Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 1

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 1

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 1: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 1. ???? RAWANIN ?? ZALINCI ????

3,334 words

???? RAWANIN ?? ZALINCI ????

????????????????

FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????

?????????? 16/9/2024.....??????

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????

??STEP TWO....??????

E__________________1??

GIDANSU KHADIJAH ????

Daga Zainab har mamanta an ransa wanda zai kalli ?an uwansa ya ce ya yi shiru, sun shiga tsananin tashin hankali. Basu ?ara tsorata bama sai da suka kalli baban Zainab ?in ya dai'na motsi, ya yi tsit alamar rai ya yi halinsa.

Wani irin ihun da Maman Zainab ?in ta kurma mai sauti sai da yasa Zainab ta tsorita sosai ta mi?e tsaye. Daga wannan ihun da ta kurma bata sake yin kwakkwaran motsi daga in da take ba, kawai ta sulale ?asa ne, kan ka ce me ta dai'na numfashi, numfashinta ya ?auke diff alamar ta sume.

Da gudu Zainab da diro ?asa daga saman gadon, har lokacin kuma jini na cigaba da malala daga cikin babanta, yadda kuka san hanyar ruwa ta fashe, kuma babban abin takaicin ma fa?uwar da ya yi yana murkusoso sai ya kwanto a kan wukar dake cikin nasa, hakan yasa wukar ta kara lumewa a jikinsa, shiyasa jinin ya yawaita sosai, dan ba ?aramin ciwo ya ji ba, ga shi a tsakiyar cikin nasa ta caka mashi wukar, abin ya munana sosai!!.

Waje Zainab ta nufa domin ta duba Khadija, ta rasa me zata yi wa iyayen nata ne yasa ta bi bayan yar uwarta.

A takaice dai maman Zainab bata tashi farkawa ba sai da ta ?auki awa uku masu kyau a sume, an zuba ruwa an zuwa ruwa, amma shiru bata farfa?o ba, daga karshe suka kyaleta suka zubawa sarautar Allah ido.

Lokacin da ta farfa?o kuwa sai ganin kanta ta yi a wani irin ?aki mai kama da cell na ?an'sanda. A hankali ta fara bin saman celling da kallo, idanunta sun kumbura luhu luhu, sun kuma yi jajir kamar jini ne kwance a cikinsu.

Tunanin baban Zainab ne ya fa?o mata a ranta, hakan yasa ta yun?ura zata mi?e da zafinta kuma a ru?e. Sai dai kash ta kasa iya mi?ewar, sakamakon jikinta duk ciwo yake yi mata, ga??anta sunki koda motsawa.

Hakura ta yi ta cigaba da kwanciya a saman tabarman da take ?in. A hankali ta fara sauko da kallonta da kallon celling da take yi izuwa ?asa dan taga a ina take a kuma wani hali take! Wasu irin siraran hawayen takaici ha?e da danasani mai girma ne suka fara zirara daga idanunta izuwa saman ?uncinta.

Kwatsam ba zato ba tsammani tana sauke idanun nata ?asa sai saman kofar shigowa wanda yake kofa ce ta burglaris, wato kofar cell kenan.

Zaro idanu ta yi a tsorace, jikinta har kerma ya fara yi, cike da mamaki take tunanin ina su Khadija da baban Zainab ?in? In da take ?in babu kowa bare ta yi tambaya. Sake yunkurin mi?ewa ta yi a karo na biyu, cikin tashin hankali da ru?ani take. Jikinta sai kerma yake yi, idanunta sun cicciko da kwallah sosai ga kuma wasu na zuba.

A wannan karon ma kasa mi?ewar ta yi, saboda jikinta duk a mace yake, ga bala'in ciwo da yake yi mata. Tunani ta fara yi a kan me ya kawota cell kuma? Me ta yi?.

Rasa mai bata amsa ta yi, hakan yasa bata gaji ba ta sake yunkurin mi?ewa a karo na uku, sai a lokacin ta fahimci cewa kafarta na ?aure da wani sarka irin na ?aure manyan ?arayi. Kara zaro idanu ta yi tare da fara ?o?arin tunawa ko zata iya tunano abin da ya faru a baya?!.

A can gida kuwa sai kuka Zainab take ta yi, ta ?unshe kanta a cikin ?aki tun bayan da ?an'sanda suka tafi da mamar ta su.

Abin da ya faru shi ne, fitar da Khadija ta yi domin zuwa kiran mutane su zo su taimaka masu, tana fita bakin gidan nasu bata ga kowa ba, babu mutane, dukka mazan unguwar tasu sun tafi masallacin jumma'a, dan lokacin an fara sallar jumma'a.

Ganin hakan yasa a ru?e ta nufi hanyar fita daga unguwar nasu izuwa bakin titi ko zata ha?u da wasu su taimaka mata, basu da nisa da titi. Bata ?arisa fita ba wata dankareriyar mota kirar Bugatti la voiture noiro baka kirin sai kyalli take yi ta faka a gabanta.

Tana ?o?arin kaucewa motar ta ra?a gefenta ta wuce sai gani ta yi an bu?e kofar motar. Wasu maza biyu kyawawa farare tas tas masu sanye da suit ash color ne suka ?alle kofar motar suka fito. Daga ganin mazan nan ba Nigerian mens bane, daga gani daga ?asashen masu jajayen kunnuwa suke, dan kuwa jajir suke kamar ka ta?a jini ya fita, ba irin farin Nigeria bane, ga kyakkyawan gashin kai bakin kirin, sannan idanunsu tas kamar an ?iga zaiba, kwayar idanun kuma bakin kirin har wani ?an kyalli yake yi, suna da kyau kam masha Allah, matasane da ba zasu wuce 25 years ba a duniya.

Sai dai da kallo ?aya zaka yi masu ka san basu da imani, saboda fuskokinsu babu alamarta ko ka?an, a turnuke fuskokin nasu suke sosai. Ga su dai dirarrun maza ne sosai sosai, kira kamar su suka yi wa kansu.

Da yake tana cikin ru?ani da tashin hankali sai bata ma bi ta kansu ba, hasalima bata ?aga idanun ta kalli koma su waye bane, kai tsaye ta ra?a gefensu zata wuce, kamar wata mahaukaciya haka ta zama.

Bata kai ga wucesu ba suka damketa suka wurga cikin motar tasu, ga motar da tinted a jikinta. Ihu ta fara kurmawa da karfi karfi. A hanzarce suka fa?a cikin motar suma, suna shiga kuma bayan sun rufe kofar ji kake tsit Khadija ta dai'na wannan ihu, kamar wa?an da suka yi mata wani abin...... To fa, su waye su?.

Cikin kwanciyar hankali suka yi reverse na motar tasu, a hankali suka takata suka bar unguwar, suka mi?i hanya.

Abin da yasa kenan su Zainab suka ga ta jima bata dawo ba, ita kuma Zainab ?in bayan mamarta ta suma sai ta fito a guje kamar mahaukaciya, dan ta nemo jama'a da kuma ?ar uwarta.

Kasancewar ta fito a guje kamar mahaukaciya yasa ta shiga gaban wani mai mashin da ya ?auko wata mata, ai kuwa bata ankara ba sai jinta ta yi a ?asa. Ko ka?an bata wani damu ba, da yake Allah ya takaita mashin ?in bai ji mata ciwo sosai ba, tureta kawai ya yi ta fa?i ?asa, ?ar kwarzanewa ta yi a hannunta sakamakon wani dutse da yake a kusa da ita ta fa?a kansa.

Baiwar Allah hankalinta baya a jikinta, sai ta mi?e cikin ka?uwa da tashin hankali. Da gudu ta nufi bakin titi. Mai mashin da yake ?o?arin banka mata ashariya saboda shiga gabansa da ta yi, kafin ya bu?e baki ma ta mi?e da gudu ta barshi da baki a bu?e, bai san me take ji ba, bai san bala'in da yake kanta ba.

Bata ?arisa isa ga bakin titi ba sai jin jiyar motar ?an'sanda a gabanta ta yi, birki ta ja ta tsaya da nufin idan sun wuce sai ita ma ta nufi bakin hanyar, kasancewar hanyar fita daga unguwar tasu zuwa bakin titin babu wani fa?i sosai.

Ganin Hauwa a gaban motar ?an'sanda ne yasa Zainab ?in bata san lokacin da ta juya ta fasa isa ga bakin hanya dan neman mutane ba, ta juya ta bi bayansu, dan tasan cewa definitely gidansu wannan mota ya nufa tun da ga Hauwa a ciki....... Ashe ?an'sanda Hauwa ta je tattarowa.

Suna isa bakin gate ?in suka fara dirowa ?asa daga saman bayan motocinsu, ba tare da ?ata lokaci ba suka nufi cikin gidan, ?an'sanda shidda ne cif suka zo, sai Hauwar da ta kirasu, shegiya ko ?an'kwali babu a kanta.

Ita ta yi masu jagoranci har izuwa ?akin nasu in da maman Zee ta kashe baban Zainab ?in. Suna shiga suka sami maman Zee a sume, duk da take a sumen kuma bai hana sun tafi da ita ba, hands gloves suka sanya a hannayensu kafin su ta?a baban Zainab ?in, sai da suka ?auke shi a hotuna kala kala ma kafin su ta?a shi. A takaice dai wannan shi ne abin sa ya faru.

Zainab tana kuka kada su tafi mata da mamarta, amma haka suka wuce da ita tana sume bata san me yake faruwa ba, sannan suka tafi da Hauwar ma, dan kara gudanar da bincike, shi kuma baban Zainab wasu ?an'sanda ne na daban suka zo suka ?auki gawarsa izuwa asibiti, dan a yi gwaje gwajen da za'ayi.

Hauwa a police station ?in ne da suka je ta kira Hajiyarsu baban Zainab da wayar baban Zainab ?in ta sanar mata da cewa maman Zainab ta kashe baban Zainab, gawarsa tana police hospital, dan haka su zo.

Ai kuwa babu ?ata lokaci sai gasu sun hallara a station ?in bayan Hauwar ta gaya masu a division ?in da suke.

?an'sanda sun yi sun yi maman Zainab ta farfa?o daga sumar nan da ta yi sun ?asa, sun yi ta zuba mata ruwa, amma bata farfa?o ba. Hakan yasa suka yi duk gwaje gwajen da zasu yi ?in tana sume.

Shatin zanen hannunta ne a jikin wukar dake lume a cikin baban Zainab ?in, suna gwajin farko ya tabbatar masu da hakan, hakan yasa suka gasgata dukkan zantukan da Hauwa ta gaya masu, sun yarda, duk wani bincike da zasu yi ya tabbatar masu da lallai maman Zainab ce ta yi wannan kisan kan, wannan dalilin yasa suka jefata cell tun kafin manyansu su iso kan case ?in.

Ita kuwa Hajiyarsu baban Zainab ?in da take ta faman kuka tun da ta zo, ?an'sanda sun ce ta koma gida, kin yarda ta koma ta yi, fa?i take sai maman Zainab ta biyata ran ?anta, azzaluma ta kashe masu bangonsu, da shi ka?ai suka dogara, shi ne mai yi masu komai, dan haka wlh sai ta biyata ?anta, maman Zainab dake sume bata san wainar da ake toyawa bama baiwar Allah, sai banka mata ashariya kala kala suke yi tana sume. Maman Haidar kam ma har da wani cewa wlh ba zasu yarda ba dole ita ma a kasheta kamar yadda ta kashe shi azzaluma kawai.

Da kyar dai aka samu ?ar'sanda mace ta ja Hajiyar suka tafi zata mayar da ita gida, haka su Maman Haidar suka bisu, Maman Hanif kam ta ?asa iya furta ko kala bayan ruwan hawaye da take yi, banda ruwan hawaye babu abin da take yi, ita dai tasan maman Zainab ba zata ta?a kashe baban Zainab haka kawai da gangan ba, dan ita ta san soyayyar da yake a tsakaninsu, ta san irin yadda baban Zainab ya rin?a jigila a tsakanin Kano da Kaduna saboda ita, sannan ta san yadda maman Zainab ?in ma take son shi, so ita bata ma yarda cewa maman Zainab ?in ce ta kashe shi ba, zargin Hauwa ce ta yi hakan take yi a ranta, dan ita fa kwata kwata bata kaunar Hauwa, amma Hajiyarsu da Maman Haidar fa suna kaunar Hauwar duk da balai'n da take surfa masu, da alama ta kai sunansu wajen bokanta ne, sai dai aikin bai kama maman Hanif ba, dan dai ita kam babu son Hauwar ko ?igo a ranta, sai ma zallar tsana da take yi mata.

Ko da aka mayar da su gidan baban Zainab ?in, a bakin kofar gidan suka isko Zainab a zaune tana tikar kuka kamar ranta zai fita, ta rasa ina zata sanya rayuwarta, babu uba yau, sannan ?an'sanda sun tafi da mamansu, ga kuma Khadija shiru bata dawo ba.

?ar'sanda da ta rakosu ta dawo da su gidan tana juyawa suka fara halin nasu, tana barin gidan maman Haidar ta fara surfe da nikar bala'in a kan wlh ba zasu ta?a hakura su yafewa maman Zainab ba, dole a kasheta kamar yadda ta kashe masu bangonsu ma jingina.

(Ni kam na ce sai yanzu kenan suka san cewa shi ?in bango ne a gare su???)

Kasancewar har da Hauwa ?an'sanda suka saki da nufin idan wani abin ya taso zasu nemeta, hakan yasa ita ma ta fara rera nata kukan munafurcin tana fa?in wlh haka ne ba zasu yafe jinin baban Zainab ba.

Dama fa ita Hauwa idan baku manta ba dukiyar baban Zainab ?in kawai take so ba shi ba, so ita mutuwar tasa ma rage mata hanya ya yi, ya zame mata tsanin da zata ta?a ta cinma burinta ne, dama ko maman Zainab bata kashe shi ba ita Hauwar ta shirya yadda zata sanya a ?atar mata da shi bayan ta gama kwasan abin da zata kwasa, so ita wannan kasheshi da maman Zee ta yi hanya ta rage mata, wani dama ne ta samu, yanzu tunanin da yake a cikin ranta kawai shi ne ta yadda zata yi ta rufe bakin kowa ta kwashe komai na marayun Allahn nan Khadija da Zainab ta gudu abinta, shiyasa ma kuka ga ta yi saurin zuwa ta kira ?an'sanda domin su tafi da maman Zainab, tasan idan maman Zainab ?in tana cikin cell abubuwa zasu tafi mata yadda take so sa?anin idan tana gidan, bokanta ya gaya mata asirinta ba zai ci maman Zainab ?in ba, ba zata iya rufe mata baki ba, domin a yanzu maman Zainab ta tsaya tsayin daka a kan ibada, ta koma ga Allah sosai, hakan yasa babu wani aiki da zai iya kamata.

Sanin hakan yasa Hauwar ta yi azaman jefata a cell, dan in tana gidan zata katse mata duk wani abin da ta shirya, kuma bata isa ta ?auki ko tsinke a gidan ba, amma yanzu kunga maman Zainab tana cell, iyayen baban zee ?in kuma ta sanya an yi masu aikin cusa masu kaunarta, saura mata aiki ?aya shi ne ta rufe bakunansu ta yadda zata gudanar da komai babu wanda zai iya ce da ita uppan........ E lallai akwai kura, ina Khadija? Sai Allah ka?ai yasan su waye suka ?auketa, ina kuma zasu kaita baiwar Allah.

Wani irin tsananin tsana Hajiyarsu baban Zee ta ji take yi wa maman Zee da ?a?anta gaba?aya...... Ni kuwa nace to me laifin ?a?an nata? Su suka yi laifin ne? Ko a wajen Allah laifin wani baya shafar wani, amma jahilci yasa Hajiyarsu ta ha?e da su dukka ta tsana kamar ta kashesu, sai fa?i take maman Zainab ta gama da su ta tona masu asirin da Allah ya rufa masu, shikenan sun shiga uku sun lalace.

Maman Hanif kam har izuwa yanzu ta kasa iya furta ko uppan. Banda zagi babu abin da maman Haidar take surfawa Zainab dake zaune a bakin kofa tana tikar kuka, yarinyar nan kamar ranta zai fita, kuka take yi ba ji ba gani, idanunta har ?an?ancewa suka yi, sun kumbura sun yi jajir, idan ka ganta sai ta baka tausayi, sai kuma ka tsorata da ganin idanun nata, saboda yadda suke jazur da su.

Ko sannu bata ce da su ba, duk zagin da maman Haidar take yi mata bata ko ?ago idanu ta kallesu ba, hasalima hankalinta baya a tattare da ita ne, bata jin me ma suke fa?e.

Maman Haidar na zagi Hauwa na ?ara ingizata, har da kara cewa ai dama maman Zainab ta kai sati tana cewa sai ta kashe baban Zainab, dan haka wlh har su Zainab ?in ma kada su bari, ai suma mugun iri ne, dan halin uwarsu suka ?auko.

Ita fa Hauwa fama take yi taga yadda zata yi ta kawar da su Zainab ?in, sannan ta rufewa kowa baki ta kwashi dukiya ta yi pacakanta da su son ranta, ta ha?a kayanta ta koma Kaduna....... Gaskiya ba karamar mayyar son abin duniya bace Hauwar nan, ba kuma ?aramar azzaluma bace ba.

Da dai suka ishe Zainab da zagi kamar zasu cinyeta ?anya, sai ta mi?e ta nufi cikin ?akinsu, ji take kamar zuciyarta na ?onewa da wuta, su barta ta ji da abin da take ji mana, amma suna kara mata wani.

Ko da ta shiga ?akinma ba su barta ba, maman Haidar ta ce ta fito daga ?akin nan munafuka, yadda kuka san ba jininsu ba ce, kamar ba jinin baban Zainab ?in ne yake gudu a jinin Zainab ?in ba, suka murje idanu, suka sanya yarinya a gaba da zagi da ba?a?en maganganu kamar ita ta aikata laifin ba mamanta ba.

Da maman Hanif ta yi ?o?arin basu hakuri su rabu da ita, ai kuwa ita ma maman Haidar ta hau zaginta babu kakkautawa, wai bata kishin jinin ?an uwanta, kamar ba yau bawan Allahn nan ya rasu ba, sun zauna sai kace nace suke yi, tun ruhinsa bai gama sauka a masaukinsa ba sun fara wala?anta bayansa, sun fara cin zarafin ?a?ansa kamar ba nasu ba.

A takaice dai Zainab da ta ga ba raga mata zasu yi ba, sun isheta da magana, sai ta kama hanyarta ta nufi barin gidan. Maman Haidar ce ta ce ina zata je munafukar banza.

Ko sannu bata ce masu ba, bata ma sake ?aga idanu ta kallesu ba, abin da take ji a cikin zuciyarta ma ya isheta, haka ta yi banza da su ta nufi waje, sai magana suke ta yi mata, ina ko waigowa bata yi ba, sai kiranta suke yi.

Tana fita ta fara neman ina Khadija take, tana tafiya tana hawaye bibbiyu, wani na bin wani gwanin ban tausayi.

Ni kai'na na tausayawa maman Zainab da ?a?anta wlh, kowa da kalar tasa ?addara a rayuwa, ba ta yadda Allah baya jarabtar bawa, amma kuma my people's ina son ku san wani abu, duk wanda kuka ga yana shiga cikin kaddarori to wlh Allah ya fi sonsa, Allah yana jarabta imanin bawa ne kawai idan yana kaunarsa, kada ki ga kina shiga cikin wasu matsaloli ki yi tunanin ko Allah baya tare da ke har ki fara tunanin kauce hanya, wlh wlh wlh Allah yana jarabtar wanda yake so ne kawai, to fata na dai a nan shi ne Ubangiji Allah ya bamu ikon cin rabawarmu a rayuwa koma wace iriya ce, sannan ?arin wata haske shi ne duk abin da kike so kike kauna a rayuwar nan ki saki a nan kaddararki da jarabawarki take, hadisi ne in gantaciya, domin na baku misali a aikace yasa na zaje na yi rubutu a kan part ?in su maman Zainab, duk abin da ya faru da maman Zainab mu kaddarine da ga Allah, kuma ku sani kaddara da jarabawar ta faru da ita ne a kan abin da ta fi so ta fi kauna wato baban Zainab, a dalilinsa komai ya faru, saboda son da take yi mashi yasa har ta kauce hanya, dalilin son da take yi mashi yasa abubuwan duk suka faru da ita, da bata son shi da hakan ba zai faru ba, so misali na baku a aikace ba a labarce ko a kwatance ba. ?ar uwa ki kasance mai yawan rokon Allah a kan abin da kika fi kauna, hakan zai sa idan kaddara da jarabawa zasu afka maki bisa wannan abin ya zo maki da sauki, saboda yawan addu'a, fatan kun gane? To rayuwar maman Zainab tarin karatu na tara maku a wajen dan ku ilmantu, Allah ya bamu dacewa ya kuma yafe mana kura kuranmu.

??????????????????????????????????????

KINGDOM OF POWER??????

A karo na almost 8 Yah Jawad ya sake gwada kiran number Jaish, sai ya ji number a kashe. Guntun tsaki ya ja kafin ya ce. "Aikin me ka yi jiya da har yanzu baka tashi daga barci ba? Wato na dameka da kira shi ne har da kashe wayar ko? Zamu ha?u ne".

Ya kai karshen zancen zucin nasa tare da kai kallonsa kan Chuchu dake goge ?an bakinta da tissue. "Kin gama mu je ko?". Gya?a mashi kai ta yi alamar e.

"Amma Yah Jawad ka ?an ci abincin mana". Ta fa?a kamar zata yi kuka, sam bata ji da?in yadda yaki cin abincin bane.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull