Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 3

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 3

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 3: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 3. Saukar wani irin gigitattacen mari da ya ji a saman ?uncinsa ne yasa ya dawo…

3,366 words

Saukar wani irin gigitattacen mari da ya ji a saman ?uncinsa ne yasa ya dawo daga duniyar tunanin da ya afka. Nan take ya kai hannunsa ya dafe kumatun nasa tare da sauke kallonsa a kanta, tun da yake da ita ko da sukan wasa bata ta?a dukansa ba, wannan mari da ta yi mashi ya kara tabbatar mashi da abin da yake zargi na cewa bata da gaskiya ne yasa take ?oye rayuwarsu ga kowa, rashin gaskiya ya bayyana karara a tatare da ita, in dai kuwa haka ne yau sai ta gaya mashi wanenen shi wanene babansa? Wani ?angare na zuciyarsa ce ta amsa mashi da yes kada ya yarda sai ta gaya mashi wanenen shi?.

Cikowa tab idanunsa suka yi da kwallah saboda zafin marin da ta dalla mashi, marinta ba wasa ba, akwai tsananin zafi. Da yake fatarsa akwai haske hakan yasa shatin yatsunta biyar da Allah ya bata suka fito ?aro ?aro a saman face ?in nasa. Wani irin ra?a?i zuciyarsa take yi mashi, ji yake tamkar an ?aurata a saman wuta. Dannewa ya yi tare da furta.

"Mamma please ki barni na je na cece rayuwarta, idan ta mutu me zan cewa ?ar uwarta Sweetie? Idan mum ?insu ta bayyana ta tambayeni amanar da ta bani me zan ce mata? Ni kai'na nasan idan ta mutu nima ba zan rayu ba, in dai kina sona da gaske to ki barni na je na nemota!". Yana kai karshen maganar wasu siraran hawaye suka fara ganganrowa a saman ?uncinsa, ba kukan marin da ta yi mashi yake yi ba, kukan rashin Pretty ya fara yi, idan mamma bata barshi ba da alama zai iya mutuwa, da alama Pretty ce rauninsa dan ga shi duk jarumtarsa yau a kanta yana kuka!.

"Kamran ba in da zaka je, kenan dama kullum wajensu kake zuwa? Who're they? Har amanarsu kenan aka baka? A ina kasan amana? Who told you this word?".

"Mamma ki bari idan na je na nemota na dawo sai mu yi magana, please kada mu tsaya magana a yanzu ta yi mun nisan da ba zan iya ganeta ba, duk wani lokaci da zamu ?ata a nan ki sani rayuwar Pretty ce taka cikin ha?ari, kin fa san yadda Forest ?in nan yake, please mamma........."

Tsawar da ta daka mashi a kan babu in da zai je ne yasa ya ha?iye sauran maganar dake bakinsa bai amayar ba.

"Kamran kamar yadda na gaya maka tun farko babu kai babu mutane to hakance har yanzu, babu ruwanka da mutane, ko mutuwa mutun zai yi a gabanka ka tsallake ta kansa ka wuce, babu ruwanka da kowa, ni ka?ai ce kake da shi a duniya, haka kuma zamu cigaba da rayuwarmu, dan haka babu in da zaka je, ka wuce mu tafi!!". Cikin ?aka murya ta yi maganar, da alama ta fara hasala sosai.

"I can't go anywhere without seeing my Pretty! Mamma meyasa kike yin hakan? Kenan nima kina son idan wasu suka ganni ina bakin mutuwa su tsallekeni su wuce ba tare da sun taimaka mun ba?..........."

Katse shi ta yi da cewa. "Kai ba zaka mutu ba! Kai daban kake da mutane, babu wanda ya isa ya kasheka, ba mutun kake kamar sauran mutane ba, dan haka kamar yadda na ce babu in da zaka je to babu in da zaka je, ka wuce mu tafi, babu mutuwar da zaka yi da har mutane suki taimakonka!!". Yanzu ma a kausashe ta yi maganar, da alma ranta ya fara ?aci sosai.

"Mamma na gaya maki ni ba zan je ko'ina ba sai naga Pretty, amanatace, bazan ta?a bari rayuwarta ya salwanta ba, dan haka ki tafi kawai ni zanje nemanta, she's my wife my everything, mum ?insu ta bani aurenta, ita ce bugun numfashina, idan har kina son na cigaba da yin numfashi a duniya to ki barni na je na nemota kada ta yi mun nisa, please mamma ki fahimceni, nasan halinta sosai, yanzu haka tana can tana gudu tana kara afkawa cikin daji, kada ta je ta afaka wani wajen, please ki tausaya mana.....".

Katse shi ta sake yi da cewa. "Waye ya gaya maka aure? Waye ya baka wannan kalmar? Wanenen ya gaya maka me mata yake nufi? Yaushe kasan soyayya? Wani maci amanar ne ya gaya maka dukka wannan?". A karo na biyu mamaki ya bayyana a saman fuskarta.

Gyara tsayuwarsa ya yi, ido cikin ido ya kalleta, babu ko shakka, duk wasu shakkarta dake cikin kwayar idanunsa sun kau, cike da rashin tsoro ya furta. "Okey mamma daman kenan da gangan kika ?oye mun dukka wa?an nan abubuwa da kika tambayi waye ya gaya mun su? Kenan kin san komai kika reneni cikin duhun kai?! Sai kika koya mun ilimin da ba amfanata zai yi ba, wanda zai amfaneni kuma sai kika ?oye mun kika ki sanar da ni, to amma kin tabka babban kuskure da kika koya mun reading, na iya karatun da zan karanta storys, sannan kin yi kuskuren ajiye litattafai a ?akinki da har na gani na karanta, ni yanzu dukka bama wannan ba, ki gaya mun ina babana yake tun da kin san komai......."

Tashin hankali, wani irin zaro idanu ta yi, bata ta?a zaton abin zai kai masu haka ba, wani irin bugawa da zuciyarta ya yi ne yasa cikin hanzari ta dafe saitin kirjinta, kanta har juya mata yake yi jin ya ambaci ina babansa? Nan take ta ji jiri na ?o?arin ?ibarta.

"Ki bani amsata! Where's my father? Yau ina son sanin wanene ni?!".

"Kamran ni kake yi wa magana haka?". Babu ko shakka ya gya?a mata kai. "Yes Mamma ke nake yi wa magana haka, kawai amsa my questions...."

Wani irin zufa ne ya fara tsastsafo mata a gefe da gefen face ?inta, ji ta yi duniya ya yi mata zafi, nadamar hanashi tafiya neman Prettyn da ta yi ta fara yi, yanzu ga shi allura tana ?o?arin tono mata garma.

"Kamran baka da wani baba sai ni, ni ce ka?ai kake da shi, dan haka kada ka sake yin magana a kan hakan......"

"Mamma i knew everything now! Mace bata ta?a haihuwa ita ka?ai! Dole sai da namiji! Dan haka tell me where's my father?!".

Shiru ta yi ta kasa iya sake bu?e baki, ta rasa me zata ce da shi.

"Mamma ki bani amsar ina babana!!......". Ya fa?a da karfi.

Katse shi ta yi cikin ?aga murya. "Idan ka sake magana a kan babanka zaka mutu, zaka mutu Kamran....."

?an zaro idanu ya yi yana kallon yadda ta yi maganar cikin tsarguwa da alamun rashin gaskiya ya bayyana sosai a tattare da ita.

"Mamma koma me zai faru ni dai ki gaya mun ina babana? Wanenen ni? Ina familyna suke! Yanzu duk nasan komai".

"Kamran wai wani maci amanan ne ya gaya maka dukka wannan? Wani azzalumi ne yake son raba uwa da ?anta?! Wani bakin mugu ne wannan?! Waye ya ce maka kana da baba? Waye ya koya maka wannan karatun?! Ka gaya mun shi!". Cikin tsawa ta yi maganar.

"Mamma ni kawai ki fa?a mun ina babana? Idan kika fa?a mun zan fa?a maki daga baya sai ki yi duk tambayar da zaki yi, yanzu dai ina babana? Wanenen ni".

To fa yanzu an bar maganar zuwa neman Pretty ma, abu ya ?au zafi kenan, mamma ta tonawa kanta bala'in da yake ?o?arin fin karfinta, saboda kafiya da kafurar zuciya irin tata ga shi yanzu ta ja wa kanta yaronta na cikinta yana jayayya da ita, abin da bai ta?a yi ba, bata ta?a yin magana ya tsaya yana mayar mata da martani ba sai yau, yau ?in ma ya tsaya yana kallon cikin kwayar idanunta yana fa?a mata magana dai'dai gwargwado, Hasbunallahu wani'imal wakil, duk abin da ya faru ita ta jawa kanta, ai yaro ba'a yi mashi kafiya irin haka, barema shi da ya girma har haka? Ai yama yi kokarin na danne son sanin wanenen babansa da ya yi na tsawon lokaci, kowani ?a zai so ace ga babansa a tare da shi suna zane cikin farinciki, amma saboda biyayya da kaunarta da yake yi yasa ya danne bai bu?aci lallai sai ta fa?a mashi in da baban nasa yake ba, ya hakura ga shi yanzu ta ja yana fito na fito da ita a kan hakan.

Wani irin yawun wahala ta ha?iye, ji take ma?ogoronta ya yi wani irin bushewa da jin tambayoyin ?an nata, yawun bakinta ya kafe kamar mai yin azumi, da kyar take iya kakalan yawun ta ha?iye, da kyar ma yake wuce ma?ogoronta, ji take ma?ogoron nata kamar an toshe mata shi ne.

"Kamran idan ka sake magana a kan babanka zaka mutu nace maka, mutuwa kuma mafi muni a rayuwa, kamar yadda ka taso baka san kowa ba, sai ni, to haka zaka ri?e ka manta da duk wasu tunanin banza".

"But Mamma why? I want to know my father ko da kuwa hakan ce zata zama sanadiyar numfashina na karshe, just tell me where's he? Ni zan je in da yake koda kuwa ya fi wuta zafi dole na tinkaresa!! Na kusancesa!!".

Tsawa ta daka mashi mai sauti, cikin fusata, idanunta sun ka?a sun yi jajir, jijiyon kanta har wani mimmikewa suka yi, da alama ranta ya kai kololuwa wajen ?aci, har wani huci take yi kamar zakanya. "Kamran ina gaya ma zaka yi mutuwar wala?anci in dai ka sake yin magana a kan babanka! Kai ba mutun ne kamar kowa ba! Kai ba kamar sauran mutane kake ba! Kai na daban ne, farautarka ake yi kamar yadda ake karautar ruwa a sahara mai tsananin zafin rana! Zaka mutu idan ka fita! Zaka! Dan haka ka tsaya a in da na tsayar da kai!!".

"Mamma i can't! I can't gaskiya! Idan kuma kina son na bi maganarki so tell me who I am?! Where's my father and my family?! Why are you hiding our life anytime?! Am tired! Am tired Mamma! I want to see my father and my family, cos I can't stay with you again! Tafiya zan yi na nemo babana and Prettyta even wannan shi ne ganina dake ta karshe!"......... Tashin hankali.

??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????

????RAWANIN ?? ZALINCI ????

????????????????

FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????

?????????? 16/9/2024.....??????

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????

??STEP TWO....??????

E__________________3??

Wani irin gigitacen mari ta sake dallah mashi wanda ya sanya shi yin tangal tangal kamar zai fa?i ?asa. Cikin ?unar rai ta ce. "Babu in da zaka je! Daga yau idan ka sake yi mun magana a kan babanka ko wasu banzaye can tsinannun da suka kur?ata maka tunani sai ran?a ya ?aci fiye da tunaninka, ni ka?ai kake da shi a duniya, dan haka ka goge komai dake cikin ranka, daga yau ma ba zaka sake fita ko nan da can ba..." Ta kai karshen maganar cikin tsananin ?acin rai tana furzar da huci mai zafi, tana kai karshen maganar kuma ta finciki hannunsa da karfin tsiya har sai da ya furta wash da karfi.

Cikin fusata ta jashi da karfin gaske suka kama hanya, azaban zafin jikinsa yake ji saboda fincikarsa da ta yi da karfi, ciwon da damisar ta ji mashi wajen duk yana yi mashi ra?a?i, amma haka ta cigaba da fincikarsa har suka isa gida.

Zuciyarsa tafasa take yi mashi, gaba?aya ga??an jikinsa yana yi mashi ciwo. Wani ?angare na zuciyarsa tana gaya mashi ya tirge yaki binta, ya bijirewa maganarta kawai ya gudu ya tafi neman Pretty da babansa amma kafin nan ya fara zuwa ya duba lafiyar Sweetien da yake tunani tana cikin ramin can.

?ayan ?angare na zuciyar tasa kuma tana ?ara gaya mashi girman uwa, tuna mashi da irin fafutuka da famar da Mammar ta yi a kansa take yi, tunawa ya rin?a yi da yadda ta sha wahala a kansa, ta sadaukar da komai nata dan shi, har rayuwarta ta sha sanyawa a ha?ari dan ta ceci tasa rayuwar, a yanzu idan ya bijire mata sam bai yi mata adalci ba, a yadda kuma yake karatun Alkur'ani yake karanta fassararta da English yasan cewa in dai ya yi wa Mamarsa haka Allah ba zai barshi ba, uwa ta wuci wasa. Amma kuma yana son sanin babansa, yana son sanin ?an uwansa, zuciya bata da kashi, ba zai iya hakura bai je ga su Pretty ba, ba zai iya hakura bai nemo in da take ba.

Wasu irin zafafan hawaye ne suke bin ?uncinsa, a tunanin mammar saboda marin da ta yi mashi ne yasa yake wannan kukan, bata san cewa shi ko zata ?aure shi ta kwana tana dukansa in dai zai rayu da safe ta rabu da shi ya je ga Pretty da babansa zai yarda da hakan ba, sam bai ma ji zafin marin da ta yi mashi ba, azaban zafin dake cikin zuciyarsa ta take zafin marinta. Ra?a?i zuciyarsa take yi mashi, ya rasa mafita.

Haka ta cigaba da jansa har izuwa cikin ?akinsa. Da karfi ta turashi ya fa?a saman gadonsa, da alama ta manta da cewa yana da ciwo a jikinsa, ?acin rai ya rufe mata idanu bata ganin komai face ta san yadda zata yi ta hana shi ko le?a waje......... Lalla Mamma ta ?ebo da zafi, da karfi da ya ji zata raba soyayyar da Allah ya ha?a, Allah ne ya sanyawa Kamran kaunar Pretty, ba dan komai yake sonta ba face dan Allah, shi kansa ko kashe shi zaka yi ka tambayi meyasa yake sonta sai dai ka kashe shi, dan ba zai baka dalili ko guda ?aya ba, saboda tun ranar da ta fa?o duniya, ko cibiya ba'a yanke mata ba, a haka yana ?aura idanunsa a kanta zuciyarsa ta kamu da kaunarta, a wannan lokaci me zai so? Shiyasa nace maku ba dan komai yake sonta ba face dan Allah, son da yake yi mata kaddararsa ce, a tare aka haifesu da Sweetie, meyasa bai ta?a jin son Sweetien ba sai Prettyn? Dame tafi Sweetie? Babu abin da ta fita da shi, amma a haka zuciyarsa ta kafe Pretty take so while ita kuma Sweetie tana sonsa, son yaya da kanwa kawai yake yi wa Sweetie, Pretty ce kaddararsa, ita farincikinsa, sau ?aya ya ganta ranar da aka haifeta, a ranar ya ?auketa da hannunsa, ya ceci rayuwarta, tun daga lokacin kuma sai da ya shafe shekaru goma bai sake ganinta ba, amma dai'dai da rana ?aya bai ta?a mantawa da ita ba, kullum tana cikin tunaninsa, a tsawon wa?an nan shekaru da suka yi basu tare kullum yana cikin ?unci da damuwar rashinta, ya zo ya ganta sun sake sabo, har soyayyarta mai zafi fin na baya ya kara shigansa, sun saba, ita ma tana son kasancewa a tare da shi kullum, rana tsaka kawai mamma ta rabasu? Ta ce kada ya sake fita ma bare ya nemosu? Yanzu bashi da tabbacin suna mazauninsu ko basa nan? Bai san ina takamaimai suke ba, wannan abin da ta?a zuciya, anya zai yarda da hakan kuwa? Ku dai kun san yadda yake jin sonta a ransa.

Cusa kansa ya yi cikin katifar tasa, wani irin kukan zuciya yake yi mai tsuma rai, har wani irin shessheka yake yi kamar wanda ake zarewa rai, ji yake yi kamar zai iya ha?iyar zuciya ya mutu, gaba?aya zufa ta wanke mashi jiki.

Ko ka?an a wannan lokaci mamma bata ji tausayinsa ba, ta ?auka soyayyar wasa yake yi wa Pretty, dan tana ganin kamar bai san menene so ba, ta ?auka ha?uwar yau ce kawai ko na ?an kwanaki, bata san sun jima a tare ba tare da saninta ba, batasan soyayyar bata wasa bace, sannan bata yanzu bane, soyayya ce da ta faro tun ranar da aka haifeta, rashin sanin daraja da mutuncin soyayya yasa sam bai bata tausayi ba. Da alama zuciyar mamma ya rigada ya bushe, ta kekashe bata jin tausayin komai da kowa, har shi kansa ?an nata bata tausaya mashi, ashe ba'a banza take bashi irin horon da take bashi ?in nan ba, babu tausayi a ranta yasa komai magiyar da zai yi mata a kan ya gaji ta bari ya huta, amma bata ?aga mashi kafa har sai ya cike lokacin da ta ?eba mashi, bawan Allah.

Tana jin irin kukan da yake yi mai tsananin ratsa zuciya, amma ta yi burus da shi tasa kai ta fice daga ?akin. Kai tsaye waje ta nufa domin ta samo igiya irin na jijiyar itace mai karfi ta ?aure shi, dan ta ci alwashin ba zai sake fita waje ba bare ya je gurin wa?ansu har su sake kur?ata mashi tunani.

Kukansa ya cigaba da yi yana addu'ar Allah yasa ya mutuma kawai ya huta, dan zuciyarsa ba zata iya jure rashin Pretty ba, ga tunanin Sweetie da yake a ?ayan ?angaren zuciyar tasa, yana tunanin makantar nan nata, yanzu idan Pretty ta ?ata ita kuma ya zata yi? Yasan da wuya Pretty ta iya dawo da kanta cikin wannan ramin nasu, dan hanyar da ta bi ma sam sam bashi da ha?i da in da suke, dajin nan yana da girma kuma yana da ha?ari, akwai namun dawa sosai a cikinsa, da wuya Pretty ta iya kai labari, da wuya ta rayu in dai ta cigaba da tafiya a kan wannan hanya da take, tunani yake ya Sweetie zata rayuwa ba mai yi mata jagoranci zuwa in da take da bu?ata kamar yadda Pretty take yi mata?. Addu'a yake yi Allah yasa wannan sadaukin ya ha?u da Prettyn ko kuma ta ha?u da mai tamakonta.

Tun yana iya kuka mai sauti har sautin ta dai'na fita, ban da ruwan hawaye babu abin da yake fita daga idanunsa. Babban damuwansa ma amanarsu aka bashi, bai ri?e amana ba, ya karya yardan da aka yi mashi, idan ya tuna da hakan sai kara rushewa da kuka, yarda da shi yasa mum twins ta bar sakon ta bashi amanarsu, ta san zai iya ri?esu ne yasa ta bashi, amma ga shi yanzu mamma tasa ya kasa cika amanar da ya kar?a.

Saboda tsananin sabo da yake a tsakaninsa da Rocky ne yasa Rockyn ya zo bakin kofar ?ogon yana ta zuba masu kurnani, da alama yana jin kamar Kamran ?in bashi da lafiya ko wani abin makamancin haka, kun san fa ita dabba idan ka yi sabo sosai da ita sai ku zama kamar twins, bare shi da a gabansa aka haifi Kamran ?in, tun Kamran yana jariri suke tare, ai dole ma ya ji hakan a jikinsa.

Ko da Mamma ta dawo hannunta a ?auke da igiyoyi masu karfin gaske, a bakin kofa ta isko Rocky, kun san ba zai iya shiga ciki ba. Yana ganinta ya nufeta yana gurnani. Sarai ta san me yake yi wa, amma sai ta yi kamar bata sani ba, ta sharesa zata wuce.

Tsalle ya fara yi yana kama jikinta alamar baya son ta tafi. Sam taki yarda ta bi ta kansa, sai ma ture shi da ta yi ?o?arin yi ta wuce, hakan yasa ya yi tsalle sosai zai capketa, da sauri ta wuce ciki ta barsa.

Ai kuwa da karfinsa da Allah ya basa ya fara ?o?arin lallai sai ya bita cikin wannan kogon yau, sai dai ina, kogon dutsene mai karfin gaske, wane shi ya iya fasata ya shiga, haka ya rin?a gurnani yana tsalle ya bugi jikin kogon har ya jiwa kansa ciwo.

Har cikin ransa Kamran ?in ya ji zafin wannan ciwo da Rocky ya ji, haka kawai ya ji zuciyarsa ta tsananta zafin da take yi mashi, hakan yasa ya fahimci lallai wani abin yana faruwa da wanda yake kauna, so sai ya ?aura zarginsa a kan Pretty, ya yi tunani ko itace wani abin yake faruwa da ita, sam bai kawowa ransa Rocky ne ya ji ciwo ba, dan baya tunanin akwai wanda zai zalinci Rocky ko ya yi mashi wani abin a wannan dajin, shiyasa sam bai kawowa ransa shi ?in bane.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull