Kenza eBookz

Raina kama book 1 complete - Chapter 10

Raina kama book 1 complete - Chapter 10

Raina kama book 1 complete Chapter 10: Raina kama book 1 complete Chapter 10. “maybe ma gibe ki ganni Momma dan nagama abinda ya kawoni�?. “shikenan babu…

4,459 words

“maybe ma gibe ki ganni Momma dan nagama abinda ya kawoni�?. “shikenan babu damuwa, amma kana ganin a masarautar ku babu Wanda yasan kazo?�?. “babu Wanda yasani momma, hatta da Harun, sai Muftahu kawai�?. Cikeda mamaki tace “Muftahu kuma?�?. “eh Momma miya faru?�?. Tayi d'an jim sannan tace “babu komai, amma ka dinga kula dai Muh'd�?. Shima yad'anyi shiru yana nazarin maganarta, sai kuma yace “ok Momma insha ALLAH�?. Yana ajiye wayar kuwa saiga Muftahu ya shigo, kallonsa Galadima yayi. Muftahu dake shirin zama yace “yalla6ai barka da rana�?. “ykk?�?.‘cewar galadima�?. “wlhy Alhmdllh, dama akan yarinyarne, kagafa har yanzu bamuji daga gareta ba�?. Murmushin gefen baki Galadima yayi, sannan yabud'o massage d'in da Munaya ta turo masa yamik'ama Muftahu wayar. Babu musu Muftahu ya kar6a, saida ya gama karantawa sannan ya d'ago yana kallon Galadima fuskarsa washe da murmushi, “Alhmdllh yalla6ai ta amsa Ashe?�?. Kallonsa kawai Galadima yakeyi cikeda nazarinsa, yana mamakin yanda Muftahu ke d'okantuwa da wannan maganar auren, tunda yabashi damar binciken su Munaya bai barsa ya hutaba, haka kawai sai zuciyarsa ta d'arsa masa wani Abu, musamman idan yay dubi da yanda Muftahu ya nuna tsantsar farincikinsa dayace zai auri yarinyar na shekara 1. to koma dai miye, zai sanya masa idanu. Muftahu yace, “yalla6ai to yanzu ya za'ayi dasu mai martaba ne?�?. Galadima dake latsa d'ayar wayarsa yace, “no, karka damu da wannan, zan k'arasa komai kawai�?. Kamar Muftahu baiso hakanba, amma saiyayi murmushin yake, “shikenan ALLAH ya tabbatar da alkairi, yasa ayi damu�?. d'ago ido Galadima yayi ya kallesa, “to miye kuma na wannan doguwar Addu'ar? Saikace wani auren gaskiya?�?. “Hakane kuma yalla6ai, sorry�?. Shiru Galadima bai amsaba. falon ya d'auki shiru kowa da tunaninsa.

★★★★

Harda safe inata yawan duba wayata kozanga replay daga Galadima amma shiru, hardai munubiya tace “wai miye bini-bini saiki duba waya?�?. Kallonta nayi ina k'ak'alo murmushin yak'e nace “babu komai fa�?. Badan ta yardaba ta k'yaleni, cigaba mukayi da aikin da innarmu ta samu. Aryaan yashigo yana kuka, muduka mukace miya faru kaikuma?. Cikin kukan yace “ba Abdul bane ya dakeni, wai dan Zainab ta zubamin ruwa na rama�?. Nace “ina Abdul d'in?�?. “Suna wajen fanfo�?. ‘cewar Aiyaan daya shigo yanzun�?. “Auntynmu kuma wlhy sosai yabama Aryaan mari a fuska, sannan ya halbeshi ga k'afarsa har yafad'i�?. Da hanzari nafice daga sashenmu, na iske Abdul da sauran yaran gidanmu a bakin fanfo suna wasa da ruwa, rankwashin Abdul nayi tareda murd'e kunnensa, “mi Aryaan yamaka ka dakesa dan k'aniyarka?�?. Hannuna yadafe saboda zafin dayaji na murd'ar kunnen, cikeda tsiwa yace “yoba Zainab ya daka ba danta watsa masa ruwa bata ganiba�?. K'eyarsa na mangara, “to ina ruwanka, Zainab d'in ba k'anwarsa baceba? kokuwa dan kai mama d'aya ta haifeku? daga yau kasake dukan wani acikinsu saboda yadaki Zainab ko Fahad saina lallasaka agidannan, masu shegen 'yan ubancin tsiya, iyayenku duksun 6ataku da k'in 'yan uwanku jininku�?. nak'are maganar dakuma rank'washinsa. Aikam ya daddage ya kwantsama kuka, kaikace wani uban bugu namasa.

Kamar jira gwaggon haleematu keyi tafito tana tambayarsa miya faru?. Fad'a mata yayi waina mareshi da murd'a masa kunnen saboda ya daki Aryaan, harda cewa na zageta. Hummm tamkar dama kad'an take jira damu, har k'ofar d'akinmu taje tana zazzaga masifa da zagina. Innarmu tafito tana tambayar miya faru? dan ita bama tasan an bigi Aryaan d'in ba. Maimakon tama innarmu bayani saita koma kanta da cin mutunci, kamar innarmu tayi shiru amma yau saita kasa. Ta kalli Goggon haleema tana murmushi, Sadiya bakinki yasan mizai fad'a, inba hakaba zan baki mamaki agidannan wlhy, bakinki ya tsaya iya maganar yara, idan kika kuskura iyayena suka kuma shiga a furicinki zakiyi nadamar sanina�?. Innarmu nagama fad'a tashigewarta. Galala gwaggon haleematu da duk matan gidanmu sukayi da mamaki, duk kuma sai shakkar innarmu ya shigesu, Ashe akwai ranar dazata iya maidama wani murtani acikin gidan?. Murmushi nasaki, sannan nabama Munubiya dake kusadani hannu muka tafa, nace “ho innarmu, kina aljanna ina binki da addu'a, haka nakesonki agidannan, kiringa watsema kowa aniya�?. naja hannun Munu.... muma muka shige ciki. Abbanmu dake kallon komai ta window d'akinsa yasaki murmushi yana girgiza kai, yasan gaba d'aya halayen Munaya nashine, yarinyar batada tsoro, amma yau Ai'sha ta birgeshi datama Sadiya haka, koba komai tasaka musu shakkarta azukatansu.

Aikan kowa jiki babu kwari taja k'afarta tashige d'aki tana gulma da zuciyarta. Gwaggon Haleema kam ai saida Nusaiba taja hannunta sannan ta iya d'aga k'afarta.

Koda muka Shiga sai innarmu tahau mana fad'a akan dukan Abdul d'in da nayi, hak'uri kawai na bata danni yau raina fes, innarmu tafara maida murtani.😅

★★★★�?

Da k'yar ya iya bud'e idonsa ya janyo wayarsa dake ringing, batare da ya dubaba ya amsa yasaka a kunne. “Assalamu alaika Muhammad kana lafiya?�?.. Zaram ya mik'e zaune tareda watstsayewar dole saboda jin muryar mai martaba mahaifin Momma papi.........✍�?

To ko mai martaba zai amince da auren Munaya? duk da baisan kai tsaye auren yarjejeniya baneba🤔?.

Karku manta Amincewar mai martaba itace ta kowa.

Muje zuwa my guys⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🤚🏻✋�? [4/22, 2:17 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*

*_HASKE WRITERS ASSO...💡_* _(Home of expert and perfect writer's)_

*_♦RAINA KAMA......!!♦_* _{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

👉🏻1�?8�?

..........A Asibiti gado suka bani, sunata fad'an yanda jinina ya hau sama, su mamakima suke yi 'yar k'aramar yarinya dani amma inada hawanjini, shin miyayi zafi haka?. Su Abba dai kasa cewa komai sukayi, dan su kansu abin na yata6a zuciyarsu. Wannan karonma Mama Rabi'a da Munubiya ne suka kwana a wajena, washe gari da yamma saiga 'yan gidanmu wai sunzo dubani, bamuyi mamakiba Dan munsan ba domin ALLAH sukazoba, kawai sunzo ganin kwafne. Duk suncika d'akin da surutu akan wai suna mamakin miya samin hawan jini?. daga mama Rabi'a har Munubiya babu wanda yabasu amsa. Doctor ne yashigo yace sud'an ragu wasu su fita baranda dan ALLAH, duk fita sukayi harda mama Rabi'a aka barmu iya mu yaran kawai, dansu Fiddausi duk hadasu akazo. Ina daga kwance kan gado ina sauraren hirar dasukeyi, wai safara'u da Halimatu ne sukaje gidan su Siyama tai tamusu yatsina da d'aukar kai, saikace ba 'yan uwanta ba, mijinta yadawo sukayi shigewarsu suka barsu afalo har yamma sannan suka fito, mai makon tabasu hak'uri sai cewa tayi wai dama basu tafiba🤣. Wannan abun daya faru shine yajawo rigima a gidanmu jiya da daddare, har saida su Abba suka tsawatar. Murmushi kawai nayi Na gyara kwanciyata, a zuciyata ina fad'in maganinku ai, baku masu dangiba..........gabana yafad'i, saboda jin tamkar k'amshin turarensa. da sauri Na d'ago kai saboda jin su Fauziyya ma sunyi tsit daga surutun dasukeyi suna kallon bayanmu. Wani yaam naji a raina domin ganin Galadima da tawagar dogaransa, sai wani dake gefensa amma ba muftahu bane, (Harun ne). Sanye cikin k'ananun kaya wad'anda suka fidda ainahin k'irarsa ta cikakken namiji, fuskarnan kamar kullum babu walwala. Mu 4 ne kawai a d'akin, dan haka yana tsaye a gadon farko da alama tanbayoyi yakema matar dake jiyya a gadon. gani nai yasaki wani guntun murmushin gefen baki sannan ya kalli harun, bansan miya cemasaba nagadai yabaro wajen yana tunkaro gado Na biyu. A hankali Na lumshe idanuna wani Abu Na tsikarar zuciyata mai kama da tsoro da rud'ani. Sauran 'yan uwana kam sun zuba masa idanu tamkar zasu cinyesa, kowacce takasa furta komai a fili saida a zuciyarta take tattaunawa da yaba Galadima d'in. Annanma yayi kusan mintuna hud'u sannan ya tunkaro gadon takusa damu, dan nice ta k'arshe. duk da akusa damu yake banajin miyake fad'a, saidai motsin la66ansa kawai nake gani, tabbas Galadima naji da Girman kai da mulki, kallo d'aya zaka masa ka tabbatar da tsantsar sarauta da mulki dake yawo a jinin jikinsa....... tunda naga yanufo inda nake sai kawai narufe idanuna gaba d'aya. Su Munubiya duk suka risina suna gaidashi. Hannu kawai ya d'aga musu yamatso jikin gadon danake. Tsantsar mamakine ya bayyana a fuskarsa, yad'anyi kamar zai nunani da hannu saiya kuma fasa, su safara'u kam duk sun zubo mana idanu suga yanda za'a kwashe. Munubiya ce cikin k'arfin hali tace “Munaya ki tashi ana miki magana fa�?. daka ganta kasan a tsorace take maganar. Shima juyowa yayi ya kalli Munubiyar domin jin kuma Muryata, maganar Muftahu ta fad'o masa arai dayace yaran twins ne, kuma ba'a iya banbancesu. Suma Kansu dogaran NASA da Harun duk sunyi tsuru suna kallonmu, domin babu wanda baiga jaridarba a wancan lokacin. Maganar sace tasaka kowa maida hankali a kansa, nidai har yanzun idona arufe suke, cikin basarwa da nuna halin ko in kula yace, “ya jiki?�?. tamkar bayaso haka yayi maganar. Nima cikin dakiya da shariyar kamar yanda yamin nabud'e idona nace “Alhmdllh�?. Kamar yanda yake tambayar kowa nima haka ya tambayeni miye matsalata?. Na d'a6e baki sannan nace “masassara�?. Harun ya kalla, danshi baima fahimci minake nufiba. Murmushi harun yayi, danya fahimci bai ganeba, cikin gyara tsayuwa yace “tana nufin fever�?. Caraf fiddausi tace, “ranka yadad'e k'arya take hawan jinine�?. Juyowa yayi ya kalli fiddausin da fararen idanunsa wad'anda suka nemi zautata, bai Ce komaiba ya janye ya maida kan Munubiya, “Sister naga drugs d'innan?�?. yafad'a kamar anmasa dole. Ko kad'an Munubiya bataji maiya fad'aba, dan a saman la66ansa yayi maganar, tana shirin sake tambayarsa d'aya daga cikin dogaran ya maimaita mata a tsawace. Nikaina saida Na bud'e ido saboda tsawar, Na bankama dogarin harara ina magana k'asa-k'asa yan da babu mai jina, kajimin shegen dogari, dan tace batajiba zakawani daka mata tsawa?, shi mizaisa bazai bud'e baki yayi magana yanda kowa zaijiba? Mutum sai azabar Girman kai mtsoww, koma R bai iyaba. Duk maganar danake la66ana ne kawai ke motsawa, shikuma idon nasa nakan la66ana, dukda duba kwalin drugs dayakeyi, tsaf ya karanci duk maganar danakeyi. yayi wani munafukin guntun murmushi yana mik'ama Munubiya magungunan. Juyawa yayi yama Harun magana, sannan ya juyo ya kalleni yana fad'in “ALLAH yak'ara lafiya�?. Harara Na zuba masa batare da tunanin zai ganiba, amma sai caraf muka had'a idanu. Janye idanunsa yayi a kaina yajuya yabar wajen yana cije lips d'insa da mamakin yarinyar nan da batada tsoro. su Safara'u Na zuba masa godiya, duk da zukatansu Na mamakin yanda yanuna tamkarma bai sanmu ba. Ko kallonsu baiyiba ya d'aga musu hannu, sukuma sunyine dama danya tanka musu. Harun ya tambayi Munubiya wane doctor ne ke dubani?. Ta Sanar masa. Addu'a yaymin sannan yabar wajen shima.

Lumshe idanuna nayi zuciyata Na kaikawo, yanda Galadima yayi, saiya kuma tabbatar min da mafarki dai nayi kenan, bawai gaba da gaba ba yace muyi Auren Contract ba kenan. Innalillhi, mike shirin faruwa danine ni Hussaina, hawayen dasuke neman zubomin nai k'ok'arin had'iyewa, Munubiya kanta tashiga kogin mamakin yanda Galadima yay tamkar ma komai baita6a faruwaba, shin kodai shi baiga abinda yafaru a jaridar baneba?.... Batada mai bata amsa, su safara'u ma magana suketayi k'asa-k'asa a tsakaninsu, alokacinne kuma matan gidanmu suka shigo. Mamansu yaa hameed take tambayar wai wananan bashine Galadima ba na jikin jaridar nan?. “wlhy shine kuwa mama�?. cewar Fiddausi. Haleematu ta kar6e da fad'in “mama kinga yanda ya nuna kuwa? tamkar ma bai gane su twins ba balle ya nuna yama San abinda yafaru a bayabaya tsakaninsu�?. Murmushin mugunta mamansu ya hameed tayi, “yo ai dama saboda irin haka ake cewa Ku kare mutuncin kanku, danshi namiji komi yayi adone, sannan shi d'an manyan mutanene, ko kallonsa da abin babu mai sakeyi, amma Ku gashi har ana fasa aure, kamun kai dai dad'i gareshi ai dama, kum.......�? Shigowar doctor tasaka maman su yaa hameed yin shiru, korarsu yayi gaba d'aya, yace subarni Na huta. Basuso hakanba, dan shirya cin zarafinmu maman yaa hameed tayi. Daganan gida suka wuce suna 'yan gulmace-gumacensu da dariyar mugunta.

★★★★�?

Galadima kuwa yana gama zagaye-zagayensa a asibitin na duba marasa lafiya gida suka wuce. Bayanin doctor yabashi mamaki, wai wannan 'yar yarinyar keda hawan jini, itako miyayi zafi haka a rayuwarta�?. wani sashi na zuciyarsa yabasa amsa da (6atancin da akai muku). Lips d'insa ya cije yana jan dogon tsaki, shikad'ai yasan burin daya d'auka akan dukkan Wanda yasamu da hannu a wannan lamarin. Sun biya birnin gayu plaza yaga komai yana tafiya dai-dai, daga nan suka koma masarauta.

★★★★

Nima a ranar da daddare aka sallamoni, nadawo gida nacigaba da shan Magani, yayinda biki keta gaba towa kuma.

Har yanzu innarmu tana cikin damuwa dani kaina akan zancen aurena daba asan taka maimai angoba. Zancen galadima kuwa ai tini na shareshi, dan nabarsa amatsayin mafarki nayi, musamman kuma dana bincika banga number wayan daya baniba, a wayata kuma tun randa na tura masa massege na gogeta dama gudun kar wani yagani.

Yanda 'yan gidanmu suketa rawar kai akan bikin saran 'yan uwanmu innarmu batayi, bazama ka ta6a d'auka itama zata aurar da 'ya'ya har biyu baneba. Mama Rabi'a ce ke tsaye akan komai, sai aunty salamah datazo da magunguna ta d'id'd'irka mana, mu bamusan namiye ba, takumace mudinga sha, saikuma had'ad'd'en sabulun wanka da mai data had'a mana, ga wasu turare masu sirrin k'amshi, takuma gargad'emu daga yanzu muna saka hijjab duk inda zamuje da nik'af, domin fatarmu tasami nutsuwa kar rana ta maidamu gidan jiya. Ni dai dagani har munubiya da to kawai muke binta, kuma duk abinda tace muyi munayinsa. Abbanmu yakira mama Rabi'a yabata wasu kud'i akan tak'ara amana siyayyar kayan kitchen da 'yan uwa keyi, tunda ita innarmu bawasu dangi ne da itaba dazasu tara mata. Sosai tamasa godiya, sanan tasanarma innarmu, ko babu komai taji dad'i, harma tamasa godiya itama. Tafiya mama Rabi'a tayi da k'ud'in, washe gari suka Shiga kasuwa itada inna lami, kaya masu k'yau suka sissiya mana dai-dai gwargwadon k'arfinmu. aka adanasu gidan inna lami duka.

*_kwanci tashi_*

Babu wahala wajen ubangiji, yau gashi abinda kowa yake jira yazo, domin kuwa ankawo lefen Haleematu, gaskiya angonta yayi k'ok'ari, akwati 5 abinta, kuma kaya masha ALLAH, sai-dai hakan bai hana 'yan gidanmu gulmaba, washe gari kuma aka kawo kayan Safara'u da Fiddausi. Suma dai kam saidai mak'iyi, amma jikin maman safara'u yayi sanyi, dan gaskiya kayan sauran duk sunfi nata. Itama dai akwati biyarne, amma kayan cikine basukai na sauranba. Again washe gari saiga na Fauziyya da Munubiya, mama Rabi'a tasan komai dake wakana a gidanmu, dan haka suka dage sukaima Munubiya lefe na 'Yar gata, wlhy ba fariyaba lefenta yafi na kowa, ranar har kukan dad'i nayi, domin banyi zaton hakanba. itama dai fauziyya angonta yayi k'ok'ari gaskiya. Tuni hassadar matan gidanmu tafito fili suka fara yada habaici wai an aro kaya anzo ana musu burga, da anyi aure sai ake maidawa d'ai-d'ai. Dagamu har innarmu babu Wanda ya tanka musu, dan munsan yau dai mune aciki sune a kwana🤣🥴.

Rashin kawo nawa lefen kuwa ko a kwalar rigata bai dameniba, dan bama sanin mijin nayiba balle nadamu dawani lefen banza. saima Munubiya ce harda kukanta rurus akan wai saidai araba mana kayanta mu biyu. Nifa dariyama tabani wlhy. Ganin ni babu lefe yasaka su baba k'arami siyomin kaya masu k'yau na fitar biki har kala 10, aka d'inka min, sai takalma da bags da veils masu k'yau suma. Habaici dai kam munshashi wa su innaro da matan gidanmu, danma ita innaro gwaggo Safiyya na hanata ne, da bamu san tijarar dazata zubarba a ranar kam. A haka aka shiga satin biki, mu bamu wani gayyaci k'awayeba, daga Bilkisu sai su Ayusher, ashe Ayusher ta buga invitation na k'awaye suka raba itada Bilkisu bamu saniba. Abin mamaki ranar kamu sai ganin k'awayenmu mukayi harna secondary. munji dad'in hakan sosai kuwa. A ranar kamun saiga wasu mata hud'u sunzo wai dangin miji nane, su mama Rabi'a sukayi musu tarba ta mutunci, ba a nuna musu komaiba kuma, dukda a yanayin shigar talauci da sukazo, saidai zund'e da gulma irinta 'yan biki. Matan gidanmu kam komai ya kaimusu dai-dai, sai dariya da yada magana a kaikaice sukeyi. Da aka kaisu su gaisa da innaro taita musu yatsine-yatsine, harda tanbayarsu waisu garinsu ba'a lefene? dabasu kawoma jikartaba?. Basuce komaiba sai murmushi kawai da sukayi.

Washe gari kuma akayi k'unshi, mudai namu aunty Salamah ce tamana, tana tsaye akan komai namu tamkar yayarmu ciki d'aya. A ranar kuma akaje a kaima sauran amaren jere, harda Munubiya, amma ni banda ni, tunda ba'asan ina za'aje ayiba. Aranarma Munubiya tayi kuka, nidai ina k'ok'arin danne zuciyata, saboda nabama innarmu kwarin gwuywa karta tada hankalinta. Aiko Alhmdllh ta dake tamkar komai baya damunta, tashige cikin abokan arzik'inta sunata harkoki. kowanne 6angare yacika da dangin matan gidanmu, abin tamkar fariya, namu 6angarenne kawai keda sauk'in jama'a, hakama gidan innaro yacika da danginta da dangin kakanmu.

Tunda aunty Salamah tagama yimana k'unshi da gyaran kai dana jiki sai muka nufo hanyar gida, saboda yaa marwan yazo neman Munubiya harsau biyu, sai kiran wayarta yake yana masifa saboda tare yake da abokansa. hakan yasa muka taho gida. Gashi Yau zamuyi sister's and brother's day, duk da dai saima da yamma.

★★★★�?

Galadima dake zaune a makeken falon Ummu hasheem, yanata bin jerin akwatinan da kallo, ga wasu daga 'yan uwansa zazzaune sunata kuma kimtsa kayan, aunty Mimi ta kalleshi, “kunga zanma mantafa, my k'ani ina kayan dana baka kayo gaba dasune?�?. Yatsine fusaka yad'anyi yana gyara zamansa, “nifa nama manta inda suke, shiyyasa nace bazan d'akkoba ai�?. Wata uwar harara ta watsa masa tace, “lallai bakada kai yaro, bar ganin matarka za'a kaimawa, suka 6ata biyana zakayi ehe�? Murmushin gefen baki yasaki yana lumshe idanu, cikeda k'asaitarsa yace, “Samha! jeki bedroom d'ina ki duba, maybe suna can�?. “bama kada tabbas kenan?�? cewar mom. Bud'e idanunsa yayi yana murmushi, “no mom insha ALLAH sunama can. ni yanzu kam kun sallameni natashi natafi? dan zansa aje a d'auko su Akash a airport �?. Ummu Hasheem tace “kaje kawai, dama dan kaga kayanne, tunda kuma kace komai yayi ai shikenan�?. Mik'ewa yayi yana fad'in “thanks you Ummu, nabarku lafiya�?.

Tunda yasamu yay escape sai ya sauke ajiyar zuciya, shi dariyama suke bashi dagasu har su papi, su Dan basu san auren shekara d'aya bane dabasu dinga wannan rawar k'afarba, sun wani zauna sun had'a uban kayan lefe, yad'an ta6e bakinsa kawai yana nufar sashensa.

Komai na gidan sarauta mai tsarine, dan haka kai lefen MUNAYA da suke shirin yima a tsare akayisa, (papi ne yace Subari sai yau ana gobe d'aurin aure sai akai, tunda gidan su munaya basusan kosu su wayeba). An tsara iya wad'anda zasu kai lefenne. Bayan an gama zuba akwatunan a wata farar mota mai k'yau sabuwa dal aka rufe, driver ne kawai zai shiga cikin motar. Sai kuma motoci 6 da aka zaba wad'an da zasu kai lefen. Motar farko dogaraine, ta biyu kuma kuyangi ne, sai guda biyu 'yan cikin gidansu Galadima ne su hud'u, ko wacce mota mutum biyu, sauran biyun kuma 'yan 6angaren masarautar su Momma, suma su hud'u, kowacce mota biyu. sai Samha datasa kuka saitaje taga matar Uncle Sam. Aunty mimi harta korata da zare mata idanu saiga Galadima motocin na niyar tashi. Da kansa yabud'e mata gaban motar da aka saka akwatinan yace tashiga nan, idan taje ta gaida masa matarsa. Cikeda d'oki tace zataji Uncle Sam, bazaka bada komai akai mataba. Kansa yad'an dafe dan yakula Samha na neman k'uresa, shikuma yafad'a mata maganarne domin yanason agaban jama'a yadinga yana tsantsar k'aunar Munaya, a bad'ini kuma suna zaman aurensu na contract, shiyyasa ko lefennan baiji tsadar kud'in saba yabud'e bakin aljihu aka zuba kaya masu azabar k'yau, gakuma kud'in da Mai martaba yabada shima, dakuma sauran k'annen mahaifinsa. Hannu yasaka a aljihunsa yana duba kozai samu wani Abu, amma babu komai sai wata chocolates guda biyu, wadda ya d'akkota ne zaiba khaleel d'azun yama manta, mik'ama Samha yayi yace “gashi kibata�?. Da dariya samha ta kar6a tace “Uncle ta gode to�?. Kansa kawai ya jinjina mata ya shirin barin wajen. motocin suna fita daga masarautar saiya sauke ajiyar zuciya kawai.

★★★★

Gidanmu ya cakud'e da hayaniyar da akasan gidan kowanne biki da ita, bare mu daya kasance har auren mutum 6, dukda sai gobene d'aurin aure kuwa, yara sunata wasansu da tsalle-tsalle.

A jere motocin suka shigo cikin anguwar, jama'a sai binsu da kallo sukeyi, dai-dai k'ofar gidanmu driver daya san gidan yay parking. Babu Wanda yay mamaki a 'yan kawo lefe, domin kuwa dama labari ya karad'e masarautar cewar Galadima'yar talakawa zai aura. Dogarawa da kuyangi suka fara fitowa, sannan suka bud'e motor da akwatina suka suka fara fitarwa. Nanfa jama'ar anguwa sukayi cirko-cirko suna kallon ikon ALLAH dan ganin akwatinan da aketa fitarwa daga mota. Batare da neman isoba Kuyangin suka fara kwasar akwatinan suna shiga dasu gidanmu..............✍�?

😂😂😂 Team innaro kufito mu caskale yau🙊🤸🏻‍♀ ⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀

Asha weekend lafiya😅✋�?

*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu👏🏻😭_* [4/22, 2:17 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*

*_HASKE WRITERS ASSO...💡_* _(Home of expert and perfect writer's)_

*_♦RAINA KAMA......!!♦_* _{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

👉🏻1�?7�?

.........Cikeda girmamawa yace, “Ranka ya dad'e barka da dare?�?. “barkan ka dai Muhammad. dama kashigo k'asar kenan?�?. Gabansa yad'an fad'i, danshifa yama manta mai martaba baisan yazo k'asarba, dakiyar dole ya aro yace, “wlhy kuwa nashigo d'azun yin wani aiki, amma gobema idan ALLAH ya kaimu zan koma�?. “tofa, gobe gobe? kuma gashi inason ganinka a goben�?. d'an jimm yayi, irin tamkar baisan komaiba, cikeda shakku yace, “ranka ya dad'e lafiya dai ko?�?. “lafiya k'alau, wata muhimmiyar magana nakeson muyine�?. “to shikenan, zanshigo insha ALLAH �?. “to madalla saina ganka�?.

Dafe kai Galadima yayi yana mamakin kansa, anya kuwa baima kansa d'aurin gorobo? koda yake idanfa yayi hak'uri shekara 1 ne ko 2 kacal, inma komai yafito kafin cikar shekarar zai sawwak'a matane, yad'an murmusa sannan yakoma ya kwanta abinsa cikeda tunani barkatai.

★★★★�?

Rashin reply d'in Galadima ya dameni, haka dai naita danne zuciyata dankar innarmu da Munubiya su fahimta, nacigaba da harkokina tamkar banida wata damuwa a zuciya, saima sallar dare damuka fara dagewa da tashi nida Munubiya, gakuma azumin damuka tashi dashi yau litinin. Duk da innarmu ta fahimci inada damuwa batacemin uffanba, saidai tausayina na damun zuciyarta, tana dannewane kawai. Munubiya kam tsaf tagama fahimta ta, amma itama saita nuna bata fahimci komaiba, taje tasamu innarmu da maganar son a d'aga bikinta again. “munubiya ba wannan yakamata muyiba, addu'a yakamata muyima 'Yar uwarki, idan da rabo saikiga ALLAH ya kawo mata miji a cikin watanni 2nan dasuka rage kinji. nima nasan tana acikin damuwa, amma tana dannewa a zuciyarta saboda farin cikinmu. addu'ar dazamu mata itace tsantsar k'aunarta a garemu�?. “shikenan innarmu, insha ALLAH zamu kuma dagewa da fad'ama ALLAH, itama ALLAH ya kawo mata ta hanyar da batayi zatoba, ya sakanka mata fiyeda sadaukarwar datayi, innarmu nasan sadaukarwar da 'Yar uwata tayine yasakata a wannan halin, ta sadaukar da farincikinta saboda ni, mizanyi na biyata nikam�?. Murmushi innarmu tayi, tace, “addu'a�?.

★★★★�?

Washe gari yatashi ya shirin tafiya masarautar su Momma, Harun yakira yace ya nema masa ticket. Cikeda mamaki Harun yace, “yaushe kashigo k'asar Galadima?�?. K'aramin tsaki yaja, dan shifa yama manta Harun baisan da zuwansa ba, Link d'in hannun rigar milk d'in shaddarsa yake k'okarin sakawa, cikeda dakiya yace, “jiya nazo da daddare, kuma inagama yau zan koma�?. “tofa, amma baka cikin masarauta?�?. “no a hotel Na sauka�?. “ok barato a nema ticket d'in, sai muzo mu d'aukeka�?. “karka damu harun, banason kowa yasan nazoma, muhad'u dakai kawai a airport �?. Koda suka yanke wayar sai yaja tsaki, gaba d'aya yakoma mak'aryaci, abinda yatsana arayuwarsa fiye da komai kenan (k'arya) amma sai gashi shi yana zundumata, “Astagafurullh�? yashiga maimaitawa a zuciyarsa. Tsaf yafito cikin shadda milk color (nakula yana k'aunar milk) d'inkin rigar 3quarter, harda su hula, yayi k'yau sosai, yafito ainahin sa na cikakken bahaushe kuma basarake, ya fesa turaraensa Na kullum, komai nasa dayazo dashi ya had'a a waje d'aya. sannan yakashe kayan wutar bedroom d'in. Afalo ya iske Muftahu zaune yana jiransa, yad'anyi mamaki amma sai bai nunaba, yabashi hannu suka gaisa. Muftahu yace, “zaka dawo ta nan kenan?�?.. Kai Galadima yad'aga alamar a'a, sannan yanufi kayan wutar falon yafara kashewa. saida yagama komai sannan ya kalli Muftahu alamar suje. Murmushi kawai Muftahu yayi, danya lura yau miskilawanne aka.

Sun isa airport, lokacin shima harun harya je, mamakine ya kama harun Dan ganin Galadima tare da Muftahu, shima yanzu yana mamakin yanda Muftahu ke kuma kusanta kanshi da Galadima, baice komaiba yabashi hannu suka gaisa kamar yanda yabama Galadima. Harun yanason suyi magana da Galadima amma ga Muftahu a wajen, sai kawai yashare akan sayi a waya kawai. Basu wani dad'e a airport d'inba jirgin su Galadima yatashi.

★★★★

Yau hankalin kowa a tashe yake agidanmu saboda gwaggo Safiyya da aka kawo batada lafiya, dayake ba'anan kusa damu take aureba, tanacan wani gari daban, tun lokacin bikinsu yaa Hameed tamasu Abba complain akan batajin dad'i, amma kunsan maza darashin d'aukar Abu serious, sai basu maida hankalinsuba. Ita kuma kunya tahanata kuma musu maganar, har aka gama biki ta tafi, ashe baiwar ALLAH ciwo nata cin jikinta babu Wanda yasani, tun tanayi a tsitsaye har takai ga kwanciya, yaranta sun kaita asibiti amma basuga wani canjiba, hakanne yasa suka maidota gida, Dan aganinsu dai su Abba sunfi mahaifinsu k'arfi. Aiko suna isowa babu 6ata lokaci aka wuce da ita asibiti. Dan danan aka fara bata taimakon gaggawa. Muda innarmu ne kawai da innaro a asibitin, amma matan gidanmu babu wace tabimu, kusan mudasu baba k'arami muketa shiga da fita a asibitin dan ganin komai ya dai-daita. Kusan yamma saigasu Safara'u lokacin ma gwaggo Safiyya tana barci, yaranta duksunyi jigum-jigum da innaro saboda tashin hankalin dasuke ciki. Har dare ba'abar kowa yashiga wajen taba, sai su Dady kawai, ganin dare yayi akace mu muje gida kawai. Haka muka tafi akabar innaro da aunty habiba d'iyar gwaggo safiyyar ta uku, itama tayi aure amma tafito, yanzu zawarci takeyi. saikuma yaa Anas da aka barmusu saboda ko wani Abu zai taso.

★★�?

Tunda yafito daga jirgi ya hango tawagar masarautar kakannin nasa, yasan tarbarsa sukazoyi, inhar zaishigo haka sukeyo gayyar tarbarsa, saikace wani bak'o daban, gefe yayi da fuskarsa dankarsu gansa, sashen motocin da akan d'auka drop ya nufa, duk manyan motocine da aka tanada dama domin irinsu, d'aya yabud'e da Kansa yashige da sauri, alamar yayma driver d'in suje. Tacikin glass yake kallonsu yana murmushi, yanda suketa d'aga kai nason hangosa, suna fita daga airport d'in ya kwantar da kansa ajikin seat ya lumshe idanunsa yana tunanin wane hukunci mai martaba zai yanke akan maganar, shin ya amincene? Kokuwa?. Driver yace, “oga ina muka nufa?�?. Bai bud'e idonsaba kuma bai d'agoba, yace “gidan sarki�?. Ta madubi driver n ya kallesa, “yalla6ai ko kaine ma dai akazo tarba daga masarauta?�?. Murmushi kawai yayi batareda yace komaiba. Jin bai amsaba sai driver yakama bakinsa ya tauke shima. Ganin shine yasa dogarai suka bari aka shigar dashi har cikin masarauta, tunda yafito bayi da hadimai keta zubewa suna kwasar gaisuwa, hannu kawai yake d'aga musu, fuskarsa ad'an sake take, bai d'aureba baikumayi murmushi ko dariya ba kai tsaye. Tuni an kar6i kayansa an nufi sashin inno dasu, shikuma yanufi fada, Dan yasan yanzu Sarki suna fadanci.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull