Kenza eBookz

Rawanin zalinci 1 complete - Chapter 77

Rawanin zalinci 1 complete - Chapter 77

Rawanin zalinci 1 complete Chapter 77: Rawanin zalinci 1 complete Chapter 77. Waje ta samu ta karshen hall ɗin ta zauna, ta rasa dalilin da yasa kawai ta…

3,370 words

Waje ta samu ta karshen hall ɗin ta zauna, ta rasa dalilin da yasa kawai ta ji hawaye sun fara gangaro mata a saman face ɗinta, har wani irin shesshekar kuka take yi mai tsuma zuciyar mai sauraro, ita wannan bala'i ya fi karfin shekarunta, ta rasa ya zata yi, ji take yi kawai kamar ta yi wani laifin da zai sanya a kasheta kawai ta huta da wannan bala'i, tana kewar babanta, tana son sake ganinsa koda sau ɗaya ne, idan ta tuna cewa babanta yana hannun masu nikaf, kuma zasu cutar da shi idan bata mayar da hankali ta yi aikinta da kyau ba, sai ta ji wani irin kuka mai karfi ya zo mata haɗe da karfin gwiwar zata iya yin komai a kan baban nata, idan kuma ta tuna wanene Ramish da yadda ta kalli suffarsa da kirarsa sai ta ji zuciyarta ya karaya ta fara yi wa kanta fatar mutu. Ta rasa ina zata saka rayuwarta ta ji sanyi.

Sosai take kuka, kasancewar babu jama'a a wajen yasa ba'a san tana kukan ba, can kashen hall ɗin ta je ta zauna, wajen babu kowa sai camera dake iya ɗaukar hoton wajen, murzan kukanta take yi son ranta wata kila ta huce takaici.

Kamar daga sama ta ga an miƙo mata handkerchief fari tas wanda kamshinsa ya daki kofofin hancinta har sai da yasa ta ɗan lumshe idanunta.

Waye kuma da karfin halin miƙo mata handkerchief? To bari dai mu leƙa KINGDOM OF POWER kafin mu dawo sai mu duba wanene da ƙoƙari ya miƙo mata handkerchief ɗin.

KINGDOM OF POWER 💪🔥💘

Kwance Gimbiya Chuchu take a saman bed ɗinta a cikin room ɗinta bayan an sauko daga sallar jumma'a kenan, ta bawa kofar shigo cikin room ɗin nata baya, tana maƙale da waya a kunne tana magana ƙasa ƙasa kamar wata maras gaskiya, yadda kuka san mai yin soyayya.

A ruɗe Gimbiya Zunaira ta shigo cikin ɗakin idanunta a cike tab da kwallah, ga farin cikin idanun nata sun ɗan yi ja, kwayar Hazel eyes ɗin nata kuma ya kara launi sosai, da alama ta ɗan sha kuka kafin ta zo room ɗin, face ɗinta da ɗan danshin ruwa alamar ta wanke fuska kafin ta zo.

Tana zuwa ta haye saman gadon tana faɗin. "Aunty Chuchu ki tashi na shiga ukuna!".

A tsorace Chuchu ta juyo, dan bata yi tsammanin shigowar mutun ɗakin nata ba, kuma bata ji shigowar autar ba, so hakan ya ɗan tsoritata.

"Auta lafiya?!". Ta tambayeta a ruɗe, ta yi maganar kuma ba tare da ta cire wayar daga kunnenta ba.

Daga ta cikin wayar tata da yake hannunta Rizwan ya tambayeta da lafiya ita da waye?.

A takaice ta amsa mashi da. "Auta ce ta shigo mun ɗaki babu sallama ta tsoritani, ina ɗan zuwa Yah Rizwan bari mu yi magana da ita".

Da okey ya amsa mata. Cikin hanzari ta katse kiran nasa tare da ajiye wayar a gefe, sannan ta juyo da jikinta gabaɗaya ga autar. Ganin idanun kanwar tata cike tab da kwallah ga alamar ta sha kuka kuma yasa ta zaro idanu tare kuma da kara ruɗewa. "Auta lafiya idanunki suke cike da hawaye? Meyake faruwa ne?". Ta yi maganar tana miƙewa zaune.

A tsananin ruɗe autar ta fara yin magana. "Aunty Chuchu na shiga uku, wani abin ne ya fito mun a kirjina, wanka na je yi sai na jishi ya fito mun kamar dutse, ko dai asiri aka yi mun ne? Dan na ji ance ana iya yi wa mutun asiri kala kala". Tana magana hawayen suna ganganro mata a saman fuskarta.

Hakika akwai shaƙuwa mai karfi a tsakanin Zunaira da Chuchu, duk abin da yake damun Zunaira ba zata tinkari kowa ba sai ta fara tunkarar Chuchu ta gaya mata kafin ma ta gayawa Mommarta, basu ɓoyewa juna komai, yanzu haka abin da Yah Jawad ya yi wa Chuchun jiya auta tana nan da shi a ranta zata gayawa Chuchun bata manta ba, abin da yasa jiyan bata sami damar gaya mata ba barci ne ya ɗauketa, lokacin da suka dawo daga wajen yawon nasu, suna shigowa cikin gida suka isko su Sarina a parlourn, shi ne suka zauna yin hira da su har lokacin cin abinci ya yi, ita kuma Chuchu ta shiga ɗaki ta canza kaya, bayan sun ci abinci ne suka wuce ɗakin Chuchun da nufin in sun je auta zata gaya mata ga abin da Yah Jawad ya yi mata a gidan zoo da kuma sauran guraren da suka je, to suna shiga cikin ɗakin kuma Yah Jawad ya kawowa Chuchu wayarta, bayan ta karɓa sai ta ce ya bata number Yah Rizwan, ba musu ya bata, bai kuma kawo komai a ransa ba dan yayansu ne ai, ita kuwa ta sanya number a wayarta ta kira Rizwan ɗin, bai ɗauki call ɗin ba a lokacin, hakan yasa ta ajiye wayar ta nufi toilet dan yin wanka.

Ita kuma auta tana kwance a saman gado tana jiran ta fito ita ma ta shiga, yau a ɗaki ɗaya zasu kwana. Bayan ta fito ta yi shirinta cikin kayan barci masu kyau da tsada, sannan ta haye gado, ita kuma auta ta miƙe ta shiga toilet ɗin da nufin idan ta yi wanka ta yi shirin kwanciya sai tazo su yi hira ta sanar da Chuchun.

Sai dai ko da ta fito daga wanka sai ta tarar da Chuchun tana waya da Yah Rizwan, hakan yasa da ta gama shiri ta zo ta kwanta a kusa da chuchun, tun tana sauraron hiran da suke yi da Yah Rizwan ɗin har barci ya yi awon gaba da ita, washegari da safe kuma suka tashi da batun rashin lafiyar mama, wannan dalilin yasa autar bata samu damar gaya mata ba. To mu koma kan labarinmu.

"Menene ya fito maki ɗin in gani?". Chuchu ta faɗa tana zaro idanun nan nata waje kamar zasu faɗo ƙasa, ta tsorata ita ma tun kafin tasan menene.

A hanzarce auta ta fara zuge zip ɗin rigarta ƙasa tana faɗin. "Ga shi nan ki kallah". Ta yi maganar tana sauke wuyar rigar tata kasa tare da nunawa Chuchun breast ɗinta.

Wani irin dariya ne ya kubcewa Chuchun, dariya ta shiga yi har da rike ciki. Baki auta ta saki tana kallonta. Sai da taga dariyar tata ba mai karewa bane yasa ta fasa mata kuka mai ɗan sauti wadda hakan yasa dan dole Chuchu ta tsayar da dariyar tata.

"Yanzu me kuma abin dariya a nan? Kina ganin abu ya fito mun amma kike mun dariya". Autar ta faɗa cikin kuka.

"To auta ba dole na yi dariya ba".

A kule ta ce. "To idan kika tsaya kina dariya na mutu fa?".

Murmushi kaɗan Chuchun ta sake yi kafin ta ce. "Ba zaki mutu ba, ai ba wani abin bane, girma ne ya zo maki, ke baki yi mamakin ya aka yi ni da su aunty Aneesa muke da breast manya ke baki da shi ba? To kema naki ne ya fara fitowa, sai a dai'na wasa da su Hoorain, a dai'na yi wa maza magana, yanzu an girma, eyee autarmu ta girma ta fara kirgan dangi". Tana magana tana guntse dariya.

Sai yanzu auta ta fahimci menene, nan take ta ji wani irin kunya ya kamata, da sauri ta mayar da rigarta tana turo baki, danasanin meyasa ta nunawa Chuchun ma ta fara yi, har da wani cewa da tasan haka ne ai ba zata gayawa kowa ba, da farko ma Yah Jaish ta so fara zuwa ta gayawa kafin ta gayawa Chuchun sai ta gayawa Mommarta, ashe Allah ya taimaketa ma da bata je ta gayawa Yah Jaish ta kuma nuna mashi ba.

Nima na ce amma da ta je ta gaya mashi zan yi mata dariya kam, yanzu ma n yi mata, Chuchu ta kalle mata tula tulanta da suka fara fitowa😅😅😅😅😅 bye my people's sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu.....

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 5/9/2024.....✍️📚🌹

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________46🔥

"Meyafaru our Auta?". Ta tambayeta tana ɗan murmushin.

"Babu komai Aunty Chuchu". Ta yi maganar kamar zata fasa kuka, ta kuma yi maganar tana sanya hannu ta goge kwallar da yake a saman face ɗinta.

Ɗan rungumota kaɗan Chuchun ta yi tare da ɗan bubbuga bayanta alamar rarrashi tana ɗan tsokanar.

"Sai ki sanar da Yah Omar ko?". Cikin zolaya ta yi maganar.

"Allah Aunty Chuchu ki bari mana bana so". Ta yi maganar kumatu a kumbure kuma cikin shagwaɓa.

"To na bari, amma kin manta ke da Yah Omar akwai amana ne? Bafa ki ɓoye mashi komai shi ma kamar yadda baki ɓoye mun, wannan ne yanzu ba zaki iya gaya mashi ba? Lallai Auta kenan yanzu babu amana da nuna kauna? Kin manta yawan gaya mashi da kike yi cewa shi ne pleasurenki? Tun ba'a je ko'ina ba an fara ɓoyewa pleasure abubuwa". Still cikin zolaya ta yi maganar.

"E ɗin Aunty Chuchu na ɓoye mashi ɗin, kuma kema Allah da ban nuna maki abuna ba".

Wani irin dariyar iyashege ta tuntsure da shi, cikin dariyar take faɗin. "Kai menene kuma abunki ɗin to? Bashi da suna ne".

A ƙule Autar ta raba jikinta dana chuchun tare da ɗaukar wata jibgegiyar pillow da ta sha rigar bedsheet mai matuƙar tsada da nufin ta fara dukan Chuchun da shi.

Ai da gudu Gimbiya Chuchu ta sauka daga gadon tana faɗin. "Bari ma na je na gayawa su Aunty Sarina har da Aunty MieMie cewa Auta ta fara kirgan dangi, ta girma".

Da gudu Autar ta biyota tana faɗin. "Allah Aunty Chuchu ba zan barki ba kuma mun ɓata, kada ki sake yi mum magana, babu ruwana dake daga yau". Tana magana tana binta da gudu.

Kai tsaye part ɗin King Chuchu ta nufa sai dariya take yi kamar wata zararriya, yau Auta na neman kasheta da dariya.

Tana gudu tana waigo Autar taga ko ta kusa isota har ta shiga parlourn King, sai waigowa take yi bata ankaraba ta ji fa bugi faffaɗar kirjin mutun. Baya baya ta yi tana ƙoƙarin faɗuwa tare da ƙoƙarin dakatar da dariyarta da yake shirin zama kuka duba da yadda ta yamutsu fuskarta, da alama ta bugu sosai saboda gudu take yi.

Wuyar doguwar rigar jikin nata ya riƙo tare da janyota gaba ya tsayar da ita a kan kafafunta bai bari ta faɗi ƙasa ba.

Auta ko a jikinta da gudu ta ƙariso wajen ta fara sauke mata wannan pillown a gadon bayanta tana faɗin. "Kuma ko na dakeki ba zan huce ba, mun ɓata kenan, tabbas mun ɓata da gaske!".

A hanzarce Jawad ɗin ya sanya hannunsa ya tare dukar da Autar take kawo mata ba kakkautawa. Saura kaɗan Chuchun ta kifa a kan kirjinsa saboda dukan da Autar ta yi mata ta baya da pillown na ƙarshe yasa ta yi gaba kamar zata kifa, shi kuma a lokacin yana sanya hannunsa zai tari pillown kenan, hakan yasa ta kusa kifawa a kirjin nasa.

"Sorry our Auta tuba muke yi". Yah Jawad ya faɗa yana riƙo pillown da hannunsa ɗaya.

"Allah ya Jawad ni na zan yi sorry ba, yau mun ɓata da Aunty Chuchu baram baram!". Tana magana tana kwaɓe fuska tare da turo baki.

Cike da iya shege da tsokana tana murje gaban goshinta ta ce. "Yah Jawad to ka tambayeta me nayi mata da zata kama dukana haka?". Tana kai karshen maganar wani dariyar ne ya so kubce mata duk da turɓune fuska da ta yi lokacin da ta buge da kirjinsa, maganar a tambayi Autar yasa ta ji dariya ya zo ya kori kukan da take ƙoƙarin yi wa yayan nata.

Kuka Autar ta sanya masu tare da juyawa zata bar wajen dan ta ji cewa Yah Jawad ya tambayi me Gimbiya Chuchu ta yi mata. A hanzarce ya riƙo hannunta bai bari ta bar wajen ba. Cikin sanyin murya ya ce. "Zo Autarmu, zo ki gaya mun me ta yi maki in rama maki yanzun nan".

Habawa me Chuchu zata yi face dariya, shi Yah Jawad fa bai san tambayar me Chuchun ta yi mata bane yasa zata gudu ya zo yana wani tambaya shi ala dole zai rarrasheta kuma ya rama mata.

Hawayen gaske ta fara yi mashi bata ce komai ba, sai wani irin harara da take wurgawa Chuchun da waɗan nan dara daran idanuwan nata. Shi dai Jawad ya rasa gane me matsalar, sun saka shi a duhu.

"Ki faɗi me na yi maki Yah Jawad ya rama maki ya ce". Chuchu ta faɗa ita ma tana jefa mata hararar.

Bakinciki kamar Auta ta sanya hannu a kai ta kurma ihu. Faɗawa jikin Yah Jawad ɗin ta yi tana ɓoye fuska tare da fara yin hawayen gaske, dan ranta ya ɓaci sosai, Chuchu ta kureta.

Wani irin kallo mai wuyar fassaruwa Yah Jawad ɗin ya jefawa Chuchun kafin ya sassauta muryarsa kasa sosai. "Me kika yi mata Jannat?".

Da sauri Autar ta ce. "Babu abin da ta yi mun Yah Jawad". Tana magana tana goga kanta a kirjinsa.

Izuwa yanzu ya fahimci abin sirri ne a tsakaninsu Chuchu take yi mata wasa da hankali take kuma sanyata kuka a banza. Dan haka sai ya ce. "Shikenan our Auta, jeki abinki yanzu zan bata punishment ba tare da na ji ma me ta yi maki ba". Ya yi maganar yana shafa kyakkyawa arab hairnta da ko ɗankwali bata ɗaura ba ta shigo room ɗin na Chuchun a ruɗe, dan a tunanin wani abin ne ya sameta.

Da sauri ta raba jikinta da na shi tare da nufar hanyar komawa room ɗin na Chuchun rike da pillown tana faɗin. "Allah Aunty Chuchu ba zan yafe ba idan kika gayawa wani".

Juyawa da gudu ita ma Chuchun ta yi da nufin ta bi bayanta dan ta ji Yah Jawad ɗin ya ce zai bata punishment, ba zata iya ɗaukar punishment ɗinsa ba.

Aikuwa bai bari ta bar wajen ba ya yi saurin riƙo hannunta tare da janyota ta dawo in da take tsaye ta tsaya. Ƙasa da murya sosai ya yi kamar wani na yi mashi laɓe, kamar kuma maras gaskiya ya fara magana, ita kuma Auta ta yi tafiyarta sai kumbure kumbure take yi.

"Me kika yi mata? Meyasa zaki saka mana ita kuka?". Yana magana yana kallon cikin kwayar idanunta, while ita kuma tana ɗan satar kallonsa ta wani yi ƙasa da kai kamar wata mai ɗaukar darasin hadisi a islamiya!.

"Babu fa komai Yah Jawad". Ta faɗa a sanyayye.

Shiru bai sake yin magana ba, domin ya shagaltu da kallonta, gaskiyar uncle Abbas da King da suke cewa in dai zai haɗu da chuchu sai ya karewa ƴarsu kallo tsab sannan yake kama kansa, ashe dai sun san komai.

Jin ya yi shiru bai sake yin magana bane yasa ta ɗago ido dan ta ɗan saci kallonsa. Ai kuwa tana ɗagowa suka yi four eyes.

"Yah Jawad in tafi?". Ta faɗa ba tare da ta kawar da kallonta daga saman fuskarsa ba, sai dai ba kallon cikin kwayar idanunsa take yi ba.

"Ban gama kallonki ba ai my Jannat". Ya faɗa ba tare da yasan lokacin da hakan ya fito daga bakinsa ba, sai da ya ji ta ce. "Kallona kuma Yah Jawad? Na yi kyau ne?".

Nisawa ya yi, kamar mai jin barci ya furta. "Over ma kuwa kika yi kyau".

"To Yah Jawad ka mun hoto". Cike da zumuɗi ta yi maganar.

Wani irin cool ajiyar zuciya ya sauke tare da ciro wayarsa ɗayar. "Where's my other phone da na baki jiya?".

Sai a lokacin ta tuna da wayar. "The phone is in my room, in je in kawo shi yanzu?". Murya a warware ta yi maganar.

Girgiza mata kai kawai ya iya yi alamar a'a, bai iya sake furta komai ba sai matsowa da ya yi kusa da ita tare da shiga camerar wayarsa, sannan ya ɗaura hannunsa ɗaya a saman shoulder ɗinta. Zafafan hotuna ya fara ɗaukarsu, ita da ta ce ya ɗauketa ita kaɗai ya ɓige da ɗaukarsu a tare.

Sai canza style suke yi sun manta da cewa a parlourn King fa suke, ga shi yau King yana da baki sosai saboda zuwan su Ramish da za su yi gobe, jama'a suna ta kai koma a part ɗin, already kun san dama akwai part na saukar muhimman bakinsa na kusa sosai a cikin part ɗin nasa, so su Jawad suna tsaye ne a tsakanin wannan ɓangare na saukar bakin da kuma hanyar nufa master room na King.

Canza style ya yi daɗi harda kwanciya a saman kirjinsa ta yi, yau abin nema ya samu, Chuchu mayyar ɗaukar hoto, to ga dama ya samu, mai hanata ɗaukar hoton ya takura mata yau da kansa yake ɗaukarta, ai style kuwa sai abin da kuka gani.

Suna tsaka da kashe hotunansu basu ankareba kawai sai tsinkayo muryar Akka suka yi a cikin kunnuwansu tana sababi, ta nufo parlourn ɗin ne tana ta surfa sababi da masifa, da alama wani ya taɓota. Tun daga nesa take faɗin. "Ai Zuhair shi ne ya mori aure, ku cigaba da yi, har ku kwanta a gadon ajalima kada ku dai'na, yo ni idan baku yi haka ba ai sai nace sam sam Zuhair ba mata ya aura ba, kuma idan baku yin haka ai sai na sa a bincika mun ku ko da wata munafurcin a ƙasa, dan cikakkun mata kam dole sai sun ɗana wannan kishi, shi kuma Abbas ba yadda ban yi da shi ba dan ya ƙara aure ya ji daɗin aure amma yaki, shi sam ba aure ya yi ba, dan idan baka haɗa mata biyu a gida suna nuna kishi karara kamar dai matan Zuhair suna faɗa a kanka ba to ba aure ka yi ba, ku ta yi abinku shi ne dai'dai, wadda ta fi sanin kan duniya ta kwace Zuhair ɗin ya tattare a wajenta". Sai sababi take yi.

(Jama'a kun ji mun wannan tsohuwa da bala'i 🤔 ita fa har dattijon arzikinta wato mijinta King Abdul Malik ya kwanta dama ita kaɗai ce matarsa, bata da kishiya, amma take cewa uncle Abbas ya karo aure, Akka sam bata son zama lafiya, ga rikicin tsufa, mata suna faɗa tana kara hura wuta 😅)

Jin motsinta tana surfa wannan uban sababin yasa Jawad yaja hannun Chuchun da sauri suka haura izuwa master room na King, domin idan ya bari Akka ta kama shi da Chuchu a ɗan wannan lungu to fa ya shiga uku, ai ta rinƙa takurawa rayuwarsa kenan, idan ma bata ce zai lalata mata jika ba, dama kun san ba shiri suke yi ba, kullum cikin faɗa da samun saɓani suke, kuma idan baku manta ba Akkar ta sha shiga tsakaninsa da Chuchun tana rabasu faɗa, so tasan basa shiri sam sam, yanzu kwatsam ta gansu a tare a wannan ɗan hanya na zuwa master room ai shikenan ya shiga uku a cikin wanna kingdom ɗin, ba zata barshi ya zauna lafiya ba, kuma abin da yake gudu na kada Jaish ya san halin da ake ciki na tsakaninsa da Chuchun fa to sai ya sani idan Akka ta gansu, bugu da kari Mammiensa ma sai ta sani, kuma ɓoye mata yake yi dan yasan bata son alƙarsa da ƴaƴan King Zuhair, shi kuma a part ɗin ya taso ya girma, ya fi sabawa da su fiye da ƴan uwansa su Sarina ɗin ma, amma bai san dalilin Mammaien ɗin tasa na bata son taga yana alaƙa da ƴan uwan nasa ba, jini ɗaya suke amma tana son raba jini da karfi da yaji.

Kai tsaye room na King suka nufa da gudu, wajen hawa ƴan ƙananan stage da suke a bakin kofar room ɗin na King Chuchu ta yi tuntuɓe ta faɗi, gudun da suke yi ne yasa bata lura da sun iso wajen ba.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull