Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 71
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 71: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 71. Sai a lokacin ne ta amsa da. "Dama nace maki barci nake yi ne? Duk kyansa…
3,339 words
Sai a lokacin ne ta amsa da. "Dama nace maki barci nake yi ne? Duk kyansa babu ruwana da shi, Hamma Faisal nake so". Tana magana tana harara.
Siririn murmushi Jumma ta yi, sannan ta ce. "Tom shikenan, ni dai bari na zo na wuce gida kada Inna ta yi mun fa?a, koma menene sai mun ha?u da yamma a dandali, zan so ganin yadda hammanki kuma mijinki zai yi maki kwalliya......"
Datse mata numfashi ta yi da cewa. "Waye zai yi wa kwalliyar?".
"Amaryarsa Mahnoor zai yi wa mana, idan ya zo yi sai ki hana shi mu gani, ke anya Mahnoor ba sai ya yi maki ta karfi bama zaki yarda da shi kuwa? Bari zan gayawa Inna, wlh zan gaya mata zagin mijinki kike yi".
Da sauri ta ri?on hannunta, marairace murya ta yi kamar zata sa kuka, ta ?an tsuke fuska kafin ta ce. "Dan Allah Jumma ki yi hakuri kada ki cewa Inna ina zaginsa, kin san dai zata yi mun fa?a koma ta dakeni ko? Dan Allah kada ki fa?a".
"To naji ba zan fa?a ba, amma ki yi mun alkawarin zaki yi mashi duk abin da Inna take karantar damu dangane da miji? Sannan kuma ki mun al?awarin zaki dai'na tunanin hamma Faisal, tunaninsa kawai zaki rin?a yi!".
Tun da ta fara magana take gya?a kai sama alamar ta yi alkawarin, sai da ta dasa aya ne ta ce. "Na yi maki alkawari In Sha Allah zan yi dik abin da na sani iyakar iyawata, dan Allah dai kada ki gayawa Inna komai".
"To ba zan fa?a ba, yanzu dai bari na je gida sai mun ha?u da yamma a wajen shagalin bikin, akwai shagali yau, wani irin kwalliyar kece raini zan yi, a matsayina na babbar kawar amarya sai na fi kowa kyau, harta amaryar da angonta zai yi mata kwalliyar ma sai na fita kyau". Ta kai karshen maganar tare da mikewa tsaye.
Sakar mata hannunta Mahnoor ?in ta yi tare da yi mata sai anjuma ta gode da ziyara da kuma shawara. To kawai ta amsa da shi, sannan ta fice waje.
Karkatawa ita kuma ta yi ta kwanta abinta, tunani cike fal a ranta ta lumshe idanunta kamar mai jin barci.
Ita kuwa Jumma tana fitowa ba zato ba tsammani kwatsam ta gansa a kusa da ?akin bappan yana gyara itatuwan da bappa ya saro dan su ha?a bukka, a yanayin yadda ta gansa sai taga kamar ya jima zaune a wajen, dan kuwa har yana ?an ha?a zufa, rana ta iso in da yake.
Gabanta ne ya yi wani irin fa?uwa, addu'a ta fara yi a kan Allah yasa bai ji abin da suka yi ta fa?a ba, ga shi ta yi ta sakin baki ita sarkin magana.
Shi kam tamkar bai san da ita a wajen ba, har ta wuce bai ?ago ya kalle ba.
Ita kuwa Mahreen da suka yi wa wayo suka ka?ata wajen bappa dan su yi hira, wlh la?ewa ta yi ta baya tana jin maganganunsu, sai da ta ji komai sannan ta gudu wajen bappan a cikin gona, tana zuwa a fesa mashi komai tsab, ta fara bashi labarin tun daga farko tiryan tiryan, wai ai ga su Mahnoor can suna hira a kan yadda zata zauna da Hamma, ta tona masu asiri yarinyar nan.
Bappa dake ta ?o?arin saro wasu itatuwan ne mamaki tasa sai da ya dakata, dama ya saro wasu ya kawosu gida Jaish yana gyarawa, sai ya dawo karo wasu. Bai ta?a tunani su Mahnoor sun san wannan karatun ba, bai san cewa Jumma take koya mata ba. A ransa ya kara jin cewa lallai Mahnoor tana son Jaish tun da har take bada labarin yadda zata zauna da shi, bai san cewa Mahreen ta kwa?e maganganun bane, shi ne bai fahimce ta da kyau ba, ta ?auki labarin da Jumma ta bayar sai ta bashi a matsayin Mahnoor ce ta fa?i hakan, maganganun Mahnoor ?in kuma sai ta bashi labari a matsayin Jumma ce ta fa?i hakan, ta juya kan zancen gaba?aya.
Bawan Allah mamaki yasa ya ajiye addar wukar dake hannunsa yana tunanin gara dai ya samu ya mi?awa Jaish wannan yarinya ya huta, ayi masu ?akinsu su koma can, ko yaushe ta yi wayo haka bashi da labari?
Mahreen uwar ha?a bomb, ta bashi labarin da ya ?aga hankalinsa, ta kama kanta ta haye saman bishiyar gwaiva tana aikin tsinka ko a jikinta, ta barosa a tsaye a wajen.
My people's ya kuke tunanin wannan zama zata kasance, shin Jaish zai yarda ya yi biyayya ga al'adunsu? Mahnoor zata yarda bappa ya yi masu ?akinsu su biyu kawai? Zata yarda ta zauna da shi? Ya makomar Faisal bawan Allah? To dai dukka nan da lokacin ?an?ani zaku ji komai, mu le?a KINGDOM OF POWER mu dawo.
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...???????
___________KINGDOM OF POWER????
MOMMA AND KUYANGA MAMA HAULAT.
A fujaje kuyanga mama Haulat ta ?ago kanta tare da zaro idanu tana kallon Mommar, while ita ma Mommar ita take kallo.
"Ranki ya da?e gimbiya Momma kina nufin dama kin san mammie green snake under green grass ce?". A ru?e ta yi tambayar.
Jinjina mata kai ta yi alamar tabbatarwa da tasan komai shiru kawai take yi, duk wasu bibiyarta da suke yi tana sane, duk wani makirci da munafurcin da suke shirya mata tana sane da su, lokacin su ne kawai adbata da, ba su isheta kallo ba, dan ita tasan ta ri?e Allah, ta yarda da tauhidinta, dan haka bata da wani sauran fargaba.
Da hannu ta yi wa mama Haulat nuni da ta je kawai ta bata waje.
Jiki ba kwari ta mi?e, cike da ru?u da damuwa ta nufi waje, ita ce amintaciyar Momma, duk wasu sirrukan da Mommar take ?oyewa ta sansu, babu abin da bata sani ba, shiyasa ta girgiza da jin zancen cewa Mommar tasan duk wasu abubuwan da suke faruwa shiru kawai take yi, akwai matsala.
A can cikin fada kuwa, sai tattaunawa King yake kara yi da dattawan cikin fadan, yanzu aiyuka biyu ne a gabansu, na farko yakar Queen Zarina wanda ya zamar masu dole, dan su basa yafiya in dai aka ta?osu, sun ma yi kokarin da suka ?aga mata kafa har ta ?an kwana biyu basu ladabtar da ita ba, ba dan komai suka yi hakan ba kuma face saboda rashin nutsuwa da suke ciki na ?atar Spender.
Abu na biyu kuma da yake gabansu shi ne neman dik in da Spender yake su dawo da shi, yanzu dik hankalinsu a tashe, kullun suna cikin zaman tattaunawa ta yadda zasu shawo kan matsalarsu, abin ya ?aga hankulansu.
After some hours.
Rana ta yi sanyi alamar ta kusa fa?uwa, garin ya yi tsit tamkar babu mutane, sai harkokin gabansu kowa yake yi, kafa ta ?auke har a kan tituna, akwai alamar hadarin ruwan sama sosai a sararin samaniya.
Sanye take da doguwar malesian gown, ta ?aura short winter jacket mai hula a sama, ta sanya hular a kanta.
Fitowa ta yi daga part ?in Momma zata nufi part ?in Akka, da farko a tare suka fito da Auta, sai Autar ta ce bari ta koma ta canza kaya dan tana jin sanyi.
Shi ne ta koma ta sako Turkish casual warm ware a jikinta, tana fitowa domin ta bi bayan Chuchun sai ta ha?u da uncle Taheer da ya fito daga part ?in mama, shi ne ya ce tazo su je lambun dad su yi hira ta ?ebe mashi kewa, ba dan ta so ba ta bi bayansa suka tafi.
Ita kuma Chuchu sarkin waya, tana tafiya tana latsa waya bata ganin gabanta, saura ka?an su yi karo da Yah Rizwan, ambatar sunanta da ya yi ne yasa ta farga tare da ?ago kai a hanzarce, sai ta yi baya ka?an.
"Wani irin danna waya ne wannan my Jannaty? Idan kika je kina bugu da wani abin fa?". Cikin sanyin murya ya yi maganar.
?asa ta yi da kai. "Ka yi hakuri Yah Rizwan zan gyara".
Siririn murmushi ya saki. "To shikenan, amma yanzu kin yi wuyar gani my Jannaty, tun jiya nake magiyar a bani dama mu ga juna anki ko? To laifin me na yi?". Cikin zolaya ya kai karshen maganar.
"Baka yi laifin komai ba Yah Rizwan, kuma kai ai baka laifi, Allah ya hanani ganin ranar da za'a ce ni Jannat ka yi mun laifi, kawai dai barci ne jiya ya ?aukeni muna waya, da safe kuma na je school, da muka dawo na gaji sosai sai na kwanta sai yanzu na samu na tashi na yi wanka na fito, dama kai nake ?o?arin kira yanzu".
Wani irin sanyi ya ji a ransa na yadda ta ce shi take ?o?arin kira a yanzu, ya ji da?i, a ganinsa ta damu da shi, zuciyarsa tana yaudararsa akan ta damu kuma tana sonsa sosai, ita kuwa a duk lokacin da take tare da ?aya, in ma Jawad ko Rizwan ?in to mantawa take yi da tana soyayya da ?aya, abin kamar ba lafiya ba, sai ta ha?u da ?aya take tunawa da suna soyayya ashe.
"Ina zaki je yanzu to?". Cikin nutsuwarsa sosai yake, yana da kamala da nutsuwa matu?a, ga hankali da sanin yakamata, ga kuma kaunar ?an uwansa.
"Part ?in Akka zan je". Ta bashi amsa kanta a ?asa, tana jin kunyarsa sosai ba kamar Yah Jawad da suke karewa juna kallo har cikin ido ba.
"To yaushe zan samu a bani dama mu zauna mu yi hira?". Ya yi maganar ha?e da le?o face ?inta.
Tana ta sakin murmushi ta ce. "Anjuma da daddare, yanzu zan je part ?in Akka ne mu tafi gaishe da mijin Aunty Sarina da ya zo ni da Aunty Fanan".
?an zaro idanu ya yi tare da fa?in. "Wace Sarinar kuma wani miji? A yaushe ta yi miji ban sani ba?".
Idan baku manta ba da safe lokacin da King ya yi sanarwar shi baya wajen, so bai san da batun zuwan saurayin ba.
"Da safe ne dad ya ce akwai wasu yarima da zasu zo wajen Aunty Sarina da kuma Aunty Fanan, to su ne suka zo yanzu, baka ji jiniya da busoshi ta ko'ina bane ?azun?".
Sai a lokacin ya tuna da ?azun ya ?an ji jiya ka?an, sai dai hakan bai wani ?auki lokaci ba ya ji komai ya yi shiru tsit, abin bai sa ya yi tunanin ko baki suka yi ba, dan yadda ya ji jiniyar bata wani yawaita ba kuma ba'a jima ba ta ?auke, bai san cewa commander Zafar ne ya taka masu birki yasa suka kashe jiniyoyin nasu ba, basu san dokokin kingdom of power ba, sun wani shigo da jiniyar motocin ?an'sanda, a dokar masarautar kuma babu wanda ya isa ya shigo masu cikinta kamar wani shegen kwaro, kowa kansa a ?asa zai zama idan zai shigo, baka isa ka zo ka ce zaka nuna kaima wani shegen bane, dan fa wajen manyan kai ka zo, dole ka rusuna ka zama tamkar bawa a gabansu, hakan yasa commander ya daka masu warning ya kuma sanya suka kashe jiniyar suka ?ariso ciki suna masu ?as?antar da kansu ?asa. Kai kingdom of power duniya ne, dik wani ji da kanka da isarka sun take ka, suna mulki bisa dokokinsu masu ?arfin gaske, sun ci ka masu power ?in da gaske, ba mai keta dokokinsu ya zauna lafiya, wane mutun!!.
"Okey na gane, to jeki zamu yi magana da su dad ?in". Ya kai karshen maganar tare da sa kai ya wuce yana mai kallon face ?inta.
Ita ma wucewa ta yi tare da cigaba da latsa wayar ta, ta sunkuyar da kanta ?asa, bata sanin in da take takawa saboda hankalinta gaba?aya yana kan waya, hotunan sabbin kaya take dubawa wanda zata nunawa Aunty MieMie ta buga masu odersu ita da auta.
Tafiya kawai take yi saura ka?a ta buga kanta da jikin bangon wajen kwanar da zata sadaka da part ?in na Akka, ba zato ba tsammani kwatsam sai ji ta yi ta buga kanta da kirjin mutum.
A hanzarce ta ?ago kai dan taga wanene?. Yana tsaye ya har?e hannayensa a saman kirjinsa, tun daga nesa ya hangota tana zuwa tana latsa waya, shiru ya zuba idanu yana ta kallonta, sai da ya ga zata buga kanta da jikin bangon wajen ne ya yi maza ya shiga tsakaninta da bangon ta fa?o saman kirjinsa.
Ganin shi ne yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da mayar da kanta a saman kirjinsa ta kwantar. "Yah Jawad ?ina ina kewarka sosai, ina ka shiga tun safe?".
(Wato ana iya hege a cikin kingdom ?in nan, shi Rizwan ya ce yana kawarta ta yi wuyar gani, bata ce tana kewarsa ba bata ce mashi komai ba, amma ta zo ta wani ce wa Jawad tana kewarsa, wato wani abin ma sai gaba fa my people's.............??)
Kura mata idanu ya yi yana kallonta ba tare da ya furta uppan ba. Tana daga kwance a kirjin nasa ta turo baki. "My melody ka yi magana mana! Wai ko kai baka yi kewata bane?". A shagwa?e kamar zata yi kuka ta yi maganar.
Shiru bai amsa mata ba, kuma bai dai'na kallonta ba.
Yun?urawa ta yi zata bar jikinsa tana fa?in. "Kenan ni ka?ai ce na yi kewar ka ko? Ba damuwa". Ita a dole ta yi fushi ne zata tafi.
Hannunsa dake saman kirjinsa ya saukar tare da rungumota da su da kyau, cikin wata iriyar kasalalliyar murya ya furta. "Yau da rigima ake ji kenan? To ban da abinki Jannat ai kin san dole zan yi kewarki ko? Kewar taki ce ma tasa na ?asa yin magana da na ganki, kin san ya nake ji a rai'na kuwa?".
Kai ta girgiza mashi alamar a'a idanunta a tsaye cikin nasa, while shi ma kallonta yake yi.
"To ji nake yi idan ban mayar dake cikin kirjina mun cure mun zama abu guda ba ba zan ji sanyi a rai'na ba, dan haka a daina yi mun rigimar nan haka.......". Da kyar ya iya kai karshen maganar sakamako ido ?aya da ta kashe mashi dan tsokana.
Ajiyar zuciya ya sauke ya kasa yin magana, ta goge mashi hadda, ashe ita ma ta iya kashe ido ?aya.
"Yah Jawad yauwa ka ?aukeni hoto ina tsaye full ka ji?".
Jinjina mata kai kawai ya yi ba tare da ya iya furta kalma ba. Wayar dake hannunta ta mi?a mashi tare da raba jikinta da nasa. Baya ka?an ta ?an koma tare da tsara style na yadda za'a ?auketa hoton.
Ba musu ya shiga camera, sai dai kuma saboda neman tsokana irin nasa sai ya sanya mata filter kare, ta zama mai doggin kunnuwa da katon hanci, a haka ya yi mata hotuna kala biyar.
A hanzarce ta ce ya kawo ta gani, ba musu ya mi?a mata wayar yana ?unshe dariyar muguntar da ta ciyosa, dan yasan zasu kai ruwa rana yau.
Tana ?aura idanunta a kan hotunan a fujaje ta ?ago da kallonta a kansa, ai a ?ari wata iriyar dariyar mugunta ta kubce mashi, da gudu ya bar wajen ya nufi part ?insa.
Aikuwa da karfi ta furta wlh ba zata hakura ba, ba zata barshi ba, tana magana hawaye yana zuba, da gudu ta bi bayansa dan ta ?auki fansa, ta ci alwashin ba zata kyalesa ba.
Kai my people's na rubutu yau fa, kai kun samu long page over. Saura ku bani hote comments kuma.
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...???????
??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????
??RAWANIN ?? ZALINCI ????
????????????????
FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????
?????????? 12/11/2024.....??????
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????
??ZANGO NA BIYU....??????
37
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...???????
A can part ?in uncle Abbas kuwa, manya manyan motoci ne shake a parking space na part ?in, bakin Sarina and Fanan ne suka iso, ga manya manyan bodyguards masu tsaronsu, ga jama'ar fada wato dogarawa, harabar gidan a cike yake da jama'a, su kuwa bakin an wuce da su wajen saukar baki bisa jagoranci uncle Abbas da ya tarbesu hannu bibbiyu. Sun samu tarba ta girma da girmamawa.
Sarina tana can tana shiri, muguwar makirace yarinyar nan, tasan da cewa tana da diri mai kyau, kuma my people's kun sani dai a dik cikin ahalin King Abdul Malik daga kan ?a?a har izuwa jikoki babu munana, gaba?ayansu kyawawan gaske ne, sai dai kyan wani ya fi na wani, coz tasan tana da kyau, gata doguwa, dik wasu shika shikan kyau ta cikasu, haka ta zauna ta tsara kwalliyar da dik wanda ya ganta sai ya sake waigawa, ta sanya wasu shegun matsastsun kaya da su ka bayyanar da surar jikinta.
Burinta a nan shi ne ta kwa?aita masu surar jikinta ta yadda ko sun tafi tunaninta zai hanasu sakat, sannan ta tabka masu rashin mutuncin da sai sun yi danasanin zuwansu wajenta, tana burin su tafi suna masu danasanin zuwansu, sannan kuma su tafi suna masu kwadayin surar jikinta, sha'awarta ta hanasu sukuni, su sha bakar wahala wajen yaki da zuciyoyinsu dan su cire tunaninta, wannan shi ne dalilin da yasa dik namijin da aka ce zai zo wajenta sai ta tsaya ta tsantsara kwalliya na wuce tsara, sannan ta tunkari in da yake.
Shegiyar mata ce yarinyar, ta san kan duniya sosai, sai dai ni kuma na ce in ta san wani ai bata san wani ba ko my people's? Mu je dai zuwa.
Wani irin ?an iskan athletic wear ta sanya, kayan sun matseta sosai, dik wasu albarkatu na jikinta sai da suka bayyana, ta sake arab hairn nan nata har baya, sannan ta sanya wani she?anin high heel, daga karshe sai ta ?aura wani irin after dress mai kama da transparent net a saman dressing ?in nata, ta ?aura silk scarves a kanta, wasu irin siraran doggin diamond earrings ta sanya a kunnenta, ta yi kyau kam na karya.
Yanayin dressing ?in nata dai tafi kama da tantiriyar shai?aniyar karuwa, sam bata yi kama da mutanen kirki ba, dik kuma abin da take yi kada ku manta mammie ?insu ke goya masu baya.
Sai dai kuma hali ya sha banban a wannan waje, dan kuwa lokacin da Mammie ta sa?awa Fanan ga yadda zata yi ta kori wannan yariman nata sai ta ce wlh ba zata iya ba, ita ba zata yi mashi rashin mutunci ba, su kyaleta tasan ta yadda zata yi ta rabu da shi lafiya, sosai mammie ta ji haushin hakan, amma ba yadda ta iya face ta kyaleta ?in, dan idan ta ce zata ?aga murya uncle Abbas zai iya sanin me yake faruwa, idan kuma ya sani kun san ba zasu wanye lafiya ba, asirinta ne zai tonu.
Wani irin luxury glass cup ta ?auka, abin sha ta zuba a ciki dai'dai tsakiyar cup ?in, sannan ta shiga room ?in Mammienta ta yi mata sallama.
Sai sa mata albarka Mammien take yi tana yi mata fatan nasar. Me kuke tunani Sarina zata yi wa wannan guy ?in? Muje dai zuwa.
Ita kuwa Fanan dressing ta yi tamkar ?a?an manyan sarakuna da ake ji dasu, dressing irin ta addinin musulunci, har da alkyabbar ta ?aura a saman kayan jikin nata, ta fito a jinin sarautarta da kyau.
Ita kam Sarina ai ta yi nisa bata jin kira, cikin wani irin shai?anin takun da dik in da ta taka sai halittun jikinta sun motsa ta nufi wajen nasu.
Duk wasu bodyguards kai har da mayakan dake cikin part ?in sai da suka ji wani abin ya motsa masu a lokacin da suka sau?e kallonsu a kanta, dik sai da suka kwa?aitu da surar jikinta, ta ja hankulan su sosai, ta tafi da imanin dayawa daga cikinsu.
Harta tsofaffin dake cikin dokaran yariman sai da suka ha?iyi yawu na ganin santala santalan cinyoyinta game da coca colar shape ?inta, ga bayanta yadda yake wani juyi.