Rayuwa da gibi complete na batul mamman - Chapter 30
Rayuwa da gibi complete na batul mamman Chapter 30: Rayuwa da gibi complete na batul mamman Chapter 30. "Akwai mutumcin da ya wuce auren da aka ɗaura mata?…
4,479 words
"Akwai mutumcin da ya wuce auren da aka ɗaura mata? Kuma na nanata miki cewa ba Taj bane ya ce ta zo su tafi. Yaya Hayatu ne ya ce ta bi mijinta."
"Zancen nawa dai ya fito. Ya ce ta bi shi saboda yana ganin ya isa. Ni bana son wani ya rainaka ne." Ta faɗi da ƙanƙanuwar murya.
"Nayi zaton kin yi min sanin hagu da dama ashe ba haka bane? Wallahi kuɗi ko muƙami ba zai sa na wulaƙanta ƴata ba. An riga an ɗaura aure. Bai kamata na nuna mata bijerewa umarnin mahaifin mijinta garesu daidai bane. Ko har kin manta matsayin da muka haɗu da Taj tsakaninsa da babansa?"
Jikinta sai ya sake yin la'asar. Ta kama bakinta bayan ta bashi haƙuri. Bawan Allah dama ba riƙo gare shi ba. Nan da nan ya kashe wancan zancen ya sako maganar kai amarya tunda ya san dole za a dawo da Hamdi daga gidan Alh. Hayatu. Sai da su ka gama tsara komai ya koma ya kwanta ita kuma ta fito falo.
A firgice ta sami Zee tana kai kawo. Zee ɗin na ganinta tayi maza ta rufe ƙofar falon kada kowa ya ji.
"Yaya kada ki tada hankali idan ki ka ji me zan faɗa."
"Allah Yasa dai lafiya Zee."
"Jiya Hamdi bata dawo gidan nan ba."
Da gangan Yaya ta ce "kai haba?"
Zee ta sake kwantar da murya "Wallahi kuwa. Nayi ta kiran wayarta bata ɗauka. Sai da asuba tayi min message wai tana gidan su Ya Taj."
"Indai haka ne ai babu damuwa."
Zee kasa ɓoye mamakinta tayi. Da tsammanin faɗa ta zo sai ta samu ba haka ba. Yaya ta gama tsokanarta sannan ta taimaka tayi mata bayanin me yake faruwa. Su ka gama dariya da tunanin me za su ce da mutanen da suka kwana idan aka fara cigiyar amarya.
*** Hajiya, Umma da Mama sai da safe Inna ta sanar dasu duka abubuwan da su ka faru a gidan da daddare, har ma da baƙuwarsu. Murna a wurinsu ba a cewa komai. Dawowar Taj abin farinciki ne da shi kaɗai ya cancanci ayi ƙwarya ƙwaryar walima saboda farinciki.
"Amma banda abin Alhaji me zai sa ya taho da Hamdiyya bayan tare da mahaifinta su ke?" Umma ta faɗi bayan sun ɗan nutsu da murnar.
"Kema dai Jamila kamar baki san halin mijin naki ba. Ƙarshenta gani ya yi kamar Taj ya damu shi ne zai taho masa da ita don ya kwantar masa da hankali. Son ƴaƴa kuma a wajen mutumin nan ai ba a magana." In ji Mama.
Wata uwar guɗa su ka ji daga falo. Dama suna ɗakin Mama ne. Inna ta sallami kowa ta bar Hamdi saboda baccin da ya sake ɗauketa bayan tayi sallar asuba.
Fitowa su ka yi iyaye, ƴaƴa da jikoki. Ashe Amma ce tayi fitowar sassafe ko wanka bata yi ba. Hijabi kawai ta ɗora akan rigar baccinta ta fito. Tana ganin matan gidan, musamman Inna sai ta kama kuka.
"In da na san aure ne zai dawo da Taj gida ai da ko kwana guda ba zai yi a matsayin ɗan da uba ya kora ba. Kai, Allah mun gode maKa."
Waɗanda basu sani ba duk sun ji a lokacin. Murna da farinciki kamar me. A wajen Taj ta sami labari tun daren. Nan falon nasu su ka kira Kamal ya shigo da Taj. Sai abu ya koma kamar ranar kowa ya ƙara ganinsa tun tafiyarsa ta farko. Waɗanda basu kwana a gidan ba ma duk an kira su. Kafin bakwai sun cika gidan. Taj murmushi kawai yake yi. Yana cikin farinciki fiye da kowa. Ciwon kan ma ya tafi gabaɗaya ya tafi. Zuciyarsa kamar yau aka dasa masa ita. Babu damuwar komai a ciki. A gaban ƙafafun Amma ya zauna akan kafet tare da ƴan uwansa. Baka jin komai sai hamdala da ake yawaita yi.
"Kai ku duba min Hamdiyya ko ta tashi."
Hajiya ce tayi maganar tana mai duban ƙofar ɗakin Inna. A take mutum uku ƴan mata da wasu biyar cikin jikoki su ka miƙe a guje kowacce tana cewa ita za ta duba.
"Mijinta na zaune wa ya aike ku?" Mama tayi musu tsawa. Sai kuma ta kalli Taj "tashi kaje mana."
"Ina?" Ya tambaya don bai san kan gidan ba yanzu.
"Tana ɗakin Inna" cewar Firdaus.
Tashi ya yi kafin yana waige "wanne ne?"
Yayinda wasu ke nuna masa, masu hankali wannan tambayar fami tayi musu. Inna mai yawan kawaici sai gata ta duƙar da kai tana share hawaye. Ace ɗan halak bai san ɗakin mahaifiyarsa ba a gidan ubansa! Tabbas wannan abu akwai ciwo.
Yana ganin halin da su ka shiga ya yi saurin barin wajen domin baya son ayi ɗa kwance uwa kwance. Murnar kowa za ta koma kuka. Abin da ba zai so ba. Tafiyarsa kuwa tsokanar ƴan uwansa ta janyo masa. Aka yi ta masa dariyar shaƙiyanci. Hakan sai ya hana koke koken da iyayensu su ka fara.
* Hamdi ta fi minti goma sha biyar tana son fitowa amma tana kunyar mutan gidan. Na farko bata san lokacin da kowa ya fita ba saboda bacci.....'bacci a đakin uwar miji don abin kunya' shi ne abin da ta fara faɗawa kanta da ta farka. A saman kayanta na jiya kuma taga an ajiye sabuwar doguwar riga an cireta daga leda amma da tag. Da ta ɗaga wani irin ƙamshi ne mai daɗaɗa ruhi yake tashi a jikinta. Babu makawa turara ta aka yi. Ga wata ƙaramar ledar an saka sabon brush. Ta san ita aka ajiyewa. Banɗaki ta shiga tayi wanka a gurguje ta fito. Bata son kowa ya shigo ya ganta. Musamman Inna. Gaban dressing mirror ta zo ta tsaya ta shafa man da Innar ta nuna mata jiya. Daga nan bata sake taɓa komai ba ta saka rigarta mai kyau ta yafa ƙaramin mayafin ta fita falon ɗakin. Nan ma babu kowa shi ne ta dinga zuwa ƙofar fita tana dawowa.
Buɗe ƙofar taji anyi tayi saurin gyara zama a zatonta Inna ce. Sallamar da ya yi ce ta sake tada mata hankali. Idan wani ya shigo ya gan su a ɗakin fa? Idan Inna....
"Baki amsa min sallama ba kin tsaya kina yaba Salman Khan daga sama har ƙasa." Taj ya faɗa yana zama a kan kujerar da take.
Da sauri ta tashi tsaye tana kallon ƙofa ta ce "Ni ba kai nake kallo ba" da ƴar tsiwarta saboda ba wai ta manta abin da ya yi bane jiya.
"As if..." sai kuma ya koma kallon falon yana inhaling ƙamshinsa kafin ya miƙe tsaye "Wanne ne ɗakin baccin Inna?"
Da hannu Hamdi ta nuna masa. Yadda ya dinga tafiya ne ya taɓa mata zuciya. Ta bi bayansa har ciki. Nan kam har lumshe idanu ya dinga yi saboda yadda ƙamshin ɗakin yake nutsar masa da zuciya. Irin ƙamshin da ya dace da Innarsa. Mai sanyi, daɗi da kuma kama waje ya zauna a ran wanda ya shaƙe shi.
Juyawa tayi za ta fita ta bashi wuri sai kawai taji ya janyota ya rungume ta baya. Duƙar da kansa ya yi daidai kunnenta. Wani nau'in ƙamshin ya shaƙa mai daɗi. A ransa ya ƙudurta neman sunan mai sayarwa a wajen Inna don ba za a bar matarsa da gidansa a baya ba.
" Yau ma arziƙinki na ci aka ce na shigo ɗakin Inna kamar yadda Alhaji ya barni na shigo gidan nan domin ki. I owe yoy big time Hamdi. Thank you."
Tausayinsa taji kamar daren jiya ta ce "Na taya ka murna Happy."
"Kin dai taya mu." Ya juyo da ita suna fuskantar juna.
"A'a fa. Ni dama tun farkon zuwana Alhaji bai koreni ba."
"Sai ni uban ƴan taurin kai ko?"
"Ni dai ban faɗa ba" tayi murmushi.
"Kin ayyana a ranki na sani." Ya kama hannuwanta yana murmushi.
"Ka dai tsargu kawai saboda baka da gaskiya"
Janta ya yi wajen gadon "Zo mu ɗana gadon Inna."
"Ni kaza?" Hamdi ta ce a firgice "kada ka janyo min abin faɗa har jikoki mana."
Zillewa tayi ta fita daga ɗakin ya bita falo kafin ta fita.
Haƙuri ya bata akan maganganum Alhaji ga Abba jiya. "Abin da nayi jiya har yasa ki fushi was for you Hamdi. Na san baki ji daɗi ba amma ina so muyi clearing issue ɗin kafin anjima."
Da ya san amsar da za ta fito daga bakinta da bai tayar da wannan maganar ba. Kallonsa tayi. Kallo mai tarin ma'anoni. A wajenta kuwa da manufa ɗaya tayi shi...(na san abin da nake yi).
"Uba uba ne Ya Taj. Nagode da baka barni na yiwa Alhaji rashin kunya ba da yanzu ina nadama don ba tarbiyar gidanmu bace. Amma ina so ka sani cewa WALLAHI ba zan taɓa sakin jiki a gidanka ba sai Alhaji ya ɗauki Abbana da darajar da Allah Ya bashi."
"Me kike nufi?" Taj ya tambayeta da yaji komai nasa ya fara kwancewa.
"Aurena kayi ba sadaka aka baka ba. Allah Ya sani ba zan iya ɗauke kai ina gani ana yiwa mutum mafi girman daraja a wurina irin haka ba. Sai in ga kamar nima na yarda bai kai a girmama shi ba."
"Amma ni wane irin girma ne bana bashi?"
Abin da bata son farawa don kar ta kasa dainawa ne ya zubo. Hawaye. Hankalin Taj ya sake tashi. Ya matso ta matsa baya.
"Ba da kai nake ba. Ba kuma faɗa nake da Alhaji ba. Amma kai ma ka san irin matsayin da ya bashi daga maganarsa ta jiya. Kana gani ko zuwana nan ba shawartarsa ya yi ba duk da dai an ɗaura aure. Ko don ya taɓa yin daudanci ne?"
A lokacin ya gane Hamdi bata da labarin ainihin abin da yake tsakanin iyayensu maza. Bata san sanayyarsu ta wuce ta zaman unguwa ɗaya ba. Akwai sauran rina a kaba kenan. Amma da ta buɗe ƙofa ce ta kawo ƙarshen zancen.
Sam bata nuna musu taji maganganunsu na baya bayan nan kuma ta fahimci inda suka dosa ba. Faɗan hana Hamdin fitowa tayi masa.
"Abinci za ta ci a mayar da ita gida."
***
Wayar Alhaji ce ta tayar da Ahmad daga baccin da ya koma. Kamar yadda dalilai daban daban su ka hana yawancin mutan gidansu bacci, shi ma haka Salwa tayi sanadin wargaza nasa zaman lafiyar da ta gayyato Anti Zabba'u gidansa.
Ana kiran assalatu da ya tafi masallaci su ka tattara za su bar gidan ko tsinke basu gyara ba daga ɓarna da almubazzarancin da su ka yi da daddare. Suka taɓa ƙofa su ka ji a garƙame. Ya sanya kwaɗo ta waje da zai fita. Anti Zabba'u ta dinga ruwan ashariya tana cewa tafi ƙarfin Ahmad ya wulaƙanta ta.
"Mu gyara gidan nan kawai kafin ya dawo. Ni bana son rigima." Wata a cikin ƴan matan ta ce.
Rai a ɓace Anti Zabba'u ta ce "An faɗa miki saboda shara ya rufemu? Nuna isa ne kawai da cin mutumci irin na uwarsa."
"Duk da haka gara mu gyara. Zan fi son mu fita salin alin kafin ya fahimci halin da waccan mara kunyar take ciki."
Da wannan maganar su ka duƙufa. Gyaran dai sai a hankali amma dai yafi babu. Duk abin da su ke yi kuwa Anti Zahra tana jinsu tayi zamanta a ɗaki. Mami ma taji komai tana cike da takaicin ba za ta iya ɗaukar mataki ba.
Da ya dawo don kansa ya ce su bar aikin saboda yadda su ka tasarma damalmala gidan. Ruwan mopping wannan klin aka zuba masa kuma ba a bari ya narke ba aka matse mop ɗin sama sama aka soma yaɓawa a ƙasa.
"Ga gidanka nan za mu fita amma wallahi Ahmad bashi kaci. Wannan wulaƙancin sai kayi nadamarsa."
"Boka ne fa ki ke taƙama dashi. Ni kuma da wanda ya busawa bokayen rai na dogara. Ki ajiye makaman kawai ayi zumunci Fisabilillahi."
Ƙwafa tayi. Ranta yana tafarfasa. Mutumin da ta bawa kuɗinta kuma aiki bai ci sai ya yi nadama shi ma.
Sun zo fita Ahmad ya ce "ina Salwa?"
Kamar jira suke kuwa yana magana su ka fice gabaɗaya a gurguje. Bai tsaya tambayarsu ko lafiya ba ya shiga ɗakin ya ganta a zaune a kan kafet da kumburarriyar fuska tana kuka.
"Tunda bugun fanke kaɗai su ka yi miki ki taso ki gyara gidan nan yanzu yanzu."
"Yaya baka ganin fuskata ne?" Ta sauke mayafinta yadda zai gani da kyau.
"Allah Ya ƙara. Maza ki fito ki gyara gidan. Amma ki fara duba ko Mami tana buƙatar wani abu."
Kwanciyarsa kenan Alhaji ya kira. Dama ya tsorata saboda yayi wuri mutum ya amsa waya. Hankalinsa sai ya nemi barinsa bayan ya faɗa masa me Salwa tayi da kuma babban abin wato ciwon Kamal. Muryarsa kuma rawa take yi sosai.
"Ban faɗawa kowa ba sai kai. Ina buƙatar ka zo mu yi shawara Ahmad. Zan iya rasa Kamal a kowacce daƙiƙa."
"Kayi haƙuri. In sha Allahu zamu sami mafita. Gani nan zuwa."
"Ka taho da Salwa." RAYUWA DA GIƁI 31
BATUL MAMMAN💖
YA HAKIMU gwanin Sarkin
***
"Salwa kuma Alhaji? Wani abu tayi?"
Ahmad ya yi tambayar ne saboda a tunaninsa ciwon Kamal kaɗai ya isa ya gigita Alhaji. Me zai sa ya tuna da Salwa har ya nemi a taho da ita a lokaci mai mahimmanci irin wannan?
Gwiwa a sage ya tambaye shi "Laifi tayi ko?"
"Kai dai ka taho min da ita."
Yana bashi wannan amsar ya gane ko ma mene ne ba abin wasa bane tunda lalura mai girma kamar ciwon ƙodar Kamal bai hana shi nemanta ba. A kitchen ya same ta da himilin kwanuka kamar a gidan ake taron biki. Ko tausayi bata bashi ba don taurin kai da kafiya gami da son zuciyarta ne ya jawo mata. Abu guda ne dai. Ya sanyawa ransa sai ya bi kadin dukan da aka yi mata a cikin gidansa. Su Habitti ba a ci bulus ba. Muƙullin mota ya ɗauka ya ce da Zahra kiransa ake yi a gida game da bikin Taj ya fice.
Da ya kira Salwa su tafi ba ƙaramin rawar jiki ta dinga yi ba. Bata san ina za su je ba amma hankalinta duk ya tashi. Tayi zaton ya canja shawara ne zai kai ta tasha ta koma gida. Ta dinga bashi haƙuri da magiya. Bata san damuwarsa ta ninka duk wani abu da ya shafeta ba. Ciwon Kamal ya ɗaga masa hankali sosai.
Haƙurin da take bayarwa kamar ba shigarsa yake ba. Shi ne ta koma barazana "Yaya Ahmad kada ka ɓata kuɗinka. Ba zan tafi ba domin na tabbata Taj zai zo gareni da ƙafafunsa. Ko mun je Bauchi zan shigo wata motar na dawo."
Ko ci kanki bai ce mata ba. Bashi da wannan lokacin. Ita kuwa bata sam ta shiga one chance ba sai da ta gane hanyar ina su ke bi. Ta zaro idanu da su ka ƙanƙance cikin kumburarriyar fuskarta. Ta kama ƙofa a tsorace tana kokawar buɗewa a titi.
"Me za ka kaini ayi min? Yaya Ahmad buɗe min na fita."
A haukace take dukan gilas tana neman yi masa ɓarna. Ya juyo ransa yana suya ya daka matsa tsawar da ta gigita ta. Saboda tsorata da tayi a lokacin da za a tambayeta sunanta da wuya ta faɗa farat ɗaya.
"Salwa!!!"
Laƙwas tayi a kan kujera har su ka isa. Su ka shiga falon tare ya sami gidan a cike fam. Zuciyarsa a take ta faɗo ƙasa daga ƙirjinsa saboda mummunan tunanin da ya zo masa. Allah Ya taimake shi su na ganinsa aka soma bashi labarin abin farincikin da aka wayi gari dashi a gidan. Idanunsa su ka sauka akan Kamal zaune a tsakiya. Wata irin ajiyar zuciya yayi mai ƙarfi sannan ya sami damar sakin ransa ya shiga cikinsu. Ko gaisawa basu gama yi ba Alhaji ya buɗe ƙofar ɓangarensa ya kira shi.
"Ahmad kai fa nake jira."
Da saurinsa ya tashi har yana tuntuɓe. Kamal ya sha jinin jikinsa. Ƴar hira da dauriyar da yake yi ya kasa jurewa. Ɗakinsa zai koma kawai kafin Alhaji ya neme shi. A hanyar fita ya yi kiciɓus da Salwa. Da yake bashi da masaniyar me yake faruwa sai bai canja mata ba.
"Salwa? Ashe tare kuke ki ka tsaya a nan?" Ya kalli fuskarta "me ya same ki haka a fuska?"
Yuuuu idanu su ka dawo kanta. Jiki a mace kamar magen da aka tsamo daga lamba two ta ƙarasa ciki tana raɓe raɓe. Ƴaƴan gidan dai babu sauyin fuska amma iyayensu ko kallonta basu yi.
"Zamewa nayi."
"Allah Ya sauwake" ya ce ya fita.
Ita kuma ta ƙaraso aka gama yi mata sannu sannan ta matsa gaishe da su Inna.
"Hajiya ina kwana?" Ta durƙusa a gabanta.
"Lafiya" ita ce taƙaitaciyar amsar da ta samu ba tare da sakin fuska ba.
A ranta tayi tsaki. Ai dai ba ita ce ta haifi Taj ba take wani sha mata kunu. Ko ita Innar bata fi ƙarfin a kai sunanta gaban malam ya ƙulle mata baki ba. Nan gaba ma wajen malamin Ummi za ta je domin da alama zai fi na Mami iya aiki. Muskutawa tayi ta ƙara matsowa ciki.
"Mama..."
Mama bata jira ta gama gaisuwar ba ta tashi abinta tana duban Amma.
"Uhmmm, Jamila duba ki ga me Taj da Hamdiyya suke yi a ɗakin nan har yanzu shiru."
Jin furucinta yasa gaban Salwa ya faɗi, ya sake faɗuwa. Baki ya kama rawa kamar mazari ya ji kiɗa. Dama ga fuska a kumbure. Sai tayi wani irin yanayi mara kyau duk suna gani.
Umma tayi dariya "kema dai Mama da rigima kike. Ba kya ko tsoron me za a buɗe a tarar? Sabon aure basa son sa ido fa. In ba haka ba kuwa sai aji kunya."
Inna tashi tayi zumbur ta bar musu wajen. Su ka dinga dariya banda Amma da bata gane manufarsu ba.
"Takwara me ki ka mayar min da ɗa ne? Ki ka sani ko bacci ya samu tana yi?"
"Sai ya zauna korar mata sauro ko?" In ji Hajiya.
Umma da Mama sai shewa harda tafawa. Ƴaƴan na gani amma su ma basu san me ake yi ba.
Ita dai Amma tashi tayi ta barsu suna kallon suman zaunen Salwa a fakaice. Ta zubawa ƙofar ɗakin Inna da Amma ta nufa ido tana jiran ganin da gaske Hamdi za ta fito daga ciki ko yaya? In tana ciki me ya kawota gidan da sassafe? Ko dai ita ma murnar ta zo taya shi? Ai kuwa da an kira iyayenta marasa kamun kai. Me zai hana su jira ido na ganin ido? Don baƙin naci an biyo shi har gida a lokaci irin wannan da yake buƙatar ahalinsa.
*
Duk da ba komai Amma ta ji ba amma iya maganganun da su ka shiga kunnuwanta sun fahimtar da ita me yake faruwa. Akwai wani abu da Alhaji ya yiwa mahaifin Hamdi. Jikinta kuwa ya yi sanyi sai dai wayewa da sanin yau da gobe yasa ta je musu da fuskar rashin sani. Bayan ta gama ɗorawa Taj laifin hana Hamdi zuwa cin abinci, sai ta shiga ta riƙo hannunta.
"Sai da na shigo nake jin ashe jiya rigimar babanku ta haɗa dake." Hamdi ta sunkuyar da kai kawai tana murmushi "Zo ki ci abinci in kai ki gida in kuma bada haƙuri kada ace ba za a bamu ke anjima ba."
Sake yin ƙasa Hamdi tayi da kanta cike da kunya. Balle da Taj ya ce shi zai kai ta.
Ya ce da Amma "Akwai maganar da za mu yi da ita."
"Fita idona Taj." Ta harare shi.
"Please mana Ammata."
"Don ƙaniyarka ka san irin bikin da ake ta yiwa Hamdi a falo?"
"Ni kuma?" Hamdi ta fito da idanu.
Amma kuwa sai dariya ta sami damar tsokanarta domin a yanayin fuskokinsu ba za ta so su fita ba. Gidan akwai manya da masu experience da yawa. Yanzun nan za a harbo jirginsu a gane da matsala.
"Harda masu cewa ko a biyo ku da abincin nan idan ya so sai muje mu karɓo miki kayanki a gida."
"Ya Rabbi, to ya zan yi? Ko kada na fita?"
Kai da ganin idanunta da jin muryarta ka san hankalinta ya nausa da nisa. Kunya, tsoro da jin nauyi sun cika mata ciki. Da Taj ya dubeta sai da yaji kamar ya kamota a gaban Amma ya ɓoyeta cikin jikinsa. She looked so cute and innocent kamar ba bakinta bane ya gama zaro masa zantuka ɗazu.
"Wasa take yi miki. Ko Amma?" Ya rage murya shi ma ɗin ba son jin wata magana babba yake yi a bakin ƴan gidan nasu ba.
Dariya Amma tayi musu. Tana yi musu fatan alkhairi a zamansu. Sun dace sosai da juna. Sweet young Hamdiyya and Charming Happy Taj. Za ta cigaba da sanya musu ido a fakaice ta gani ko za su shirya ba tare da tsoma bakin manya ba tunda ta kula basa so a sani. Idan basu daidaita ba sai ta shiga tsakani kafin ƙaramar magana ta zama babba.
Hamdi ce ƙarshen fitowa daga ɗakin bayan Amma da Taj. Salwa ta kasa ɓoye baƙinciki da kishinta a fili. Wata irin zabura ma tayi daga zaune. Numfashinta ya nemi yankewa. A zatonta turaren jiya sake janyo ɓaraka zai yi tsakaninsu. Me Hamdi take a gidan?
Wata zuciyar ta kwaɓeta da sauri. Ko dai har an sami matsalar? Maybe shi ne aka turo su gida sulhu. Munafukar dariya tayi a zuci. Ta miƙe tsaye domin ta nunawa kowa matsayinta a wajen Taj. Kashe murya tayi tana kwarkwasa.
"Ya Taj"
Ai fa ta zo gidan yawa. Idanu sun fi goma a kanta. Hamdi wani malolon abu taji ya mata karan tsaye a wuya. Faɗi take tana nanatawa In sha Allahu ba za ta sake kiransa da Ya Taj ba. Sunan ko daɗi babu ashe, bata sani ba sai yau.
Taj kuwa Hamdi kawai ya kalla tayi kamar bata jinsu. Murmushi ma take yi abinta da ƴan uwansa suke ta nuna mamakinsu akan kwanan da tayi basu sani ba. Aka dinga yiwa ƴan kwanan ɗakin Inna surutu. Su ka ce ita ta sanya su yin shiru saboda kada su tashi Hamdin da hayaniyarsu. Shi da ya san akan tsini yake ba zai yi kuskuren sake ɓata mata rai ba. Kawar da kansa ya yi kamar bai ji ba. Yana gudun me zai faru idan ya amsa. Ta sake shaƙa har wuya. Abinci ƴan uwansa su ka kawo wa Hamsi shi ne ya samu ya fita wajen Kamal.
Amma ta karanci duk motsinsu. Me yake faruwa ne wanda bata sani ba? Zama bai ganta ba. Ɗakin Mama ta shige inda Inna ta shiga ta zauna jin abubuwan da bata san da su ba. Mamaki mabayyani ta nuna akan wannan sabon al'amari.
"Ashe yarinyar nan bata da wayo ban sani ba? Ana soyayya dole ne?"
"Gabaɗaya ta ɓata rawarta da tsalle. Halin da uwarta ta so nuna mana a gidan nan shi ne ita ma take son gwadawa."
Umma kallon Mama tayi da mamaki "kada ki ce min asiri ne ya koreta, don na tabbata ko ita ce autar mata akan ƴan biye biye tsaf Alhaji zai nuna mata ƙofar gida."
Hajiya ta murmusa "ai har yau bai san mun san ainihin me ya dinga faruwa ba. Bayan wani asirin ma a gabanmu take yi kawai don ta san ta ɗaure mana baki. Ai ke dai anyi abu fa a gidan nan. Allah kada Ya maimaita mana kawai."
"Amin. Don dai kam ko Taj ya rasa mace in sha Allahu babu shi babu wannan yarinyar." Cewar Mama.
Hirar shekarun baya su ka koma yi. Inna ta sake kaɗuwa da jin wace ce Mami. Ashe zama bai ganta ba kuwa. Dole ta dage ta nesanta Taj da Hamdi daga Salwa.
*
"Yaya haka Ahmad? Ni da na kira ka mu san abin yi sai ka kama kuka?"
Ahmad bai san cewa duk bayanin da yaji a waya bai kama ƙafar wanda ya ji yanzu ba. Ƙodar duka biyu Kamal ya rasa kuma wai cikin su ashirin da bakwai babu wanda tasa za ta yi. Idan babu mai taimakon Kamal a cikinsu daidai yake da babu Kamal ɗin.
"Alhaji bayaninka fa yana nufin duk yawanmu ba za mu amfane shi ba tunda babu jinin wanda ya dace dashi."
"Haka su ka yi min bayani da likitan."
"Anya ba ya faɗa bane kawai saboda baya son takura kowa?" Ahmad ya yi tambayar da basu san amsarta ba.
Alhaji sai ya shiga tunani. Tabbas kowa a gidansa ya yi fice akan wata halayya. Indai ana batun sadaukarwa to Kamaluddin ɗinsa shi ne na farko. Wuyarta ka nema zai baka ko shi ne abu na ƙarshe a tare dashi. Ba abin mamaki bane in ya zamo yaƙi yarda a cire ƙodar kowa a dasa masa.
Wannan tunanin kaɗai ya haskaka zuciyar Alhaji. Zai nemi Kubra ta haɗa shi da likitan da ya dace a Aminu Kano Teaching Hospital. All hope is not yet lost.
Sun tattauna yadda za su yi idan aka yi rashin sa'a da gaske babu wanda jinin nasa ya yi daidai. Alhaji ya sanyawa ransa daga yau zuwa sati in ba a dace ba za su bar ƙasar. Ɗan lokacin ma ya bari ne saboda su sami damar yin booking ɗin asibitoci a ƙasashen waje. Duk wanda aka sami appointment da wuri, shi za su je. Baya son su fara tafiya a can ma ace ƙodar ake buƙata dole kuma babu mai bayarwa.
Da su ka gama ne Ahmad ya ce "maganar Salwa..."
"Yauwa..." ya tashi "mu je ƙasan. Wani rami nake son toshewa kafin ya zama ƙofa."
Gaban Ahmad faɗuwa ya yi "Alhaji ka sami labarin tana son Taj ne? Nayi mata faɗa. Ko a hanyarmu..."
"Bana fatan abin da zai sa na ci zarafin jininka Ahmad. Amma tabbas idan Salwa ta cigaba a turbar da ta ɗauka to lallai za ta fuskanci fushina."
Hankalinsa ƙara tashi ya yi. Me kuma tayi?
Bai sami amsarsa ba sai da su ka shiga mota ya matsa mata da tambaya saboda abin da Alhajin ya yi ya bawa kowa mamaki. Hamdi ya nema suna saukowa. Amma ta ce masa ya yi sa'a kuwa domin yanzun nan suke shirin fita ita da Hajiya da Na'ima wadda ke bin Hajiyayye za su kai ta gida.
"Da kun koma kun ɗaukota kuwa" cewar Alhaji yana shafa kan ƙananun jikokinsa "ni na kawota. Idan ba a jira na mayar da ita ba sai a nemi izini na kafin a kaita gida."
"Mun kusa yin laifi ashe. To Allah Ya bada haƙuri" in ji Umma.
Gabansa Amma ta kawo Hamdi. Ta durƙusa ta gaishe shi kai a sunkuye. Yadda ya amsa mata da sakin fuska har Inna sai da ta jinjina lamarin.
"Ni dai ba zan bar magana a cikina ba." Amma tayi maganar da ta janyo hankalin kowa gareta "da mun san aurenki ne zai dawo da Taj gidan nan Hamdiyya ai da ranar da ya fita zai dawo. Sannunki Hamdiyya tauraruwar Tajuddin."