Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 73

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 73

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 73: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 73. Kanta a sunkuye tana kallon ?asa ta jinjina mashi kai tare da furta. "In Sha…

3,352 words

Kanta a sunkuye tana kallon ?asa ta jinjina mashi kai tare da furta. "In Sha Allah ko dan kai zan cigaba da kasancewa da murmushina, nagode sosai da ka fahimceni, ina yi maka fatan alkhairi".

Kawar da kallonsa daga kanta ya yi cikin jin kunar rasata da ya yi, dogarin ya rufo kofar motar, sauke glass ya yi a in da ya ce mata ya gode, daga haka bai kara furta uppan ba aka tashi motocin nasu. Tana tsaye a wajen tana kallonsu har suka danna hancin motocinsu waje da gudu.

Shi ma idanunsa a kanta har suka bar gidan, motocin yariman Sarina na fita ne nasu ya take masu baya.

Ajiyar zuciya ta sauke na ganin sun fice, godiya ta ?aga hannu ta yi wa Allah da ya sanya ta rabu da wannan yariman lafiya, yarinyar kirki, ita dai bata bi shawarar Mammienta ba, ta fito fili ta gaya mashi gaskiyar dake cikin zuciyarta na cewa tana son Jaish, ba fa?a ba komai, suka gaisa cikin mutunci, ya isar mata da kudurinsa a kanta, bata katse shi ba har ya gama jawabansa, sannan ne ta fara da bashi hakuri kafin ta ?aura mashi da sauran bayanai.

Da yake mai ilimi ne shi ?in sai ya fahimceta ya kuma yi mata uzuri, suka yi hira cikin mutunci da mutunta juna, ta yi ta bashi hakuri yana ce mata ba komai wlh, ai bai sani ba ne, da ya san tana da wanda take so ma ba zai zo ba, dan haka ita ma ta yi hakuri.

Cikin fara'a da girmama juna suka rabu abin gwanin birgewa sa?anin Sarina da nata saurayin.

______________________????

Har cikin ?aki ta bisa tana fa?in Allah ba zata rabu da shi ba, sai dai ko da ta shigo cikin room ?in baya nan, babu shi a ?akin.

Duba shi ta fara yi dan dai ita tasan taga shigowarsa, yana shigowa ta biyo bayansa, sannan ace baya ciki, to ina ya shiga?.

Balconynsa ta fara le?awa, wayam baya nan, a hanzarce ta zo ta nufi toilet dan wauta. Wayam baya ciki, yanzu da yana ciki ma haka zata shiga dan yarinta na mata gizo a kai.

Bincikarsa ta fara yi babu kakkautawa, tsabar shiririta har da le?a kasar gado, tana yi tana hawaye, ni kam na ce Jawad mage ne da zai shiga kasar gado ya ?uya fisabilillahi idan ba shirme irin ma Chuchun ba.

Ta ko'ina sai da ta le?a except bayan curtains kawai, ta sha wahala bata gansa ba, sai ta haye saman gadonsa, ta kwanta tare da rungumo pillow tana cigaba da kukanta tamkar wadda aka daka.

Kamar daga sama taga an kashe wutar ?akin, ai a fujaje ta mi?e zaune a tsakiyar gadon tana rarraba idanu kamar an tare ?era ga tarko, ?akin ya yi duhu sosai saboda curtains gaba?aya a sake suke. Zaro idanu ta fara yi, kumatu a kumbure ansha kuka a ?oshi ta furta.

"Yah Jawad bana so, dan Allah ka kunna wutar, ka dai san duhu tsoro yake bani ko?". Tana magana hawaye suna kara tsananta gudu a saman face ?inta. Muguwar matsoraciyar duhu ce, bata kaunar rashin haske ko ka?an! Tana iya sumewa ma idan duhu ya yawaita.

Shiru bata ji motsin kowa ba, kamar zata saki fitsari a wandonta ta sake fa?in. "Yah Jawad dan Allah ka bari ka ji, wlh ina jin tso........."

Bata kai karshen maganar ba sai ji ta yi ya rungumeta ta baya, ta tsorata sosai sai ta wage baki zata fasa mashi ihu. Da sauri ya rufe mata shi da hannunsa, a kunne ya ra?a mata kalmar sarkin tsoro yi mun shiru.

?o?arin kai mashi dukan wasa ta yi tana ?o?arin kwace kanta daga ri?on da ya yi mata. Jawota mai gaba?aya ya yi ta fa?a jikinsa yana fa?in. "Sorry my beb kin ji?".

Harara a duhu ta banka mashi, tana shasshekar kuka ta furta. "Dan Allah ya Jawad ko wutar lamp ne ka kunna, kaga ina jin tsoron duhu sosai, ko dai ka manta ne?".

Kai ya girgiza mata alamar a'a bai manta ba, ?asa ?asa ya ce. "Tun da kina jikina bai kamata ki ji tsoro ba".

Kai kawai ta gya?a mashi alamar haka ne, amma bata furta kalma ba, ta yi shiru tare da kwantar da kanta a kirjinsa.

"My beb kin san me nake tunani kuwa?".

Ba tare da ta ?ago ko ta yi magana ba ta girgiza mashi kai kawai alamar a'a bata sani ba.

"Tunani nake yi ko dai na yi wa dad batun aurenmu ne? Wlh na gaji da ?uye masu da nake yi, ina bu?atar kasancewa da ke a kullum ba tare da wani shamaki ba".

Tana dai lafe, kasa kasa a shagwa?e ta ce. "Da zanfi kowa farinciki kam my melody".

Da sauri ya ce. "Da gaske kike yi? Kin yarda na bayyanar da soyayyarmu na kuma nemi aurenki?".

Kai kawai ta gya?a mashi alamar e, wani irin farincikin da ya ji ne har bai san lokacin da ya matseta a jikinsa sosai ba, har sai da ta furta washe ne ya farga ya ?an sassauta mata ri?on yana sauke ajiyar zuciya.

Shiru suka yi na ?an lokacin, shi ya afka tunanin ?an uwansa Jaish wanda da shi yake kwana da shi yake tashi a cikin ransa, kullum tunaninsa ina ?an uwan nasa ya tafi? Ga shi har yana shirin yin aure bai dawo ba, yau tsawon watanni kenan. Abin ya yi mugu mugun ta?asa, dik ya zabge sosai, dan ma Momma tana tsawatar mashi ha?e da rarrashinsa a kan ya kwantar da hankalinsa ?an uwansa yana nan dawowa nan ba da jimawa ba, amma dik da hakan ya kasa samun nutsuwa, kullum yana cikin fargabar labarin da zai ji a kan ?an uwan nasa.

Ita kuwa rufe idanu ta yi babu jimawa barci ?arawo ya saceta, dan daren jiya ta biye mashi, bata yi barci ba suka rinka zuba hira, da safe kuma ta tafi school, shi ne yasa barci ya tarun mata sosai.

Saukar numfashinta irin na mai barci da ya ji ne ya fargar da shi tare da dawo da shi daga duniyar tunanin da ya afka.

Ajiyar zuciya ya sauke tare da matsawa ka?an, a hankali ya kwantar da ita, ya janyo pillow ya sanya mata a wajen kanta, ya kuma janyo bargo ya lullu?eta. A gefenta ya kwanta shiru, jikinsa dik a mace na tuna Jaish da ya yi, ji yake yi tamkar ya sanya hannu bisa kansa ya zunduma ihu ko zai ji sassauci a ransa.

A ?angaren Auta da uncle Taheer da suke cikin gonar dad kuwa, sai janta da hira uncle Taheer yake ta faman yi, yana son su saba da ita sosai, ita kuwa ta tasa waya a gaba tana ta danne danne.

Wani irin sako aka turo mata ta nutsa ciki take ta aikin karantawa, abin ya bata mamaki kuma ya ta?ata sosai, sai take ganin kamar wannan yarinman ne da ya nemi izinin neman aurenta dad yaki yarda, kamar shi ya turo mata da sa?on, dan taga sa?o ne na zallar madarar kalaman soyayya masu ratsa zuciya.

Gaba?aya sai ta ji wani irin yanayi ha?e da nutsuwa ya ratsata, dik da bata son shi sai da ta ji sakon nasa ya yi matu?ar birgeta, ya zuba kalaman da zasu kwantar da hankalin mai karantawa, da alama ya iya tsara zance sosai, ga wani irin yaba kyanta na daban da ya rin?a yi, addu'oi sosai ya rin?a kwaranya mata.

My people's kun ga ta in da yarima zai ?ullo wa Autarmu kuma ko? Ko waye ya bashi numberta? Wai ana so dole ne ma?. Muje dai zuwa, kowa ya iya allonsa ya wanke, iya ruwa fidda kai! Ni dai ina gefe ina shan maltina mai sanyi!.

Yar tahali?ar nan bata san lokacin da ta fara sakin murmushi tana karantawa ba, lokacin da ta zo karshen rubutun sam bata so ya kare ba, bata gaji da karanta yabonsa a gareta ba, ya tsara zance iya zance.

Haka kawai saboda da?in kalamai sai ta tsinci kanta da yi mashi reply, mutumin da tana ji dad ?inta ya ce ya dakatar da shi daga zuwa in da take, amma sai ga shi tana yi mashi reply a what'sapp, har da murmushinta.

Aikuwa tana tura mashi reply tamkar jira yake yi ya sake maido mata da sakonni masu zafin gaske, kalamai masu zafi da suka fi na baya.

Tuni ta nutsa cikin karantasu, ya ja hankalinta matu?a, sai surutunsa uncle Taheer yake yi bata ma san da yana yi ?inba.

Idan muka waiwaya muma waiwayo gidansu Khadija kuwa.

__________________________????

GIDANSU KHADIJAH ?? ??

Kwance take saman gadonsu ita ka?ai a cikin ?akin, Zee bata nan, da alama akwai in da ta je ne. Ta yi nisa cikin barcin da take yi, ta kudundune a cikin bargo saboda sanyin safiyar, jiya da ruwan sama suka kwana, ruwa tamkar da bakin kwarya haka ya rin?a zuba, kun san irin wannan barci na sanyin ruwan saman da?i ne da shi ga nauyi.

Dan haka barcinta ya yi nauyi matu?a, ga cikinta a yanzu ya kara girma sosai, ya bayyana, a cikin fari dai tamkar zata haihu yau ko gobe, sai dai cikin nata watansa bakwai ne, da sauran two months.

A hankali Hauwa ta turo kofar ?akin nasu ta shigo, tafiya take yi tamkar sabuwar ?arauniya, kamar bata son ta?a ?asa, tana sanye da wani shegen hijabi har yana jan ?asa na munafurci, ita fa Hauwa wlh ko takaba matar nan bata yi ba, baban Zainab yana rasuwa da sati biyu ta shiga yawon zawarcinta abinta.

Wai shin ina Sadiq? Ina hajiyarsa? Ina maman Haidar? Mu je dai zuwa.

?akin nasu da ?an duhu kasancewar dukkannin labulaye ?akin a sake, haka ta rin?a lalla?awa a cikin wannan duhu ta nufi wajen drawers na gadon, Khadija tana ta barci bata sani ba.

Cikin san?o ta fara bubbu?e drawers ?in, ko tsoro bata ji ba, bata fargabar Zee ta shigo ta kamata, haka ta bubbu?esu dikka ta caje ko'ina a cikinsu tsab, sai dai bata ga jakar ku?in ba.

Mi?ewa ta yi ta koma wajen wardrobe ?insu, a hankali ta bu?e kofarta, sai dai ga mamakinta sai ta ga cikin wayam babu komai, ko ?an'kwalinsu babu a ciki, ina suka kai kayan sakawar tasu kenan? Ta jefawa kanta tambaya.

Waigowa ta yi ta nufi wajen bayan gado, matar nan tsabar kwarin gwiwa har da hayewa saman bed ?in ta le?a ta baya ko Allah zai sa ta gani.

Wayam babu komai, saboda tsabar karfin hali har da saukowa ta nufi toilet dan ta duba ta gani.

Babu in da bata bincika a cikin toilet ?in nan ba, har da bu?e cikin wc tsabar kanta famko ne babu komai a ciki, tsab ta bincike ko'ina, ita fa bata tunanin ga wajen da ya dace ace abu makamancin haka ya kasance, idan ba rashin basira ba fisabilillahi me zai kai jaka cikin wc idan ba tunanin dabobi irin na Hauwa ba!.

Fitowa ta yi sumomoi sumomoi tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki, ta nufi hanyar fita daga cikin ?akin, tamkar zata rusa ihu na rashin samun biyan bu?atarta.

Khadijah kuwa har lokacin bata farka ba, Allah sarki abin ku da barcin mai ciki.

Har ta kai bakin kofa zata fita kenan sai tunanin ta ji sun ce yau zasu tafi Kaduna ya fa?o mata a cikin ranta, cikin sauri ta juyo ta dawo cikin ?akin, tabbas ta ji suna hira daren jiya a kan yau zasu ta fi wajen kakarsu a Kd, to da yiwuwar shiyasa suka kwashe kayansu dake cikin wardrobe ?in dikka suka sanya a akwaiti kenan, to dik yadda aka yi wannan jakar ku?in ma tana cikin akwatin.

Ai kuwa jin wannan tunani nata ya yi mata da?i ne yasa taji tamkar ta kurma ihun da?i, har da yar tsallenta, kamar har ta ga ku?in ta gama take ji a ranta.

A hanzarce ta fara neman ta ina akwatin kayan nasu yake? Ta sake duba cikin wardrobe babu, ta duba wajen gado nan ma babu, nan take ta fara ?aure fuska dan ta ga alamar murna zai koma ciki, tsabar shegen son abin duniya har toilet sai da ta sake komawa ta duba, nan ma babu komai.

Kamar zata yi kuka ta nufi hanyar fita daga ?akin, har ta kai kusa da bakin kofa sai kuma ta juyo da sauri ta nufin gefen wardrobe ?in ta wajen jikin bango kusa da mirror.

Aikuwa tana zuwa ta isko jakar ku?in a saman akwatinsu da suka gama shiryata tsab saura tafiya, bayin Allah sun shirya komai nasu tsab, jiran Zee kawai Khadija take yi ta dawo su tafi, ta je kwaso masu sauran wasu abubuwan da zasu bu?ata ne a tsohon gidansu, shi ne Khadija ?in ta ce bari ta ?an kishingi?a ta huta kafin ta zawo su wuce tasha in da zasu hau mota, shiyasa Hauwa ta tashi hankalinta sosai ta ?asa hakuri har sai da ta shigo masu ?aki neman ku?in, dan tasan yau zasu tafi, idan suka tafi kuma shikenan ta rasa wannan ku?i.

Wannan ku?i na Khadija fa idan za'a canza shi a ku?in Nigeria to ba za'ayi maganar millions of naira ba, sai dai billions of naira, da alama wanda ya bata wannan ku?i a gaskiya yana ?aya daga cikin manyan masu ku?in kasarsu, kuma a haka take tunanin buga shari'a da shi ta ?ata mashi suna idan ta haihu! My people's thinks about that fa da kyau, mutumin da zai kwashi ku?i makudai irin wa?an nan ya baka ai kasan ya wuci tunaninka, kuma a hakan fa ka?an ya ?an tsakura daga cikin dukiyar tasa ya bata, a haka zata ja da shi? Ni dai a ganina gaskiya Khadija zata yi ganganci in ta ce zata yi hakan, kuma wlh zata iya janyo matsalar da zai sa ta rasa ranta, kai bama ita ka?ai ba harta Zainab idan abin ya kwa?e ba tsira zata yi ba! Ku dai duba mun wannan lamari fa.

Akwai matsala gaskiya, da ta yi hakuri ta barwa Allah komai, ko ba ji ma ko ba da?e gaskiya zata yi halinta, domin kuwa Allah bai yi alkawarin tallafawa azzalumai ba, mu je dai zuwa.

Wani irin uban tsalle da ta daka tare da kware baki zata yi ihu ne sai ta tuna ashe a cikin ?akinsu take, jikinta na kerma ta kai hannu a kan jakar ku?in, idanunta garau ta waro a kansa.

Mu koma baya ka?an, kwanaki hu?u da suka wuce maman Haidar ta dawo Kano, dik ta rame ta kwanjame, tamkar ?ashi da rai haka ya zama, abin tausayi kuma shi ne har wa yau bata sami damar ganin Haidar ?in ba. Wasu ma idan ta je wajensu cemata suke yi an kashe su Haidar ?in ai, dan haka ta dai'na wahalar da kanta, an rufe babinsu yanzu ta koma gida.

Sam taki yarda Haidar ya mutu, tana ta shan wahalar bibiyar manya dan ta samu sahihin ainahin labarin in da yake ko da ba zata samu damar ganinsa ba. Yanzu haka karewan da ku?in hannunta ya yi ne yasa ta dawo gida ba dan ta so ba, babu mai bata abinci bare abin sha, a ?asan gada ma take kwana, ba ta da wata mafaka, ganin yunwa yana ?o?arin yi mata illah ne yasa ta gudu ta dawo domin ta ?an harha?a wasu ku?a?en ta sake komawa.

Sai dai kuma tana dawowa ta iske mummunar labari na rasuwar mahaifiyarsu, aikuwa wani ihun da ta kurma ta yanke jiki ta fa?i ne har yau ba'a sake gane kanta ba, tana gadon asibiti tare da maman Hanif dake jinyarta, ko le?a asibitin Hauwa bakar munafuka taki yi, kuma ko naira biyar taki basu su yi jinya, sai dai maman Hanif ?in ce yar albarka take ta ?awainiya, baiwar Allah ita ma ba karfi ne da ita ba, abinci ma da kyar suke iya samun cin sau biyu a rana, amma dik da hakan bai sa ta juyawa ?an uwan nata baya ba, dik wanda ya shiga matsala dai ita ?in ce kawai take tsaya mashi.

Wannan a takaice kenan abin da yake faruwa, su Khadija sun je asibitin har sau biyu suna dubata, a lokacin bata farfa?o ba, yanzu da ta farfa?o kuma ko magana bata iya yi, sai shiru kawai tana bin mutane da ido, sannan ta samu cutar mutuwar ?arin jiki wato paralyze, ?arin hagunta ya mutu gaba?aya daga hannun har kafa, bata iya motsa shi, innalillahi wa inna ilahir rajiun, ya Allah mun tuba, mun tuba ya Allah, Allah ka rabamu da mummunar ?addara, kasa mufi karfin zu?atanmu, ya Allah ka karemu daga zalintar wani da har alhakinsa zai bibiyemu, hasbunallahu wani'imal wakil. Kun ji abin da yake faruwa a halin yanzu, to mu koma kan labarinmu!.

STORY

cikin hanzari Hauwa ta dauke jakar ku?in nan ta fice da shi, kai tsaye room ?inta ta nufa. Tana shiga ta datse kofa, tana shigewa kuma ?akinta Zee na shigowa cikin parlourn hannunta ?auke da jakar school ?inta mai shake da wasu kayan sakawansu da litattafansu.

Bata san da Hauwa ta shiga ?akinsu ba, dan bata ganta ba, ta shige ?akinta.

Kai tsaye nasu ?akin ta nufa, tana zuwa ta haye gado tana kiran suna Khadija da ta tashi su tafi kada rana ta yi. Da kyar ta iya samu Khadijar ta farka tana wani yin uban mi?a ha?e da hamma.

"Aunty khadina ki tashi mu tafi rana tana yi".

Idanu jajir saboda barci, murya irin na mai barci ta furta. "To kin ?auka mana kayan ne?".

Kai ta gya?a ha?e da cewa e. Mi?ewa zaune a tsakiyar gadon ta yi, jikinta sanye da hijabi har ?asa, saukowa kasa ta yi suka nufi wajen akwatin, Zee ce ta janyoshi ta fito da shi tsakar ?akin.

"Zee ina kamar jakar dake kan akwatin? Ko dai kin sanyata a ciki ne?". Har lokacin muryarta irin na masu barci ta yi tambayar.

Zee ?in kuwa cike da zumu?in son ganin Sadiq, burinta kawai su tafi, a ?age take da son ganin sun bar gidan, sai kawai ta ce. "E ina ga na ha?esu a ciki kawai, yanzu ke aunty kadina ki ?auki jakar school ?in nan naki ki goya a baya bari na ja akwatin nan mu tafi ko?".

Da to Khadija ta amsa, ba tare da sun duba jakar ku?in sun tabbatar tana cikin akwatin ko bata ciki ba kawai suka ja suka fice daga gidan ba tare da sun bi ta kan Hauwa ba, suka rufe kofar room ?insu da key suka kuma sanya key ?in a aljihun jakar bayan Khadija ?in.

Dama already Zee ta fitar da ku?in motarsu a gefe kafin su shirya kaya, dollars dubu ?aya ?aya guda hu?u ta fitar, wai ku?in mota da ku?in cin abinci, a hakan ma fa dan wani ?an islamiyansu da ya zo kawo masu ziyara tare da tambayar lafiya kwana biyu basu je islamiya ba ya gaya masu cewa dollar dubu ?aya ta fi karfin dubu ?ayan Nigeria, dan yaga dubu ?ayan a hannun Zee zata je saya masu kayan tea ranar da maman Hanif ta daki Hauwa, idan baku manta ba a ranar ciwon Zee ya tashi, shi ne Khadija ta ce ta sayo kayan tea ta zo ta sha abu mai zafi sai ta sha maganinta da daddare kenan, kun ji dalilin da yasa ku?in ya sake fita.

So ya gaya masu ku?in ya fi na Nigeria, dan haka su kai kasuwar canji a canza masu ko su kai bank, shi ne fa kuka ga yanzu suna ?an daraja ku?in har suke ganin dubu hu?u zai iya kaisu Kaduna daga Kano har su ci abinci.

Ko da suka hau mashin suka je suka sauka a tasha sai suka bashi dubu ?aya ta dala, basu tsaya ?ata lokaci ba suka shiga cikin tashar, kun san tasha dama idan ka je har rububin kwatar kayanka ake yi a sanyasu a mota, to haka suma aka yi masu.

Mai mashin ?in kuwa, ganin hankalinsu baya a kansa, basu tambayi canji ba sai ya buga mashin ?insa ya gudu abinsa, gaskiya ta yi ?aranci over a duniyar yanzu, jama'a bin haramun suke yi da gudu suna ?o?arin kamata su ci, Allah ka kiyashemu cin haramun.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull