Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 2
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 2: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 2. "Kina son in ci ne?". Ya fa?a tare da ?a?alo murmushin dole dan ya kwantar mata…
3,328 words
"Kina son in ci ne?". Ya fa?a tare da ?a?alo murmushin dole dan ya kwantar mata da hankali, amma zancen gaskiya hankalinsa a tashe sosai yake, kawai Rizwan ya gaya mashi kada ya bari kowa yasan me yake faruwa ne yasa ya danne, amma ga dukkan alamu maganar da suka yi da Rizwan ta yi mugu mugun ?aga mashi hankali.
A hanzarce cikin farinciki ta furta. "E Yah Jawad ina son ka ci".
"Zaki bani a baki?". Ya fa?a yana kura mata ido, kuma ya yi maganar yana ?ara ?a?alo murmushin.
Kai ta gya?a mashi. "E zan baka a baki Allah in dai zaka ci".
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, da alama maganar ta yi mashi da?i sosai. Gaya mata abin da zai ci ya yi, da sauri ta zuba mashi tare da ?aukar spoon na fara ?ebo mashi.
Saitin ?an bakinsa ta kai mashi tana sunkuyar da kanta ?asa. A fili ya furta. "A matsayin wa zaki bani abincin a baki?".
"Yayana da na fi kauna". Ta bashi amsa. "Da gaske kin fi kaunata sama da kowa?". Ya yi tambayar da alamar mamaki a saman fuskarsa. Kai ta gya?a mashi alamar e.
"Meyasa kika fi kaunata?".
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta fara jero mashi bayani. "Saboda kafi sake mun fuska sama da su Yah Bilal, sannan ka fi su kaunata, kana mun duk abin da nace nake so, kana wasa da dariya da mu sa?aninsu Yah Bilal da ko murmushinsu ma ban ta?a gani ba, sannan kan......."
Katseta ya yi da cewa. "Meyasa kika ce nafi kaunarki Jannat?".
Girgiza kai ta ?an yi. "Yah Jawad ni ma ban sani ba, kawai dai nasan kafi kaunata shiyasa na fi kaunarka sama da kowa, daga kai kuma sai Yah Rizwan, sai Yah Raj, ku ka?ai nake so".
Ajiyar zuciya ya sauke tare da kai hannunsa ya ri?o hannun nata, bakinsa ya kai spoon ?in, a tare da shi da ita suka juye mashi abincin a cikin baki yana kallon face ?inta.
Sake mayar da spoon ?in ta yi zata ?ebi abincin bayan ya saki hannun nata. Hannun nata ya sake ri?ewa yana fa?in. "Ajiye spoon ?in ki ciyar da ni da hannunki".
Ba musu ta ajiye ta fara ?iba da hannunta tana bashi a bakin. Sosai ya ci abincin, bai yi zaton zai ci mai yawa har haka ba, amma da yake suna hira tana bashi sai ya ci mai ?an yawa.
Bayan sun kammala ya ce su je ya kaita school akwai in da zai je. Mi?ewa ta yi tare da ?aukar jakarta suka nufi waje.
Dai'dai zai fita part ?insu mai gaba?aya, family part na King kenan, a dai'dai katafaren gate ?in suka ci karo da Mammie tana shigowa, da alama ta biyo bayan Aliyah ce.
Shi kuwa Jawad yana ri?e da hannunta, sai hira take zuba mashi suna tafiya, dama zai je amsa kiran mammie ?in ce kafin ya wuce ya kaita school, shiyasa suka nufo kofar fita ba tare da mota ba, shi fa Jawad gaba?aya ya mance da cewa Mammie ta ce kada ta kara ganinsa a tare da Chuchun.
Dakatawa daga tafiyar da yake yi ya yi. Da kallo ya bi Mammien, bata ce mashi ko kala ba saboda jiga jigan zakunan matasan mayakan dake tsaron gate ?in, saboda su yasa Mammien bata tanka masu ba ta wuce kawai. Ganin ta wuce bata ce masu ko sannu bane yasa shi ma ya juya ya bi bayanta, kuma har lokacin yana ri?e da hannun Chuchun.
Parking space suka nufa, bai bi Mammaien cikin gida ba, ya shiga motarsa kawai dan ya kai beb ?insa school, lokaci ya tafi sosai, ta kusa yin latti, su Fanan har sun tafi sun barta, sun nemeta dan su tafi tare, da suka san tana tare da shi sai suka tafi abinsu.
Wucewa da ita school ya yi, ita kuwa Mammie tana shigowa part ?in kai tsaye wajen Momma ta nufa. My people's duk yadda kuke tunnin makircin Mammie ya wuce tunaninku, lumbu lumbuce ita ?in, nunawa take yi babu wanda ya kaita son zaman lafiya, nunawa take yi tana kaunar Momma kamar ranta, ta manne da Momma kamar me, suna shiri, Allah sarki Momma bata san true colonta ba, bata san cewa ita ?in musa ce a zahiri fir'auna a ba?ini. Haka take nunawa Mummyn Gimbiya Chuchu ma kauna over, Maman Gimbiya Aneesa ce kawai basu shiri, basu ha?a inuwa da Mama, kamar wuta da audiga haka suke, kar ta san kar ne, dukkansu sarakan makirci ne, kun san idan fa kana aikata abu sai kaga kamar kowama aikatawa yake, hakan yasa basu zama inuwa ?aya, in dai suka ha?u sai aikawa juna ba?a?en maganganu da habaici game da harare harare suke yi, sukam sun fitar da kishin balbalin nasu a fili.
Kuma yadda kuka ga Mammie da iya makircin nan haka Gimbiya Sarina take, Fanan dai babu ruwanta, nutsatsiya ce, ba ruwanta da makirci da kirsa, amma Sarina kam ita ta sha nonan Mammaie ?in haikam, Mammaien na cire kafa ita kuma zata sanya nata kafan a munafurci da kirsa da kisisina ha?e da makirci, ?ar karama da ita amma idan ta ha?a maka wani makircin sai ka yi zaton macece yar shakaru 50 wadda ta ga jiya ta ga yau, ba'a banza ta zama master team ?in su Obaid and Omaid ba ai, iyashegensu ne kusan ?aya, sai dai su sunfita, amma akwai kamanceceniyar halayya da wasu dabi'u a tsakaninsu.
A parlourn ta isko Momma, kusa da ita ta zauna tare da sakar mata fuska kamar wata ta Allah, sannan ta ?aga mata gaisuwa.
Mommar ma duk da murmushi bai wani dameta ba, ba zaka ta?a ganin tana murmushi da wa?ansu ba sai da yaranta, su ne kawai suke ganin murmushinta sai King namu, amma ganin Mammie ?in ta sakar mata murmushi yasa ita ma ta ?an saki ?an siriri murmushi kafin ta amsa gaisuwar tata.
Cike da kwarewa a iya kirsa da makirci ta fara janta da hira, ba komai yasa take son jan Momma da hira kuma take yawan zuwa wajenta sannan ta nuna tana kaunarta over ba face dan san sanin wani sirrin Momman, gaba?aya matan gidan banda Mummyn Gimbiya Chuchu duk suna zargin Momma tana ?oye masu wani sirri tsawon shekaru, sun buga sun buga suna son sanin gaskiya, amma da yake ita bata ma san suna yi ba, kuma da zuciya ?aya take zaune da su, shiyasa Allah bai basu ikon sanin komai a kan hakan ba. Wannan dalilin yasa ita Mommar da Mama basu shiri ko ka?an, dan mama tana zargin tabbas akwai abin da Momma ta ?oye masu a tsakaninta da King.
Sosai Mammie ta zage tana ta janta da hira, Momma fa bata da yawan magana wlh, amma nacin Mammie take sawa ta rin?a ?an tayata hirar jefi jefi. Ba komai yasa bata da yawan magana ba face fa?ar da mahaifiyarta take yawan yi mata a kan kada ta bari kowa ya san sirrinta, kishiya fa ba'a bar bawa yarda gaba?aya bace, shi ne yasa bata sakewa ta saki baki tana magana, in kunji tana hira sosai to da yaranta ne ko kuma da masoyinta King.
Mommar izuwa yanzu ta fara mamaki a kan yanayin hiran Mammie a duk lokacin da ta zo in da take, a duk lokacin da ta zo bata da hira da ya wuce na shekarun baya, ba zata ta?a yi mata hira kan abubuwan yanzu ba, sai dai ta yi ta ka?ale ka?alen abubuwan da suka su?e. A gaskiya da can baya an yi wani irin zama a cikin family part ?in nan, ba ?aramin fa?a aka yi ba, Momma ta sha bakar wahala a gidan fiye da tunaninku, bata shiri da kowa, kusan haukatata aka yi a cikin gidan, akwai lokacin da har ya zamana tana zaune ita ka?ai tana magana, wani lokaci sai ta yi ta buga kanta a bango har sai ya fashe ya yi ta jini, wani lokaci kuma ta yi ta faman kuka babu gaira babu dalili, abubuwa dai kala kala, to babban abin da yake damun Mammie har ita da Mama suke zargin akwai abin da Mommar ta ?oye masu shi ne lafiya da ta samu sosai, yadda take gudanar da rayuwarta yanzu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, abin ya basu mamaki, suna son sanin ya aka yi hakan ta faru?.
Haka dai Mommar ta cigaba da biye mata suna hira sama sama, ita kuma Aliyah tana wajen Mummyn Gimbiya Chuchu, sai hira suke yi kamar kawaye, Allah sarki Mummy fa bata san mijinsu Aliyah take hari ba. Mama kuwa sai yanzu jikinta ya fara ?an rage ra?a?in da take ji na azabtarwan su Omaid da suka yi mata.
After some hours.
Da misalin karfe ?aya na dare, shirye take cikin wasu irin ba?a?en kaya, doguwar riga ce tana ja a ?asa, sai ta ?aura bakar alkyabbarta a saman kayan, shi ma alkyabbar yana jan ?asa, cikin wani irin tafiya wadda takun sahu baya bayyana ta fito daga cikin ?akinta. Ta kofar baya ta fita daga part ?in nasu.
Tafiya ta fara yi cikin taku kamar na marasa gaskiya ta mi?i wata hanya mai tsawo. Ta ?an yi tafiya mai ?an nisa ka?an, duk in da ta zo giftawa idan ta kalli warriors a wajen sai ta la?e, da yake warriors ?in suna kai komone a cikin masarautar sai ya zamana idan sun wuce sai ta fito ta cigaba da tafiya.
Wani irin canza kala idanunta ya yi izuwa red color sosai lokacin da ta kusa isa bakin babban gate na farko na masarautar. Bakin gate ?in shake yake da manya manyan zakunan warriors a wajen, jiga jigai masu ji da karfi ranon commander Zafar, a tsaye suke kamar wa?an da aka sassa?a. Ta gabansu ta zo ta wuce amma basu sami damar iya ganinta ba, canza taku ta yi izuwa takun ?asaita lokacin da ta zo giftawa ta gabansu. Wucewa ta yi kai tsaye ta nufi waje. Tana fita wajen gate ?in kuma ta ?ace ?at, babu ko alamarta...............
To fah, dama ta kira waya ?azun ta ce karfe ?ayan dare su ha?u a in da suka saba ha?uwa, ko da waye zasu ha?u? Me zai yi mata? Dama ita matsafiya ce? ?ar surkulle ne ita kenan?. Ku ?an lalla?a da wannan page ?in kafin mu fara yin long pages.????
??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????
????RAWANIN ?? ZALINCI ????
????????????????
FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????
?????????? 16/9/2024.....??????
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????
??STEP TWO....??????
E__________________2??
??????????????????????????????????????
FOREST?????
Tafiya yake yana layi ba tare da ya san in da ya dosa ba, burinsa kawai ya ganta, ita ce a cikin tunaninsa.
Cigaba da zuba jini ya rin?a yi a duk wata kafa da wannan damisar ta yakushesa. A hankali hankali ya fara ganin dajin na juya mashi, idanunsa na ?o?arin rufewa ruf, sai ?o?arin bu?esu yake yi, amma abin ya ci tura, domin already duk wata ga?a a jikinsa ta yi la'asar, duk wata karfi ta kare mashi a yanzu.
Har ya iso bakin wata rami mai kama da karamin rafi, cike ramin take tab da ruwa, kasancewar baya iya gani sosai sai bai kalli rafin ba, cigaba da saka ?afafunsa kawai yake yi yana tafiya ba tare da yasan in da yake takawa ba, shi dai Pretty kawai yake tunanu.
Wani irin jiri da ta ?ebesa ne ya tafi luuuu zai kifa gaba?ayansa a cikin wannan ramin.
Kamar walkiya haka mutun ya bayyana a gabansa tare da tareshi ya fa?a saman kirjinsa. Kamar dai kullum, fuskarsa na sanye da wannan rawani da yake rufe fuska, iya kan idanunsa irin na Pretty kawai zaka iya gani.
A lokacin kuwa idanun Kamran ?in sun gama rufewa, baya iya ganin kowa kuma baya gane komai, bai dai suma ba kam.
A saman shoulder ?insa wannan jarumin sadaukin ya sa?a shi, sannan ya nufi wata hanya da shi, tafiya yake cikin nuna tsantsar jarumta, daga ganinsa kasan dakakken namiji ne mai ji da lafiya.
Saman wasu ganyayyaki ya kwantar da Kamran ?in bayan sun yi tafiya mai ?an nisa, da alama shi ya shirya ganyayyakin. Hannu yasa ya ?arisa yage rigar jikin Kamran ?in, dama already damisar ta ?an yayyageta, so sai ya ?arisar da yageta kawai.
Wasu kwarya dake gefe guda ya bu?e ?aya, cikin zafi zafi yake aiki, da alama jininsa a tafashe yake, kwayar idanunsa duk in ya lumshe ido ya sake bu?ewa sai sun tafi da imanin mutun, saboda kyansu, sak idanun Pretty and Sweetie, ga idanun nasa shi ma dara dara.
Maganin launin green color ne a cikin kwaryar, duk wani waje da wannan damisa ta fasa a jikin Kamran sai da ya bi ya zuba mashi wannan maganin. Cikin ?an?anin lokaci Kamran ya fara dawowa cikin hayyacinsa, da alama maganin aiki yake yi kamar magic.
Mi?ewa ya yi daga wajen ya nufi wajen wata bishiya dake gabansu ya tsaya a wajen bayan ya mayar da kwaryar gefe ya ajiye.
Shi kuwa Kamran a hankali idanunsa suka fara washewa, da alama ya dawo cikin hankalinsa. ?an dishi dishi ya fara ganin mutumin, da yake a ta gaban ganinsa mutumin ya tsaya, sai kara waro wa?an nan manyan idanun nasa yake yi yana son ganin wanene? Amma ganinsa bata gama washewa ba, dishi dishi yake gani.
Mutumin ya juya mashi baya, iya bayansa kawai yake iya gani. Jin alamar Kamran ?in ya fara dawowa dai'dai ne yasa ba tare da ya juyo ba, in a low voice sosai ya furta. "Where's Nufaysat?" Ha?i?a yana da sanyin murya tamkar Sweetie ce ta yi magana, kun san dama ita tana da sanyin muryar, Pretty ce mai zazzakar murya kamar busar sarewa, amma Sweetie ko ?aga murya ta yi sai kun ji shi a sanyaye, saboda sanyinta, ga da?in saurare, dukkansu ita da Pretty voice nasu akwai da?in saurare sosai, sai ma idan suna karatun Alkur'ani mai girma.
Mamaki ne ya kama Kamran ?in, dan shi bai san su waye Nufaysat ba, kuma ya ji voice ?in mutumin tamkar na Sweetie, sai abin ya ?aure mashi kai. A hankali ya fara ?o?arin motsa la??ansa alamar yana son ya yi magana, sai dai kuma tongue ?insa ya yi mashi mugun nauyi, ya kasa iya motsa ta.
Still wannan mutu bai juyo ba, jiran amsa kawai yake yi a kan ina su Nufaysat?. Kamran kuma baki ya kasa bu?uwa, saboda azaban da ya sha a hannun bakar damisar nan, duk ya jigata.
Motsin da suka ji alamar mutun ya tinkaro in da suke ?in ne yasa wannan sadaukin ya bar wajen a ?ari, da alama ?oye kansa yake yi ga kowa.
Yana barin wajen Mamma ta iso wajen cikin zafinta, tana tafiya kamar wata jarumar mayakiya, gefen face ?inta yana ?an zubar da jini, alamar damisar ta ji mata ciwo a wajen, ta biyo sahun ?an ta ne.
Dai'dai lokacin da ta iso wajen, a dai'dai lokacin shi kuma Kamran ?in ganinsa ya gama washewa, ?o?arin mi?ewa ya fara yi, amma sai ya kasa, kamar wadda aka ?a??aurewa ga??an jiki.
Da sauri mamman ta ?ariso wajen nasa, a gabansa ta tsugunna tare da kura mashi idanu tana ganin maganin da Sadauki ya sanya mashi.
"Kamran who did all this thing to you?". Ta fa?a tana kara zaro idanu. Girgiza mata kai ya yi tare da cewa. "I don't know him".
Sosai take ganin maganin, a matsayinta na babbar likitar gargajiya bata ta?a ganin irin wannan magani ba, bata san wani ganye bane, ga shi babu halin ta sani, saboda ganyen an murjeta sosai, so ba zata iya ganewa ba. Yau tsawon shekaru 25 zuwa 26 tana wannan aiki na likita, amma bata ta?a sanin irin wannan magani ba.
Yau a karo na farko ta shiga cikin mamaki sosai, hannu ta kai ta ?auki wannan kwaryar, zubawa maganin idanu ta yi tana mamaki sosai, yau dai an samu wani abin da ya bata mamaki a wannan dajin.
Dawo da idanunta a kan shi ta yi. "Kamran tell me who treat you? Who help you?".
Sake girgiza mata kai ya yi tare da ce mata bai sani ba shi ma. Mi?ewa tsaye ta yi da kwaryar a hannunta, tafiya da shi zata yi ya je ta yi bincike a kan wani irin ganye ne wannan.
Hannu ta mi?a mashi a kan ya ri?e ya mi?e tsaye su tafi. Kasa iya mi?ewar ya yi duk da ya ri?e hannun nata, hakan yasa ta ajiye kwaryar tare da du?awa kamar ?an baby ta sa?e shi sai saman shoulder ?inta, sannan ta ?auki kwaryar maganin ta nufi hanyar komawa...... Kai Mamma ba dai karfi ba kam, kakkarfan macece sosai.
Suna tsaka da tafiya ya ce. "Mamamma take me down zan iya tafiya yanzu". Ba musu ta sauke shi, dan ya ?an ji kwari.
"Mamma ki je zan zo in sameki". Ya fa?a tare da gyara tsayuwansa. Kallon tuhuma ta wurga mashi kafin ta ?aure fuska sosai. "Ina zaka je?".
Kai tsaye ya ce mata. "Neman Pretty zan je, ban san in da ta nufa ba, kuma kin san dajin nan yana da ha?ari sosai, kada ta je ta fa?a wani wajen mugayen dabbobi su cutar mun da ita, gaskiya ba zan iya zama ba". Bawan Allah ita ce ka?ai a cikin tunaninsa, dan yana ganin kamar Sweetie tana mazauninsu, dan a tunaninsa ai ita bata fita, kuma haka ne, da ni da ku duk mun san bata fita, so ya yi tunanin Pretty ce kawai ta fito damisar ta ritsata, shiyasa baya zancen Sweetien.
"Who's she?!". Ta fa?a murya a kausashe. "My pleasure". Ya bata amsa cikin halin ko in kula, ba wani damuwa a tattare da shi. Da alama fa Kamran hankalinsa baya jikinsa, da alama ya manta cewa da Mamma yake magana.
Gyara tsayuwa da kyau ta yi, wani irin kallo da ta wurga mashi sai da tasa ya ha?iyi yawu da kyar, da alama kallon yasa ya dawo cikin hankalinsa. "Your pleasure?!". Ta maimaita kalmar cikin kausasshiyar murya.
Nan take ya ji harshensa ta yi mashi nauyi, sai a lokacin ya fahimci ya yi kuskuren su?utar baki, yanzu idan ta rabasu fa ya zai yi? Idan ya gano Pretty ta ce kada ya sake zuwa in da suke ko kuma ta koresu a dajin ko ta bi dare ta salwantar masu da rayuwarsu ya zai yi? Wannan tunanin yasa ya fahimci ya tabka babban kuskure a magana, yasan da cewa tsab Mamma zata iya bin dare ta kashesu, ba zuciyar imani ne da ita ba, amma duk da haka yana yi mata biyayya, shi kansa bai san meyasa yake yi mata biyayya sosai har haka, a yanayin renon da ta yi mashi bai kamata ma ace yana tsoronta ko yana yi mata biyayya har haka ba, duk da cewa e munsan ko fa?a zasu yi zata yi mashi dukan mutuwa, dan ba sa'arsa bace a fagen iya fa?a, ?ashinta ya rigada ya yi dahu da fa?a, amma biyayyar da yake yi mata har ta yi yawa, baya ta?a ja da maganarta, yanzu haka da ya kasance yana karatun Alqur'ani mai girma ma kullum kara kaunarta yake yi, dan yanzu yana kara sanin girma da darajar mahaifiya.
"Kamran amsa me a ina ka santa? Ashe kana da wata pleasure bayan ni?".
Shiru ya yi ya kasa yin magana. Tsawa ta daga mashi mai karfi a kan ya bu?i baki ya bata amsar da take tambayarsa a kai ko ransa ya ?aci.
Wani irin ra?a?i yake ji zuciyarsa take yi mashi, burinsa kawai ya je ya ceci Pretty, ya nemo in da take kada wani abin ya cutar da ita, amma mamma tana neman dakatar da shi, shi gaskiya a wannan ga?ar baya jin zai iya yi mata biyayya ya kyale ran Pretty ya salwanta.