Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 4

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 4

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 4: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 4. Da gaske babu tausayawa Mamma ta ha?a kafafunsa dukka biyu ta ?aure yana daga…

3,320 words

Da gaske babu tausayawa Mamma ta ha?a kafafunsa dukka biyu ta ?aure yana daga kwance. Yana jin duk abin da take yi mashi, amma ko kwakkwaran motsi bai yi ba bare a sa ran zai tirje mata, shiru ya kwanta yana cigaba da kukan zucinsa, irin wannan kuka babbar ha?ari ce kuma babban barazana ce ga lafiyar ?an Adam, tana ta?a zuciya, kuma tabbas mamma ta san da haka, amma gudun kada ya fita ya ce zai tafi neman babansa yasa ta danne duk wani zafin da take ji a zuciyarta na kukan da yake yi ta ?aure shi hannu da kafa. Ko ka?an bata yi ?o?arin rarrashinsa ba, saboda tana ganin kamar idan aka kwana biyu haka shikenan zai sauko ya hakura da komai ya kuma manta komai su koma kamar da, wannan dalilin yasa bata yi ?o?arin rarrashinsa ba.

Allah sarki rayuwa kenan, wa?an nan bayin Allah ya suke ji a cikin ransu?. Sweetie da Pretty da suka kwanta ciki ?aya, aka haifesu tare, suka sha nono tare, basu ta?a rabuwa da juna kona wuni ?aya ba, koda yaushe suna tare, suna kaunar junansu fiye da tunaninku, basu da kowa sai junansu, rana tsaka aka rabasu, ko ya Pretty take? Ta mutu ko tana da rai? Ina Sweetie?. Shi Kamran da ya zo ya samesu a tare ma ya ji zafin rabuwa da su har haka bare kuma su da suke tamkar chewing gum da gashi, hanta da jini, kun san idan chewing gum ya manne gashi baya saki gaba?aya, haka zalika hanta bata rabuwa da jini, to haka Sweetie da Pretty suke. Fatana dai Allah yasa suna da rabon sake ganin juna, Allah ya ha?a fuskokinsu.

??????????????????????????????????????

KINGDOM OF POWER ??????

1:30 Am. Karfe ?aya da rabi na dare. Kwance Gimbiya Chuchu take a saman gadonta bayan ta kammala wayar da take yi da Rizwan, har 12:30 suka kai suna waya, sai zuba mata kalaman soyayya yake yi, yana ta kara sanya zuciyar baiwar Allah tana narkewa a sonsa, yau Yah Jawad bai zo in da take ba sam sam, da alama akwai abin da ya ri?esa, tun safe da ya kaita school sai kuma da daddare da suka ha?u a dining room ya rin?a tsokanarta ta ?asan table kamar ranar har sai da ta kusa saka mashi kuka sannan ya rabu da ita ta ci abinci. To tun lokacin ba su sake ha?uwa ba, tana kewarsa sosai da sosai.

Barci na ?o?arin ?aukarta sai ji ta yi an turo kofar ?akin nata. A hanzarce ta juyo da kallonta izuwa kofar ?akin nata. Sanye yake da single fara tas, sai short da bata wuci zuwa tsakiyar cinyarsa ba, gashin kansa a hargitse sosai, kamar wanda ya taso daga barci ko kuma wanda ya fito daga gidan mahaukata ko dai wanda aka yi wa kirso aka warware ba'a taje an gyara ba.

Zaro idanu ta yi tana kallonsa da mamaki ta kasa yin magana, ita dai tasan wlh Yah Jawad baya yin irin wannan dressing ?in ya fita haka, ko part ?insa suka je idan babu full kaya a jikinsa baya basu izinin shiga room ?insa har sai ya zura jallabiya a jikinsa, amma yau sai ga shi tsakar dare da irin wannan shiga, ga kansa kamar bayan bushiya, duk ya wargaje gashin, yanayinsa ma kamar wanda ya yi tatul da giya, dan har wani layi layi yake kamar zai fa?i.

Zabura ta yi ta mi?e zaune tare da fa?in. "Yah Jawad lafiya? Meyasa baka yi barci ba?".

Wani irin mayen kallo yake binta da shi wadda bata ta?a ganin ko da sunan wasa ya yi mata irinsa ba. Haka kawai ta ji wani irin tsoronsa ya dira mata. Kallonta yake yi kamar zai cinyeta ?anya.

Ta yi magana almost baki biyar, amma yaki tanka mata, murje idanunta ta fara yi domin ta tabbatar bafa mafarki take yi ba. Duk murje idanun da zata yi tana cire hannu sai ta ganshi a tsaye yana dai cigaba da binta da wannan mayen kallon.

Dallawa kanta mari ta yi duk dan ta farkar da kanta daga barcin da take yi a tunaninta, dan ta kasa yarda cewa zahiri take gani. Ko da ta mari kan nata ma still dai shi ?in ne a tsaye da gaske ba mafarki ba. Kamar wani tsohon maye ya fito da harshe ya ?an lashi red lips ?insa yana binta da mayen kallo. ?ara tsorata ta yi da ganin hakan.

Ai bata san lokacin da ta diro ?asa daga saman gadon ba, duk ta ru?e, jikinta nan take ya fara kermar tsoro, hankali a tashe ta nufi in da yake, a cewarta zata fice daga ?akin ta bashi waje, dan kada ya yi mata wani abin duk da cewa har yanzu ta kasa yarda cewa ba mafarki take yi ba.

Tana zuwa kusa da shi da nufin ta ra?a gefensa ta wuce, sai zuba sauri take yi jiki na kerma. Da hannu ?aya ya fisgota ta fa?a saman kirjinsa.

Tsoro ne ya kara kamata, zuciyarta na dukan uku uku kamar zai fasa kirjin nata, jiki sai kerma yake yi. Murya na rawa ta ce. "Yah Jawad wajen Momma zan je".

Kara matseta ya yi a jikinsa. Da jin haka sai ta fara ?o?arin kwatar kanta, da karfi ya ?an?ameta kamar zai ?allata. ?o?arin kwala ihu ta yi, toshe mata baki ya yi da karfi yana ?o?arin cire mata kayan jikinta.

Izuwa yanzu gaba?aya tsoro ya gama dabaybayeta, karfi tasa tana ?o?arin kwatar kanta. Ai kuwa haka ya ha?e hannayenta dukka biyu ya ri?e da hannunsa ?aya, ya matse mata baki da ?ayan hannunsa, haka ya jata izuwa saman gadonta, tirgewa take yi a kan ita ba zata hau gadon ba, sakin hannayen nata ya yi da nufin ya ?agata cak ya wurga a gadon.

Ai kuwa yana sakinta ta samu hanya ta watsa a guje zata fita. Da gudu ya bi bayanta ya damkota, wage baki ta yi zata kurma ihu, a ?ari ya kai.............

Ko me ya shiga kan Yah Jawad yau kuma? Anya lafiya yake kuwa? Fya?e yake ?o?arin yi mata kenan? Meya fito da shi karfe ?aya na dare? Anya bai sha wata kwayar ba?. (To ni dai na ce su twin's Obaid and Omaid basa nan bare na ce ya yi masu ba dai'dai ba sun yi mashi wata tsiyar da suka saba??)

??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????

????RAWANIN ?? ZALINCI ????

????????????????

FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????

?????????? 17/9/2024.....??????

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????

??STEP TWO....??????

E_________________4

Ai kuwa yana sakinta ta samu hanya ta watsa a guje zata fita. Da gudu ya bi bayanta ya damkota, wage baki ta yi zata kurma ihu, a ?ari ya kai ya rufe mata bakin. ?o?arin rabata da kayan jikinta ya fara yi ta karfin tsiya.

Ai kuwa ta gartsa mashi cizo a hannu da karfin gaske har sai da ya saketa ba shiri, dan ta fasa mashi fatar hanni. Ihu ta kurma tare da ?o?arin gudu a karo na uku.

Sake damkota ya yi da karfin gaske, hannunsa in da ta cijesa sai jini yake yi, wani ihu da ta daddage ta kurma da iya karfinta na karshe ne ya daki dodan kunnen momma dake zaune a saman dadduma tana karatun Alkur'ani mai girma. Sosai ihun ya daki dodan kunnuwanta, da yake room ?in chuchu and auta a part ?in ta yake, Chuchun tana da ?aki a part ?in mummynta ma, amma ta fi kwana a part ?in momma, ita fa renon Momma ce, bata shaku da mummynta kamar yadda suka shaku da Momma ba, shiyasa ita da Auta akwai amana sosai, tare suka taso ne.

Shiru mommar ta ?an yi tana tunanin ihun Auta ne ko na Chuchu? Dan voice ?insu kusan iri ?aya ne saboda tsananin shakuwa, kuma ai jini ba wasa ba, mamaki momma take yi a kan ihun me suke zundumawa cikin tsakar daren nan.

Tana tsaka da tunanin ihun ya kara dira a kunnenta a karo na biyu, a wannan karon ihun ha?e yake da kuka, da alama kuka take yi, cikin nutsuwa Mommar ta rufe Alqur'anin dake hannunta, sannan ta mi?e tsaye, door room ?in ta nufa da nufin ta fita waje izuwa wajensu taga me yake faruwa?.

A hankali ta mur?a handle na kofar da nufin ta bu?e ta ta fita. Sai kuma me? Sai jin kofar ta yi a datse kamar an datse shi da keys sama da goma, kofar a datse take gam gam tamkar ba'a ta?a yin amfani da ita bama. Gaba?aya gidan babu wanda ya ji ihun da Chuchun take yi kuma sai ita Mommar kawai, ita ma dalilin ?aya zuwa biyu ne yasa ta ji, na farko bata yi barci ba, na biyu kuma karatun Alkur'ani da take yi ya kore duk wasu shai?anun da suke arear room ?inta wa?an da zasu iya hanata jin ire iren hakan, wannan dalilin yasa ta ji ihun.

Sake mur?a handle ?in ta yi da karfi a ?o?arinta na bu?ewa, amma ina kofar taki bu?uwa, mamaki ne ya kamata sosai, ha?i?a tasan ire iren wannan abin yana faruwa da ita, shiyasa tun farko da ta ji ihun Chuchun bata ?aga hankalinta ba, dan tana tunanin irin abubuwan da ake yi mata a baya ne yanzu abin ya sake dawo mata, idan baku manta ba a baya ana yawan yi mata ihu ko kuka da muryar Gimbiya Zunaira, so yanzu ma ta ?auka hakance, sai dai abin da ya bata mamaki shi ne, ba'a ta?a ri?e mata kofar ?aki ba, gara ma na toilet.

Karfi ta sanya wajen sake gwada bu?e kofar, amma ina abin ya ci tura, tun daga nan ta fahimci ba lafiya ba, tun daga nan hankalinta ya yi mugun tashi, tasan koma waye mai wannan ihun yana tsaka mai wuya, kuma ba lafiya. Sautin ihun ne ya kara dokan dodan kunnuwarta a karo na uku, hakan yasa hankalinta ya kara tashi, jikinta har tsuma yake yi, burinta kawai ta je taga me yake faruwa saboda karfin hali, babu tsoro a tattare da ita.

Da sauri ta juya ta koma wajen bed ?inta, wayarta ta ?auko jiki na kerma, har wani tsuma take yi. A hanzarce take daddanna numbers ?in da take bu?atar kiran, bayan ta gama shigar da number sunan my world ne ya bayyana. Kira ta danna mashi, amma ina kirar taki tafiya, sai wayar ma ya nuna mata sam babu network, da ta matsa ma sai wayar ta ?auke gaba?aya.

Wurgi da wayar ta yi a saman gadon, a hanzarce ta juya ta koma bakin door ?in, jikinta na kerma ta fara karanto duk adduar da ta zo bakinta, da karfi ta sanya hannu tana jan handle ?in kofar tana rero addu'a.

Cikin ikon Allah kofar ta bu?e, kamar wadda bata da cikakken hankali haka ta nufi waje. Kai tsaye ?akin Auta ta fara nufa, tana bu?e kofar ta hangota kwance a saman gado, wutar lamp ya haske kyakkyawar face ?inta, sai sharara barci take yi cikin kwanciyar hankali.

Da sauri ta janyo kofar ta rufe mata tare da nufar ?akin Chuchu. Mur?a kofar ta yi domin ta bu?e, amma sai kofar taki bu?uwa, tamkar yadda kofar ?akinta ya yi haka shi ma wannan ya yi. Kofar a datse gam.

Gaba?aya jama'ar gidan barci suke shararawa kamar gawarwaki, duk abin da yake faruwa basu ji ba, shi kuwa King da bai yi barci ba yana saman dadduma part ?insa yana da ?an nisa da nasu, akwai ratar da ba zai iya jiyo su ba, hakan yasa bai ji me ake yi ba.

Ganin kofar a rufe kamar yadda nata ya yi ruf ne yasa ta gane cewa lallai lallai akwai matsala, ya fahimci daga ?akin Chuchun wannan ihun yake fitowa. Addu'a ta fara yi tana tura kofar da karfi karfi!.

Ta ?auki almost 5 mins a wajen kafin ta samu kofar ta bu?e, kasancewar da karfi karfi take tura kofar sai yasa da kofar ta bu?e ta kusa fa?uwa kasa, da karfi ta shiga cikin ?akin a tare da kofar.

Jujjuya fararen idanunta ta fara yi tana bin ko'ina da kallo. Tsit ?akin ya yi kamar babu kowa, a hankali hankali shesshekar kukan Chuchun yake tashi, tana kwance a saman gadon, ta yi ruf da ciki, kayan barcin jikinta duk an yagesu kamar wadda ta yi fa?a da damisa, fuskarta gaba?aya ya yi jaga jaga da hawaye baiwar Allah, har da majina.

Mamaki da al'ajabi ya hana Mommar motsawa daga in da take tsaye, ta rasa me zata yi, ganin abin take yi kamar a mafarki, ga shi dai bayan Chuchun babu kowa a cikin ?akin.

Ni kam na ce toh ina Yah Jawad ?in?.

Ta jima a tsaye tana bin ?akin da kallo, sai jujjuya idanu take yi, jin sautin shesshekar kukar Chuchu yana kara karuwa ne yasa ta dawo daga duniyar tunanin da ta afka. A hankali ta ?aga kafarta ta fara takawa. Kai tsaye wajen bed ?in ta nufa. Cak ta tsaya a tsakiyar ?akin sakamakon motsin da ta ji kamar mutun ne a bayanta. Fargabar juyawa ta ji gudun abin da zata gani, ga shi kuma tsakar dare ne sosai, a lokacin almost karfe ?aya da minti talatin.

Wani irin kasala da tsoro ne ta ji ya rufeta, a hankali ta fara jiyo sautin kuka kamar na mage a kunnuwarta ta baya. Ajiyar zuciya ta sauke tare da furta Hasbunallahu wani'imal wakil.

Nan take ta ji kwarin gwiwa da kwarin zuciya ya ziyarceta. Da karfi ta juyo domin ta ga me yake motsi a bayanta?. Sai dai ko da ta juyo bata ga komai ba. Sake sauke wani ajiyar zuciyar ta yi tare da ?aga kafafunta ta cigaba da tinkarar gadon.

A karo na biyu ba ta ?arisa isa wajen bed ?in ba ta sake jiyo takun sahun mutun a bayanta yana biyota. A wannan karon cikin sauri ta juya. Ai kuwa tana juyowa wani irin haske ne ya kashe mata idanu, yadda kuka san an dalla mata wutar fitillah mai bala'in haske. Karfin hali irin nata yasa bata datse idanunta ba, cigaba da zarosu ta yi a cikin wannan haske.

Wani irin idanu ta gani a cikin haske, green eyes irin masu hasken nan ta gani, ga idanun dara dara suna bala'in kyalli, idanu kawai ta iya gani, sam bata ga mamallakin idanun ba, bata ga face ?insa ko face ?inta ba, idanu kawai ta gani suna yawo a cikin wannan hasken.

Da yake akwai ta da karfin hali da jajircewa sai ta kara zaro idanunta tana kallon wannan idanun ido cikin ido, babu ko tsoro a ranta, da alama ta saba da irin wa?an nan masifun sosai, gidan King zama cikinsa sai masu karfin imani da kuma karfin hadda dan fa?a da shai?anu, idan ba haka ba kana cikin gararin, dan idan ka yi ba dai'dai ba da daddare ba kai ba barci............

A takaice dai duk yadda aka yi a tsoratar da ita ta gudu abin ya ci tura, ba su san da jinin Modarawa suke tare ba, ai Modarawa basa gudu kuma basa ja da baya, duk wuya duk da?i, komai bala'i sai sun isa in da suka tinkara matikar Allah ya basu tsawon kwana, so basa ja da baya bare gudu, bare kuma ita Momma da take da shegen karfin hali kamar Akka ce ta haifeta, ko da yake babanta ai yayan Akkar ce, Husaininta ne, so fin haka ma zata aikata.

(Ni kam my people's zan so ganin Akka na yaki?? wato tarihin Akka a lokacin ?anmatantaka fa zai bada citta ???? dan haka kada ku ga laifin su Omaid, sun gada ne har ya yi masu yawa, ta gefen uwa da uba dukka ba sauki, kun ga su Chuchu ai suna da mix, dan mummy ba jinin Akka ba ce, ba jinin Modarawa bane, amma su twin's fa? Gaba da baya jinin Akka ce ke gudana a jikinsu, uwa ba sauki haka uba ma, sannan kakarsu ta gefen uba, ta gefen uwar ma duk tsatso ?aya ne da gefen uban, ai kunga su kam sai shirin Allah kawai, sai abin da kuka gani, Zunaira ce kawai ta fita zakka a cikinsu, ita ce mai sanyi hali sai Guyson da sai ka ta?o shi yake fa?a, su twin's kuwa ba sai ka ta?osu ba, idan baka burgesu bama sai sun maka azaba??)

Da dai suka fahimci ba zata tsorata ba, sai suka yi ?o?arin canza salo ta hanyar sanya mata kuka da muryoyi kala kala dan su do?e mata kunne ta dai'na jin sautin komai. A nan ne ita kuma ta fara rero masu karatun Alkur'ani mai girma na duk wata sura da ta zo bakinta.

Ai kuwa ko aya ?aya bata gama karantawa ba wannan haske ya ?ace ?at, nan take ?akin ya yi wani irin tsit, sai a lokacin ita ma Chuchun ta iya ?ago kanta daga kifuwar da ta yi a saman gadon.

A zabure ta mi?e zaune, jikinta sai kerma yake yi, wani irin razana ce bayyane a saman face ?inta, da alama ta tsorata sosai, a ru?e take bin ?akin da kallo kamar mai neman wani abin. Tana sauke idanunta a kan Mommar ta saki wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, da gudu ta diro ?asa daga saman gadon. Tana zuwa ta fa?a jikin Mommar tana kara tsananta kukanta.

Ita kuwa Momma ta yi shiru tana ?o?arin fahimtar wani abin, sai da Chuchun ta fa?a jikinta ne ta sauke ajiyar zuciya tare da rungumeta. Cike da al'ajabin abin ta fara tambayarta me ya faru?.

Kuka take yi sosai ta kasa iya yin magana, ganin haka yasa Mommar ta kara rungumeta sosai tana ?an bubbuga bayanta, a haka suka nufi room ?inta. A saman gado ta zaunar da ita, sannan ta janyo bargo ta lullu?eta da shi.

Har lokacin jikinta na kerma, gani take kamar Yah Jawad ?in yana nan. Da kyar Mommar ta iya lalla?ata ta yarda ta kwanta, bayan ta kwanta ne Mommar ta mi?e ta ciro mata wasu kayan barcin Auta da suke ?akin nata. Da kanta ta sanya mata su sannan ta tofa mata addu'oi, bayan ta kammala sai ta haye gadon suka kwanta tare.

Ba jimawa barci ?arawo ya yi awon gaba da Chuchun, ita kuma Momma kamar yadda taga rana haka ta ga dare, sai tunani take yi a kan to me yafaru? Waye ya yi yunkurin yi wa Chuchun fya?e? Ga shi har an rabata da kayan jikinta gaba?aya saura pant kawai, sosai ta afka duniyar tunani a kan wanenen? Meyake faruwa? Dan dai ita bata ga mutun ba a ?akin da ta shiga, ko dai da ya ji motsin fitowarta ne ya gudu? Ko kuma ya ?uya a cikin toilet ko wani wajen?. Haka dai ta rin?a tunane tunane har asuba.

Washegari da safe da zazza?i mai zafi Gimbiya Chuchu ta farka, jikinta zafi kamar wuta, da alama zazza?in firgici ne, ta ?asa iya tashi ma, ko sallar asuba a kwance ta yi bayan Momma ta yi mata alwala kenan.

Sai kuka ?asa ?asa take yi saboda zazza?in, da alama bata da juriyar ciwo, tana da raki sosai. Sosai momma ta rin?a rarrashinta, da kyar ta samu ta yi shiru, mi?ewa ta yi da nufin ta je ta sanar da King batun zazza?in.

Zata fita kenan a bakin kofa suka ci karo da Auta tana shigowa, gaisuwa ta ?aga mata, cigaba da tafiya ta yi tana amsa gaisuwar.

Ko da ta je part ?in King sai ta isko shi a tare da Mummyn Chuchun da kuma Yah Jawad sai Aunty MieMie suna hira, gaisuwa ta ?agawa King, bayan ya amsa ta gaishe da mummyn ma, sannan Yah Jawad da Aunty MieMie suka ?aga mata nasu gaisuwar.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull