarwa har hak'oransa Na bayyana. Yace, “Abie ai dakai suke kama duka, Amaturahman cema tad'an d'ebo mamansu kad'an”.
[8/19, 6:14 PM] 🙇🏻♀Da Rarrafe🙇🏻♀: Abie yay Murmushin jin dad'i, yana shafa kan Abdurraheem da yay barci, gaskiya Galadima ya fad'a, dan shima tun randa yafara ganinsu ya lura da haka. Sund'an ta6a hira, har Galadima ke kawo maganar Aunty Mimi akan yakamata tayi aure hakanan, domin zaman bashida amfani haka, ko wani yamaka k'yak'yk'yawar fahimta wani bazai makaba, tunda ba wuce auren tayiba. 100% iyayensa sun gamsu da zancensa, sunkuma amsa masa da isha ALLAH zasu zama Na musamman da ita. Kwantar da Abdurraheem yay musu sallama akan zaije yad'an rage barci.
Tunda ya shigo yay tozali da Munaya barbaje a gado, murmushi yad'anyi yana cire Bottoms d'in rigarsa harya k'araso cikin d'akin, hanging d'in rigar yay sannan ya zauna saman sofa yana cire takalmansa, mitsawar da Munaya tayi tana juya kwanciya yad'ago ya kalleta, aransa yace hajiyata ko an farajin azuminne?. Harya gama hidimarsa yazo gefenta ya kwanta bata saniba, dayake ba motsi mai k'arfi yay tayiba, Dan yasan batada nauyin barci, gudun karta tashi yay tayin komai a sannu.
*****
Duk musulmin ALLAH Na k'warai daya wadatu da ibada inhar lokacin salla tayi ko barci yake saiyaji a jikinsa, kokuma yayta mafarkin ana sallar, hakance ta kasance ga Munaya da Galadima, kusan atare suka farka, kowanne bakinsa d'auke da addu'ar tashi barci. mamaki ya kamani ganinsa gefena, Dan bansan yama dawoba, ya min murmushi nima Na mayar masa da murtani ina shafa fuskarsa. Cikin lumshe ido nace, “Yaushe ka dawo?”. Hannunsa ya d'ora saman nawa dake kan fuskarsa, yad'an rufe ido ya bud'e akaina, murya k'asa-k'asa yace, “Tun d'azun mana, kinata barci abinki”. Yatsine fuska nad'anyi ina zame hannuna da k'ok'arin tashi. Nace, “Wlhy barci bai wani isheniba shiyyasa nad'an rage yanzu kafin time d'in shiga kitchen”. Shima tashi yay zaune yana jinjinamin kai. Shiya fara shiga wanka, saida ya fito sannan nima Na shiga nayo. Koda ya fita salla ya dawo bai koma cikiba, sai suka zauna a harabar gidan shi da Abie suna hira, dayake kullum Galadima cikin bashi labarin abubuwan da suka dingi faruwa yay lokacin yana jiyya, wani yay murmushi, wani dariya, wani kuka, yana kuma yabama Galadima bisa ga gwarzan takar dayayi ta kare mutuncin ahalinsa da rik'e martabarsa. Har time la'asar suna zaune a wajen, da taimakon Galadima Abie yataka zuwa massalaci, dan inhar yana gida haka sukeyi, bayan sun dawo awajen suka sake zama, Galadima ya kirani nabama Samha System d'insa takai masa. Da to Na amsa, Na hau sama Na d'akko nabata.
K'arfe biyar dai-dai muka shiga kitchen ni da Samha da kuku, sai Hadiman gidan guda biyu dake taimaka mana da wasu ayyukan. Cikin nutsuwa muka gabatar da dad'ad'an abincin bud'a baki, wasu namu Na Hausa wasu kuma Nan. Gab da magrib muka gama, munbarsu k'arasa komai Na k'imtsa kitchen d'in da shirya abincin. Wanka nakesonyi ga Amaturrahman Na kuka, Momma kuma tace babu inda zani saina shayar da ita. Dole Na zauna ina dungure kanta. Oho batasan ma inayiba, itadai taji abinda take buk'ata a baki kawai. Ganin tad'ansha na d'auketa muka haye sama dan karma Momma tace saita k'ara. Na iske Galadima yana wanka, ni bammasan ya shigo cikiba, Na kwantar da Amaturrahman Na kuma sauka, nasan dole yana d'akin za'a kira salla, dabino da ruwa Na d'oro a k'aramin tire nazo Na ajiye, ina ajewa kuwa yana fitowa. Sannu da aiki yamin, Na amsa ina manna masa Sumba a hannunsa dana kama, nai saurin shigewa bathroom. da kallo ya bita yana murmushi, ya kalla hannunsa data sumbata shima ya sumbaci wajen. Fitowata wanka yay dai-dai da cikar lokacin kiran sallar magrib, a bakin gado Na iskesa zaune Amaturrahman Na kwance kusa dashi tana wuntsil-wutsil da k'afafu, idonta nakan hasken globe, shikuma yana kallonta yana murmushi da video d'inta awaya. Batare danayi tunanin komaiba Na k'araso garesa da nufin bashi dabinon, amma saiya jawoni nafad'o jikinsa, dukda laimar ruwan dake jikina. Babu wani k'arin bayani ya d'aura bakinsa saman la66ana, idanu Na waro masa Na tsorata da mamaki, amma saiya kashemin ido d'aya da cigaba da abinda yake. Kusan mintuna biyu nasamu ku6ta. Ina yunk'urin tashi ya kuma hanani. “O ALLAH, azumi fa kakai my King, shine kafara da jan magana mai makon Neman ruwa ko dabino?”. Wani miskilin murmushi yayi da huramin iska saman ido. Farfar Na fara da idanu. Yakuma Murmusawa, “Bazaki ganeba babie na nayi missing d'inkine, kinga ai lada biyu, gatakai azumi gata d'abbak'a sunna, ni ai ga dabino Na nan, yawunki kuma shine ruwana”. Ya k'are maganar yatsansa a la66ana. Tura kaina nayi a jikinsa ina Murmushi. Ya rungumeni da shafa bayana shima yana murmushin.
K'arshe dai sai a d'akin mukai sallar magrib sannan muka sauka k'asa shan ruwa. Jinai gaba d'aya kewar y'an gidanmu tazomin a yau, Na tuna yanda muke had'uwa k'wanmu da kwarkwata a runfa shan ruwa, murmushi naita saki dajin kewarsu mai yawa da d'okin son ganinsu. Aunty Mimi data lura dani tace, “My K'anwa yadai?”. Nakuma fad'ad'a fara'ata ina cewa “Na tuno gidane kawai Aunty”. Murmushi duk sukayi, Galadima dake gefena ya mintsini cinyata kad'an, d'agowa nai Na kallesa ina d'an 6ata fuska, gwalo yay min kad'an yana d'auke kai cikeda basarwa tamkar bashi yayiba. Saida na tabbatar bamai kallonmu sannan nima na rama, aiko zafin yasakashi kad'an garage ya 6arar da kunun da yake sha, yay saurin rik'ewa. Sannu muka shiga masa, na Fiske abina tamkar banyi komaiba. Muna had'a ido ya cije lips da min gargad'i da ido akan zai kamanine. Nima gwalo namasa.
Abinda basu saniba tun farkon fara lamarin Abie da Momma suna kallonsu, dan haka yanzu sai suka kalli juna suna murmushi.
A gurguje please⛹🏻♀😏
★★★★★★★★★
Kwan uku da fara azumi Sauban ya iso India, bak'aramar birkicewa yay da ihun ganin Abie ya samu lafiyaba, hardasu kuka rurus, Abie ya rungume Autansa d'aya zama sangamemen Saurayi yana mai jin farin ciki da k'aunarsa. A ranar sai sabuwar murna ta tashi kuma, haka muka wuni cikin farinciki biyu, na zuwan Sauban da gimama farincikin daya riska. Haka azumi yacigaba da gangarawa, kullum saina kira su Abbanmu da sauran jama'ar gidanmu namusu barka da shan ruwa, hakama y'an uwana sunta turomin sak'on massages kenan kulum namin barka da shan ruwa.
Azumi na kwana 15 muka kai Abdurraheem Asibiti, Yakuma samun binciken kwararrun Likitocin zuciya, suka dubashi da k'aramin dabaru wajen kula da rainonsa, sai magunguna da zai iya sha a matsayinsa na yaro k'arami.