Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 70

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 70

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 70: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 70. Jini ne yake zuba daga kafarta ta dama, da sauri ya kai hannu ya ri?o kafar…

3,372 words

Jini ne yake zuba daga kafarta ta dama, da sauri ya kai hannu ya ri?o kafar tata, jini sosai yake zuba, sam bai iya gane me ya sameta a wajen ba, saboda jinin ya wanke wajen, shin yankace ko dai wani abin ne ya soketa har ya fasa fatar kafar haka? Jini sosai ya rufe wajen ciwo baka iya gani, ga jinin nata jajir da shi.

Dawo da kallonsa saman face ?inta ya yi, ta datse idanu gam, ba abin da zaka gani face hawaye dake bin ?uncinta kamar ruwa ya faso hanya. Da alama bata ma san yana kanta ba.

?an mi?ewa ya yi, ya du?a ya ?auketa cak suka nufi cikin gida. Bappa dai yana ta ?o?arin gyara wajen da zasu yi bukkar kusa da ?akinsu Mahnoor ?in ta gefe haka.

Gaba?aya kunya ya ji tamkar ?asa ta tsage ya shiga ciki na ganin bappa a tsakar gidan, sai ya ji dama bai ?auketa ba, wato shi fa wlh kunyar a jininsa take, ba wai tsiya bace kamar yadda Jawad yake tsokanarsa da shi, ai kunga ko zai ji kunyar kowa ban da Yah Jawad, so shiyasa Jawad ?in yake ganin kamar iyashege ne ba kunya ba dan shi baya nuna mashi yana jin kunyarsa.

Ko kallon in da bappan yake yaki ya yi, yadda kuka san ya gefar da ita a ?asa haka yake ji, sam bai yi tunanin zai isko bappan a tsakar gidan ba, da Allah ba zai ?aukota ba sai dai ya taimaka mata ta mi?e ta taka da kafafunta su dawo.

Shi fa wlh ko da Mahreen baya son jerawa mutanen gari su gansu bare kuma bappa, kunya hakan take bashi. Allah sarki yaron Mommarsa mai alkunya.........??

Saman wata dutse da suke zama su goge kafa idan sun fito daga wanka ya zaunar da ita, sam ?an tahali?in nan yaki yarda ya juyo in da bappa yake, yana ganin kamar idan ya juyo zasu ha?a idanu ne.

Shi kansa bappa abin ya yi matu?ar bashi kunya yadda ya ?aukota ya keta wajen nan jama'a suna wucewa ya shigo da ita, amma da yake yana kaunarta sosai sai ya danne kunyar a ru?e ya fara tambayarsu meyafaru kafarta ke jini?.

A dai'dai lokacin Mahreen ta fito daga cikin ?aki tana zabga uban hamma kamar zata ci babu, da alama da yunwa ta taso daga wannan barci.

Ganin abin dake faruwa yasa ta yi saurin ?arisowa wajen tana tambayar hamman nata me ya faru?.

Bai kulasu ba ya yun?ura zai mi?e ya bar wajen, cikin jin ra?a?in ciwo ta ri?o wuyarsa yadda ta sa?alosa lokacin da ya ?auketa ha?e da fa?in zafi kafarta yake yi mata, su taimaka mata su cire mata zafin.

Shi kuwa kunyar bappa yasa zai bar wajen dama, baya son su ha?a ido, ba wai dan baya son taimaka mata ko bai ji tausayinta ba, aa, ko ?aya, hasali ma ya so ya wanke mata kafar, ya wanke jinin sai ya duba menene ya ji mata ciwo a wajen.

Bappa ya lura da kunyarsa yasa Jaish ?in yake son gudu ya bar wajen, bai san cewa shi kansa abin ya bashi kunya ba, in gaya maku Mahreen ce kawai bata ji komai ba, dan kun san ita kunya ya yi gabas ne ita kuma ta yi yamma, sam basu da ha?i.

Ganin yadda ta ri?e mashi wuya gam tana kuka ha?e da magiyar a cire mata zafin ne yasa ya koma ya tsugunna a gaban nata, a hankali ya kai hannunsa ya fara ?o?arin cire hannunta da ta sarkafe wuyarsa da shi.

Hakan yasa bappa ya ji ba zai iya ganinsu ba, sai kawai ya fice daga gidan ya basu waje, ya nufi gonarsa na su tomatoes dake kusa da gidan, dan ya je ha fara saro itacen da zai ha?a masu bukka da shi kafin su gama abin da suke yi.

Ganin bappan ya fice ya basu waje ne yasa sai ya fasa cire hannun nata daga wuyarsa, dama wai zai cire hannun nata ne dan ya samu ya bar wajen, yana son taimaka mata amma idan bappa na wajen ba zai yi ba, da tafiyarsa zai yi abinsa, amma tun da bappan baya nan sai ya kai hannu ya kamo kafar tata.

A gabansu Mahreen ta tsugunna, idanu jajir da su saboda barci, ga yunwa, sai daka hamma take yi, kamar zata yi kuka ta kai hannu ta sa?alo wuyarsa saman hannun Mahnoor dake wuyar tasa, lallausan kumatunsa ta shafa da ?ayar hannun nata, cikin fuskar tausayi ta ce. "Hamma meyasami Adda Mahnoor ?ita?".

Dawo da kallonsa saman face ?inta ya yi, hannunsa ?aya ya kai ya shafi face dinta kafin ya yi mata alama da ba komai, sannan ya yi mata alamar ta kawo mashi ruwa.

Ba shakka akwai sha?uwa sosai a tsakanin shi da Mahreen, sha?u kam mai karfi ma.

Da sauri ta mi?e ta nufi cikin kitchen, ruwa ta ?ebo a cikin butar karfe irin na mutanen da ?in nan ta dawo da shi in da suke.

A gabansu ta tsugunna ta mi?a mashi. Kar?a ya yi, hannunsa yasa a saman wajen ciwon ya fara zuba ruwan yana wanke mata jinin.

Sosai ta kara tsananta kukan nata, saboda ruwan sanyi da ya ta?a ciwon, sai ya kara azabar zafi.

Yana wankewa wata jinin tana ?ul?ula, sai dai kuma da ya wanke ya gano babbar ciwo ta ji sosai, wani kwalba ne ya fasa mata fatar har nama, ya yanketa sosai da sosai.

A hankali wani irin tsananin tausayinta ya ratsa zuciyarsa sosai, tsumma mai tsabta ya bu?aci Mahreen da ta kawo mashi.

?aure mata kafar ya yi ko zai samu jinin ya ?an tsagaita su saka magani, dan shi ma a yanzu ya san magunguna da dama na gargajiya.

Mi?ewa ya yi ya ?auketa izuwa ?akin bappa, da sauri Mahreen ta rufa masu baya. Saman gado ya zaunar da ita, sai a lokacin ta sakar mashi wuyarsa, dan ta ?an ji sassaucin zogin.

Juyawa ya yi zai fita sai kuma kamar wanda aka cewa ya juyo, yana jiyowa suka ha?a idanun, dan jin zai fice yasa ta yi saurin waro idanu dan tagansa kafin ya fita.

Yana ha?a idanu da ita tunanin yadda ta tashi hankalinta a ?azun da kaska ta hau hannunsa ya fa?o mashi, ya ji da?i sosai yadda ta ru?e ta kuma taimaka mashi, ta nuna tsantsar tausayinta a gare shi, tuna hakan yasa ya juyo ya dawo, ya fasa ficewa.

Da sauri ta sunkuyar da kanta ?asa tana mamakin me ya dawo da shi kuma?.

Sai surutu Mahreen take zuba masu babu wanda yake iya jin me take fa?a, dan kuwa duk sun afka duniyar tunani.

A kusa da ita ya zauna yana kai hannu ya ri?o kafar tata, mamaki ne ya kusa sanyata suma, bata ta?a zaton hakan ba. Ita dai Mahreen sai tambayar ina Nenne take take yi, ba wanda ya bata amsa, ni kuwa princess Teema na ce Nenne ai ta saki kanta da kanta, bappa dai ba ruwan, ta ha?a kaya sai gidan Ar?o abinta, dan dai bappa namu na gargajiya kam bai sake ta ba, kuma bai ce ta tafi gidan Ar?o ba, rashin albarka ne irin tata da rashin ilimin sanin darajar miji, kai ita bama tasan me ake nufi da miji ba, kan fanko ne.

Alama ya yi mata da hannu a kan har yanzu wajen yana yi mata zafi?. Mamaki ya hanata iya amsawa, ta yi suman zaune, kanta a ?asa ta kasa iya ?agowa.

Ya fahimci ita ma kunya ce da ita sosai kamar shi, hakan yasa ya saki kafar tata tare da mi?ewa ya nufi waje da nufin ya je ha tsinko magunguna ya zo ya ha?a mata, sam baya son su ha?u da bappa a yau ?in nan, dan haka yana fitowa ya bi ta baya dan karsu ha?u.

Ai kuwa ya gudu bai tsira ba, dan kuwa bai yi zaton bappa yana wannan gona na su tomatoes ?in ba, can kuma ya shiga dan ya ciro abin da zai ciro. Yana sanya kai unexpect suka yi ido hu?u, ai wani irin kunyar da ya ji tamkar ya ce ?asa ta tsage ya shige ciki, sai ya ji kamar ya juya ya fasa shiga, gaba?aya sai ya ji ya rasa sukuninsa.

Shi kam bappan da yake yasan halin kayansa sai ya kawar da kansa kamar bai gansa ba, dan baya son ganin ?an nasa a cikin takura, bayan son yaga ya takure kansa saboda kunya, sai ya matsa can cikin gonar ma ya bashi damar shiga ya yi abin da zai yi ba tare da ya takura kansa ba.

Ya fahimci sarai bappa ya gano yana tsananin jin kunyarsa, ya fahimci da gangan ya wuce can cikin gonar ya bashi waje, ajiyar zuciya ya sau?e tare da ?arisawa wajen bishiyar zogale, dan ganyenta yana tallafawa wajen tsayar da jini, idan jinin ya yawaita over wajen zuba to yana ragesa, idan kuma ba dayawa sosai bane yana ?auketa gaba?aya.

Bari na baku magunguna biyu zuwa uku dangane da zogale domin mu karu da juna kafin na wuce. Ina masu ulcer? To zogale takuce, ku matso kusa. Komai karfin ulcerki idan kika samu furen zogale, ki gyarata ki wanketa tsab, sannan ki zuba a tukunya, ki sanya ruwa kada ya wuce litter ?aya, sai ki ?aurata saman wuta, idan ta tafasa sosai, ki sau?eta ki tace, sai ki zuba zuma a cikin ruwan ki sake ?aurata a wuta ta tafasa na minti uku zuwa biyar, sai ki sauke, da ?an ?uminta zaki rin?a sha, da izinin Allah zaki rabu da ulcer.

Magani na biyu, ki yi wa ganyenta shanyar inuwa, idan ta bushe ki dakata ta yi laushi sosai, ki samu nonon shanu mai kyau, sai ki rin?a zuba tea spoon uku na garinta a cikin nonon kina zuba zuma tea spoon biyu, ki garwaya sosai ki sha, wlh yana matu?ar saukarwa da mace ni'ima, yana kuma maganin sanyin ciki sosai.

Na uku, ki rin?a dafa ganyen zogalen kina tace ruwan, ki zuba zuma ki sha, yana matu?ar wanke jini, yana kashe kwayoyin cutar sanyi na ciki, tana matu?ar saukarwa da mace ni'ima sosai, ki gwada zaki sha mamaki In Sha Allah.

Kina iya dafa ruwan ganyen, ki zuba a cikin buta kina tsarki da shi, yana matu?ar gyara wajen sosai, yana kashe kwayoyin cuta, sannan yana ?auke duk wani wari. To ya isa haka mu koma kan karatunmu, sai kuma wani lokacin.......... A karshen littafin nan da izinin Allah zan baku wasu sirrika, ina matan da mazansu ke biye biyen matan banza a waje? Ina iyayen da suka fuskanci jarabawa na ?a?ansu suna shaye shaye da bin matan banza? Ina iyayen da ?a?ansu basa jin maganarsu? Sun bijire masu basa ji? Ina iyayen da suke fuskantar matsalolin tsakaninsu da ?an uwan miji? Baki yi masu komai ba su ?auki karan tsana su ?aura maki? Ina matan da mazansu suke wahalar da su ba tare da kina da hakkinsu ba? Baki yi wa namiji komai ba kawai ya rin?a azabtar dake yana cusa maki bakinciki? Ina masu son mallake zuciyar mai gida? To duk ku matso, a karshen littafin nan zan baku wani sirri na musamman, amma ki tabbatar da cewa tsakaninki da Allah kike zaune da kowa, kada ki cutawa kowa, sirri ce ta musamman, magani ne irin ta addinin Musulunci, in dai zaki yi shi yadda yake to da izinin Allah duk wata damuwarki zata warware, zaki samu waraka da yardan Allah, sai dai ina kara ha?aku da Allah da ku zauna da kowa da zuciya ?aya, domin da ki cuci mutum gara shi ya cuceki, kada ki je Allah ya mallaka maki zuciyar oga kuma ya zamana kina da kishiya ki cuta mata! Ki ji tsoron Allah ki sani akwai mutu, ni dan saboda iyayen da yaransu ke biye biyen mata, da matan da mazansu ke biye biyen matan banza a waje ma yasa zan bada, a dai ji tsoron Allah na fa?a na kara fa?a, wlh duk wadda tasan da kudurin niyar cutar wata ko wani a ranta ya Allah kasa ko zata yi sau miliyan kada bukatarta ta biya ato, babu ruwana, In Sha Allah a karshen littafin nan na yi maku tanadi na musamman, fatana dai Allah ya kaimu da rai da lafiya, ina kaunarku my people's.......??

STORY ??

Sinko dik abin da zai bu?ata ya yi, ya dawo cikin gidan.

Kai tsaye bappa room ya nufa, zaune ya iskota ita da Jumma ?ar Inna Rabi, sun yi wa Mahreen wayo sun koreta, sai suka kama hira a kan aurensu, Jumma tana kara bata shawarar ta yarda ta zauna da Jaish, kun san fa ita Jumma ta ?an waye, dan tana zuwa cikin birni tallar nono, so ta fi Mahnoor wayo nesa ba kusa ba, ta san wasu abubuwan na duniya, sannan bugu da ?ari mamarta malamar addini ce sosai, ta koyar da su daidai gwargwado, so yanzu sai ?o?arin wayarwa da Mahnoor kai take yi a kan ta yarda ta zauna da shi zata ji da?i.

Aikota fa Inna Rabin ta yi a kan ta zo ta kira mata Mahnoor ?in, dan Innar ma ta samu labarin auren da aka ?aura wa Mahnoor ?in, shi ne ta ce ta kira mata ita tana son yin magana da ita. Shi ne da ta zo ta samu ta ji ciwo a kafa sai ta samu waje ta yi zamanta suka kama hira a kan gidan miji, yara sun girma Inna Rabi bata sani ba.

Wani irin tsoro ne ya kama Jumma na ganin yau gata ga Jaish a ?aki guda, ta kafeshi da idanu tamkar zata cinye shi, shi kuwa da bai san da wata halitta a wajen ba, abin da yake gabansa kawai yake yi, a kusa da ita ya tsugunna tare da kamo kafar tata, cikin nutsuwa yake murje ganyayyakin magungunan da ya tsinko yana sanya mata a ciwon.

Sai washe take fa?a, sai ma da ya sa hannu ya bu?e ciwon nata da kyau zai ?iga ruwan ganyen zogale da ya murje ya matse, datse idanu ta yi tana kuka a hankali hankali.

Jumma kam tamkar zata sume, abin ya yi matu?ar burgeta yadda yake yi wa matarsa magani cikin nutsuwa da takatsantsan ga tsantsar kula, sai dai kuma a tsorace take, dan har yau har gobe yana ru?ar da ita idan taga kyansa.

Ba ita yake yi wa magani ba, amma it ce jikinta yake kerma.

Bayan ya gama abin da yake yi ya mayar da tsummar ya ?aure mata kafar, dik da jinin ya tsaya da zuba hakan bai sa ya cire tsummar ya jefar ba, saboda yana son maganin ta nutsa ciki ciwon sosai.

Mi?ewa ya yi tare da ?an ?aura hannunsa a kanta alamar sannu ya yi mata, daga haka ya nufi waje.

Kamar jira take yi ya fita, yana kurewa ganinsu ta yi maza ta ce. "Amma gaskiya Mahnoor baki da hankali!".

Cikin jin zafin ciwo ta zaro idanu kafin ta ce. "Mekuma na yi na rashin hankali Jumma?".

"Mema baki yi ba! Yanzu dan tsabar rashin hankali da rashin mafa?i ne kike ?o?arin ha?a hamma Faisal da wannan jarumin namijin? Me kuma wani hamma Faisal? Ki duba fa ki ga yadda ya yi maki magani a yanzu, komai cikin natsuwa, ki ga kalar jaruntarsa a jikinsa fa! Ke kam baki da hankali wlh". A kule ta kai karshen maganar, ji take yi dama ita ce ta same shi!.

"Jumma amma dai kin san cewa hamma Faisal ?in ma idan ya ga naji ciwo irin haka hankalinsa zai ta shi ko? Kuma da kike maganar Hamma ya yi mun magani ki sani shi ma hamma Faisal ?in fa wlh tsab zai yi mun magani kamar yadda hamman ya yi mun a yanzu, ko ma dai fin hakan". Tana magana tana ciza la??anta alamar tana jin zafin kafar tata.

A hanzarce ta capki zancen da cewa. "A'a wlh Mahnoor, baki son gaskiya ne kawai, amma ke kanki kin san hamma Faisal dai ba zai yi maki magani kamar yadda wannan hamman naku ya yi maki ba, ki duba kiga yadda yake gudanar da komai nasa, abin gwanin ban sha'awa, wlh da ma nice na same shi ai da na more". Da iyaka gaskiyarta take magana kuma cike da confidence!.

Harara ta wurga mata da wa?an nan idanun nata da suke jajir ?in, sannan ta ce. "Hmmmm Jumma kenan, ni dai koma me zaki ce hamma Faisal shi ne a raina, shi nake so! Da shi kuma na saba".

Ita ma hararar ta wurga mata kafin ta amsa da. "Ai kuwa gara ki fara son wannan hamman naku, dan wlh babu kwatan kwacinsa a garin nan, amma a juri zuwa rafi watarana tulun zai fashe, idan bappa ya mi?a mashi ke ki ce ba zaki je ba mu gani".

A kule ta ce. "Ba zan je ba ?in kuwa".

Tuntsirewa da dariya mai ?an sauti Jumma ta yi, cike da shakiyanci da iyashege tana dariya ta ce. "Allah da gaske ba zaki je ba amaryar hammanta?".

Kai ta gya?a bilhakki da gaskiyarta ba zata je ba.

Kara fa?a?a dariyar tata ta yi, cike da tsiya ta ce. "Kada fa watarana a wayi gari na zo kawo maki ziraya kina cikin ?aki ki ce mun hamma yana nan in tafi ba zaki fito ba".

A harzuke ta ce. "Me zan yi da shi a cikin ?akin da har idan yana nan zan ce ki tafi?. Wai ke waye ya ce maki ma ni zan yarda mu zauna ?aki ?aya ne? Tab ni ai ina ?akinmu ni da ?ar uwata! Hauka nake yi zan zauna da shi?!". Ta kai karshen maganar tana banka mata harara.

"Me ake yi a cikin ?aki dama? Ai na gaya maki idan bappa ya mi?a mashi ke kice ba zaki je ba". Tana kai karshen maganar ta sake tuntsurewa da dariya, Inna Rabi tana can tana jiranta ta tsaya nan tana iyashege.

Shiru ta yi mata bata amsa ba, dan ta lura idan ta biyewa Jumma wlh tsab zata sanyata kuka.

?an matsowa kusa da ita ta yi, da kyar ta dakatar da dariyar tata, kamar wata maras gaskiya ta yi wani ?asa da murya, sai dai cike da iyashege ta fara magana kamar haka. "Kin san me Mahnoor?".

Girgiza mata kai ta yi alamar a'a bata sani ba. "Akwai wata uwar ?akina a birni, matar suna da ku?i sosai, gidansu akwai kyau, tana sayar nono cikin katon kwarya su saka a cikin wani abin da yake yin sanyi (freezer) baya lalacewa, sannan tana sayan man shanu sosai a wajena, kullun ina kai mata nonon kwarya guda, matar tana bala'in sona, ta ce ina yi mata kyau, ita take koya mun wasu abubuwa, da kam ma ta ce wai ?anta zai aure ni, shi kuma yaron ya ce shi baya son wadda bata yi makaranta ba, baya son yar kauye mai tallar nono, har da cewa ya yi ya tsaneni, amma mamarsa tana da kirki sosai, ta bani hakuri ta ce idan aure na ya zo har nan garin zata zo ta kawo mun abubuwa kyauta, kema zan koya maki duk abin da ta koya mun dangane da miji".

?an dakatawa ta yi tana sauke ajiyar zuciya kafin ta cigaba da cewa. "To a gidan na ji suna fa?in mazansu wato mazan birni suna da shegen jarabar tsiya sosai, dan haka sai ki shirya, kinga ke mijinki wlh ?an birni ne, dan ni ba zan ta?a yarda daga kauyen yake ba, saboda bai yi kalar kauye ba". Ta kai karshen maganar tana ?an karkata kanta ta le?o hanyar fita daga ?akin dan taga babu mai zuwa dai ko?!.

A ?an tsorace ta zaro idanu tare da fa?in. "Me kuma wani jaraba?".

Matsowa ta yi dab da kunnenta, ?asa ?asa ta yi mata ra?ar menene jaraba tana ?unshe dariyar iyashege.

Ko me ta gaya mata? Su dai suka sani, a dubu ta zaro idanu tare da juyowa suka fuskanci juna. Tuntsurewa da dariya Jumma ta sake yi tare da kawar da zancen ta hanyar canza topic na magana a in da ta ce.

"Allah Mahnoor ina gaya maki ko a birni da nake zuwa, dik yawace yawacen da nake yi Allah ban ta?a cin karo da jarumin namiji kyakkyawar gaske irin mijinki ba, gara maki ki farka tun wuri ki rungumi abinki".

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull