Kenza eBookz

Rawanin zalinci 1 complete - Chapter 87

Rawanin zalinci 1 complete - Chapter 87

Rawanin zalinci 1 complete Chapter 87: Rawanin zalinci 1 complete Chapter 87. Magana ta gaskiya ba hakance tasa Sadiq ya bar garin Kano ya kama hanyar…

3,348 words

Magana ta gaskiya ba hakance tasa Sadiq ya bar garin Kano ya kama hanyar Kaduna ba, abin da yasa shi ne, wani irin mummunar cin mutunci baban Zainab da Hauwa suka yi mashi a kasuwa, ga lissafi sun yi dallah dallah amma Hauwa ta ce da baban Zainab karya ne ya saci wasu kuɗaɗen, wai ba zai yiwu ace iya wannan ribar kawai aka samu a shagon ba, gudun irin haka fa yasa Sadiq ɗin yake ciyar da su maman Zainab ɗin da kuɗinsa, harta su maman Haidar idan suka zo kasuwa a kan basu da abincin ci daga aljihunsa yake cire kuɗin ya basu, duk dan kada ya taɓa naira biyar ɗin baban Zainab, amma da yake Hauwa makirace, kuma tana jin haushin marin da ya yi mata, sai da ta sa baban Zainab ya ci mutuncinsa a bainan nasi, ya yi mashi kaca kaca, shi kuma Sadiq ga shegen zuciya kamar ɗan kuturu, hakan yasa ya haɗa kayansa ya nufi gidan iyayensa in da zai bugi kirji yace ya isa a can, har police Hauwa ta ce baban Zainab ya kira su zo su tafi da Sadiq ɗin, da kyar masu shagunan kusa da su suka bata hakuri ta hakura, mata kamar wata kanwar shaiɗan. Wannan shi ne a takaice abin da ya faru a tsakaninsu da yasa Sadiq ɗin ya bar Kano, yaki gayawa ƴar uwa tasa gaskiya ne kawai dan baya son ya ɗaga mata hankali, baya son kara mata zafi a kan zafi, shiyasa ya ce mata sun yi lissafi lafiya lou!!.

Sosai maman Zainab ta rinƙa kuka, sai hakuri yake bata ita kuma tana yi mashi magiyar ya dawo dan Allah, daga shi sai su Khadija take gani ta ji daɗi a rayuwarta, sune kaɗai suka rage mata, sune kaɗai farincikinta a yanzu.

Duk magiyar da ta yi mashi ya kafe a kan lallai shi ba zai dawo ba, ta yi hakuri kawai, daga ƙarshe dai ya bata hakuri tare da kashe wayarsa ya yi switch off ɗinta mai gabaɗaya dan ma kada ta sake kiransa.

A wannan daren dai sai da barci ya kasance ɓarawo ya saci maman Zainab, nan ma har wuraren karfe 2, bakinciki da ɓacin rai ya hanata rintsawa baiwar Allah.

Washegari da safe haka ta farka idanunta a kumbure luhu luhu, saboda kuka da ta sha ga kuma rashin barci, tana farkawa ta fito kuma Hauwa ta ce lallai lallai ita zata yi masu kayan ƙarin kumallo, rai a ɓace ta ce ba zata yi ba, baban Zainab ya ce ta yi ko ranta ya ɓaci.

Danne zuciyarta ta yi ta girka ba dan ta so ba, yau dai su Khadijah basu je school ba, dan basu taho da uniform ɗinsu sabon gidan ba, ga shi yau jumma'a, so basu taho da uniform ɗin da suke amfani da shi ranar Friday ba.

A takaice dai babu daɗi suka yi ƙarin kumallo a gidan, duk wanda ka gani ransa a cunkushe banda Hauwa da take cikin farinciki, ranta fes, sai daɗi take ji tana kuntatawa maman Zainab.

Da misalin karfe ɗaya na rana tana zaune a parlour ita da su Khadija, Zainab tana kallo a Tv, Khadija kuma ta buga uban tagumi kamar yadda mamanta ta yi.

"Mama ina kawu Sadiq ne? Ba zai zo gidan nan bane?". Cewar Zainab.

Wani irin ƙululun bakinciki maman ta ji ya taso mata. "Khadija tashi ki je ɗakina ki ɗauko mun wayata bari na gwada numbersa ko yanzu kam zata shiga, tun safe nake gwadawa bata shiga". Da to Khadija ta amsa mata.

Bata kai ga miƙewa ba sai ga Hauwa da baban Zainab sun fito. Yana shirye cikin wata haɗaɗɗiyar shadda chocolate color, ya yi kyau sosai, da alama masallacin jumma'a zai je, ita ma Hauwa ta ci kwalliya cikin abaya brown color.

Gaisuwa Khadijah ta ɗagawa baban nata, a takaice ya amsa ba tare da ya bi ta kanta ba ko ya ɗaga idanu ya kalleta ba. Zata wuce cikin kenan ya ce. "Khadija ki shirya Hauwa ta ce lallai yau a ɗaura aurenki da Haidar bayan mun sauko sallar jumma'a, dan haka ki shirya su Maman Haidar zasu zo su ɗaukeki".

Wani irin kuka Khadijan ta fashe da shi mai matuƙar tsuma zuciyar mai sauraro, da gudun gaske ta afka cikin ɗakin maman nata, wani irin jan numfashi da take yi cikin kuka sai ta baka tausayi, kamar zata haɗiyi zuciya. Da gudu Zainab ta tashi ta bi bayanta.

Ita kuwa Hauwa wani irin murmushin mugunta take ta faman saki. Miƙewa tsaye maman Zainab ta yi, cikin wata iriyar murya da ba zaka iya fassara halin da take ciki ba ta furta. "Baban Zainab kada ka yi wannan kuskuren, wlh billahi Haidar ba zai aura mun ƴa ba, kada ka bijiro da abin da zai sanyaka yin danasani, wlh a kan farincikin ƴaƴana na yarda komai ya faru, zan iya barin maka gidanka a kan wannan aure".

Hauwa ce ta ce. "To me laifi dan yarinya ta auri ɗan uwanta na jini? Kyamar dangin nasa kike yi ne? Amma kuma ke kin haɗa jini da shi ko?......"

Cikin ɗaga murya tare da zafin rai haɗi da ɓacin rai maman Zainab ta ce. "Hauwa ban kasa dake ba, a wannan gaɓa idan kika saka mun baki a maganata zan ci uban, wlh wlh wlh idan kika sake saka baki a maganar nan babu uban da ya isa ya dakatar da ni daga sumar dake a cikin gidan nan, sai na yi maki dukan uwar ala tsine, ke sai na yi maki abin da wlh ke da kanki ba zaki iya gane kanki ba, kin san halina bani da full stop idan aka kureni, in dai ba so kike hajiya ta haifi wata Hauwar ba, ki sake saka mun baki shegiya mai kama da kazar mayu".

Juyowa ta yi ta kalli baban Zainab ɗin. "Honey ka tafi masallaci abinka, kada ka dakata kowa, idan an ɗaura auren ka kirani ka sanar da ni". Cewar Hauwa. Ta yi hakan ne kuma dan tana tsoron maman Zainab, tana tson sake yi mata magana, amma tana da bakin yin magana da baban Zainab ɗin kam ai, a ranta kuma ta ƙuduri niyar yau sai an ɗaura auren nan ko dan taga ya maman Zainab zata yi.

Kai Hauwa dai anyi sheɗaniya makirar mace.

Sa kai baban Zainab ɗin ya yi zai wuce ya fita ba tare da ya ce da maman Zee uppan ba, ko kallon in da take ma bai yi ba.

A ɗari maman Zainab ta sha gabansa tana faɗin. "Kada ka haɗa wannan aure, zaka yi danasani".

Wani irin mari ya zabga mata wai dan ta sha gabansa, rai a ɓace ya daka mata tsawa ta bashi hanya ya wuce.

Ɓacin rai iya ɓacin rai yau ranta ya ɓaci, dama ga baƙincikin tafiyar Sadiq, sannan ga bakincikin da ya ƙunsa mata da safe na sanyata ta yi girki da ya yi, ga na jiya da daddare, sai abin ya haɗu ya yi mata yawa, yanzu kuma ga marin da ya dalla mata, sannan ga future yarta da yake ƙoƙarin lalatawa ta hanyar aura mata Haidar, ta ƙuduri niyar ba zata bari hakan ya faru ba!!.

Hauwa dake tsaye a bayansa kaɗan ne ta ce. "Yes honey, wlh ka kyauta da ka mareta, kai sa'arta ne da zata tare maka gaba?".

A wani irin kaunace maman Zainab ta ɗauketa da wani irin wawan mari wadda sai da ta ga wani haske ya gifta a gabanta idanunta, yau ɓacin rai ya rufewa mmn Zee ido. Cakumo wuyar rigarta ta yi da nufin ta yi mata ɗan iskan duka. Baban Zainab bai bari hakan ta faru ba ya fara ƙoƙarin kwatarta, wasa wasa yaga idan bai saka karfi ba ba zai iya kwatarta ba.

Cikin fushi yasa kafa ya kwashe kafafunta sai ga mmn Zee a kasa rigijib, har lokacin kuma bata saki wuyar Hauwar ba, a tare suka yi ƙasar, ta ƙanƙame wuyar tata kamar mage a saman ɗan siririn reshen bishiya da idan ta sake saza faɗo, kunga dole ta ƙanƙame da kyau. To haka maman Zainab ta ƙanƙame wuyar Hauwa!.

Mari baban Zainab ɗin ya sake kai mata, daga karshe ya fara haɗa mata da duka, Hauwar ma ta fara kai mata duka domin ta kwaci kanta, ta ji shaƙa shegiya, ta ji kamshin lahira, dole ta fara kai duka dan ta samu ta tsira da ranta.

Dukan da baban Zainab yake kai mata ne ya yi mata tsananin zafin da yasa ta saki Hauwar, a guje ta miƙe ta nufi kitchen, sabuwar wuƙa ta ɗauko wadda ba'a taɓa amfani da shi ba, dan komai na cikin kitchen ɗin sabbi ne. Da gudun gaske ta yi kansu da wukar faɗi take yi yau ko sama zata haɗu da ƙasa sai ta kashe Hauwa, sai dai duk abin da zai faru ya faru.

Sanin halinta da balai'n bakar zuciya yasa Hauwar ta ruga a guje ta yi ɗakinta. Da mahaukacin gudu ta rufa mata ba, kamar wata mahaukaciya haka maman Zainab ta zame masu, hauka take yi masu kamar wadda take da aljanun kukar buluhi a kanta.

Da gudu baban Zainab ya bi bayansu. Ihu Hauwa ta fara yi tana kewaye ɗakin dan ta ceci rayuwarta, ita kuwa maman Zainab yadda kuka san bata san menene hankali bama yau, binta take yi kawai tana faɗin. "Yau idan kinga baki mutu ba to ni ce nan na mutu, shegiya mugun iri, ina kika ce ke shaiɗaniya ce? To ki tsaya dan ubanki, yau sai dai hajiya ta haifi wata Hauwar!!"

Sai kewaye ɗakin suke yi, a hau gado a sauka, duk maman Zainab sai farfashe abubuwan cikin ɗakin take yi. A haka baban Zainab ya iskosu, da gudu ya yi ƙoƙarin shiga tsakaninsu dan ya rabasu, ai kuwa maman Zainab zata cakawa Hauwa wukar sai ta caka mashi a tsakiyar cikinsa wajen cibiya. Dama da Hauwa taga ya shigo sai ta tsaya a saman gadon, dan tasan zai tare mata, shi ne maman Zainab ta nufota da wukar, zata caka mata shi kuma ya shiga tsakani.

Nan take jininsa ya fara yin wani irin tartsatsi kamar wutar welder, ga wukar ta cakesa har can cikinsa, gabaɗaya kaifin wukar ta lume a cikin nasa. Kan kace me ya zube ƙasa a kan gadon, jini ne yake zuwa kamar an buɗewa ruwa hanya.

Wani irin mahaukacin ihu maman Zainab ɗin ta saki tare da yin kansa tana kiran sunansa, ita kuwa Hauwa waje ta nufa a guje kamar mahaukaciya tana kurma nata ihun.

Da gudu su Khadija suka fito daga ɗakinsu jin irin ihun da mamansu take kurmawa, kai daga jin wannan ihu kasan bana lafiya ba, dan ihu take kurmawa tamkar maƙoshinta zai ɓalle, sai ambatar sunansa take yi.

Gwanin ban tausayi shi kuma sai shure shure yake yi kamar wadda ransa yake fita, ƙafafunsa sai kaɗawa suke yi, ko'ina na jikinsa kakkarwa yake yi, harta gashin kansa sai da suka mimmiƙe tsaye, wani irin zara zaran jijiyo ne suka fito ɓaro ɓaro a hannunsa zuwa ƙafafunsa har gaban goshinsa da kuma wajen wuyarsa, wahala ta fito da su, nan take ya yi wani irin fari kamar ba shi ba, har lokacin jini na feshi kamar wutar welder, haka zalika har lokacin yana ta shure shure, idanunsa sai juyawa sama suke yi, bakin ciki sai ƙoƙarin ɓacewa yake yi, wani irin zufa dake tsastsafo mashi yana wanke ko'ina na jikinsa sai ya baka tausayi, fuskarsa kamar an watsa mashi ruwa, ya jike sharkaf da zufa, kayan jikinsa duk sun jike da zufar azaba!!.

Ai Khadija na leƙowa taga abin da yake faruwa sai ta yi waje da gudu domin ta kira mutane su zo su taimaka masu kada babansu ya mutu, ita kuwa Zainab ta yi kansa da gudu tana ihu, Hauwa kuma sai Allah kaɗai yasan in da ta nufa...... Tashin sense!!! Akwai matsala fa my people's😥💔

Shin baban Zainab zai mutu ko zai rayu? Ina Hauwa tsohuwar makira? Ya makomar maman Zainab?.

Zuciyata ba zata iya jurar ganin tashin hankalin da waɗan nan ahalin suke ciki ba, bari dai na leƙa Dubai muga me yake faruwa a can, my people's yanzu littafin RAWANIN ZALINCI zai fara ɗaukar 🔥 dan yafi karfin ɗaukar zafi sai dai wuta, mun dai kusa isa ga RAWANIN ZALINCI da gaske!.

Second to the last page of book 1 my people's. 💘🔥

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 14/9/2024.....✍️📚🌹

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________52🔥

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🕊️🌼🕊️

ABU ABDUSSALAM EMPIRE 🤍🔥

A karo na biyu ma wahala Leesharh ta sha sosai wajen neman mai kai abinci, sai dai kuma bata ci nasara ba har yanzu, sake dawowa cikin ɗakinta ta yi, a bakin gado ta zauna, uban tagumi ta buga tana tunanin mafita, mahaifinta ne kawai a ranta, shi kaɗai take tunawa, ta ci burin yau ta yi magana da shi.

Sallamar Sharifat a cikin room ɗin ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta afka. Da kallo ta bita, ta kasa iya amsa mata sallamar, dan hankalinta baya a jikinta, duk ta yi la'asar.

Kusa da ita Sharifat ta zauna, cikin sanyin murya ta ce. "Leesharh Yah Guyson ya gaya mun kin yi kuka a kan wani abin ya shiga maki cikin ido ko?".

Kai ta gyaɗa mata alamar e haka ne. "Eyya sorry, amma kuma dan wani abin ya shiga cikin idanun ki hakan doesn't mean sakacin masu aiki ne, i told Yah Guyson kada ya ce laifinsu ne, kada a hukuntasu, be cause yau rana ce ta taro, baki dayawa sun zo, a wajen shige da fice ma za'a iya samin kwari ai".

Da sauri ta amsa mata da. "Yauwa Sharifat, even me abin da na gani kenan, please ki rarrasheshi kada ya ce za'a hukunta masu aikin nan, please ya yafe masu".

"Leesharh tell me the truth, what's wrong with you? I already saw many problems in your eyes, so please feel free and tell me!".

Tsuru tsuru ta yi da idanu, yanzu me zata ce da Sharifat? Ta tambayi kanta da kanta.

"Leesharh from which country you came here?". Ta sake jefa mata tambaya, Sharifat tana zargin ko Leesharh tana kewar iyayenta ne yasa take shiga damuwa haka, kamar dai yadda Guyson ya yi hasashe ɗazun, suna ganin yarintarta sosai, suna ganin bata kai a rabata da iyayenta ba, shiyasa suke yawan tambayarta ko tana kewar iyayenta ne, basu ma san ita Leesharh ai ta jima rabonta da iyayenta ba, idan da sabo yanzu ta saba da kaɗaicinsu.

"Am from Nigeria". Ta bata amsa a takaice, ta yi maganar kuma kanta na'a ƙasa tana kallon ƴatsun hannunta. "Do you mean Nigeria African?". Ta faɗa tana zaro idanu alamar mamaki.

Kai ta gyaɗa mata alamar tabbatarwa daga Nigeria take. "From Nigeria you came here because of work? Kai dole ki yi missing na parents naki, dole ki shiga damuwa, but why your parents zasu yarda su barki ki zo nan aiki? Su ba zasu ji kewarki bane? And su basu ga akwai nisa bane?". Tana maganar still mamaki ne sosai a saman face ɗinta.

Shiru ta ɗan yi mata, kamar zata fashe da kuka take ji, zuciyarta na yi mata zafi, Sharifat ta taɓo mata in da yake yi mata kaikayi, ta tuna mata da iyayenta, duk sai ta ji wani irin.

"Sorry ko Leesharh, dole ki rinƙa kuka na kewar parents ɗinki, in saya maki waya ki rinƙa magana da su dan ki rage damuwa da kewa?".

Sai a lokacin ta zaro nata idanunta da suka girmewa na Sharifat a girma, idan ta zarosu kamar ka ruga a guje. Ko me ta tuna sai kuma ta ɗan yi ƙasa da kai.

"Leesharh meyasameki kuma? Is there any problem again?".

Kai ta girgiza alama a'a babu komai. "Leesharh talk to me now! should I buy phone for you? Saboda ki rinƙa kiran parents ɗinki, I don't want to see you always crying and worried".

A takaice Leesharh ta ce mata. "I don't have anyone in my life, I don't have a mother and i don't have a father, they're not alive, they're all dead". Ta faɗa kamar zata yi kuka, kuma ta gaya mata hakan domin Sharifat ɗin ta rabu da ita da zancen saya mata wayar nan, kada ta zo ta saya mata waya hakan ya zame wa babanta babbar baraza, dan masu nikaf basu bata damar yin amfani da wata waya ba bayan wanda suka bata, shi ma kunji sun gargaɗeta a kan kada ta kuskura ta kira kowa da shi, so hakan yasa ta ce bata da har da uba, ni da ku mun san iya mamanta ce kawai bata raye, amma ta haɗa harda babanta dan tsira daga wajen Sharifat kada ta saya mata waya. Tasan cewa duk abin da zata aikata a kan mahaifinta masu nikaf zasu ɗauki fansa, idan ta yi kuskure babanta ne zai ji a jikinsa! Hakan yasa take taka tsantsan sosai!.

Wani irin mugun tausayinta ne ya kama Sharifat ɗin na jin cewa bata da iyaye, Allah sarki duk sai ta ji jikinta ya yi sanyi, ji ta yi zata yi ƙoƙari ta ɗauketa kamar yar uwarta dan ta rage mata raɗaɗin rashin iyaye, da yake ita da Guyson akwaisu da zuciyar zinari na tausayi sosai, ga hakuri kamar damo, basu da faɗa kuma basu son hayaniya, kowa ya zauna da su sai ya ji yana tsananin kaunarsu, saboda kyawawan halayensu.

Ɗan matsowa ta yi ta rungumeta tana yi mata sannu a kan rashin iyaye. "As from today i am your sister kin ji? Sorry ko?". Ta faɗa tana mai kara jin tausayinta sosai.

Ita ma Leesharh ɗin duk jikinta ya yi sanyi, tana jin kaunar Sharifat ɗin tamkar ƴar uwarta na jini, saboda kauna da ta nuna ma, duk sai ta ji bai kamata ace ta yi abu komai ƙanƙantarsa dan ta cutar da bayin Allah nan ba, ita tama rasa a wani matsayi zata ajiye Sharifat da Guyson, babu ruwansu da girman kai, mahaifinsu yana da murya mai karfin faɗa aji kuma dole ayi abin da ya ce a faɗin ƙasar, ga ɗimbin dukiya da shi kansa bai san adadinsu, ga matsayi a siyasance, sannan ga matsayi a sarauce, ga tarin masu kaki kala kala a ƙarƙashinsa, duk wata kaki a faɗin ƙasar bata isa ta motsa ba ba tare da izininsa ba, karfin iko gare shi ba kaɗan ba, amma su Sharifat duk basu ɗauki hakan a bakin komai ba, abin duniya bata damesu ba, basu ɗaurawa kansu girman kai ba, Guyson kam ma ai shi ta ko'ina ma jinin mulki ne yake gudana a jikinsa, ta sama da ta ƙasa, amma babu ruwansa da girman kai ko kyamar talaka, yana son kowa da zuciya ɗaya.

A can wajen walima kuwa. Tun da suka je wajen Guyson yake ta ƙoƙarin dannar twins Obaid and Omaid, shi Omaid ma ya hakura ya barwa cikinsa abin da yake tunani dan gane da Leesharh, dama shi kun san ya iya takunsa. Obaid kuwa sarkin bakar zuciya, sai cika yake yana batsewa, shi lallai lallai dole sai Guyson ya yarda Leesharh criminal ce, har da wani cewa su basa hasashen abu kuma ya zama karya. Shi kuma Guyson ya ce sam ba zai yarda a kan ita mai laifi bace kuma abin zargi, saboda shi baiga laifin da ta yi masu ba, kuma shi ba zai yarda ya zargeta ba, ya kafe masu a kan lallai ita ɗin mai gaskiya ce, sune kawai basu sonta.

Tun da suka shigo wajen yayyun nasu suke yi masu kallon tuhuma except Abu Abdussalam da ya buƙaci su zo kusa da shi su zauna ya yi kewarsu, Abu Abdussalam yana bala'in kaunar Momma da King Zuhair, shiyasa yake kaunar ƴaƴan nasu.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull