Rayuwa da gibi complete na batul mamman - Chapter 31
Rayuwa da gibi complete na batul mamman Chapter 31: Rayuwa da gibi complete na batul mamman Chapter 31. Dariya aka kama yi. Ita kuwa ta cigaba da cewa…
4,463 words
Dariya aka kama yi. Ita kuwa ta cigaba da cewa "Allah kuwa da gaske nake. Ji fa irin fara'ar da kake yi mata Yaya Hayatu. Irin ka yi na'am ɗinnan da auren hands down."
Hararar ƙanwar tasa ya yi ya ce "A'a hands up."
Yaran kuwa me zasu yi banda dariya. Da kowa ya nutsu ne Alhaji ya ce ina Salwa. Tana daga gefe ta kawo wuya da abubuwan da ake yi a falon. Tasowa tayi kamar ƙwai ya fashe mata a ciki. Tayi zaton magana zai yi mata a gabansu sai ya ƙara gaba ta bishi. Kowa na gani amma ba a san me yake cewa ba.
"Kin ga matar Taj ko?"
Shiru tayi da farko. Ya nanata tambayar da wata irin murya mai cikar kwarjini.
"Kin ga Hamdiyya matar Taj ko?"
"Eh" ta gyaɗa kai da sauri.
"Kin kuma fahimci me yasa na nuna miki ita ko?"
Nan ma eh ta ce ba tare da jiran ya kuma tambaya ba.
"To kada na ji, kada na gani Salwa." Ya juya mata baya "ki je Ahmad ya mayar dake gida."
*
"Yarinyar nan ya nuna min" ita ce amsar Salwa ga Ahmad da ya kusan kai mata duka akan ƙin amsa masa tambayar me Alhaji ya ce mata da farko.
"Wace yarinya?"
Ciki-ciki ta ce "matar Ya Taj."
"You are the least of my problems Salwa so ko ki buɗe baki ki bani amsa ko ki riƙe abinki duk ke ta shafa." Ahmad ya faɗi da faɗa-faɗa.
Yadda su ka yi ta faɗa masa. Ya kalleta yana mai taɓe baki.
"Kina gab da yin nadama mara amfani idan baki dawo daga rakiyar zuciya ba. Duk wanda ya bari tasa ta mulki tunaninsa da wuya yake cin riba. Dubi yadda gabaɗaya ki ka sauya akan wannan obsession ɗin naki. Kin zubar da mutumcinki ana ta takawa a banza."
Ci kanka bata ce masa ba. Yana magana ma Ummi take turawa text tana neman inda za su haɗu yau. Ta riga tayi nisa bata jin kira. Burinta kawai Taj ya so ta ko iyayensa basa so kuwa sai sun yi aure.
***
GIDAN TAJ DA HAMDI
(Sponsored by annurifoods, nafsbedding and meensincense)
Jeren gidan amarya ba mai yawa bane ta ɓangaren gidan Abba Habibu. Inna tayi rawar gani da nunawa fiye da tunaninsu. Ta cika gidan da komai na buƙatar amarya da ango. Sai dai kuma duk da haka Abba da Yaya basu fasa yin nasu ba. Makusantansu ma sun nuna bajinta ba kaɗan ba. Kayan zaƙi na gara irinsu dubulan, alkaki, nakiya, gireba, bakilawa da cincin Ƴar Ficika da muƙarrabansa ne su ka yi. Abin ka da tsofaffin takari, nasu ya sha bamban sosai da wanda aka saba.
Iyaa kuwa gidan ƙanwarta taje a hotoro aka rakata wajen wata ƙwararriya a harkar kayan kaɗi da abubuwan abincin gargajiya. Samira Muhammad kenan, mai Annurfoods. Mace mai faram faram da iya mu'amala. Tun abin da ya haɗa Ummi da Hamdi a makaranta Iyaa take neman hanyoyin daɗa wanke iyalinta duk da su Yaya basu canja musu fuska ba. Bayan gudunmawar kuɗi da su ka bayar shi ne ta haɗo wannan. Da ta kawo kayan Yaya kasa rufe baki tayi. Wanda ta haɗawa amarya dole ta ajiye domin babu yadda za a kai Hamdi ba tare da kayan annurfoods ba. Garin kuka da kuɓewa masu kyau a madaidaitan bokiti. Sai daddawa wadda ana haɗa kayan Anti Labiba ta ce ita dai ayi haƙuri sai ta ɗiba saboda daɗin ƙamshinta. Babu warin nan mai hawa kai mutum ya rasa inda zai yi da ransa. Sai nau'in yaji daban daban. Jan yaji mai tafarnuwa da wanda babu, na daddawa da kuma na ƙuliƙuli. Niƙaƙƙiya da kuma markaɗaɗɗiyar gyaɗa (gari da paste), garin ɗanwake, garin kunu wanda yaji duka kayan haɗi da kuma soyayyen man shanu mai daɗin ƙamshi. (Samira Muhammad 08039183880, instagram @annurfoods.ng)
"Altine wannan kaya basu yi yawa ba?" Faɗin Yaya tana jin kamar tayi kuka saboda karamcin da ake ta nuna musu.
"Ina abin yake Jinjin?"
"Haba dai, wannan yafi ƙarfin a bi shi da kalmar ina abin yake. Ke dai Allah Ya biyaki da mafificin alkhairi."
Iyaa ta ce "amin Ya Allah."
Sajida aka damƙawa kayan a hannunta da umarnin idan sun je gidan tunda da wuri za su fita kafin a kai amarya ta saka komai a inda ya dace.
Ana haka su Amma su ka yi sallama. Allah Yasa sauran safiya ce. Babu baƙin fuska a gidan. Aka sauke su a falo. Hajiya ta fara da bawa Yaya haƙurin tafiya da Hamdi da Alhaji ya yi. Don ta rufa masa asiri ma ta ƙara da cewa yayi haka ne kawai don ya kula suna cikin damuwar ciwon Taj.
Yaya tayi murmushi. Gashi dai an shigo gidan amma hannun Hamdi yana cikin na Amma a gefen Hajiya tayi mata riƙo na ƴar da ake ji da ita.
"Wallahi babu komai. Da nan da can duk ɗaya ne."
"Kin sami labarin Alhaji ya yiwa Taj izinin komawa gida?" Amma ta yi tambayar saboda ita fa a yanzu wannan yafi bikin ma a wajenta.
"Ƙwarai kuwa..." sannan Yaya ta taya su murna.
Cikin mutumci aka gama komai. Za su fita Amma da bata iya shiru ta ce da Yaya don Allah wane irin turare ne aka saka a ɗakin yake fitar da ƙamshin da su ke ji tun shigowarsu? Hajiya girgiza kai ta kama tana murmushi. Amma bata iya baƙunta ba. Sai dai idan bata ga fuska ba. Ta gode mata dai saboda ita ɗin ma surukuta ce ta hanata tambaya tun shigowarsu. Daɗin ƙamshin ba daga nan ba. Bayan kujera Yaya ta nuna musu. Inda aka ajiye turarukan wuta a cikin bokitai an rurrufe bakunansu da salatif.
"Ko kunnawa ba'ayi ba. Na gidan ƴarku ne."
Tashi Hamdi tayi ta bar falon. Yaya ta ƙwalawa Zee kira. Tana shigowa ta ce ta ɗauko a buɗe musu su gani.
"Haba Maman Hamdi? Don Allah kada a buɗe. Ƙamshin ne ya yi min daɗi na kasa barwa cikina" Amma ta faɗi da sauri.
"Ni dai ban ga komai a ciki ba. Nan kuke ta cewa an zama ɗaya" cewar Yaya tana kama guda ɗaya "in sun je gidan yanzu ma buɗewa zasu yi su zuzzuba a rufe sauran."
Da ƙyar su Hajiya su ka hanata buɗe musu. Bayan tafiyarsu ta sanya a ranta lallai za ta sayi wani ta aika musu. Zuciyarta kuwa fari ƙal don daɗi. Duk da ana ta yaba ƙamshin a gidan tayi zaton na ganin ido ne kawai. Sai yanzu da waɗanda basu san dashi ba su ka yi magana ta kuma gaskatawa.
Matar Halliru maƙobcinsu Hairat ce ta dinga zuzuta kyau da ingancin turarukan wata ƴar garinsu Bauchi. Da farko Yaya har cewa tayi duk turarukan Kano ace sai ta nemi na wani gari? Matar Halliru taƙi haƙura domin ta san me za su rasa idan ba a saya ba kamar na lokacin bikin Sajida. Na wajenta da basu da yawa ta kawo. Zee ta kunna da yamma. Sai da kowa ya fito tsakar gida ranar. Washe gari Yaya ta karɓi numbar Amina (08036387204, instagram @meens_incense). Ta kira su ka yi ciniki akan farashin da idan ka karɓi turaren ma sai ka ce sadaka kawai aka baka.
Da turarukan su ka iso kasa rufe baki tayi don murna. Ta dai ɓoyesu kafin Hamdi ta dawo gida ranar saboda ko za ayi mata faɗa sai ta kunna. Soyayyarta da ƙamshi ta daban ce. Ga dai turaruka kala kala, kwalaccam ɗinta kuwa abar duƙan ƙirji ce (I mean it, the scent simply calms the heart), sai kuma humra irin wađanda sai hancin da yaci karo dasu ne kawai zai gane.
Haka aka tattara komai aka zuba a mota domin kammala gyare gyare kafin zuwan amarya.
***
Banɗaki Ummi ta shiga da waya ta turawa Alh. Usaini saƙo cewa jiya ma Salwa ta sake shafawa Taj turaren nan. Kuma da alama anyi nasara domin ta sami labari a daren aka kai shi asibiti. Daga maganar da taji Baba Maje da Iyaa suna yi bayan wayarsa da Abba Habibu da safen ta fahimci ba rashin lafiya bace kawai ta kama shi. Salwa kuma ta tabbatar mata a text. Ita Iyaa da wuri ta tafi gidan bikin. Ta barsu in sun gama girki da gyaran gida sai su biyota kafin dai a fita da amarya. Yana karantawa ya kirata.
Da ta ɗauka tsoro ya bata da taji ya fashe da wata irin dariya mara daɗin ji.
Da jindaɗi ya ce "Ƙarshen wannan ɗan daudun ya zo."
"A'a fa, ba ɗan daudu bane" Ummi taji ba za ta iya shiru ba. Ko makaho ya shafa Taj ba zai kira shi ɗan daudu ba, balle mai ido. Idon ma irin nata mai son abu mai kyau.
"Ummi kenan. Wai me ya hanaki cewa ayi aikin da za ki sami soyayyarsa maimakon wannan sakaryar Salwan?"
"Bana ra'ayin namijin da kowa ke rububi." Tana ji Alh. Usaini ya yi dariyar rashin yarda.
Tunanin Taj ya so ta bai zo kanta ba saboda tayi nata binciken akan waye shi. Labarin mahaifinsa kaɗai ya isheta dalilin mayar da kwaɗayinta. Sannan ta san cewa ko ana muzuru ana shaho a yadda Baba Maje yake ganin darajar Abban Hamdi, da wuya ta gaske a barta ta aure shi. Ita kuwa abin da take ji a kansa ba na irin mu'amalarta da banzayen samarinta bane. Ya girmi hakan. Shi yasa kawai taga babu mafita sama da rusa shi. Ita da Hamdi kowa zero. Mafi munin hassada kenan.
"Ki tabbatar kin je kai amarya kuma kin bibiyi me suke ciki na ƴan kwanakin nan. Kin san na faɗa miki aikinsa a hankali yake ci."
"Bana son yin abin da zai sa a zargeni. Ba wani shiri muke da Hamdi ba kuma kowa ya sani."
"Sai ki san yadda za ki yi." Ya ɗaga mata murya kamar wata ƴarsa.
Bai san bashi da wani kwarjini a idonta ba. Yana shiru ta ce "Ban gane ba? Wannan abu fa duk kai ne da riba. Idan ka damu ka sa malamin da ya yi maka aiki akan Taj ɗin ya tura aljanu su binciko maka mana. Mtseww"
Wayarta ta kashe ta sake buga tsaki. "Aikin banza. Ni za ka ɗagawa mur..."
Haɗiye maganar tayi cikin tashin hankali saboda haɗa ido da tayi da Siyama. Ita kuma cikin sauri da ta karanci fuskar Ummin sai ta kama ɗaɗɗaga ƙafa.
"Fitsari, fito don Allah."
Fitowar Ummi tayi tana wasiwasin Siyama taji wayar da tayi ko kuwa.
Gaba na faɗuwa Siyama ta dakata a bakin ƙofa ta nemi mafita don kaɗan daga aikin Ummi tayi mata wani abu idan ta san ta ji. "Naji kina ta gunaguni da tsaki, ba dai flushing ki ka yi yaƙi tafiya ba? Kada na shiga nayi gamo."
Ba kunya Ummi ta saki fuska harda ƴar dariya "shiga ki ganewa kanki" ta turata ciki. Siyama na nuna kamar bata son shiga ta bari Ummin tafi ƙarfinta. Fitsarin da ya kawota da gaske ta daina ji. Tabbas akwai manaƙisar da Ummi take shiryawa Hamdi da Taj tunda taji sunayensu. Hankalinta ya tashi. Har su ka tafi gidan bikin tana faman satar kallon Ummi.
Da zuwansu babu daɗewa ta nemi keɓewa da Iyaa. Ummi kamar an tsikareta ta tashi tayi musu laɓe. Da taimakon Allah ta sami basirar lauya zancen. Wata maganar daban ta ɗauko har Iyaa za ta fara yi mata faɗan me yasa ta janyota akan shirme, sai ta ƙifta mata ido. Ganin haka sai ta kalli bakin Siyama da ta faɗi sunan Ummi iya leɓe. Wannan yasa ta fahimta.
"Iyaa za ki barni zuwa kai amarya har ango yazo? Ni fa ban taɓa zuwa ba."
"To naji sai ki biyo yayanku don na san zai je ko don ɗauko Zee."
Murna ta kama yi harda rungume Iyaa. Da wannan ta samu Ummi ta daina saka mata ido har ta sami damar sanar da Iyaa wayar da taji.
"Ban ji ance komai ba amma ko da wani abu zai biyo baya to da hannunta wallahi."
Sallamarta Iyaa tayi ta jingina da bango domin gabaɗaya jikinta ya mutu. Nauyi taji jikin yayi mata ta sulale a wajen kawai ta zauna. Babu abin da take yi sai kiran sunan Allah da neman agajinSa. Haƙiƙa kowane ɗa da halinsa yake zuwa. Tarbiya bakin gwargwado sun bawa ƴaƴansu. Amma tun ƙananun shekaru tanƙwara Ummi ke wahalar dasu. Bata da bakin ɗorawa ƙawaye alhakin ɓata mata ƴa domin kuwa duk inda Ummi ta zauna ita ke shugabantar waɗanda take mu'amala dasu. Ita ce boss mai sawa da hanawa. Ko dai kawo ƙara da wasu iyayen ke buri da alfaharin gara a kawo musu ƙarar ƴaƴansu akan su kai na wasu da tayi ke bibiyarta? Duk inda Ummi ta zauna sai tayi faɗa kuma ana bincike ita ce mara gaskiya. Kuskurenta a lokacin da suke cikin yaran yarbawa a tsakiyar Agege shi ne na jindaɗi da Ummi bata taɓuwa. Babu mai yi mata kwarjini ko ya bata tsoro. Kana cewa kule take ce maka asss. Wata maƙociyarta bahaushiya a lokacin ta kan ce
"Iyaan Baballe ki daina murna. Duk da cewa ba ma son a zalinci yaranmu to amma fa idan sun fita ya dace ki dinga addu'ar kada su taɓa ɗan kowa. Babban abin alfaharin rayuwa shi ne kayi dace kai ko wani naka bai zama silar ƙunci ko zubar hawaye ko jinin wani ba. Sannan kaima kada ɗan kowa ya yiwa naka. Ko babu komai akwai baki da ido kuma su ɗin gaskiya ne. Allah Ya kyauta."
Amsarta a lokacin ita ce tunda suna zaune a waje irin wannan ba za ta so yaranta su zama lusarai ba. Wannan mata kuwa ta nuna mata cewa duk runtsi ai gara idan an je gaban Allah ka zama mai kai ƙara da a kai ƙararka. Za ta koyawa yaranta su ƙwaci kansu amma kada su zama silar rigima kuma banda zalunci da wuce gona da iri. Manzon Tsira SAW cewa yayi kada mu cutar kuma kada mu bari a cucemu.
Hawaye ya zubowa Iyaa. Ta ɗauki laifin ta ɗorawa kanta. Cin zalin da Ummin da dinga yiwa Siyama ne yasa ta canja tsarin tarbiyar lokacin. To amma ɗan wannan guntun sakacin da kuma halayyar fiɗrar da aka haifeta sun riga sun yi tasiri.
"Allah na tuba. Allah Ka duba min."
Wata walwala da jindaɗinta duk sai su ka kau a lokacin. Ciwon kai ta ɗorawa laifin hakan da Yaya ta tambayeta game da sauyin da ta gani a tare da ita.
* "Kai Happiness me ya same ka haka ka kumbura?"
A madadin sallama abin da Taj ya fara cewa kenan da ya shiga ɗakin Kamal.
Son faɗawa Happy gaskiya yayi sai dai kuma a ganinsa faɗa a yau ba ƙaramin rashin adalci bane. Babu yadda za ayi Taj ya san gaskiya kuma ya tare a gidansa a yau. In ya yi haka kuwa ya cutar da Hamdi.
"Wai ashe kifi ne jikina baya so yanzu ni ban sani ba? Jiya da ka kula tun a wajen dinner bani da kuzari. Kifi na ci last kafin mu tafi."
"Subhanallahi. Kuma Alhamdulillah tunda an gano. We'll just avoid it don a zauna lafiya."
"We? Kai kuma me zai sa ka daina ci?" Kamal ya tambaye shi.
"Ai ka sanni da kirki. Ba zan so na dinga ci a gabanka ba."
Da dabara Kamal ya sauya zancen da dai yaga Taj ya yarda.
"Wai ni ya na ganka haka kamar ba wanda ya kwana gida ɗaya da Hamdi ba?"
"Akwai ƙura fa Happiness. Alhaji ya ɓallo min ruwa jiya." Ya faɗa masa abin da ya faru.
"Tabɗijam ake cewa ko cabɗijan...yanzu kana nufin ni da kai yau duk pillow za mu runguma?"
Bugu Taj ya kai masa ya goce "ta Allah ba taka ba. In sha Allahu gadona da naka yau sai an sami bambanci."
"Salman Khan na Hamdiyya wato ana yi maka kallon salihi ashe ashe ba haka bane." Kamal ya faɗi yana yi masa dariya.
"Aure dai nayi...idan mutum yaji haushi wata asabar ɗin mu kai shi ɗakin doctor"
"Maimakon ka zo mu zanta yadda za ayi a shawo kanta tun kafin ƴan kai amarya su watse ka zauna tsokana."
"On a serious note kana ganin abin da take so zai samu yanzu? Alhaji fa take so ya canja yadda yake yiwa Abba. Bata san na fita son hakan ba ta ɗauki fushi dani."
Shawarwari Kamal ya soma bashi sai dai a yau ko kusa zancen ba shigarsa yake ba. Ya riga ya san da me zai kama Hamdi a hannu. Damuwarsa yanzu canjin da ya gani tattare da Kamal mai yawa tsakanin jiya da yau. Happiness is hiding something. Yana ji har cikin ɓargonsa. Ko maganganun da suke yanzu yana hango pain ɗin da ɗan uwansa yake ƙoƙarin ɓoye masa. Dole zai yi wani abu a kai. Kamal bai fi shi wayo ba.
* Wannan asabar ta kafa tarihi mai girma a gidan Alh. Hayatu. Yinin bikin Taj da aka shirya yi a gidan wan Inna sai ya dawo gidan mahaifinsa. Ƴan uwa na kurkusa da su ka san me ya wakana tsakanin uba da ɗa sun taho harda maza irinsu dattijon arziƙi Yaya Babba su ka yi fatan alkhairi su ka tafi tare da Alhaji. Aka dinga kiran ƴan biki cewa venue ya canja last minute. Ƴaƴa, surukai da jokokin Marigayi Alh. Sule Maitakalmi sun gwangwaje cikin farinciki. Inna da ƴan uwanta su Hajiya anko su ka yi da Amma uwar goyon Taj. Ango ya fito tsakiyar dangi babu shayi ko tararrabi gwanin ban sha'awa.
Wai aka ce taɓa kiɗi taɓa karatu. Da yake a gida suke matashin ɗan Yaya Kubra ne yayi musu DJ. Ba kunya ita da kanta ta ce masa ya kunna musu waƙar da ta faɗa masa tun a gida. Ta sanya autar Alhaji Surayya tayi coordinating komai. Layi aka yi a jere tun daga Yaya Hajiyayye har ita Surayyan. Dukkaninsu sanye da anko iri ɗaya na shadda light brown. Ɗinkin mata irin ɗaya, haka ma na mazan. Daga kan Yaya Hajiyayye kuma ta jere Inna, Umma, Mama da Hajiya a gefe da gefen juna.
DJ ya saki waƙa su ka dinga bi. Hurry hurry come carry your baby go Come and see my mother ahh....
Kowa sai ya bar abin da yake yi ana kallon zugar gidan Alh. Hayatu. Babu wanda bai yi rawa ba idan an zo kansa, har Ahmad da tun safe yake cikin ƙunci. Sai yanzu da yaga Kamal yana walwala har yafi Taj rawar ma ya sake. Bayan sun gama matsawa su suka koma gefe suna nuna uwayensu ana ta dariya.
Wani abin burgewa shi ne da Taj ya taka har gaban Amma yana nunata da hannuwansa biyu yana faɗin come and see my mother. Bata san lokacin da ƙwala ta zubo mata ba. Ya rungumeta a wurin yana ɗan dukan bayanta.
A wurin kowa har angon wannan wunin is the best event. Kowa yaji daɗi. Ana la'asar Mama ta ce ayi haramar ɗauko amarya a kaita gidanta.
*
Ƙarfe biyar da rabi motocin kai amarya su ka cika layin gidan Abba Habibu. Motoci na alfarma da kece raini. Taj bashi da wasu abokai na a zo a gani sai cikin ƴan uwansa. Su ne kuma su ka cika wurin ƙwai da kwarkwata. Kowa ya zo ɗaukar amaryar Taj.
Su ma biki suka yi sosai. Gidan Abba Habibu babu masaka tsinke. Abinci da abin sha sai mutum ya ture.
Ƙarfe uku aka shige ciki da amarya. Kayan gyaran jikin da Amina Meens_insense take yi Hairat matar Halliru ta saya domin yau. Ba don nisa ba da ita da kanta za ta sake yiwa Hamdi gyaran nan kafin a kaita. Sake scrubbing jikin tayi ta turarata sosai. Bayan an gama ta sanyata ta tashe jikinta da kwalacca ɗin meens ɗin. Sannan tabi gaɓoɓi da oil ɗin scentmania. Ita kanta Hamdi duk kukan rabuwa da gida da ta fara sai da ta dakata ta shaƙi ƙamshin sosai.
"Hamdi kada ki yi wasa da ƙamshi. A jikinki da gidanki. Rahama ne shi babba kuma abokin yaƙi da nasarar kamo zuciyar maigida. Mace mai wayo bata bari mijinta yaji wari a jikinta."
"Ba za ki amsa ba uwar miskilanci? Ana baki darasi kin wani haɗe rai." Cewar Sajida tana harararta da gefen ido.
"Idan na amsa ace bani da kunya. Nayi shirun kuma ban tsira ba. Me ya hanaki yi min kara ki ce to?" Hamdi ta rama hararar.
"Ba laifinki bane. Gidan miji za ki kwana yau, dole ki min rashin kunya." Sajida ta faɗa da rawar murya.
"Kinga kin saka ta kuka ko?" Zee ta matsa jikin Sajida ganin har ta soma zubar da hawaye.
Jiki a sanyaye Hamdi ta matsa kusa dasu "ni me na ce don Allah. In ranki ya ɓaci ki faɗa min mana. Meye na kuka?" Ita ma sai ƙwalla.
"To ni wa zan rarrasa cikin ku?" Zee ma ta kama kuka.
Rungume juna su ka yi suka kama kuka haiƙan. Ta tabbata yau su uku kowa makwancinta daban. Aure abin so kuma abin alkhairi ya rabasu.
Hairat fita tayi ta basu wuri. Ana ganinta a waje aka fara tambayar ko Hamdi ta gama shiri.
"Yaya leƙa ɗakin." Ta ce da Yaya.
"Ga iyayensu nan..." Yaya ta faɗi cikin kunya.
Hairat kuwa ta ce ita ya dace taje. Ƴan uwan nasu ma su ka goyi baya. Tana shiga ta samesu su uku suna sharɓar hawaye. Da su ka ganta wajenta su ka ƙarasa kowacce kukanta ya ƙaru. Ta fara yi musu nasiha sai gashi tabi sahu. Sai da aka ji shiru aka biyo bayansu. Inna Luba da kanta da sanya Hamdi a gaba ta saka kaya. Riga da zani na leshi mai ɗan karen laushi. Fuskarta babu makeup sai hoda da kwalli da ɗan pink lipstick sama sama. A haka ma tayi kyau sosai.
"Har a fita ban yarda ki sake sanya min ƴa kuka ba. Ki daure ki riƙe hawayenki don Allah."
"Haba Inna? Ba ma ta ni kike yi ba sai Yaya?" Hamdi ta kyaɓe fuska.
"So so ne Hamdiyya..." cewar Inna Luba tana dariyar tsokanar jikar tata.
"Amma son kai yafi ko? Naji da ana cewa wai mutane sun fi son jikokinsu akan ƴaƴa."
Inna Luba ta kaɗa baki ta ce "Duk ƙarya ne."
"Ai kuwa sai na faɗawa Yaya ta daina jin babu daɗi idan kina shareta."
"Zo nan don ƙaniyarki" Inna Luba ta yafito ta ta gudu.
Matar Kawu Abduƙadir ƙanin Abba Habibu ce ta zauna da Hamdi bayan ta gama shirin ta bata kayan gyara ba mata da sati guda kenan ana bata ta shanye.
"Ki kula da abincin da kike ci da tsafta. Wannan sinadari ne. Kada ki dinga yi musu shan ƙoshi don Allah. Komai saisa-saisa yafi"
Sunkuyar da kai tayi har ta gama yi mata bayani ta tashi. Daga nan gida ya kaure da guɗar shigowar dangin Taj. Cikin Hamdi ya yamutsa da wata irin fargaba. Kukansu ita da su Zee ya dawo sabo fil. Aka fita da ita ko Abbanta da taci burin gani bata sanya a ido ba. Yadda ya bar gidan ranar kai Sajida ita ma haka yayi mata. Ba zai iya ganin fitarsu ba.
A motar Kamal aka sanya amarya. Mummy matar Yaya Babba da uwargidan Alh. Lurwanu wan Inna su ka saka ta a tsakiya. A gaba kuma wata Anti Zinatu ce.
Rantsuwa kala kala Kamal ya yiwa Yaya Kubra akan lafiyarsa kafin ta bari ya fito. Tana barazanar za ta tona masa asiri yayi dariya.
"Ni za ki lallaɓa kafin na tona naki asirin. Alhaji da Yaya Ahmad sun san da ciwon. Na rufa miki asiri ne dai kawai..."
"Alhaji ya sani? Kamal ka kyauta kenan? Idan ya san nima na ɓoye ka san me zai min?" Ta katse shi a tsorace.
"Shi yasa nace ki barni na fita kada na janyo miki" dariya ya yi mata ta bashi hanya da zai fita ya ce "ba maganarki ce bana ji ba, sai dai ina so ki min haƙuri don ban sani ba ko wannan ne abu na ƙarshe da zan yiwa Taj."
Haka ya fita ya barta tana share hawaye. Ta gama ƙarar da duk basirarta da waɗanda za ta nema amma ba a dace ba.
***
Gidan amarya ko yaya yake sai kaji ana son barka. Balle kuma gidan Tajuddin da Hamdiyya. Duk wanda ya shiga da santin gidan yake fita. Kayan ƙawa da ƙyale ƙyale an saka amma masu aji wanda basu cika waje sannan basu fiye ƙyalƙyali ba. Harkar girma da girma kawai. Inna da masoyanta waɗanda su ka goya mata baya sun yi rawar gani sosai. Haka zalika Abba Habibu da Yaya. Basu kwanta anyi musu komai ko don gudun raini da wulaƙanci.
Da sunan Allah a baki da zuci iyaye su ka kai Hamdi ɗakin aurenta. Aka kuma umarci ƴan uwanta da su bar kuka haka nan saboda ta sami nutsuwa. A gidan aka yi sallar magariba sannan aka soma tafiya. Yan matan dangin amarya da ango kowa da irin salon nasiha da shaƙiyancin da yake yiwa amarya a kunne. Da aka watse ya rage Sajida da Zee sai Siyama da sa'aninsu daga ƴaƴan ƴan uwan Abba Habibu. Sun zage sun sake gyare komai kafin shigowar angwaye. Iyaa bata bari Ummi ta bi su ba.
*
Taj ya haɗuwa da Alhaji kafin su fita. So yayi su gana su kaɗai ya ƙara yi masa godiyar dawo dashi cikin ahalinsa da yayi. Sannan yana so ya faɗa masa yanayin Kamal da baya yi masa daɗi. A ƙarshe ya roƙe shi ya matsawa Kamal ɗin ya sanar dashi damuwarsa. Tunda ya san ba zai kalli idon Alhaji ya yi masa ƙarya ba.
Da Ahmad su ka shiga wajensu Hajiya. Kowanne ɗaki idan yaje sai anyi masa addu'a. Sisters ɗinsa su ka kama koke koke. Ahmad ya haɗasu manya da yara ya dinga faɗa.
"Auren ku ke yiwa kuka?"
"Kwanansa ɗaya a gida fa zai sake tafiya."
"Sai ka koma basu gaji da ganinka ba" cewar Ahmad yana haɗe rai don baya son ɓata lokacin da ake yi.
Taj ya kanne ido ɗaya ya kawar da kai gefe "ni dai Hamdi"
"Lahhhh"
Suna tsokamarsa wai bashi da kunya da ya faɗi haka a gaban iyaye ya ce su ma basu da ita da su ka kawo zancen ya sake kwana. Aka gama wasa da dariya su ka fito. A hanya ya fara faɗawa Ahmad damuwarsa akan Kamal.
"Gabana har faɗuwa yake yi idan ya faɗo min a rai. Gani nake kamar ba wani ciwon allery."
Ahmad yayi ta maza sosai da ya iya daurewa ya cije yadda Taj ba zai gane ba.
"Ka tambaye shi?"
"Ina ɗauko maganar yake neman hanyar canjata."
"Kada ka sa komai a ranka. Zan binciko maka."
Ajiyar zuciya Taj yayi "nagode Yaya."
Shiru su ka ɗanyi kafin Ahmad ya ɗauko zancen Salwa.
"Naji duk abin da tayi. Kayi haƙuri. Yau na so ta koma Bauchi amma ban sami zama ba."