Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 75

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 75

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 75: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 75. In takaice maku labari dalilin mutuwar maman Mahnoor ?in ya sanya zuciyarsa…

3,362 words

In takaice maku labari dalilin mutuwar maman Mahnoor ?in ya sanya zuciyarsa ta ladabta, tun daga lokacin da ta kwanta dama ya shiga damuwa mara misiltuwa, har jinya sai da ya yi, daga wannan lokaci ya rin?a neman gafara a wajen Allah, ya kuma roki Allah da ya sassauta mashi wannan zuciya tasa, yasa a masallaci aka yi mashi addu'a, so a lokaci ne Allah ta kar?i addu'ar tasa zafin zuciyar ta tafi, ya zama so silent, dama can mutumin kirki ne, zuciyar ce matsalar.

A takaice shi ne kuka ga ya zama haka, dik abin da yake yi wa mutane na kyautatawa a yanzu zaku ji yana cewa Allah ya kai ladar wa maman Mahnoor, ita yake yi wa hidima, wannan dalilin yasa yake yiwa Mahnoor ?in kauna ta daban, a takaice kenan yadda aka yi ya zama na kirki kuma na daban a cikin kauyen nasu, sannan mai ?an wayewa dai'dai gwargwado, dan haka mu koma kan labarinmu.

Saman wani benci irin dogayen nan Inna Rabi ta zaunar da Mahnoor da kanta a ?asa, shi ma bappa ya sha sabon ?inkin kayan sallarsa da ya ?inka, dama ya ?inka ya ajiye sai sallah ta zo ya yi amfani da ita, haka yake yi kowace shekara, yana ?inkin sallah da wuri ya ajiye, to a wannan karon dai sara ta zo a kan ga?a, ya samu na shagalin biki.

Kowa a wajen ya yi kwalliya sosai, wasu dan cin nama suka zo, wasu dan ganin gulma, wasu dan Allah, wasu dan suga aljani Jaish, wasu kuma dan suga shin mijin Mahnoor zai yi nasara ne ko zai fa?i, wasu dan kaunar da suke yi wa bappa da kyautatawar da yake yi masu. Kowa dai da abin da ya kawowa. Sai gutsiri tsomi ake ta yi a kan Jaish ?in.

Kada ku so ku ga Mahreen kanwar amarya, idan kuka ganta na tabbata sai cikinku ya yi ciwo saboda dariya, sai hidima take yi, ga shi ta je kusa da wuta zata ?auko namar da ake gasawa, dan ita tana son abincin wajen biki hajiya mandiya ba.

Aikuwa tana zuwa ta ha?a uban zufa, kada ku so ku ga yadda power face ?inta ya zama, abin na manya ne, kawalliyar fa?arta wato Zainabu Abu ce ta matso kusa da ita tana rokarta nama.

"Ki je ki ce in jini a baki". Ta fa?a cikin nuna isa, irin ita ce fa kanwar amaryar nan ta bada umarni dole abi. Ga shegen son girma kamar wata gembu.

Labarina yana da tsawo, ba zan tsaya ?ata lokaci a wajen shirirtar ?an kauyen nan ba, dan wlh akwai labarai a gaba, yanzu wasan zai fara, ba'ayi komai ba, dan jiga jigan shegun ma basu bayyana ba, akwai sauran tafiya kafin mu kai kansu, sai a fara buga wasan, dan haka ba zan tsaya cinye space da nake da shi a nan ba, so bari mu duba al'adun nan nasu in short, dan ma akwai abin da idan naje book 3 zan dawo dubawa a wajen bikin ne ya sa zan tsaya bada labarin, dan in mun je gaba in na tuna maku da wajen biki anyi kaza ku gane!!.

Sai da suka ci suka sha, nama kamar hauka, masu kwasa suna kaiwa gida sun kwasa, anyi gashi sosai.

Jaish dai yana zaune kusa da bappa, kansa na kallon ?asa, dan ya gaji da kallonsu ya ce, ga shi kuma ya yi wa bappa alkawarin zai yi hakuri ayi komai da shi tsab a gama, dama tun kafin so zo wajen sai da bappa ya rokesa da ya yi hakuri ya cika al'adunsu, shi kuwa ya ce babu abin da bappa zai nema a wajensa ya gagara yi mashi, dan haka ya yi alkawarin tabbas zai yi iya ?o?arinsa ya yi abin da ya dace, shiyasa yanzu da ya gaji da kallonsu ?in ma haka ya jure ya yi ?asa da kai bai tashi ya bar wajen ba.

Mahreen tana zaune kusa da Mahnoor, Jumma da ta ci kwalliyarta sosai ita ma tana zaune a ?ayan gefenta, sun sakata a tsakiya kenan, dan bata da ?awaye, Jumma ce kawai kawarta, ita ma saboda tana zuwa Islamiya a gidansu yasa suka saba sosai har haka.

Su Inna Rabi suna kan tabarmar a cikin runfa, jama'a suna zazzaune shiru. Kun san fa yanzu android phone ta ratsa har kauye, so a nan ma akwai ?an gayu masu vivo, ga wani ?an iskan Mp ?insu kato mai kama da irin manya manyan Radion nan na masu tallar maganin basir a kasuwan nin nan.........??

Mp suka kunna, suka sanya wakar sauta fasitaka wa?ata mivima ta metu, wai kun san fassarar abin da ake fa?a a wa?ar nan kuwa?.....??

Sai chashewa ake yi, ga matasan mata da maza sai rawa suke yi a gefe, kun san sun iya caku?uwa mata da maza su yi ta chaskale rawa abinsu, wlh yadda suke rawar tamkar wa?an da aka sanyawa battery, kalan ?an tsana masu magana, sai wani ka?a kayuka da dogayen wuyoyi suke yi.

Ai Mahreen ta ce baku iya ba ku bani waje, wani irin yawan da yarinyar nan take yi yadda kuka san rawan shegun karuwai, sai Allah ka?ai ya san mata daga ina ta koyo irin wannan rawa haka, yadda kuka san indiyawa masu rawa a club, har da wani girgiza tamkar wata mai cutar farfa?iya, dama tasa jan power ta zama irinsu.........??

Abin ba'a magana, a tsakiya suka sakata sai tikar uban rawa take yi, Mahnoor kuwa sai satar kallon angon nata take yi, yadda ta ga ya yi ?asa da kai sai ta gane a dame yake, an takura shi dayawa, shi baya son hayaniya, dik sai ta ji tausayinsa ya kamata.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A..???????

Da misalin karfe 5 dai'dai Inna Rabi ta ce a dakatar da wannan ki?an, dan lokaci gudanar da abubuwa ya yi, ai anci an sha, kuma an ?an watsa jini wajen ra?ashewa, dan haka yanzu saura a nutsu ayi kallon amarya da ango, a kallah yadda zasu kula da junansu.

Bisa al'adar dama a halin yanzu yan uwan miji ne zasu fara bawa amaryar umarnin da ta ?auki kwano ta ?ebowa mijinta namar da aka gasa ta zo ta bashi a baki, su kuma nasu kenan, to kun ga shi Jaish bashi da ?an uwa a wajen, dan haka sai Inna Rabi ta wakilci yan uwan nasa a in da ta yi wa Mahnoor wannan umarnin. Dama bappa ne ya ce mata ta zama uwa kuma ?an uwan Jaish ?in a wajen taron.

Baiwar Allah kunya kamar ?asa ya bu?e ta nutse ciki, haka ta mi?e tsaye, idanun gaba?aya jama'a a kanta, tamkar zata kurma ihu, Jumma ya ?an ri?ota suka nufi wajen da Inna Rabin take zaune cikin mata a ?ar?ashin runfar da aka kafa saman tabarma.

Sabuwar plate dal a ledarta Innar ta basu, da yake bappa yasan al'adun nasu sai ya shirya komai da kansa, har plate ?in dik shi ya saya, dozen ya sayo, sai ya ajiye mata sauran a cikin bukkarta. Dik wannan bidiri da ake yi Nenne bata nan, ko le?au taki le?owa, harda Ar?o yana wajen saman kujerar sarautarsa na musamman, amma ina bakar zuciyar Nenne ya hanata zuwa. Kun san yan uwan Ar?o su ne ?an uwan bappa, dan shi ne kawunsa, ?an uwan maman Mahnoor da nace maku sun zo yan uwan Inna kakarta ce. So shi Ar?o ya zo, ?an uwansa ne suka ki zuwa.

Wajen gasa namar ta nufa, a tare da Jumma suka je, gaba?aya masu gashin namar matsawa suka yi suka bata wajen, dan da kanta zata zuba mashi, da ?an uwansa suna nan zasu gani ne tasan abu mai kyau ne ko bata sani ba, idan ta za?o tsokoki masu kyau da laushi to tasan abu mai kyau kenan, ana sa ran abubuwa masu kyau zata rin?a bashi idan suka tare a gidansu, idan kuma ta za?o irinsu hanji da huhu tun daga nan ?an uwansa zasu fara jefanta da maganganu ace ya yi za?en tumun dare, bata san abu mai kyau ba.

Yo Mahnoor da take nutsestsiya mai hankali yaushe zata ?auko abu maras kyau?. Dama dai Mahreen ce kila ta za?o mashi ra'ayinta, amma Mahnoor jajayen tsokoki masu kyau da laushi ta za?o mashi, da zafinsu, sai titirin hayaki yake yi, ga shi sun gasu sosai.

Tun da ta fara za?ar namar bappa ya tashi ya bar wajen, dan kunya ba zata barshi ya iya kallonsu ba, dama saboda Jaish ?in ya zauna a wajen, a gefensu Ar?o yakamata ya zauna, shi kuma Jaish dama da abokansa zai zauna, amma da yake bashi da aboki ne sai yasa bappa da kawu Ibrahim kanin maman Mahnoor ?in suka zauna a tare da shi, to kunga a matsayin bappa na uba ai ba ya zauna ayi wannan abin da ake yi tare da abokan ango ayi da shi ba ko?.

Shi ne yasa ya bar wajen, ya bar Jaish ?in da Ibrahim, shi ma Ibrahim ?in yaso barin wajen a matsayinsa na kawunta, amma bappa ya ce mashi ya daure ya zauna tun da Jaish dai bashi da kowa........ Wayyo wai ina Yah Jawad, ya zo ya ga ikon god yau, ina ga da idan Jawad ya fara dariyar mugunta sai ya suma saboda dariya, dan ?an duniya ne, yana can yana cin amanar Yah Rizwan, ya sanya Chuchu a ?aki har da kashe wuta....??

A gabansa tazo ta tsugunna ita da Jumma, kansa ya ?ago ya kalleta, dik sai ta ji tsoro da shakkarsa ya kamata, kasa ?aukar wukar ta yi ta yanko ta sa mashi a baki.

Sai jira jama'a suke yi su ga kwakwaf. Mahreen sarkin wutar ciki ne ta ce. "Adda Mahnoor ki bashi mana". Wato ita Mahreen an katse mata jin da?i ne, ayi maza ayi dan a sakar mata ki?a ta cigaba da taka rawanta, ta cire gyalen kayan nata ta ?aura a kunkuminta, rawa ne ya yi da?i, sam kada ku ga laifinta.

Yaufa wani ?agun kai na daban take ji da shi, dan ta saka sabon kaya kuma mai kyau na yan birni, sai kallon ?askanci take yi wa kowa. Mahreen manyan ?asa.

Dafa shoulder ?inta Jumma ta yi alamar ta daure ta bashi, shi kuwa kallon face ?inta kawai yake yi, tabbas yana jin da?in kallonta, saboda yanayin da yake shiga na kokarin tunano Zunaira da yake yi.

Kamar zata yi kuka ta sanya hannu ta ?auki wukar, ?an ?arami ta yanka mashi, sai tiriri yake yi, ji take yi kamar ba zai kar?a ba ko ta bashi, kamar zai yarfata a cikin mutane, shiyasa ta kasa iya fara bashi da wuri.

Aikuwa ta gudu bata tsira ba, dan kuwa ko da ta kawo mashi saitin bakinsa sai yaki bu?e bakin, ya tsareta da idanu yana ta kallonta.

Sai kallonsu jama'an suke yi suna jira su ji dalilinsa nakin karbar nama. Kamar zata mutu saboda kunya, ga shi ya ki kar?a abin ya kara kunyatata sosai.

?an ta?a shoulder ?insa Ibrahim ya yi, nisawa ya yi tare da dawo da kallonsa a kan Ibrahim ?in, alama ya yi mashi da ido a kan ya kar?i namar da take bashi, kallon namar ya yi da kyau, kamar ba zai kar?a ba, sai kuma ya tuna yadda suka yi da bappa kafin su zo wajen, hakan yasa ba dan ya so ba ya bu?e baki.

Lokacin da ta zo saka mashi a bakin sai da ta ji duniya ya yi wani irin juya mata, saboda a lokacin ta matso sosai ta kuma kalli face ?insa da kyau, hakan yasa ta ji kamar wadda aka jonawa shocking a jiki.

Kar?a ya yi ya fara taunawa a hankali cikin nutsuwa.

A ?a'ida sai ta bashi namar ya ci ya ?oshi, amma ina shi ya karya masu doka tun a karon farko, dan kuwa da ta yun?ura zata yanko mashi na biyu, hannu ya ?aga mata alamar baya da bu?ata.

Abin ya yi matu?ar bawa jama'ar wajen mamaki, ba'a ta?a yin angon da ya yi irin abin da ya yi ?in ba. Bappa kam da yasan halin kayansa sai bai wani damu ba.

Nan take aka fara tsegumin anya angon nan yana sonta kuwa? Anya ba kawai bashi ita aka yi ba? Kun san jama'a da dama burinsu suga laifinka ko ka?an ne su yi ta ririta shi wa duniya, aikuwa haka aka yi, su Nenne dake gida ma har sun samu labarin abin da Jaish ya yi a wajen bikin, ya ce ba zai ci abin hannun amaryarsa ba, wannan ai cin mutunci ne.

Da yake a yanzu yana jin fulatancin sai yake tsinkayo maganganun mutane ?ai?ai a cikin kunnensa, ya ji sai aibata abin suke yi, har da masu cewa anya wannan ba zaluntar Mahnoor ?in zai yi idan aka dam?a mashi ita ba kuwa?.

Hakan ta ?an sosa mashi rai, da farko bai yi niyar yin al'adun nasu ba, amma jin yadda jama'a suke ta faman ririta kin kar?ar namar da ya yi har suka sanya Mahnoor ?in kuka sosai ne yasa ya kuduri niyar zai yi ko dan ita Mahnoor ?in da take marainiyar Allah.

Tana tsugunne a gaban nasa ta kasa mi?ewa saboda tsananin kunya, kuka ta fara yi jin yadda jama'a ke tufa albarkacin bakinsu a kanta, wasu sun yi mata dariya, ?an uwan bappa da basu a wajen, tsintar labarin ma suka yi har da cewa Allah ya kara Allah yasa angon ma ya azabtar da ita dan kawai Allah ya ?addara ba rabon Faisal bace ita ?in shikenan daga samun labari suka hau banka munanan fata.

Sam ran bappa bai ji da?in yadda jama'a suke ta zagin ba, ba'a ta?a yin amaryar da aka zaga haka kamar ita ba, abin ya sosa mashi rai!.

Kwatsam suna tsaka da surutansu sai ya gwada masu shi ma ?an duniya ne, ya yi abin da ya ja suka rufe bakunansu tsit. Abin da ya yi kuwa shi ne yadda take tsugunne a gaban nan nasa tana kuka sai ya kai hannu ya ri?o shoulder ?inta, ?agota ya yi tare da zaunar da ita a kusa da shi in da bappan nata ya tashi kenan, dama shi zamansu a kusa da shi ba bakon abu bane a wajensa, kada ku manta shi ?in aljanin Mahreen ne, abin da har saman cikyarsa Mahreen ?in tana zama. So bai ji wani shakkar zaunar da ita a kusa da shi ba!.

Kar?ar plate ?in namar dake hannunta ya yi ya mi?awa Jumma dake tsugunne a gabansu ta mi?e da shi ta mayarwa Inna. Sannan ya hau share mata hawaye da kyawawan fararen tafukan hannunsa tare da nuna alamar rarrashi. Daga karshe ma sai ya ?an jawota jikinsa, ya kwantar mata da kanta a saman gefen kirjinsa yana ?an bubbuga bayanta da hannunsa ?aya alamar rarrashi.

Habawa ji kake tsit ya kashe bakin masu cewa baya sonta, ba'a ta?a yin irin angon da ya yi hakan a kauyen ba, harda runguma e lallai a cewarsu ya tabbata kula na daban zai bata.

Bappa ransa fes, ya ji matu?ar da?i hakan, dama shi bai ji haushin abin da Jaish ?in ya yi da farko ba, haushin jama'ar kawai ya ji, dan in baku manta ba shi yana ganin kamar suna son junansu, so yasan Jaish yana sonta, shiyasa bai damu ba. Yanzu kuma da ya rarrasheta sai abin ta ?ara faranta mashi rai.

Shiru ta kwanta a kirjin nasa tana shesshekar kuka a hankali hankali, gaba?aya ta rasa a wani duniya take, ta rasa farinciki take ji ne ko bakinciki.

Ihu jama'a suka fara yi suna yi masu tafi suna fa?in wai ya kai namiji.

Inna Rabi ce ta katse masu ihun nasu ta hanyar kawowa Jaish ?in kayan kwalliya cikin tray a gabansa, wai ya yi mata kwalliya su hau dutse, dan bappa ya cire batun girki a ciki, saboda shi da kansa yasan Jaish kam ba zai iya yin girki ba gaskiya, dan haka kada su wahalar da shari'a.

Ba musu ya kar?i kayan kwalliyar, irin kayan kwalliya ce dai ta kauye. Shiru ya zubawa kayan kwalliyar idanu yana kallonsu, shi da bai san me ma ake yi da su ba, bai san a ina ake sanyasu ba.

Muryarta cikin kuka ?asa ?asa ne ya katse mashi tunani da cewa. "Hamma zan taimaka maka". Tana daga kwance a jikin nasa ta yi maganar....... Eye su Mahnoor an fara sanin da?in duniya, har da wani zata taimaka mashi, eye amarya ta angonta kenan, da gaskiyarki taimaka mashi kada ayi mashi dariya.

Kawo mata kayan kwalliyar ya yi gabanta alamar to ta taimaka mashi ?in, dama a cikin tray ?in silver aka zuba su.

A hankali ta ?an ?ago kanta, hannunsa ?aya yana ta bayanta yadda yake dan bubbugata a hankali, jama'a sai kallonsu suke suna mamaki, dan su dai sun san ba haka ake wannan al'adar ba, Jaish ya kawo masu sabon salo, komai sai ya canza da nasa salon, su fa amarya tana zaune saman kujera ango zai tsugunna a gabanta ya hau yi mata kwalliya babu mai taya shi suke yi, amma shi da yake nasa na daban ne amaryar har taya shi zata yi, abin nasu ya bada kala.

Powder ta ?auko daga cikin kayan, kasa ?asa yadda ko kawunta dake gefensu ma bai ji me take fa?a ba ta fara yi mashi bayani a kan me powder da yadda zai sanya mata.

Tana kai karshen maganar ta ?ago ido dan ta saci kallonsa, karaf suka ha?a idanu, dan ita yake kallo.

Da sauri ta yun?ura zata sunkuyar da kanta, ?aura tray ?in ya yi a saman cinyarta, sannan ya ri?o ha?arta da hannun nasa, ya ?agota suna fuskantar juna, ya iyahi me jama'a zasu yi banda ihu, sun ga salon Jaish ?in ma ya fi nasu bada kala............

Sosan powder ya ?auko da hannunsa dake saman bayanta, kurawa face ?inta idanu sosai ya yi, har wani irin yar ya ji a jikinsa, tsikar jikinsa gaba?aya sai da ya tashi, ji ya yi kamar bashi da lafiya, amma haka ya daure ya fara shafa mata powder.

Tafi jama'a suka fara yi suna ihuuu alamar jin da?i. Ka?an ya shafa mata, sannan ta nuna mashi yadda zai sanya mata kwalli.

?aukowa ya yi da nufin yasa mata, a wannan lokaci ya zamar mata dole ta bu?e idanu su kalli juna ido cikin ido dan ya iya saka mata.

Da kyar ta iya bu?e idanun nata, sai kuma me? Sai ga Mahnoor ta mace da kallon face ?insa, ta mance da kunya, shi ma macewa ya yi da kallonta, ya mance da cewa kwalli zai sanya mata, idanunsu suka sar?afe juna...... Da alama wa?an nan ma'auratan sun afka duniyar sama jannati, waye ya ce soyayya karya ce? To koma me dai ina da Maltina ta mai sanyi ni dai??

(Sai dai matsalar angon baya cikin hayyacinsa, ko ya zai kasance idan ya dawo dai'dai??? Shin zai kar?eta a matsayin mata ko a'a? Mu je dai zuwa, lokaci zai warware mana komai.)

Sun macewa kallon juna har sai da Mahreen ta ce masu. "Hamma ka saka mata kwallin mana, ni fa ina so ne ku gama ku haura saman dutsen nan mu kuma a saka mana wa?a mu cigaba da rawanmu har ku dawo, amma kun tsaya kuna ta wani kallon kanku, to ba kun san juna ba dama?".

Mi?ewa shi kuma bappa ya yi ya bar wajen ma mai gaba?aya, ya nufi gida abinsa, ya yafe murnar da za'ayi idan Jaish ya gama cike wa?an nan al'adun nasu, dama idan ango da amarya suka cike al'adun, akwai wata murna na musamman da iyayensu zasu yi dan ?a?ansu sun cancaci zama a tare kenan, to shi dai ya yafe wannan murna, kunya tasa ya bar wajen da sauri.

Shi ma Ar?o dik da yake matsayin kakansu yau Jaish yasa kunya tasa ya bar wajen, da sauri, dikka manyan iyayen dake wajen sai da suka watse, dan kunya, su a yadda suke yin nasu al'adar ba wata soyayya da ango zai nuna bare har aje ga batun kallon juna da runguma, suna yin nasu ne tamkar dai yaya da kanwa haka amarya da angon zasu kasance, kawai shi ya zo ya goge masu hadda ya wani tsare yar mutane da ido, ai dole iyaye su matsa su basu waje.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull