Rayuwa da gibi complete na batul mamman - Chapter 32
Rayuwa da gibi complete na batul mamman Chapter 32: Rayuwa da gibi complete na batul mamman Chapter 32. Katse shi yayi "Yaya Ahmad don Allah mu bar zancen.…
4,485 words
Katse shi yayi "Yaya Ahmad don Allah mu bar zancen. Ƙanwarka ce. Nima kuma ƙaninka ne. Na san babu sani ko goyon bayanka saboda haka kada ka ja zancen nan ko ka bani haƙuri. Ita ce ma zan bawa saboda ƙin karɓar tayinta da nayi."
Samun gidan yawa irin na Alh. Hayatu mai tattare da haɗin kan iyali ba abu ne mai wahala ba. Na farko mutum ya zaɓo mata nagari sannan ya tafiyar da mu'amalar gidansa a bisa tsarin shari'ar musulunci. Na ƙarshe kuma ya dage da addua. Saɓani a yau da kullum dole ne. Amma a ƙalla wasu abubuwan da dama sai dai kaji ana faɗi ba dai a gidanka ba.
A farfajiyar gidan su ka haɗu da sauran ƴan uwansu da tsiraran abokai. Sai Safwan da Baballe. Ahmad ya ce ba zai shiga ba a matsayinsa na wan ango. Su Kamal ne su ka raka shi ciki.
"Ya Taj ina ledar kazar amarya? Ko tana mota?"
Abba ne ya yi tambayar kafin su bar bakin motocin. Taj ya tsaya turus, wallahi ya manta ana wannan siyayyar. Bai taɓa raka ango ba amma Kamal ya faɗa masa.
"Subhanallahi...zo ka siyo min." Ya zira hannu a aljihu.
"Gashi na siyo" Kamal ya ɗago ledoji biyu daga gaban motarsa.
Rungume shi Taj yaje ya yi. "What will I ever do without you?"
"Sake ni dalla kada ka sani kuka" Kamal ya ture shi. Taj yaƙi saki. Bishir da wani cousin ɗinsu harda ƴar ƙwalla.
"Ya aka yi ka san ban saya ba?"
"Wallahi jiki na ne kawai ya bani."
Murmushi suka yi sannan Taj ma ya karanto addu'a kafin ya shiga gidansa karo na farko a matsayin mijin aure.
A falo su ka sami ƴan matan amarya da amaryarsu a tsakiya an lulluɓeta da laffayar jikinta. Tana ji ana gaishe gaishe an barta da faɗuwar gaba. Ta kama hannun Sajida tayi masa kyakkyawan riƙo kamar za ta tsinke mata shi.
Addu'a da fatan alkhairi aka yi musu a mutumce. Babu wannan rashin kunyar rungume rungumen sabbin aure da ake a gaban mutane. Ko kuma maganganu na rashin ɗa'a tsakanin angwaye da amare. Da aka gama Safwan ya ce ya kamata su tashi haka nan. Waɗanda za a kai gida su fito a kai su.
"Ni dai ina da abin cewa guda ɗaya kacal. Happy..." Taj ya kalli Kamal.
"Mrs Happy..." Hamdi ma ta ɗaga kai a hankali amma bata buɗe fuska ba.
"Duk abin da za ku yi, ku ji tsoron Allah. Ku yiwa juna uzuri kuma ku kyautatawa juna zato."
Yanzu dai bata yi kuka sosai ba da zasu tafi sai hawaye. Taj ya fita ya raka su sannan ya rufo ƙofa ya dawo.
Hamdi tana nan bata motsa ba. Ya yi murmushi ya ƙarasa kusa da ita ya zauna. Gabanta ya kama dukan tara tara. Yau da anyi an gama. Inda take yanzu gidansu ne ita da Taj. Magana take jira ya yi ko wani motsi duk taji shiru. Ba zato taji saukar abu a gefenta. Ta ɗaga kai da sauri, kafin ta buɗe fuskar Taj yasa hannu ya haɗe gaban laffar ta saitin fuskarta.
"Ni zan buɗe. Kada ki ɓata min tafiyar tarihin wannan daren."
Komawa tayi jiki babu kuzari ta zauna da ta gane babbar rigarsa ce ya ajiye a kusa da ita.
Rage tsayi yayi a gabanta ya ce "Zan taɓaki Hamdi. Kin bani dama?"
"Na'am?" Hamdi taji wata baƙuwar murya ta fito daga bakinta ma'abociyar tsoro.
"Na fahimci a tsorace kike ne shi yasa na faɗa miki."
Kafin ta sake yin magana taji hannuwansa a duka kafaɗunta ya tayar da ita. Sannan ya kama laffayar ya soma warwareta har ta ƙare. Ya kalleta daga sama har ƙasa ya godewa Allah a ransa.
Babu zato daga gareta kawai taji ya janyota jikinsa ya sanya hannuwanta a gefe da gefen cikinsa sannan ya rungumeta. Sun ɗauki lokaci a haka kowa yana fama da yanayin da ya shiga kafin ya ɗago haɓarta yana kallon idanunta.
"Mun shirya Hamdi? Kin daina fushin?"
"Ba fushi nake ba."
"Har akan maganar ɗazu?"
"Ɗazu gaskiyata na faɗa maka ai" ta ɗan kawar da kai.
"Kina nufin yau ni da gwaurayen da su ka fita daga gidan nan bamu da bambanci?"
So tayi ta haɗe fuska don ya san mahimmancin abin da ta faɗa amma wannan maganar sai da tasa ta yin murmushi.
Sannan ta ce "Haka ne."
Hannunta ya riƙe su ka zauna "su rungumi pillow nima na runguma kenan fa?"
"Uhmm" ta amsa kunya na kamata.
Taj ya kalleta da kyau ya ɓata rai "ke Allah kuwa da sake. Sadaki fa na biya."
Da dabara ta ɗora hannu a kan bakinta don kada yaga dariyar da take neman yi.
"Aka biya maka dai." maganar ta fito kamar ba daga bakinta ba.
Ƙayataccen murmushi ya yi "Lallai, kin ce wani abu. Zan tuna miki a lokacin da baki zato." Ledojin da Kamal ya ajiye akan centre table ya buɗe "zo mu ci abinci. Kuma kada ki ce kin ƙoshi."
"Ƙoshi kuma? Yunwa fa nake ji."
Ƙasa ta zamo abinta ta zauna. Taj ya shagala da kallonta ta nuna masa ledojin da ido.
"Ba za ki taimaka min ba?"
"Amarya nake. Yau ɗaya ina zaune kayi min komai."
"Burina ma kullum na taimaka miki." Ya wuce kitchen ya samo tray da kofuna.
Tana zaune ya buɗe ledojin ya ajiye tray ɗin a tsakiyarsu. Akwai youghurt da juice, sai snacks irin su doughnut, croissant da pizza. Ga kwali madaidaici a ciki akwai cake da aka rubuta beautiful beginning Happy and Mrs Happy.
"Allah Sarki Happiness mai sona da gaskiya." Taj ya yi magana yana kallon Hamdi a kaikaice.
Ta gane da biyu yayi magana shi yasa ta ce "Wallahi kuwa, Allah dai ya ƙaro aminci."
Taj ya yi ƙwafa kawai ya buɗe ledar gasashshiyar kaza da gurasa.
"Wanne za ki ci?"
"Mene ne wannan?" Ta nuna croissant ɗin.
"Abincin maza ne." Ya tsokaneta.
Yana rufe baki ta ɗauka ta gutsira harda lumshe ido ta ce da daɗi.
"Na ce miki na maza ne."
"Nima ai ta mazan ce"
Hamdi is just too cute. Yadda take maganar kaɗai ya gama hargitsa masa tunani.
"Har mu nawa?"
"Ga Abbana, ga Halifa sannan..."
Ya zuba mata idanu. Dole taji kunya ta saki murmushi.
"Sannan kuma ga Happy nawa."
"Happy naki." Ya maimaita da murmushin jindaɗin. Ture tray ɗin ya yi ya dawo kusa da ita kamar zai mayar da ita jikinsa ya ce "saboda Allah da gaske kike to akan maganar nan?"
"Da gaske nake."
"Amma in banda ke wa yake kama wani da laifin da ba nasa ba?" Ya marairaice mata.
Yadda komai tayi yake taɓa masa zuciya bai san ita ma haka yake a wajenta ba.
Haɓarta ta ɗora akan tafin hannunta ɗaya tana kallonsa ta ce "Yanzu ya kake so ayi?"
Kalmomi neman ɓace masa suka yi saboda har cikin zuciyarsa yake jinta.
"Stop acting all coy..."
"Meye coy?" Tambayar ma a yangance tayi ta.
Ba kuma wani abu bane yasa take yi masa haka sai don kada ya ɗauki zafi akan shawarar da ta yankewa zamansu. Soyayyarsa tana jinta kamar da ita ta rayu. Ɓata masa rai is the last thing on her mind. To amma me zai faru idan zama yayi zama sai kawai Alhaji ya yiwa Abbanta abin da zata ji haƙurinta ya ƙare? Idan wataran ta kasa riƙe bakinta ta rama fa? Da wane ido za su kalli juna ita da Taj?
"Acting all lovey dovey,.. and shy...and bold, and...."
"This?" Hamdi ta saƙala hannuwanta a wuyansa.
Gabaɗaya su ka tafi. Sai da ya kaita kan kafet ɗin. Fuskokinsu na kallon juna. Numfashinsu na gauraya sannan zuƙatansu na bugawa lokaci guda.
"Hamdiyya"
"Taaajjj" sunansa ya fito da wani irin shauƙi kwatankwacin yadda ya kirata.
"Duk abin da za ki yi, ki ji tsoron Allah kada ki ɗauki alhakina."
Murmushi mai kama da dariya tayi "Ba zan ɗauka ba."
Tausayi ya bata ta danno wuyansa ya ƙara yin ƙasa. Ta ɗago kanta a hankali su ka haɗu. Bata sani ba ko don yau a gidansu suke babu fargabar da yake barinta da ita ta tunanin wani zai gansu. Sakin jiki tayi ta bari yana kissing ɗinta kamar ranar ya fara. Sai da zancen ya fara fin ƙarfinta ta shiga neman ƙwatar kanta.
"Yunwa...yunwa nake ji Allah."
Ƙarfin hali ya yi ya sake turo mata tray ɗin da su ka ture da ƙafa. Kallon duk motsinta yake yi ta rufe ido.
"Ni gaskiya kunyarka nake ji. Ka daina kallona."
"Ji min gulma. Ki gama tumurmu..."
Hannu tasa ta toshe masa baki "ba ni bace."
Taj ya kama dariya "haka ne. Mrs Happy ce."
Ƙin kallonsa tayi. Saboda kunyar da ta rufar mata bata san ta loda abinci da yawa a gabanta ba.
"Ni fa ba ci zanyi ba." Ya yi maganar yana bin gefen kunnenta da wuya da bakinsa.
"Nima na ƙoshi." Ta matsar da tray ɗin. Abin da yake mata ya toshe duka senses ɗinta.
"Cikinki duk ya cushe ko? Tashi kawai muje mu kwanta." Ya tayar da ita jikinsa.
Harararsa tayi tana magana da shagwaɓa "Amma dai a tarihin angwaye kai ne ka fara hana matarka cin abinci ranar da aka kawota. Duk labarin da nake ji tura musu abinci ake yi ko basa so."
"Cewa za ki yi duk na fi sauran son matata. Ba zan takuraki ba but I promise you komai dare ki ka ji yunwa ki tada ni. Zan kawo miki abinci."
Da gaske...ba a taɓa cinye Taj da magana. Hankali kwance ya lauya zancen ya fitar da kansa.
Abincin da ba a ci ba kenan. Ɗakinta ya rakata wanda yake da ƴar tazara da nashi ta shiga wanka shi kuma ya koma falo. Yana kwashe abincin nasu yana rausaya. A fridge ya ajiye komai inda ba za su lalace ba. Ya ɗauki robar youghurt ɗaya ya kai ɗakin Hamdi da kofi sannan ya tafi nasa ɗakin.
Youghurt ɗin ta fara sha tana mamakin yadda aka yi yunwar da take ji ta ɓace. Ta gama shirinta tsaf yadda aka yi mata huɗuba a gida. Sassanyan ƙamshi yana tashi koina a jikinta. Ta kawo hijabinta har ƙasa ta ɗora akan rigar baccin da ta saka mai santsi wadda ta tsaya mata a gwiwa.
Taj ma nutsuwa ya yi ya gama shirin bacci sannan ya taho ɗakinta. Wani abu ne ya bashi mamaki da yana shiryawar har ya kashe masa dukkan karsashi da ɗokinsa.
Da ya saka kaya ya fesa turaruka da body spray sosai amma sam bai ji ƙamshin ko guda ba. Ya ɗauki turaren ya kara a hancinsa amma har lokacin babu. Ya koma toilet ya đaga sabulunsa wanda yanzu da yana wanka yake sake yaba ƙamshinsa sai yaji yanzu baya jin komai.
Zuciyarsa wani irin harbawa tayi. Yaje ya buɗe fridge nan ma babu komai. Hankalinsa a tashe ya ɗauki kwalin juice ya kafa kai don yana son jin sanyi a zuciyarsa. Sai dai me??? Harshensa kwata-kwata babu ɗanɗano.
Afuwan 🙏🙏🙏 Its late, I know. RAYUWA DA GIƁI 32
Batul Mamman💖
This page is sponsored by NAFS-BEDDINGS (Nafisa Tofa 08034581454). A trusted and reliable plug for bedsheets and duvets. A trial is all it takes to get conviced. Ƴar uwa a yar da ɗan yagwalgwalin zanin gadon nan da ya gama tashi daga wanki ɗaya a sayi garanti!
*
Rashin walwala da kuzarin Taj har su ka idar da sallah yasa Hamdi wasu irin tunani marasa daɗi. Me tayi masa? Ko wani abu ne ya same shi? Ko kuwa wani abu yaji wanda bai yi masa daɗi ba? Idan sun haɗa ido sai ya yi murmushin da iyakarsa fatar baki. Cikin idanunsa fargaba take gani. Tayi zaton mata ko ace amare ne kaɗai su ke shiga yanayin tsoro a irin wannan dare. Ashe harda maza. Kai, amma bata zaton haka a wajen Taj. Anya kuwa irin abin da yasa zuciyarta tseren da take yi tun ɗazu shi ne a ransa?
Suna zaune kowa akan abin sallarsa ta zuba masa idanu. Abu ne da bata taɓa samun damar yi ba a baya. Indai suna tare shi ne da kallon. Ko satar kallonsa ta so yi da wuya ta sami cikakken minti guda kafin ya sake juyowa. Amma abin mamaki yau da ake zaton wuta a maƙera sai aka sameta a masaƙa. Tafi minti goma tana nazartarsa bai sani ba. Daga zaune ta ja jiki ta matso kusa dashi tunda dama babu nisa tsakaninsu.
Muryarta a tausashe ta ce "Wani abu ne ya faru?"
"Me ki ka gani?" Taj ya faɗi yana miƙe ƙafafunsa. Sannan ya sanya hannunsa a kafaɗarta ya dawo da ita jikinsa.
"Babu komai tunda baka son faɗa min."
"Am fine Hamdi. Gajiya ce kawai."
"Allah Ya warware. Ka kwanta kayi bacci zuwa safiya za ka ji sauƙi in sha Allah." Bata yarda ba. Kuma ta san cewa shi ma da ya faɗa ya san bata yarda ba ɗin.
Neman abin cewa yake yi wanda zai kwantar mata da hankali sai wata ƙaƙƙarfar atishawa ta zo masa. Sau biyar yayi ta a jere. Kowacce ta fito sai ya ce Alhamdulillah. Ita kuma ta bi masa da YarhamukAllah.
Tabbas a cikin ambaton Allah akwai rangwame ga bayi. Tun a ta uku Taj ya soma jin ƙamshin ɗakin da na jikin Hamdi sun cika ƙofifin hancinsa. To dama sihirin ba ayi shi don ya kama shi da wuri ba. Musamman Alh. Usaini ya nemi wanda zai shiga sannu a hankali saboda Taj ya zata cuta ce. Idan haka ta faru asarar dukiya kawai zai yi ta yi wajen neman magani. Babu lallai in shi ko wani nasa ba masu yarda da harkar sihiri da bokanci su yi tunanin neman karya aikin da Ayar Allah.
Shi dai tunda yaji wannan ƙamshin ya tashi da ƙarfinsa ya sungumi Hamdi yana faɗin Alhamdulillah.
"Wai don Allah me ya faru?"
Hancinsa ya ɗora akan nata tana cikin hannuwansa ya ce "its nothing" ya kama juyi da ita. Daga nan ya manta da komai ya kuma mantar da ita. Daren ya zama tarihin Tajuddin da Hamdiyya su kaɗai.
***
Wai bahaushe ya ce kayi da kanka kafin ayi da kai. Tunda Kamal ya faɗawa Yaya Kubra cewa Alhaji da Ahmad sun san da ciwonsa ta kasa samun kwanciyar hankali. Gani take kowane lokaci Alhaji zai iya kiranta. Abin da zai biyo baya kuwa sai Allah. Ilai kuwa wajajen goma na dare sai ga text ɗinsa. Bangajiyar biki ya fara yi mata sannan ya rubuta
(Ki nemi izinin mijinki. Ina son ganinki gobe da safe.)
Bacci ɓarawo da tarin gajiya ne su ka yi awon gaba da ita ba don ta so ba. Maigidan nata ta faɗawa komai a hali na tashin hankali.
"Wallahi ba ya son ɓoye ɓoye. Goben nan ban san me zai yi min ba."
"Baki kyauta masa bane kema kin sani. Ba don ya neme ki ba da nima zan nuna miki kuskurenki na biyewa Kamal. A wautarsa gata yayi muku na yin shiru. Amma a zahiri cutar kansa ya yi. Ance a problem shared is a problem solved. Bamu san ta inda za a dace ba da ya faɗa da wuri."
Wannan magana ƙara dagula mata lissafi tayi. Washegari a daddafe ta jira ƙarfe bakwai da rabi tayi ta kama hanya ta tafi gida. Waya ta ɗauka ta kira Alhaji. Yayi mamakin sammakonta.
"Idan kina da aikin safe ne ki wuce Kubra sai na same ki a office idan na shirya."
"A'a Alhaji. Na san akan abin da kake nemana. Babu aikin da zan iya idan baka fahimceni ba."
Katseta yayi da ya gane me take nufi. "Jira ni a ɗakin Kamal."
"To Alhaji. Kayi haƙuri don Allah." Ta faɗi da rawar murya.
Ko amsata bai yi ba ya kashe wayarsa. Yaƙi jinin ƙumbiya ƙumbiya. Shi yasa yake jan su a jiki tun basu da wayo. Ko fensir wannan bai yarda wani ya zo ya ce wane na buƙata ba. Ya fi son ka je da kanka ka faɗa.
"Ban faɗa masa komai ba." Kamal ya tabbatar mata da ta shiga ɗakin.
"Nafi tunanin gaya min zai yi. Gara da na faɗa masa gaskiya a waya don ban san yadda zanyi na fidda kaina a gabansa ba."
Sai bayan kimanin minti sha biyar Alhaji ya shigo tare da Bishir da Abba. Kana ganinsu ka san basu san me yake faruwa ba. Sun dai kama bakinsu tunda sun san koma mene ne yanza za su ji. Ita dai Yaya Kubra tana haɗa ido da Alhaji ta sunkuyar da kai. Daga daren shekaranjiya zuwa yau ya faɗa. Dakakkiyar shadda ce a jikin shi ruwan toka. Babbar rigar a ninke Abba ya rataya a hannunsa. Kwarjini iya kwarjini sai Alh. Hayatu.
Da kakkausar murya ya ce mata "Kin kyauta."
"Alhaji don Allah..." ta fara cewa tana zamowa daga kan gado.
"Ya isa." Ya zauna a inda ta tashi. Yaran nasa su ka zagaye shi a ƙasa banda Kamal da ya hana motsawa daga kan kujera.
"Wace gudunmawa shirunki ya sama min?"
Iya bincikenta na ƴan uwansu na kurkusa (gidansu Alhaji da Hajiya) ta sanar dashi. Abin al'ajabi cikinsu babu mai blood group AB(-). Ana bikin Taj ta tura musu survey link na google form inda ta buƙaci su cike da cewar research (bincike) ne take yi da ya shafi aikinta. A ciki tayi tambayar da mutum sai ya saka sunan dangin da ya fito. Ta haka ta rarrabe kowa.
"An sami masu rhesus negative mutum huɗu."
Alhaji ranƙwafowa yayi kamar da haka ne zai ji me za ta ce sosai.
"Biyu ba za su iya yi masa amfani ba domin ɗaya A ne, ɗayar kuma B."
"Ina jin ki Kubra."
"Masu O negative biyu da za su iya taimaka masa, ɗaya ɗiyar ƙanwar Hajiya ce."
"Mata suna iya bayarwa ne?" Alhaji ya tambayeta hankalinsa a tashe. Bishir da Abba su ka sake shiga duhu.
"Eh, amma...amma da wuya a samu nata. Widad ce. Yaranta biyu tana da cikin na uku" Yaya Kubra ta faɗi, ita ma kanta tana cikin jin ciwon hakan.
Kamal ya dube su. Irin wannan abin yake gudu. "Alhaji don Allah..."
"Ka rufe bakinka Kamal" ya tsawatar masa. Ya juya ga Yaya Kubra "Sai wa kuma?"
"Ɗan Widad ɗin na farko mai shekara biyar. Yayi ƙanƙanta."
"Wai me ake buƙata ne Yaya Kubra?" Abba ya gaji da jin maganar da bai fahimta ba kuma yana ganin masu yinta cikin rashin nutsuwa.
"Ƙoda ce Abba. Duka ƙodojin Kamal ciwo ya cinye su." Alhaji ya bashi amsa da kansa.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Abba da Bishir kuka su ka fashe dashi. Alhaji ko hanasu bai yi ba. Kowanne yana cewa a cire tashi. Da su ka ji ba da ka za a ɗauka ba nan ma sun sake shiga tashin hankali. Kamal mai ciwon shi ya koma rarrashinsu.
"Amma fa ni ban gane ba. Me yasa masu A da B ba za su iya bashi ba, bayan kuma su ma ɗin negative ne? Jiya fa nayi ta bincike Kubra. A da B duka donors ne." Cewar Alhaji da sanyin jiki.
"Haka ne Alhaji. Mai B ɗin sickler ce."
Alhaji ya ce "Ita ma mace? Bana ma son a kai ga ɗaukar na mace. A ɗin fa?"
"Ɗan Kawu Sayyadi ne (ƙanin Hajiya). Shi kaɗai ne bayan mu nan wanda ya san da ciwon Kamal. Naje na same shi. Ban ko roƙa ba ya ce a shirye yake da aje a cire tasa. Shekaranjiya kafin naje wajen bikin test muka fara zuwa aka yi masa." Ta ja numfashi sannan ta ce "yana da Hepatitis."
"A taƙaice dai ...Ya Rabbi....Allah na" Alhaji ya danne ƙirjinsa da ya kama wani irin ciwo.
Duka su ka rufar masa. Yaya Kubra ta tashi zata koma mota don motar likita ba ta rabuwa da kayan bada kulawar gaggawa.
"Dawo ki zauna." Alhaji ya tashi ya dafa kafaɗar Kamal "akwai Allah kaji ko." Ya dubi Abba "ka haɗa muku kaya kai da Kamal akwai jirgi gobe. Yanzu zan sa Ahmad ya sayi ticket ku tafi Saudiyya."
"Alhaji ni fa? Me zan yi?" Bishir ya tashi tsaye da zafin nama yana goge ƙwalla.
"Tare zamu bisu jibi da Ahmad. Bana son iyayenku su gane komai. Kawai zan ce musu Umra zamu ni da yarana maza."
"A nan za ku barni Alhaji?" Yaya Kubra ta soma sabon kuka.
"Kina da visa ne?" Da sauri da amsa cewa akwai "ki tattaro komai na asibitinsa a wajen Dr. Mubina jibin sai mu tafi. Ki san me za ki faɗawa iyayenki tunda kin ƙware a rufa-rufa." Kai ta sunkuyar.
"Me zan faɗawa Taj?" Kamal ya yi tambayar ga Alhaji.
"Zai yi zargin baka haƙura ba shi yasa baka haɗa da shi ba." Inji Bishir.
Alhaji wayarsa ya ɗauko daga aljihun gaban rigarsa ya dubi lokaci. Yayi wuri ya kira mai sabon aure. Sai ya ce da Kamal,
"Ka faɗa masa zamu je Umra amma ba da shi ba. Yaje ya yiwa matarsa passport a nemi visa a sanar dani sai su tafi daga baya."
Da ya fita ya kulle musu ƙofar ɗakin sai ya sami damar barin zazzafar ƙwallar da ya danne a gaban ƴaƴansa saukowa. Sau ɗaya ya haɗa ido da Kamal yaga yayi masa murmushi na wanda ya karɓi ƙaddararsa hannu biyu.
"Ya Allah ban isa ba. Ba iyawata bace ta bani ƴaƴan nan. Allah nagodewa ni'imominKa gareni. Da rauni da gazawata na zo gareKa cikin ƙanƙantar da kai. Ka ceci rayuwar ɗana Ya Ubangijina." Bayan shekaru masu ɗimbin yawa ya sami kansa da fashewa da kuka mai ciwo da cin zuciya. Yana ƙaunar ƴaƴansa kamar rai. Waɗanda ya rasa a ɓari da biyu da su ka tafi da ƙananun shekaru har yau yana jin abin a ransa.
Tsayuwarsa ya yi a wajen yana neman nutsuwa amma idan ya tuna haƙuri irin na Kamal sai yaji zuciyarsa tana zafi. Duk gidan shi ne yafi kowa damunsa akan maganar Taj. A dalilinsa ya haƙura ya bar iyalinsa suna mu'amala da Taj ɗin. Domin da fari niyarsa ya yanke shi daga jikinsa gabaɗaya.
Ƙofar ɗakin Yaya Kubra ta zo da shirin fita taji sautin da mahaifinta yake dannewa. Bata san lokacin da ta koma da baya ta ɗora kukan ba. Abba da Bishir su ka kara kunnuwa su ka ji. Kowa ya koma ya zauna da kuka. Shi kuma ya koma ciki ya shige ɗaki ya rufe ƙofa.
"Magana ake ta Kamal yana da rai har yanzu. To me hwaru?" Kamal ya faɗi yana dariya.
"Ni ban taɓa tsanar wannan kalmar ba sai kamar yau." Abba ya sha kunu.
Yaya Kubra tayi murmushi "dole ka sako wasa kafin Taj yaji wannan maganar."
"Don Allah ki bar tayar min da hankali. Da me kike so in ji? Ciwon ko tararrabin abin da zai zo yayi?"
***
"Siyama kin tabbatar duk abin da Iyaa ta faɗa min gaskiya ne?"
Yadda Baba Maje ya ɗauki zafi sai da gaban Siyama ya faɗi. Ta dai san cewa ba gulma ta kawo ba tunda cutar da mutum taji za ayi take son hanawa da ikon da Allah Ya bata.
"Da gaske ne Baba."
"Kirawo min Ummin"
Tashin muryar iyayen nata ne ya fito da ita daga ɗaki inda taji Baba Maje na rantsuwar sai ya karya Ummi. Iyaa kuma tana tare shi. Da ƙyar ta samu ya nutsu shi ne ta ce masa,
"Taurin kai gareta ka sani. Idan baka bi komai a hankali ba wallahi ko me zai faru ba faɗin gaskiya zata yi ba."
Bai daina faɗan ba sai dai ya haƙura da zancen zuwa ya tasheta da duka. Hankalin Siyama sai ya tashi shi ne ta fito yake tambayarta.
"Ita hayaniyar nan bata tasheta ba?" Ya faɗi yana girgiza ƙafa da kallon ƙofa.
"Yanzu zan taso maka ita. Amma don Allah ka bi komai a sannu."
Ɗakin nasu Iyaa ta shiga ta taso Ummi. Har ta fara kiran bacci bai isheta ba Iyaa ta daka mata tsawa. Haka ta biyota tana zumɓura baki. A zatonta aiki ne za a saka ta. Sai gata tayi ido huɗu da Baba da su ka sauko ƙasa.
"Ke Siyama hau sama ki ɗauko min wayar Ummi."
Firgigit duk wani baccin iya shege da hammar ƙarya su ka gudu.
"Wayata Baba? Ke tsaya Siyama."
Siyama ta dakata. Baba ya zaro mata idanu ta kama bin bene ba shiri.
"Baba me nayi? Don Allah kada ka duba min waya." Ummi ta juya za ta hau benen.
"Ki ka kuskura ki ka hau benen nan sai nasa Baballe ya karyaki."
Cak ta tsaya "Baba me nayi?"
Bai kulata ba don bata cancanci hakan ba har Siyama ta sauko ta bashi wayar.
"Ɗakinku ɗaya. Ki faɗa min gaskiya, akwai wata ko babu?"
Mugun kallo Ummi ta watsawa Siyama. Ita kuma jikinta ya ɗan yi sanyi.
Iyaa ta ce "Baki ji me aka ce miki bane?"
"Akwai"
"Ɗauko min."
"Baba don Allah..." Ummi ta zube a ƙasa tana magiya. Abubuwan dake cikin wayar dake ɗakin sun fi ƙarfin me wayar. Dukkan wata mu'amalarta ta waje da fitintinunta suna ciki.
Ba jimawa Siyama ta sauko saboda a ƙasan filo Ummi ta ajiyeta da ta raba dare tana dannata jiya.
"Zan saurari Habibu don nayi imanin indai wani abu ya faru gidan ƴaƴansa ba zai ɓoye min ba. Idan abin da Siyama taji kina ƙullawa ya tabbata to ki kuka da kanki. Sannan in ki ka saka ƙafa a ƙofar gida to kada ki dawo na yafeki." Ya kalli Iyaa da Siyama "duk wanda ya bata aron waya ba da yawuna ba."
Wayoyin ya kashe a gabanta ya tashi ya shige nasa ɗakin. Ummi ta rasa gane kuka ya kamace ta ko me. Abin da yake taso mata yafi ƙarfin hawaye ko kalaman da take jin tana son zazzagawa Siyama.
***
Ahmad ya so ƙwarai ya kira baban Salwa akan ya turo a ɗauketa. Da wannan niyar ya shiga ɗakinta inda ya mayar da Mami bayan tafiyarsu Anti Zabba'u ya shiga da ya gama wayar. Ɗakin wari yake yi mai ɗauke numfashi. Ya yi mata kallo ɗaya ya juya. Nan ya barta tana so tayi kuka amma bakin ma ya karkace sai dai hawaye kawai. Kallon da yayi mata na takaici ne da baƙincikin halin da ta saka kanta kuma su ma ta jefa su.
Mami bata da kowa sai ƴan uwa waɗanda ta jima da barranta kanta daga garesu saboda abin duniya. Bata zuwa sabgar kowa sai dangin dangiro da abokan arziƙi masu kuɗi. Jininta dai ta datse zumunci da rashin mutumci saboda ita tana gidan mai kuɗi. Yau ga ranar ƴan uwa amma babu wanda zai nema ya taimaka masa da kula da ita. In ya ɗorawa Zahra wankin kashi da fitsarinta ba ƙaramin rashin adalci hakan zai zama ba. Yau da gobe sai Allah. Gashi Mamin a baya bata nuna mata ƙauna saboda akwai wadda ta so ya aura. Wannan tunanin yasa shi fasa neman Salwa ta tafi. Ita ce mace kuma dolen Mami. Zai saka mata ido kafin ya sami wadda zai dinga biya.
Shawarar da ya yanke ya faɗawa Zahra. Ta bashi goyon baya da alƙawarin za ta dinga taimakawa ita ma.