Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 74
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 74: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 74. Motar saura passenger hu?u dama, da zuwansu yanzu saura mutun biyu, zama…
3,293 words
Motar saura passenger hu?u dama, da zuwansu yanzu saura mutun biyu, zama Khadija ta yi a cikin motar ita kuma Zee ta ce bari ta je ta tambayi in da ake canza ku?i zuwa ku?in Nigeria ta canzo masu su samu su biya ku?in mota.
Mai motan da zai ?aukesu ?in ta nema, Allah ya taimaketa sai ta nuna mashi dollars dubu ?aya ta ce tana son ta je ta canza ta izuwa ku?in Nigeria ne dan ta biya ku?in mota ya nuna mata wajen da ake canzawa, Allah ya rufa mata asiri bata nuna mashi dikka ukun ba, kamar tasan ku?in darajarsu ya wuci tunani, kuma bata sani ba, kawai dai ta za?i ta nuna mashi guda ?ayan ne.
Aikuwa zaro idanu ya yi waje, cikin ka?uwa ya tambayeta shin tasan nawa ne a hannunta kuwa?. Girgiza mashi kai ta yi alamar bata sani ba.
Ganin e da gaske bata san darajan ku?in bane yasa ya ce mata zai canza mata to, duniya babu gaskiya, gaskiya ta yi ?aranci, zalinci ta yi yawa, ba amana, bawan Allahn nan bai ji tsoron Allah ba ya ?auki dubu goma ya bata ya kar?i dallar da darajarta ya kai almost 1.5m da dauriya.
Da yake bata san darajarta ba sai ta kar?i dubu goman ta yi mashi godiya, sai ta sake tanbayarsa nawa ne ku?in motarsa, ko tsoron Allah babu har da wani cewa ba damuwa ya yafe mata, wannan ku?in da ya bata su yi ku?in mashi idan sun sau?a a Kd.
Ko da yake ya fi wasu fa, da wani ne ma a duniyar yanzu wlh da kwace ku?in zai yi ya gudu, gara shi ya basu 10k dan a tunaninsa iya ku?in hannunsu kenan, ya ?an ji tausayinsu kada ace basu da wani ku?i su sau?a a tasha su rasa ya zasu yi, shi ko tsoron kada gaskiya ta bayyana ko kuma ?an uwansu su zo ?aukarsu a tasha su gane gaskiya a kamasa ma bai yi ba, shi dai yana jin da?i ya yi cuta mugu, shi dai ya samu ku?i a tunaninsa.
My people's wani fata zaku yi wa Zainab and Khadija a halin yanzu? Ga su dai zasu ?auki hanyar Kaduna, me kuke tunanin zai faru? Shin zasu ha?u da Sadiq ?in nasu kuwa? Zasu kai labari ko yaya? Mu dai je zuwa.
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...???????
??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????
??RAWANIN ?? ZALINCI ????
????????????????
FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????
?????????? 12/11/2024.....??????
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????
??ZANGO NA BIYU....??????
__________38
In short haka mota ta tashi da su suka nufi Kaduna, har a lokacin babu wadda ta yi tunanin ina jakar ku?insu yake? Da gaske yana cikin akwatin ne ko babu, su dai kawai sun tafi.
_______________________________???? _______________ JIMETA YOLA?????
Tsab bappa da Jaish suka ha?a bukkar da shi Jaish bai san ta mecece bace, shi dai ya taya bappa aiki kawai.
Suna kammalawa ana kiran sallar azahar, alwala bappa ya yi tare da ce mashi ya yi alwalar shi ma su je masallaci.
Kin yi ya yi ya samu waje saman dutsen goge kafarsu ya zauna, kamar dai mai jiran wani abin, bappa kuma da ya kammala alwalar sai ya nufi masallaci a zuwa idan Jaish ?in ya kammala ya same shi a masal.
Zamansa ya yi saman dutsen da ya zauna da Mahnoor ?azun, kamar mai tunanin wani abin ya buga uban tagumi a tsakiyar rana, ya yi shiru.
Tana ?ingisa kafa ta fito daga cikin ?akin na bappa, yana zaune ta zo zata wucesa, da idanunsa ya yi mata alamar ina zata je a tsakar ranar nan haka? Ga shi rana ta take sosai.
Kitchen ta nuna mashi tare da ce mashi. "Ruwan wanka zan ?aura maka hamma".
Alama ya yi mata da hannu a kan ta koma ?aki kada ta kara jin wani ciwo a kafan nata, kada ta fama ciwon nata.
"To hamma idan na koma waye zai sa maka ruwan wanka?. Ka gani dai kai baka iya sakawa ba, ga shi ko masallaci kaki zuwa saboda baka yi wankan ba, bari zan iya ?aurawa ai sai kai kuma ka juye to idan ya yi zafi".
Tambayarta ta hanyar alama da hannnu ya sake yi a kan ina Mahreen ne take? Ita bata iya aikin komai ba face barci, yanzu ma tana can tana zuba barci ne.
"Mahreen tana barci, kuma koda idanunta biyu ma bata iya hura wuta ba, bari dai na ?aura maka ?in".
Kai kawai ya jinjina mata ba tare da ya sake yin wani motsi ba.
Wucewa ta yi izuwa cikin kitchen ?in, kafarta sai zogi yake yi mata, haka ta tsugunna ta hura wutar, ta ?auko tukunya ta zuba ruwa izuwa rabi a ciki, sannan ta yunkura zata ?auka ta ?aura a saman wuta, sai kuma ta ?asa, saboda a kan yatsun kafafunta take tsaye, idan ta ce zata ?auki tukunyar yatsun nata suna iya karyewa ma, dan kun san dai ba zasu iya ?aukar gangan jikinta cikin sauki bama bare kuma ace ta sake nauyinta sosai zata ?aga abu mai nauyi, akwai wahala.
Du?awa ta yi a karo na biyu zata ?auka, kamar daga sama taga farar hannunsa yasa ya kar?i tukunyar, a saman wutar ya ?aura mata ba tare da ya yi mata wata alama ba, ya juya ya nufi waje abinsa.
Da kallo ta bi bayansa tana tunano zantukan Jumman Inna Rabi, ita kanta yanzu sai ta fara ganin kamar ya fi Hamma Faisal ?inta sosai, da soyayyar Faisal ya rufe mata idanu yasa bata ganin kowa da wani fasali idan ba shi ba.
Komawa ?aki ta yi ta kwanta, tana jinsa lokacin da ruwan ya yi zafi ya juye da kansa ya ?ebo na sanyi ya surka. Wanka ya je ya yi abinsa, yanzu fa shi ma ya saba da abubuwa dayawa nasu, yana cin irin abincinsu, yana kuma shan nono da fura, rayuwa kenan, kana naka Allah na nasa, dik wanda kuka ga yana ihun shi bai iya abu kaza ba bai iya abu kaza ba, hmmmm bai je in da zai iya dan dolensa bane.
Bappa kuwa tun da ya yi sallah bai dawo gidan ba, kasuwar kauyen gabansu nan ya nufa, kauyen tafi nasu girma, har ?an primary school suna da shi, so akwai kasuwa mai dan girma, a nan suke sayen abubuwa.
Abubuwan amfanin gida irin nasu na kauye ya je sayawa Mahnoor ?in kamar yadda yake a al'adance, har da su samiru dikka, ya saya masu katifa da dik abin da za'a bu?ata.
Ko da ya dawo gidan Jaish baya nan, ya tafi yawonsa cikin kauye. Cikin sabuwar bukkar da suka ha?a ?in ya shigar da kayan, Mahreen ta tashi barci a lokacin, ita ta taya shi aiki, ?an uwansa dik sun ki zuwa in da yake, saboda ya hana Faisal Mahnoor ya bawa wani, abin ku da kauye wai gaba suke yi da shi, da yake su basa raina abin yin gaba, ga basa manta gabar komai daren da?ewa.
Shi ne yasa suka ki zuwa taya shi murnar auren, bawan Allah ko a jikinsa, a cikin zuciyarsa abin ta yi mashi zafi, amma a fuska sam bai nuna hakan ba.
Haka suka shirya komai tsab shi da Mahreen, Mahnoor tana barci. A daren ranar dai a ?akin bappa Jaish ya kwana kamar yadda suka saba, ita ma Mahnoor a ?akinsu ta kwana, dik da an ha?a masu ?akinsu bappa ya ce sai anyi biki an gama za'a kaita ?akin nata.
Washegari da safe suka tashi da shirin yin biki, sai hidima Mahreen take yi, tana ta up and down, shige da fice, ba zama busyn body, abin yi ya samu Addarta da Hamma aljaninta suna aure.
Bappa kuwa sai lalla?a Jaish yake yi yana rarashinsa ha?e da rokonsa da ya yarda ya je wajen bikin nan ya kuma kar?i al'adunsu hannun bibbiyu. Ba dan ya so ba ya amince da hakan, sai dan yana matu?ar ganin girman bappan sosai, yana kuma jin kunyarsa!.
Ku?i sosai da a kallah zasu kai 100k bappa ya dam?awa Inna Rabi da ta je cikin gari ta yi wa Mahnoor sayayyar kayan kwalliyar da za'ayi mata kwalliya a wajen bikin, da kuma kayan sakawa, sannan ta sayawa Jaish ?in ma kayan sakawa da dai dik abin da ya dace.
Bawan Allahn nan shanunsa har guda uku ya sayar yau da safe dan ayi hidiman bikin nan cikin gata da birgewa. Kun san bappa fa yana yawace yawace, so ya ?an waye abinsa.
After some hours.
Bayan sun yi sallar la'asar, zaune take ita da Mahreen a cikin ?akinsu, sun yi wanka, ita Mahnoor tana shafa mai a fatarta, ita kuma Mahreen tana zabga powder a fuska kamar dai yadda ta saba.
Sallama aka yi masu a kofar ?akin nasu, kallon juna suka yi suna mamakin jin muryar Inna Rabi yau a gidansu, dan bata zuwa saboda masifar Nenne, kuma su sun mancema yau ake bikin.
Mahnoor ce ta danne mamakin nata tare da amsa mata sallamar, cikin ?akin ta shigo kai tsaye, sai kallonta suke yi har cikin ido, Mahreen ta zaci ma ta biyota ne har gida ta zaneta dan yau basu je islamiyyar ba, dan tasan ita ?in uwar yin laifi ce acewarta.
"Inna ina wuni". Cewar Mahnoor.
Fuskarta cike tab da fara'a ta amsa da. "Lafiya lou Noor".
Mahreen ma ?aga mata gaisuwa ta yi tana cigaba da labtaka powder dai.
"Mahreen a rage powder nan haka mana". Inna ta fa?a tana kallonta.
"Ai sai ki ?arisar maku da shi a tashi ?aya, ke baki san ka?an ka?an ake shafawa bane? In ma kika shafa dayawa ai ba zaki yi kyau ba". Ta kai karshen maganar tana maido da kallonta a kan Mahnoor.
Baki ta turo gaba. "Inna dandali fa zan je, bappa ya ce in je in same shi a can, kin ga kuma yau auren Adda Mahnoor ?ina za'ayi, dole na fi kowa kyau". Kamar zata yi kuka ta kai karshen maganar.
Sai a lokacin Mahnoor ta tuna ashe wai bikinta ake yi yau.
"Dik da haka a dai rage powder, idan kina son ki yi kyau ma ai ka?an zaki saka, sai ki fi kyau haka".
To kawai ta amsa kumatu a kumbure, ita a dole bata ji da?i ba za'a rage mata make up ?inta.
Dawo da kallonta a kan Mahnoor da ta takure waje guda Innar ta yi, ta wani ha?e jikinta waje guda, saboda daga ita sai ?aurin kirji, mai take son ?arisa shafawa ta sanya kaya, amma Inna tazo tasa ta jin kunya, sai ta kasa iya ?arisa shafa mai ?in ma, ta zauna shiru kanta a ?asa.
"Mahnoor ki karisa shafa man mana, jiranki fa muke yi mu tafi". Cewar Innar.
To ta amsa kanta a ?asa, ta kasa iya ?agowa, tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta kai hannu ta ?ebo man ta cigaba da murzawa a jikinta kunya kamar ta shige cikin ?asa, ita da kullum ba dare ba rana tana tare da hijabi a jikinta, yau kawai Inna ta zo ta sani kalleta da ?aurin kirji, dik sai ta ji babu da?i.
Ni kam na ce Jaish dai ya ji da?i wlh, ya samu matar da bappanta ma rabonsa da ya kalli iya wuyarta ma tun da ta fara wayo, kullum cikin hijabi, ta killace jikinta, ko mata ?an uwanta bata yarda su gani ba bare maza, ko Mahreen bata samun ganinta babu hijabi, yau ?in ma ta wanke hijabin ne ta shanya yasa Inna ta shigo ta sameta a haka.
Ledar hannunta da ta shigo da shi Innar ta mi?a mata tana fa?in. "Kar?i wannan kaya ne da bappanki ya bani ku?i a kan naje cikin gari na saya maki, ki sanyasu, akwai na Mahreen a ciki........".
Jin akwai na Mahreen a ciki yasa ta yi zafin namar kwace ledar daga hannun Innar, Mahnoor da ake mi?awa bata kai ga kar?a ba ta rigata, tuni ta mi?e tsaye tana sakin uban murmushi.
A hanzarce ta fito da kayan, blouse ne masu kyau, dogayen riguna ne, dikkansu kala uku uku ta saya masu, rigunar da gyalensu, kayan suna da kyau, sai dai kayan takaici Inna ta tashi ta je ta ?auko masu kaloli marasa kyau kamar mutun ya kurma ihu, wani irin yellow irin mai paw ?in nan, da kuma wani ja jaw haka, sai kuma ruwan omo ta ?auko masu, wai a haka tana gani ba kalar da ya kaisu kyau, ga shi iri ?aya ta saya masu, haka takalmar da ta saya masu ?in ma, yellow da baki, irin takalmar masu high ka?an ?in nan, ba abin da ya fi bakanta mun rai ma kamar wannan yellow doguwar rigar, ga riga har riga amma kamar ka kurma ihu saboda rashin kyan kala.
A haka su kam suka rin?a murna, wai kayan ya yi masu kyau, tuni Mahreen ta fito da wannan yellow ?in ta zurmu?a ga jikinta, da alama dama sun fi son abu paw mai haske haka.
Ai kuwa tana sanyawa sai ta zama kamar aljana albojel, dama ga uban powder da kwalli a fuska, idanun nan sun ji kwalli marau, abin sai wanda ya gani.
Wannan idan ka ganta da daddare ka yi gudu ne har da zawo a wando, dan ba abin da zai hana baka ce aljana bace, da alam yau Jaish ba zai ganeta ba, dik wannan kauna da shakuwa dake tsakaninsu ina ga yau sai ya gudu idan ya ganta.
Ita kanta Inna sai da ta ce. "Mahreen ki cire wannan riga ki saka ?aya mai kalar omon nan, ita ce zata fi dacewa da kwaliyar nan taki tun da tana da ?an duhu, ke kuma kwalliyar taki ta yi paw".
Inna tana son ta cire yellow ne ba dan komai ba sai dan ita kanta taga ya yi wani paw, ga fuskarta kamar jan ?osai ya ji kayan alatun bature.
Aikuwa make kafa?a ta yi. "Ni Inna wannan nake so gaskiya, yafi kyau da haskakawa".
Bata da za?in da ya wuce ta kyaleta, idan ba haka ba yanzu sai ta tsayar masu da iyashege da kukan banza, gara kawai ta rabu da ita taje a kamar aljanar sai ya fi mata.
Ita kuwa Mahnoor da ko ta kan Mahreen ?in bata bi ba, dan tasan Mahreen dai ba canzawa zata yi ba. Mi?ewa ta yi abinta ta ?auki riga mai ruwan omon ta nufi bayan kofa, ?uye ta yi ta sanya kayan, ba laifi sun yi mata kyau, dan ita bata yi pente penten komai a face ?inta ba, hakan yasa kayan suka zauna mata dai'dai.
A takaice dai haka suka shirya, Inna ta yafa mata gyalen rigar a kanta, ta ri?o hannunta suka fito waje. Cincirindon mata ne sosai a wajen, dik makota da abokan arziki ha?e da kawayen mamanta, ?an uwan Inna kakarta dik sun zo daukarta zuwa wajen taron, ?an uwan bappanta ne kawai ko mutun ?aya bai zo ba, sun ki zuwa dan an hana Faisal ita. Inna Rabi ita ce malama shiyasa aka ce ta shiga ta fito da ita.
A can wajen da za'ayi taran bikin kuwa, kasan wata katuwar dutsen dake kauyen ne, gaba?aya an gama shirya komai, matasa da ?an'mata a cike ta ko'ina, ga dattawa da sa'anin juna, ta ko'ina mutane, an kafa runfuna manya manyan, sannan an shinfi?a tabarmu manya a cikin runfar, runfar dattawa maza daban, runfar mata daban.
Biki fa gagaru suke shiryawa idan ma baku sani ba, dare suke ?atawa suna shagali, kowa da irin al'adarsu a duniya, su kuma kunga irin nasu, kuma kowani al'ada ba wai suna yin shi ne dan nisha?i kawai ba, a'a, kowanne da nufinsu a kansa. An ?awata wajen sosai, harda kwalliya irin nasu dai na kauye suka yi wa wajen. Abin ya ?ayatar matu?a.
Daga can gefe akwai wata rami babba a in da ake ta aikin hura wuta a cikinta, dama ramin saboda bukukuwansu suka tonasa, dan aji da?in yin shagali da kyau ana cin nama.
Shanu manya manya guda biyu babba ya bada aka yanka, dama a al'adar yadda suke bikinsu, za'a yanka shanu a wajen, sannan a wajen za'ayi ta gasa namar kowa yana zuwa yana yanka ya ci yadda yake so, cikin wannan rami da suka hura wuta a saman ramin ake ?aura karafunar gashin namar, mata masu yi wa namar ha?in kayan miya suna aikinsu, masu gasawa ma suna aikinsu, dik yadda ?an kauye ke son dabbobin sun nan dai haka suke yin wannan al'adar, kun san fulani da masifar son dabbobinsu, amma dik da haka in dai za'ayi biki sai sun yi wannan al'adun ta iyaye da kakannin. Aci nama har a ?oshi, sai dai ba'a ta?a yanka shanu biyu ba sai a wannan biki ta Mahnoor, kowa shanu ?aya yake yankawa ?arsa, shi bappa ya nuna masu da banbanci ya yanka biyu!.
Yanzu ma haka aka yi, matasa majiya karfi ne suka kayar da shanun, aka ?auresu Ar?o ya yanka, Jaish kam sai ganinsu kawai yake yi, shi fa wani lokaci idan suna yin wani abin wlh kallon tantiran mahaukata yake yi masu bawan Allahn nan, dan bai saba ba.
Bappa yana ?o?arin sosai, dik kayan da Jaish ?in yake sakawa fa bappan ne yake shiga gari ya saya mashi, shi dai bappan yana da kirki sosai, amma yakamata mu ?an ji labarin bappan nan ka?an dan mu san daga ina ya samo wannan kirkin nasa.
To shi dai mutun ne ba mazauni ba, yanzu ma ba dan Jaish ba da ba zai zauna a garin har ya ?auki tsawon lokaci har haka ba, baya wuce wata ?aya zuwa biyu idan ya dawo, idan kuma ya tafi yana iya kai 6 month up haka, to a baya dai bappa mafa?acin mutun ne sosai, dik da akwai ?an wayewa a tattare da shi, sannan yana da ilimin addini, amma haka yake da fa?a sosai, auren soyayya suka yi da mahaifiyar Mahnoor, yana sonta sosai, amma saboda bakar zuciya da iya fa?a yasa yake gallaza mata.
Ya wahalar da ita sosai har ta kai ta ce ba zata iya zama da shi ba, mafa?aci ne sosai fiye da tunaninku, ga saurin fushi, abu ka?an idan ta yi mashi haka zai hauta da fa?a, kun san maman Mahnoor ?in yar uwarsa ce, so yana ganin kanwarsa ce, wani lokaci har hannunsa yake ?aurawa a jikinta da sunan duka, a lokacin da take da cikin Mahnoor ?in ya ta?a dukanta da har cikin ya kusa zubewa, daga haka ta gudu ta koma gida.
Amma dik da haka ar?o ya datse idanunsa ya sake dawo da ita, kun san iyayenmu sai ayi ta kai masu karan miji suna cewa mutun ya yi hakuri ya yi hakuri, ba bincike ba bibiyar lamuran mutun, haka dai sai ayi ta ce mata ta yi hakuri komai zai wuce, watarana sai labari, ina mai tabbatar maku da bakincikin bappa maman Mahnoor ta bar duniya, a lokacin Nenne tana ?ar matashiya.
Kai in takaice maku zance an haifi Mahnoor da kwana uku ma sai da ya daddallah mata marika a kan dan ta ?auka mashi wasu magunguna da ya ajiye ta yi amfani da su bata tamnayesa ba, kuma a hakan fa ba wai baya sonta bane, yana sonta, kawai dai zafin zuciya garesa da rashin hakuri, ga shegen saurin fushi.
Wani lokaci sai ya yi mata wani abin idan ya fita wajen kiwo sai ya yi ta faman danasani maras amfani, idan ya dawo kuma ba zai hana shi in ta yi laifi ka?an ya wawwaka mata marika ba, aikin kenan kullum.