Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 76

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 76

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 76: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 76. Sai dai kuma da bappa ya tafi manyan dattawa ma suka tafi sai yan kallon suka…

1,168 words

Sai dai kuma da bappa ya tafi manyan dattawa ma suka tafi sai yan kallon suka fara tsoron Jaish ?in, su dama dan bappa suka tsaya, suna ganin kamar idan bappan yana nan ba abin da zai same su. Amma dai saboda tsabar soyayyar Jaish da salonsa ya burgesu sai basu gudu ba, suka tsaya ganin gulma.

Maganar Mahreen yasa ya farga tare da sauke ajiyar zuciya, a hankali ya kai tsinken kwallin cikin idanun nata, ?an kyaftasu ta yi saboda idanu basa son bako. ?an tsuke fuskarsa ka?an ya yi dan a tunaninsa ya ji mata ciwo ne yasa ta kyafta idanun, shi ne ya ?an tsuke fuska alamar sorry kenan.

Sosai ta ji da?i yadda har alamar tausayinta ya bayyana a saman face ?insa kowa yana iya gane hakan, godiya ta yi wa Allah. Jumma uwar soyayya and lecture ai antashi kanta, Jaish ya goge mata hadda, tuni ta karisa wajen saurayin nata da shi ma yana wajen, ba ko kunya ta gaya mashi haka zasu yi a ranar nasu bikin.

Ni ko nace ai dama babu wanda ya kaiku iya iyashege idan kuka ga abin da ya yi dai'dai da ra'ayinku.

Cikin nutsuwa, salo mai jan hankali ha?e da kula da tausayawa ya sanya mata kwallin. Shi kansa sai da ya kara shagala da kallon idanun nata, yaki sakar mata ha?a, saboda kwallin ya kara fito da hasken idanun nata suka yi tas, ta ?ara kyau sosai.

Inna Rabi ma fa ta gudu, Jaish ya ja ta ji kunya ta ware, yanzu matasa ne kawai suka rage a wajen, yara sun gogewa iyayensu hadda, sun ja iyayen sun ji kunya sun gudu.

"Hamma saura janbaki fa". Ta fa?a tana rufe idanunta, dan kallon da yake yi mata ya yi mata yawa.

Yadda ta motsa lips ?inta a kusa da shi sosai ta furta saura janbakin nan ba ?aramin tafiya da imaninsa ta yi ba, sai ya dawo da kallonsa a kan ?an bakin nata.

Mahreen dai sun fara shiga hakkinta, ita dai ayi a haura dutse su tafi a sakar mata ki?a, kun san dama idan suka haura dutsen ma ba wacewa jama'a zasu yi ba, cigaba da bidirin bikin za'ayi ana abubuwa har sai sun dawo.

"Hamma ka saka mata jan bakin mana da wuri, sai kallon bakinta kake yi kamar zaka cinye shi". Cewar Mahreen sarkin azar?a?i, yarinyar nan taki bari soyayya ta kullu, ta saka masu idanu.

Hannu ya mi?awa amaryar tasa a kan ta bashi janbakin dan shi bai san me shi ba. Idanunta a rufe har sai da ya ta?a kumatunta sannan ta bu?esu, a hanzarce ta mi?o mashi janbakin.

Ai irin wannan al'adun ma ko mutun baya son yarinya in dai kyakkyawa ce sai ya fara sonta, bare ma idan ya zo yi mata kwalliya yana kallon face ?in nan nata, ai dole ya afka duniyar lovayya, uhmmm dama ga Mahnoor da shegen kyau, Jaish ka shiga tarko, ni kuma princess Teema ba zan yarda ba, sai na raba wannan al'amari, dik wadda ta ji haushi ina gidanmu ta zo ta sameni.......????

A hankali ya bu?e janbakin ya fara goga mata a ?an lips ?in nata, dik sai ya nemi sukuninsa ya rasa, wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa ce take ratsa shi, bare ma idan ta ?an motsa lips ?in nata, dik sai ya rasa gane kansa.

Da kyar bawan Allahn nan ya iya ?arisa saka wannan janbakin, ta yi kyau sosai, dan bai cika mata abubuwan a face ?in nata ba, ka?an ka?an ya saka, ba'a ta?a yin amaryar da aka yi wa kwalliya mai kyan nata ba, kyanta ya ?ara bayyana.

Haba me zai faru? Ai tsalle Mahreen ta yi ta dire, ta ce allan baram daga yau Jaish ne zai rin?a yi mata kwalliya, wato dama ya iya kenan ko? Shi ne baya yi mata.

Ita kanta Mahnoor ?in ta yi mamakin yadda ake ta yaban kwalliyar tata, Jumma sai santin hakan take ta yi.

Shi dai kawu Ibrahim kunya ta kusa nutsar da shi cikin ?asa, ni kuwa nace ai wlh da Jaish yana ainahin Jaish ?insa, kuma yana son mace za'ayi wannan biki ai da bama zaku iya zuwa ba saboda kunyar da zaku sha na abin da zai yi. Yau da alama yaron Mommarsa ya mance da yana jin kunyar bappa ya wani tsare mashi ?a da kallon kauna!.

In takaice maku labari haka ya mi?e ya sa?eta cak a saman shoulder ?insa, ya kar?i wutar torch light da kawu Ibrahim ya mi?o mashi.

Shi ana goyon amarya dan kar a gaji da wuri, shi kuwa yana ?aukarta a saman shoulder ?insa, komai na al'adun nan sai da ya canza masu da nasa salon mai ?ayatarwa.

Dutsen ya rinkara gadan gadan, tana fa da tsawo da fa?in sosai dutsen, ga bishiyoyi da ciyayi sosai a sama, kun san haka duwatsu manyan nan suke, akwai bishiyoyi a kansu.

Haurawa ya farayi jama'a suna yi masu addu'ar adawo lafiya, ga mangariba ta fara kawo kai, ni kam nace Allah yasa ya ci angwancinsa a saman dutsen kafin ya sauko ba shikenan biki ya kare ba? Daga nan sai su wuce gida ya yi jinyarta, idan suka ga ya sauko sa ita bata da lafiya ai dole a dakatar da dik wasu tsarfa na al'adun nan a barshi ya wuce da ita gida, haba al'adu ne haka kala kala kamar ba gobe!! Ko ya kuka ce my people's? To mu dai bisu saman dutsen muga ya suke tafiya ato, dan mu sai mun le?a komai dallah dallah!!......??

Suna haurawa aka saki ki?ar nan nasu dai na yaren fillanci, habawa Mahreen ta ce ku bani waje, tuni ta afka cikin ?an'mata da samari aka fara ra?ashewa.

Su kuwa Jaish sun yi tafiya mai nisa kafin nan ya fuskanci lokacin sallar mangariba ta yi, da yake saman dutsen akwai ?an ramukan da zaku tarar da ruwan sama da ya taru a cikinsu, sai ya sauketa kasan wani bishiya da nufin ya ?auro alwala ya yi sallah, ya kunna wutar tocin da suka bashi ya mi?a mata a kan ta zauna ta jirasa bari ya yi alwala ya zo.

Ga garin akwai hadari sosai alamar ruwan sama za'ayi, da rabon ruwa zai yi wa wasu duka.

"Hamma nima zan bika na yi alwalar!". Ta fa?a a sanyaye.

Da yake safiya a saman dutsen sai anbi a hankali, idan ba haka ba in mutun ya yi garaje ?asa zai fa?a, sai ya mi?a mata hannunsa a kan ta zo ya ri?eta su tafi a hankali, dan kada ta je ta fa?i ?asa.

Cikin ?ari ?arin jiki ta mi?e ta ?arisa garesa, hannunta tasa cikin nasa, gaba?ayansu sai da suka ji wani irin yanayi na musamman da basu ta?a jin irinsa ba tana ratsasu.

Ri?eta da kyau ya yi suka fara tattakawa zuwa wajen da yake zaton zai samu ruwan.

"Hamma ina jin................

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...???????

??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull