Kenza eBookz

Rawanin zalinci 1 complete - Chapter 86

Rawanin zalinci 1 complete - Chapter 86

Rawanin zalinci 1 complete Chapter 86: Rawanin zalinci 1 complete Chapter 86. Saman carpet ya yi mata umarnin ta ajiye mashi abincin, a hanzarce ta karɓi…

3,355 words

Saman carpet ya yi mata umarnin ta ajiye mashi abincin, a hanzarce ta karɓi umarninsa tare da aiwatarwa.

Bayan ta fita ne ya ce da Chuchun ta zo su je su yi breakfast a tare. To ta amsa mashi da shi, hannunta ya riƙo suka nufi wajen kayan abincin.

Zama ya yi tare da zaunar da ita a kusa da shi. Cup mai shake da coffee mai zafi ya ɗauko ya kai mata bakinta. Ba musu ta buɗe baki ta fara karɓa. Wayarsa ce ta fara kara daga cikin aljihun coat ɗin jikinsa. Hannu yasa ya ciro wayar tasa.

Yah Rizwan, shi ne sunan da ya bayyana a saman screen ɗin wayar. Cigaba da bata coffee ɗin ya yi yana haɗa mata da pepper soup na kaza mai bala'in daɗi. Cike da kaunar yayan nasa ya ɗauki wayar yana kuma mamakin kiran da yayan nasa ya yi mashi da sassafe haka.

"Assalamu alaikum Yah Rizwan barka da safiya". Ya faɗa cikin nutsuwa, yana magana yana yanko tsokar kazar yana cusa mata a baki. Ta saki jiki sai ci take yi abinta.

"Jawad ka tashi lafiya?". Rizwan ya tambaya, daga jin muryarsa kasa yana kaunar ɗan uwan nan nasa sosai, sannan muryarsa da alama damuwa matuƙa a tattare da ita.

Da lafiya lou Alhdulillah ya amsa mashi da shi, sannan ya ɗaura da cewa. "Yaya ya naga ka kirani da sassafe haka? Ko dai akwai wata matsala ne?". Sai a lokacin Chuchu ta ɗago idanu tana kallonsa jin ya ambaci matsala.

Daga ɗayan ɓangaren ya amsa mashi da. "E akwai matsalar babba ma kuwa, amma ba ita ce tasa na kiraka ba, na kiraka ne dan naji ya ka kwana? Ya kuma ka tashi? Jiya ban samu ishasshen barcin kirki ba, saboda tunaninka".

Miƙawa Chuchun cup ɗin coffee ɗin ya yi tare da miƙewa tsaye ya nufi hanyar fita yana faɗin. "Matsala kuma Yah Rizwan? To matsalar me? Meyake faruwa?"

Bin shi da kallo ta yi har ya ficewa ganinta. Cigaba da cin abin nata ta yi tana tunanin to matsalar me aka samu kenan?.

After some minutes ya dawo cikin ɗakin fuskarsa babu annuri ko kaɗan, da alama Rizwan ɗin ya gaya mashi wani abin da ya ɗaga mashi hankali sosai, jikinsa duk ya yi sanyi sosai kamar ba shi ba. Kusa da ita ya koma ya zauna yana faɗin. "Jannat ci abinci da wuri na kai ki school akwai in da zanje".

Cikin sanyin murya ta ce. "Yah Jawad kai fa? Ba zaka yi breakfast ɗin ba ne?".

Kai ya gyaɗa mata alamar e ba zai ci ba, sannan ya ɗaura da cewa. "Sauri nake yi, ki ci da wuri in kaiki school ke dai, idan na dawo daga in da zan je zan yi breakfast ɗin".

"Yah Jawad meyasameka naga fuskarka ta sauya haka". Ta faɗa tana kallon face ɗin nasa.

Babu komai ya amsa mata da shi, sannan ya fara ƙoƙarin kiran number Jaish domin su gaisa su kuma yi magana, dan basu yi wayaba, ya so ya kira shi tun farkawarsa daga barci, amma bai samu dama ba, ya sha'afa.

Ringing wayar ta yi har ta katse ba'a ɗaga ba, duba time ya yi a danƙareriyar watch dake hannunsa. 7:05 am, yakamata ace Jaish ya tashi barci yanzu ai. Ya faɗa a bayyane tare da sake gwada kiran number.

A karo na biyu ma ba'a ɗaga ba. Knocking na kofar ɗakin da aka yi ne ya ja hankulansu shi da ita izuwa bakin kofar. Kasa ƙasa ya furta wanene?.

Daga wajen kuyangarsa ta amsa mashi da ita ce, tazo tana son fara yin aikinta ne na gyaran ɗaki. "Ki je sai anjuma ki dawo". Ya faɗa yana dawo da kallonsa a kan wayarsa da call ya shigo ciki yanzu.

Mammie, shi ne sunan da ya bayyana a saman screen ɗin wayar. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ɗauki call ɗin, yana sonta, ya ɗauketa kamar uwa, saboda yana ganin cewa tana son su kuma ta rike su kamar ƴaƴan cikinta.

"Good morning Mammie". Ya faɗa cikin sanyin murya.

Tana daga zaune saman sofa a fatafaren parlournta, ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, kamar kullum tana cikin haɗaɗɗen kwalliyar nan nata na alfarma, ga ruwan madaran gwala gwalai da ta zuba wuya da hannu, ta fito a hamshakiyarta, ta ko'ina dai bata da makusa sai bakar zuciyarta, kyakkyawar macece ga iya ɗaukar wanka, sai dai kash, kyan ɗan macijine. Daga gefenta wata hamshaƙiyar budurwace take zaune mai tsananin kama da ita, daga gani ba tambaya kasan kanwarta ce, dan sun yi kama sosai, yarinyar ba zata wuci 25 to 27 years a duniya ba, ita ma kyakkyawace, ga shi ta iya ɗaukar wanka kamar Mammie ɗin, yanzu haka ta sha wanka, duk wanda ya kalleta sai ya sake waigowa ya kalleta, da alama abin ya samo asali ne, duk yadda aka yi ainahinsu ƴan son gayu ne sosai.

"Morning Jawad how was your night?". Ta faɗa tana kallon kanwar tata.

Bayan ya amsa mata sai ta ce. "Kafin ka tafi office ka sameni a parlour mu ɗan yi magana".

Da okey kawai ya amsa mata, katse kiran ta yi tana bin kanwar tata da kallo. "Aliyah lafiya kike cunkushe rai haka?".

Kara tunɓune fuska kanwar tata ta yi kafin ta ce. "Aunty ba dole na turɓune fuska, ni ban san ya zan yi ba, saboda King nake zuwa gida nan, amma har in je fadarsa in gaishesa in fito baya ɗaga idanu ya kalleni, kuma ni ina matuƙar sonsa Aunty"............. Tashin hankali kenan, yau ake yinta, ita King ɗin da kansa ma take so ba ƴaƴansa ba, lallai wannan ta ɗebo da zafi, kai bama da zafi ba ta ɗebo mai tafasa!!.

Wani irin zaro idanun Mammaien ta yi, tamkar idanunta zasu faɗo ƙasa. "Amma dai Aliyah baki da hankali! Ko dai kin sha wani abin ne yau kafin ki zo gidan nan! King Zuhair ma kike magana ko wani King ɗin da ban sani ba?!". Cikin tashin hankali ta yi maganar.

Kara turɓune fuska sosai ta yi. "Aunty idan ba King Zubair ba wani King muke da shi mai power a ƙasar Tunisia? King Zuhair nake magana a kai mana, kuma shi nake so, shi nake burin aura, In Sha Allah kuma ni ce cikon matarsa ta huɗu! Da ni zai rufe kofa, ko ana ha maza ha mata wlh sai King ya aureni!!". Babbar magana!.

"Aliyah lallai mutuwa kike nema, wlh idan baki yi hankali ba a ɗanya ƴaƴansa zasu cinye namarki, wai ke Aliyah ni da nake nan ina ta faman yadda zan yi in ga King auri Jahiz ɗan autan su King ɗin, shi ne bashi da aure, bai taɓa yin aure, matashi saurayi ne mai jini a jika, ga shi shararren mai kuɗi, duk duniya ta san shi, ya fi Abbas fa kuɗi nesa ba kusa ba, ke in takaice maki ma wlh zai iya fin King Zuhair ɗin ma kuɗi, ga shi sabon jini, shararrene da duniya dukka suna san shi, shi ba iya ƙasar Tunisia ne kawai aka san shi ba, duniya gabaɗaya ta san shi, shararren ɗan kwallo ne da yake bugawa Real Madrid, ke kanki kin san da haka, kin san Jahiz ganinsa da ido ma ba abu bane mai sauki, ko a cikin family na kusa kusa ba kowa yake samun damar ganinsa ba, ni kai'na da nake matsayin matar yayansa ma idan ya zo gidan nan ba samun ganinsa nake yi ba, idan kinga na gansa to yayansa yana nan, nan ne zai shigo wajen yayan nasa, a nan nake samun damar ganinsa, kuɗi iya kuɗi yana da shi, ga shi sabon jini matashi, me kuma zaki buƙata....."

Katseta Aliyah ta yi da cewa. "Sarauta! Yana da sarauta ne? Duk kuɗinsa a banza idan ba shi da mulki, burin mulkar ƙasar Tunisia nake da shi ni ba kuɗi ne a gabana ba, burina in yi mulki, in zama mai faɗa aji, dan haka yasa nake son zama mace ta huɗu da zata rufe kofa a zuciyar King Zuhair....." Tashin sense!!.

"To idan mulki kike so ai magajin masarautar zaki ci burin ki aura, magajin wannan powerful seat ɗin zaki kwaɗaitu da son aura, ga Ramish! Ga Bilal! Ga Suraj! Ga Jaish! Sannan ga Aryan! Ɗaya daga cikinsu yakamata ki zaɓa ai, dan sune zasu gaji wannan kujera mai matuƙar power da karfin ikon, in dai burinki ki zama mai faɗa a ji a faɗin ƙasar Tunisia ne to ɗaya daga cikinsu zaki buƙata........"

Kara kwaɓe fuska ta yi tare da wurgawa Aunty tata wani irin kallo mai kama da zargi. "Gaskiya Aunty kanki baya kawo wuta sam sam, ni fa ba ce maki na yi ina son in auri wanda zai yi mulki a nan gaba ba, so nake na haifi wanda zai yi mulki a nan gaba, kina tunanin ko na auri ɗaya daga cikin ƴaƴan King zan samu yadda nake so ne? Gaskiya Aunty sam baki tunani mai kyau, ai ko na auri magajin kakkarfar kujerar izza buƙatata bata biya ba, dan dai ke da kanki kin san ƴaƴansa ba masu juyuwa bane, baki isa ki juyasu yadda ranki yake so ba! Amma idan kika auri uban kika haifi naki ƴaƴan, ko ba yanzu ba nan da shakaru 20 zuwa da 25 zaki zama yadda kike burin ki zama, zaki zama mai karfin iko, a duk lokacin da aka ce ɗanki ne a saman wannan the most powerful seat ɗin, sannan ya sanya powerful Crown a kansa, ai kinga daga nan zaki murza kambunki son ranki a faɗin ƙasar, amma idan kika biyewa ƴaƴan nan nasa sai su ce maki basu son sarauta kamar dai Yah Abbas, kin ga shi ma ya ce maki baya sha'awar sarauta, to nasan ƴaƴansa ma yadda suke shararrun ƴan bokon nan ba wani mulki da za su yi, shiyasa bana son na auri magajin mulki, nafi son na haifi magaji wadda ko ya ce baya son ya yi mulki zan tursasa shi dole ya yi, sannan shi Jahiz da kike magana kada ki manta bashi da gadon mulkin nan a yanzu, dan King yana da yara, da bashi da yara ne sai kaninsa ya hau kujera........"

Kallon tsab Mammie ta yi mata. "Lallai Aliyah kin girma, waye ya ce maki Jahiz bashi da gadon mulki? Yana da shi mana, idan su Ramish suka kekashe ƙasa suka ce basu da ra'ayin mulkar ƙasar Tunisia ai dole idan King ya tsufa Jahiz ya karɓesa tun da Abbas baya ra'ayi".

Cike da rashin respect a maganar tata ta furta. "Aunty koma dai menene ni magajin nake son haifa, magajin da ko baya son mulki zan tursasa shi yi dan cinmma burina, dan haka ni King Zuhair ne burina, shi nake son aura!".

"Aliyah King Zuhair ya fi karfinki, Jahiz shi ne zaɓin da na yi maki, dan haka ki dai'na maganar King!!".

Cigaba da wurga mata kallon zargin ta yi, a ƙule ta ce. "Aunty saboda kema kina da burin auran King Zuhair ɗin shi ne kike son hanani ko? To ki bari mana kowacce ta gwada sa'arta, a cikinmu duk wadda ta samu nasarar mallakarsa ai shikenan duk ɗaya muke, ni dai ba zan hakura da burina kuma muradina ba"............... Tashin sense, lallan yanzu KINGDOM OF POWER zai kama da wuta, na ce ba my people's mu gayawa Aliyah wacece Momma ne ko dai mu bari ta Momma ta gwada mata karfin jinin Modarawa?🤔 Tab kuna tunanin da Momma King ya fara aura ma zai kara aure ne? Ai da ba wannan magana kuma kun sani, hmmm Hajiya Aliyah momma kam dai'dai take da zamaninki, ga Mama a gefe, sannan ga mummy, uwa uba ga su Ramish, wai kuna tunanin su Ramish zasu yarda King ya auri wadda suka girma ne?🤔 Gaskiya akwai rikici a wanan gida ba kaɗan ba.

"Aliyah ni kike gayawa ina son auran King Zuhair? A yaushe muka yi hakan dake?". Ta yi maganar cike da mamaki tana kuma zaro idanun.

"Kina mamakin ya aka yi nasan burinki ne Aunty? To bari ki ji ranar da kika je gida ina jinki ke da mama kuna magana a kan ke dama ba Yah Abbas kike so ba, King Zuhair kike so, dan burin mulki kike da shi, kuma ko za'a mutu ko za'ayi rai, ko rai nawa zaki iya salwantarwa domin ki auri King ki haifi maganin Crown of Kingdom of power!!".

Kara zaro idanu sosai Mammie ta yi, bata taɓa tunanin bayan mahaifiyarsu akwai wadda tasan da wannan magana ba, sirrinta ne kuma burinta!.

"Aunty ki dai'na yin mamaki fa, kuma ki dai'na ƙoƙarin hanani mallakar abin da zuciyata take so, Crown na kingdom of power rawani ne da kowani basarake yake burin samunsa, kujerar mulkin kingdom of power kujerace da jiga jigan sarakuna masu karfin iko suke fatan su zauna a kansa, masarautu ba adadi ne a ƙarƙashin wannan masarauta, duk wani karfin ikon mai karfi a faɗin ƙasar nan dama maƙota ƙasashe duk a ƙarƙashin King Zuhair suke, a haka kike son nayi wasa da wannan dama? Sanin kanki ne fa shiga in da King Zuhair yake ma ba ƙaramin abu bane, ke kanki kin san ko da yatsa ka nuna gate na farko na shigo cikin masarautar nan sai an datse maka hannu, duk wani karfin iko da isa tana nan! Wlh kamar yadda kika ce ko rayuka nawa zaki iya salwantarwa domin ki mallaki King, ni ma hakance, zan iya aikata komai dan na mallakesa, dan haka da ni dake lokacin buga wasa a tsakaninmu ya yi, kowacce ta gwada sa'arta kawai....." E lallai akwai cakwakiya ba kaɗan ba!.

Tana kai karshen maganar ta miƙe fuuu abayar jikinta na ja a ƙasa ta nufi waje, bata zame ko'ina ba sai family part ɗin King, kai tsaye wajen mummy ta nufa, dan ita mummy ƴar baruwa na ce, kowa nata ne, kowa ya zo gidan hannu bibbiyu take tarbansa, shiyasa suke sonta, tana da hakuri haɗi da kawaici, ainahin mahaifiyarta ƴar Nigeria ce, kuma ita ba yar kowan kowa ba ce, tana da taimakon mutane da kuma saukin kai sosai, ba kamar Mama da Momma ba, ku kunsan Momma tana da kyan zuciya, wargi ne kawai bata ɗauka! Iadan ka kawo mata ba dai'dai ba yanzu zata nuna maka cewa jinin Modarawa ne yake gudu a jikinta. Mama kuma sai ka rasa me matar nan take so a duniya, sai bala'in masifar tsiya, ga ɗan banzan kishi na masifa.

Da kallon mamaki Mammie ta bi Aliyah har ta kurewa ganinta, mamaki da al'ajabi ya hanata yin magana, tunani take yi wai yaushe Aliyah ta girma da har take cewa su ƙara ko wacce tata ta fisheta?. Ita ma fa Mammien ba wata babba bace take wani cewa yaushe Aliyah ta girma, Aliyah ɗin ce fa mai bi mata a wajen haihuwa, kada ku manta Sarina ce ƴarta ta farinta, so ita ma ba wata babbar mace can can bace, iyayi ne kawai.

Wayarta ta ɗauka tare da miƙewa ta nufi cikin bedroom ɗinta tana faɗin. "Dani kike yi Aliyah, yaushe ma aka haifeki da har zaki ce mu ƙara akan muradina? Ke har kin isa ina son abu kuma a yunwace nake da na cinma burina a kansa ki ce kema kina son shi? Wlh ba'a haifeki ba! Tsab zan gyara maki zama, zan gwada maki banbancin shekaru..."

Ta kai karshen maganar tata tana zama a gefen bed ɗin nata, dai'dai lokacin kuma wadda take kira a waya ya ɗauki kiran. "Misalin karfe 1 dare mu haɗu a in da muka saba haɗuwa". Shi ne abin da ta gayawa wanda ta kira ɗin. Tana gama faɗin hakan ta katse kiran tare da buga uban tagumi tana tunani.

(Ni kam na ce uncle Abbas da King sun ga ta kansu, shi yanzu uncle Abbas kenan ya Mammie zata yi da shi tun da ta ce yayansa take so? Shi kuwa King yaga ta kansa kowa son shi yake yi, bawan Allah bai ma san ana yi ba, momma ki shirya ga kishiyar karfi da yaji na dole nan Aliyah tana zuwa, zaki tashi daga amarya 😅 Mama kuma kishi zai karu😅 family part ɗin King zai kama da wuta, 🔥 mummy baiwar Allah dai babu ruwanta, da rabon za'ayi yaki ba kaɗan ba, da rabon su Ramish zasu yi kisan kai ko na ce kashe kashe😅 hmmmm KINGDOM OF POWER kuma yanzu nasu wasan zai fara🔥 ina commander ZAFAR sai ku shirya, ni dai bari na tafi Nigeria gidansu Zainab dan jin ya ake ciki).

GIDANSU KHADIJAH 😥💔

Hakura maman Zainab ta yi ta karɓi wannan ɗaki da Hauwa ta zaɓa mata, a ciki ta kwana, bakinciki kamar zai kasheta, ta fara danasanin zuwanta sabon gidan nan, dan bakinciki kala kala Hauwa take kunsa mata, tsabar mugunta dan ta kuntata mata ma da daddare tasa baban Zainab ya sanyata ta yi masu girkin dare, har da gaya mata kalar abincin da take son ta girka masu Hauwar ta yi.

Idan ran maman Zainab ya yi dubu to ya ɓaci, amma haka ta daure ta yi girki tare da taimakawar su Khadija, ita kuwa Hauwa tun yamma da ta gaya mata ga abin da zata yi masu, suka ci wanka ita da baban Zainab ɗin suka nufi kasuwa, ta tasa shi a gaba wai sai dai su je ya karɓi komai nasa daga hannun Sadiq, haka ya shirya suka tafi, maman Zainab ta yi girki tare da su Khadija.

Sai can wuraren karfe 9 na dare su Hauwar suka dawo, a lokacin maman Zainab sun kammala girki ta zubawa su Khadija sun ci nasu, ita ma ta ɗan tsakuri kaɗan ta ci, bakinciki ya hanata cin abincin na kirki, so kaɗan ta tsakura.

Tana gama cin abincin bayan sun yi sallar mangariba da isha'i ta wuce ɗakinta ta kwanta, su Khadija ma suka wuce nasu da Hauwa ta basu suka kwanta, Zainab ta yi addu'ar barci ta kwanta, ita kuma Khadija ta ɗauro alwala, dan kwanciya bai ganta ba iyayenta suna cikin masifa.

Maman Zainab tana kwanciya sai ga kiran Sadiq ya shigo cikin wayarta, haka kawai ta ji gabanta ya faɗi da ganin kiransa. Ɗauka ta yi cike da fargaba. A hankali ta yi sallama kamar mai jin tsoron wani abin ko wadda bakinta yake ciwo.

"Assalamu alaikum Maman Zainab na manta ban gaya maki ba ni fa ina hanyar Kaduna, da farko massages naso in tura maki, amma sai dai nace bari kawai na kiraki". Cewar Sadiq ɗin.

A zabure ta miƙe zaune a tsakiyar gadon, zaro idanu waje ta yi. "Sadiq me zaka je yi a Kaduna? Kuma sai ka tafi baka sanar da ni ba? Yanzu da ka tafi ya kake son na yi da rai'na? Da waye zan yi shawara? Waye zai rage mun raɗaɗin da yake damuna a rai'na?! Ina kake son na sanya rayuwata na ji daɗi? Mutuwa kuke son nayi ne?". Tana magana wasu zafafan hawaye suna biyo ƙuncinta.

"Ki yi hakuri maman Zainab, dole ce tasa na tafi, amma kinsan ni ma ba zan so rabuwa dake a irin wannan hali da kike ciki ba, shiyasa nace maki da farko sms naso in yi maki ba kira ba, saboda kada na ji kukanki, da ina turo maki sms zan kashe wayata, amma ki yi hakuri Allah yana tare da ke!!".

"Sadiq to me yayi zafi da zaka tafi ka barni? Kana da wata ƴar uwa a duniyar nan biyu na ne? Ko dai ka dai'na sona ne". Cikin raunin murya haɗe da karyewar zuciya ta yi maganar.

"Ko ɗaya maman Zainab, ban dai'na sonki ba, yama za'ayi na dai'na sonki? Ai ba zai yiwu ba, yanayi ne yazo da dole na yi nisa dake, idan ba haka ba zan iya aikata kisan kai wadda kema kanki ba zaki so na yi hakan ba, ba zan iya jurar cin kashin da suke yi maki ba, baban Zainab ya zo kasuwa da yamma, ya karɓi komai da komai nasa, mun yi lissafi da shi da Hauwa, komai ya fita yadda yakamata, kuma mun yi a rubuce yasa hannu na sa hannu a kan na mayar mashi da komai ɗinsa, shi ne naga ya dace na koma gida in je in kula da mama".

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull