Rayuwa da gibi complete na batul mamman - Chapter 43
Rayuwa da gibi complete na batul mamman Chapter 43: Rayuwa da gibi complete na batul mamman Chapter 43. A falon gidan Abba Habibu, shi ne da Alh. Hayatu su…
523 words
A falon gidan Abba Habibu, shi ne da Alh. Hayatu su ke hira irin tasu ta manya. Hirar yawanci ta iyalansu ce da abubuwan da su ka shafi rayuwar yau da gobe.
Can dai Alh. Hayatu ya ce "ni kuwa Habibu akwai abin da nake sha'awar ci amma na kasa faɗawa iyalina tunda ban saba ba."
"To ya aka yi ka san kana so tunda baka ci?"
"Ka san jikoki akwai kyauta. A baki aka zo aka bani rannan da aka yi. Si ka tayar min da kwaɗayi amma ban isa na nemi ƙari ba kada na zama abin surutu a gidan."
Abba Habibu ya miƙe yana dariya "ban yi ritaya ba har yanzu. Ya sunan sa in dafa maka?"
"Wainar fulawa" Alh. Hayatu ya faɗa yana wani basarwa don kada Abba Habibu yayi masa dariya. Bai tsira ba kuwa don sai da ya yi masa dariyar sannan ya shiga kitchen.
Bayan minti talatin Alh. Hayatu ya ɗora babbar rigarsa a saman kujera wai kada ta ɓaci da manja. Ya zauna a kan kafet yana cin wainar fulawa yana jindaɗi sai ga wayar Kamal sun wai wuce asibiti da Hamdi shi da Mubina da Taj. Iyayensu sun biyo bayansu.
Ya kalli plate ɗin ko rabi bai ci ba kamar kada ya tashi don wannan tafi wadda aka yi a gidansa daɗi. Sai da ya ƙara loma guda sannan ya tashi su ka tafi asibitin. Suna shiga Mubina na fito musu da jariri.
Abba Habibu ya ce a miƙawa Alh. Hayatu. Yana karɓa sai cewa ya yi "wainar"
Abba Habibu ya yi saurin cewa "Wai ina wa?"
"Wai ina maigidan nata?" Alh. Ya wayance.
"Gamu nan fa Alhaji."
Ya juya ashe sun wuce kowa a wurin bai sani ba. Farin kaya mai tonon silili Inna ce ta fara cewa
"Mene ne wannan a gaban rigarka Alhaji?"
"Ina babbar rigarsa za ki ce" in ji Mama.
Hajiya ta ce "Ƙamshin manja nake ji kamar wainar fulawa."
Alh. Hayatu da Abba Habibu su ka soma kame kame duka wajen ya kaure da dariya.
Basu bar asibitin ba sai da aka fito da Hamdi kowa ya ganta lafiya. Alh. Hayatu ya miƙa mata jaririn da amarya Zee ta ƙanƙame bayan iyaye sun gama saka masa albarka. Ya miƙawa Hamdi bayan ta zauna akan gado.
" Hamdi ga Habib Tajuddeen Hayatu. Allah Ya raya shi bisa sunnar Ma'aiki SAW. Allah Ya sa ya yi koyi da kyawawan halayen mai sunansa."
"AMIN" kowa ya amsa da farinciki.
Abba Habibu da bai taɓa zaton wannan karamcin ba ya rasa me zai ce sai kawai ya dinga murmushi yana godiya ga Allah da Ya nufe shi da ganin wannan rana.
Alhamdulillah bata gushe daga bakinsa ba har ya kwanta yana tunanin rayuwar duniya mara tabbas. Ace har ya yi ƙimar da za a yi masa takwara?
"Allah na gode Maka. Ya Rabbi Ka ƙara shiriya da albarka ga iyalanmu da mu kan mu. Ka raba mu da bin hanyar taɓewa. Ka dawo da ɓatattun cikin mu hanya madaidaiciya. Amin"
HAMDAN KATHIRAN ƊAYYIBAN MUBARAKAN FIHI. Ya Allah Ka yafe min kurakuran da su ke ciki. Ka sa mu amfana da darrusan. AMIN