Rawanin zalinci 1 complete - Chapter 40
Rawanin zalinci 1 complete Chapter 40: Rawanin zalinci 1 complete Chapter 40. "Tambayarka nake yi ka bani amsa ba ka sake jefo mun wata tambaya ba". Ta…
3,316 words
"Tambayarka nake yi ka bani amsa ba ka sake jefo mun wata tambaya ba". Ta faɗa a dake, irin ita big star ɗin nan, babu wasa.
Shiru ya ɗan yi yana mamakin abin, shi da kansa wlh bai san me a tsakaninsa da ita ba, kawai tana burgesa ya sani, duk cikin ƴaƴan King ita da auta ne suka fi burgesa, shiyasa in dai zasu haɗu sai ya ɗaga idanu ya kallesu, bayan haka bai san wani abin ba kuma.
"Mammie Jannat is my sister, bayan haka kuma ni ban san wani abin ba, babu komai a tsakaninmu".
Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ta sauke wanda sai da ya bashi mamaki, to me matsalarta da Chuchu ɗin da har zata damu kanta har haka dan ta gansu a tare? Ita Mammie ɗin nan lamarinta akwai ɗaure kai.
"Kana iya tafiya, amma kafin nan ka saurareni da kyau, naga kwana biyun nan kana yawan kasancewa tare da Chuchu, to bana da buƙatar hakan, bana son na sake ganinku a tare".
Da yake shi bai kawo komai a ransa ba, kuma bayan cewa Chuchu sistersa ce babu wani abin a ransa, sai ya amsa mata da okey kawai, sai dai abin ya ɗan bashi mamaki yadda ta ɗauki zafi a kan abin, sai ka ce Chuchu ɗin wata bare ce, kamar ba kanwarsu ba, kamar ba ɗiyar King ba, ai wannan ko kuyanga ce sai haka, lokaci guda ta wani ɗauki zafi daga ganinsu a tare, to wai ma ta ina ta gansu a tare har take zargin da wani abin a tsakanin nasu? Idan ma da wani abin kenan hanawa zata yi? Iko dai sai Allah, wannan lamari da ɗaure kai da ban mamaki, ga shi dai burinta ne su Sarina su auri ƴaƴan King, to shi Jawad kuma laifin me ya yi da ba'a yi mashi wannan fata?............🤔
Miƙewa ya yi ransa fes ya nufi waje bayan sun yi sallama, to dama shi me zai dame shi tun da a ganinsa dama babu wani abin a tsakaninsu? Ai shi normal ne, a ganinsa ko ta ce kada ya sake haɗuwa da Chuchu ma normal ne ba wata matsala.
Yana fita kai tsaye Company Jaish ya nufa, dan dama haka suke, wani lokaci sai su haɗe waje ɗaya su yi zamansu a office suna hira.
Mammie kuwa yana fita ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da miƙewa ta haye saman bed ɗinta tana tunani, ko me take tunawa oho mata.
After some hours.
Da Gimbiya Sarina, Gimbiya Zunaira, Gimbiya Fanan da kuma Gimbiya Aneesa ne zaune a saman katafaren bed ɗin Akka, wai sun zo duba kafar Gimbiya Chuchu, Akka ce nan ta gaya masu cewa kafar tata har yanzu yana ciwo bai warke ba, dama idan baku manta ba na gaya maku cewa sun fi yawan zama a part ɗin Akka, so suna dawowa daga school suka shigo part ɗin, a lokacin ita kuma Akka ta gama shiri zata nufi fada, dan ta je ta yi magana da King a kan su Yusuf, saboda a dokance za'a yanke masu hukuncin ba a familance ba, so dole sai a cikin fadar.
Sai hira auta da Gimbiya Chuchu suke yi, dama sun saba kamar wasu kawaye, Gimbiya Sarina tana latsa wayar Mammienta da ta shigo da shi, har yau Jawad bai bata wayarta ba, Fanan da Aneesa suna hira, dan suma suna shiri sosai.
"Aunty Chuchu kin ki ki gaya mana menene ya sameki a kafa ko?". Cewar auta, ta yi maganar kamar zata yi kuka, sarkin son ƴan uwanta kenan.
"Auta na gaya maki nima ban sani ba, da safe kawai na tashi naga kafar tawa tana ciwo, ba kema kin gani da safen ba?".
Gyaɗa mata kai auta ta yi alamar e ta gani.
Zata sake yin magana Gimbiya Aneesa ƴar mama ta rigata da cewa. "Ba wani nan ki faɗi gaskiya, ba Yah Jawad bane ya baki punishment?".
Dama na gaya maku duk wani labari da kuke so ku tambayi Aneesa ta sani, ko daga ina ta jiyo wannan kuma oho mata dai, ahalin gidan nan lamarinsu sai su.
Shiru kaɗan Chuchu ta ɗan yi kafin ta ce. "Haka ne, Yah Jawad ne ya saka kneel down, shi ne yasa kafafuna suke yi mun ciwo".
Zaro idanu waje Auta, Sarina and Fanan suka yi, basu yi zaton hakan ba, Sarina da Fanan sun ɗauka su kawai Yah Jawad ya tsana yake horarwa idan sun yi laifi, to yau dai ga shi harda Gimbiya Chuchu ta hau layi, hakan yana nufin kowa daga cikin bai tsallake ya horar da shi ba.
"A gaskiya Yah Jawad mugu ne". Cewar Sarina, ta yi maganar tana kwaɓe fuska, dama basa shiri sam sam, bata sonsa dan yana takura mata.
"Wlh Aunty Sarina ni babu ruwana idan ya jiyoki, kema kin san sauran idan ya ji abin da kika ce mashi". Cewar Fanan, tana magana tana zare ido, alamar tsoron Jawad ɗin sosai take ji.
Wani irin kallon up and down Sarinar ta wurga mata kafin ta ce. "Ni narasa ma meyasa su Yah Jawad suka zauna a gidan nan, kowa ya koma nasa gidan mana, ko kuma su tafi Dubai wajensu mai ran karfe sun fi buƙatarsu mu bama da buƙatarsu".
Aneesa ce ta ce. "Zaki iya zuwa ki gaya masu su tafi su baki waje ai".
"Dake nake magana ne? Ko mi sa'ar wasarki ce". Ta faɗa cikin izza. Dama nagaya maku da Sarina da Aneesa basu zama inuwa guda, kamar wuta da audiga suke.
"Ba dani kike yi ba, amma kuma na baki amsa ko kina da abin yi ne? Ke har ma kin isa ki yi da ni?". Cewar Aneesar.
A fusace Sarinar ta buɗi baki zata yi magana sautin tafiya ya daki doduwan kunnuwansu, wadda ya sanyasu nutsuwa tsit, da alama sun san mai wannan tafiya, dan harta ita kanta Chuchu dake kwance ɗan gefe da su sai da ta kara nutsuwa sosai, yadda kuka san waɗan da aka yi wa wahayin ganin mala'ikan mutuwa, duk suka wani yi tsit, Auta ce kawai bata canza daga yadda take ba.
Ƙasa kasa ya yi sallama kamar mai ciwon baki, yana sanye da wando three cuter a jikinsa, daga ta sama kuma polo shirt mai bala'in kyau, wandon ash color ce rigar kuma fara kal, ya yi kyau sosai, da alama bai jima da dawowa daga office ba.
Har suna rige rige wajen haɗa bakin cewa. "Good evening Yah Jaish".
Kallo ɗaya ya yi masu ya kawar da kansa tare da tambayarsu ina Akka take ba tare da ya amsa gaisuwar tasu ba, yana magana kamar wadda bakinsa yake ciwo.
Tsabar tsoronsa da suke yi sun kasa iya bashi amsa, Auta ce kawai ta ce. "Yah Jaish Akka tana fada".
Bai sake yin magana ba ya miƙo mata hannunsa a kan ta zo su je ta raka shi. Da sauri ta sauƙo kasa daga saman bed ɗin ta nufesa, hannunta ya rike suka nufi waje, kowa a gidan bashi da ɗan rakiya biyun auta, ita ce mai raka kowa duk in da zai je a cikin gidan, babu ruwanta, ita fa kowa sonta yake yi, ita ma kuma tana son kowa abinta.
Suna fita daga part ɗin suka ci karo da jarumi abin alfaharin KINGDOM OF POWER, wato HOORAIN yana tsaye shi da wani dakakken jarumin mayaki suna magana.
Cool murmushin nan nata mai kara fito mata da tsantsar kyanta tare da ɗan dimples ɗinta ta sakar mashi tare da cewa. "Hoorain tun jiya ban sake ganinka ba".
Jaish yana jinsu bai yi magana ba, bai ma ɗago yaga Hoorain ɗin ba, sai dai ya ɗan ji babu daɗi a ransa da autar tasu ta cika sakewa kuyangun gidan har ma da mayaka fuska, ita kowa nata ne, baya son hakan sam, amma bai nuna ba, yana rike da hannunta suka cigaba da tafiya kawai.
Ƙasa da kai Hoorain ya yi, har wa yau yana cikin kayan yakinsa tare da wannan hula da ta hana a kalli face ɗinsa, sarai ya lura da Jaish bai so auta ta yi mashi magana ba, hakance ma tasa ya iya bakinsa bai amsa mata ba, sai dai ya bita da kallo ta ƙasan ido kawai, yarinyar tana burgesa yadda ta fito daban a cikin ƴan gidan, bata da girman kai ga girmama mutane.
Sai da suka ɗan wucesu ne wannan mayakin da suke a tare ya taɓa shoulder ɗin Hoorain ɗin tare da faɗin. "Kabi a hankali abokina".
Jinjina mashi kai Hoorain ɗin ya yi tare da cewa. "Nagode manta kawai mu cigaba da maganar mu". Ya yi maganar kamar dai yadda ya saba yinta cikin sanyin murya kuma ƙasa ƙasa kamar baya son yi.
Ita kuwa auta a duniya tana son ganin face ɗin Hoorain, sai dai duk kuma lokacin da ta ce mashi ya cire wannan hula ta kallesa sai wani abin ya gifta a tsakaninsu ya hana shi cirewa, tana jin daɗin kasancewa da Hoorain ɗin a matsayin mai bata tsaro sosai, saboda yadda yake kula da ita ya fi sauran mayakan da suke kula da su Gimbiya Chuchu.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻
❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 31/7/2024.....✍️📚🌹
For information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
E____________25🔥
🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️
A ɓangaren su Aneesa kuwa, kamar dai yadda suka saba ne, kullum in suka haɗu da Sarina waje guda matuƙar iyayensu basu a kusa to fa rabuwarsu bata daɗi, dan haka a wannan karon ma Yah Jaish yana fita suka dasa daga in da suka tsaye da surutan nasu, ko wacce sai shegen son girma da nuna isa da izza.
Fanan da ta lura zasu cika mata kunnuwa sai ta miƙe ta nufi waje abinta, dan ba zata iya ba, ba yau bane farau. Ita ma Gimbiya Chuchu gyara kwanciyarta ta yi tare da basu baya tana fuskantar headboard na gadon, dan ma kada su takura mata sosai sai ta janyo duvet ɗin Akka ta rufe har kanta tana sauke nannauyar ajiyar zuciya, abokiyar hirarta wato auta ta tafi, dama ita idan ba da auta ba bata cika yin hira da kowa ba, ɗan gara ma Fanan, wani lokaci suna hira sosai, amma Sarina da Aneesa wlh babu mai iya halinsu sai su, murɗaɗɗun mutane ne wanda ba zaka taɓa gane ina alkiblarsu take ba.
Duk kuma faɗar da zasu yi fa a iya baki ne kawai yake tsayawa, ko da sunan wasa basa daka hannu a jikin juna, ba wai kuma dan basu iya faɗar ba, ina ai su faɗa a jininsu ma take, kawai dai basu taɓa ko da gwadawa bane, dan sun san zasu daku dukar mutuwa ma kuwa a hannun Jaish in suka yi faɗa, ina ga bugun da zai yi masu ko ganga iyaka, hakan yasa sai suke tsayawa a iya surutan nasu kawai.
Yanzu haka suka yi surutun nasu tsab suka kammala ba tare da ɗaya ya taɓa koda alkyabbar jinin ɗaya ba. Aneesa ce ta fara miƙewa ta fice daga cikin ɗakin. Ita kuwa hjy Sarina sai ta gyara ta kwanta a saman bed ɗin tare da cigaba da taɓa wayar Mammie abinta.
Da daddare misalin karfe 9 kowa ya kammala cin abincin darensa, masu saurin yin barci ma har sun yi barci, wasu kuma suna shirin yin barci.
Akka tana part na uncle Abbas, dan tun da yamma ya ce kansa na yi mashi ciwo, kuma gobe yake son komawa, so Akka tana wajensa, ta je duba ciwon kan nasa.
Gimbiya Chuchu ce kawai kwance a saman bed ɗin Akkar, ita kuwa Gimbiya Zunaira tana wajen Mommarta yau, ta je ta wani haye mata saman bed tare da tada kai da cikyarta suna ta hira na tsakanin uwa da ƴa, kamar wasu ƙawaye, sai shafa lallausan bakin arab hairnta momma take yi, tana ta bata labarin ƴan uwata su uncle Rahab kenan da suke can Dubai.
Ita dai Momma har ga Allah tana wahala rayuwarta a wannan masarauta, shiyasa take yawan zuwa Dubai, ko da kuma ta gayawa mahaifinta ga abin da yake faruwa da ita, sai dai ya ce mata ta kara tsananta addu'a sosai, yau tsawon shekaru talatin kenan tana fama da wannan matsala, sai dai yana yin sauki, ya fi taso mata ne a duk lokacin da ta samu ciki, har ta haifi wannan ciki tana fama da wannan mahaukacin razanar da ita da ake yi, ba kalar halittar da bata gani, wani lokaci idan abin ya yi tsamari har suma take yi, sai an danganata da likitoci, amma kuma idan bata da ciki tana fin shekara biyu zuwa uku bata ga wani abin tsoro ba, sai jefi jefi.
Da yake tana tsananin kaunar gimbiya Zunaira sai aka fi yawan tsorata da fuskar Zunaira ɗin, da tsakar dare zata jiyo muryar autar tata tana ta faman kuka a cikin toilet, idan ta tashi ta je ta duba kuma sai ta ga yes fuskar Zunaira ɗin ce, amma kuma babu gangar jiki, sai jini dake zubo mata daga hancinta, bakinta izuwa wuyarta, wani lokaci idan ta taso daga kan gado da addu'ar tashi daga barci, sai bata tsorata zaka ji ta furta sunan Allah sai abin ya ɓace, amma duk ranar da ta manta bata tashi da addu'ar tashi daga barci ba to ba shakka tana mahaukacin razana har ta kurma ihu, kuma abin baya ɓacewa sai dai ya kara razanar da ita, baya rabuwa da ita har sai ta samu ta furta wata addu'a ko sunan Allah. Haka baiwar Allah take ta fama, ta kuma ƙasa iya gayawa King Zuhair ga abin da take fuskanta, mahaifinta kawai ta iya gayamawa, shi ma kuma da alama saboda babban malami ne sosai kuma sarki mai karfin iko ne yasa abubuwan basu iya rufe mata baki a kansa ba, ta iya gaya mashi. Ko mahaifiyarta bata iya gayawa ba.
Sai hira suke zubawa kamar wasu ƙawaye, a haka Jaish ya shigo ya samesu, sanye yake da kayan barci masu bala'i kyau da tsada, already ya nemi izinin shigowa ta hanyar turo mata massages a wayarta, saboda ko da ya zo parlourn bai sami su kuyanga Mama Haulat ba, sai kawai ya turo mata sako, ta kuma amsa mashi da ya shigo, shi ne yasa ya shigo.
Kasancewar suna a saman bed sai shi kuma ya zauna a saman bedside drawer kusa da lamp dake a kunne yana bada wuta light green.
"Good evening my Momma". Ya faɗa yana sunkuyar da kansa ƙasa.
"Yah Jaish ɗazun baka bani amsata ba". Cewar auta.
"Evening Jaish how was the night?". Cewar Momma.
Alhdulillah ya bata amsa kafin ya ce da auta. "Which amsa kenan?".
Ɗan turo baki ta yi kafin ta ce. "About my journey to Dubai, ina son dawowa a tare da yaya Omar ne fa".
Shiru ya yi mata bai amsa ba, dan ya rigada ya yanke hukunci babu in da zata je, abin da next week Omar ɗin zai dawo, dan haka ta jira shi a nan kawai.
Hannun Mommarsa da take ta faman shafa lallausan gashin auta ya riƙo cikin nasa, a hankali ya zura mata wani haɗaɗɗen dankareran diamond ring irin nata da ya cire mata ranar, dama idan baku manta ba ranar ya cire mata nata ring ɗin saboda ya yi mata kaɗan, to shi ne ya yi waya wa a powerful king of Dubai ya aiko mashi da wani irin wannan sak, wato kakansa kenan wanda ya haifi Momma ɗin kuma uncle ga King Zuhair kani ga Akka kenan, dama idan baku manta ba na gaya maku King Zuhair Momma ƴar uncle ɗinsa ce ya aura, aure dangi ne.
Sosai ta ji daɗin wannan ring ɗin, wani sanyi ne ya ratsa mata zuciya yadda ƴaƴanta suke nuna mata so, ya cire wancan da kasa ya kuma kawo mata mai ɗan girma ya saka mata, baban abin birgewa ma ko da ya sanya mata ring ɗin sai da ya ɗan sumbaci hannun nata da wannan ɗan ƙaramin bakin nasa, sannan ya ce.
"Momma ring bai taɓa burgeni ba before, but a hannunki is so very very beautiful da har na ji ina sha'awar sakawa ni ma, you're so special our Momma". Cikin nutsuwa tare da sanyin murya ya yi maganar.
Wani irin madarar daɗi ne ta ji ya kara lulluɓeta, yabo yana da daɗi, amma kuma irin yabon da Jaish yake yi mata ya fi na kowa daɗi. Shi kuma Jaish ɗin a duniya iya ita da King kaɗai ya iya yabawa, ko auta idan ta yi kwalliya suka haɗu ta tambayesa ta yi kyau, kai kawai yake gyaɗa mata, wani lokaci ko kallon kwalliyar tata ma baya yi, amma idan Mommarsa ce ya rinƙa yabon kyanta kenan koda bata yi kwalliya ba, ita da King kaɗai ya iya yabawa a duniyarsa, bayan su ko kansa bai iya yabo ba, yo shi da a duniya ma kwata kwata da mutane huɗu zuwa biyar yake iya buɗe baki ya bawa amsa, saura sai dai ya bisu da ido ko kuma ya gyaɗa masu kai, idan kun ji ya buɗe baki yana magana voice nasa na ɗan fita da sauti kaɗan ma to da Mommar ce ko King, su biyun nan yake yi wa magana har voice nasa ta ɗan fita, saboda baya son ya zamana ya yi masu magana basu ji ba sai sun sake wahalar da kansu wajen sake tambayarsa me ya ce? Baya son haka shiyasa yake ɗan buɗe murya idan zai yi masu magana, bai ɗauki iyayen nasa abin wasa ba, sune komai nasa, yana bala'in kaunarsu fiye da komai, da da hali ma ina ga har abinci zai rinƙa tauna masu dan kada su sha wahala.
"Yah Jaish baka yi magana ba". Cewar auta, ta yi maganar a shagwaɓe sosai.
"Baby I will think about it, ki bari zuwa gobe".
Ya bata amsa yana sakin hannun Mommar tasu.
"Allah ya yi maka albarka my son". Cewar Momma.
Da Amin ya amsa mata kafin ya sake cewa. "Momma zan iya tafiya ko kina buƙatar wani abin?".
Girgiza mashi kai ta yi alamar bata buƙatar komai zai iya tafiya.
Miƙewa tsaye ya yi tare da kai hannunsa ya shafi lallausan kumatun auta da ta tsare shi da idanu. "Sarkin kallon mutane ayi addu'ar barci kafin a kwanta". Ya faɗa haɗe da ɗan jan karan dogon hancinta.
Wani irin cool murmushi ta sakar mashi har sai da dimples ɗinta suka lotsa, wani irin sihirtacen kyau ne ya kara bayyana a saman face ɗin nata, dama ita fa ba baya ba wajen kyau, wlh ta fi su Jaish ɗin dukka kyau, yadda kuka san duk an haɗe mata kyansu ne aka cure waje guda aka bata, idan ka gansu dai dukka zaka san cewa ƴaƴan Momma ce saboda jini ba wasa ba, amma dai ta fisu kyau har twins Obaid and Omaid, Yah Omar dukka, ita ce tauraruwarsu.
Ɗan yatsarsa karami ya ɗan saka mata a ramin da dimples ɗin nata suka lotsa, ya ɗan danna wajen kafin ya ce. "Naki ya fi na kowa kyau a gidan, kin yi mana wayo". Ya yi maganar kasa kasa tare da ɗauke hannunsa daga saman face ɗin tata. Sai binsu da kallo Momma take yi, gwanin ban sha'awa abin, akwai soyayya da kauna mai karfi a tsakaninsu. Daga King har Momma dukka suna da dimples, hakan yasa gabaɗaya ƴaƴan Momma suke da shi, ita ma Gimbiya Chuchu tana da shi, amma Gimbiya Aneesa ƴar Mama bata da shi, uncle Abbas yana da shi, amma su Sarina duk basu da shi, Akka ce tushen dimple ɗin nasu, duk da ta tsufa idan tana magana zaka gansa a face nata ɓaro ɓaro.