Kenza eBookz

Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 18

Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 18

Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 18: Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 18. Bari ya yi sai da Kamal ya bar gidan Ahmad sannan ya fice. Ya kusa…

3,318 words

Bari ya yi sai da Kamal ya bar gidan Ahmad sannan ya fice. Ya kusa isa gidan Yaya Babba sai kawai ya canja shawara. Taɓo mai adaidaita sahun ya yi.

"Don Allah ka yi haƙuri. Kantin Kwari zani."

"Malam lissafin kuɗinka fa zai canja."

Taj ya zura hannu a aljihu ya zaro dubu uku sabbi fil ya bashi.

"Ko akwai ciko?"

Mai adaidaita ya saki murmushin da ya koma dariya.

"Yallaɓai sai dai idan kuma sadaka za ka ƙara min akan wannan."

Taj dake neman taimakon Allah sai ya ƙara masa dubu biyu.

"Idan mun je in jira ka ne Yallaɓai?

"Da ka kyauta. Inda ka đauko ni zan koma."

*

Alh. Hayatu na zaune a cikin ofishinsa dake hawa na biyu a katafaren ginin store ɗinsa mai suna Maitakalmi Enterprises dake kantin Kwari yaji ana ƙwanƙwasawa tare da sallama lokaci guda.

Muryar wani yaron shagon ce wanda ya kasance ɗa a wajen wata da su ke ƴan maza zar da ita.

"Kawu dama..."

"Matsa na shiga" Taj ya ce da ɗan saurayin.

Da sauri ya yi gefe, yayin da Alhaji ya tashi tsaye saboda gane muryar da ya yi.

"Me ya kawo ka?" Ya ce da kakkausar murya.

Yaron da ya nuna masa office ɗin don bai taɓa zuwa ba tunda aka yi ginin sai yau ya kalla. Cikin sauri ya rufe ƙofar ya bar wajen. Taj ya juyo ya kalli mahaifinsa sai kawai ya sauke gwiwoyinsa duka biyu a ƙasa.

"Alhaji na zo neman izini da amincewarka ne." Ya faɗi yana kallon uban.

"Dama nayi wannan isar a rayuwarka ne?"

Zuciyarsa dokawa take da ƙarfi saboda fargaba. Amma ya san cewa indai ya rasa goyon bayan Alhaji, ba zai taɓa auren wadda yake so ba.

"Ka fi ƙarfin komai a rayuwata."

"Shi yasa ka zaɓi barina akan ka ajiye burinka?"

Taj ya girgiza kai "baka bani zaɓi ba a lokacin da ka koreni Alhaji. Hukunci kawai ka yankewa kuskurena."

Zuciyarsa hasala tayi. Ɗan nasa ya fishi gaskiya. Wannan ne ya ɓata masa rai.

"Rashin kunya ka zo ka yi min?"

"Ban isa ba." Ya ɗaga kai daga durƙuson da ya yi "aure nake so ka yi min gobe don Allah."

"Ka fara shan ƙwaya ne Tajuddin? Ni za ka tunkara da wasan kwaikwayo irin wannan?"

"Ƴar wajen Habib Umar ce. Simagade na Soron ɗinki."

Yana gama magana ya rufe idanuwansa saboda jiran saukar mari daga Alhaji. Da yaji shiru na wasu daƙiƙu sai ya buɗe idanunsa. Abu na farko da Alhaji ya fara ce masa shi ne,

"Me ka ke taƙama da shi ne Taj? Kuɗin da kayi ne kake jin ya isa ka kawo min zancen banza irin wannan?" Ya nuna ƙirjinsa "Ni? Ni za ka cewa kana son auren ɗiyar Habibu?"

"Bana taƙama da komai Alhaji sai matsayina na jininka. Ka juya min baya a karo na farko amma Allah Ya tsareni daga faɗawa rayuwar da kake guje min. Ba yin kaina bane. Ba kuma isarka bace ko tawa. Albarka ce kawai daga Allah wadda na tabbata kullum kana roƙa min."

Kallon mamaki kawai Alhaji ya dinga yi masa. Yana kuma tuno kalaman Gwaggo na ƙarshe ƙarshe a gare shi da take cewa Taj tamkar shi ne a madubi. Yadda yake haka ya haifo ɗa irinsa. Duk lokacin da yake son taƙwara ɗansa, to ya fara bari shi ma duniya ta tanƙwara shi.

"Shi yasa yanzu ma ka shirya saɓa min saboda kana jin komai zai tafi yadda kake so?"

"Wannan karon ina jin tsoron idan ka barni kada na saɓawa Allah akan soyayya..."

"Kai Taj ka kiyayeni. Ni kake faɗawa waɗannan maganganun?" Alhaji ya furta kansa na yi masa wani irin nauyi.

"Ina sonta Alhaji." Ya faɗa kai tsaye abinsa.

"Ita ƴar Habibun?"

"Eh."

"Zo ka zauna"

Don dai shi tsayuwa tana neman gagararsa. Kan kujera su ka koma. Alhaji ya daɗe yana tunani kafin ya ce da Taj,

"Ka tafi gida ka jirani."

"Gidan Yayan za ka zo?" Ya tambaye shi da wata irin murna don ya san ina yake nufi.

"Gidana nake nufi Tajuddin. Ka je can ka jirani."

Godiya ya yi ya tashi ya fita. Sanin me Alhaji zai ce sai Allah. Shi dai buƙatarsa ita ce ya sami damar yin auren da zai fidda Abba daga kunya gobe da izinin mahaifinsa. Haƙuri ya bawa mai adaidaitan ya ce inda za shi ya canja. Mutumin ko a jikinsa tunda ya caski kuɗi.

*

Mutane sun kai biyar da Alh. Hayatu ya bawa aikin yi masa duk wani binciken da ya dace akan Abba Habibu. Kafin isha'i dukkanin bayanai sun riske shi. Tun daga zamansa a Lagos bayan ya yi aure har batun auren babbar ƴarsa da za ayi gobe. A duka bayanan yafi mamakin dalilin da yasa Taj da Kamal nemo Simagade. Da kuma aikin da Taj ya bashi. Share wannan ya yi ya kira mahaifin Safwan domin kuwa ya san shi duk da ba wai abokai bane. Shi kuma yadda yake mutunta Alhajin yasa ya faɗa masa auren nan fa babu da dalilinsa. A ƙarshe yadda ya fahimta wanda kuma da ƙamshin gaskiya a ciki, auren ragewa Habibu baƙinciki Taj yake son yi.

Dariya ce ma ta kama shi. Wato ta wannan hanyar Habibu ya zaɓi ya dawo cikin rayuwarsa. Lallai zai nuna masa kuskurensa a lokacin da ya dace.

*

Gida kowa murna ganin Taj ya shigo kuma ya ce Alhaji ne ya yi masa izini. Inna harda kukan farinciki. A gidan ya yi Magriba sannan Kamal ya dawo. Yana ganinsa ya sha jinin jikinsa.

"Wace tsiyar ka ƙulla?"

"Alkhairi dai. Zancen auren Hamdi nayi masa."

A harzuƙe Kamal ya ce "ba ka da hankali ko? To wallahi yana da bindiga. Ƙarshenta ma harbeka zai yi."

Taj ya ƙyalƙyale da dariya. Kamal ba dai tsoro ba. In anyi magana kuma ya ce Taj ɗin ne matsoraci.

Wuraren tara na dare Alhaji ya dawo. Yana hawa sama ya kira Taj. Bai nuna masa ya san komai ba. A gabansa ya kira Yaya Babba ya yi masa magana.

"Ɗanka ne ya ɗauko aure bagatatan. Wasu matsaloli ne su ka taso da su ka sanya auren dole ayi gobe. Zan zo gidanka da safe kafin lokacin mu yi magana."

Yaya Babba farincikin jin Alhaji ya tsayawa Taj bai bashi damar zurfafa tambayoyi ba.

"Kana iya komawa gidan yayan naka. In sha Allahu gobe za a ɗaura."

Godiya mara adadi Taj ya yi masa.

"Ba sai ka faɗawa matana na ba domin ko Abu ba za ta baka goyon baya ba. Zan yi musu magana da kaina."

Duk da cewa a zuciyarsa yana jin kamar shigo shigo ba zurfi Alhaji yake masa, sanin cewa baya magana biyu yasa bai ji ko ɗar ba. Ya tabbata za ayi auren in sha Allah.

***

Gidan Abba Habibu tamkar ba shi bane jiya da yamma ake ta hayaniyar shirin zuwa sisters' eve. Yau shiru kamar babu mutane. Gashi dai ba a yi shelar me ya faru ba. Amma ganin ƴan biki babu walwala sai kowa ya sha jinin jikinsa.

Banda ƴan mazan gidan Alhaji babu wanda ya san da maganar ɗaurin auren sai ƴan uwansa maza. Su duka mamaki bai hanasu haɗuwa a masallacin juma'ar da za ayi auren bayan an idar da sallah ba. Kamal ne ya bawa Taj sababbin kayansa masu babbar riga. Ya tuƙosu a mota zuwa masallacin. Sai dai jikinsa tamkar anyi masa duka. Gani yake akwai abin da zai biyo bayan wannan ɗanyan kai na Taj. Alhaji ba zai barshi ya sha ba.

Ana idar da sallah Liman ya yi sanarwar ɗaurin aure kamar yadda aka faɗa masa. An fara da Abubakar Maje Garba (Baballe) da Zeenatu Habib Umar akan sadaki naira dubu hamsin. Masallaci ya đauki kabbara.

Abba yana share ƴar ƙwallar farinciki sai yaji an taɓo shi. Yana juyawa damansa ya yi tozali da Alh. Hayatu. Ba ƙaramin ruɗewa ya yi ba kuwa.

"Kwantar da hankalinka. Sunan yarinyar wajenka da Taj yake so za ka bani. Ina fata ka yi masa izinin aurenta."

Abba baki ba rawa ya ce "Yaya Hayatu..."

"Kada ka damu. Nima short nktice da ya bamu ne ya hanani zuwa mu yi maganar. Ya sunanta."

"Hamdiyya."

Alhaji ya juya fuskarsa ba yabo ba fallasa ya faɗawa Yaya Babba. Shi kuma ya sanar da Liman. Nan aka sake sanarwa. An ɗaura auren Tajuddin Hayatu Sulaiman da Hamdiyya Habib Umar akan sadaki dubu ɗari biyu.

A karo na uku sai ga wani tsoho an gunguro shi akan wheelchair. Ba kowa ne ya turo shi ba kuwa illa Safwan. A gaban Abba ya tsayar da kujerar. Ya ɗuka a kunyace. Tsohon ya dubi Abba da murmushi a fuskarsa.

"Ni ne mahaifin Sabi'u. Kuma ni zan yiwa jikana waliyyi. Ina fata za ka haƙura da abin da ya faru jiya wanda bani da masaniya. Sai ɗazu yake cewa wai an fasa. Shi ne na kira Safwan ɗin ya yi min bayani."

Baba Maje ne akan gaba wurin cewa sun amince. Nan take Liman ya ɗaura aure na uku. Safwan Sabi'u Mamman da Sajida Habib Umar.

Allahu Akbar Abba sakaya fuska ya yi cikin babbar riga yana kukan farinciki. RAYUWA DA GIƁI 17

Batul Mamman💖

*** "Ayyyyyyiririiiiiiiii. Allah mungode maKa. Hajiya Jinjin uwargidan Habibu namu asa goshiia ƙasa a miƙa godiya ga Sarkin sarakuna. Allah Ya kwashe miki ƴan matanki a sa'a guda. Wannan farar juma'a ta amare uku ce rigis. Sai a saurari zuwan ƴan dugwi dugwi iyalan Baba."

Ba kowa bane da wannan aiki sai Ƴar Ficika daga soron gidan. Yana gama magana kuma yaransa su ka amshe guɗar su na yi. Yaya fitowa tayi daga ɗakinta inda ta fake da shiryawa ta zauna rarrashin Sajida da Zee. Hamdi na gefe ita ma tana basu baki tare da taya su kuka.

Anti Zinatu ce kaɗai ta san zaman me su ke a ɗakin. Ita ce ma ta tura musu Yayan domin wani ciwon uwa kaɗai ke iya maganinsa.

Hamdi na jin muryarsa ta haɗe rai bayan fitar Yaya daga ɗakin. "Wai namiji kenan. Mtsewww."

Lulluɓi Yaya tayi ta fita soron. Ƴar Ficika ya wangale baki.

"Sai muka ji abin arziƙi ko Jinjin? Allah Yasa abokan zamansu ne."

Ita ma takaicin ɗaga muryar tasa take yi. Ga zaƙin murya gashi bai iya tausasa harshe. Ta tabbata kowa na jinsu a ciki.

"Da ka ɗan rage maganar saboda ƴan biki ba su san auren Zee aka ɗaura ba maimakon Sajida. Sannan kana cewa amare uku sai ayi zaton..."

"Ba zato bane Jinjin. Ƴaƴan Simagade sun zama farinwata sha kallo. An so tozarta shi sai gashi Allah Ya aurar dasu lokaci ɗaya."

Yaya dai bata fahimci inda ya dosa ba. Gani take wani zancen yake haɗawa da wani. Sai kawai ta koma ciki. Aka yi ta tambayarta me yake nufi kuwa don duk sun ji.

"Shirmen Ƴar Ficika ne. Shi da ko wurin ɗaurin auren basu je ba?"

Rufe bakinta ke da wuya Halifa ya shigo gidan kamar an jeho shi daga sama. Haki yake da ƙarfinsa saboda gudun da ya sha ba na wasa bane. Tun daga masallacin juma'ar unguwarsu har gida. Tafiyar kimanin minti talatin. Ƙafafunsa sun yi buɗu buɗu.

"Yaya! Yaya!!" Ya dinga ƙwala kira kamar makaho na neman ɗan jagoransa.

"Kai Halifa lafiyarka kuwa?" Wata maƙociyarsu ta tambaye shi.

"Ina Yaya?" Ya faɗi yana dariya.

Banda Yaya, duk matan da su ke gidan fitowa su ka yi. Yana ganinta ya taho da sauri, sai kuma ya tsallaketa ya rungume Sajida.

"Wai mene ne Halifa? Ka sanya mu a duhu" cewar Inna Luba.

Murmushi ya yi yana duban ƴan uwansa.

"Yaya an ɗaura. Duka su ukun an ɗaura musu aure."

Dafa shi Inna Luba tayi zuciyarta na bugawa. "Nutsu ka yi min bayani. Su waye su ka yi auren?"

"Ya Sajida da Yaya Safwan."

Sajida ta bar jikin bangon da ta jingina tayi da sauri, ta rufe bakinta da hannu. Wasu zafafan hawaye suna sauko mata. Hamdi ta rungumeta tana cewa "Alhamdulillah."

Anti Zinatu ta ce "Mata biyu aka aura masa kenan? Naji ka ci mutum uku."

Ya murmusa da farincikinsa "a'a, sai Ya Hamdi da Happy."

Inna Luba ta ware idanu a tsorace "Hafi? Mutum ne?"

Yadda yake murna kai ka ce shi ne angon mata uku. Gyarawa ya yi yadda za ta gane da kyau. "Ya Taj. Shugaban inda Abba yake aiki yanzu."

Cikin Hamdi wata irin ƙullewa ya yi. Taji ya saki lokaci guda yana neman tsinkata a gaban mutane. Duk da haka danne shi tayi da hannu biyu.

"Kai ka san bana son wasa irin wannan. Wace Hamdin kake nufi?"

"Wallahi ke ce Ya Hamdi. Babansa kawai muka gani ya cewa Abba yana nemawa ɗansa aurenki. Sadakinki fa dubu ɗari biyu. Cash in faɗa miki."

Daga inda ya yi rantsuwar ita Hamdin ta daina jin komai sai bugun zuciyarta. Wannan wane irin mugun wasa ne Halifa yake yi mata haka? Aure? Ita ce tayi aure kamar wata kayan wasa? Kuma wai da Taj. Waye ma Taj? Kamar ta san sunan.

Sama-sama taji muryar da ko gane mai ita ba yi ba tana cewa "Ku riƙeta...Sajida kama hannun. A'a rungumota kawai kada ta kai ƙasa."

Luuu haka taji ƙafafunta suna narkewa su kaɗai za su kaita ƙasa. Kafin ta gama faɗuwa aka tallafota zuwa falo. Akan doguwar kujera aka kwantar da ita. Ana yi mata fifita. Daga nan ba za ta iya tuna me ya faru ba.

***

Ƴan uwa da abokan arziƙi dafifi su ka yi wajen taya Abba murna a masallacin. Yadda al'amura su ka kasance maƙiyi ne kaɗai zai ce bai jidaɗi ba.

Baba Maje baki har kunne shi da Baballe. Murna yake yi, ya sami damar kyautatawa amininsa bayan abin da Ummi tayi. Don tun daga lokacin shi da Iyaa su ka ja baya da iyalin Abba. Suna masu jin kunyar abin da ƴarsu tayi. Duk rashin son fita sai ya zamana Yaya ce mai ƙoƙarin zuwa. A yawan ziyarar da take kai musu ne Baballe yaga Zee ya ƙyasa. Ashe rabonsa ce bai sani ba.

A ɓangaren Taj kuma inda mahaifinsa yake ya zauna tare da ƴan uwansa. Kawunnai ne na ɓangaren Alhaji shi kaɗai sai ƴan uwansa su Ahmad. Yadda ya hana Taj faɗawa su Inna tun jiya, haka ya tsallake ƴan uwansu maza da dukkanin abokansa.

Mutane na ragowa ya tashi da sauri ya fita. Ƙaninsa Baba Amadu ya tare shi ganin sun nufi wurin motocinsu.

"Haba Yaya Hayatu. Ba za mu tsaya mu gaisa da baban amaryar ba za mu tafi?"

"Baka gane shi bane? Habibu ne fa. Meye abin gaisawa a nan?" Ya amsa a wulaƙance

Daga nan gaban Taj ya faɗi. Su ka haɗa ido da Kamal kowannensu da tunanin da yake ransa. Yaya Babba kuwa haɗe rai ya yi.

"Da alama akwai manufar da ta sanyaka amincewa auren nan bagatatan. Dama nayi mamaki da ka sanar dani jiya a ƙurarren lokaci. To amma saboda Taj ne shiyasa na zo don kada sai an zo ɗaurawa ka ce ka fasa don kawai ka muzanta shi."

Alhaji ya yi murmushi "bani da wata manufa. Auren fitar da ubangidansa a daudanci daga kunyar al'umma yake son yi kuma nayi masa don kada ma a sami bakin zagina."

Kallon tsananin mamaki Taj ya bi shi da shi. Bakinsa ya mutu. Tun ba a je ko'ina ba ya gane shigo-shigo ba zurfi Alhaji ya yi masa.

"Alhaji don Allah ka tsaya" Ahmad ya roƙe shi don baya jindaɗin ganin manya su na sa'in'sa.

"Kaima ban maka izini tsayuwar ba. Yanzu ku sai ku yi musabaha da mutum irin wannan?" Ya nuno Abba da yake tahowa inda suke da ƴan abokansa.

Abin ban sha'awa babu ɗan daudu ko ɗaya. Dama su Ƴar Ficika ne. Shi kuma tunda a gabansa mahaifin Safwan ya ci mutumcin Abban sai ya ce shi da yaransa ba za su ɗaurin auren ba don kada a sake samun matsala.

Bawan Allah bai san wainar da ake toyawa ba. Da ya iso hannu ya miƙawa Yaya Babba gami da rissinawa sosai cikin girmamawa. Har sai da Taj yaji wani iri.

"Yaya barka da rana?"

Fuskarsa shi ma a sake ya ce "Sannu Habibu. Shekaru da yawa. Gashi mun zama surukai."

Abba ya murmusa "ina ni ina surukuta da ku Yaya? Ƴa taku ce. Sai dai ace ta bar gida ta sake komawa gida."

Ragowar ƴan uwan Alhaji su ka ƙarbi musabaharsa saboda Yaya Babba ya buɗe musu hanya. Ransa fari ƙal ya sake rissinawa ya miƙa hannu ga Alhaji.

"Yaya Hayatu ..."

Kallon da Alhaji ya yiwa hannun yafi ƙarfin a kira shi na wulaƙanci. Sai dai a ce ƙasƙanci. Domin ba ma da duka ƙwayar idon ya kalle shi ba. Duniya bai ga abin da zai sa ya kama wannan hannun da ya gama lalacewa da bleaching ba. Knuckles ɗin (gaɓoɓin yatsu) duka baƙaƙe ƙirin. Ragowar hannun kuma fari da ɗigo ɗigon baƙi.

Yawu mai ɗaci Taj ya haɗiya ganin Abba ya shanye abin da aka yi masa tamkar babu komai. Hannun kawai ya mayar ya ƙara duƙawa.

"Barka da rana."

"Kaga tashi don Allah. Bana son wannan ɗabi'ar taku ta gaisuwa kamar maroƙa."

"Alhaji" Taj ya kira sunansa da ɗan ƙarfi ba tare da tunanin komai ba sama da son ya tunatar da shi me yake aikatawa a gaban mutane.

Ko kallonsa Alhaji bai yi ba. Yaya Babba ne ma ya yi masa alama da ya yi shiru kawai.

Ba tare da nuna ɓacin rai ba Abba ya miƙe yana murmushi. Zuciyar Taj ta kasa jurar ganin wannan abu. Barin wurin ya so yi. Hannun Kamal a jikin babbar rigarsa ya hana shi motsawa.

Alhaji ya ce "Ina son ganinka yau bayan Isha'i. Ai ka san gidana ko?"

"Gaskiya ban sani ba. Amma ko Taj sai na biyo in sha Allahu."

Alhaji ya yi irin murmushin nan na ɓacin rai. Yana magana ciki ciki "na manta yanzu kai ne uban. To kada ku wuce Isha dai." Ya kalli Taj "kai kuma kada ka manta dokar gidana a kanka. Da ishan ma don ni na kiraka ne."

Mota ya faɗa abinsa direba ya ja. Abba ya sake yin murmushi yana ɗagawa motar hannu tare da faɗin "Allah Ya kiyaye hanya."

Hannun nasa Taj ya sauke masa ya nuna masa Baba Maje "Abba kaje ga abokinka can ina jin kai yake nema."

Sai da ya tafi ƴan uwan Alhaji su ka soma bashi baki. Baki ma kasa motsawa ya yi saboda ɓacin rai. Ya dai dinga gyaɗa kai kawai. Yaya Babba ne ƙarshen yi masa magana.

"Ina so ka sani cewa a musulunci iyaye suna da babbar daraja. Bana so abin da Hayatu yake yi maka ya zama sanadin da za ka mayar da martani. Domin idan kayi haka lallai kayi asara. Baka jidaɗinsa ba a duniya kuma a lahira ma ba za ka sami rangwame ba."

Godiya sosai ya yiwa Yaya Babban sannan su ka tafi.

Ahmad na ganin babu sauran manyan ya ce masa "mu tafi gida mu san yadda za mu yi da matan gidan. Na san dukkaninmu ba za ta yi mana kyau ba. Ace kayi aure babu wadda ta sani."

Kafin yanzu da wannan tunanin Taj ya kwana. Amma ƙullin da Alhaji ya soma yi masa ya sa ya daina damuwa.

"Baka ji yana yi min tuni akan kada na shigar masa gida ba?"

"Ni kuma a ganina wannan shi ne lokacin da ya dace ka take wannan dokar ka shiga gidan. Rayukansu za su ɓaci. Sannan bana jin za su yarda su biyoka gidan Yaya. To a ina ka ke jin za ku haɗu har ka yi musu bayani na fahimta? Don ni ban hango sun amsa wayarka ba balle su saurareka" cewar Abba wani sarkin zuciyar.

Bishir ɗan salihin cikin mazan ya ce "Ɗauko sun dai ya dace ayi su haɗu a gidan Yaya ko gidan Yaya Babba."

Agogo Ahmad ya kalla. Lokaci na ƙurewa kuma ba su sami matsaya ba.

"Mu je gidana ayi shawara. Zan kira su Yaya Hajiyayye dukkaninsu yanzu a hanya. Idan ya so ko mu kaɗai ne sai mu je mu yi musu bayani."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull