Rawanin zalinci 1 complete - Chapter 75
Rawanin zalinci 1 complete Chapter 75: Rawanin zalinci 1 complete Chapter 75. Haƙiƙa kuwa ya sha kwalliya fiye da kullum, duk da cewa shi dama tun…
3,350 words
Haƙiƙa kuwa ya sha kwalliya fiye da kullum, duk da cewa shi dama tun ainahinsa ɗan kwalliya ne, babban yaro ne ɗan kwalisa, shegen son gayunsa ma yasa suke ce mashi Guyson, amma fa gayun da ya ci yau na musamman ne, ƙananan kaya ne a jikinsa, wandon jeans and polo shirts masu bala'in kyau launin white color up and down ɗin dukka, ya gyara kyakkyawar dark black arab hairn nan nasa, abin ba'a magana, kamshi kuwa duk yadda ka kai ga sonta ina ga Guyson ya fika sonta, yana bala'in son kamshi sosai.
Wani irin faɗuwar gaba Leesharh ta ji da jin sunan Yah Ramish a bakin Sharifat.
"Kai Masha Allah, Allah ya dawo da shi lafiya, shiyasa naga anata hidima a gidan". Cewar Leesharh.
"E ai dole kiga ana hidima, da Yah Ramish, Yah Rizwan, Yah Bilal, Yah Raj su ɗin na musamman ne a wajen Abbie, yana ji da su fiye da tunaninki, kamar shi ya haifesu, shekaru dayawa fa suna nan ya ki yarda ya bari su je ƙasar Tunisia, saboda ba ya son su yi nisa da shi, yanzu ma ba dan Queen mama bata da lafiya ba da ba zai iya barinsu su yi nisa da shi har haka ba, ko tafiyar da kika ga Yah Bilal ya yin nan dan saboda aiki ne, badan haka ba suna nan a tare da Abbie". Ta kai karshen maganar tare da zuro kyawawan kafafunta kasan bed ɗin.
Miƙewa Guyson ya yi yana faɗin. "Is time, Shareefat lokacin zuwa airport ya yi". Ya kai karshen maganar tare da nufar hanyar fita.
Da sauri ta miƙe ita ma tana faɗin. "Wait for me mana Yah Guyson, Leesharh zan bisu airport, sai na dawo, idan kuma zaki bini ki zo muje, a jerin tawagar motacin Yah Ramish zamu tafi".
Da sauri ta girgiza kai tare da faɗin. "A'a ina tsoron binki, sai dai kun dawon kawai".
"Me kike tsoro?". Cewar Guyson. Ya yi maganar tare da tsayawa daga tafiyar da yake yi, ya ɗan juyo gareta.
"Ina tsoron waɗan nan securitys masu face mask ɗin, da kuma waɗan can masu manya manyan bindigun, fuskokinsu tsoro yake bani".
Murmushi ya yi har sai da haɗaɗɗiyar dimple ɗinsa ta lotsa. "Kada ki ji tsoronsu, babu abin da za su yi maki, kawai face ɗinsu ne kullum a fusace, amma ai ba zasu yi wa mutun komai ba ba tare da ya yi masu laifi ba, dan haka ki dai'na jin tsoronsu".
Da okey kawai ta amsa mashi, amma fa tsoro kam dole ta ji, waɗan nan fusatattun mutane masu kama da dodannin, ita idan aka ce mata waɗan nan securitys ɗin suna cin namar jikin mutun ɗanya ma ba zata musa ba, domin kuwa fuskokinsu babu ɗigon annuri ko sauki a kansa, waɗan nan idan suka kama mutun ya yi masu laifi Allah sarki, sai dai wani ba shi ba, sun iya ganawa bawa azaba.
Wucewa Guyson ɗin ya yi ya nufi waje, da sauri Sharifat ta riƙo hannunsa tana murmushi, a haka suka fice daga ɗakin suka bar Leesharh. Ta ɗan jima a zaune tana tunanin saƙon da aka turo mata yau da safe, saƙo ne da masu nikaf suka turo mata a kan lallai ta nemi wanene or wacece take kaiwa Ramish abinci a cikin ma'aikatan dake gidan, idan ta gano wanene to lallai ta san ta yadda zata yi su ƙullah alaƙa, su sami kusanci sosai, idan suka saba shikenan akwai wani aikin da zasu bata, wannan shi ne saƙon, yanzu ya za'ayi ta nemo mai kaiwa su Ramish abinci a cikin ma'aikatan gidan nan fisabilillahi? Ma'aikata ba ɗaya ba biyu ba, kowani hawa da nasa ma'aikatan, ita da kwata kwata ma bata san a wani hawa su Ramish ɗin suke ba, ba ta taɓa ganinsu ba, yanzu ya zata yi kenan? Wannan shi ne abin da ya tsaya mata a ranta take ta aikin tunani a kansa tun safe.
Daga karshe dai ta miƙe ta nufi waje domin ta koma cikin room ɗinta, sai tunanin take yi ko dai ta tambayi Sharifat wacece take yi wa su Ramish aiki ne? Ko kuma ta tambayi su Radia? Tana tsoron tambayarsu kuma kada hakan ya zamar mata matsala, kada wani abin ya zo ya faru ace ai ita ce ta taɓa neman masu yi mashi aiki ta shiga uku.
Babbar parlourn ta fito tana tafiya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki. Wani irin razana ta yi tare da zaro idanu tana kallon Ummie dake a zaune a saman sofa mai zaman mutun uku tare da wata jibgegiyar hajiya ita ma tana zaune a saman sofa mai zaman mutun uku. Sosai Leesharh ta zaro waɗan nan manya manyan idanun nata tana ganin wannan mata.
"Wlh ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba wannan ita Hajiya two seater da ta ɗauko ni daga AAJ House". Ta faɗi wannan magana a cikin zuciyarta tana mai cigaba da kallon matar.
Matar bata lura da ita ba, haka zalika ita ma Ummie bata lura da ita ba, da yake parlourn yana da matuƙar girma, daga in da suke zaune da in da take akwai rata sosai da sosai, so basu san da ita a cikin parlourn ba, su suna a saman sofas da suke ta kusa da dining room ne, ita kuma kunga tana ta ɓangaren ɗakinsu Sharifat, akwai rata a tsakaninsu.
Hannu ta kai ta sake goge idanuta sosai domin ta tabbatar da abin da take gani. Tabbas dai wannan mata ce a cewarta, duk da tasa nikaf lokacin zuwanta AAJ House ta ɗauketa, hakan bai sa yau da tazo gidan nan babu nikaf ta ganeta ba, LEESHARH akwai ƙwaƙwalwa sosai, da idon wannan mata ta iya ganeta babu nikaf, idan baku manta ba dama tana iya banbantasu da yanayin idanunsu, to fa hakance yasa take tunanin wannan jibgegiyar hajiya ita ce hajiya two seater.
Lallai akwai cakwakiya, kenan makashin Ramish suna a tare da shi? Meya kawo wannan hajiyar gidan? Wacce iriyar alaƙa yake a tsakaninta da familyn Abu Abdussalam? Ya abin yake? Anya tana da alaƙa ta jini da su kuwa? Wacece ita?. Alƙalamin na ne kawai zai warware maku wannan cakwakiya, ku dai mu cigaba da tafiya, mun kusa cinwa ainahin in da RAWANIN ZALINCI yake........🥱
Salallaɓawa Leesharh ta yi ta nufi hanyar fita daga parlourn ba tare da sun ganta ba, tunani take yi kenan haka kamannin masu nikaf ɗin nan yake? Haka kamanin hajiya two seater yake?!
Kanta ya ɗaure sosai, ta kuma shiga ruɗani, ji ta yi ta dai'na gane komai, a haka ta fice daga parlourn cikin dabara ba tare da sun ganta ba. Sai hira suke zubawa a tare da Ummie, da alama suna cikin farinciki tare da annashuwa.
Leesharh tana shiga cikin room ɗinta ta nufi wajen windownta dake fuskantar harabar gidan, ta zuge windown tare da janye labule ta tsaya tana kallon cikin gari, tunani ya taru ya yi mata yawa a cikin ƙwaƙwalwata, har ji take yi kanta yana yi mata ciwo, wannan wace iriyar bala'i ce? Ta tambayi kanta da kanta.
Tana tsaye a wajen jerin gwanon danƙara danƙarar motocin masu zafa suka fara fitowa daga cikin parking space na gidan, sun kasance a jere cikin tsari, hakan ba ƙaramin burjewa ya yi ba, motocin ƴan'sanda uku ne suka yi gaba, sannan waɗan nan jerin motoci suka rufa masu baya, sai motocin sojoji uku suka take masu baya. A kallah motocin zasu kai 15, da alama airport suka nufa, da kallo kawai ta bisu har suka fice.
Da fitarsu bai fi da minti biyu ba wasu jeren danƙara danƙarar motocin ma suka sake danno kai daga parking space ɗin, taɓe baki ta yi tana mamaki tare da kara jijjinawa girman gidan Abu Abdussalam, bata san daga ina parking space na gidan ma yake ba, ita dai tana ganin motocin kawai suna ketowa ta harabar gidan wadda kuma take da yakinin daga parking space suke fitowa, dan duk motocin gidan ne, duk suna ɗauke da tambarin gidan. Motocin da suka fita na farko na su Ramish, Dr Raj and Rizwan ne, na biyun nan kuma na sauran ƴan uwa, duk airport suka nufa dan tarbo Bilal, ga motocin dukkansu suna da tinted, ba zaka iya ganin waɗan da suke a ciki ba.
Cikin kwanciyar hankali suka hau saman wannan haɗaɗɗiyar shinfiɗaɗiyar titin da ta fita zuwa babban gate na fita unguwar tasu, yadda motocin suke tafiya kai ɗaya sai sun burgeka.
Ba normal airport suka nufa ba, kai tsaye AL MINHAD AIR BASE suka nufa, wato airport na AIR FORCE kenan, kada ku manta shi Bilal AIR FORCE ne.
Ko da suka isa airport ɗin jirgin su Bilal ɗin bai sauƙa ba, saura five mins ya dira. Hakan yasa suka yi parking a katafaren parking space na airport ɗin, sai dai babu wanda ya fito daga cikin motar tasu, duk suna ciki. Babban airport ne sosai, kalar fentin bangon airport ɗin ma kalar uniform na air force ɗin ne, dan airport ɗinsu ne, ga jiragen yakinsu bitjik ta ko'ina.
Ta ko'ina idan ka juya dakakkun jami'ai masu sanye da kakin air force ne cike a cikin airport ɗin, sai kai komo suke yi, kowannensu ka ɗaga ido ka gani ba zaka so ka sake ganinsa ba, saboda yadda kyawawan fuskokinsu suke a turɓune a kuma fusace, dakon jiran jirgin ƴan uwansu jami'an kawai suke yi, kowannensu ka gani a shirye yake da a mutu ko ayi rai, sun riga da sun sayar da rayukansu, yanzu fa idan suna yaki da zarar an yi bombing na jirginsu an jefe shi daga sama fa shikenan, kashesu bai da wuya, shiyasa ba kowa yake yarda da aikin ba, gara sojoji sau dubu, su sojoji suna iya ɓuya a sunkuru idan ana yaki, su kuwa air force da suke sararin samaniya kowa yana gani, ana jefa nakiya zata yi bombing na jirgin yakin nasu, ko gawarsu kuma ba'a samun gani, dan tarwatsewa suke yi, wasunsu kuma jirgin mai ɗauke da ƙananan nakiya ake tasa ta bi tasu ta yi bombing su tarwatse, musamman idan ƴan ta'addan da suka je yaƙan shegun kai ne, abin baya masu ta daɗi, sai mai taurin rai yake yarda ya yi wannan aiki. Ko shi Bilal Mummynsa ta so ta hanashi yin wannan aiki, King ne ya ce a'a namiji da jarumta aka san shi, shi bai haifi rago ba, jarumai ya haifa, dan haka Bilal zai yi wannan aiki tun da ita ya zaɓa, kun san halin King ai, akwai tafasasshen jini, ita ma Akka ta zage har da karawa abin armashi, wai idan Mummy ba zata iya ganinsa a gabanta yana wannan aiki ba to ya haɗa kayansa ya koma Dubai, wannan shi ne dalilin da yasa tun farko suka dawo Dubai da zama abinsu, Akka ce nan ta hurawa abin wuta, kun santa ita ma akwai son sabgar jarumta, bata da wasa, bata son ragwaye, wannan da namiji ne ita ban san a iya ina zata tsaya ba, duk ta reni su King sun taso da Barden zuƙata, babu tsoro sai ma ban tsoro da suke da shi.
Jiga jigan Fighter Jets ne suka dinfaro airport ɗin. Jiragen A400M Atlas da C-130J Hercules, sune a gaba da suka fara saukowa a filin saukar jirgi na airport ɗin. Da saukarsu kamar da two mins haka sai ga wasu Typhoon FGR4 da F-35B Lightning suma suka yi landing, dukka jirage ne na AIR FORCE. Jirgin F-15 Eagle ce a tsakiya, wadda kuma ta kasance ita ce na Bilal ɗin, a cikinta yake, sannan jiragen Typhoon FGR4 da F-35B Lightning suka rufa mashi baya wajen sauka, su ne suke takewa F-15 Eagle na Bilal ɗin baya, so nasa tana dira da kamar minti biyu suma suka dira.
Nan take jami'an Air force ɗin da suke cike a wajen suka fara cincirindon ƙarisawa wajen jiragen.
Jaruman Jami'an Special weapons and tactics guda biyar ne suka fito daga cikin jerin gwanon motocin su Ramish. Gabaɗaya fuskokinsu a matuƙarn turɓune, kamar waɗan da aka aikowa da saƙon cewa wutar jahannama zasu shiga, kun ga kuwa ai ba zaman lafiya mutun ya ji zai shiga wuta.........😅
Duk suna sanye cikin bakaken kaya ne, harta takalmar dake a kafafunsu bakake ne, ga su dai fararen arab guy's kyawawa, amma kada ku so kuga yadda suka haɗe rai kamar ba lafiya ba. Bubbuɗe kofofin motocin nasu Ramish su ka yi, hannayensu na sanye cikin black hands gloves, from up to down dai shagar bakake ne, ba uniform ɗinsu suka sanya ba.
Omar da Sharifat ne suka fara fitowa kafin su Dr Raj su rufa masu baya. Ramish shi ne a karshen fitowa, sai da ya kalli kofar F-15 Eagle na Bilal ta buɗe sannan shi ma ya zuro kafafunsa dake a sanye cikin wasu tsadaddun shoes masu matukar kyau waje. Da alama yana son su fito a tare da Bilal ɗin ne, Dr Raj da Rizwan sun yi gaba abinsu, shi kuwa ko da ya sako kafar tasa waje ma sai da ya nuna wannan, izza da fadanci tasu ta jinin sarautar kafin kuma a cikin nutsuwa ya fito waje..............
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻
❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 4/9/2024.....✍️📚🌹
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
E____________45🔥
Masha Allah. Sanye yake da tsadaddun suit masu zafa, idanunsa a sanye da white glass kamar medicated, dogo ne sosai kamar King Zuhair, kyakkyawar gaske ne ajin farko, da gani kasan jikan Akka ne, ya fi kama da King sosai, sai dai fa ya fi King Zuhair hasken fata gaskiya, shi fari ne tas har ya ɗan yi yellow yellow, King Zuhair kuwa ya ɗan yi ja, yana da kirar jaruman maza sosai, kamar renon Commander Zafar, arab hairnsa ba'a magana, ta sha gyara sai kyalli take yi, tana kwance luf ka tsantsi, kun dai san yadda gashin larabawa yake, to haka suma dai ƴaƴan King dukkansu gashin kan nasu yake, daga matansu har mazan dukka akwai gashi mai matuƙar kyau kam.
Taku yake yi cikin natsuwa, sai dai da kallo ɗaya zaka yi mashi kasan e lallai jarumin namiji ne sosai mai jini a jika, duba da yadda yake a buɗe kuma yana tafiya ne da jikinsa sosai, ba shi da kiɓa sosai, yana dai murmure, Rizwan ya ɗan fisu kiba a cikinsu.
Kai tsaye wajen F-15 Eagle ya ɗin ya nufa, a daidai lokacin shi ma Bilal yake ƙoƙarin saukowa, shi yana sanye da kakinsu na air force, sai dai kakin yaki ne a jikinsa ba normal ba.
Special weapons and tactics uku ne suka takewa Ramish ɗin baya izuwa wajen F-15 Eagle jet ɗin. A lokacin da ya isa wajen Bilal ɗin ya fito sun rungumi juna da Rizwan har ya sake shi ya rungumi Dr Raj suna ƙoƙarin raba jikinsu.
Yana ƙarisawa wajen, shi kuma Bilal ɗin ya yi saurin sakin Dr Raj suka yi hugged ɗin juna shi da Ramish ɗin, da ka gansu ba tambaya kasa lallai waɗan nan jinin King Zuhair ne, da shi da Bilal banbancinsu kaɗan ne, ya fi Bilal tsawo, haka zalika ya fishi da shekaru, sannan ya ɗan fi Bilal hasken fata da kyau, amma aka ce jini ba wasa ba, akwai kamar jini sosai a tsakaninsu.
Da yanayinsu zaka fahimci suna cikin farinciki, sai dai dukkansu babu alamar murmushi a saman fuskokinsu.
"Yah Bilal nafa riga Yah Ramish ƙarisowa wajenka, amma shi ne ka rungumesa kaki kulani ko?". Cewar Guyson dake tsaye kusa da Sharifat yana ƙoƙarin tura wayarsa a cikin aljihunsa.
"Our Guyson ai naga waya kake yi tun da ka ƙariso nan, da waye kake magana?". Bilal ɗin ya bashi amsa, voice nasa sak na King Zuhair, da alama jinin King ya fi na su Mummy karfi sosai, hakan yasa dukka ƴaƴa suke kamanceceniya da shi.
"Waya na yi da daddy, shi ya kirani, shiyasa na ɗauka, ai kasan idan ba daddy ko su Momma ba ba zan ɗauki call ɗin kowa ina murnar ganinka ba". Ya faɗa yana ɗan tuɓune fuska, irin shi gaskiya ba'a kyauta mashin nan ba.
Raba jikinsu suka yi, sannan Bilal ya rungumi Guyson ɗin haɗe da riƙo hannun Sharifat dake tsaye ta yi shiru kamar wata mai sauraran kira'ar Alqur'ani mai girma, sai binsu da kallo take yi.
"Shikenan our Guyson". Cewar Bilal ɗin.
"Yah Bilal sannu da dawowa". Cewar Sharifat ɗin.
Yana riƙe da hannunta ya amsa da. "Yauwa lil sis, fatan kuna lafiya?"
Sai sakin ƙayatattcen murmushin take yi ta amsa da. "Lafiya lou Yah Bilal".
Sakin hannun nata ya yi yana ƙoƙarin raba jikinsa da Guyson. "Wato Yah Bilal lil kawai ka gani ko? Ita ce kawai ka tambaya ya take? Ni baka damu da kasan ya nake ba ko?". Cewar Guyson ɗan rigima. Ya yi maganar kamar zai yi kuka.
Idan da sabo sun daba da mitarsa, shi dai kada a nuna wani ya fishi a gabansa, sai shegen kishi tun yana ƙarami, yanzu wai dan me za'a tambayi Sharifat ya take shi ba a tambayeshi ba, kenan anfi damuwa da Sharifat a kan shi, shi ne yake yi wa raki.
Kallonsa da ido kawai Bilal ɗin ya yi ba tare da ya yi magana ba, domin idan ya biyewa Guyson sai su kwana a nan. Tsayawa Guyson ɗin ya yi a kan shi ba zai tafi ba tun da dai sun nuna sun fi damuwa da Sharifat a kan shi har suna tambayarta ya take shi ba wanda ya tambayi ya yake?.
Ramish ne yasa hannu ya ɗauke shi cak kamar ɗan baby ya saɓa a shoulder ɗinsa suka nufi wajen motocinsu, domin ba biye mashi zasu yi ba, idan ya fara raki kamar wata kaza mai kwanci yake.
Jiga jigan jaruman jami'an air force guda shidda ne suka ƙariso wajen Bilal ɗin, dai'dai lokacin da shi kuma y ƙarisa wajen jerin gwanon motocin su Ramish domin su koma gida. Cikin girmamawa suka ɗaga hannu suka sara mashi, sannan ɗaya daga cikinsu ya ce "Sir office zamu wuce ne?".
Yana riƙe da hannun Sharifat da ya kama tun lokacin da Ramish ya ɗauki Guyson suka nufo wajen motocin, shi kuma sai ya riƙo hannun Sharifat ɗin ya rufa masu baya. Yana riƙe da hannunta ya amsa masu da. "No gida zan wuce, ni da office sai next week kila". Cikin harshen larabci suke maganar.
A cikin mota gidan baya Ramish ya sauke Guyson yana jefa mashi wani irin kallo mai kama da harara. Murmushi Guyson ɗin ya sakar mashi domin yasan ma'anar wannan kallo. Wucewa Ramish ɗin ya yi ya zaka ta ɗayan side ɗin ba tare da ya yi magana ko ya sake bi ta kan Guyson ɗin ba.
Buɗe mashi kofar motar jami'in Special weapons ya yi, ya shiga kusa da Guyson ɗin ya zauna, shi ma Bilal wannan motar ya shiga suka sanya Guyson a tsakiyarsu, ita kuma Sharifat ta shiga wata motar na daban.
Kamar yadda motocin suka shigo a jere haka suka tashi a jere bayan su Rizwan dukka sun koma cikin nasu motocin. Da haka suka nufi gida. Jami'an air force mota guda suka yi masu rakiya zuwa gida, dan Bilal ya ce ba zai je office nasu ba, gida zai wuce, shi ne zasu yi mashi rakiya su tabbatar da ya isa gida lafiya, sannan su koma headquarter ɗinsu.
A wannan karon gudu sosai motocin suke shararawa a saman shinfiɗaɗiyar titin. Hakan yasa cikin ƙanƙanin lokaci suka isa gida.
Leesharh dake kwance a saman gadonta ne ta ji diran motoci a cikin gidan, jiniya ya karaɗe ko'ina, motocin ƴan'sanda da sojojin dukka sun saki jiniya kamar zasu tafi filin daga, hakan yasa jiniyar take tashin kai, ta yawaita sosai.
A hanzarce ta diro kasa daga saman bed ɗin nata, da sauri ta nufi wajen window domin ta leƙa taga su waye ne?.