Kenza eBookz

Rayuwa da gibi complete na batul mamman - Chapter 42

Rayuwa da gibi complete na batul mamman - Chapter 42

Rayuwa da gibi complete na batul mamman Chapter 42: Rayuwa da gibi complete na batul mamman Chapter 42. Yanzu rayuwarsa ta koma bibiyar abokai da tsofaffin…

4,488 words

Yanzu rayuwarsa ta koma bibiyar abokai da tsofaffin yaransa yana maula. Wataran a dace wataran kuma a wulaƙanta shi. Da ya gaji ne ma ya goranta mata rashin gara da kayan ɗaki. Ita kuma saboda ɗanyen kai ta kira Anti Zabba'u. Ranar anyi sa'a ƙanwarsa ta zaga ta bayan idon iyayensu ta aiko masa da kaji da jallof ɗin shinkafa ta gaske. Kafin ya dawo daga wajen abokinsa sun cinye tas. Ita kanta Salwa bata ko ɗanɗana ba. Tana ta magiyar kar su taɓa aka rasa mai sauraronta ma. Ɗan uwa aka ce rabin jiki. Ahmad ya tausaya mata sosai. Kayan ɗaki da electronics babu abin da bai tanadar mata ba amma ta watsa masa ƙasa a ido.

Suna zaune ya danne fushinsa yana ta yi mata nasiha tana ta kuks sai ga Alh. Usaini. Takalman namiji kawai ya gani ya yi jifa da ledar hannunsa ya zare belt ya afka musu. Salwa na ganin shi ta tashi ta tsaya a gaban Ahmad ta bubbuɗe hannuwa da ƙafafu ta kare shi. Ai kuwa belt ta sauka a jikinta ta gantsare don azaba. Ya sake ɗagawa karo na biyu Ahmad ya miƙe. Kwarjini da cikar mutumtakarsa su ka sanya Alh. Usaini yin laƙwas kamar dafaffen alayyahu.

Ahmad ya riƙe belt ɗin tare da hannunsa ya nuna masa Salwa.

"Duk abin da za ka yi, musamman wanda ya shafi mu'amala da mutane kaji tsoron Allah. Da kai da ita da gurɓatacciyar rayuwarku ku ka haɗu amma hakan ba yana nufin da ita za ku ƙare har ƙarshen rayuwa ba in kun so."

Ficewa yayi ko waige babu. A waje yaci karo da ledar da Alh. Usaini ya yar. Taliya ce leda ɗaya sau mai, maggi da kayan miya na naira ɗari biyu. Wani abu yaji ya tokare masa wuya. Yanzu Salwa ake ciyarwa a haka? Lallai kowa yaƙi sharar masallaci zai yi ta kasuwa.

Ya koma gida cike da damuwa. Ya kira Abban Salwa akan maganar kayan ɗaki ya ce ya rabu da ita. Darasi yake so ta koya a cikin auren nan. Hujjojin da ya bashi duka ya gamsu da su. Duk da haka washegari ya tura ƴar ƙurƙura gidan shaƙare da kayan abinci.

"Idan da kuɗi a wayarka don Allah ka bani aro na kira Yaya Ahmad nayi masa godiya."

Tsaki ya banka mata ya tashi ya fita da sauri ya bi bayan mai ƙurƙurar nan da gudu. Sai da ya kusa ƙarshen layi ya tsaya. Yana faman haki ya ce ya taimaka masa da numbar wayar wanda ya aiko shi. Mutumin ya karanto masa ya kwafa. Da numfashinsa ya daidaita ya kira shi.

"Dama godiya na kira nayi maka."

"Ku dai ku ji tsoron Allah daga kai har Salwa. Rayuwar da kuke ciki Allah Ya azurta masoyanku da fin ƙarfinta. Cikin minti guda za a iya canja komai ma rayuwarku amma Allah bai bayar da iko ba. Hakan kaɗai ya isa ya zame muku izina. Allah Ya kyauta."

Tunawa yayi da wani kalamin da yaji daga bakin Abban Salwa wanda shi kuma Baban Alh. Usaini ne ya faɗa masa a lokacin da ya nemi shawararsa game da makomar rayuwar yaran nasu.

"Yunwa, ƙishi da rashin kayan more rayuwa zai sa su yi laushi harma ka ga nadama nan ba da jimawa ba a tare da su. Biyewa wannan ba ƙaramin ganganci bane. Yunwa ta ishi kowane shege darasi. Yanzun nan za ka ga mutum ya shiga taitayinsa. To amma fa ƙoshi shi kuma yana fito da ɗan iska cikin mutane. Da zarar tumbi ya ɗauka sai kowane rashin daraja ya biyo baya indai mutum ba nagari bane. Shin Alhaji ba ka ganin yadda almajirai su ke rashin mutumci a unguwa idan abinci ya wadace su? Wani fa a ƙofar gidanka zai zubar da abinci ya ce ka bashi gaya ko babu nama."

Abban Salwa ya gyaɗa kai "wannan gaskiya ne."

"Ina son Usaini amma nafi son gyaruwarsa. Idan mu ka yi saurin karaya akan su to ka sani komawarsu gidan jiya abu ne mai sauƙi. Irinsu bayan addu'a da nasiha dole a bari su gane cewa kyautatawa ce daga Allah privileges ɗin da su ke samu ba wai dolensu bane don sun isa. Suna buƙatar duniya tayi musu atishawar ƴan tsaki!"

Abu ne mai wuya iyaye su iya ɗauke kai idan ƴaƴansu su ka shiga irin wannan yanayin to amma fa wani lokacin dole a tauna tsakuwa don aya taji tsoro.

***

"Zancen Port Harcout naji tana yi a waya wallahi. Don Allah kayi wani abu kafin ta ƙarasa shiga duniya mu shiga uku."

Iyaa ke wannan maganar da Baba Maje tana kuka sosai. Sababbin tsare-tsare Baba Maje ya kawo cikin gidan bayan fitowar Ummi daga police station. An karɓe babbar wayarta sannan ba a barinta ta fita ko ƙofar gida. Ƙawayenta tun daga soro ake sallamarsu. Dangi kuma aka sami abin so. Kowa ya buɗe baki a gidan biki ko suna zancenta ake yi ana aibata halinta. Isassu ma har gidasu ke zuwa su faɗi maganganu son ran su. Yarinya a cikin gidansu ta zama mujiya. Tsangwama ta ko'ina fuskantarta take yi.

Watarana Iyaa ta fita sai tayi mantuwa. Ta dawo za ta wuce ɗakinta sai taji Ummin tana waya tana faɗawa wanda su ke magana ya saya mata ticket ɗin luxurious bus za ta fito nan da kwana huɗu. Iyaa ta sulale ta fice bata bari ta san da zuwanta ba. Sai dare ta sami Baba Maje ta faɗa masa.

"Ummi tamkar ba jinin mu ba. Yarinya sai azabar taurin kai da son zuciya. Duk abin da yake faruwa bata saduda ba" Tana kuka tayi maganar.

"Kada ki yi furucin da zai kai ki ga nadama akan Ummi. Ni dai na fahimci hanyoyin da muka ɓullo ba za su haifi ɗa mai ido ba. Ina kuma tsoron ace jini na ta shiga duniya."

"To yanzu meye abin yi?"

"Aure zan yi mata."

"Da wa? A dangin mu wa za ka tursasa ya bari ɗansa ya aureta?"

"Kofur Ɗanliti zai auri Ummi" Baba Maje ya faɗi da wani sense of relief.

Iyaa tayi shiru kafin daga bisani ta ce "haka ne."

"Ko kina da wata shawarar? Irin wannan auren ba shi mu ke yi mata sha'awa ba tsakani da Allah."

Magana su ke yi ƙasa-ƙasa cikin alhini gwanin ban tausayi.

Iyaa ta numfasa "yanzu za ayi ta aibata auren ana yamaɗiɗi da mu a cikin dangi da unguwa idan aka ga mijin da ta aura. Wasu ma su ce Allah Ya ƙara pi."

"Sai mu toshe kunnuwanmu tunda ba a canjawa tuwo suna. Mune dai iyayen Ummi duk inda za a je a dawo."

"Amma kana ganin za ta zauna? Mutum irin Kofur ɗinnan yana da abin riƙe mata sama da guda?"

Shima kansa Baba Maje ba wai son zaɓin nasa yake yi ɗari bisa ɗari ba. Da babu ne dai gara babu daɗi.

"Haka za mu haƙura don sau dubu gara ace abinci ne bata da shi a gidan miji da dai ta shiga duniya. Indai da rai da lafiya ba zan bari yunwa ta kama ta ba alfarmar Annabi SAW."

"Wahala za ta ƙaru a kan ka. Ba gara mu nemi wata dabarar ba?"

"Ummi bata jin magana kema kin sani. Kuma wannan shawarar da na yanke ba rashin so bane ya janyo. Ban san yaya lahira take ba amma a iya abin da Allah Ya hore min in ji a duniya game da iyalina, sai nake ganin ko aljanna na samu ba zan ji daɗinta ba idan wani cikinku bai riskeni ba a can. Ina tausayin makomar ƴata idan ba ta yiwa kanta karatun ta nutsu ba." Kawai sai ya soma hawaye.

Kusa da shi Iyaa ta koma su ka riƙe hannu suna kuka mai ratsa zuciya.

"Bawa baya sanin matsayin ibadarsa sai ya koma ga Allah. Kuma muna yi ne cikin kyautata zato da cikar yaƙini to amma bamu san baɗini ba. Yaya kike ji za ta kasance ace duka gidana babu wanda ya dace balle ya ceci sauran? Ai ance ana bawa salihan bayi ceto ko? Shi yasa na damu sosai."

"Kafin ma a kai ga lahira ba ka ganin kamar iyalin Habibu sun ja baya da mu? Ka duba fa hatta aikin da aka yiwa Jinjin sai Baballe ne ya ji a wajen Zinatu."

"Kai anya kuwa? Kada mu ɗauki haƙƙinsu." Baba Maje ya faɗi duk da yafi yarda da zancenta.

A sanyaye ta ce "nima bani da tabbas, hasashe ne kawai duba da abubuwan da su ka faru. Ka san Allah da Siyama ce ta auri yaron da ya fito daga irin gidan nan namu sai na sa an sako min ita. Zan ji tsoron kada Ummi ta cutar da ita."

"Kamar kin shiga zuciyata. Ina ta tunanin ko dai in sa ya sauwaƙe mata. Ƙila sun kasa faɗa mana ne saboda kawaici."

"Allah Yasa bai taɓa musu ƴa ba. Ka san yaran yanzu da mugun rashin haƙuri."

"Zan tuntuɓe shi. Tunda auren dama ba na soyayya bane. Zumunci mu ka so ƙullawa kuma da alama ba zai yiwu ba."

Wani abu Ummi taji ya wuce mata mai ɗaci. Ta juya a hankali ta koma ɗakinsu. Ɗazu ta ga fitar Iyaa sai ta zargi ko ta ji wayar ds tayi. Shi ne ta biyo ta da Babansu ya dawo. Jikinta ɓari ya dinga yi har ta isa ta faɗa kan gado. Da yake zuciyar ta jima babu tunanin komai sama da son kai, hassada da sharholiyar duniya, sai ta kasa kuka. Ta kuma rasa addu'ar da ya dace tayi. Haushin kanta kawai take ji da takaicin jin wayarta da Iyaa tayi.

*

Kofur Ɗanliti har gida ya zo neman auren Ummi bayan fitowarta da kwana ɗaya. Ta zauna ta sille shi da rashin albarka iri-iri. Baba Maje sai ya bashi haƙuri ba don komai ba kuwa shi ne yadda yake gudun me zai je ya dawo. Ummi idanunta a buɗe suke. Kada tayi wa Ɗanliti abin da auren zai zo ya mutu da wuri. To amma da alama zai iya riƙonta duk botsarewarta. Haka dai yake gani amma bashi da tabbas. Saboda haka bayan shawararsu da Iyaa, sai ya kira shi su ka yi magana.

"Me yasa kake son auren Ummi duk da ka san wani abu cikin halayenta?"

Ɗanliti ya yi murmushi da confidence "ina sonta ne Baba."

"Me yasa kake son mace irinta?"

"Haɗi daga Allah. Kuma da naji laifinta sai na tuna da tawa samartakar." Gyara zama ya yi domin jindaɗin abin da zai faɗa. "Baba ni fa tsohon ɗan daba ne."

Kallon Baba Maje yayi yana jiran ganin tsoro ko firgici sai yaga babu ko ɗaya. Neman ƙarin bayani kaɗai yake iya gani. Ɗanliti sai ya yi masa tun kafin ya tambaya.

"Nayi dabanci da shaye-shaye sannan na taɓa tsibbu." Baba Maje yaji hankalinsa ya tashi amma kuma a yanzu dai bashi da wani zaɓi.

"Abubuwa ne da na san za ka sami labarinsu idan ka tashi bincike a kaina shi yasa nake faɗa maka. Na riga na tuba tuntuni ina aiki kamar yadda ka sani."

Wata zuciyar tana ƙwanƙwasarsa akan ya fasa yayinda wata take tuna masa da me zai iya faruwa idan Ummi ta shiga uwa duniya.

"Na baka amanarta. Don Allah idan ka ga abin yafi ƙarfinka ka dawo da ita gida. Bana son a kai ƙadamin da za ta gudu domin yanzu ma iƙirarin da take kenan." Yanayinsa ya nuna tsantsar damuwarsa "ba na son zama abin nuni da kwantace ace ƴata ta shiga duniya."

"Ba za ta shiga ba da yardar Allah. In Allah Ya so sai kayi alfahari da bani ita."

Da daddare a ranar ya faɗa mata shirinsa a kanta bata ce komai ba. Abin ya bashi mamaki sosai. Haka dai yana ta tsoron kada a wayi gari ta gudu kafin auren amma yaji shiru. A fuska da baɗini bata son auren amma ta rasa gane me yasa ta kasa kataɓus. Auren tubabben ɗan tsubba zata yi bata sani ba. Surkulle da siddabaru babu wanda bai iya ba, kuma babu wanda bai shirya yi ba a kanta domin ya samu ta zauna dashi. Ko bayan zuwansa na farko ba wai haƙura ya yi ba, shiri ya tafi sakewa.

Ƴan uwan Baba Maje da ya neme su akan bikin sun yi murna ƙwarai. Ashe kowa na tsoron kada ya roƙi alfarmar haɗata da nasa ɗan saboda mugun halinta. A ranar da ya kamata ta gudu, a ranar aka shafa fatiha tsakaninta da Kofur Ɗanliti.

***

BAYAN WATA UKU

Taj da Kamal sun duƙufa aikin gyara ko ace jeren sabon gidan Abba Habibu da Yaya. Hawa na uku kuma na ƙarshe a ginin gidan abincin da aka bashi ya mayar gida. Ko sisi basu bari ya kashe cikin kuɗin da Dr. Hadifi ya ba shi ba. Iyalin Alh. Hayatu musamman Kamal su ne suka yi komai.

An sallamo su daga asibiti jiki ya yi kyau sosai. Duk da haka Taj ya hana shi ayyukan ƙarfi. Shi da Abba su ke ta kai komo. Abba Habibu da Alh. Hayatu kuma sun fita ana ƙarasa cike-ciken takardun shaidar mallaka da sanya hannun hukumomin da su ka dace.

A can gidan da Alh. Hayatu ya kama kuma Inna Luba da Baba Malam (Alhaji ne ya biya masa) sun iso kwana biyu da su ka wuce. Su Amma da Yaya Babba ma duk sun zo amma sun wuce Madina. Sai an gama gyare-gyaren gida da restaurant gabaɗaya za su rankaya dukkaninsu su tafi gida. Su Abba Habibu za su koma su kimtsa a tsanake sannan su koma a fara sana'a.

Hamdi da Mubina sun biyo su amma sun fita saya musu abinci. Da su ka dawo da ledoji niƙi-niƙi masu sauke kaya duk sun tafi tare da Abba. Babu kowa sai mazajensu.

Ɓata fuska Hamdi tayi suna shiga falon ta zube ledojin hannunta.

"Happiness kaga rigima ko? Don Allah ban ce su zauna in siyo abincin ba? Yanzu gashi nan ta dawo tana wani ɓata rai."

Kamal ya tashi cikin nutsuwa don har yanzu baya yarda ya saki jiki kamar da.

"Angel me ya sami ƙanwata ne?"

Mubina ta kalle shi ta mayar da dubanta ga Hamdi wadda abin mamaki ta fashe musu da kuka.

"Kun gama da ɗakunan?" Mubina ta tambayi Kamal.

"Eh amma me ya same ta?"

Shi da Taj duk sun shiga damuwa. Taj ya koma kusa da ita yana son ɗago mata kai taƙi yarda. Mubina ta nuna hanyar ɗakunan da ido, Kamal ya fahimta sai ya tashi ya bi bayanta. Suna shigewa ciki Hamdi ta faɗa kan Taj ta sake dasa kukanta daga farko.

"Don Allah ki yi min bayani mana. Me na yi miki?"

Cikin kuka ta labarta masa "naje sayan ice cream wai sai da aka zo kaina mutumin ya ce babu chocolate."

Mamaki ya kama Taj "shi ne kike kuka? Yaushe ma ki ka fara son chocolate flavour ɗin?"

"Yau shi nake so."

Tashi ya yi "bari na fita na nemo miki I am sure ba za a rasa.

"Ba zai zama irin nasu ba. Ni shi nake so."

Taj yaga abin na gaske ne sai ya koma lallaɓata.

"Ko in yi miki? Mine will taste even better."

"Na su nake so" ta tura baki.

"Ahhh to gaskiya Mubina ta zo ta duba min ke. Alamu sun nuna rigimar nan ba nan kusa za ki daina ta ba." Ya rungumeta yana dariya.

Ture shi tayi "ni lafiyata ƙalau kawai ka samo min chocolate ice cream."

"In ki ka ce nima na zama cream ɗin ai zama zan yi maman babyn Taj." Ya dinga kashe mata ido.

Kunya taji ta rufe ido tana dariya.

"Auuuu. Kin ma sani kenan. Tun yaushe?"

Leɓenta ta taune tana murmushi "a hanya Mubina ta sa mu ka tsaya a clinic."

Rungume juna su ka yi Hamdi tana tunanu. Yanzu haihuwa za ta yi ta zama maman wani? Kuma idan an ɗaga baby a ce na Taj ɗinta ne. Lallai Allah ne mai juya al'amura yadda ya so.

Katse mata tunani ya yi "zo mu ci abinci." Ta zauna ya ce "mun kusa komawa gida na sami ƴancin dafa miki abin da ranki yake so."

"A baki za ka bani."

"An gama."

A cinyarsa ya ɗorata. Rabi cin abinci rabi rarrashi da kalamai masu daɗi.

* Murnar ƙaruwar da za su samu su ka gama yi sannan Kamal ya langaɓe kai ya ce "Doctor zo ki gani ban warke ba har yanzu?"

Tayi dariya "Sai nan da wata uku."

"Come on Angel. Kada fa ki fara ɗaukin haƙƙina. Ni dai gaskiya so nake ki tare."

"Yanzu ba tare muke ba?"

"Tariyar gaske nake nufi. Ni ma so nake ki fara rigimar ice cream."

"Sai dai hot cream."

"Wasa ma ki ka mayar da maganar ko? Do you even love me Angel?"

Mubina ta koma gabansa ta durƙusa a gabansa ta kwantar da kanta a cinyarsa sannan ta sanya hannuwanta ta zagaye shi.

"Har ka fara kokonton son da nake maka?"

"I ....I am sorry." Ya shafa fuskarta "na fiye rashin haƙuri ko?"

"No, ni ce dai na fiye tsoro. I just don't want to take any chances."

"Ke ce likitan, dole nayi biyayya. Allah Ya kai damo ga harawa dai kawai."

Dariya tayi "In ce amin kuwa? Wannan addu'a kamar ana yi min tanadin cin zali."

"Meye wani cin zali? Ai kawai ki ce addu'ar mugunta nayi miki."

"Ni dai ban ce ba"

"Ni na ce"

Sun ɗauki lokaci suna zolayar juna da nunawa juna soyayya kafin yunwa ta hana su sukuni. Ya tashi zai je falo ɗauko mu su nasu abincin Mubina ta ce ya yi haƙuri domin kuwa bai kamata ya je inda ƙannensa su ke ba a wannan lokacin.

"Kema dai kin fiye assumptions. Ina gidan ai babu abin da zai faru."

Mubina ta ce "do you want to bet?"

"Happy fa ba kunya gare shi ba. Na haƙura." Ya koma ya zauna yana yamutsa fuska.

Sai da Mubina ta gama yi masa dariya sannan ta tuna masa da za su iya kiran su a waya. Taj ɗan duniya sai cewa yayi wai Kamal ya so yiwa Mubina horon yunwa ne, if not me ya hana shi fitowa?

"Mu da har muna tunanin rufo muku ƙofa on our way out."

"Ni ne fa Happy, na san ka farin sani. Mayar da maganar kaina kake son yi?"

Mubina da Hamdi dariya su ka dinga yi musu kawai.

***

Sati biyu ya rage bikin Zee wanda aka sanya wata shida bayan komawar su Abba Habibu Saudiyya. Sajida a lokacin watanta guda da haihuwar Ihsan mai sunan surukarta. Gidan Abba Habibu ya sha gyara amma ba mai yawa ba tunda yanzu babu mai zama.

A zuwan su na farko Abba Habibu ya nunawa Baba Maje rashin jindaɗinsa da ya tayar da maganar raba auren nasu. Aka tambayi Zee ko tana son rabuwar ta ce a'a.

Su Yaya sun nuna musu cewa zumunci yanzu aka fara in sha Allahu. Har gidan Ummi ma sun je. Babu alamun yunwa a tare da ita amma fa ba sai an faɗa ba fuskarta ta nuna bata jindaɗin rayuwar auren. Duk masifarta dole ta sanyawa zuciyarta haƙuri domin kishiyoyinta sun dama ta sun shanye. Uwargidan ma ƴar sara suka ce kafin aure. Ta biyun kuwa ƴar damfara ce ta buga misali. Da su ka shigo hannun Kofur Ɗanliti zance ya sha bamban. To ga Ummi ma ta zo hannu. Jiki magayi!

Da za su koma da Zee da Halifa aka tafi. Abba Habibu ya gayyato Ƴar Ficika da wasu cikin yaransa masu igama su ka koma tare. Nan fa sana'a ta kankama babu kama hannun yaro. Ta ƙarfin cin tuwo su ka canja akalar rayuwarsu daga ƴan daudu abin ƙyama zuwa maza masu sana'ar abinci. Sai ga Ƴar ficika ya sami mata, wata ƴar dattijuwar takari. Mata ta zage ana ta sana'a da ita maimakon yawon unguwa unguwa neman abin yi. Cikin watanni kacal rayuwarsu ta sauya gabaɗaya. Duka kuma albarkacin sadaukarwar da Yaya tayi wadda bata taɓa tunanin wani mahaluƙi zai saka mata a kai ba.

*

Dinner ta ƴan boko, ƴan gayu kuma masu kuɗi Kamal ya shiryawa Zee. Bai yarda ko sulai biyar wani ya saka masa ba. Taj ya ce zai ɗauki nauyin abinci amma yaƙi. Zama ya yi aka yi lissafi ya cake wa Happy Taj kuɗinsu. Ango Sadiq wato Baballe kuma ya sha gargaɗi da jan kunne akan ya riƙe amanar ƙanwarsa. Abin na Kamal dai harda ƴar barazana.

Yaya saka shi tayi a gaba saboda ɓarin kuɗin yayi yawa.

"Kamal don Allah ka saurarawa kanka haka nan. Wallahi domin Allah na baka ƙodar nan. Kana saka ni jin nauyinka da na su Hajiya. Ɗawainiya da kashe kuɗin ya yi yawa."

"Yaya da ke ki ka haifeni za ki ce kyautatawar da nake muku da ƙannena ta yi yawa?"

Yaya tayi shiru.

"Yaya da kin san yadda ɗan Adam yake ji idan ya hango ƙarshen rayuwarsa kuma babu hanyar gudu da baki ga wauta ta ba. Ga ciwo ga tashin hankalin sanin bani da wata mafita." Idanunsa su ka yi jawur amma bai bari ƙwalla ta zubo ba "ga kuɗi, ga dangi amma babu mai ceto. Yaya, a wannan lokacin ban dinga tuna komai ba sai ranar da kowa zai juyawa masoyinsa baya saboda tsananin tashin hankali. Duk wanda Allah bai taimaka ba a lokacin to dole ya cire rai da samun kowane irin taimako." muryarsa ta soma rawa "na hangowa kaina rayuwar barzahu da tashin hankalin da mara rabo zai riski kansa... bani da tabbacin tsallakewa. Komai ya zo gab sai Allah Ya kawo ki. Yaya babu tunanin taki makomar da ta iyalinki ki ka kwanta aka cire taki ƙodar domin na sake shan iskar duniya. Domin iyayena su share hawayensu..." ya miƙe tsaye "ban isa na biya ki ba amma kuma ba zan taɓa gajiya da yi miki hidima ba in sha Allahu. Kin isa, kin cancanta. Don Allah kada ki sake nuna rashin jindaɗin ki idan nayi wani abu."

Ƙwallarta ta goge tayi masa murmushi "idan da ni na haifeka zan karɓi duk abin da ka kawo min cikin farinciki amma duk da haka zan ce maka ka dinga yi saisa-saisa saboda kaima ka kusa zama baban wasu. Haihuwa ba a yi mata tanadin gobe ko jibi sai ta baka mamaki. Sayen pampas kaɗai ya ishe ka ka gane ba ka da wayo" ta ƙare maganar tana dariya.

"Ki yi min addu'a kawai, Allah Ya ƙara buɗa min. Tanadi kuma in sha Allahu zan kiyaye shawararki."

"Allah Ya yi maka albarka Kamal banban ɗan Jinjin"

"Abu Khadija za ki ce." Ya sunkuyar da kai yana susar ƙeya.

Tare su ka yi dariya sai ga Abba Hayatu nan.

"Agolan gidana me ka ke yi a nan ka zo ka saka min mata kuka?"

"Sirrin uwa da ɗa ne Abba."

"Nima yanzu mu ka gama namu sirrin da Taj babban ɗana."

Kamal ya ce "Sirikinka dai. Mijin ƙanwata."

Yaya da Abba Habibu dariya su ka yi. Kamal ya fita ya shiga mota su ka tafi gida da Taj da yake gidajensu babu nisa da juna. Mubina tana gida laulayi ya make ta amma ta gama shiri Hamdi kuma ciki ya tsufa sosai. Haihuwa ko yau ko gobe.

*

Kukan Hamdi na huɗu kenan yau saboda Taj ya ce ba za ta je dinner ba. Da ya shigo kallon juna su ka yi kowa ya ɗauke kai. Yana fitowa daga wanka da gangan ya leƙo falo.

"Taso ki fito min da kaya."

"Suna kan gado."

"Turare fa? Wanne zan saka?"

Ta sake kawar da kai "Na fesa a jikin kayan"

"Body spray fa?"

"Akwai akan dressing mirror." Ta san jan magana ne kawai tunda abubuwa ne da yake yiwa kansa.

Ya koma ya shirya cikin ankon su na shadda shi da su Kamal. A gabanta ya tsaya ya cika mata hanci da ƙamshi mai daɗi.

"Menene ne kuma?" Ta ce da muryar kuka.

"My goodbye kiss."

Da kumburarrun idanunta ta harare shi "na ajiye a ƙofar gida."

"Wannan kuma ba ki isa ba. Ki min kawai na tafi."

"You are looking for my trouble." Ta tura baki tana jan hanci.

"Yep."

"Wai me nayi maka ne?"

"Kin kasa kallona saboda kina fushi ki ce nayi kyau."

Satar kallonsa tayi ta ce "kayi kyau."

"Ko ke fa. To tashi ki shirya mu tafi."

Maganar a bazata ta shiga kunnuwanta. Ta tashi da ƙarfinta ta rungumo shi tana dariya.

"Da gaske kake?"

"Idan naƙuda ta taho ki tabbatar kin riƙeta tunda rigima ta sa ba ki son zama a gida."

Da dariya Hamdi ta ce "ni fa ba bikin ne ya dame ni ba. Ƴan matan da za su ji ka burgesu nake son na hana samun dama. Ka sanni da kishi."

Taj ya tuntsire da dariya. Ya zauna ya ce mata nan da minti shabiyar idan bata fito ba zai tafi. Da sauri ta dinga komai. Ta fito a minti ashirin da biyu. Taj yana zaune yana waya. Hannunta ya riƙe su ka fita daga gidan tare.

* Biki yayi biki domin ya sami halartar mutane da dama cikin ƴan uwa da abokan arziƙi. Ƴan uwan Yaya da ƴaƴansu sun zo daga Batsari tare da Inna Luba. Ya'u ya zama na hannun daman Yaya Kubra domin har ta mayar da shi makaranta. Amma da su Anisa harda Hajjo su ma sun zo. Ƴar ficika da matarsa ba a barsu a baya ba. Haka dangin Alh. Hayatu da na matansa na kurkusa duk sun zo.

Ahmad ya taho da Zahra sannan ya ce Salwa lallai sai ta zo saboda shi bai ga amfanin ƙauracewa mutane ba. Idan ana haɗuwa ko yaya yau da gobe za a iya yafe mata.

To ashe Ummi ma da kishiyoyinta harda maigidan Kofar Ɗanliti su ma sun taho. Hamdi ta tako da ƙyar take ɗaga ƙafa taji kamar da mutane a gefenta. Ta juya hagu ta haɗa ido da Salwa gayauna. A ɓangaren dama kuma Ummi yangaura. Kowacce ta lalace ta fita hayyacinta. Su ukun suna yiwa juna kallon kallo su ka tsinkayi muryar Taj daga bakin ƙofar hall ɗin.

"Ke da na ce ki jira ni a mota in fara sama miki wurin zama? Na zo na ɗauke ki?"

Salwa da Ummi su ka bi shi da kallo. Ya fi Taj ɗin da su ka sani cika, kyau da ɗaukar ido. Aure ya karɓe shi kamar yadda ya karɓi matarsa. Ko me su ka ji a ransu ba su furta ba.

"Ka zo ka tayani tafiya dai."

Taho wa ya yi Hamdi ta saƙale hannu a waist ɗinsa saboda support su ka dinga takawa tare har su ka ɓacewa ganinsu. Sai su ka sake kallon juna, kowacce ta buga tsaki. Za su fara cacar baki sai Ummi ta kula Alh. Usaini yana tahowa. Yadda Salwa ta fige shi har ya fi ta. Wata muguwar dariya ce ta suɓuce mata bata sani ba. Kamar daga sama taji muryar Kofur.

"Ummi ban hana ki dariya irin wannan ba?" A gefensa hagu da dama kishiyoyinta ne.

"Wai, sannu fa." Salwa ta ce sannan ta rama dariyar da tayi mata.

*

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull