Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 6

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 6

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 6: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 6. Habawa a wani irin zabure ta yun?ura, an fasa yi wa Bappa shagwa?a, aljanun…

3,336 words

Habawa a wani irin zabure ta yun?ura, an fasa yi wa Bappa shagwa?a, aljanun dukan sun motso, Mahreen mai kar?awa wata ?ancinta ma bare kuma ace ita aka tsokano? Ita fa take tsayawa ta yi dambe da duk wa?an da suka ta?o Mahnoor, dan ita Mahnoor ?in sam bata da fa?a, tana da sanyi, idan anyi mata ba da?i sai dai ta samu waje ta zauna ta sha kuka, to Mahreen take tsaya mata a buga dambe, tsabar fa?arta yasa yanzu aka dai'na tsokanar Mahnoor mai idon mujiya a kauyen, ai ganganci ne ma ka ta?o Mahreen ka yi tunanin zata barka, wlh komai daren da?ewa ba zata manta ba kuma bazata hakura ba, duk randa kuka ha?u sai ta rama, gata da iya fa?a, duk ta yagushe maka jiki da faratun hannunta, kamar wata mage, idan kuna fa?a tsalle take yi ta haye jikin mutun ta shakesa kamar mage, ta yi ta yagushe maka fuska, bazata ta?a bari kuma ka yakiceta ba, sai ta yi ta zullewa har sai ta yi maka lahani, duk kuma abin da zata yi Bappa baya ta?a ganin laifinta, shiyasa ko ta jibgi ?a?an mutane ba'a kawo kara wajen Bappa ko Nennenta, dan kuwa basu kar?ar laifinta, gara ma Bappa zai bawa wa?an da suka kawo karan tata hakuri ya ce yarinya ce, ranar kam ma da ta fasawa wata baki sai da Bappa ya basu kyautar ?an marakin saniya kafin suka hakura, sun ce sai sun ?auki fansa sai sun rama, hakan yasa dole ya basu wai aje a yanka a gasawa yarinyar nama ta ci bakin nata ya koma normal, sai da ya yi haka suka hakura, ita kuma Nenne idan kika kai mata karar Mahreen uban masifa zata hau surfa maki ta ce ?arta kawai aka sakawa ido a kauyen nan, yarinya kamara zasu cinyeta da baki!.

Mahreen akwai shagwa?a sosai dan Bappa ya shagwa?ata sosai ba karya, sannan akwai fa?a dan fa?arta ma gado masifar ta yi daga wajen Nennenta, in tana masifa fa har wani rufe idanu take yi hannu na rawa ya yi sama ya yi ?asa, ?ugu na rawa kamar ana ka?a burugalin burga nono, haka take ri?e ?ugu tana sama tana ?asa, ta in da take shiga ba tanan take fita ba, sai dai bata shiga harkar kowa ne, haka kawai bata kama mutun da fa?a, idan kunga tana fa?a to tabbas ta?ota aka yi, idan kuma aka ta?ota wlh wannan fa?ar bata karewa cikin sauki, idan yarinyar bata gudu ko ta mi?a wuya ta bada hakuri ba, wlh sai Mahreen su kwana suna gwabza fa?a ba zata gaji ba, so bata fa?a sai an tsokaneta ko kuma an ta?a mata ?ar uwarta Mahnoor, nan ne zaku ga balbalin bala'i in mai tafasa in jita. Yarinyar nan ta yi suna a wannan kauyen fiye da tunaninku, manya da yara kowa ya santa, gata da ?an banzan farinjini, bata isa ta gifta wani guy ?in saurayin bai ce mata hllo ?an mata ba.........????

Su fulanin daji kunsan suna auren wuri gaskiya, kamar Mahreen ?in nan takai ayi mata miji idan an samu, wadda bata kaita bama ana yi masu miji har ma aure, shi dai Bappa ya bar ?a?an nasa ne a cewarsu yana jiran ?a?an yayansa maza da suka tafi kiwo na tsawon shekaru biyu, sun tafi yawon kiwo har ?asashen makota, dama kun san suna yin haka, to su yake jira idan sun dawo zai aura ma ?aya Mahreen sai a ha?a da Mahnoor dake da nata saurayin shi ma na gida ne, yana son ha?a aurensu lokaci guda ne yasa bai aurar da Mahnoor ?in ita ka?ai ba.

Da sauri Bappan ya ri?ota. "Haba gajin Bappa, ki kyaleta mana tun da dai ta gudu, ai ta ji tsoronki ne yasa ta gudu, tun da tana tsoronki yi hakuri ki ?aga mata kafa". Ya fa?a cikin sigar rarrashi.

"Da gaske bappa ta ji tsorona?". Ta fa?a tana zaro idanu. Duk wannan fa?uwa ?asa da ta yi tana birgima tana kuka ashe babu hawaye ko tsilo a face ?inta, ashe ihunta kawai take kwararawa babu hawaye, kai wannan yarinya sai shirin Allah. Amma dai wani lokaci tana da gaskiya wajen kwatawa kanta ?anci har ma da ?ar uwarta.

"Kwarai kuwa gajin Bappanta, ta ji tsoronki sosai ma kuwa".

Wani irin tuntsirewa da dariya ta yi tare da fara yin tsalle tana fa?in. "Shikenan Fatu ki je na yafe maki tun da kin ji tsorona, yeee ta ji tsoro a bata kunun zakin da ya yi sati ta sha ta bugu ta hau aiki".

Mahnoor dake tsaye tun ?azun tana kallonsu ne ta ce. "Mahreen Allah ya nuna mun ranar da zaki dai'na fa?a, Bappa kazo muje ka ga wani abu a bakin ruwa, sai kiranka nake yi baka amsa ba".

Yana ?o?arin yin magana Mahreen ta rigasa da cewa. "Adda Mahnoor zan daina fa?ane kawai idan suka dai'na zagin kwalliyata".

?an girgiza kai ta yi kafin ta amsa mata da. "Ai Mahreen ba zagin kwalliyar taki suke yi ba, na sha fa?a maki saboda basu iya ha?a??en kwalliya irin taki ?in bane yasa suke zaginsa, da zaki koya masu irinsa tsab zasu dai'na zagin su fara yin irinsa...."

?ara zaro fararen idanun nata ta yi. "A'a gaskiya wlh ba zan koya masu ba munafukai kawai". Ta yi maganar a shagwa?e sosai.

"Bappa zo mu je ka ga wani abin, ke kuma Mahreen ki dawo da dabbobin nan kusa, sun yi nisa sosai".

To ta amsa mata tare da sanya kai da ?ar gudunta ta wuce tana murmushin da ya kara mata kyau sosai, ta ji da?i ?ar uwarta ta ce tafi kowa iya kwalliya a kauyen........ E da gaske wannan yarinyar akwai shiga rai, nima dai ta shiga rai na.

Wucewa Bappa ya yi izuwa in da Mahnoor ke tsaye, a cikin ransa yana addu'ar Ubangiji Allah ya shirya mashi Mahreen ?in nan nasa, Allah ya rabata da shegen son fa?ar nan, fargaban da yake yi kada wata yara ta ta?o wadda zata yi mata duka, ba zai iya jure a daketa ba, yana kaunarta sosai, duk wadda ta ta?a mashi lafiyarta sai sun buga shariya a wajen Ar?o da shi, so shiyasa yake yi mata addu'ar Allah yasa ta dai'na fa?ar ma tun kafin a kai ga haka.

Daga ?an baya baya Mahnoor ta tsaya bata iya ?arisawa bakin kogin ba. Shi kuwa Bappa da ganin kamar mutun ne a wajen yasa ya yi saurin ?arisawa wajen dan ya ganewa idanunsa.

Zuba mashi ido sosai Bappan ya yi yana kallon yadda fuskarsa take da kuma yadda yake kwance a bakin ruwan, rabin jikinsa duk a cikin ruwan, kyakkyawa ne sosai, farine tas da shi, soft skin ?in nan nasa sai wani sheki yake yi, ga fatar tasa luwai luwai kai ka ce bai ta?a fita rana ba. Yanayin yadda yake kwance a bakin kogin ba ?aramin mamaki ya bawa Bappa ba, abin ya ?aure mashi kai. Ita kam Mahnoor ta tsorata sosai, ta koma baya tana fa?in. "Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun ". A cikin zuciyarta, dan a nata tunanin aljani ne ba mutun ba, dan kyakkyawan gaske ne, ga wannan dark black curly hair nan nasa ya kwanto mashi har saman goshinsa, da yake ruwan kogin ya ji?a gashin nasa, sai ya manne mashi a fuska, duk da idanunsa a rufe, hakan ba zai hana ka gane cewa yana da manya manyan idanu ba, ga lips ?in nan nasa ya yi pink color sosai kamar na mata, ?an ?arami da shi, yana da dogon hanci sosai, hancin nasa kuma bai yi irin dogo zur ?in nan ba, a'a ya yi ?an dai'dai mai matu?ar kyau da ?aukar hankali, ya kuma yi dai'dai da face ?in nasa, ya kara kawata kyansa ba ka?an ba.

Kwata kwata bai yi kama da Nigerians ba, suit ce mai bala'in kyau da tsada a jikin sa, launin ask color ce, daga ta ciki kuma, long sleeve shirt ce fara tas. Duk da yana kwance, hakan bai hana ka ga cikakkiyar tsuransa ta kiran karfi da lafiya tare da jini a jika a tattare da shi ba, ga dukkan alamu yana da ala?a da manya manyan mutane, duba da irin tsadaddun kayan da suke jikinsa, watch dake hannunsa ma kawai abin kallo ne, diamond watch ce mai matukar kyau da ?aukar hankali, kafarsa na sanye cikin wata dankareriyar half cover ash color mai bala'in kyau, neck tight dake wuyarsa ta manne mishi a wuyar tasa ta samar lallausan fatarsa, saboda ruwa da ya jika shi, yana da tsawo sosai, ga fa?in kirji tamkar wani zaki.

Tsugunnawa a kusa da shi Bappa ya yi babu ko tsoro tare da sanya hannunsa a bakin kofofin hancinsa dan ya ji shin yana numfashi ne ko baya yi.

Ko ka?an baya numfashi kamar ma babu rai a tattare da shi, duba da yanda ya yi wani yellow sosai, ga kuma face nasa da alamar kumbura a tattare da shi. ?agowa Bappan ya yi cikin harshen fillanci ya ce "Mahnoor ?in Bappa ki ka?o mun jakin guda ?aya bari na ?aura shi a kanta mu je gida".

"Bappa kada ka ?auke shi, aljanine fa, ni ban ta?a ganin mutun mai shegen kyau irin haka ba". Ta yi maganar tana zaro idanu.

Cike da ?a zolaya ya ce. "Kin ta?a ganin aljani ne? Kuma waye ya ce maki aljani yana da kyau? Ko dai kin ta?a ganin kyakkyawan aljani ne ban sani ba...?"

Kara ja da baya ta yi, jikinta har ya fara kerman tsoro, ita dai bata ta?a ganin kyau irin nasa ba, sannan ga shi kwance a cikin ruwa, sai hakan ta kara sanyawa fuskansa ya yi wani iri a gareta. "A'a bappa, ban ta?a ganin aljani ba, amma dai ban ta?a ganin mutun irin wannan ba".

A takaice ya ce mata. "Nima ban ta?a ganin mutun irin wannan ba kam, ina dai ganin masu irin yanayinsa, amma ina da ya?inin ba aljani bane, mutun ne wannan In Sha Allah, kada ki damu je ki ka?o mun jaki bari na nemo wani ya tayani kama shi mu ?aura a saman jakin".

To ta amsa da shi tare da wucewa da sauri, kirjinta sai dukan uku uku yake yi, addu'a take yi Allah ya sa dai mutun ne ba aljani ba, dan ita dai bata ta?a ganin mutun kamar haka ba.

Cikin hanzari ta je ta ka?o jakin ta dawo, ko da ta dawo wajen bata sami Bappan ba, hakan yasa ta tsaya daga ?an nesa da kogin ka?an, taki yarda ta ?arisa wajen, dan gani take kamar idan ta je aljaninne zai tashi ya kamata, ita dai bata gama yarda cewa mutun bane.

A wajen ta tsaya har Bappa ya dawo tare da wani mutun, sanin halinta yasa Bappan bai ce lallai dole sai ta matso kusa da mutumin ba, kar?ar jakin kawai ya yi tare da ce mata ta koma wajen Mahreen bari ya kai mutumin gida.

Da sauri ta juya, kamar zata kifa ?asa, sai waigo su take yi, tana gani suka ?aura shi a kan jaki, jikinta na kerma ta wuce wajen Mahreen.

Zaune ?ar?ashin wata bishiya ta isko Mahreen ?in tana shan raken da ta karyo a gonar Bappa. A kusa da ita ta zauna tare da fara gaya mata cewa Bappa ya tsinci wani aljani mai kama da mutun.

A ?ari Mahreen ta zaro idanun nan nata. "Aljani kuma Adda Mahnoor?". Ta zaro ido alamar mamaki da tsoro tana magana, amma hakan bai hana ta karyi rakenta ta cigaba da sha ba....... Wannan yarinyar akwaita da abin dariya, tana tambaya tana shan rake.

"E Mahreen aljani, idan kika ga kayan jikinsa ban ta?a ganin irinsu ba, har da wani igiya ya ?aura a wuyansa, kinga takalmarshi? Ya so ya yi iri ?aya da na kafarki, ga shi nan fari tas, kuma shi kalar fatar jikinsa sam sam ba irin namu bane, shi fatarsa ma ban san ya zan ce maki ba, amma dai ba irin na mutane bane, dan ban ta?a ganin irinsa ba, ya ?aura wani abin mai ?aukar ido a hannu (agogo) kin ga ga shin kansa? Ba irin namu bane, yana da kyau sosai ba irin kyau ?in mutane ba......"

(Magana ta Allah Mahnoor ta cuci Jaish da ta ha?a takalmar ?afafunsa da na ?afafun Mahreen, gaskiya ta gama cutarsa?? Mahreen mai takalmar kiwo me ha?insa da tsadaddiyar cover fisabilillahi???)

Zubur ta mi?e. "Adda Mahnoor bari na je na gansa, ri?e mun sandar nan....." Tun bata kai karshen maganar ba ta mi?a mata sandar tare da sanya kai da gudu ta wuce, maganar ma a hanya ta ?arisa ta.

Tana barin wajen sai ga wani kyakkyawan matashi chocolate color ya ?ariso wajen, hannunsa na ri?e da sandar kiwonsa. Matashi ne da ba zai wuci shekaru 22 ba a duniya, ba karya yana da kyau sosai, suna ?an yanayi da Mahnoor ?in ma, daga gani ba tambaya zaka san dangi ?aya ne, dan wa?an nan dara daran idanun nasu kusan iri ?aya.

?aure fuska ta ?an yi da ganinsa. A kusa da ita ya zauna yana washe baki. "Mahnoor ina Bappa da Mahreen yau kuma?".

Cike da nuna kulawa ta fara magana, sai dai ta ?aure fuska alamar tsare mutuncinta. "Ina kwana Hamma Faisal".

Fuska ba yabo ba fallasa ya amsa mata da lafiya lou, sannan ya ?aura da maimaita tambayar inasu Bappa?.

"Bappa ya je gida, Mahreen kuma yanzu ta bar nan ta bi bayansa". Ta fa?a tana ?an murza sandar Mahreen dake hannunta a ?asa, ta kuma yi maganar tana kallon ?asa, ko da sunan wasa bata ?ago sun ha?a ido ba.

"Mahnoor meyasa a duk lokacin da muke tare kike ?aure fuskarki ne? Sai na ganki kina hira da murmushi da su Bappa, amma ni baki yarda ki yi hira da ni ma bare har ki mun murmushi, sai ki ?aure fuska sosai mena yi maki ne?".

Ajiyar zuciya ta sauke, ba tare da ta ?ago kai ba ta amsa mashi da. "Hamma Faisal babu abin da ka yi mun..." "To ko kin dai'na sona ne?". Kai ta girgiza mashi. "A'a ban dai'na ba".

"To meyasa baki son yin hira da ni ko ki yi mun murmushi kamar yadda kike yi da Bappa da kuma Mahreen?".

Sam babu alamar zata yi murmushin a saman face ?inta, tamkar bata ta?a yin murmushin bama, fuska kala biyu take da shi yarinyar nan, idan ta ?aure fuska sai ka rantse da Allah bata ta?a sanin me murmushi ba, ?aurin fuska yana zama a face nata sosai kuma yana yi mata kyau, haka zalika idan ta yi murmushi sai ta baka sha'awa, sai kaga kamar kullum haka fuskar tata take, musamman idan dimple nata ya lotsa, so in ma murmushi ko akasinta duk suna dacewa da face ?inta kuma suna ?ara mata kyau.

"Hamma Faisal ai baka yi abin da zai sanyani yin murmushin bane, ita kuma Mahreen ai kasan halinta, in dai kana zaune da ita dole sai ta baka dariya ma ba murmushi kawai ba, shi ne yasa kawai bana murmushi ba dan wani abin ba". Cikin sanyin murya sosai ta yi maganar.

"To amma dai kin san ina sonki ko?". "E na sani, nima ai ina sonka". Guntun murmushi ya yi.

Shiru ne ya biyo baya na ?an lokaci, shi ya katse masu shirun da cewa. "Ya aka yi yau kika biyo Bappa kiwo ne ma?".

Har lokacin bata ?ago ta kalle shi ba ta amsa mashi da cewa. "Bappan ne ya ce nazo mu tafi, kuma ai dama kaga idan yana nan muna binsa kiwo sosai, idan baya nan kuma Nanne ce take hanamu bin kawu Ibrahim, shiyasa bama zuwa".

Zai sake yin magana Mahreen ta iso wajen da gudu tana haki, da alama ta ci gudu ne ta ?oshi.

"Adda Mahnoor wlh da gaske maganarki take, kin ga mutumin nan kuwa? Tabbas ba mutun bane, Bappa kuma fa gida ya kaishi, yanzu fa?a suke yi da Nenne a kan Bappa ya ce in dai mutumin yana da rai to shi zai yi jinyarsa har ya warke, idan kuma suka bincika ya mutu to sai a binnesa, shi ne Nenne ta ce wlh Bappa ba zai ajiye mata aljani a gida ba, salon tsakar dare ya tashi ya shake mata wuya ya kasheta, Bappa kuma ya ce ba zai je ya wurga da shi ba, ya shigar da shi ?akinsa har da kwantar da shi a saman tabarman da yake jinyar marasa lafiya, ya kafe sai ya yi jinyarsa idan yana da rai, Nenne kuma ta ?auki mayafinta ta tafi gayawa Ar?o abin da Bappa ya yi, kuma ta ce ba za ta dawo gidan ba har sai Bappa ya fitar da aljanin nan". Ta ?are maganar tana tsugunnawa a kusa da Mahnoor ?in tare da sauke ajiyar zuciya. Get

"Ke chali chali, wai bana ce ki rin?a nutsuwa idan zaki yi magana ba? Yanzu dai babu abin da na gane a maganar nan taki, yarinya sam bata da nutsuwa, kai na rawa kamar mazari.." cewar Faisal.

"Babu ruwanka da ni Hamma Faisal, tun da nazo nan ai ban yi magana da kai ba, kuma ai na ganka, maganarce kawai ba zan yi maka ba, ni fa nace ma ka dai'na shiga harkarta, kasan bana sonka tom!"......... Tab mai kankanta kenan, yau ga ikon god, wato ita idan bata son mutunma kai tsaye zata gaya mashi, a tsirara zata fitar da kalmar sai dai ayi wacce za'ayi, aiki ga mai kareka!!.

"To dama wayace ki so ni? Nima ai kin san ba sonki ?in nake yi ba, waye zai so aljana ma irinki? Yarinya kamar jikar Lami mai kafar shamuwa, Mahnoor idan ana iska kada ki bari ta rin?a fita na sha gaya maki, idan ba haka ba wata rana zaku nemeta a rugar nan ku rasa, dan tsab iska zai yi sama da ita............"

Ai kuwa bai ?arisa maganar ba ta zunduma ihu tare da mi?ewa ta mi?i hanya sai wajen Bappa. ?an siririn murmushi Mahnoor ta saki kafin ta ce. "Hamma Faisal yau babu kai babu zaman lafiya tsakaninka da Bappa".

Mi?ewa tsaye ya yi yana fa?in. "Shiyasa zan gudu yanzu, kuma ba zan dawo ba sai gobe, ba zan bari mu ha?u da shi ba yau, sai zuwa gobe idan ya huce".

Murmushi kawai ta ?anyi bata ce komai ba, sa kai ya yi ya wuce yana tunanin yadda zai kauce haduwarsa da Bappa a yau, ?a?an gwaggo da ?a?an kawu suke shi da su Mahreen ?in, maman Faisal kanwar Bappa ce, kuma shi Faisal shi Bappa ya baiwa auren Mahnoor ?in, yanzu mijin Mahreen ake jira ya dawo sai a aurar da su.

Nikam har na ji tausayin mijin da zai auri Mahreen gaskiyar, za'a sha dambe, dole kuma ya koyi rarrashi kamar Bappa.

Yau dai Mahnoor ita ka?ai ta zauna tare da wa?an nan uban tilin dabbobin, Mahreen tun da ta kai karar Faisal wajen Bappa bata dawo ba, lallashinta Bappan ya yi tare da kwantar da kanta a saman cinyarsa har ta yi barci, amma kafin ta yi barci sai da Bappan ya yi mata alkawarin zai yi maganin Faisal ?in, ta ce ita dai ya ce kada Faisal ?in ya sake yi mata magana, idan ba haka ba watarana sai ta fasa mashi kai da itace idan yana zaune bai sani ba, zata zo ta bayansa ta buga mashi, har da nunawa Bappan yanda zata yi ta fasa mashi kan nasa, da kyar ya shawo kanta, sai da ya yi alkawarin zai shiga tsakaninsu, daga yau Faisal ba zai sake kulata, sannan ne ta hakura ta kwanta ta yi barci.

??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????

????RAWANIN ?? ZALINCI ????

????????????????

FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????

?????????? 19/9/2024.....??????

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????

??STEP TWO....??????

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull