Rawanin zalinci 1 complete - Chapter 23
Rawanin zalinci 1 complete Chapter 23: Rawanin zalinci 1 complete Chapter 23. Irin wannan daula na part ɗin Momma tamkar ba za'a mutu ba, wani irin shegen…
3,310 words
Irin wannan daula na part ɗin Momma tamkar ba za'a mutu ba, wani irin shegen king bed ne a cikin bedroom ɗin nata, yana da matuƙar girma bed ɗin, headboard nasa ya kai har kusan saman bangon, king bed ɗin nan ba kanana makudan dukiya Jaish ya zuba wajen sayarsa ba, daga ƙasar itali aka saye shi. Idan ka shiga cikin bedroom ɗin ma sai ka ɗauka ba'a duniya kake ba, ga wani hamshaƙin kamshin room perfume da yake tashi haɗe da daddaɗar sanyin Ac. Curtains dake jikin door and windows ma kawai abin kallo ne, baki ya yi kaɗan ya zayyano maku haɗuwarsu.
Shinfiɗe wannan bed ɗin yake da shinfiɗa ta alfarma irin na gidan manya manyan sarakuna, komai na cikin wannan luxury bedroom ɗin launin dark ash and golden color ne, hakan ba ƙaramin ƙawata idanun mai kallo ya yi ba.
Zaune Momma farar mace mai farar aniya, kyakkyawa kuma tauraruwar amaryar BARDE KING ZUHAIR ABDUL MALIK take a tsakiyar bed, shigar manya manyan ƴan gatan gimbiyoyi ne a jikinta, ga wani tsadadden alkyabba sky blue a jikinta, tana a sanye da hular alkyabbar a kanta, hakan yasa fuskarta bai bayyana sosai ba, ga shi ta sunkuyar da kai ƙasa tana kallon face ɗin Gimbiya Zunaira dake kwance a kusa da ita, ta tada kai da laps ɗin Mommar nata tana shafa jikin wani kyakkyawar wolf da yake a hannunta, wolf ɗin kyakkyawa ne sosai fari ƙal da shi, sai dai ɗan karami ne, amma yana da yelwar gashi sosai a jikinsa, hakan yasa Gimbiya Zunairar take jin daɗin shafa lallausan gashin jikin nasa.
Sai hira suke yi tamkar ba uwa da ƴa ba, kamar wasu ƙawaye, Momma tana ta shafa wannan kyakkyawar dark black curly hair Zunairan, abin gwanin birgewa.
Daga saman wani irin haɗaɗɗen luxury carpet wanda aka kawata samansa da wasu haɗaɗɗun throw pillows masu tambarin gidan sarauta Mama Haulat ta zube gwiwowinta a ƙasa, cikin girmamawa ta ɗan risinar da kai tana mai faɗin tana neman izinin yin magana.
Cikin sanyin murya momma kyakkyawar mace mai farar zuciya ta tambayeta "Menene yake tafe dake Haulat?". .
"Dama ranki ya daɗe Yah Jaish ne ya ce a sanar dake zai shigo". Tana magana tana ƙara risinar da kai, alamar girmamawa.
Ai a dubu ɗari gimbiya Zunaira ta miƙe zaune daga kwanciyar da take jin Mama Haulat ta ambaci sunan Yah Jaish............
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻
❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 16/7/2024.....✍️📚🌹
For information 0816139058 Whatsapp me only!!.
🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
E____________15🔥
Ai a dubu ɗari gimbiya Zunaira ta miƙe zaune daga kwanciyar da take jin Mama Haulat ta ambaci sunan Yah Jaish.
A hanzarce ta sauƙo kasa daga saman gadon, da gudu Wolf nata ya rufa mata baya, ɗan karami da shi gwanin ban sha'awa.
"Haulat je ki ce mashi ya shigo". Momma ta faɗa cikin sanyin murya, sai dai fa ita ma voice ɗin nata akwai kaifin mulki a tattare da shi, dama kuma ai dole a samu haka, uba sarki, kaka sarki, sannan miji sarki, ai mulki ya gama bin jininta, fin haka ma za'a samu a tattare da ita, izza da isa take da taƙama a jininsu yake, bare dama su fa modarawa sun yi kaurin suna na wuce misali wajen nuna isa, izza da kuma zuciyar bala'i, jininsu a tafashe yake, basu yafiya kuma basa ɗaga ƙafa, amma fa sai an taɓosu, haka kawai basu faɗa.
Miƙewa Mama Haulat ta yi tare da nufar waje bayan ta amsawa mommar da "Toh ranki ya daɗe Allah ya kara tsawon rai tare da nisan kwana farar mace mai farar zuciya".
Ko sannu momma bata sake cewa ba, da alama ita ma dai so silent ɗin ce, alamu sun nuna gadon shiru shiru su Jaish suka yi.
Gimbiya Zunaira kuwa tana fitowa parlourn bata nufi kowa ba sai wajen yayan nata, sai sakin uban murmushi take yi tamkar wadda aka yi wa albashir da kyautar gidan aljanna, baiwar Allah tana masifar son ƴan uwan nata, haka suma suna masifar kaunarta sosai.
Tana zuwa ba tare da ta yi mashi magana ba ta faɗa jikinsa tana ƴar dariya har gaf teeth nata dake a tsakanin kyawawan fararen hakwaranta suka bayyana.
Kyakkyawar hannunsa ya kai ya shafa kanta kafin ya ce. "Where's your hijab?". Ya yi maganar can kasa kasa.
Tana mai cigaba da sakin ƙayatattcen murmushin nan nata mai kara fito da tsantsar kyanta ta bashi amsa da.
"Na manta da shi a bedroom na Momma, ai tsabar murnar na zo na ganka ne yasa na manta, ina su mai ran karfe da su Yah Omar?".
Shiru ya yi mata yana kallon face nata yadda take zuba murmushi, yana bala'in kaunar kanwar nan tasa, baki ma ba zai iya faɗar son da suke yi mata ba, saboda tana da kyan zuciya kamar dai Mommarsu Gimbiya Rahilarh kenan.
"Auta wato Jaish kawai kika kallah a parlourn ko?". Cewar Aunty MieMie.
Kwanciya ta yi a saman kirjin yayan nata tana faɗin. "Aunty MieMie yanzu fa Yah Jaish shi ne sabo, ke ba ɗazun da muka baro wajen uncle Abbas na je wajenki ba? Shi kuma Yah Jaish yanzu ya kai almost 2 weeks fa ban ganshi ba, ki bari na gama ganinshi sai na zo wajenki".
"Kina da gaskiya". Cewar Yah Jawad.
Mama Haulat ce ta katsesu da cewa tana neman izinin yin magana.
Daga Jaish har Jawad babu wanda ya amsa mata, ko kallon in da take ma basu yi ba, su fa idan na ƴan uwansu ba to kowa a ƙasƙance mara galihu suke kallonsa.
"Haulat me Momma ɗin ta ce?". Cewar Gimbiya Aunty MieMie kenan.
"Yanki ya daɗe ta ce Yah Jaish ɗin yana iya shigowa".
Jinjina kai kawai Aunty MieMie ta yi ba tare da ta sake ce mata ko sannu ba, sai dai ta ɗaga mata hannu alamar zata iya tafiya ta basu waje.
Da gudu Wolf ɗin Auta ya zo ya haye jikin Jaish ɗin shi ma, ya manne da auta gam abinsa.
"Ɗagani na tashi baby". Cewar Yah Jaish.
Da sauri ta miƙe tsaye rike da ɗan Wolf nata dan su bashi damar ya miƙe ɗin shi ma.
Tashi ya yi cikin nutswa ba tare da ya sake yin magana ba ya nufi katafaren kofar da zata sada shi da cikin bedroom ɗin. Da ido Jawad da Aunty MieMie suka bishi, basu ce da shi ko ubban ba, kuma basu da niyar tashi su bi bayansa, da alama su ba ganin Momma suka zo yi ba, sun rako shi ne kawai, kuma sai suka kyale shi ya shiga shi kaɗai, dan ɗa da uwa akwai sirri a tsakaninsu.
Komawa jikin Aunty MieMie auta ta yi ta haye saman laps nata tare da kwanto da kanta a saman shoulder ɗinta tana murmushi.
Da ɗan karfi Aunty MieMie ɗin ta ja dogon hancin nan nata har sai da autar ta ce. "Wash Allah na Aunty MieMie kin cire mun hancina".
"Dama ai hancin naki ya yi tsawo sosai, gara na rage maki shi". Aunty MieMie ta bata amsa.
Ɗan kawar da kai Jawad ya yi yana faɗin. "Aunty MieMie baki nemi zaman lafiya ba, ki rasa hancin wanda zaki rage a gabaɗaya gidan nan sai na babyn daddy?". Ya kai karshen maganar yana miƙewa tsaye saboda call ɗin da ta shigo mashi cikin wayarsa a yanzu. Karar wayar kawai ya ji, tun bai duba ya ga wanene mai kiran nasa ba ya miƙe kamar yasan mai kiran nasa already. Kofar fita daga parlourn ya nufa, da yake kofofin da naura suke aiki kuma suna amfani ne da motsin ɗan adam, yana zuwa wajen kofar ta buɗe kanta da kanta.
Waje ya nufa ba tare da ya ce da Aunty MieMie ko uppan ba. Yana fitowa suka haɗu da Gimbiya Chuchu da ta fito daga cikin elevator a yanzu, ita ma wajen Momma zata je, dama renon Mommar ce ita, shiyasa kuka ga ta fi shaƙuwa da Gimbiya Zunaira sama da kowa a cikin gidan, a part ɗin Momma ta saba zama time da take karama, da ta girma ne ta koma part ɗin Akka, sam bata son zama a wajen mummy wato mamarta sosai, baiwar Allah da alama zama da Momma mace mai farar zuciya ne yasa ita ma take da saukin kai duk da bata kai Zunaira ba.
Kamar dai kullum aikin da aka saba, tana fitowa daga cikin elevator ta fara ɗaukar kyakkyawar fuskarta a hoto da wayar Fanan da yake a hannunta, idan baku manta ba Yah Jawad ɗin ya kwace nata wayar, hoto dai ba zata fasa ɗauka ba, abin ya bi jininta, ita da ko barci ta tashi sai ta kashewa kanta hotuna kala kala bare kuma ace ta yi wanka ta yi kwalliya, ai abin ba'a magana, shi ne har da aro wayar Gimbiya Fanan.
Tana aikin ɗaukar hoto tana tafiya, sai turo ɗan bakin nan take tana canza style kala kala, sam bata lura da mutun yana zuwa ba, da yake yanayin takalmar kafafunsa smooth shoes ne, irin na yawo a cikin gidan nan, suna da laushi sosai ta yadda sam basu kara idan mutun yana tafiya, hakan yasa sam bata ji tahowarsa ba.
Shi kuwa tun da ta fito daga cikin elevator yake kare mata kallo, ta canza shigar da yake a jikinta ɗazun izuwa wasu haɗaɗɗu kuma tsadaddun kayan, dama ita ƴar wanka ce, ga masifar san kwalliya, kamshi da kuma gyaran jiki kamar me. Sai tinkarosa take yi kallonta na a kan screen ɗin wayar, sam bai kauce mata daga hanya ba kuma bai yi mata alamar tasan mutun yana gabanta ba.
Karo suka yi ta bugu da faffaɗar kirjinsa a in da wayar Fanan ɗin ta faɗi ƙasa saman beautiful tiles ɗin, ji kake tas karar wayar.
A razane ta ɗago da kallonta izuwa kansa, dan taga wanenen?. Shi kuwa ɗaure fuska sosai ya yi tamkar bai san me ake cewa sakin fuska ba bare murmushi.
Ganin shi haka yasa ta yi wani irin ja da baya, murya na rawa ta fara cewa. "Kayi hakuri Yah Jawad wlh ban ganka bane, kuma......".
Bata kai karshe maganar ba ta dakata sakamakon wani kallo mai kama da harara da ya watsa mata, shi dai bai san ya zai yi da Chuchu da Sarina a kan waya ba, su biyun nan idan suka rike waya sai sun baka haushi, bare ma ita chuchu mayyar hoto da videos, kana zaune baka sani ba sai dai kaga ta ɗaura maka camera a fuska tana yi maka video kamar ka aiketa, ita kuma Sarina mayyar chatting ce, shi ne yasa Yah Jawad ɗin ya kwace wayoyinsu ɗazun, sai kuma gata dana Fanan ta karɓo, kai Allah mai iko, yanzu haka idan ya karɓi na Fanan ɗin ma anjuma na Mummy ko Momma or Akka zata ɗauko, na Akka kuwa bai isa ya kwace ba, dan bala'in tsohuwar nan ba iya ta zai yi ba! Zaman ka lafiya kada ka bari Akka ta kamaka ka yi laifi, idan hakan ya faru ka shiga talatin, ta in da take shiga ba ta nan zata fita ba, ta iya faɗa. Irin dai faɗa na normal tsofaffi da jikokinsu.
Shiru ta nutsu tana muzurai kamar wata maras gaskiya, sai wani ƴan kame kame take yi. Shi kuwa ya kafeta da ido yana tunani wai me zai yi ya raba yaran nan da cutar waya ne? Dan wayar ta zama cuta a garesu.
Kunsan idan ana kallon mutun duk sai ya rasa nutsuwarsa, ko da kuwa kallon mutunci da soyayya ake yi wa mutun yana rasa nutsuwarsa bare kuma kallon neman kalar hukucin da za'ayi wa mutun, ai kunsan dole Gimbiya Chuchu ta tsargu ta rasa nutsuwarta sosai.
"Wayar waye wannan?". Ya tambaya calmly kamar mai ciwon baki.
"Am.....inm...... Wayar Aunty Fanan ce..." Tana magana words ɗin suna rarrabewa saboda tsoro.
Miƙa mata hannunsa ya yi akan ta bashi wayar ba tare da ya sake yin magana ba.
Jiki na kerma ta tsugunna kasa ta ɗauko mashi wayar tare da miƙo mashi ita.
Bai kai ga karɓa ba call ya sake shigowa wayarsa da take a cikin aljihunsa, kira ta ɗaya da ta biyu duk sun katse, yanzu na uku ne ya shigo.
Burus ya yi da call ɗin da ta shigon ɗin, ya kai hannunsa ya karɓi wayar da Chuchun take miƙa mashi, sannan ya ce. "Anjuma ki sameni a bedroom ɗina". Yana gama faɗar hakan yasa kai zai wuce ta.
A hanzarce ta matsa ta bashi hanya. Wucewa ya yi ba tare da ya sake kallon in da take ba.
Tsayuwa ta yi tana bin bayansa da kallo ranta a cike tab da takaicin abin da yake yi masu na kwace masu wayoyi ya hanasu sakata su wala, ji take kamar ta je ta ja kunnen nan nasa ko zata huce takaicin da yake a cikin ranta.
"Allah Yah Jawad ɗin nan ya iya mugunta". Ta faɗa a fili tare da murguɗa baki kafin ta wuce ta nufi kofar shiga parlourn Momma. Shi kuma Jawad elevator ya hau zuwa second step.
A ɓangaren Jaish kuwa, ɗan bakin nan nasa a ɗauke da sallama kasa kasa ya shigo cikin bedroom ɗin na Momma.
A wannan karon bata a saman bed nata, ta sauko kasa samar shinfiɗin alfarma da ake yi wa gimbiyoyi a cikin bedroom nasu dan hutawa, yanayin shinfiɗin kamar da gashin ɗawisu ake yinsu, amma kuma ba gashin ɗawisu bane, carpet ne na alfarma da ake kyarasa haka kamar da gashin ɗawisu, ga bala'in laushi, sai tashin kamshi yake yi, sannan an zuba mata throw pillows manya manyan a saman shinfiɗin, dan kishingiɗa aka zuba mata su idan zata kishingiɗa sai ta yi amfani da su, ta fito a ainahin cikakkiyar gimbiyarta, alkyabbar yana kara fitar mata da kyanta sosai.
Kusa da wani throw pillow dake a gabanta Jaish ya ƙariso ya zauna a saman shinfiɗar da take ɗin kenan.
"Sannu da hutawa Momma". Ya faɗa kansa na'a ƙasa yana kallon shinfiɗar, dama na gaya maku muguwar kunya ke gare shi, sam baya son haɗa idanu da mutane.
Gyara zamanta ta yi a in da ta kara dakewa a cikin alkyabbar. "Jaish ka dawo lafiya? Ya gajiyar hanya ya kuma ka baro mun su Abbana?".
"Kowa yana lafiya Momma, and suna gaisheki sosai".
Bawan Allah ko part nasa bai leƙa ba, yana dawowa kawai iyayensa ya fara buƙatar gani, sune sama da komai a garesa, baya wasa da su kuma bi haɗasu da kowa ba, idan ba ya zo ya gansu ba ko wanka ba zai iya zuwa ya yi ba, shi ne yasa ya fara da fada ya duba daddynsu sannan ya taho wajen Mommansa, a kullum idan ya dawo daga tafiya haka ko daga office sai ya bisu ɗaiɗai ya fara duba suna cikin aminci kafin ya tafi ya je ya yi abin da zai yi.
"Ina amsawa ina Omar?". Ta yi maganar tana kai hannunta saman kyakkyawar bakin gashin kansa, a hankali ta fara shafa kan nasa tana saka mashi albarka.
"Baka je part naka ba ko?". Ta sake jefo mashi wata tambayar tana mai do da kallonta a saman kyakkyawar face nasa.
Nisawa ya yi kafin ya bata amsa da. Omar yana gidan uncle Rahab babban yayanta kenan, sai ku ya ɗaura da cewa. "Ban je part nawa ba, ai kinsan ba zan iya zuwa ko'ina ba har sai na zo na ganki".
"Allah ya yi maka albarka my son, ina alfahari da ku".
Da amin ya amsa mata kafin ya ce. "Momma kina lafiya ba wata matsala in wuce part nawa?".
"Lafiyata lou Alhdulillah nake, amma da ka je gidan Yah Rahab ya kasami su Jannat?".
Shiru ya ɗan yi na a kallah one mint kafin ya ɗago da kallonsa ya ɗan kalli face nata kaɗan, sannan ya sake sunkuyar da kan nasa ƙasa, sai ƙoƙarin tuna su waye kuma su Jannat a duniyar nan yake yi? Amma ina ya kasa tuna su waye su, dan bai ma san da su ba a duniya, ƴaƴan uncle ɗin nasa ne da shi bai ma san da zamansu a duniya ba, su kuwa sun san da shi, har ma sun saka shi a cikin zuciyoyinsu, dan muguwar farin jinin ƴan'mata ke gare shi sosai, duk in da ya shiga sai ya shiga can cikin zuciyoyinsu, amma shi sam baya kula kowa. E babbar magana kenan, lallai Jaish ka cika cikakken ɗan duniya, ƴaƴan uncle ɗin nasa ne ma bai sansu ba.
"Ba dai su ma su Jannat ɗin baka sansu ba kam?". Ta yi maganar tana aikin kallon face nasa da ya wani sunkuyar da kai ƙasa.
"Momma i don't know them". Ya bata amsa yana kai hannunsa ya riƙo nata guda ɗaya a cikin nasa.
Shiru ta yi a kan maganar su Jannat ɗin, dan tasan fin haka ma zasu aikata, dama ta yi sa'a suka san uncle Rahab ɗin kenan, kaɗan daga aikinsu su ce basu san sauran uncles ɗin nasu ba.
"Mommana zan iya tafiya?". Yana magana ya ƙoƙarin cire mata wani dankareran tsadadden diamond ring da yake manuniyar yatsarta, zoben ya kama mata yatsa sosai ne, har ya fara cin namar jikinta.
"Meyasa zaka cire mun? Zoben Ummiee na ne fa".
"Ummm shi ne yasa kika ki cirewa har ya fara cin maki namar jikinki ko? Tom ni dai ba zan iya ganin shi yana ƙoƙarin cutar mana da ke na barshi ba, zan cewa Ummiee ta aiko maki da wani, dan nasan nata daban ne". Ya kai karshen maganar tare da zare ring ɗin a hankali cikin dabara ta yadda ba zai yi mata zafi ba, tamkar ma bata san an cire ba, duk da kuma yake ya kama jikinta.
Murmushi kaɗan ta yi a cikin zuciyarta tana ƙara godewa Allah da ya bata ƴaƴa masu matuƙar kaunarta har haka, sun san farincikita ko bata gaya masu ba, haka zalika sun san bakin cikinta ko bata bayyana masu ba, sun san abin da take so da wadda bata so.
"Momma zan je na yi wanka na ɗan yi barci, inason gobe na fita office da sassafe, kinga almost 2 weeks bana nan, so yakamata na je office gobe dan naga me ake ciki".
"Jaish barci yamman nan fa bashi da kyau, idan ka yi shiri yanzu zaka tashi da ciwon kai".
"In Sha Allah zan kiyaye, but now am feeling to much of sleeping, zan yi kaɗan kin ji mommata?". Ya yi maganar in a low voice sosai!.
"Tom shikenan, ka kula sosai Allah ya yi maku albarka".
Da Ameen ya amsa mata kafin ya miƙe tsaye rike da ring ɗin nata, sannan ya nufi kofar fita da wannan taku nasa cikin nutsuwa haɗe da fadanci. Da idanu ta bishi har ya fice daga cikin ɗakin, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana mai kara godiya ga Allah a cikin zuciyarta.
Yana fitowa ya iske Aunty MieMie da Gimbiya Chuchu and Zunaira suna ta hirarsu, Yah Jawad baya wajen, tamkar zai tambayi Aunty MieMie ina Jawad yake? Sai kuma ya fasa tambayar yasa kai kawai ya wuce ba tare da ya bi ta kansu ba.
Ita ma Aunty MieMie bata ce mashi ko uppan ba, dan tasa da wuya ya amsa mata, Gimbiya Chuchu dama saboda ance mata yana cikin ɗakin ne yasa ta nemi waje a parlourn ta zauna, dan haka yanzu yana fita ta yi maza ta miƙe ta nufi cikin ɗakin da murnarta. A hanzarce auta ta miƙe ta rufa mata baya, suka bar Aunty MieMie ita kaɗai, gyarawa ta yi ta kwanta a samar sofar tare da fito da wayarta ta fara latsawa.