Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 72
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 72: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 72. Tana dinfarar bakin kofar shiga ta kara canza salon tafiyarta izuwa mai jan…
3,366 words
Tana dinfarar bakin kofar shiga ta kara canza salon tafiyarta izuwa mai jan hankali sosai, sam bata ?aga idanu ta kalli ko mutun ?aya daga cikin wa?an da suke harabar gidan da suka shagala da kallon surarta ba, kai tsaye ta afka ciki abinta.
Sam bata yi fargabar ko zata ci karo da uncle Abbas ko wani nata a ciki suna gaisawa da bakin ba! Ba shakkar kowa bare tsoro yarinyar nan ta afka ciki ba tare da ta yi sallama ba sai wani ?an iskan excuse da ta ce masu.
Ta kuwa yi sa'a babu kowa a ciki sai yariman da wani abokinsa ?aya, sai dogarawa guda biyu da suke tsaitsaye a kansu ta bayansu dan basu tsaro.
Hannunta na rike da wannan cup mai ?auke da abin shan a ciki, wani irin ?an iskan taku ta iya izuwa tsakiyar parlon, idanunta na'a kan abin shan nata, sam bata ?ago ta kalli in da suke ba!.
Ai yarima da abokin nasa basu san lokacin da suka mi?e tsaye ba, gaba?aya kallonsu a kanta yake, da alama fa ha?anta ya cinma ruwa ta ?angaren sace zuciyar yarima, ko da yake dama can soyayyarta ta kawo shi, ba dole aka yi mashi ya zo ba!.
Wani irin ?an iskar kallo ta bi dogarawan dake bayansa da shi, cikin tsantsar nuna isa da jiji da kai irin na jinin sarauta ta furta. "Me wa?an nan ?azaman kuma suke yi a nan? Ko da su zan yi hiran?".
Da alama yarima dai sai sorry za'ace, dan kuwa kamar fa ya tafi, dama tun da ya ganta a wajen taron da mummy ta ha?a yake ta faman santin kyanta da surar jikinta, sai kuma yanzu gata a gabansa cikin shiga mai tada hankalin lafiyayyun maza, ai dole ya rikice.
Ga shi namiji har namiji, arabs guy ne lafiyayye kuma ?an gayu da ba zai wuci 28 to 30 years ba, ya yi shiga irin ta prince masu ji da kansu, yana wani shan kamshi ga mutane, sai dai a gabanta tuni ya mance da cewa shi yarima ne mai ji da isa da izza, muryarsa har tana ?an kerma wajen bu?e baki zai bata amsa, sai dai bai kai ga furta uppan ba abokin nasa ya rigasa da cewa.
"Ranki ya da?e dogarawa ne masu bada tsaro............"
Hannu ?aya ta ?aga mashi alamar ya dakata da yin maganar, cikin wani irin isa ta juyo da kallonta a kansa, ga idanun nata sun kara haske saboda bakin kwallin da ta sanya masu, idan ta juyasu sai kaga wani irin fari na musamman, ga shi ta iya juyasu kuwa, matsiyacin kallon up and down ta yi mashi kafin cikin nuna isa a wala?ance ta ce.
"Who the hell are you da zan yi magana da wani ka tsoma mun baki a cikin maganata? I think bakaga kalar hakan a tattare da ni ba ko?!".
Wani irin shan jinin jikinsa yarima ya yi, domin kuwa bai ta?a zaton haka take mafa?aciya ba, shi kallon so silent ma ya yi mata a karon farko, bai san cewa ja'irar yarinya bace.
Shi kuwa abokin nasa da ya kasance ?a ne ga kanin mahaifinsa, dikkansu dai jinin sarautar ne suma, suna ji da izza da isa sai ya wani uban ?aure fuska, ya dubeta da kyau up and down, sannan ya ja wani ?an siririn tsaki, a tsiyace ya furta. "Rubbish! Yana da kyau ki san da wanda kike magana fa, am not your mate, and am n...........".
Katse shi ta yi ta hanyar ?aga mashi hannu a karo na biyu, sannan ta kawar da kallonta izuwa kan wanda take zaton shi ne yariman, dan ita a cikinsu bata ma san wanenen yarima na ainahi ba.
"I don't have time for listening all this your nonsense! What i want to know here is between the two of you who's the prince? Is it you or him?" Ta yi maganar tana nuna su da ?an yatsar hannunta manuniya.
"And among the two of you who should I going to talk?, answer me as soon as possible because I have something a lot to do!". Ta kai karshen maganar tana tsayar da kallonta a kan dogarawan da suke bayan nasu.
Abokin nasa zai sake yin magana cikin fushi da fusata dan a ganinsa ta raina mashi wayo, kun san jinin sarauta basu ?aukar wasa.
Dakatar da shi yarima ya yi ta hanyar ?aga mashi hannu, sannan ya furta. "Ni ne yarima gimbiya Sarina".
Nisawa ta ?an yi tare da nuna abokin nasa da manuniyar yatsarta ha?e da dawo da kallonta a kansa, cike da class take magana, babu hayaniya sai zallar jiji da kai, yadda zaku san e ba wawiya bace, wayayya ce mai ji da kanta.
"Okey ban san kai ya kake da shi ba, even do dai bana son ?aga idanu na sake ganinka a cikin parlourn nan, coz ba kai kazo neman auren ba, shi da ya zo neman auren ma i don't have time for him ma bare friends or familynsa, you have to go out now!". Tana kai karshen maganar ta maida kallonta a kan dogarawan nasa.
"Sai na furta maku ku fita ku bani waje ne kuma?". A tsiyace sosai ta yi masu magana, cikin nuna ?as?anci a garesu.
Daga dogarawan har abokin nasa shi suka zubawa idanu suna kallo, ta bakinsa kawai suke jira su ji.
Wani irin murmushi ya saki wanda da ka ganta kasan e lallai ?a?alota ya yi, dan kuwa murmushin takaicice, ya ji haushin abin da ta yi masu, a ?an tsagaice ya furta. "You can go outside by her permission, I don't have to say anything, coz my words and hers will all go together"
Zaro idanu abokin nasa ya yi, da mamaki yake kallonsa, kenan yarima ya goyi bayanta a kansa? Lallai to da matsala, wannan yarinya maras kunya da idanunta a tsaitsaye a tsakar ka, bata jin kunya ko nauyin zagin babban ne yarima yake tunanin ita ta dace da rayuwarsa? Har yake ?o?arin nunawa tun yanzu ta fi mashi kowa? To da matsala gaskiya.
"Adam har da ni yau kake cewa zan iya fita waje bisa umarnin wata ba sai ka ce komai ba? Ni ne fa?".
A ?an takaice ya ce. "And so?! Ko dai ba zaka fita ?in bane?". A dake ya yi maganar.
Tun da dogarawansa suka ga haka sai suka kama kansu salum alum suka fice, da farko sun so su ce mashi ya yi hakuri ya barsu saboda mai martaba mahaifinsa ya ce in dai ba toilet ya shiga ba to su tabbatar duk wani motsin da zai yi suna a tare da shi, su bashi kula na musamman, amma ganin harda abokinsa tun na yarinya da suka taso a tare ya dakawa magana maras da?i a kanta sai suka shafawa kansu lafiya suka yi ta kansu.
Daga haka abokin nasa bai kara furta ko uppan ba ya nufi waje zuciyarsa tana tafarfasa kamar an ?aura dalma a wuta, fa?i yake yi a ransa wlh ba zai bar Sarina ba, kuma in dai yana raye yarima ba zai auri wannan shegiyar yarinyar ba, dik wanda ya ci tuwo da shi wlh miya ya sha, za ta gane annabi Isa ba ?an Allah bane annabin Allah ne.
Suna fita ta ?aga cup ?in dake hannunta ta kai saitin bakinta, ka?an ta ?an yi sipping na drinks ?in ta cire, matsowa kusa da shi ka?an ta yi, ya saki ido, hanci da kuma baki yana ta kallonta, ya manta da shi fa Prince ne.
_________________________????
"Ban san ya kake da suna ba, kuma bana da bu?atar na sani, dan babu abin da zai kare ni da shi, but let me tell you abin da kai zaka karu da shi kuma it will help you so much".
Tun da ta fara magana ?an bakin nata yake kallo ba tare da ya motsa daga in da yake tsaye ba, shi a duniya yana bala'in son mace haka mai cike da kwarin gwiwa a kan dik abin da tasa a gaba, sannan ta zamana bata tsoro ko shakkar kowa, mai furta magana one by one cike da class kamar dai ita, dan haka wannan abin da take yi sai ya ?ara tafiya da imaninsa sosai da sosai.
A dab gabansa ta matso ta tsaya, sannan ta sake kai cup ?in bakinta ta yi sipping ka?an ta cire, ido cikin ido ta kallesa, babu ko shakka bare tsoro ko kunya, cike ma da wala?anci a muryar tata ta fara magana.
"Ban sani ba ko kana da ?wa?walwar gane abubuwa ne, ko dai fanko ne kan naka, but even do dai nasan ba zaka rasa brain na ?aukar wa?an nan maganganun nawa da zan fa?a ba, dan maganganu ne da komai dakikancin mutun dole ya fahimcesu!". Tashin sense.
Dakatawa ta yi tana kara yatsune fuska ha?e da nuna gadara. Still har a lokacin yarima dai bai furta kalma ba, sai dai shi ma ya kurawa tsakiyar kwayar idanunta kallo.
"I don't want to see your legs in this kingdom again, because i really hate u! Ka koma ka sanar da cewa baka yi nasara a soyayyarka ba! A nema maka ha?in gida kamar yadda aka saba yi maku!!".
Sake yin sipping na abin shanta ta yi dan ta ji da?in shuka mashi rashin mutuncin nata son ranta, kun san ko masifa zaka yi idan kana kora abu mai sai komai ya fi tafiya dai'dai.............??
Ki ji ma?ogwaro sanyi na ratsata, sai kin ma fi tuna irin rashin mutuncin da zaki zabga sosai, a duk lokacin da sanyi ta ratsa sai kin tuna shika shikan rashin mutun kala goma......??
In ji wata ta yi wani magana ku gani, ai gaskiya na fa?a!!.
Shi ko bawan Allah yadda kuka san mutun mutumi haka yake tsaye kikam, sai ma mujiya da yake binta da shi.
"Kai baka ga kalarka bane? Irinku ai basu da wata za?i a rayuwarsu sai abin da dattawa na gida suka za?a masu, irinmu ne ke da za?i a duniya, even do dik wanda ya yaudareka da sunan kana da za?i kuma zaka iya playing roll naka a kan hakan to he really done bad and he lied to you !!". Ta kai karshen maganar tana ?an zaro mashi idanu, alamar yasan da gaske take yi!.
Sai a lokacin ya nisa tare da sauke hannunsa daga saman kirjinsa da ya har?e, da alama ko ka?an bai ji zafin maganganunta ba, dik da ta sako iyayensa a cikin maganganun nata, dan su ta kira da dattawa a baya, shi ya fahimci maganar tata da ta yi su a dunkule, dik ya fa?a?asu a ma'aunin ?wa?walwarsa ya kuma gane in da ta dosa.
Dan haka sai ya kai hannu da nufin ya kar?i cup ?in dake hannunta. Ba musu ta sakar mashi cup ?in tare da janye hannunta da sauri wai dan kada ya ta?a mata jiki.
Cikin nutsuwa ya kai cup ?in bakinsa, one sipping ya ?an yi tare da cirewa, cikin ?asaita da kwanciyar hankali ya ?an yi step biyu, ya ?an wuceta ka?an sai ya tsaya, ba tare da ya juyo gareta ba, ya bata baya kenan, cikin kwarewa ya furta.
"Zazzafa kuma kyakkyawa, you really try beb". Yadda ya kai karshen maganar cikin wani irin slow a hankali ga salo mai ?aukar hankali!.
Zaro idanu sosai ta yi, ba na mamaki ba, na tsantsar haushin abin da ya fa?a, da alama shi ma cikakken ?an duniya ne sosai, ita ta yi shigar banza ta zo gabansa ba tare da ta tuna abin da zai je ya dawo ba, yanzu ya yi maganar banza a kanta kuma tana ?ata rai game da jin haushi.
A fujaje ta juyo garesa, ya bata baya ha?e da har?e hannayensa a saman kirjinsa. Wani irin matsiyacin ?an iskar kallo ta wurga mashi kafin ta bu?i baki da nufin ta yi magana, sai dai kuma ya rigata furta.
"Yana da kyau na lashi zumar zazzafa gimbiya gaskiya, Gimbiya Sarina ko ya kika ce?". Ya yi maganar tare da juyowa gareta a wannan karon.
Yana juyowa saura ka?an su mannu da juna, saboda ta juyo gare shi ita ma.
Wani irin kallon tsana take bin shi da shi, tamkar ta sha?esa ya mutu take ji.
Wani irin shu'umin murmushi ya sakar mata kafin ya kyasta mata yatsunsa a saitin face ?inta cike da duniyanci.
Wani irin ?an iskan kallo ta watsa mashi kafin ta sake yunkurin bu?e murya dan ta yi magana, sai dai a wannan karon ma bai bari ta furta uppan ba ya dakatar da ita ta hanyar ?aga mata hannu, ba dan ta so ba ta yi shiru.
A maimakon ya sauke hannun nasa da ya ?aga mata ?asa, sai ya sauke a saman lallausan wuyarta, cike da iyashege ya furta.
"Yanzu lokacin yin magana na ne ba naki ba gimbiyata, the way na barki kika yi maganganunki son ranki har kika gama, the waye zaki dakata dan sauraron nawa!". Yana magana yana shafa neck ?in nata, a hankali yake gangaro da hannunsa izuwa saman kirjinta, idanunsa suna tsakiyar tata.
A hankali ya wani lumshesu da alamar da?in latsa skin ?inta da yake yi tana ratsa shi, har da wani furta ishiiiiiii irin ya ji zazzafar nan.
Wani irin zaro idanun waje ta yi, bata ta?a zaton haka daga garesa ba, tunani ta fara yi a kan ko dai ya sha irin abin da Yusuf ya sha ne shi ma? Amma kuma da ya zo gidan ai bai ci komai ba, kuyangun da zasu kawo mashi abinci ma ai basu rigada sun ?ariso ba, fruits da aka kawo masu ma ga shi nan basu ta?a shi ba, to me ya shiga kansa kenan da zai latsa mata jikinta a cikin gidansu? Ta jefawa kanta tambaya.
Ya lumshe idanu yana wani shafe mata jiki, dab da zai shafa mata kirji ba zato ba tsammani kwatsam ya ji saukar dalleliyar mari mai tsada a saman lallausan kumatun nan nasa mai kama da bread, ga kumatun nasa da tsoka a cike ?ul ?ul hannun zai ji laushin mari, dan yana da ?an cika.
A gaskiya ya maru kuwa, ji kake tasss, sai da ta dakarkare tsakaninta da Allah sannan ta dalla mashi ita, da yake yana da hasken fata, balarabe ne, sai da yatsun hanunta suka kwanta a saman fatarsa, har wani irin ?an jiri jiri ya gani.
One step ta matsa baya da shi, cikin kunar rai na ta?a mata jiki da ya yi ta furta. "Banza ?azami jahili! Ashe dai ban yi karya ba da tun farko na kiraka da jahilin da?i?i, wannan jikin da kake gani dan mutum ?aya aka yi shi a duniya, babu wanda ya isa ya ta?ata ya zauna lafiya! Shashasha kawai". Tana magana tana sau?e huci kamar wata zakanya, ta kai karshen maganar cikin masifa ha?e da ?an ?aga murya, sannan ta kara two step tsakaninta da shi.
Idanunsa ne suka ka?a suka yi jajir kamar wuta, ransa idan ya kai dubu to yau ya ?aci, tun da uwarsa ta haifesa ba'a ta?a marinsa ba, shi ?in ?an gata ne, sai yau wata ta maresa? Lallai kuwa ta ?ebowa kanta ruwan zafin dafa kanta da kanta.
A dai'dai wannan lokacin wasu kuyangu biyu suka shigo cikin parlourn bakinsu a ?auke da sallama, ?an'mata ne masu ?ananun shekarun da a ?allah zasu kai 22 haka, hannunsu ?auke da tray ?in abinci mai girma wanda yake shake da cima iri daban daban a ciki, dukka tray guda biyun a shake suke tab.
?arisowa ciki suka yi, a tsakiyar parlourn saman carpet suka zubesu, sannan suka zube gwiwowinsu a ?asa domin su kwashi gaisuwa a gun yarima.
Basu kai ga bu?e baki su furta uppan ba Sarina ta kai hannu ta fisgi cup ?in drinks ?inta dake hannunsa, babu tsoro bare shakkar komai ko tunanin abin da zai je ya zo kawai ta watsa mashi wannan drinks ?in gaba?aya a face ?insa ta gangaro har jikinsa.
Rai a matu?ar ?ace ta yi wurgi da cup ?in ?asa ya fa?i ya tarwatse, bata jira ganin reaction da zai ?auka ba ta juya cikin ?acin rai ta nufi waje.
Yadda take tafiya da sauri sauri ya ja hankalin kowa dake harabar gidan har da abokin yariman a kanta, gaba?aya suka bita da na mujiya, bata zame ko'ina ba sai room ?in Mammienta.
Tana shigowa parlourn ta ci karo da Rizwan da ya fito daga part ?in King, ya je sun gaisa da Akka ce ya kara yi mata batun aurensa da chuchu da yake son ayi cikin satin nan kafin ya koma.
Akka dai ta yi na'am da hakan, har ma ta ce mashi on this coming Friday za'ayi komai, sosai ya ji da?i, da kallo ?aya zaka yi mashi kasan yana cikin farinciki ainun.
Amma dik wannan farincikin da yake ciki suna cin karo da Sarina cikin irin wannan shiga da yake jikin nata sai da farincikin ta kau daga kan face ?insa, nan take ya ?aure fuska sosai.
Sai dai kafin ya yi mata magana har ta shige room ?in Mammienta, dan wani uban sauri take zubawa, tamkar bata gansa ba ta wucesa da sauri, da alama kasancewarsa shiru shiru mai sauki kai sosai yaja suka rena shi.
Dan a dik jikokin Akka babu mai saukin kansa, ga fara'a, kunga ai basa gigin kawo wa Jawad iyashege, da Jawad ne wlh kome ta kwaso, ko da wuta take tafiya sai ta tsaya ta kwashi gaisuwa cikin girmamawa, amma da yake wannan gajeran dangarta ne sai ta wucesa fuuuu kamar kunfa.
Da ya so ya bi bayanta izuwa ?akin mammie ?in, sai kuma ya fasa ya nufi nasa part ?in a zuwan zai yi mata magana idan suka sake ha?uwa.
Shi kuwa yarima wani irin murmushi ya saki na abin da ta yi mashi, sai dai da alama murmushin takaici ce, a face ?insa bai nuna ya damu ba, daga ta cikin zuciyarsa kuma tamkar ya mur?e wuyarsa ya mutu yake ji saboda wani irin ?acin takaici da ya ji, ba'a ta?a yi mashi irin wannan cin mutuncin da ta yi mashi ba, ace dik izzarsa da isar nan tasa Sarina ta wala?anta sa har haka?! Abin da kunar rai gaskiya.
Waje ya nufo shi ma ba tare da ya ?aga idanu ya kalli kuyangun da suka kawo mashi abincin ba. Yana fitowa ya nufi motarsa tare da bada umarnin su tashi motoci su tafi.
Da ido abokinsa ya bisa da shi yana addu'ar Allah ya kara, dan ko ba'a gaya mashi ba ya san rashin mutunci Sarina ta yi mashi, da yake abokinsa ne sai ya iya gane hakan y a face ?insa!.
A dai'dai lokacin kuma ita ma Fanan ta fito a tare da nata yariman daga ?ayan part ?in, sai murmushi yake yi ita ma tana murmushi kuyangu biyu suna take mata baya, shi ma dogarawa biyu suna take mashi baya.
A haka ta rakosa har wajen mota, sai kwasan gaisuwa sauran dogarawansa dake jiransa a wajen suke yi a wajenta. Cikin mutunci ta rin?a amsa masu.
A jikin motarsa ya jingina bayansa, cikin sanyin murya ya furta. "Na ji matu?ar ?aci da takaici na rashin samunki a matsayin mata da na yi Fanan, amma ba komai kana naka Allah yana nashi, na gode da karranawa kuma na ji matu?ar da?i, ina yi maki fatan Allah ya ha?a kanku ke da wanda kike so ?in ya kuma baku zaman lafiya".
Kanta a ?asa ta furta. "Amin ya Allah, ina godiya sosai da addu'a, ni kai'na na ji babu da?i da zuciyata ta riga fara son wani ba kai ba, ina yi maka fatan samun mace tagari tamkar yadda kake nagari mai tsoron Allah".
"Amin Fanan, amma ba zan gaji da fa?in na yi babban rashi ba, na kuma ji ciwon hakan sosai a zuciyata, kuma na tabbata zan cigaba da jin zafin hakan na har abada, na so ki sosai Fanan, tun da na ?aura idanuna a kanki sonki ya shigeni, amma babu komai na barki lafiya, please keep smiling like the way you're, murmushi tana yi maki kyau sosai". Yana kai karshen maganar ya matsa daga jinginar da ya yi da jikin motar.
Wani dogari ya yi saurin zuwa ya bu?e mashi kofar motar, a back seat ya zauna idanunsa a kanta.