Kenza eBookz

Rawanin zalinci 1 complete - Chapter 22

Rawanin zalinci 1 complete - Chapter 22

Rawanin zalinci 1 complete Chapter 22: Rawanin zalinci 1 complete Chapter 22. Izuwa yanzu Khadija ta gama fahimtar lallai iyayen nata sun sami gagarumin…

3,330 words

Izuwa yanzu Khadija ta gama fahimtar lallai iyayen nata sun sami gagarumin matsala a tsakaninsu, hakan yasa sai ta yi ƙoƙarin jan babanta da hira dan ya saki jiki ya ci abinci sosai, tasan ba abin da ya fi so irin ya gansu suna karatu sosai, dan haka sai ta ɗauko mashi zancen karatu, ta rinƙa bashi labarin irin karatun da ta sha yau a school. Ai kuwa nan take ya ɗan ware suka fara maganar karatu suna cin abinci, a haka ta ja shi da hira har ya ci abinci sosai wanda bai zata ba, Zainab kuwa da yake hankali bai gama zama ba, da suran yarinta, sai ta zauna tana zuba kallo a Tv tana loda abinci abinta.

A haka suka yi hira su kaɗai har zuwa karfe tara na dare, yau dai Sadiq shi ya shigo ya ɗauka masu abincinsu. Karfe tara na cika su Zainab suka miƙe suka nufi bedroom nasu bayan sun yi wa baban sallama.

"Kada ku manta ku yi addu'a fa". Ya faɗa tare da miƙewa shi ma ya hau kashe kayan kallo da su wutar ɗakin, dan shi ma shiga zai yi tun da maman Zainab bata nan, ba wani hira da zai zauna yi kuma, gara mashi ya je ya lallaɓata ta daure ta fito ta ci abinci, ga shi ko na rana ma bata ci ba..............💔😥

Cikin bedroom ɗin nata ya nufa, ya kuma yi sa'a bata rufe kofar ba, bawan Allah yau ko wanka ma bai yi ba, kuma ta haɗa mashi ruwan wanka kamar yadda ta saba, shi ne kawai bai je ya yi ba, saboda damuwa.

Bakinsa a ɗauke da sallama ya shiga cikin ɗakin, tana kwance a saman bed kamar ɗazun da rana, maganganun Aunty Hauwa kawai take tunawa.

A gefenta ya zauna da nufin ya fara yi mata magana. Amma ina yana zama ta miƙe a hanzarce ta fice daga cikin ɗakin ta bar shi zaune, bedroom nasa ta je ta shiga tare da rufo kofar ta murza key, sai ka ce shi ne ya yi mata laifi, abin da shi ma ba laifinsa bane, amma ta kasa yi mashi uzuri a kan kishin...........MATA MUTANENMU😅😅

Ji ya yi gabaɗaya duniya tana juya mashi, ya rasa menene ma yake yi mashi daɗi a duniyar nan, har wani kara sara mashi kansa yake yi, ya rasa me zai sake yi kuma, jingina da jikin headboard na gadon nata ya yi yana tunanin me zai sake yi kuma? Ni ma na rasa wannan abin da me ta yi kama, dan haka bari na bar waɗan nan ma'auratan na leƙa wani ɓangare, wata kila kafin mu dawo maman Zainab zata ɗan sauko kaɗan........😥💔

Amma kafin mu leƙa KINGDOM OF POWER bari na baku amsoshinku sannan na kara maku haske a kan labarin, masu tambayata mun koma baya ne, ma'ana yanzu labari nake bayarwa ne, amsa ita ce a'a, ni ban koma baya ba, ai idan da zan koma baya na bada labari zan sanar daku, gaba muka ci ba baya ba, masu cewa Gimbiya Zunaira ita ce maman twins saboda suna tunanin mun koma bada labarin baya da ta wuce ne to ba haka abin yake ba, ai kuna gani ina rubutu a kan Gimbiya Zunaira kuma ina rubutu a kan su pretty wato twins, su pretty fa shekarunsu goma a yanzu, ita kuma Zunaira shekarunta shaɗaya, da shekara ɗaya kawai ta fisu, to taya za'ayi ta haifesu fisabilillahi,🤔 so rayuwar FOREST daban rayuwar KINGDOM OF POWER daban, fatan kun gane? Ɓangare biyu ne a wajen ba wai ɗaya ba, so yanzu dai zamu fara shiga cikin sarautarmu domin mu nemo shin ina RAWANIN ZALINCI take? Sai muga ko zamu iya fafatawa da ita.🥱

🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️

KINGDOM OF POWER💪🔥

Wasu irin shegun shirga shirgan dankara danƙaran motoci masu numfashi ne suka danno hancinsu a cikin Masarautar. Tun da waɗan nan motoci suka danno kai a saman shinfiɗaɗiyar titin dake tsakanin babban gate na shiga da second gate kowani mayaki da kuma bayi suka nemi waje su tsaya, motoci goma ne cif, dukka launin motocin sun kasance maroon color, guda ɗaya na tsakiyar ne kawai black color, waɗan nan motoci tamkar wasu jirage da suka danno kai, kace ba'a kan ƙasa suke tafiya ba, saboda tsantsar kyau, ga ɗaukar idanu, sam kukan motocin baya fita sosai, ba zaka taɓa cewa suna kuka ba, saboda haɗuwarsu, na manyan kai ce.

Kai tsaye part na BARDE suka nufa, basu ja burki a ko'ina ba sai a katafaren parking space na part ɗin mai matuƙar girman da zai iya ɗaukar motoci sama da guda 50.

Suna kashe motocin ba'afi da ƴan sakanninba wasu shirga shirgan bodyguards masu shiga cikin dark ash suit suka firfito daga cikin motoci maroon colors ɗin, bodyguards ne da suka san aikinsu, karfafan gaske ne, babu alamar wasa a tattare da su, aikin kawai suka iya aikatawa, duk suna sanye da face mask a face nasu.

Wani shirgegen bodyguard mai ji da lafiya da karfi ne ya zo ya ɓalle marfin black car ɗin nan, ya buɗeta cikin girmamawa. A take sauran bodyguards ɗin suka ja gefe guda suka tsaitsaya alamar suna jiran na cikin motar ya fito.

Sun ɗauki a kallah good 5 mins da buɗe kofar motar, amma babu wanda ya fito, tamkar babu kowa a cikin motar, su kuwa bodyguards ɗin sun kame waje guda suna jiran ya fito.

Sai da aka kara almost 2 mins, sannan ya sako kafafunsa waje a hankali kamar mai tsoron taka ƙasa. Sanye yake da wata haɗaɗiyar cover shoe irin na gidan sarauta, cover ta haɗu matuƙar haɗuwa, launin white color, sai kyalli duwatsun jikinta suke yi, kun dai san yadda takalmar sarauta suke dai ko? Takalma ne na gani na faɗa waɗan da ake narka maƙudan dukiya wajen sayansu, To haka na kafarsa take, daga ta cikin takalmar yana sanye da uncle sos a kafafun nasa, sai kafar wandonsa da ta kasance wandon jeans blue color. Koma wanenen a cikin motar nan da alama jinin sarauta na gudu sosai a jikinsa, duba da yadda fitowa daga cikin mota ma kawai sai an yi ta da isa da izza, ya shanya bodyguards ɗinsa a tsaye tamkar wasu mutun mutumi, kamar an sassaƙasu a tsaye, shi kuma yana zaune, da alama jinin King Zuhair ne da gasken gaske kuwa.

Ko da ya zuro kafafunsa waje ɗin ma sai da ya ɗauki almost 2 mins kafin ya fito daga cikin motar. Hannunsa na riƙe da waya, da alama tun ɗazun da yake zaune a cikin motar wayar yake latsawa.

Aka ce faɗa ɓatawa ko? To shi ne wannan, dan tsayawa zayyana haɗuwar wannan matashi ma ɓatawa ne.

JAISH kenan. matashin saurayi ne da ba zai haura 25 years a duniya ba, da kallo ɗaya zaka yi mashi kasan cewa e lallai wannan yayan gimbiya Zunaira ce, saboda fuskarsa iri ɗaya da nata, sai dai kwayar idanuwansa da suka bambanta da nata, shi nasa kwayar idanun baki ne, ita kuma nata kunga hazel eyes ke gareta, banbancin idanu ne kawai ya bambanta face nasa da ita, kyakkyawar gaske ne, ga wani haɗaɗen saje da ta kara sawa ya fito a ainahin jinin Modarawan larabawa da gaske, Cikakken namiji ne mai cikar sura tare da haiba da kamala, da ganinsa kasan e lallai shi ma ya taɓa renon commander ZAFAR, gashin kansa na larabawa a kwance luf bakin kirin yana wani sheki, ya sha gyara, da alama ba ƙananan kuɗi yake kashewa gashin nasa wajen gyaranta ba, dan da gani ba tambaya ba gyaran kananan kai ba ce, ta manyan kan ne. Yana da innocent face sosai, so silent ne, sai dai da alama akwai zafin nama da kuma zuciya, baya shiga harkar kowa, nutsatse mutun ne shi ɗin, ga bala'in kamun kai da yasa ake yi mashi kallon mai bala'in girman kai, baya da yawan magana, ga kuma bala'in kunya ke gare shi, sannan baya son ɗaga idanu ya kalli mutane, wasu suna fassara hakan da kunyar da yake da shi, a gaskiya mutun ne mai kunya sosai, dan ko mahaifiyarsu gimbiya Rahilarh baya kallonta ido cikin ido, haka Allah ya yi shi. Bugu da ƙari komai zaka yi wa JAISH a duniya ba zaka wani burgesa ba, irin mutanen nan ne da komai suka fiya yawan burus da shi, ba kasafai abu ya cika burgesu ba, amma fa mayen shan coffee ne kuma, kusan za'a ce abin a jinin gimbiya Rahilarh yake, dukka ƴaƴanta mayun coffee ne na bugawa a jarida, ko tsakiyar rana zaka gansu da cup ɗin coffee mai zafi suna sha, harta gimbiya Zunaira ɗin ma haka take da shan coffee, sai dai kuma basu taɓa shan coffee ɗin kowa sai wanda mamarsu Gimbiya Rahilarh ko kuyanga Haulat suka haɗa, a cewarsu babu wanda ya iya haɗa coffee sai mutane biyun nan, ga su da shegen kyankyani, basu son datti ko kaɗan, saboda su wani lokacin Gimbiya Rahilarh take shiga kitchen ta yi coffee da kanta. JAISH yana kaunar ƴan uwansa da iyayensu sosai, idan kaga yana magana to da ƴan uwan nasa ne, bayan su baya ɗaga idanu ya kalli kowa a cikin gidan, ƴan matan cikin family duk sun saka mashi ido, sai dai kowacce bala'in tsoron tunkararsa take yi, saboda wannan rashin maganar tasa yasa suke ɗaukarsa mai zafin rai sosai, kuma yana da zafin rai ɗin ba sai na faɗa ba, dan kunsan duk mutun mai shiru shiru irin haka fa ba'a magana wajen zuciya da zafin rai, baya ɗaukar wasa, hakan yasa suke shakkarsa sosai, best friend ɗin Yah Jawad ne.........😅

Shigar kananan kaya ce a jikinsa, sai dai ya ɗaura wata haɗaɗiya kuma tsadaddiyar suit fara a ta saman rigar jikinsa, da suit ɗin da takalmar kafafunsa haɗe da rigar jikinsa duk iri ɗaya ne white colors, wando ce kawai blue jeans. Sai tashin wani daddaɗar fitinannen kamshi yake yi.

Cikin takun jarumta haɗe da ƙasaita ta jinin sarauta ya nufi hanyar barin parking space ɗin nasu. A hanzarce bodyguards ɗin nasa suka yi yunƙurin rufa mashi baya.

Kyakkyawar farar hannunsa ɗaya ya ɗaga masu ba tare da ya yi magana ba, alamar baya buƙatar su bi bayansa. Cak suka tsaya kamar gumaka, shi kuwa ya wuce izuwa cikin gida.

Duk in da ya zo wucewa sai mayakan dake arear wajen su risinar da kai ƙasa alamar girmamawa, kuyangu kuwa kasa suke zube gwiwowinsu.

Yadda kuka san JAISH bai san da mutane a duniyar nan ba haka yake cigaba da tafiyarsa ba tare da ya ɗauke waɗan nan sexy eyes ɗin nasa daga kan screen ɗin tsadaddiyar wayarsa da yake kallah ba.

Kai tsaye babbar Fada ya nufa. Yana sako kafarsa Sallama ya fara zuba mashi kirari haɗe da jinjina kala kala. Sai dai kash, ko kallo sallama bai samu daga gare shi ba, ciki kawai ya wuce abinsa, dama na gaya maku dukka ƴaƴan BARDE KING haka suke, Zunaira ce mai kula irinsu sallama, amma saura ai ko kallo daga garesu su Sallama basu samu, dan iyayen zafin kai ne da nuna isa tare da izza, ga ji da kai, basa ɗaukar raini ko wargi.

Kai tsaye wajen King Zuhair ya nufa.

BARDE yana dake a saman kujerarsa, ya sha naɗin RAWANIN fara kal, rawanin ta zaune mashi tamkar dan shi aka yi ta, sai fifita da gashin jimina ake yi mashi, a kujerar dake gefensa wata haɗaɗiyar kyakkyawar gimbiya ce dake sanye cikin alkyabbarta fara tas, kyakkyawa ce sosai, da kallo ɗaya zaka yi mata kasan e lallai ita ce jaruma gimbiya MieMie, kamaninta ɗaya da King Zuhair ɗin, da alama yau zama na musamman za'ayi a fadar, dan daga jefe guda ga uncle Abbas da Jawad.

Da ɗan mamaki Jaish yake kallon uncle Abbas and gimbiya MieMie, tunani yake yi a kan ko me ya faru suka haɗu a fada haka? Dan shi yanzu dawowarsa kasar ma kenan daga Dubai wato wajen kakaninsa da ƴan uwan mamarsa da kuma ƴan uwan Akka, so bai san komai ba.

Gaisuwa ya je ya kwasa wajen King Zuhair kafin ya ƙarisa wajen uncle Abbas, bayan ya gaisheshi ya wuce wajen Aunty MieMie, tana dake cikin alkyabbarta, sarauta iya sarauta, da ganin face nata kasan babu wasa a tattare da ita, macece mai fara'a sosai, amma da yake tana da Tiger face wajen faɗa, sai yazama idan ka ganta sai ka yi tunanin bata da fara'a sam sam, kuma jarumtarta yana ɗaya daga cikin abin da yasa ake yi wa face ɗin nata kallon mai Tiger face.

Bayan ya gaisa da Aunty MieMie ne ya miƙawa Jawad kyakkyawar farar hannunsa suka yi musaba, daga haka ya wuce saman sofa kusa da Jawad ɗin ya zauna yana binsu da kallon me ya tarasu a nan to?.

Daga stage na kasa kuma su commander ZAFAR ne a zaune a saman nasu dankara danƙaran kujerun na alfarma, yau har da abin alfaharin KINGDOM OF POWER wato HOORAIN duk a cikin fada, HOORAIN shi ne mayaki na farko da wannan shifiɗaɗiyar masarauta take alfahari da shi fiye da tunaninku, saboda jarumtarsa da jajircewarsa. Da alama zama na musamman za'ayi.

Gyaran murya King Zuhair ya yi, cikin izza da mulki ya fara magana a nutse. "Na taraku a nan ne ba dan komai ba sai dan muna da buƙatar shiga filin daga!". Ya kai karshen maganar tare da ƙara dakewa a cikin alkyabbarsa.

Cikin nuna halin ko in kula Jawad da Aunty MieMie suka sauke ajiyar zuciya, da alama basu damu da jin hakan ba.

Shi kuwa uncle Abbas cewa ya yi. "Yaya filin daga kuma? Na menene? Kuma su waye zaku yaƙa?".

Nisawa Barde ya yi kafin ya ce. "Ai ka sani tun da muke da masarauta guda ɗaya kawai muke takun saƙa a duniyar nan, sune suke ganin cewa yanzu sun yi girma kuma sun bunƙasa sun kawo karfin da yakamata su bar ƙarkashinmu su fara cin gashin kansu wanda hakan kuma ba abu bane mai yiwuwa, dole su kasance a karkashinmu kamar yadda yake tun farko, idan kuma ba haka ba to a karo na biyu zamu sake yaƙarsu". Yana magana words nasa na fita one by one, cikin nutsuwa da tsantsar jarumta a voice nasa.

"Amma yaya ba shekarun baya da suka wuce bane kuka yakesu har sai da suka yi mubaya suka miƙa wuya, suka kuma ce sun tuba ba zasu sake ƙoƙarin gwada kwanji da mu ba?! Yanzu kuma me ya sake shiga tsakaninku?!". Cewar uncle Abbas.

Shiru Barde ya yi na a kallah 2mins kafin ya amsa da cewa. "Haka ne, a shekarun baya haka suka ce, amma yanzu suna ganin sun mayar da asarar da yakin baya ta ja masu, suna ganin yanzu sun sake kawo karfi a karo na biyu, duk wasu ƙaidoji da ya dace a yaki masarauta sun cika shi, duk wasu dokoki da idan masarauta ta taka ya kai a yaketa to sun takata, sun wuce iyakarsu ne yasa dole mu mayar da su kan hanya tun wuri, tun da sun yi abin da ya kai a yaƙesu ɗin".

"To amma yaya ka fara tura masu da warning mana". Cewar uncle Abbas.

Gimbiya MieMie ce ta karɓi zancen da cewa. "E daddy, ka daka masu warning a karo na biyu, tun da a doka ma sai an yi wa masarauta warning ɗaya biyu a na uku ne idan basu canza ba sai a yaƙesu, to mu daka masu warning a karo na biyu, idan basu ji ba sai a hura mana bososhin yaki kawai".

Shiru ya ɗan yi na ƴan sakanin kafin ya buƙaci jin ta bakinsu su Commander ZAFAR and su Malam lima da sauran manyan cikin fada.

Dukka kowa ya amince da a sake tura masu da saƙon warning, idan ba su ji ba sai a yake su, dama kwanaki an tura masu da warning na farko, suka yi burus da shi tamkar basu ji ba.

Jinjina kai Barden ya yi alamar gamsuwa da maganganun manya manyan cikin fada da kuma ƴaƴansa da kanin nasa, sannan ya rufe da cewa zai yi tunani a kan maganarsu.

Miƙewa Jaish ya yi cikin girmamawa ya ce da mahaifin nasa zai shiga cikin gida ya ga Mommansa, dan da kewarta ya dawo.

Jinjina mashi kai kawai Barde ya yi ba tare da ya yi magana ba. Nufar kofar da zata sada shi da cikin part ɗinsu ya yi. A tare gimbiya MieMie da Yah Jawad suka miƙe suka rufa mashi baya.

Jerawa suka yi a tare, sai dai a tsakiya suka sanya Aunty MieMie, da haka suka nufi elevator da zata kai su izuwa part ɗin Mommansa.

Sai tsokanar Jaish Aunty MieMie take yi wai ya ɗan yi ƙiba wannan tafiyar da ya yi, Dubai ta karɓesa sosai. Ko sannu bai iya ce mata ba, ya dai yi shiru yana jinta kawai, kamar wani gunki. Jawad ma da yake dama sun saba zama kamar kuramen, sai bai iya cewa komai ba, Aunty MieMie ce kawai take maganarta kuma ta bawa kanta amsa, dama ta iya sakosu a gaba kullum tana tsokanarsu a kan zata ga ta yadda zasu tunkari mace da sunan soyayya, bare ma shi Jaish sarkin kunya ga iya nuna halin ko in kula da iya yin banza da mutane, kullum idan suka haɗu suna hira sai ta saka shi a gaba wajen cewa zata ga karshen kunyarsa nan da lokaci kaɗan, zata ga zai iya cewa yana son mace ce ko zai tabbata babu aure, sai dai ya yi mata shiru kamar dai kullum, dan bashi da abin faɗa, maganarta ma sam bata shiga mashi cikin kunnuwansa.

A haka har suka isa katafaren part ɗin Momma wanda ya fi na kowa kyau da ƙawatuwa a gidan, an fi zuba kayan alatu na more rayuwar sosai a cikin part ɗin, saboda ƴar sarki ce kuma jikan sarki, sannan matar sarki, bugu da ƙari kuma ƴaƴanta manya manyan biloniyas ne na duniya, Jaish ba ƙaramin mai kuɗi bane, babban kai ne wanda ake ji da shi na wuce misali, sannan ƴayƴun Mommar maza da mata dukkansu kamshaƙan masu kuɗi ne kuma masu muryar faɗa aji faɗin Dubai dama a sauran manya manyan ƙasashen duniya, hakan yasa take da gata na wuce misali, shiyasa part nata ma daban yake dana kowa.

A saman wasu shegun luntsuma luntsumar sofas suka zauna, Aunty MieMie ta zauna a saman sofa mai zaman mutun biyu, Yah Jawad da Jaish ɗin kuma suka zauna a saman sofa mai zaman mutun uku.

Kuyangu masu yi wa Momma hidima a part ɗin nata a kallah zasu kai goma, sai dai kuyanga mama Haulat ce kawai take iya shigo mata har cikin babbar parlournta, saura duk suna ta part ɗin kitchen da sauransu. A yanzu ma Kuyanga mama Haulat kawai suka samu a cikin katafaren parlourn tana aiki, ga wani haɗaɗɗen kamshi tare da sanyin Ac mai ratsa zuƙatar masu shaƙa dake tashi a cikin parlourn, ta ko'ina tsab tsab tamkar yanzu aka zuba komai na cikin parlourn, tamkar yanzu aka cirosu daga cikin ledarsu, white floor tiles nan sai wani ɗaukar idanu yake yi saboda haskensa, babu datti ko ɗigo, mayun tsabta ne, basa shiri da datti ko miskala zarratin daga Mommar har ƴaƴan nata, bare ma Omar, GUYSON suke ce mashi a gidan, saboda shegen iya ɗaukar wanka da gayunsa, mayen buga basketball kenan kuma sarkin shan coffee...... Ya dai kammala secondary school yana shirin dawowa mu dama da shi......😅

Mama Haulat tana ganinsu ta zube gwiwowinta a ƙasa ta hau kwasar gaisuwa. Aunty MieMie ce ta ɗan yi kokari wajen amsa mata kafin ta tambayeta ina Mamma?.

"Ranki ya daɗe tana cikin bedroom nata a tare da auta gimbiya Zunaira". Ta basu amsa cikin rawar murya, tamkar ta yi masu laifi sun ce zasu hukuntata, duk ta firgice baiwar Allah.

"Jeki sanar da ita cewa zan shigo". Cewar Jaish, ya yi maganar kasa kasa da wannan sexy voice ɗin nasa.

A hanzarce ta amsa da toh cikin girmamawa, sannan ta miƙe da sauri ta nufi katafaren kofar da zai sadata da cikin luxury bedroom ɗin wanda kofar ma kawai abin kallo ne, tsadadden sosai.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull