Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 5
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 5: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 5. Cikin nutsuwa ta sanar da King abin da yake faruwa na Chuchu tana zazza?i, amma…
3,231 words
Cikin nutsuwa ta sanar da King abin da yake faruwa na Chuchu tana zazza?i, amma bata sanar da shi abin da ya faru a daren jiya ba, ta ?oye saboda dalilin ?aya zuwa biyu, ba wani dalili bane kuma face ta yi tunanin koma wanenen ya shiga ?akinta ya yi ?o?arin keta mata mutunci to ?an gidan ne, dole kuma tsakanin Jawad da Jaish ne, ita bata san Jaish baya nan ba, so ta ce dole tsakanin su biyun nan ne, dan sune kawai mazan gidan da suke nan, wannan dalilin yasa ta yi shiru bata yi maganar ba, tana son idan Chuchun ta samu lafiya sai ta tambayeta wanenen ya yi ?o?arin yi mata hakan? Idan ta gaya mata sai ta san matakin da zata ?auka, wannan dalilin yasa ta yi shiru bata yi magana ba.
King ya ce mata yana zuwa ya duba jikin nata, Aunty MieMie da Yah Jawad suka mi?e tare da fa?in bari su dubo jikin nata, mummy dai tana zaune bata ce ko uppan ba, kamar Chuchun ba yarta na cikin ta bace, da alama tana da alkunya da kawaici sosai, tun da taga momma ta tsaya a kan rashin lafiyar ?ar tata sai ta kawar da kanta kamar bata jin zafin a kirjinta, alhalin kuma ta shiga damuwa sosai.
"Raeesa ki zauna akwai maganar da zan yi dake, idan mun kammala sai mu dubo jikin nata kafin na wuce fada". Cewar King, ya yi maganar ne kuma da Aunty MieMie, ita ce sunanta na gaskiya Raeesa, MieMie kawai sunan gida ne da mummyn tasu ta sanya mata, kasancewar ita ce ?ar farin mummyn shiyasa bata kiranta da Raeesan ta sanya mata MieMie, da haka sunan ya bita har izuwa yanzu, Raeesan ma ya ?ace, King ne kawai yake kiranta da sunan, da yake shi da sunansu da ya yanke masu yake kiransu dukkansu, Guyson ne kawai baya kiransa da Omar ?insa sai kuma Zunaira da yake cewa Auta, my Saeadati ya ke kiran Guyson, wato farincikinsa kenan, su biyun nan ne yake kiransu ba da sunansu ba.
Komawa Aunty MieMie ta yi ta zauna kamar yadda daddyn nata ya bukata, ita kuma Momma suka tafi tare da Yah Jawad ?in.
Suna shiga ?akin suka sami Chuchun ta mi?e zaune suna hira da Auta, da alama ma kamar labarin abin da ya faru da ita daren jiya take gayawa Autar, dan ga alamar tashin hankali game da mamaki ha?e da tsoro sun bayyana a saman fuskar Autar.
Suna jin motsi shigowa ?akin suka kai kallonsu izuwa bakin kofar ?akin. Ai kuwa Chuchu na yin ido hu?u da Yah Jawad ta kusa haukace masu. Ihu ta fara zundumawa tana ?o?arin gudu ta sauka daga gadon, ko ina zata je idan ta sauka?.
Da kallon mamaki bawan Allah shi da mommar suka bita da shi, ta datse idanunta gam tana zunduma ihu, sai ?o?arin sauka daga gadon take yi, ita kuma Auta ta ri?eta gam ta hana ta sauka, sai tambayarta lafiya me yake faruwa take yi.
?arisowa cikin ?akin suka yi, da sauri momma ta ri?eta tana fa?in. "Jannat lafiya? Meyake faruwa ne?".
Banda ihu babu abin da take zundumawa, da alama bata jin me suke fa?e. Saman bedside drawer Yah Jawad ya zauna, cikin sanyin murya ya furta. "Jannat lafiyarki kuwa?".
Habawa ai tana jin muryarsa ta kara zunduma wani irin ihu mai sauti, ga shi kuma ta kasa iya yin magana, kamar wadda aka sha?ewa ma?ogwaro magana ba zata fita ba.
Kallonsa Mommar ta yi da mamaki fal a face ?inta. Zarginsa ne ya dira mata a ranta, dama su biyu ta ?aurawa ayar tambaya shi da Jaish, to kuwa tun da Chuchun ta gansa ta birkice masu har haka dole a sanya mashi ayar tuhuma.
Bawan Allah shi kuwa da bai san komai ba sai ?o?arin rarrashinta ma ya fara yi, dan zuciyarsa tana yi mashi zafi na wannan ihun da take yi, ji yake yi ba zai iya jurewa ba. Ita kuwa Chuchu ta ki bada ha?in kai ta yi magana, banda ihu ba abin da take yi, idanunta ma a datse gam, bazama ta budesu ba bare ta yi ido biyu da shi.
"Jawad jeka kai kam, barni da ita". Momma ta fa?a tana hayewa saman gadon. Ba musu ya tashi ya fice, sai dai ransa bai so ba, ya so ya rarrasheta ya ji me matsalarta? Amma bai isa ya ce da momma ta bari ya rarrasheta ba, sai kawai ya bi umarninta ya tashi ya fita fuskarsa a ?auke da damuwa fal. Mommar kuma ta yi mashi hakan ne domin ta tabbatar da zarginta, so take ta ga da gaske saboda shigowarsa yasa Chuchun kuka ne ko dai me?.
Ai kuwa yana fita ta rage sautin kukan nata sosai tana sauke ajiyar zuciya game da shessheka.
"Jannat wai me yake damunki ne? Me yake faruwa ne?". Ta yi maganar tana ?an rungumota. Lafewa a jikinta ta yi, cikin shesshekar kuka ta furta "Momma ni bana son na sake ganin Yah Jawad, please ki ce kada ya sake shigowa cikin ?akin nan"...... Babbar magana!!.
Da mamaki Mommar take sauraron kalamanta har ta kai karshen, tambayarta ta yi me yasa bata son ganinsa?. Shiru ta yi ta ?asa iya bada amsa, ita dai bata son ganinsa kawai ta sani.
Ganin ta kasa iya fa?ar dalilin nata ne yasa Mommar ta fara zargin wani abin, da yake ita akwai ta da kaifin basira sosai, su twin's ma a wajenta suka gado rabin nasirarsu, tunani ta rin?a yi anya Jawad zai aikata abin da take zarginsa a kai ?in nan kuwa?. Ni ma dai PRINCESS TEEMA ina tantanma a kan hakan, ga shi shima dai Yah Jawad ?in ya nuna kamar bai san komai ba, ko dai lumbu lumbu yake yi mana ne??? Amma bari mu le?a wani bangaren mu dawo, watakila kafin nan zamu samo mafita, dan komai a kulle yake yanzu, kila mu iya warwaresu idan muka dawo!!.
Amma kafin mu le?a wani part ?in bari na ?an yi maku wani bayani a kan tambayoyin da nake sha, yau bari na baje maku amsar a faranti?? to masu tambayata wanenen star na littafin RAWANIN ZALINCI, and wacece star mace, kun kasa iya gane star mace da star namiji bari na fara da amsa tambayoyinku, dan tun farko farkon book 1 nake samun wa?an nan tambayoyi, yau dai nace bari na amsa. Amsarku a nan shi ne kun manta nace maku littafin RAWANIN ZALINCI zai zo maku da sabon salon da baku ta?a ji ko karanta irinsa bane? Ton idan kun manta na tuna maku! Littafin RAWANIN ZALINCI yana da ?angarori da dama! Sai dai shi salonsa daban ne, a kowani ?angare suna da nasu rikicin da cakwakiyar, ba wai rubutu nake yi a kan abu guda ?aya ba! No kowace ?angare jigon labarin daban yake, ba family guda bane a cikin labarin, kowace family da nasu cakwakiyar da kuma sa?on da nake son isarwa, in short a kowace family tana da star ?inta namiji da kuma mace, haka labarin yake, sabon salo ne da na tabbata baku ta?a jin irinta ba! Amma a gaba?aya littafin akwai star guda ?aya wanda ya fita daban da kowa, haka ita ma macen akwai guda ?aya da ta fita daban da kowa, ku cigaba da hasashenku daga macen har namijin kila zaku iya ganesu kafin alkalamina ya afka cikin labarin sosai ta yadda zamu za?ulosu?? so a takaice dai RAWANIN ZALINCI yana da ?angarori da dama, sannan ba family guda nake rubutu a kansu ba, family's ne daban daban, kuma kowani family da cakwakiyarsa na daban, sannan yana da star ?insa mace da namiji, sabon salo na kawo maku ai??
Sai masu yawan tambayata tun lokacin da nake tubuta littafin TRIPLETS har izuwa kan RAWANIN ZALINCIN a kan rubutun, kuma bari na baku amsa. Ana yawan yi mun tambaya a kan yadda nake rubutu part part daban daban and kowani part da nashi cakwakiyar, sannan familys daban daban, nasamu tarin tambayoyi a kan cewa labarin baya ha?e mun ko kuma akwai wanda take tayani rubutu ne yasa baya ha?e mun kuma bana mantuwa sannan bana ?auko cakwakiyar familyn nan na sanya a cikin familyn nan dan mantuwa, to ga amsarku, a gaskiya babu wadda ta ta?a rubuta mun ko A a cikin rubutuna, ni da kaina nake zama na ?ata awa hu?u zuwa biyar ina rubuta maku labarin, haka nake raba dare ina rubutu, haka zan sanya ?wa?walwata busy, zama nake yi in kirkiro labarina, na tsara shi yadda zai kasance a cikin ?wa?walwata kafin na fara rubutawa, babu wanda ta ta?a taimaka mun da ko A, wai taya ma za'ayi wani ya yi maka rubutu ne??? Ai ba zai yiwu ba, domin labarinka a cikin ?wa?walwarka yake ba'a ?wa?walwa wani ba, ai ba zai ta?a iya rubuta maka shi yadda zaka rubuta ba, in short babu wadda ta ta?a tayani da ko A, ni nake zama in kirkiro labarina in kuma tsara kayana, sannan in hau rubutu na ni ka?ai har in kammala shi, kamar wata computer nake aiki, ni ko irin true life story da ake kar?a a rubuta ma bana yi, akwai wadda ta ta?a cewa zata bani labarinta na rubuta a cikin grp ?ina, duk wadda take cikin grp na PRINCESS TEEMA ina tunanin taga hiranmu da matar a lokacin da ta ce zata bani labarinta na rubuta nace mata a'a banaso, abin da yasa kuma shi ne, labarin da zan ?ir?iro da ?wa?walwata sai ya fi bani damar isar da sa?ona ga al'umma cikin sauki, duk ta yadda nake so zan tsara labarina da na ?irkira sa?anin true life story, so ni ba zan iya kar?ar labarin wani or wata ma na rubuta ba, na fi son na ?ir?iro kayata da kai'na ta yadda zan sarrafa shi yadda nake so, na isar da sa?ona ta sigar da nake so, na ilmantar da al'umma ta sigar da nakeso, na tafi da komaina ta sigar da nake so, na juya kayana upside down yadda nake so, wannan shi ne, fatan kun gane?! Yau dai kun samu amsoshinku dukka!!. To mu cigaba da labarinmu.
JIMETA..........NIGERIA????
Wasu irin uban lodin shanayene (Cows) suke ?etarawa ta gefen wani katafaren kogi mai girman gaske, kogin yana da matu?ar girman da ya keta har ta ma?otan garuruwa, ta gefensa shanayen suke wucewa, da alama kiwo zasu tafi, shanayene masu matikar yawan da sun kai a kallah 1000 da ?oriya, haka suka rin?a wucewa, buguma buguman cikinsu ne a tagaba, harda bo?olaye ?an kasar Cameroon a cikin shanayen. Bayan bujumayen sun wuce ne kananan cikinsu suka rufa masu baya, suma kananan suna da uban yawa ba ka?an ba, ga shanayen da kyan gani sosai, ?ul ?ul da su, sun samu kiwo mai kyau, jikinsu tas, ?ai?aikun cikinsu ne zakaga jikinsu da ?an baki baki, amma tas suke.
Bayan kananan sun wuce uban tilin garken raguna ne suka biyo masu baya, raguna ne irin masu tsawo da dogayen kunnuwar nan, kala biyu ne jikinsu, akwai mai brown da fari akwai kuma mai baki da fari. Suma ragunan suna dayawa sosai, zasu iya kai 300 haka, kuma maza ne da mata.
Bayan sun gama wucewa sai awakai suka bi bayansu, suma suna da yawa gasu manya manyan, sun ji kiwo sun ?oshi. Bayan su sai jakuna da basu wuce guda 20 ba.
Dukka wa?an nan uban tilin dabbobin da suka wuce wata yar kyakkyawar yarinya ce ri?e da sanda take daga karshensu tana ka?asu, yar ?arama da ita, ba ta wuce 8 to 9 years ba a duniya, ita ce ta ka?o wa?an nan uban tilin dabbobin har da bujumayen saniyoyin nan, duk suna a ?arkashin kulawarta.
(Ni kam abin ya bani mamaki, yarinyar da idan ta shiga cikinsu ko alamarta ba za'a gani ba wai a ?ar?ashin kulawarta suke??? abin da mamaki da kuma burgewa. Kai wayaga PRINCESS TEEMA a cikin shanaye????? Tab da na yi suma goma wlh, kai ni ai tsakanina da su in gansu a soye?????? na ci na kora Maltina mai sanyi!. Kar fa ku ce tsoronsu nake ji, sam bana tsoronsu?? ni kanwar Mammar Kamran ce, ?? jarumta a jininmu take?? tsaro zai sa ba ma zan je in da suke ba ba tsoro ba, fatan kun gane???)
Sanye take da takalmar kiwo a kafafunta, ga zanin da ta ?aura sai ta baka dariya, ?aurin zanin ma bata gama iyawa ba, na ciki ya fi na waje tsawo ta ?aura kayanta, rigar kayan fulani ne a jikinta, sai dressing natan ya kara bawa mutun dariya, barema wannan uban kwadaram ?in takalmi da tasa na kiwon, kai ba ?an'kwali, wasu kumbusa kumbusan kitso ne a kanta guda hu?u, da yake tana da tsawon gashi sosai sai jelar kitson ya sauko mata har bayanta, ga gashin nata ba?in kirin da shi sai tsantsi.
Kyakkyawar gaske ce sosai yarinyar, sai dai idanunta a tsaitsai a tsakar ka suke, da alama bata da kunya, dan akwai bushewar idanu sosai kam, ga ?an bakinta ?an ?arami da alama zai yi rashin kunya da surutu dai'dai gwargwado. Ta canca?a wani irin mahaukacin kwalliya da idan ka gani sai dariya ya kashe ka, wannan idan ka ga kwalliyar nan da daddare sai ka sume ko ka ruga a guje a zatonka aljana ka kallah, amma ita a haka gani take tafi kowa yau, ji take kanta ya yi kato saboda ta yi kwalliya, ji take babu kamarta a duk fa?in rugar Lami?o, har wani taku take yi irin na wadda ta fita daban yau.......??
Sai ?ar wakarta take rerawa cikin harshen fullanci tana cigaba da bin dabbobin tana kuma ka?a sanda, idanunta tas suke kamar farin cikin kwai, ga idanun kam sai dai muce masha Allah, dara dara da su.
Cigaba da tafiya da dabbobin ta yi har suka keta ta cikin wasu gonakin suka bar kusa da wannan kogin. Da ?acewarsu a arear wajen ba jimawa sosai wata kyakkyawar matashiyar yarinya fara tas tare da wani dattijo suka zo giftawa ta wajen kogin, da alama duk a tare suke.
Cikin nutsuwa suke tafiya suna hira, daga ganinsu kasan baban da ?a ce ba sai ka tambaya ba, dan suna kama sosai, sai dai yarinyar ta fishi hasken fata sosai, tana da tsawo sosai kamar shi, a shekaru ba zata wuce 14 to 15 years ba, kyakkyawa ce ajin farko. Zanin dake jikinta irin na wancan yar yarinyar da ta ka?a dabbobin nan ne, sai dai ita tana sanye da hijabi mai ?an girma zuwa gwiwarta, da alama tana da nutsuwa sosai, dan yadda take magana da baban nata cikin girmamawa da yin kasa da murya a kan nasa ne zai tabbatar maka da nutsuwarta.
"Bappa zan sha ruwa". Yarinyar ta fa?a cikin sanyin murya, tana murya mai da?in gaske wanda zai dace da rera kira'ar Alqur'ani mai girma. Cikin harshen fillanci ta yi maganar!.
"Tom Mahnoor jeki sha sai ki sameni a wajen Mahreen, ki kula sosai fa". Ya bata amsa tare da wucewa gaba, ha?i?a muryarsa sak irin tata yake, sun yi kama.
Nufar gangaren da zai sauketa izuwa bakin kogin ta yi, dan a saman tudu suke, shi kuma Bappa kwairaga ya bi bayan ?ar yarinya mai ka?a dabbobin nan.
Cikin nutsuwa take sauka izuwa bakin kogin, daga ganin wannan kyakkyawar innocent face ?in nata da akwai damuwa a kanta, tana da fuskar tausayi sosai.
Bakin ruwan ta tsugunna tare da kai kyawawan fararen tafukan hannunta ta ?ebi ruwan ta kai baki, da yake ruwan gudu ne yana da haske sosai, ba'a tsaye ruwan yake ba, yana gudu ne.
Bayan ta sha dai'dai yadda take bu?ata sai ta mi?e tsaye, bin kogin da kallo ta fara yi tare da sanya hannayenta ta ri?o ?ugunta. Can ta hango wani abin jibgi kamar kaya a can gefe a bakin kogin.
?an zaro ido ta yi tare da kurawa wajen idanu, bata iya ganin menene sosai daga in sa take tsaye, hakan yasa ta yi tunanin bari ta ?arisa wajen ta ga menene?. Ai kuwa babu tsoro ba komai ta nufi wajen cikin nutsuwa. Tun bata gama ?arisawa ba ta ja wani uban birki tare da gwalalo ido waje sosai kamar zasu fa?o ?asa. A ?ari ta ?an ja baya tare da wage cool voice ?inta tana kwalawa Bappa kira.
Da ?arfi ?arfi take kwala mashi kiran, amma ina, kasancewar tana da sanyin murya sai voice ?in nata baya fita sosai sam.............
Da yake dajin yana amsakuwa hakan yasa kiran nata ya dira a kunnen Bappa dake ?o?arin rabon fa?a tsakanin............
??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????
????RAWANIN ?? ZALINCI ????
????????????????
FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????
?????????? 19/9/2024.....??????
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????
??STEP TWO....??????
Da yake dajin yana amsakuwa hakan yasa kiran nata ya dira a kunnen Bappa dake ?o?arin rabon fa?a tsakanin Mahreen da wata ?ar matashiyar yarinya da zata iya finta a shekaru, a kallah yarinyar zata kai shekaru goma sha biyu haka, amma Mahreen ta tsaya sai gwabza fa?a suke yi har zani ya fa?i saura pant kawai.
Sandar kiwon nata ta rarumo zata bugawa yarinyar a tsalar ka Bappan da ya iso wajen yanzu ya yi maza ya ri?e sandar yana fa?in. "Haba gajin Bappanta (Auta kenan shi ne gaji da fillanci), meyasa zaki bugeta da sandar nan har haka?".
Gashin idanu a tsastsaye kamar wadda tasa na kanti, idanu a bushe kwalam ba alamar kunya, Bappan yana idasa maganarsa ta sanya mashi kuka kamar ba ita take jibgar ?ar mutane a yanzu ba, sake mashi sandar ta yi tare da yin zaman ?an bori a kasan wajen, kan kace me ta fara birgima a kasan kamar mai shafan aljanu, yi take yi tana kukan shagwa?a ita a dole Bappa ya kyaleta ta cigaba da jibgar ?ar mutane kamar ita ta haifota izuwa duniya.
Yarinyar kuma da ta samu Bappa ya kwaceta ai sai ta danna a guje, dama ta daku a hannun Mahreen ?in, ta germe mata a shekaru, amma saboda bala'in Mahreen ?in nan sai da ta daka yar nan lilis kamar an aikota, har kuka sai da yarinyar ta yi, tana kukan ne kuma dama zata kara kwala mata sanda a kanta dan iyashege.
Sai rarrashinta Bappan yake yi, da alama shi ya ?atata da shagwa?a da kuma fa?a, dan baya yi mata fa?a da nasiha a kan idan tana fa?a da mutane ko tana shagwa?a, sai dai ya biye mata ya yi ta rarrashi, yanzu ma fa?i yake yi tom ta tashi ta dage shi da sandar shi tun da ba zata hakura ba, ai kuwa make kafa?a ta yi tana fa?in ita dole ya barta ta kwalawa yarinyar can sandar, idan ba haka ba yau ba zata ci abinci ba.
Ita kuwa yarinyar da Allah yasa Bappa ya kwaceta ta ruga da gudu wajen shanayen kiwonta, sai da ta kusa isa wajen ta juyo tare da fa?in. "Mahreen mai kwalliyar mahaukata na fa?a ?in ki lilili ki li?eni ki mai dani cikin uwata ki fitar dani ta bakin allura idan kin isa ba iya duka kawai ba! Na fa?a kin yi kwalliyar aljanu karya na yi ne? Fuska a dame kamar fura........"