Rawanin zalinci 1 complete - Chapter 76
Rawanin zalinci 1 complete Chapter 76: Rawanin zalinci 1 complete Chapter 76. Sai dai kash, bata samu damar ganin motocin ba, dan already sun wuce izuwa…
3,353 words
Sai dai kash, bata samu damar ganin motocin ba, dan already sun wuce izuwa parking space na gidan, shi kuma parking space ɗin yana ta can gefe ne, bata iya ganinsa daga wannan window tata, dan haka bata sami damar ganinsu ba.
Mai da windown ta yi ta rufe tare da sakin labulen, sannan ta nufi waje. Babu kowa a parlournsu, kai tsaye ta nufi barin part ɗin nasu mai gabaɗaya, yau ƙasa ma take son sauƙa. Elevator ta je ta haye ta nufi ƙasa kamar wadda zata ɗauki wani abin. A hawa na biyu ta tsaya, ma'aikata sai hidima suke yi, sai kai komo suke yi, ta sha madarar mamakin ganin ma'aikatan wannan hawa suna da yawa, sai dai bata wani damu ba ta nufi cikin hawar da kyau dan ta sha kallo, ta gaji da kwanciya a ɗaki ne babu abokin hira, ga shi ba da kowa aka yarje mata ta yi hirar ba.
Su Ramish kuwa kai tsaye part ɗinsu suka nufa, shi da Bilal sun jero kamar wasu tagwaye, sai dai Ramish ya ɗan fi tsawo na gaya maku, Dr Raj and Rizwan ma sun jero kansu ɗaya. Ramish yana rike da hannun Guyson dake ta faman kunbure kunbure na anfi damuwa da Sharifat a kansa. Ita kuma Sharifat Bilal ne ya riƙe hannunta suka nufi elevator.
Sam basu leƙa Ummie ba, ita ma bata leƙasu ba sai can yamma da misalin karfe huɗu, a lokacin dakkansu sun yi wanka sun shirya cikin wasu tsadaddun suit masu bala'in kyau, zasu halarci waliman da Abbie nasu ya haɗa ne domin dawowar Bilal ɗin, sai a wannan lokacin ne Ummie ta leƙasu, ita ma ta tsantsar kwalliya cikin wani Turkey gown, kun san yawancin dogayen rigunar mutanen Turkey suna nan da kauri sosai kamar cuit, yadikansu kusan kamar yadikan suit ne, so haka rigar da ta sanya ɗin ma yake, ga rigar ta fita shape ɗinta sosai, ta sha ado kam ba'a magana, ta yi rolling gyalen a kanta.
Part ɗinsu ta isko su, kowanne a cikinsu da abin da yake yi. Ramish yana tsaye a wajen windown parlourn part ɗin nasu yana waya, da alama da King Zuhair yake waya, duba da yadda yake maganar cikin nutsuwa da kuma respect, yana wayar hannunsa na rike da wani haɗaɗɗen cup mai ɗauke da cappuccino a ciki yana sha.
Shi kuma Bilal yana zaune a saman sofa ya tasa waya a gaba yana latsawa yana kuma shan cappuccino dake a saman ɗan table ɗin dake gabansa. Rizwan da Dr Raj sai hira suke yi, jefi jefi Bilal yana saka masu baki a cikin hirar tasu, sun kammala shiri tsab, fita ne kawai basu yi ba, ga shi kuma wajen walimar ya cika da manya manyan baki, ministoci da ƴan majalisu da dai sauran masu muƙaman gwamnati haɗe da ƙananan da manyan sarakuna duk sun hallara, su da aka shirya walimar dan su kuma suna nan zaune a parlournsu suna hira, da alama ma basu so halartar walimar ba, Abbie ɗin ne ya matsa masu a kan lallai su zo, basu son ɓata mashi rai ne yasa suka aminta zasu halarci wajen.
Guyson da ya fi kowa tsantsara kwalliya a cikinsu yana kwance saman doguwar sofa, ya yi shiru kamar mai tunanin wani abin, ita ma Sharifat tana cikin room ɗinta tana tsantsara nata kwalliyar, ita kam sai murna take yi za'a yi walima.
Baki a ɗauke da sallama Ummie ta shigo cikin parlourn nasu. Dr Raj ne ya amsa mata sallamar. Cikin parlourn ta ƙariso, a saman sofan da yake fuskantar Bilal ta zauna.
"Good evening Ummie". Bilal ya faɗa yana kashe hasken screen ɗin wayarsa domin ya bata attention ɗinsa.
"Evening Yah Bilal ya hanya ya kuma aiki? Hope komai normal".
Da yes normal ya amsa mata, sannan ya yi shiru.
"Ya baku fita zuwa hall ɗin ba? Zaku fara halin naku ba?". Cewar Ummien.
Dr Raj ne ya amsa mata da. "Ummie kema dai kin san bamu son zuwa, tun da Abbie ya yi mana dole kuma sai an kusa tashi zamu je".
"Gaskiya a'a banyarda ba, kawai tun da kun shirya ku je, yana jiranku fa, nima can zan wuce sai na ji motsinku alamar kuna nan baku tafi ba shi ne na shigo, dan haka ku tashi kawai mu jera a tare, kun fa san Abbienku bashi da burin da ya wuce ya ganku a kusa da shi, nasan yanzu haka yana cikin damuwa na rashin zuwanku, yana son ya ganku kusa da shi yana nunawa abokansa ku yana kuma alfaharin yin hakan".
Ransu bai so ba, Dr Raj, Rizwan, Guyson and Bilal ɗin suka miƙe, basu son yin ja in ja da ita ne kawai yasa zasu je, shi kuwa Ramish da tun da ta shigo yake waya bai ko kalli in da take ba, sai da ta miƙe zasu fita ne ta ce mashi idan ya gama wayar ya biyosu fa, kada ya ce zai kwanta yaki zuwa dan tasan halinsa. Kai kawai ya gyaɗa mata alamar to, tare da binsu da waɗan nan dara daran idanun nasa.
Sakata a tsakiya suka yi suka nufi hall ɗin. Shi kuwa Ramish ya jima yana magana da King a waya, da kyar suka yi sallama, da alama King ɗin bai so su yi sallamar ne, sai dai Ramish ɗin ya ce mashi. "Kai daddy gobe fa zamu zo, ka bari idan muka zo sai mu yi ta hiran, yanzu Abbie yana jirana ne fa". Da haka dai ya samu suka yi sallamar da kyar.
Yana kashe wayar ya ɗaurata a saman sofa mai zaman mutun biyu, ya kuma ajiye cup ɗin cappuccino dake a hannunsa a saman table, sannan ya nufi cikin katafaren room ɗinsa.
Jim kaɗan ya fito sanye da three cuter jeans trousers sky blue, sai wata farar shirt mai karamar hannu maras nauyi mai laushi sosai, ya cire suit ɗin jikinsa, da alama ba zai je walimar ba kenan.
Wayarsa dake a saman sofa ya ɗauko ya nufi waje. Kai tsaye babban parlourn ya nufa. A saman sofas set da suke kusa da dining room ya zauna, sannan ya ɗauki wayar dake kusa da wajen na emergency ya kira masu aikin dake kitchen ɗin kasa suna girki. Bugu ɗaya aka yi picking call ɗin, dan already akwai wadda aikinta ne kawai ta zauna kusa da wayar, idan an kira ta ɗauka ta ji me ake buƙata, idan an gaya mata sai ta isarwa da masu aiki a kitchen ɗin saƙon abinda ƴan gida suke da buƙata, nan take su kuma ma'aikatan zasu karɓi umarni su fara aiki, wannan ɗaya ne daga cikin tsarin gidan Abu Abdussalam.
A takaice ya sanar da wadda ta ɗaga kirar cewa yana da buƙatar kayan marmari haɗe da ferfesu mai ruwa ruwa kuma mai zafi yana babban parlour. Already tasan wanda ya kirata, domin aikinta ne dama lallai ta tabbatar da ta riƙe muryar kowa, yana ɗaya daga cikin dokokin aikinta, kuma yau a kallah ta shafi shekaru 7 zuwa 8 tana wannan aiki, so ta san voice na kowa a cikin gidan, shiyasa na gaya maku Abu Abdussalam baya ɗaukar ma'aikata jahilai, sai waɗan da suka yi karatu sosai, dan ba'a saɓa mashi dokokin gidansa, sannan aikin gidansa yana buƙatar masu ilimi ne sosai. Tab irin wannan abu haka.....🤔
Cikin girmamawa ta karɓi umarninsa tare da sanar da masu aiki a kitchen ɗin ga saƙon Ramish nan, kuma jira yake yi, dan haka su yi sauri. Kitchen na gidan Abu Abdussalam kawai abin kallo ne, girmansa ya wuci tunaninku, ma'aikatan da suke aiki a cikinsa kawai zasu kai su 20, girki kala kala ake yi a kowani lokaci, kowacce da kalar abincin da take girkawa kuma da kalar aikin da take yi a cikin kitchen ɗin. Idan mace tana ta ɓangaren gas wata kuma tana ta ɓangaren freezers sai ka yi zaton ba'a waje guda suke ba, saboda girman kitchen ɗin, ratar da yake a tsakaninsu ba kaɗan bane, girma ne da kitchen ɗin sosai, tsakanin wajen jera pots da kuma wajen su baker ovens ma ba karamar rata bace ba, girman kitchen ɗin ya kai girman gidan wani ko in ce ya kai girman fili plot guda. emergency phones har guda biyar ne a kowani ɓangare na cikin kitchen ɗin, duk domin saƙon ƴan gida su faɗi abin da suke da buƙata a girka a kawo masu, abin fa ba sauki bane, Daular gidan Abu Abdussalam ya wuci tunaninku, maƙudan dukiya suke narkawa, albashin ma'aikin gidan a kowani wata ma kawai abin a saki baki ana kallo ne. Da yake dukka ƴan gidan manyan kai ne, duk shaggun masu maƙudan dukiya ne, hakan yasa suke pacaka son ransu, ga jiga jigan masu kuɗi su Ramish duk suna nan ai dole su more rayuwa son ransu...... Allah ka yi mana arziki mai albarka.
Ajiye wayar ya yi bayan ya isar masu da saƙonsa, sannan ya jingina kansa da jikin head na sofar, a hankali ya lumshe kyawawan idanunsa kamar mai jin barci. A can cikin hall kuwa sai jiransa su Bilal suke yi, kowa ya dake a saman nasa haɗaɗɗen sofa da aka kawata da kwalliya na alfarma kuma mai tsada, an tanadi waɗan na sofas ɗin ne domin family, sauran bakin da suka halarci walimar kuwa kowanne yana saman nasa sofar, sofas da aka tanadawa family a saman stage suke, na baki kuma a ƙasa.
Hall ɗin a cikin gidan yake, Abu Abdussalam yasa aka gina mashi ita domin yin walima ko wani taro nasa kamar dai yau, ba karamar dukiya aka narka wajen haɗa wannan hall ɗin ba, kamar ba za'a mutu ba, tsadaddun sofa set da ya zuba a cikin hall ɗin kawai kuɗinsu ya isa ya riƙe wani har karshen rayuwasa shi da iyalansa, amma duk shi a kan sofa kawai ya karar da kuɗin, ga kayan alatu da aka zuba domin kara ƙawata hall ɗin, kowani abu idan ka gani a cikin hall ɗin nan aka gaya maka kuɗinsa sai ka saki baki, gabaɗaya bangon hall ɗin ma na glass ne, abin dai sai wanda ya gani, dan faɗar tsaruwar hall ɗin nan da baki ma ba zai yiwu ba.
Sosai Leesharh tasha kwalliyarta cikin wasu dogon wando da riga, dama na gaya maku ita ma abokiyar son wando da riga ne, malesian dress ne, wandon yana da faɗi sosai kamar palazo, rigar kuma ya fitar mata da shape ɗinta, rigar zuwa gwiwanta ya tsaya, sai ɗan ƙaramin veils ɗinsa, sannan rigar yana da igiya ta wajen cikinta, ta ɗaure igiyar a baya hakan yasa rigar ta kara fito mata da shape ɗinta sosai, flat tummyn nan nata shape nasa ya bayyana sosai. Ɗaura veil ɗin a kanta ta yi ɗauri mai kyau, da yake chocolate color ce ita sai launin kayan da suka kasance red color ya yi mata kyau sosai.
Fitowa ta yi daga part ɗinsu domin ta je wajen walimar su rabawa baki drinks da abubuwan da suka da ce, already an shirya glass cups masu tarin yawa da za'ayi amfani da su a wajen, masu zuba lemuka a cikin glass cup's ɗin ma har sun fara aikinsu, masu jera glass cups ɗin a try bayan an zuba drinks ma suna nasu aikin, so su Leesharh kuma aikinsu kawai su ɗauka su rinƙa rabawa waɗan da suke zaune shiru basa motsa baki.
Kamar zata nufi ƙasa, sai kuma ta tuna to ai ita bata san ma a ina hall ɗin yake ba a cikin gidan, bata san ta wani bangare yake ba, hakan yasa ta yanke shawarar tunkarar room ɗin Sharifat ko zata sameta sai su tafi a tare, sai zuba daddaɗar kamshi take yi.
Kasancewar tasan babu kowa a cikin babbar parlourn ne yasa ta yi sallama a ƙasa ƙasa, kai tsaye room ɗin Sharifat ta nufa, sam bata lura da shi a parlourn ba, kasancewar tsakaninsu akwai rata sosai, sai dai kuma tasha madarar mamakin jin ƙamshi parlourn ya sauya daga yadda ta saba ji, kamshin perfume ɗinsa ya rinjayi na parlourn saboda karfin da perfume ɗin nasa yake da shi. Amma bata kawo komai a ranta ba ta wuce wajen Sharifat kai tsaye.
Tana tura kofar room ɗin Sharifat, ita kuma Sharifat ɗin tana sanyo kai zata fito kenan suka yi karo, gwara kansu suka yi ta yadda har sai da dukkansu suka furta wash da ɗan karfi.
Baya kaɗan Sharifat ɗin ta yi tana murje goshinta da Leesharh ta gwara mata kai. A ɗan ruɗe Leesharh ta yi mata sannu tare da ja da baya ita ma.
Ba komai Sharifat ɗin ta ce mata sannan ta ɗaura da cewa. "Kin yi kyau sosai Leesharh, ke kam kowani kaya kika sanya sai sun yi maki kyau, wajen walima zaki je ko?".
Kai ta gyaɗa mata tare da faɗin. "E can zanje mu rabawa mutane drinks, sai dai ban san a ina wajen yake ba, kafin na gama shirina kuma su Radia sun tafi, shi ne nazo tambayarki wajen".
Nisawa ta yi kafin ta ce. "Can zan je nima, muje a tare". Ta kai karshen maganar tare da sanyo kai ta fito, tasha kwalliya sosai cikin abaya, ta yi rolling gyalen a kanta, ta fita ɗas da ita abinta, launin navy blue ya yi mata kyau sosai dan tana da hasken fata.
Juyowa Leesharh ta yi suka nufi dawowa cikin babban parlourn, Sharifat ta sanya takalma mai tsini wato high heel sosai, sai kwas, kwas, kwas take yi a white tiles na parlourn, ita kam Leesharh plat shoe ne a kafafunta, suma plat shoe ɗin Sharifat ɗin ce ta bata kyautarsu kala goma sha biyar, ciki harda high heel guda biyar, amma bata saka high ɗin ba, sai ta ɗauki flat ta sanya, duk da haka ta yi kyau sosai.
Suna ƙarisa zuwa cikin parlourn Sharifat ta tsaya tana ƴan waige waige.
"Lafiya Sharifat kika tsaya?". Leesharh ta tambayeta tana binta da kallo.
"Naji kamshin perfume ɗin Yah Ramish ne shi ne nake neman ta ina yake?". Ta bata amsa tana nufar wajen kofar dining room.
Da farko kamar Leesharh ba zata bita ba, amma tunawa da ta yi tana matukar son taga Ramish ɗin yasa ta yi saurin rufa mata baya, kirjinta sai dukan uku uku yake yi, yau zata kalli wanda ta zo yin aiki a kansa, fargaba da faɗuwar gaba ne cike tab a ranta, ta takure jikinta waje guda saboda rashin gaskiya da kuma tsoro.
Ganinsa yasa Sharifat ta saki wani cool murmushi kamar budurwar da ta ɗauki shekaru tana begen ganin saurayinta sai yau ta gansa, kunsan ba ƙaramin daɗi zata ji ba, to haka ita ma Sharifat ɗin ta ji daɗi sosai har yasa ta saki murmushi ba tare da ta sani ba.
Ita kuwa Leesharh ganinsa yasa ta haɗiyi wani irin wahalallen yawu duk da bata da tabbacin cewa shi ne, amma lallai ba shakka ta ji a jikinta shi ɗin ne kamar yadda masu nikaf suka gaya mata cewa in dai ta gansa to zata ji a jikinta cewa shi ne, haƙiƙa kuwa ta ji hakan, nan take bugawar zuciyarta ya karu, faɗuwar gaba da fargaba suka karu, kanta har wani irin sara mata ya yi, a take a wajen ta ji wani irin karayar zuciga a kan wannan aiki, ji ta yi ina wlh in dai wannan shi ne Ramish to ba zata iya bin diddiginsa ba, wannan ganinsa kawai yana sanyata faɗuwar gaba, iya faɗuwar gabar kuma kawai ya isa ya kasheta, ai wlh idan bata yi hankali ba da kanta zata tonawa kanta asiri, bare ma ace su haɗa ido da shi, wannan tun bai yi magana ba zata ruɗe ta fara ce mashi ba laifinta bane turota aka yi, ta tonawa kanta asiri, har wani irin zufar tsorata da ganinsa ne ya fara tsastsafo mata, yau almost 2 month kenan tana gidan tana son ganinsa, ta jima tana begen ganinsa, yau ta gansa kuma sai ta fara danasanin ganin nasa da ta yi, duk sai ta ji dama ace bata gansa ba da ya fi mata alkhari, yanzu ganinsa da ta yi zai sanya mata fargaba, yanzu zata kasance kullum cikin fargaba da tsoron ranar tonan asiri, dama gata duk a firgice.
"Yah Ramish sannu da hutawa". Cewar Sharifat da take tsaye a kusa da shi.
Ba tare da ya buɗe idanunsa ba, ya kuma ɗauki tsawon minti ɗaya kafin ya amsa mata da. "Yauwa lil sis".
Sosai Leesharh ta kara jin faɗuwar gaba da jin voice ɗinsa, yana da sanyin murya sosai, sai dai muryar tasa akwai kaifi sosai a cikinta, daga ji kasan manyan maza ne suke magana.
A ɗan tsorace Sharifat ta sake cewa. "Yah Ramish ya baka je wajen walima ba?". Ta yi maganar tana ɗan ɗari ɗari, domin tasan halinsa baya son tambaya kuma baya son yawan magana, idan magana ta wuci biyu zuwa uku to baya amsawa koda kuwa Ummie ce ta yi maganar.
Ai kuwa ta gudu bata tsira ba, dan kuwa bai amsa mata ɗin ba, kamar babu shi a wajen. Ganin hakan yasa Sharifat ɗin ta ce da Leesharh su tafi kawai. A hanzarce Leesharh ta juya ta yi gaba, har mamaki ta bawa Sharifat ɗin na yadda ta juya a hanzarce kamar wata maras gaskiya. Amma bata kawo komai a ranta ba, sai ma tunani da ta yi na cewa kodai tsoron Yah Ramish ɗin ne yasa ta birkice haka? Bayanta ta bi kawai suka fita parlourn suka nufi elevator dan su sauƙa kasa.
Sai dafe saitin zuciyarta Leesharh take yi, dan ji take yi tamkar zuciyar tata zai fasa kirjinta ya fito waje, a gaskiya ta tsorata da ganin Ramish, wannan ma fa ba ido cikin ido ta kalle shi ba, akwai aiki kenan.
Hall ɗin kai tsaye suka nufa, yau gidan ya kara cika da jami'ai kala kala saboda ministocin da manyan bakin da suka halarci walimar, an kara tsaro sosai da sosai.
Suna zuwa Sharifat ta wuce saman stage wajen ƴan uwanta ta zauna a kusa da Guyson, ita kuwa Leesharh ta nufi wajensu Radia dake can gefe guda wajen shirya drinks. Tana zuwa ta tsaya idanunta suna a kan stage da Sharifat ta hau.
Izuwa yanzu ta shiga ruɗani sosai, faduwar gaba kuma yana neman kasheta har lahira, ba komai kuma ya hassasa mata hakan ba face ganin, Rizwan, Bilal, Dr Raj da ta yi a saman stage ɗin, ta ruɗe ta yadda har ta kasa iya banbance kamanninsu da Ramish da suka baro a cikin gida, yau rana ta farko da ta fara ɗaura idanunta a kan Abu Abdussalam bawan Allah, tana jin labarin kirkinsa bata taɓa ganinsa da ido ba, ta haura wata biyu a gidan, to yau dai ga shi nan a tsakanin ƴaƴansa.
Da ka gansa ba tambaya kasan yayan Mommar Zunaira ce, yana kama da Guyson sosai, sai ka rantse da Allah Guyson ɗan cikinsa ne ba ɗan kanwarsa ba. Ya sha farar arab jallabiya mai tsada da alkyabbarsa, rawani ya yafa daga kansa zuwa kafaɗunsa, daga sama har ƙasa fararen kaya ne a jikinsa, ɗan gara alkyabbar jikinsa ma akwai ratsin baki kaɗan a jiki, half cover shoe ne a kafafunsa masu bala'in tsada, suma launin fari, waɗan nan family yau sun haɗu iya haɗuwa. Sai dakon jiran Ramish suke yi, shi kuwa basu san ma ya tuɓe ya sanya kayan shan iska yana zaune abinsa ba, yama mance da wani zancen walima da ake gudanarwa a cikin gidan.
Leesharh dai yau fargaba da faɗuwar gaba ne suka kusa yin ajalinta, duk in ta ɗaga ido ta kalli Dr Raj and Bilal sai taga kamar Ramish ɗin take kallah, ta kasa iya ɗaukar try ɗin drinks ɗin ta kaiwa mutane, saboda kerma da hannayenta suke yi, tana tsoron ta ɗauki try ɗin ta je ta ɓarar da shi, glass cups ɗin su tarwatse a wannan haɗaɗɗen tiles ɗin, ga shi kuma yadda aka jera cup's ɗin wasu kan wasu ɗorin ɗosalo tamkar yadda ake jerawa a party na manya manyan shugabannin manyan kasashen ta duniya, sun yi kyau a ido kam, amma ɗaukarsu sai ka shirya, sai mai nutsuwa. So ita dai Leesharh ta kasa iya ɗauka, domin fargaba da faɗuwar gaba sun ja mata kerman jiki.