Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 69
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 69: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 69. "Haka ne muna jin tsoron ha?a idanu da shi, amma ina son ki sani har la?ewa…
3,364 words
"Haka ne muna jin tsoron ha?a idanu da shi, amma ina son ki sani har la?ewa muke yi mu le?esa dan muga kyansa, wlh ki godewa Allah da wannan ni'ima da ya baki, ni ba dan tsoronsa da nake ji ba wlh da babu abin da zai hanani tinkararsa in ce ina sonsa, yana da kyau sosai, ki duba gashin kansa sam ba irin namu ba, har kyalli nasa yake yi, kai koya zan gaya maki ba zaki gane ba, amma dai yana da kyau ki san cewa kin yi sa'a, wannan ko da ha?i a kwatance ba za'a ha?a shi da Hamma Faisal ba".
Shiru ta ?an yi tana tattauna maganganun a cikin kwakwalwarta, dan ita a gaskiya Faisal take so, da wuya zuciyarta ta yarda da wani bakon.
"Kada ki tsaya yin wani dogon tunani Mahnoor, tunani ba naki bane, kawai ki rungumi mijinki ku zauna lafiya, idan ma baya sonki ki koya mashi sonki, idan ma kece baki sonsa to ki koya, yana da kyau ki dai'na tunanin Hamma Faisal a yanzu, yin hakan kin dai san Inna ta ce babban kuskure, da auren wani a kanka kana tunanin wani hakan sam bai dace ba, ba tana karantar da mu hakan a islamiya ba?". Ta jefe mata tambayar tana le?o face ?inta, while hannayenta suna a saman shoulder ?inta har lokacin.
"Amma kuma Jumma kin ji fa jama'a suna cewa maye ne shi ?in?". A tsorace ta yi maganar, muryarta har kerma yake yi.
"Ke kin yarda shi mayen ne?".
A hankali ta ?ago kai suka kalli juna ido cikin ido, wani irin tausayinta ne ya kama Jumma, tasan yadda zafin so yake, yarinya baiwar Allah, marainiyar Allah, sam kukanta baya da kyan gani ga koma waye ne idan ba bakin azzalumi irin Nenne ba.
"Jumma a da can baya na yarda Hamma aljani ne, amma ban ta?a yarda cewa shi maye bane". Tana kai karshen maganar hawayen da suka cika mata idanu ne suka gangaro mata sama face ?inta gwanin ban tausayi.
"A yanzu fa? Kin yarda shi aljanin ne?". Ta sake jefa mata tambayar tana mai da kallonta a kan shanu biyu da suke ?o?arin fara fa?a a bayansu.
"A'a yanzu na dai'na tunanin shi aljani ne, shiyasa ma na dai'na jin tsoronsa, amma kuma ba zan iya zama da shi ba Jumma, wlh idan ni da shi ne kawai zan ji tsoro, har yau har gobe ina jin tsoron ha?a ido da shi". Tsananta kukanta ya yi a lokacin da ta ce idan shi da ita ne kawai zata ji tsoro.
"Shin ya ta?a yi maki wani abin na mugunta ko na ban tsoro ne?". Ta yi maganar tana kai hannu saman face ?inta dan ta goge mata hawaye.
"Bai ta?a yi mun komai na mugunta ko ban tsoro ba, sai dai ma taimakona da ya sha yi, ko ranar da su Hamma Salisunku suka biyoni zasu dakeni shi ya tare mun ya hanasu dukana........".
A hanzarce ta tari numfashinta ba tare da ta barta ta kai aya ba ta ce. "Yauwa Alhamdulillah, to kin gani, kinga shi bangone ma a gareki, ki ri?esa hannu biyu zaki sha mamakin kulawar da zai baki, ina mai tabbatar maki watarana zai hana Nenne ma zalincin da take yi maki, ki jarraba ki gani".
Tunanin abin da ya faru a yanzu na hana Nenne dukanta da ya yi ne ya fa?o mata a rai, da alamar kamshin gaskiya a maganar Jumma fa, amma to taya zata fara iya zama da shi waje guda? Wannan abu ne mai matu?ar wahalar gaske a gareta.
Ganin ta afka duniyar tunanin ne yasa Jumma ta katseta da cewa. "Yanzu abin da nake so dake ki je ki faki idanunsa ki kure mashi kallo anjuma idan kin zo islamiyya sai ki gaya mun me kika ji a ranki lokacin da kika kare mashi kallon". Ta kai karshen maganar tare da kara goge mata hawayen da har yanzu suka ki dakatawa daga zuba.
Kai ta ?ago da nufin ta yi mata magana karaf idanunta suka sauka a kansa, yana tunkaro in da suke tsaye hannunsa ri?e da sandar bappa na kiwo, da kuma igiyoyi da zai ?aure kananan shanu, basa fita kiwo da kananan ciki irin wa?an da suka kusa kai yayen nan, tsaka tsakiya kenan, a haka ake koya masu yaye, za'a rin?a fita da uwar ana barin ?a?an, tun suna kuka har su zo su fara sabawa da rashin shan nonon, a hankali hankali har su manta da shi su dai'na sha, koda uwar ta dawo sai kuga basu wani damu da su zo su sha ba, saboda sun ci abincin da ya dace da su a gidan sun ?oshi sosai, so basu wani damuwa da nonon, a haka dai har su yaye kansu da kansu daga shan nonon.
So ya nufosu da nufin ya ?aure yaran kafin bappa ya fito su tafi, yau bata dama mashi fura da nono ba ta zo ta tsaya suna hira da Jumma, ko ?umamen safe bata ?aura ba, ko wutar ma bata hura ba.
"Jumma idan na zo islamiyya zamu ?arisa maganar ga Hamma nan yana zuwa, sannan In Sha Allah na san bappa zai barni na je dandali shagalin bikinki". Tana kai karshen maganar bata tsaya jin maganar da Jumma zata sake cewa ba ta yi saurin wucewa.
Jumma kuwa tun daga nesa ta kafe shi da idanu tana kallonsa babu ko kyaftawa, tamkar taga bako daga wani duniya. A cikin zuciyarta sai santin kyansa take yi, Allah ya gani tana bala'in son ta yi ta kallon face ?insa, kun san larabawa da turawa kyan gani ne da su ga da?in kallo.........??
Sai dai kuma tana tsoron ya kalleta su ha?a ido, dan haka da ya kusa isowa sai ta yi maza ita ma ta bar wajen ta nufi hanyar gidansu, tana tafiya tana waigosa, shi kuwa in da yasa gaba kawai yake kallo, ko ya ?ago ya kalli amaryar tasa ma yaki har ta zo ta wucesa tamkar bai santa ba.
Tana shiga cikin gida ta isko bappa da ya fito daga ban?aki a yanzu, hannunsa na ri?e da buta. Cikin girmamawa ha?e da nutsuwa ta ce. "Bappa ina kwana".
Ganin alamar kamar ta yi kuka ne yasa ya amsa da. "Lafiya lou me ya sameki kika yi kuka?".
?asa ta yi da kai ta rasa abin fa?a, sai ta fara ?an kame kame kamar wata maras gaskiya.
"Mahnoor ba dake nake yi bane? Meyafaru kika yi kuka?". Fuska a ?an ?aure ya sake tambatar tata, dan a duniya babu abin da ya tsaya da ya wuce ya ganta a cikin damuwa.
"Babu komai bappa, wani abin ne ya shiga idanu na". Ta bada amsa a tsanake.
Ya fahimci karya ta yi mashi, amma bai nuna ya gane karya take yi ba, sai ya ce mata. "Ina hammanku?".
Da hannu ta nuna hanyar fita tare da fa?in. "Yana walde".
Shiru ya ?an yi yana tunani a kan abin da ya sanyata kuka, to kenan kukan nata yana da ala?a da hammansu? Dan yaga waje guda kenan suke, daga wajensa ta fito kenan, to me ya ha?asu ya sakata kuka kuma?. Ya jefawa kansa tambaya yana mai cigaba da zancen zucin nasa.
"Bappa in tafi ne? Ina son na je na kunna wuta na yi maku ?umame kafin ku tafi kiwo".
Jin muryarta yasa ya dawo daga duniyar tunanin da ya afka, dawo da kallonsa a kanta ya yi. "Jeki ki ce Hamman naku ya zo, sannan yau ba zamu je kiwo ba".
Da mamaki ta ?ago ta kallesa. "Bappa ba zaku je kiwo ba kuma? To meyasa?".
"Saboda bikin aurenki za'ayi, ba zan je kiwo ba zamu zauna ni da Hammanki mu gyara maku ?aki, anjuma da yamma a dandali za'ayi bikin bidirin aurenki kamar yadda ake yi wa kowacce yarinya a kauyen nan, ba zamu bar al'adarmu ko guda ?aya ba, kamar dai yadda ake yi tun iyaye da kakannin, ke ma dole za'ayi maki".
Zaro idanu waje ta yi, tamkar kwayar idanunta zasu fa?i ?asa, da yake ita tasan yadda al'adun nasu suke, sai yasa ta ji kanta na juyawa, yanzu fisabilillahi yaushe zata iya aikata irin wa?an nan abubuwa da suke gudanarwa a biki da Hamman nasu, to shi ma zai iya kuwa? Shi da yake sarkin kunya, har yau ya ?asa ha?a idanu da bappa, yaushe zai iya wa?an nan abubuwa, karami daga cikinsu ne ma bata abinci a baki, wai hakan ne zai sa a yarda zai iya kula da ita, sannan ya goyata a bayansa ya hau saman wani dutse dake kusa da dandanli mai tudun gaske, sai ya kwana yana tafiya bai isa sama gaba?aya ba, kuma a haka zai ?auketa a daren ya haura sai gobe da safe zai iya saukowa, a cewarsu wai hakan ne zai tabbar masu da zai iya ?aukar nauyin ?awainiyarta, kamar yadda ya ?auketa ya juri wahalar haurawa da ita sama, ya je can ?ololuwa ya sake dawowa, to haka ?aukar ?awainiyarta ba zai yi mashi wahala ba acewarsu.
Sannan idan suka sau?o ga girki da zai yi mata, sannan zai yi mata tsantsarerren kyalliya irin nasu na al'ada da ake yi wa amarya kamar yadda ake yi, ya ?aura mata ?an'kwali ?aurin amarya, wa?an nan ka?an ne daga cikin al'adun nasu, sai dai mun ha?u a dandali kwaga sauran.
Kuna tunanin Jaish zai yarda ya yi dukka wa?an nan shirme kuwa? Wajen sati fa ake ?auka kowacce rana da abin da za'a gudanar, tab?ijam! Akwai kallo sosai wlh, wayaga Jaish da yi wa Mahnoor kwalliya, yaseen ba mai hanani sai na yi dariyata, ina ma emojin dariyar yake........????
Yo hauka ake da ba zan yi dariya ba, Prince Jaish da kansa da hura wuta ya dafawa amaryar da bai ce yana sonta ba abinci a bainar nasi! Sannan ya yi mata kwalliya, ya bata abin da ya girka ?in a baki, ga goyata su hau dutse, tun farkon dare suna tafiya har daren sai ta tsala zasu isa, kuma suna isa su sake juyowa su dawo, tab e lallai bappa baka son zaman lafiya, to ni dai ina daga gefe ina kuma kora maltina mai sanyi ina binsu da eyes, babu wanda zai hana ni shan maltina ta kuma in yi dariya ato.
Zaro idanu ta yi, tunani ta fara yi a kan lallai za'a samu matsala in kuwa haka ne. Jiki ba kwari ta nufi waje, bappa da kallo ya bita, sarai ya fahimci ta shiga damuwa na jin abin da ya fa?a, amma kuma dole ayi wa?an nan al'adu kamar yadda ake yi wa kowace ?iya, shi kansa yana fargaba yana ?ari ?arin yadda zata kasance idan har aka ce Jaish ya yi wannan abin, yana ganin kamar da wuya, amma ba shi da niyar fasawa a ransa.
Can wajen dabbobin ta iskosa yana ta ?o?arin ?auresu, yanzu gaba?aya ya canza, kamar ba Prince Jaish namu ba, har duhu soft skin ?insa ta yi, dark black arab hairnsa har ta ?an yi brown ka?an, saboda yanzu baya sanya mata mayukansa da ya saba, bata samun gyara sosai, kuma ga shi yaki yarda bappa ya datse mashi gashin nasa, ba yadda bappan bai yi ba amma yaki yarda, ya ce a bar mashi kayansa a haka yake sonta.
Cikin sanyin murya ta ce. "Hamma bappa ya ce kazo".
Shiru bai motsa ba bai kuma dai'na abin da yake yi ba, tamkar bai ji metace ba.
Ganin haka yasa ta kuma cewa. "Hamma bappa ya ce yau ba zaku fita kiwo ba, ba sai ka sha wahalar ?aure dabbobin ba, ka barsu kawai". A wannan karon cikin harshen fillanci ta yi mashi magana, izuwa yanzu yana jin yaren nasu sosai, baya magana ne da tsab zai iya mayar masu da amsar dik abin da suka bu?ata, yawan zamansa da Mahreen inuwa guda ne yasa ya iya yaren sosai, dama ita ai ko baka kaunar Allah sai ta sanya ka fara kaunarsa, yo dan dole yake sauraran hirarta, tun baya gane komai har ya fara fahimtar wace duniya ta dosa dan dolensa.
Sai a wannan lokacin ya ?ago kansa jin cewa ba zasu je kiwo ba, idanu ya zuba mata ba tare da ya yi wata alama ba. A yanzu tana fahimtar dik wata motsinsa me yake nufi, dan haka ta fahimci tambaya yake son yi a kan me zai hanasu zuwa kiwo dik da bai nuna alamar hakan ba, baiwar Allah tana da basira.
"Ni ma ban san dalilin da zai hanaku zuwa ba, kawai dai ya ce na kiraka ba zaku je ba yau". Ta bashi amsa tana yin ?asa da kai. Ba zata iya gaya mashi za'ayi bikin aurensu bane, kunya abin ya bata yasa ta yi karyan bata san dalili ba.
Aikuwa bai gamsu da maganarta ba, dan kuwa ya gano karya take yi, hakan yasa sai bai motsa daga in da yake ba.
Ta fahimci dalilin rashin motsawar tasa, wato gaskiya yake son ji kenan, lallai ma ya iya tsiya shi ma. Kara yin ?asa da kai sosai ta yi, kunya kamar zata nutse cikin ?asa ta ce. "Da gaske Hamma ni ban san dalili ba".
Still bai motsa daga in da yake ba, dan bai gamsu da zancen ba.
Ganin haka yasa ta ji a ranta ko dai ta watsa a guje ta yi cikin gida ta barshi a wajen ne? Tun da ta isar da sako ya ji da kunnensa bappa na kiransa ai dole ya je. Sai kuma ta yi tunanin idan ta yi hakan ai raini ne, bappa ya garga?esu sosai a kan rai'na na gaba da su, dan haka bai dace ta yi hakan ba, to ya zata yi? Ita dai a gaskiya ba zata iya gaya mashi shirye shiryen bikinsu ake yi ba.
Tana tsaka da tunanin mafita ne sai gani ta yi ya ?aga hannunsa yana yarfarwa kamar wanda wani abin ya kama mashi hannun ya ma?ale. A ?ari ta ?ago da kanta ha?e da kallonta a kansa.
Cigaba da yarfar da hannun nasa ya yi yana son cire kaskar jikin shanu da ta ma?ale mashi jikin fata tana son shan jininsa, cizonsa ta yi a hannun yasa ya farga da ita.
Ai data ga haka bata san lokacin da ta manta da cewa tana jin kunyarsa ba, a fujaje ta matso kusa da shi tare da ri?o hannun nasa.
Bai yi kokarin kwacewa ba, saboda dayawan lokuta yana gani idan suka kama jikin bappa ita take cire mashi ta sanyasu cikin wuta, babu kaskar dayawa a jikin dabbobin nasu, saboda bappa yana yawan duba gaba?aya jikin dabbobin, rana yake warewa a kowace karshen sati ba ya zuwa kiwo, zama yake ya hura wuta kusa da su ya yi ta cire masu kaskar yana sanyawa cikin wuta, hakan yasa basu da yawa, kun san suna yawan ma?ale jikin shanu su yi ta shan mashi jini, wanda bai sansu ba wasu irin kwari ne kanana kamar ?uda da suke ma?ale jikin dabbobi suna shan masu jini, sun iya cizo sosai fa.
Har kashe shanu suna iya yi idan suka yawaita a jikinta, suna da ha?ari gaskiya, sun iya ?arna, dole ka rin? kula da jikin dabbobinka idan ba haka ba su kamu da cuta ka rasa daga ina matsalar take, kan ka ankara idan ka yi wasa sai ka ji dabbarka ta mutu.
Zuba mata idanu ya yi yana kare mata kallo a lokacin da take cire mashi wannan kaskar, haka kawai yake jin tausayinta, tana da innocent face, fuskar ban tausayi, ga shi kullum na duniya sai ya ci karo da ita tana kuka Nenne ta yi mata wani bakin izayar, hakan tasa ko bata kuka sai ya rin?a kallon face ?inta kamar tana kuka, sai ya rin?a jin tausayinta yana ratsa shi.
A lokacin da ta kama yatsun hannun nasa tana son cire mashi kaskar sai da ta ji kirjinta ya bada dum dum, saboda yadda yatsun nasa suke dogaye kuma gasu ba sirara can ba, ?an ?ul ?ul dai haka, ga su da haske kamar madara, yau dai ta ta?a jikinsa, duk sai ta ji kamar ba jikin mutun ta ta?a ba, ga wani haske da faratunan hannun nasa suke yi, har wa yau skin ?insa is very soft.
Kerma hannunta ya fara yi wajen kama kaskar, sarai ya lura da a tsorace take, sai ya basar kamar bai ganta ba.
Da kyar ta iya kamar kaskar ta cire mashi, a can gefe ta jefar da ita, sannan ta ?an ja baya ka?an daga kusa da shi tana yi mashi sannu, dan kuwa ta cijesa a hannu, ga wajen har ya yi alamar jini.
Shi kam face ?inta yake ta kallo, cikin ransa yake jin kamar ya ta?a rayuwa da ita a wata duniyar, wato tunanin gimbiya Zunaira ce take yi mashi gizo a ?wa?walwarsa ta dalilin ganin face ?inta a kusa da shi................ Ni kuwa nace anya face ?in Mahnoor idan ta cigaba da matsowa kusa da shi ba zai sa ya dawo cikin hankalinsa ba kuwa? Kuna dai ganin a duk lokacin da ya ganta kusa da kusa sai tunanin gimbiya Zunaira ta yi mashi gizo, ya rin?a jin kamar ya ta?a yin rayuwa a wata duniya ta daban, to mu je dai zuwa, lokacin zai warware mana komai.
"Hamma in tafi ne?". Ta fa?a kallonta a ?asa, tana son ?ago idanu ta saci kallonsa dan taga me yake yi, amma ta kasa gudun kada ta tsinci yana kallonta su ha?a idanu.
Shiru shiru bai amsa mata ba, sai dai kallonta da yake ta yi yana jin ?wa?walwarsa tana wani irin juyawa tamkar agogo.
One step ta yi baya kafin ta ?an ?ago da kallonta a kansa. Ai a fujaje ta sake yin ?asa da kai ganin ita yake kallo sun kalli juna ido cikin ido. Shi dai ba komai yasa ya ?asa dai'na kallonta ba face wannan tunani da yake ji na daban idan yana kallonta, abin yana bashi mamaki da yasa baya son kawar da kallonsa daga kanta.
Ita kuma sarkin tsoro, ganin yana ta kalleta yana kalle kayansa, e mana kayansa tun da dai aure ya ?auru in ji ni princess Teema taku ta amana..........??
Yana ta kalle kayansa yasa ta tsorata, nan take kirjinta ya fara dukan uku uku, a tunaninta wani abin zai yi mata, shege shai?an da kuma munafukar zuciya mai sake sake sai ta fara saka mata cewa ai dama jama'a sun ce maki shi maye ne, ba ga shi yanzu yana kalle maki jiki yana neman ta in da zai fara cinye maki tsokar jiki idan ya samu dama ba.
Ai kuwa wani irin ihu ta zunduma wanda bata san ta yi ba, kamar mai wani motsi a kai, kawai zuciya ya kai ta zai barota, wlh yarinyar nan ta zaci a cikin zuciyarta ta kurma wannan ihu, bata san a fili ta yo shi ba.
?an zaro idanu ya yi yana mamakin ihun nata, kamar wadda aka yi wa allura ko wadda aka kwalawa guduma a kai, ta wani kware baki ta zundumota, anya ma lafiya take kuwa?. Ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa.
Ita kuwa ihun da ta yi ya yi dai'dai da ta ?ago kai ta kallesa, ai kuwa hakan ya yi dai'dai da idanun da ya zaro dan mamakin abin da ta yi.
Habawa tana ha?a ido da shi taga ya zaro nasa me zata yi? Ai sai ta zunduma a guje ta yi wani irin juyawa da karfi ta nufi hanyar gida, kafa me na ci ban baka ba? Ai sai gida.
Bata ma san lokacin da takalmar kafafunta suka cire ba, ita dai gida kawai take burin ta shiga.
Sai dai bata kai ga isa gidan ba ta fa?i ?asa tare da kurma ihu mai sautin gaske.
Yana dai tsaye yana kallon ikon god da wannan yarinya, yana gani ta watsa a guje bai yi wani motsi ba, sai da ya ga ta fa?i ?asa ta kuma zunduma wani ihun ne ya ?an lumshe idanunsa tare da jan dogon numfashi. Ni kuwa nace har yanzu dai wannan fadanci ta jinin sarautar tana nan bata rabu da shi ba.
A hankali ya fara takawa ya tinkari in da take, a gabanta ya tsugunna dan yaga me yasameta ta fa?i take yin wannan ihu kuma.