Kenza eBookz

Rawanin zalinci 1 complete - Chapter 39

Rawanin zalinci 1 complete - Chapter 39

Rawanin zalinci 1 complete Chapter 39: Rawanin zalinci 1 complete Chapter 39. Su Gimbiya Zunaira kuwa suna school abinsu, bama su san me yake faduwa a…

3,354 words

Su Gimbiya Zunaira kuwa suna school abinsu, bama su san me yake faduwa a cikin family part ba, su momma ma sam basu sami labari ba, amma ita Mama ta sami labarin daga bakin wata munafukar kuyangarta mai yi mata leƙen asiri, duk wani motsi a cikin gidan Mama tana sani, tana da CID da suke yi mata aikin leken asiri sosai, haka zalika Mammie mahaifiyar su Yah Jawad, duk wani abin da yake faruwa in ma a part ɗin King ko kuma a cikin fada dukka tana sani, kamar wata aljana, sai ta riga uncle Abbas jin labarin abin da aka zartar a fada, sai ka rasa ta ina take samo labaran, ta fi mama iya bala'i sau dubu, ita nata mai lasisi ne. Yanzu haka duk abin da yake faruwa a wannan part na bakin har Mammie ta samu labari, ta ji komai da ya faru daga farko har ƙarshe, zuciyarta fari kal abinta, wani irin sanyi ne ya ratsata, dama ba ƙaramin kai ruwa rana da uncle Abbas suka yi ba a kan cewa ita bata yarda wani Yusuf ya zo wajen Sarina ba, saboda idan baku manta ba ita burinta Sarina da Fanan su auri ɗaya daga cikin Prince na kingdom of power, so ita bata burin kowani namiji ya kusanci ƴaƴan nata, shiyasa ta kafewa uncle Abbas a kan lallai ita fa bata son wannan Yusuf ɗin.

Shi kuma ya ce ba makawa Yusuf sai ya zo, idan kuma Sarina ta yi na'am da shi to aure babu fashi. Wannan dalilin yasa da ta ji cewa ga abin da ya faru da su Yusuf ɗin ta fara sakin wani irin shu'umin murmushi wanda babu mai iya fassara me murmushin yake nufi sai ita da ta yi shi, ita kaɗai tasan nufin kayanta, amma dai murmushi ne mai tattare da abubuwa da dama a cikinsa, dan bana alkhari bane.

Haka zalika duk wani abin da kake son sani a dangene da fada to ka tambayi Aneesa ƴar Mama zaka samu labari dallah dallah idan ta yi niyar faɗa, sai ka rasa daga ina ita ma take jiyo labarin komai.

Idan muka koma ɓangaren Yah Jawad da Gimbiya Chuchu a hospital kuwa, yana zaune rike da waya yana latsawa, amma shi da kansa bai san ina yake shiga a cikin wayar bama, bai san me yake taɓawa ba, saboda kwata kwata hankalinsa baya a kan wayar, yana kan waɗan nan nurses ɗin da suke ta faman shafawa Gimbiya Chuchu wasu mayuka a kyawawan kafafun nata.

Baiwar Allah idanunta sun yi jajir sun ciko da kwallah, ji take kamar ta saka ihu, amma tana tsoronsa kada ya yi mata wani muguntar.

Daga karshe kasa daurewa ta yi saboda wani mai mai zafi da suka sanya mata, hakan yasa ta kasa iya cigaba da rike hawayenta, nan take suka fara simtiri a saman ƙuncinta.

Ta wutsiyar idanunsa yake kallon yadda take ruwan hawayen, ga gwiwowin nata sun yi jajir da su kamar zasu fitar da jini.

Sam bai san lokacin da a takaice ya ce da nurses ɗin su kyaleta haka ya isa ba.

Ɗago idanu suka yi suna kallonsa, sai a lokacin ya fahimci ashe ya yi magana, ɗan kara ɗaure fuska ya yi kamar ba shi ya yi maganar ba, ya wani tsare gida tare da miƙewa tsaye daga saman bed ɗin, ji yake yi kamar ya fita waje ya basu waje su cigaba da yin aikinsu, amma kuma ya kasa iya yin haka, kuma har ga Allah ba zai iya ganin abin da suke yi ba, hakan yasa ya ɗan juyo da kallonsa a kanta.

Siraran hawayen azaba sai simtiri suke cigaba da yi a saman kumatun nata.

"Jannat bana ce kada ki bari na sake ganin hawaye a fuskarki ba? This tears is for what again?". Ya yi maganar yana kara ɗaure fuska sosai irin shi boss ɗin nan kada a rai'na shi.

Cikin jin zafin ciwon nata ta fara yarfe mashi hannayenta tare da kara tsuke ɗan bakin nan, hawayen suna tsananta gudu a face ɗin tata, a shagwaɓe ta fara magana.

"Ka yi hakuri Yah Jawad, zafi sosai kafata take yi mun, ni ban san lokacin da hawaye suka zubo na, amma na tuba ba zan sake ba....."

Da kyar ta iya kai karshen maganar tata, saboda wani irin kuka da ya so kubce mata.

Wani irin tausayinta ne ya ji ya dira mashi a ransa, amma bai nuna hakan ba, sai ya danne ya ce. "Okey now goge hawayen kuma kada ki bari wani ya sake fitowa".

Cikin hanzari ta kai hannunta ta fara goge hawaye da shi, sai dai tana gogewa wasu suna kara zubowa sosai, saboda zafin da kafafun nata suke yi mata na dalilin wannan mai da nurses ɗin nan suka shafa mata.

Ganin hannayenta sun kasa iya goge hawayen ne yasa ya ciro wani kyakkyawar white handkerchief mai laushi kamar jikin mage daga aljihun suit ɗin jikinsa, sai tashin kamshi handkerchief ɗin yake yi, a hankali ya tako izuwa kusa da ita sosai ta wajen da kanta yake. Miƙa mata handkerchief ɗin ya yi a kan ta karɓa ta goge hawayenta da shi.

Hannu ta miƙo da nufin ta karɓa, a nan ya lura da yadda yannunta ke kerma kamar mai kermar zazzaɓi. Ɗan guntun mamaki ne ya kamashi, a tunaninsa zazzaɓi ne ya rufeta, hakan yasa ya kai ɗayan hannunsa saman 4 head ɗinta dan ya ji ko jikin nata da akwai zafin zazzaɓi.

Babu wani zazzaɓi a jikinta sai ma wani irin ɗumi mai daɗi da jikin nata yake da shi, kawai shegen tsoronsa ne yasa hannunta yake kerma.

Fuskarta ya kallah da kyau kafin ya ce. "Jannat lafiyarki kuwa?".

Karɓar handkerchief ɗin ta yi tare da fara goge hawayen nata tana mai gyaɗa mashi kai alamar e lafiyarta lou.

Su kuwa nurses ɗin nan sun saki baki suna ganin ikon Allah, ya dakatar da su daga yin aikinsu, basu karisar da shafa mata magungunar ba, su ga shi bai basu izinin tafiya ba, duk ya sakasu a tsakiya, sai kawai suka saki baki suna ganin ikon god.

Ɗan karemata kallo ya yi a yadda take kwancen na a kallah one mins kafin daga bisani ya ɗago ya kalli nurses ɗin. "Muna iya tafiya ko?". Calmly ya yi maganar.

"Sir bamu kammala shafa mata magungunar ba ai".

Satar kallonta yadda take aikin goge hawayen ya yi kafin ya ce. "Wajibi ne sai an shafa su dukka?".

A hanzarce cikin girmamawa tare da ladabi da biyayya suka girgiza mashi kai alamar aa ba wajibi bane sai an sha dukka, sun rigada sun shafa masu muhimmanci.

"Bayan waɗan nan abubuwa da zaku shafa mata ko nace wadda kuka fara shafa mata da akwai wani abin da zaku yi mata ne? I mean injection or drugs?".

Nan ma a hanzarce suka girgiza mashi kai alamar a'a babu, iya waɗan nan mayukan ne kawai.

Shiru ya yi bai sake yi masu magana ba, hannu ya miƙa masu a kan su nashi mayukan da suka rage basu shafa mata ɗin ba.

Cikin rawan jiki suka ɗauko suka miƙa mashi. Karɓa ya yi tare da sa kai ya wuce ya fita waje.

Jim kaɗan ya sake dawowa ba tare da mayukan a hannunsa ba, kai tsaye wajenta ya nufa, tana kanƙame da handkerchief ɗinsa a saman ƙuncinta ta kasa cirewa, saboda hawayen nata ya ki dai'na zuba, shi ne yasa ta bar handkerchief ɗin a face ɗin tata, da hawayen sun zubo sai ta yi maza ta goge dan kada ya gani, bata san cewa duk abin da take yi yana ganinta ba, yana ganinta sarai, amma ya nuna kamar bai ganta ba, tausayinta ma sosai yake ji a yanzu.

Hannayensa dukka biyu yasa ya ɗauketa cancak ya saɓata a saman shoulder ɗinsa, kai tsaye ya nufi waje da ita ba tare da ya sake bi ta kan nurses ɗin ba, sai cikin motarsa.

A guje driver ya buɗe masa kofar motar tasa, a gidan baya ya zaunar da ita, sannan ya zagayo ta ɗayan side ɗin ya shiga.

A hanzarce drive ya shiga tare da yi wa motar key, cikin kwarewa da iya aikin sosai ya figi motar suka bar hospital ɗin, kai tsaye family part suka nufa, dan wajen Akka zai mayar da ita kamar yadda ya ɗaukota, dan idan ba haka ba wannan tsohuwa ba zata rabu da shi ya zauna lafiya ba, so gara ya mayar mata da ita ya samawa kansa salama.

Ko da driver ya yi parking ɗin motar a tampatsetsan parking space da yake a fam part ɗin, basu fito ba, tamkar Yah Jawad bai san da an iso family part ɗin ba.

Ɗan satar kallonsa gimbiya Chuchu ta yi, dan ita tana son ta je ta kwanta, barci sosai take ji, Allah ya gani ba zata iya jurar zaman nan ba.

"Sir zan iya tafiya ko kuma akwai in da zan kai ka?". Cewar driver.

Da hannu ya yi mashi alamar yana iya tafiya ba tare da ya yi magana ba. A hanzarce ya fito daga cikin motar ya mai da marfin ya rufe.

Sun ɗauki a kallah 10 mins a haka shiru yana taɓa waya wanda shi da kansa ma bai san me yake yi a cikin wayar ba, kawai taɓa ta yake yi.

Sautin canzawar numfashinta daga dai'dai izuwa na wahala ne yasa ya ɗan nisa tare da juyo da kallonsa a kanta, ya wani sakata zunbula hijabi gwanin ban dariya, sai ta kara zama ƴar karama a ciki.

Kallon second biyar ya yi wa face nata kafin ya fara magana a nutse. "Wannan punishment da na yi maki is for fitowa with sleeping dress da kika yi ne kawai, now saura na haɗani da Akka da kika yi and ɓata mun lokacin da kika yi kika hanani zuwa office, by 8:30pm ki sameni a part ɗina".

Tsabar bakin ciki bata san lokacin da ta saka mashi kuka ba, dan tasan punishment ɗinsa shi da Yah Jaish babu kyau, ji na jiya ma da ya yi mata sai da ta dangana da asibiti bare kuma ya kara yi mata wani, wai tsabar mugunta har da wani cewa iya na fitowa da kayan barcin da ta yi ne kawai, to shi kuma na haɗa shi da Akka ya zai kasance? Ga hanashi zuwa office da ta yi, wlh ba zata yarda ba, hakan yasa ta kara sautin kukan nata sai dai ya kasheta kawai ya huta, tun da su dama basu iya komai ba sai mugunta.

Zuba mata idanu ya yi yana mamakin yadda take kukan, ita kuwa ta rufe idanunta gam dan ma kada su yi ido huɗu ta ji tsoronsa ta yi shiru, ba shirun da zata yi!.

Da dai yaga da gaske take yin kukan kuma bata da niyar dai'nawa, and kuma yasan yana ɗaukarta suka shiga ciki a haka tana kuka confirm sai ya haɗu da su uncle Abbas or uncle Taheer, ko ma dai King da kansa a hanya, da wuya ya gifta har ya kai part ɗin Akka bai haɗu da ɗaya daga cikinsu ba, barema Momma, idan ya haɗu da ita ai sai ta saka shi a kwana da masifa, dan bata son abin da zai taɓa mata autarta Gimbiya Zunaira da kuma Chuchu, tana ji da ƴan mata biyun nan, bare ma Akka, ai yana zuwa wajen Akka ya shiga talatin ma ba uku ba.

Dan haka sai ya kai hannu dan dole ya jawota jikinsa dan ya rarrasheta ta yi shiru ya samu ya mayar da ita wajen Akka ya kama kansa, da dai Jaish ne wlh ko kukan mutuwa zata yi bata isheshi kallo ba, sai dai ma ya kara mata da mari, kuma hakan ba zai hana shi ya sakata ta taka da kafafunta har izuwa cikin gida ba, ai idan ma Jaish ɗin ne wlh asibitin ma ba zai kai ta ba, sai dai Akka ta yi ta surutu har ta gaji ta yi shiru, tafiya ma zai yi ya basu waje sai dai duk abin da zai faru ya faru, Jawad yana da saukin kai sosai a kan Jaish.

Ɗan bubbuga bayanta ya fara yi alamar rarrashi, duk Akka ce sila, wannan tsohu ta koma Dubai su huta, yanzu sai ta kai karansu wajen iyayensu haka take yi, ta ja masu wahala, shiyasa dan dole suke lallaɓata.

"Ya isa haka kukan! Ki yi shiru ki faɗa mun kukan me kike yi?". Ya faɗa can kasan maƙoshinsa.

"To Yah Jawad ba kai ne ba, na ce ka yi hakuri ba zan sake ba, amma kaki ka hakura, ka ce zaka kara bani wani punishment ɗin, ga shi kuma kafata tana yi mun ciwo". Ta yi maganar cikin muryar kuka, da kyar da kyar ma take iya maganar saboda kukan, har da shessheka.

"Yanzu da na ce kizo cikin part ɗina ki sameni cewa na yi zan baki wani punishment ɗin ne?".

Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a tana daga kwance a kirjinsa ya ɗaura hannunsa ɗaya a saman bayanta, ɗayan hannunsa kuma yana rike da wayarsa.

"Kin san me zan yi maki idan kika zo part ɗin nawa ne?". Ya sake jefa mata tambaya yana mai cigaba da kallon face ɗinta.

Nan ma girgiza mashi kai ta yi alamar a'a bata sani ba.

"Amma kike yin kuka a kan abin da baki sani ba?".

Shiru ta yi tare da fara goge hawayenta da handkerchief ɗinsa da yake a hannunta wadda ya bata ɗazun.

"Ka yi hakuri ba zan sake ba, na tuba". Ta faɗa a kasale, saboda kukan da ta sha ma duk yasa barci take ji over.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ganin cewa ta dai'na kukan, sannan ya kai hannu ya ɗago haɓarta daga saman kirjin nasa, ya zama suna fuskantar juna.

"Kada ki yarda ki bari na sake ganin hawaye a saman wannan kumatun naki, in kika bari hakan ta faru to zamu ɓata, yanzu dai mun shirya tun da kin ce ba zaki sake ba, sannan kamar yadda na faɗa anjuma ki sameni a part ɗina, ta shi mun a jiki mu wuce cikin gida".

Ya kai karshen maganar tare da sakin haɓar tata yana mai kawar da kallonsa daga kanta.

Ajiyar zuciya ita ma ta sauke tare da tashi mashi daga jikinsa cikin sauri, ta ji daɗi koba komai ya ce ya hakura ba zai yi mata hukunci ba, kuma ya ce sun shirya, amma fa har yanzu akwai sauran haushinsa a ranta.

Buɗe kofar motar ya yi ya fito, ya zagayo ta side ɗin da take ya buɗe kofar, a saman shoulder ɗinsa ya saɓota suka nufi cikin gida.

Bai direta a ko'ina ba sai a saman katafaren bed ɗin Akka, yana sauketa call ta shigo wayarsa, a lokacin kuma Akka bata a cikin ɗakin, tana part ɗin King saboda abin da ya faru da Sarina, ta sami labari, shi ne ta yi maza ta je ta duba ko dai da gaske anyi mata fyaɗen ne su shiga uku, Akka sarkin zafin rai, tana jin labari tun bata ƙarisa wajen ba ta ce ba makawa kashe Yusuf za'ayi, wannan tsohuwa tafi King zafin nama da zafin zuciya ga iya faɗa kamar me.

Zama ya yi a gefen bed ɗin tare da yin picking na call ɗin saboda Mammie ɗinsa ce take kiransa, dama wayoyinsa guda biyu ne, wanda ya kashe a asibitin nan ita ce wayar da yake amfani da ita ma mutanen waje, wadda take hannunsa kuwa iya familynsa ne kawai suke da wannan number, su kawai yake kira kuma suke iya kiransa da shi, gabaɗaya ƴaƴan su King suna da tsari sosai a rayuwarsu, komai daki daki suke yinsa, basu haɗa abu kaza da kaza, kowanne suna ware mashi matsayinsa da ta dace da shi, wannan dalilin yasa a koma ina suke suke zama the most responsible parsons.

"Yanzun nan ka same ni a part ɗina". Shi ne abin da Mammie ɗin tasa ta ce.

Da akey ya amsa mata da shi tare da miƙewa tsaye, zura wayar a cikin aljihunsa ya yi bayan ya karse kiran kafin ya juyo da kallonsa a kanta. Idanunta a lumshe, da alama ta yi barci, dan dama barcin take ji.

Ganin alamun ta yi barci ne yasa a hankali kamar wani mai sanɗo zai yi sata, hijabin jikin nata ya ɗan yaye sama dan ya kalli kafafun nata, wato ba zai dubata idan idanunta biyu ba, dan kada ta rai'na shi, shi ne sai da ta yi barci ne zai duba kafafun.

Ajiyar zuciya ya sauke tare da mai da kallonsa a saman fuskarta, tana rungume mashi da handkerchief ɗinsa ga sauran guntun hawaye a face ɗin nata.

Hannu ya kai ya ɗan shafi lallausan gashin kansa kafin ya furta "Am so sorry my sister, nasan babu wanda ya taɓa sakaki kuka a gidan nan sai ni, gaskiya ban kyauta ba". Ya yi maganar a fili kuma kasa kasa ta yadda babu wanda zai iya jinsa, shi da kansa yasan ya yi laifi.

Cigaba da shafa gashin kan nasa ya yi yana mai tambayar kansa Jawad what's wrong with you ne? Ka tafi Mammie na jiranka, shi ne abin da zuciyarsa take gaya mashi. Nisawa ya yi kafin ya mayar mata da hijabin nata ya rufe mata kafafun nata, sannan ya janyo duv na Akka mai bala'in laushi, kamshi, kyau da kuma tsada ya rufeta da shi har izuwa wuyarta, kafin ya sa kai ya fice waje daga cikin ɗakin da sauri.

Kai tsaye wajen Mammie ɗinsa ya nufa kamar yadda ta umarta.

Bakinsa a ɗauke da sallama ya shiga katafaren parlourn ɗinta, duniya guda, duk wannan Daula bai ishe Mammie ba har take sake neman duniya idanu a rufe, sai ka rasa me take da buƙata again, idan kuɗi ne sune suka jikata a yanzu, a cikin daula take, idan mulkin ne ai suna ciki, ta fannin siyasa ma ana damawa da su, amma ita duk fa bai isheta ba, bama shi bane a gabanta ba, burinta kawai koma yaya ɗanta ya zama shi ne the next king of kingdom of power, babbar magana akwai show, ga shi kuma da alama ita da mama kudurinsu ɗaya, kuma suna da ƴan leken asiri sosai da sosai a cikin masarautar, dan duk wanda zai yi motsi a kan idanunsu yake yi, ga dukkan alamu ma ita Mammie tasan da mama da ƴan leken asirinta sarai, saboda ta fi mama iya makirci da tsiya ba kaɗan ba.

Izinin shiga bedroom ɗin nata ya ce da Kuyangun da suke yi mata hidima su nema mashi, ya yi maganar yana a tsaye, dan bai jin kamar zai zauna ma, duk baya jin daɗi a ransa, bai so ace ya jiwa Chuchu ciwo har haka ba, sam abin bai yi mashi daɗi ba.

Yana tsaye har kuyangar ta dawo wajensa tare da bashi amsar Mammie ta ce ya shigo.

Ba tare da ɓata lokaci ba bai bi ta kan kuyangur ba ya yi maza ya wuce ciki da sauri.

Zaune saman sofa da yake set a cikin bedroom ɗin nata ya iskota. Cikin nutsuwa ya yi sallama tare da ƙarisowa kusa da ita.

Saman carpet ya zauna tare da ɗaga mata gaisuwa cikin girmamawa.

Tana shirye cikin wani arnen lace mai bala'in tsada, ta zuba gwala-gwalai a wuya da hannu, tana da son duniya over, idan ta zuba wani kwalliyar sai ka rantse da Allah ba za'a mutu ba, gata da iya shan kamshi kamar me, nuna isa da izza a kan abu. Allah yasa gabaɗaya su Sarina babu wanda yake kama da ita, su Jawad dukka uncle Abbas suka ɗauko a kamani, shiyasa suke kama da ƴaƴan King, saboda uncle Abbas da Akka yake kama haka shi ma King da Akka yake kama, sai suka cure waje guda kamar mahaifa ɗaya.

A maimakon ta amsa gaisuwar tasa, sai ta jefo mashi tambaya kamar haka. "Menene a tsakaninka da Chuchu?".

A hanzarce ya ɗago da kallonsa izuwa kanta. Ɗaure fuskar nan ta yi tamau kamar hadari, Allah dai yasa kyakkyawace ajin farko, badan haka ba yadda ta wani uban ɗaure fuska nan ai da ba zata yi kyan ganuwa ba.

"Mammie akwai wadda ya ce maki akwai wani abin a tsakanina da Jannat ne?".

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull