Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 7

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 7

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 7: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 7. Mahreen da Faisal kamar wuta da audiga haka suke, basu shiri kuma basu ha?a…

3,360 words

Mahreen da Faisal kamar wuta da audiga haka suke, basu shiri kuma basu ha?a hanya, kullum bata da aiki sai zaginsa, ta ce da Mahnoor kada ta yarda ta aure shi, in dai ta aure shi to wlh ba zata je gidanta ba, haka dai suke ta fama, ita Mahnoor da bata san me soyayyar ko da?inta ba jinsu kawai take yi, ita ina ma ruwanta da wani soyayya, Faisal ?in ne ma ya koya mata cewa tana sonshi shiyasa take fa?a mashi kalmar, amma bata san me soyayya ko me ake ji idan ana yi ba, bare wannan uwar rawan kan, yo ita idan ba fa?a da kukan shagwa?a da kuma cin abinci ba me ta sani? Ai ba ruwanta da zancen banza, ta dai san ance za'ayi masu aure, ita kanta Mahnoor da take matsayin babba ma bata san me ake nufi da auren ba bare kuma uwar rawan kai, su dai za'ayi masu aure kawai, kila sai anyi zasu san me yake nufi ko me amfaninsa.

Sai bayan la'asar Bappa ya dawo wajen kiwon hannunsa ri?e da kwanon sha mai rufe da paipai. A saman ?an'kwalinta ya sameta zaune ?ar?ashin wata bishiyar ?aure, da alama bata jima da idar da sallah ba, ta buga uban tagumi, idanunta sun ?an ciko da kwallah, da alama tunanin wani abin take yi wanda ya sanya ta kusan kuka.

Sallamar da Bappan ya yi mata ne yasa ta dawo daga duniyar tunanin da ta afka, da sauri ta goge idanunta tare da cewa. "Bappa ka dawo?".

Zama ya yi a gefenta. "Na dawo Mahnoor, kiyi hakuri ban kawo maki abinci da wuri ba, Nennenku ce ta yi tafiyarta, taki dawowa ta yi girki, ni da kai'na na yi girkin sai yanzu na kammala, ga shi kici sai mu ka?a dabbobin mu koma gida ko?".

Kallonsa ta ?an yi tare da yin ?asa da kai. "Bappa meyasa zamu koma gida da wuri yau? Ai naga kamar karfe 6 bata yi ba, ban jima da yin sallar la'asar bafa".

Jinjina mata kai ya yi kafin ya ce. "E haka ne lokacin komarmu bai yi ba, amma zamu koma ne saboda dalilai biyu, na farko Nennenku bata nan, kuma naje gidan Ar?o ?aukarta ta ce ba zata dawo ba, kinga ba wanda zai yi girkin dare sai ke, dan haka zamu koma ne ki dafa mana abin da zamu ci, sai kuma batun mutumin nan da muka tsinto, ina bincike a kan lafiyarsa, har yanzu ban iya gano yana da rai ko ya mutu ba, shiyasa zamu koma gida yau da wuri, dan haka ci abinci da wuri mu tafi". Ya kai karshen maganar tare da bu?e mata paipain da ya rufe kwanon shan da shi. Abinci ne mai rai da lafiya, tuwo ce da miyar ?anyar ku?ewa ta ji man shanu, ga nama zu?u zu?u.

Hannu tasa ta fara ci, dan hannunta a wanke tas, ba jimawa ta je ta yo alwala a bakin kogi. "Bappa ina Mahreen?". Ta yi maganar tana cigaba da cin abincinta.

"Mahreen tana gida tana zuba barci". Ya bata amsa tare da mi?ewa ya nufi wajen dabbobin nasu in da suke ?an nesa da su, sai gabsarar ciyawa suke yi.

Ha?a kansu ya yi ya ka?asu tare da fara zuba masu surutu a kan su yi hanyar walde wato in da suke kwana a bayan gidansu kenan, a bayan gidansu walden dabbobin yake, akwai tirke dayawa a wajen, wasu shanayen suna ?auresu saboda ?a?ansu su samu damar shan nono kada iyayen su ?ace cikin garke ?a?an su sha wahalar nemansu, shiyasa suke ?aure masu ?a?an, wasu kuma saboda mafa?ata ne yasa suke ?auresu a tirken, saura kuma sai su barsu a sake haka basa ?auresu, kuma babu in da suke zuwa suna tsaye a wajen.

Ita kuma cinye abincin tas ta yi tare da mi?ewa ta nufi bakin kogi da kwanon, wankosa tas ta yi, sannan ta bi bayan Bappan, dama bai yi mata nisa ba, ba jimawa ya wuceta duke tana wanke kwanon.

Kai tsaye walde Bappa ya nufa da shanayen, ita kuma ta nufi cikin gida. Tana shigowa ta nufi kitchen, bayan ta ajiye kwanon a ma'ajiyinsa ta ?auko wani ?an madaidaicin bokiti, ruwa ta ?ebo a cikin ?aya daga cikin randunar dake cikin kitchen ?in.

Kai tsaye bayi ta nufa, a gurguje ta yi wanka ta fito, da sauri ta shige cikin ?akin bukkarsu, sai sauri take yi kamar zata kifa, duk dan ta ?aura zani a kirji, kuma ta sanya hijabi, amma da yake hijabin zuwa gwiwarta kuma shima zanin da ta ?aura a kirji bai kai gwigwa ba, so singalalin kafafunta a waje shiyasa take zuba sauri dan kada wani ya shigo ya kalleta.

Zama ta yi a bakin ?ar karifarsu, man shafawa ta ?auko, mai ne irin wannan vaseline ?in na 150 ?an kananan mazubin nan, shi ta ?auko ta murje jikinta da shi, da yake sun wadatu da nonon shanu skin ?insu yana da kyan gani sosai, kun san madarar saniya tana gyara jiki, so jikinta ya yi luwai luwai.

Bayan ta gama shafa man sai ta janyo wani jaka da aka ?inka da buhu, kayan kwalliya ta fitar a ciki, powder ce da ?ar janbaki za irin mai green ?in bayan nan, shi ta ?auko ta hau murje fuskarta tana gyarawa. Lips ?inta da suke pink sosai ma kamar an sanya janbaki pink sai da ta sa mashi red janbakin, sam jan kalar bai yi mata kyau ba, kalar lips ?in tata ya fi yi maya kyau, amma da yake suna kaunar kwalliya ita da Mahreen sai sun sanya, ita iya power da janbaki take sakawa, bata sanya kwalli ko da a iya ido ne kawai, Bappa ne ya hanata sanya kwallin, a cewarsa idan tana sanya kwalli a ido bakin mutane zai yi mata yawa over, yanzu ma jama'a suna yawan magana a kan kyan idanuta, to idan ta sanya kwalli ?ara kyau sosai idanun suke yi, gasu farare tas, hakan ya ja duk wanda ya ganta sai ya yi maganar idanun nata da kyanta, shi ne yasa Bappa ya dakatar da sanya kwalli, kuma ya hanata yin kwalliya idan zata fita, shi yake sayo masu kayan kwalliyar idan ya je cikin gari, amma ya hanata yi idan zata fita, shiyasa kuka ga ita bata yi kwalliya ba time da zasu je kiwo, tana kuma kaunar kwalliyar sosai, ita ma Mahreen duk randa Mahnoor ta yi mata kwalliyar kirki ta yi kyau sai jama'a sun yi ta magana, shiyasa Bappan ya hana Mahnoor ta yi mata kwalliya, ya ce a barta ta rin?a yi da kanta, dan idan ya hanata yin kwalliyar nan ba ?aramin rigima zai yi da ita ba, amma idan ya barta tana yi da kanta ta zama kamar mahaukaciya ai kunga ba wanda zai yaba, ba wanda zai kallah ya ji ta burgesa, sai dai ma a mata kallon mahaukaciya, duk ta ?ata fuska, har a kumatu take sanya janbaki, kun ga kuwa ai sai dai ayi mata dariya, ta wannan hanyar ita kuma Bappan ya biyo mata suka zauna lafiya.

Bayan ta gama kwalliyarta ta ?auko wata ko?a??iyar goduwar riga ta atamfa daga cikin kwallar da suke saka kayansu ta sanya a jikinta, sannan ta ?aura ?ankwalin rigar. Kasancewar ita yanzu ta ?an fara girma, akwai tula tula a kirjinta sai hakan yasa bata ta?a yarda ta yi yawo babu hijabi koda kuwa a tsakar gida ne, kullum da hijabi, har barci bata cirewa, tana manne da shi, dan tana jin kunyar a ga tula tulan a kirjinta, sai wahalar da kanta take yi wajen nokesu, idan tana tafiya ta yi ta faman sanya hannu a hijabi wai dan kada ma alamarsu ya fito.

Ita kuwa Mahreen da ?an'kwalin ma sai randa aka ga daman sakawa ake sawa, idan kun ganta da ?an'kwalin to fa ranar da ta sanya kayan sallarta ta ci kwalliya mai kyau, to a ranar ne za'a ganta da ?an'kwali an she?a ?auri kamar bukkar mahaukaciya, sai a ?wama wani kwandaram ?in takalma, Allah sarki suna son yin gayu irin na ?an birni da suke gani idan suka shiga birnin da Bappansu, amma basu da kayan ?an birni kuma bama su iya irin kwalliyar ba, sai dai su yi iya kar yinsu.

Tana gama shiri ta ?auki hijabi ta sanya sannan ta fito waje ta ?auko tsintsiya, ?akinsu ta fara sharewa kafin ta fito ta share na Nennensu ta gyara, sannan ta nufi na Bappa.

Tana shiga ta ?an ja birki ganin Jaish da basu san wanenen shi ba kwance a cikin ?akin na Bappan, ita kwata kwata ta manta da cewa Mahreen ta gaya mata Bappan ya kai shi ?akinsa ya kwantar, da ta san yana nan ba zata shigo ba, dan tsoronsa take ji, ga shi Bappa da ?o?ari bawan Allahn nan ya raba shi da suit ?in jikinsa, ya rage daga shi sai singlet ?insa fara kal, daga ta ?asa kuma wani wandon yadin shadda green color Bappan ya sanya mashi, wandon tana da tsawo, a dai'dai saitin tsakiyar faffa?ar kirjinsa Bappan ya manna mashi wasu ganyayyaki, da alama magunguna ne na gargajiya da zasu taimakawa bugawar zuciyarsa, gaban goshinsa ma hakan ce, Bappan ya janye gashin kan nasa baya ya bi gaban goshin nasa duk ya mammanna mashi ganyen.

Hasbunallahu wani'imal wakil ta furta saboda bugawa da kirjinta ya yi na ganinsa a kwance haka, juyawa ta yi da sauri da nufin ta fice daga ?akin, dan ba zata iya yin wannan gyaran ba, har ga Allah face ?in Jaish yana tsoratata, ita ba ta yarda mutun bane. Mahreen kuwa da yake ba tsoro a ranta tana kwance saman katifar Bappan tana zuba barci, sam bata ji tsoronsa ba, ta dai yi mamakin ganinsa, amma har da ta?a fuskarsa ta yi dan ta tabbatar ba face ?in ?ar tsana bane, dan a cewarta fatarsa ta yi mata kama da irin fatar ?ar tsana da Bappa ya ta?a saya mata lokacin da ya je gembu wajen kakansa, da zai dawo ya saya mata kyakkyawar ?ar tsana fara tas, to shi ne take ganin fatar jikin Jaish ?in kamar na ?ar tsanan, bata yarda ba har sai da ta ta?a shi ta ji, sannan ne ta yarda ba ?ar tsana bace, dan tasan ?ar tsana roba ce, shi kuma ta ji nasa fatar da laushi sosai.

Yana a wannan hali da basu tabbatar yana raye ko ya mutu ba, haka Mahreen ta rin?a mulmula mashi kumatu wai akwai da?in ta?awa...........??

Kumatunsa ya yi mata laushi, kafin ta yi barci har da wani cewa Bappa kumatunsa laushi kamar breadi. (Ni kam nace ina Yah Jawad ya zo yaga yau yadda mace take mulmulawa Jaish sarkin kunya kumatu?? wlh idan ka biye Mahreen sai ka mutu da dariya ?? Jaish dai yau yaga ta kansa, ya fa?o hannun Mahreen sai yadda kuma hali ya yi??)

Na fara yin wani tunani fa, idan Allah yasa yana da rai ya farfa?o ma kenan haka zata rin?a ta?a mashi kumatu tana mulmulawa ta ce kamar breadi? Tab hmmmm.....??

MAHNOOR.

Tana juyowa suka yi ido hu?u da bappa da yake tsaye a bakin kofar shigowa. "Ina zaki je Mahnoor?". Ya fa?a tare da shigowa cikin ?akin.

Muryarta har kerma yake yi saboda tsoro ta furta. "Bappa Allah tsoronsa nake ji, ni har yanzu gani nake yi kamar aljani ne, dama Nenne ta ta?a gaya mun cewa akwai aljanu a kogin nan mu dai'na zuwa wajen ba Bismillah, to yau wlh na manta ban yi Bismillah ba ina ga shiyasa naga wannan aljanin, dan Allah Bappana kada ka ce na share ?akin nan ka ji? Allah ba zan iya ba".

Da yake ya san halinta da tsoro sai ya ce to ta bashi tsintsiyar bari ya sharo ?akin ya fitar mata da dattin sai ta share tsakar gidan. Ai a dubu ta mi?o mashi tsintsiyar tare da fita waje da sauri. Shi dai Bappa bai ga abin tsoro a tattare da Jaish ba, ba karya yana da kyau sosai, jinin larabawa, amma da yake shi Bappan yana shiga garuruwa da dama a fa?in Nigeria da Niger har ma da Cameroon, so wani lokaci yana ha?uwa da turawa da larabawa, ya sha ganin kyawawa sosai, har Nigerians kyawawa masu kama da larabawa da turawan ma ya sha cin caro da su, so kyan Jaish bai ?aga mashi hankali ba, haka ita ma Mahreen. Ko da yake wannan yarinyar kam me ma zai bata tsoro? Ina ga sai idan ta ga aljanin gaske kila ta tsorata.

Sharo ?akin ya yi ya fito mata da dattin, sannan ya bata tsintsiyar, da sauri ta kar?a ta fara sharar tsakar gidan. Wata yar yarinya da bata wuci sa'ar Mahreen bace ta yi sallama a kofar gidan tare da yaye labulen buhun ta shigo. Amsa mata sallamar Mahnoor ?in ta yi tare da ?agowa ta kalleta.

"Adda Mahnoor gwaggo Rabi ta ce in zo in tambayi meyasa baku zo karatun ba?"

Islamiya ce suke zuwa a gidan ma?ota kullum daga karfe uku zuwa shidda ake tashi, wata mata ce wadda suke cewa gwaggo Rabi ita ce malamar, naira 50 ake biya duk sati idan ta zago, shi ne ku?in islamiyar.

"Mahreen ce ta yi barci, ni kuma yau Bappa yana aiki sosai, bai zo wajen kiwo ya kar?eni ba sai yanzu na dawo, shiyasa bamu zo ba, amma zamu zo karatun dare In Sha Allah". Ta bata amsa tare da du?awa ta cigaba da yin shararta. Tom yarinyar ta amsa mata tare da juyawa da sauri ta koma islamiyar, dan ana can ana ta karatu.

Share gidan tsab ta yi kafin ta fito da wanke wanke ta wanke tas, da alama tana da tsabta sosai, ga nutsuwa. Bayan ta kammala wanke wanken ne ta nufi kitchen, sai da ta share shi tsab, sannan ta hau hura wutar itace ta ?aura tukunyar ?asa mai ?an girma tare da sanya ruwa rabi a cikinta, ta tada wutar sannan ta fito.

Tana fitowa Mahreen ma ta fito daga cikin ?akin Bappa tana zuba uban hamma kamar zata ci babu. "Adda Mahnoor ina abincina?".

"Kai Mahreen daga tashi? Ba batun yin sallah bare ki tuna yau bamu je islamiya ba, bare kuma wanka, ke dai abinci kawai daga tashi? To ga shi a rufe a cikin kitchen, idan kin gama ci sai ki zo mu je gidan Ar?o mu duba Nenne".

Tsalle ta yi ta dire kafin ta ce. "Wlh ni dai ba zan je ba, wai ke Adda Mahnoor bama zaki yi murna da Nenne ta tafi ba sai ki ce mu je mu dubata dan ta dawo? Ke wato ma baki damuwa da shegen masifarta ko? Tom ni ban son ta dawo, da sassafe ta tashi mutum da fa?anta da awaki, sai ta yi ta zagin awaki da karfi karfi kamar sun ce mata suna jin magana, duk ta bi ta tashi kowa daga barci, ni babu in da zanje, gara ma da Bappa ya kawo wannan aljanin, kinga yanzu dole ta koma gidan Ar?o da zama ai, ni kam ma aljanin kyau ya yi mun".

Baki Mahnoor ta saki tare da gwalalo ido tana kallonta, tasan halinta sarai fin hakan ma zata aika, amma abin da ya bata mamaki ta saki baki tana kallonta shi ne cewa da ta yi aljanin ma kyau ya yi mata, wato ya burgeta, ko tsoronsa bata ji ba.

Tana tsaka da tuna Mahreen ?in ta katseta da cewa. "Adda Mahnoor wlh kumatun aljanin nan kamar irin breadin da Bappa yake kawo mana idan ya yi tafiyar nan, idan kina ta?a kumatunsa zaki ji da?i".......... Hasbunallahu wani'imal wakil, Mahreen zata kashe mutun da dariya.

Zaro idanu sosai Mahnoor ta yi. "Kumatun nasa kika ta?a? Ke Mahreen ina kike son ki tsaya ne wai? Ai dolema kanki ya rin?a rawa, aljanu wasa ne, daga gani sun shiga kanki shiyasa baki tsoronsu, dole zan gayawa gwaggo Rabi idan muka je karatun dare, dan ta yi maki addu'a, yanzu dai zoki ci abincin ki je ki yi wanka sai muje wajen Nenne". Ta yi maganar cike da tsoron jin cewa Mahreen ta ta?a kumatun aljani.

Sake yin tsalle ta yi ta dire. "Wlh Adda Mahnoor ni ba zan je wajen Nenne ba, ke ni fa banson ta dawo nace maki".

"Mahreen kina da hankali kuwa? Wato duk nasihar da gwaggo Rabi take yi mana a kan bin iyaye ke bakya ji ko? Kina son Allah ya la'anceki ne? Mahaifiya fa? Wlh tun wuri ki yi istigifari sannan kizo ki wuce ki yi abin da nace maki mu gama aiki mu je wajenta, da take yin masifa da akwaki dake take yi ne? Ba shegen kunnenki na jin gulma yasa kike iya jiyota ba? Ni meyasa bana jin fa?ar safen nata da awakin?".

Turo bakin nan ta yi kamar zata sa kuka, cikin kuncin rai na bata son Nenne ta dawo ta nufi cikin kitchen ?in dan ta ?auki abincinta, yadda kuka san Nennen nan kishiyar mamarta ce ba mahaifiyarta ba, wai ta cika masifa.

Cigaba da aikace aikacenta ita kuma Mahnoor ?in ta yi, sai sauri take yi dan ta gama suje wajen mahaifiyar tasu a gidan kansu Ar?o kenan, shi ne mahaifin mahaifiyar tasu, kuma shi ne sarkin wannan ruga, kawu yake wajen mahaifinsu kuma, duk dangi ne.

Ita kuwa Mahreen abincinta ta ?auko ta zauna a saman kujera irin na zaman tsakar gidan nan ta fata ci tana turo baki dan bata son zuwa gidan kakan nata, kuma kakan nasu fa yana kaunarsu sosai, dan su ka?ai ne jikokinsa, amma da yake ita Mahreen bata son gaskiya, bata son ayi mata fa?a yasa ta tsanesa, dan kawai yana yi mata nasiha a kan ta nutsu.

??????????????????????????????????????

GIDANSU KHADIJAH ????

Yau kwana uku kenan da kai baban Zainab makwancinsa, wato gidansa na gaskiya.

Khadija dai shiru babu ita babu labarinta, su kuma dangin babanta basu ma bi ta kanta ba, bama su san tana nan ko bata nan ba, kuma basu damu da su sani ba, sun mayar da hankulansu kan zuwa station da hanyar kotu wai lallai dole sai an biyasu jinin Baban Zee da maman Zainab ta salwantar, sun kafe sam ba zasu ?aga kafa ba. Sadiq ya ji duk abin da ya faru, amma ya ?oye ya kasa iya gayawa mamarsu saboda tana da hawanjini ha?e da ciwon suga, yasan in ta ji me ya faru da maman Zainab zata iya ha?iyar zuciya ta mutu, ko hawanjininta ya tashi, shiyasa ya ?oye mata.

Ya zo Kanon amma an hana shi ganawa da ita, almost kafa uku yana zuwa cell ?in, amma sun hana ya ganta, tashin hankali iya tashin hankali ya shiga, wannan ba maganace da zai ?oyewa mamarsu ba, amma ya rasa ta yadda zai iya gaya mata, ko dan ta sanya maman Zainab ?in a cikin addu'a yakamata ya gaya mata, amma ya rasa hanya, bawan Allah ya rasa mafita.

Ita ma Zainab dake ?unshe a cikin ?aki tana fama da zazza?i mai zafi babu wanda ya kulata, basu bi ta kanta ba, ba dare ba rana tana cikin ?aki, bata ta?a le?owa ko parlourn, har ?aki Sadiq yake binta da abinci idan ya faki idanunsu Maman Haidar basa gidan, idan sun fita sai ya shigo gidan ya kawo mata abincin, sun hana shi shiga gidan ne yasa yake shiga a sace. Yanzu haka sai haukar neman Khadijan yake yi ba dare ba rana, har ma ya shigar da report, dan Zainab ta gaya mashi cewa Khadija tun ranar da maman nasu ta kashe babansu bata sake ganinta ba, tashin hankalin da Sadiq ya shiga sam ba zan iya fassara maku ba, kusan hauka ?an tahalikin nan ya yi. Ha?i?a ya tabka babban danasani na barinsu da ya yi ya koma Kaduna, kukan zuci yake yi yana fa?in laifinsa ne, da yana nan koma yaya zai hanata aikana wannan babban kuskuren.

Yarinyar nan Zainab duk ta fita a hayyacinta, ta dawo shiru bata magana, ko ka yi mata magana sai dai ta girgiza maka kai kawai ko ta gya?a ta, amma ba bakin magana, ta zama abar tausayi, har rama ta yi!.

Shi kam Haidar ma da alama baya garin, dan shiru kake ji, da yana nan dai zai ?an le?o koma yaya ne

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull