Raina kama book 1 complete - Chapter 11
Raina kama book 1 complete Chapter 11: Raina kama book 1 complete Chapter 11. Cike fadar take da 'yan majalissar Sarki anata fadanci, bayan an masa iso…
4,405 words
Cike fadar take da 'yan majalissar Sarki anata fadanci, bayan an masa iso yashiga da sallama, nanfa dogarai suka fara zuba masa kirari. Hannu kawai ya d'aga musu ya rissina yana mik'a gaisuwa ga Sarki. Sarki da fuskarsa tacika da fara'ar ganin jikan nasa ya amsa cikin lumshe idanu. Nan dogarai suka d'au da fad'in “sarki ya amsa maka sarkin gagara badau na gobe, an gaida magajin sarki, galadiman gagara badau, ALLAH yabaka zamani irinna sarki gagara badau. Galadima Yakuma rissinawa ya mik'a gaisuwa ga 'yan majissar sarki, suma cikeda fara'a suka amsa, kowa yasan irin tsantsar k'aunar da sarki kema jikan nasa a masarautar.
Atake anan sarki ya sallami kowa, fadanci yatashi saikuma gobe idan ALLAH ya kaimu, yau yanada ganawa ta musamman da jikansa. Haka kowa yatashi yana musu addu'ar kasancewa cikin aminci.
Tareda Galadima sarki yashiga cikin gidansa, hannunsa Na rik'e da Na Galadima, ba sabon Abu bane hakan a masarautar, duk Wanda yakwana yatashi acikinta yasan matsayin Galadima azukatan masu masarautar. Akatafaren falon sarki suka yada zango, babu dad'ewa da shigowarsu saiga jakadiya da kuyangi uku, kowanne d'aukeda babban tire, bayan sun dire komai suka zube suna kwasar gaisuwa wa sarki, sannan suka gaida Galadima. Jakadiya ma ta rissina ta gaida Galadima damasa barka da zuwa masarautarsu. Bayan fitarsu Galadima yakuma risainawa a girmame ya gaida sarki kakansa. Cike da murmushi sarki ya amsa yana kamo hannunsa, “Muhammad Sameer! kana lafiya�?. “Alhmdllh ranka ya dad'e�?. “Masha ALLAH, ya kabaromin Zeenah ta da jikin babanka da 'yan uwanka kuma su Haneefa?�?. “Momma lafiyarta lau, hakama jikin Abie Alhmdllh, suma su aunty mimin haka�?. “to Alhmdllhi, ALLAH yacigaba da jagorantar lamuranku ya albarkaci rayuwarku ta gobe da jibin jibima�?. Murmushi Galadima yayi yana amsawa da amin.
Sarki da Galadima tare sukaci abinci, (tun yana k'arami dama idan yazo gidan hakance ke faruwa tsakaninsu) Sunci sun k'oshi sukayi hamdala ga ALLAH.
babu wani 6ata lokaci sarki yashiga masa bayanin kiran nasa akan maganar da Fateema (mom) tazo masa da itane jiya, shima ya zauna yayi nazari yagane hakan shine dai-dai, Galadima ya auri Munaya. tur6une fuska Galadima yayi tamkar baisan komaiba, yace “ranka yadad'e ka gafarceni, ammafa ni bata minba ai�?. Sarki yay murmushinsu Na manyan k'asaitattun masu ji da mulki, “basai tayi makaba Muhammad, domin sanda Na aurama babanka Zeenah itama bai mataba, amma saboda biyayya dakuma tausayin d'iyar 'Yar uwarta ta amince tamin biyayya, to kaima hakan nakeso gareka, ka amsamin da to kawai saimu zauna lafiya, kasan magana biyu ba halina baceba ko�?. Jinjina kai Galadima yayi yana kuma tankwashe k'afarsa, cikeda girmamawa yace “ALLAH ya huci zuciyarka ranka ya dad'e, Na amince da za6inka, ALLAH yabani ikon rik'ewa�?. Cike da tsantsar farinciki Mai martaba ya rik'o hannun Galadima, “Muhammad ALLAH shiyi maka albarka, ya tsareka dadukkan sharri, ALLAH yabama mahaifinka lafiya kaji�?. “amin ranka ya dad'e, ngd sosai �?. Daga nan hira suka cigaba dayi cikin tsantsar soyayya da k'aunar juna, kowanne yanajin d'an uwansa sosaih a ransa. Kusan atare suka yini, inno tun tana zuba idon shigowar Galadima harta hak'ura. Galadima bai shigo wajenta ba sai bayan sallar magriba. Tundaga k'ofar sashenta hadimai keta kwasar gaisuwa, tuni labarin tahowarsa ta iske inno, hakan yasa ta k'imtsa da k'yau, ta sallami bayinta masu mata hidima. Fuskarsa d'auke da k'ayataccen murmushi ya k'araso falon, bai zauna ko inaba sai jikin kakarsa, oh my sweet inno I miss you so much wlhy�?. Kunnensa tad'anja kad'an, cikeda tsokana tace “miskili kafi mahaukaci ban haushi, aini harna fara shirin yo bikonka daga turakar mai martaba�?. Yayi 'Yar dariya yana fad'in “tuba nake ginbiyar papi�?. “ja'irin kaya, bazaka canjaba dai? ya kabaro iyayen naka da 'yan uwanka?�?. “kowa lafiya lau ranki ya dad'e�?. “to Alhmdllhi �?. Nanma hirarce ta 6alle tsakanin kaka da jikanta, kan mace me nanma an cika masa gaba da kayan itatuwa, shikuma yana zubama inno shagwa6ar daya saba tana biye masa.
Masu jiran Galadima kuwa a airport saida sukaga kowa yagama fita ajirgi babushi sannan wani dogari yakira sarkin fada yake sanar dashi sufa basuga Galadima ba. Sarkin fada yace “yo kunacan kuna shashanci yaza'ayi Ku gansa, shi harma sun shige cikin gida da sarki �?. 'yan uwansa ya sanarmawa suka tattaro suka dawo masarautar.🤣
Dole a nan masarautar ya kwana, washe gari ya zagaya duka sashen sauran matan sarki ya gaidasu a mutunce. suma dai sunmasa tarbar mutunci kamar yanda suka saba, duk da dai taciki Na ciki. Sannan sai sassan iyayensa yayun momma da k'annenta, dukda dai bako ina yashigaba. Yanzunma tare sukayi karin kumallo da maimartaba, sannan suka fita fada tare, da Galadima akayi fadanci yau, yana gefen adalin kakansa.
Washe gari da safe ya tattara inasa-inasa ya cane India, yabar tsofin da kewarsa, shima yatafi yana kewarsu.
********
Gwaggo Safiyya tacigaba da samun kulawa sosai, dukda dai tanad'an jin jiki, kullum matan gidanmu sukanzo sau d'aya, muma dai makaranta tasa bama yini a asibitin, amma kullum da safe mukanzo mu kuma dawo da yamma. Matan gidanmu kam jarabar innaro tasakasu k'ok'arin zuwa kullum, dan tace wlhy duk Wanda bata zuwa saitayi Dana sanin saninta. Wannan furuci ya d'an tsoratasu, dan kowa agidan yasan wacece innaro, idan kaga mutuncinku ya d'ore to kana cinna mata 'yan canji ta k'ark'ashin k'asane🙊, amma kana hanata gobe bazai hana ta karta maka rashin m ba🤣. (Ho innaro mu ta mutunci🤸🏻♀, ina yinki over ginbiyar Malam faruku😜🙊) ⛹🏻♀
Abin yafara tsoratani ganin har sati 1 dayin maganarmu dasu Galadima amma babuko labarinsu, tun ina saran yau gobe har na daina lissafin ma, ganin zan saka kaina a damuwa nacirema zancen a raina gaba d'aya, domin Na gama fahimtar maganar Galadima da abokinsa k'aryace, maybe ma mafarki nayi naketa shirmena kawai. A tsaitsaye damuwa tafara ramar dani a tsaye, sai idanuwa da dogon hanci. Tun ina daurewa har Abu yaso yaci tura, ciwon kai Dana k'irji suka fara zama abokaina. Ranar data kama sati biyu cif saiga bak'i su Abba sunyi, babu Wanda yasan daga ina suke, kuma su Abba basuma kowa bayanin komaiba dangane da bak'in. saida sukayi kwanaki uku da zuwa sannan naji wai wanine yakawo kud'in aurena yana son abama d'ansa. Lamarin yabama kowa mamaki, nanfa 'yan gidanmu suka hau dariyar mugunta wai kwantai dai ya tabbata kenan. Gugar zanar dasuke tayine ya fusata innarmu, tasakama Abba kuka akan bata aminceba, yaza'ayi su d'auki aurena subama mutumin dabasu saniba, idan su sun gaji dani itafa tanason kayarta. Lallashi duniya Abba yayi dan innarmu ta fahimta amma Sam tak'i saurararsa, wannan ne karon farko da yaga tsantsar fushinta. Yarasa yazai mata, dan shima lamarin Na damunsa, yarasa minene yasakashi amincewa yabada auren d'iyartasa ga mutanen?, shi dai kawai tsohon yamasa kwarjinine wlhy, dan jiyay ko kad'an bazai iya musa masaba. dukda talakawane kamarsa, harma yana ganin yafisu abubuwa da yawa.
Lamarifa yayi tsamari a d'an tsakaninnan a gidanmu, dan innarmu takasa kwantar da hankalinta, hakama abbanmu, yayinda 'yan gidanmu sukejin Dad'i kamar su had'a fati. Nikuwa uwar gayya ai ba'a magana ma, nakira number Galadima yafi sau 200 amma tak'i shiga ko sau d'aya, lokaci guda nagama fita hayyacina, 'Yar uwata kanta dukta lalace kamar itace cikin matsalar. Innaro kam ciwon gwaggo Safiyya ne ya d'auke hankalinta, duk da dai su Abba sun mata bayanin kawo kud'in nawa, amma cikin halin ko in kula tace su basu kawai, idan sun barni agidan kuwa najawo musu abin kunyar dayafi nabaya, harma tashafi sauran kannena suk'i auruwa tamkar ni. Wannan furuci ya Sosa zuciyar abbanmu, amma saiya danne saboda girman mahaifiya. An sallamo gwaggo Safiyya da kwana biyu jikina ya birkice nima, dole aka kwasheni aka kai asibiti.....
*********
A 6angaren sarki kuwa bayan tafiyar Galadima da kansa yazo masarautar gagara badau, an masa tarba ta girmamawa domin shid'in babban abokine ga kakansu Galadima wato (marigayi sarki Abubakar na lll). Mama Fulani kanta in kunga yanda take girmama sarki (Abdul'fatah idris) saikusha mamaki Ku d'auka ba itace mai ji da kanta d'innanba da tsantsar nuna sarauta(gaba da gabanta yo🥴). Sarki bai 6ata lokaciba ya sanar musu abinda yazo dashi, ganin tsantsar farinciki nayi ga mafi yawan jama'ar gidan, dan hukuncin sarki Abdul'fatah yamusu dai-dai, koba komai an k'ask'antar da Galadima d'in, Wanda yadace ace an sama masa d'iyar wani mashahurin sarki ya aura, kodan sarautar da ake da yak'inin shine yakama ta ya gada. Murmushi papi yayi, saboda ganin farinciki zancensa a fuskokin wasunsu, yasan tabbas dawata manufa suke wannan farinciki, amma hakan bai damesa ba, domin shi da k'yak'yk'yawar niyya yayi. maganar sarauta kuwa sune suke ganin bazai iyaba saida wata d'iyar babban sarki, amma shi yanada yak'inin ko d'iyar shugaban talakawan duniya koda baiwace agidan Galadima ya aura sarauta ta ALLAH Ce.
Daga baya ya tsara musu yanda yakeso Neman auren ya kasance, bawai zasuje musu da rigar mulki baneba, yanason suje amatsayin talakawa domin ganin tarbar dazasu samu daga iyayen yarinyar, daganan zai gwada yak'inin tarbiyar gidan da mutuncin iyayenta. A masarautar sarki ya kwana, washe gari sukayi shigar talakawa shida sarki jalaludden k'anin mahaifin Galadima, sai wazirin papi dana sarki, saikuma k'annen mahaifin Galadima biyu sannan aka sami tsohuwar mota suka tafi aciki bisa jagorancin wani dogari da sarki yasa yamasa binciken gidansu munaya. Abinda basuyi zatoba shi suka samu, domin tarba ta mutunci da girmamawa suka samu dagasu Abba, duk da suna kallonsu talakawa fitik harma da yak'inin sun fisu komai. Hakan ya burge sarki Absul'fatah (papi) shi kansa sarki jalaludden lamarin ya masa dad'i. Sun bada kud'in gaisuwar farko data biyu naira subu 30 kacal. Sai bayan tafiyarsu sannan su Abba sukaita mamakin kansu anya mutanen bada wani siddabaru sukazo musuba? Yazama ayi basu sansuba amma suzo su kar6i auren 'yarsu? sukuma su basu babu musu kamar sun gaji da ita. (Niko nace kwarjinin sarauta suka muku abba😜😂). Can kuma dasu sarki suka tafi sunata yabawa suma, sarki Absul'fatah dad'i dukya gama cikasa, lallai Galadima yasamu tsatson daya dad'e yana masa fata da addu'ar samu.
Momma koda papi yakira yamata bayanin bataji komaiba, saima addu'a data masa da kuma nuna farin cikinta akan lamarin, koba komai zataga auren Galadiman ta, amma saida tayi hawaye data tuna za ayi auren Galadima babu mahaifinsa, kamar yanda akayi na Haneefa (Aunty Mimi). Data sanarma Abie saiya fad'ad'a murmuahinsa, yayinda hawaye ke zirara ta gefen idanunsa, ALLAH sarki iko da falala, tun yaronsa na shekara 5 a duniya yake a wannan halin, gashi har zaiyi aure, yagodema ALLAH da wannan jarabawa shikam.
A satin papi yaje India ma da kansa, yaduba jikin Abie dakuma maganar auren Galadima dayayi musu, nanma saida Abie yay hawaye, amma sarki Absul'fatah yayta masa nasihar yawan hak'uri da kar6ar k'addara, ya nuna masa sunada yak'inin zaici ribar can. Abie yana son surukinsa kuma aminin mahaifinsa sosai, dan duk lokacin dazaizo dubashi da irin salon nasihar dazai masa wadda zai k'ara tasirantar da imani a zuciyarsa. Galadima kuwa sai wani basarwa yakeyi irin shifa abin bai d'ad'ashi da k'asaba, kuma bayason abin, aurenma dole za ai masa, haka yaytaima Abie korafi yana shagwa6a. Murmushi Abie yay tayi yana lallaahinsa da idanun. Cikin tsokana sauban dake d'ayan gefen Abie shima yace “yaa Sam to kawai ni abani kana, kaga na huta da zuwa tad'i k'ofar gidan kowa�?. Wata uwar harara Galadima ya maka masa, wadda tasaka Momma da auty Mimi da samha da jakadiya dariya, shi kansa Abie murmushine ya fad'ad'a afuskarsa.............✍�?
Wannan shine yafaru 6angaren Galadima munaya bata saniba.
Guys kuje zuwa kawai, k'ila zuwa dare kujini da bonus⛹🏻♀⛹🏻♀ ALLAH yabama munaya lafiya.
Barka da juma'a.😄✋�?
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭👏🏻 [4/22, 2:17 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_* _(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_* _{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
👉🏻1�?9�?
.......Kallone ya koma sama yayinda kuyangin suka shigo cikin gidanmu, na d'akima tuni sun fara rige-rigen fitowa, baba k'arami da fitowarsa kenan daga sashensa yak'araso ga kuyangin, domin tambayarsu daga ina haka?. Baiwa d'ayace tabashi amsa da fad'in basu kad'ai bane, masuyin bayanin suna waje. Fita yayi sukuma suka ajiye kayan gefe suka kuma fitowa domin kwaso sauran. Muna falo a zaune inna lami ta tsaremu sai mun sha romon wani nama da aka dafa k'anana, sai yatsine fuska mukeyi saboda rashin dad'in naman. shigowar Ahmad da Aryaan da gudu yasa mama Rabi'a tambayarsu lafiya?. Ahmad yace “mama wlhy bak'ine da akwatina da yawa suka shigo�?. Gaba d'aya muka zuba masa idanu, kafin wani yay masa tambaya a cikinmu mukajiyo sallamar baba k'arami. Innarmu ce tamik'e domin fitowa, ganinsa da manyan mutane cikin alk'yabbu yasata fad'in “baba k'arami bak'i mukayi?�?. Cikin washe baki yace, “wlhy kuwa maman biyu �?. Itama murmushine shinfid'e a face nata, tabasu hanya suka shigo falon, duk suka zazzauna. Muduka muka durk'usa muka gaisasu, yayinda suka kuma gaisa dasu innarmu cikin mutunci. Fita baba k'arami yayi yasa yaa Anas ya kunna Gen..... dayake babu nepa. Shikuma yakuma fita da hanzari domin nemawa wad'annan bak'i masu bazata kayan tarba, bayan yakira Dady da Abba ya Sanar musu. Kaf matan gidanmu suka shigo, kowa yanason jin daga ina kuma. Mukam d'akinmu muka koma muda su Ayusher muna hasashen bak'i daga ina haka? da gani dai kasan jinin sarautane, ko kad'an ban kawo Galadima a rainaba ma, dan narigada Na shafe labarinsa ni.
Suna cikin gaggaisawa da matan gidanmu saiga innaro tashigo, kai kace an wurgotane. baki tarik'e tana fad'in “o ni Marwanatu, manyan bak'i irin wad'annan surasa gurin sauka sai 6angaren Ai'sha? kuko bayin ALLAH daga ina haka? �?. Su aunty Mimi basu fahimci zancen taba, dan haka duk sai sukayi d'an murmushi, matan gidanmu kuwa kowacce tayi k'asa da kai dariyar mugunta Na cinta, Innarmu dai bata tankaba, hakama mama Rabi'a, sai inna lami ce tace, “yo inna in banda abinki waka hana rana fita idan lokacin fitar tata yayi?�?. Kallonta innaro tayi zatayi magana baba k'arami yashigo da sallama, su Yaa Anas na biye dashi da kayan ciye-ciye nik'i-nik'i, bayan sun ajiye suka gaishesu cikeda girmamawa suka fita. Zama baba k'arami yayi suka sake gaisawa, sannan yace, “kufayi hak'uri, mukam duk kun sakamu a duhu wlhy�?. K'asaitaccen murmushi aunty Mimi tayi, domin dama papi yamata bayani akan komai na 6oye musu dasukayi. ta gyara zamanta sosai “Alhaji daga masarauta muke, munkuma zo kawo kayan k'anwatane Gimbiya munaya�?.
Kusan kowa dake falon saida ya waro idanu waje, domin jin furicin aunty Mimi, wasuma zuciyar tasu kad'an tarage tayo tsalle waje. Aunty Mimi bata damu da yanayin nasuba tacigaba da fad'in “kuyi hak'uri fa, nasan nakuma sanyaku a wani duhun, mai martaba sarki Abdul'fatah da maimartaba sarki Jalaludden Abubakar, sune sukazo Neman auren yarinyar Ku Munaya wa d'ansu Galadima Muhammad Sameer Saifuddeen Abubakar, sun 6oye muku kansune saboda wani dalili, amma sun aikomu da sak'on ban hak'uri a gareku, yanzu dai mun kawo kayan lefen Munaya ne gasunan�?. Jin jina kai kawai baba k'arami ke iyayi, bakinsa yakasa rufuwa saboda d'unbin farinciki da al'ajabin dake dank'are a zuciyarsa, yanzu nan daman manyan sarakunane agabansu a wancan karon sukazo Neman auren d'iyansu, lallai sun godema ALLAH dabasu aikata wani Abu Mara k'yauba agaresu, lallai ya yarda kwarjinin mulkine yasakasu mik'a Auren d'iyarsu ga mutanen dabasu saniba. Ai su madam innaro sai aka zauna k'asa babu nauyi, muryarta har zuga take tace “ranki ya dad'e wai gaskene saboda ALLAH?, kokuwa wasa kikeyi?�?. Murmushi aunty Mimi tayi, sannan ta kalli su Ummu hasheem da suma suketa murmushi, kallonta ta maido akan innaro, “hajiya kaka mizaisa muzo muyi muku wasa irin wannan akan magana mai muhimmanci irin ta aure, tabbas maganar nan gaskiyace, munama fata gobe idan ALLAH ya kaimu iyanzu Munaya tazama d'aya daga cikin zuri'ar masarautar gagara badau�?. Innarmu da mama Rabi'a juna suka rungume suka fashe da kuka, yayinda innaro tamik'e ta callara gud'ar data jawo hankalin tawagar jama'ar 'yan biki, sai kawai tashiga taka rawa. Dariya sosai tamaba su aunty Mimi, shi Kansa baba k'arami dariyar yayi yana girgiza Kansa da mamakin innar tasu mai kayan arzik'i Dana tsiya. Matan gidanmu kam ba'a magana, kowacce tayi d'if takasa koda kwakwkwaran motsi, kowaccensu jitake tamkarma tafasa ihu take a nan. Muryar gwaggon halimatu na rawa tace “wai da gasken dai Munayar gidan sarauta zatayi aure?�?. “kwarai kuwa�?. ‘innaro tafad'a tana mata wani kallo, “jikata sai gidan sarauta, masu bak'in cikin kuma sai a mace�?. Lallai maganar innaro tadaki zukatan dukkan matan gidanmu, Sanin halin innaro da baba k'arami yayi saiyace duk afita abama bak'i waje susha koda ruwane. Jiki babu kwari sukaita Jan k'afa suna fita Su da danginsu 'yan biki da gud'ar innaro tajawosu shigowa. bak'in cikin kuwa k'arara a fuskokin wasunsu, maman su yaa hameed tayi taga-taga zata fad'i saida aka taryota. Gwaggo Safiyya tace “lallai jama'ar gidannan yau ake *RAINA KAMA KAGA GAYYAFA* duk Wanda kake Kallon bai kaiba to tabbas watan watarana shine zai kereka, babu ruwan arzik'i da mugun gashi, Wanda yace shine to tabbas bashi baneba�?.
Su Ayusher suka shigo suna gumtsa mana, kallonsu kawai nakeyi amma badan na gaskataba, munubiya ta rungumeni ta fashe da kukan dad'i, kallonta kawai nakeyi nakasa koda motsi, to murnar Auren shekara d'aya zanyi? Kokuwa murnar Ashe galadimane mijin nawa? bawani can da ban ba kamar yanda muketa hasashe?. Ban iya ta6uka komaiba wata k'yak'yk'yawar budurwa tashigo, daka ganta kaga wadda Hutu yagama ratsawa, babu shakka zamu iya zama sa'anin juna da ita, fuskarta d'auke da murmushi tace, “to ina amaryar Uncle Sam d'in?�?. Feena ta nuna ni da hannu itama tana murmushi. Gadon ta hayo batareda jiran abata iziniba, ta mik'amin Chocolates guda biyu tana kuma fad'ad'a murmushin nata. Cikin mamaki muryata a sanyaye na girgiza mata kai nace “yar uwa namiye?�?. Hannuna takamo tasakamin tana 'yar dariya, “inji Uncle Sam yace nabama matarsa, sunana Samha, d'iyar yayar Uncle Sam �?. Duk da mamakin daya cika zuciyata, hakan bai hani mata murmushiba, nace “nagode Samha�?. Tad'an langa6e kai alamar itad'in shagwa66iyace tace , “zan dai fad'ama Uncle Sam kin gode, lallai Uncle ya iya za6en k'yak'yk'yawar sarauniyar gagara badau mai jiran gado insha ALLAHU�?. dariya su Bilkisu sukayi, nidai nakasa cewa komai, sai d'an murmushi danayi. Ta dafa munubiya takuma fad'in inason twins sisters arayuwata, dan ALLAH nima kuna sona?�?. Yanzun kam kasa daurewa nayi, nima saida na dara kamar yanda su munubiya ke dariyar, nakula ko kad'an Samha batada girman kai irinna 'ya'yan sarauta, sannan tanada surutu gaskiya�?. Cikin shagwa6a ta langa6e kai gefe, “ALLAH da gaske nake kubarmin dariya, ina addu'ar ALLAH yasa nanda wata 9 aunty ki Haifa mana twins muma�?. Amin su Ayusher suka amsa atare. Matsowa tayi kusa dani tafara mana hotuna, nidai nakasa ma magana, lallai Samha akwai rawar kai, ta tubure da shagwa6a wai sainayi murmushi kamar yanda munubiya tayi, tanason taje tabama Galadima tagani kozai iya banbancemu. Babu yanda na iya dole na murmusa akayi, sannan mukayi gaba d'aya. Bata bar d'akinba saida mama Rabi'a tashigo kiranta zasu tafi, aikam kamar tayi kuka, dan bataso tafiyarba, sai dai tace anjima zasuzo wajen brothers and sister's event. Har k'ofar gida su Ayusher suka mata rakkiya, dan lokacin su aunty Mimi harsun fita, sunso ganina amma sukayi shiru kar aga kamar dawata manufa sukayi hakan, sun hak'ura tunda dai insha ALLAH gobe ina cikinsu. Basuci komaiba dai a kayan da'aka jibge musu sai ruwa, dan haka baba k'arami yasaka aka bisu dashi mota, yace inhar ba wai bazasu iya cin cimar tamu bane to dan ALLAH suje dashi koda bazasuci ba su bada. Godiya sukayi, suna mai yaba halaccin wannan gida mai cikeda karamci, dukda dai sunkula akwai lauje cikin nad'i gameda wannan family d'in, musamman yanda wasu suka kasa 6oye hassadarsu, aunty Mimi ta murmusa a zuciyarta tana fad'in Ashe ba masarautar mu kawai baceba keda irin wannan kitimurmurar ta family. Mukulin farar motar da aka zubo akwatinan suka dank'ama baba k'arami sukace ta amaryace. ai yanzu kam rasa abin fad'a baba k'arami yayi, yak'agara 'yan uwansa su dawo suga wad'annan tarin baiwa da hikimar ubangiji da yayma d'iyarsu, wadda akulum ake ganin mahaifiyar yaran a k'ask'ance acikin gidan, sai gashi tazama *RAINA KAMA.....*
Bak'i na tafiya gwaggo Safiyya tasaka aka baje manyan tabarmi a tsakar gida, aka fiddo akwatinan domin kowa yagani, makwafta duk sun shigo suma kam dan kar ayi babusu. Gaba d'aya gidan yacike da shewa da hayaniya, tun anama irga kayan har aka bari, saibi da idanu, 'yan bak'in ciki kam sun kume waje guda, sai kukan zuci, wasuma kasa daurewa sukayi suka bar wajen. Kasancewar su Ayusher duk suna can nashige toilet d'inmu nashiga raira kuka, nifa bammasan yanda zan fasalta muku yanda nakejiba wlhy.
★★★★
A 6angaren sister's d'ina kam su Safara'u harda kukansu, fauziyya ce kawai ta nuna farincikinta, dan har d'aki tashigo ta rungumeni tana ALLAH ya sanya alkairi. maganar tashin hankali ga jama'ar gidanmu ba'a magana, sunma rasa yanda zasu masalta lamarinma, maman yaa hameed data kasa hak'uri saita saka masifa da zage-zage wai ai munafurcine su abbanmu suka shirya, wannan zancen k'aryane akwai magana a k'asa, 'yan koranta ma irinsu momy Hadiza suna tayata. Nanfa gidan ya hargitse da hayaniya, kowa da abinda yake tofawa, innaro dai Abu biyune ya dameta, farinciki dakuma damuwar abinda tayita ma innarmu shekara da shekaru, yau kuma gashi ALLAH ya d'aga darajarta, ita dawanne ido kuma zata kalli Ai'sha. Babu Wanda ya tanka a 6angaren innarmu, saima farinciki dasu mama Rabi'a ketayi abinsu, inna lami kuwa da aunty salamah sunata callara gud'a dawasu acikin matan anguwarmu, hakanne yakuma harzuk'a su maman Safada'u, suka murje idanu sunata zuba tsiya, danginsu na tayasu. Innarmu dai tana daga cikin d'aki abinta, sai zuba murmushi take tana sharar hawayen dad'i, yau kokad'an rashin mutuncin 'yan gidanmu bai 6ata rantaba, saima wani farin ciki dasuke sakata.
🤣🤣 Maganar sisters and brothers event kam ai bai yuwuba yau, dan gidanmu gaba d'aya a harmutse yake, ga 'yan anguwa sunata turuwar zuwa ganin kaya harda mota. Nikam ma zazza6ine yagama rufeni tunda nagama kukan, duk wannan kacaniya da akeyi ina cikin bargo k'udundune, su munubiya kam sunacan tsakar gida sun kasa sun tsare akan kayan gudun masu suruf bahana😜🤣. Da k'yar aka tartare kayan aka kaisu falon baba k'arami kasancewar magriba ta gabato, sai bayan isha'i su Abba da Dady suka gani, ranar Abbanmu shima saida yayi kukan dad'i, ALLAH Sarki Ai'sha, nagodema ALLAH da wannan babban al'amari yashigomin ta 6angaren tsatsonki, kema yanzu k'ya samu 'yancin kanki agidan mijinki, 'ya'yanki zasu samu 'yanci a gidan mahaifinsu, dama akance ka yarda da k'addara kakuma godema ALLAH a yayin da ya jarabceka, Ashe sharrin da akama d'iyarsa zai zame mata alkairine, sun had'ata da babban mutum domin 6atanci agareta dashi kansa Ashe zai zama sanadin alkairi a rayuwar yaranne, dan yasan inba dan wannan abin yafaruba ina Galadima zai ga munaya har iyayensa sunema masa aurrenta? hikimar ubangiji yawane da ita, yakan jarabeka domin kankare zunibinka, kokuma danya d'aga darajarka ta inda bakayi zato ko tsammaniba.
★★★★★★
Labarin tarbar mutunci dasuka samu tuni ya karad'e masarautar, wasu kam dariyama abin yabasu, ina wata tarba dazasu samu ga talakawa fak'irai. suna dai fad'ane dan kar amusu dariya. Mama Fulani koda labarin yaje kunnenta saita ta6e baki tana murmushi k'asaita, Wanda ita kad'ai tasan fassarar kayanta.
Tsaf yagama shiryawa zaije sashen da aka sauke abokansa a cikin masarautar, dan babu damar saukesu a 6angarensa, saboda angama masa gyara tsaf amarya kawai ake jira, su aunty Mimi ma dasuka kai lefe sun Sanar da amaryarsu kawai suke buk'ata, basai su Abba sun wahalar da kansuba wajen kaita da komai. Wannan dalilin yasaka aka yanke shawarar k'arama munubiya kayan munayar kawai, da safe za'aje a kuma jera mata su a gidanta😄. Cikin takunsa na kasancewar cikakken namiji mai tashen k'uruciya ga jinin mulki dake yawo ajikinsa yafito, waya ce manne a kunnensa, yayinda d'ayan hannunsa ke cikin aljihun jeans d'insa, bayi da hadiman gidan sai zubewa sukeyi suna kwasar gaisuwa, kansa kawai yake d'aga musu yayinda yake cigaba da wayarsa da Momma wadda tana India ita batazoba. Samha tak'araso gareshi a hanzarce, “Uncle ka tsaya mana please �?. ‘tayi maganar a shagwa6e saboda ganin ya basar da ita tamkar baima gantaba�?. d'an juyowa yayi ya kalleta sannan ya d'auke idonsa yana cigaba da Murmushin sa na k'asaita saboda addu'ar da Momma ke jero musu ta zaman lafiya da samun albarka ta har abada acikin auren daza'a d'aura a gobe. jiyake tamkar yace Momma ta dainama auren shekara d'ayannan addu'a irin haka, shifa harma tausayi suke bashi yanda suke nuna farin ciki da zumud'insu akan auren, musamman idan ya kalli yanda masarautar tagama cika tab da dangi takowanne 6angare, ga tawagar wasu masarautu dasukayo gaba tun yau, hakama 'yan siyasa ba'a magana, dan ba k'aramar gayya papi da Sarki sukaima wannan aurenba, kasancewar shine jika namiji na farko dazaiyi aure a masarautar, Wanda kuma kowa ke saka ran shine magajin sarautar masarautar. Ita dai Samha tana tsaye tana kallonsa harya kammala wayar da Momma ya kashe. Had'e fuskarsa yayi yana hararta, “to maganatu miya faru kuma? kike kwalan kira tundaga wata uwa duniya?, wai sai yaushene zakiyi hankali Samha?�?. Baki ta tunziro gaba, idonta harya cika da gwalla “amma dai Uncle aina fara yin hankalin ko, kumafa wani Abu Nazo na nuna maka, naje Sashenka wannan sarkin k'ofar yawanice kana wajen mai martaba�?. Kansa kawai ya girgiza yana kallonta, saida takai aya sannan yace “to aini inada abunyi, yanzuma ba wai sauraren naki zan zauna yiba, dan nan ba India bane, ba'a ganina available ko yaushe OK?�?. Harya juya zai tafi tarik'o hannunsa tana daddaga k'afafu idonta na zubar da hawaye. Kansa ya dafe domin sanin fitinar Samha, tace, “please Uncle Sam 2munutes to�?. Juyowa yayi tamkar zai maketa, saikuma komi ya tuna ya fasa, d'an cije lips d'insa yayi yana hararta, “ke wai wace irin fitinanniyace ne?, Uwarmi to zaki fad'amin?�?. Dariya tayi tana share hawayenta dan ganin tasami nasara, wayarta ta daddana sannan ta mik'a masa. Nanma Harar tata yayi kafin ya kar6a, itace yagani a photo da 'yammata biyu masu kama d'aya, kamarma yarinyar dasuke shirin auren contract, harya yatsina fusaka zaice suwaye? saikuma yatuna. d'an murmushi basarwa ya saki kafin ya kalli Samha da ta tsaresa da idanu. “Uncle ina aunty Munaya anan? �?. Wayar yamik'a mata yay gaba abinsa yana fad'in titsiye zakimin ma kenan? an fad'a miki bazan ganeta baneba?�?. Baki ta turo tana k'unk'uni, “waikai Uncle Sam bazaka ta6a canjawa baneba? kai kenan kullum sai jan ajin tsiya, shiyya sama ALLAH yayoka jinin sarauta wlhy, Aunty Munaya kin bani da wannan mijin naki mai k'asaitar tsiya, aiko wlhy tunda kace haka saina had'a maka mugunta gobe a wajen dinner �?. Ta tuntsire da dariya saboda tuno mizata shirya masa.
★★★★�?
*Rana bata k'arya........*⛹🏻♀