Kenza eBookz

Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 19

Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 19

Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 19: Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 19. Shi dai Taj bashi da ta cewa. Motar Kamal ya shiga Abba kuma ya ja…

3,230 words

Shi dai Taj bashi da ta cewa. Motar Kamal ya shiga Abba kuma ya ja motar Ahmad su ka tafi da Bishir. A hanya Ahmad ɗin duk wata yayarsu ta kusa da ta nesa ya kira ta ya sanar da ita. Bishir aka bari da kiran sauran. Duk wadda ta sami hali ta taho gidan Ahmad. Amma banda na cikin gidansu su uku. Idan aka kirasu dole a zargi wani abu. Yadda shawara ta kaya za su haɗu su je gida wuraren biyar na yamma.

*

Kamal na tuƙi ya ɗan kall Taj "Yanzu ka fahimci me yasa nace ka bar maganar auren nan Happy? A gaban jama'a kana ganin yadda Alhaji ya tasarma wulaƙanta Abba."

Kamar bai ji shi ba sai ya yi masa tambaya. "Me yasa idan na zo da abu baya bani zaɓi Happiness? Sai dai ya bari nayi sannan ya ɗauki hukunci mai tsauri a kai."

"Saboda baka tsayawa kayi hangen me zai je ya dawo. Har cewa nayi zan auri Sajida duk don ka haƙura da gaggawar nan amma ka ƙi."

"Ko bana son Hamdi ba zan yarda ka auri Sajida ba. Yadda ya sallama ni haka zai yi maka. Sannan kuma ya ɗora laifin naka a kaina."

Kamal ya haɗe gira "akan me zai ɗora maka?"

"A dalilin kafi kowa kusanci dani mana." Taj ya bashi amsa.

Tunanin bai zo masa ba a baya sai yanzu. Tabbas da ya yi auren laifin su biyu Alhaji zai rabawa. Yana ma mamakin da ya ƙyale shi ya buɗe boutique a wurin Taj. Bai zaci zai sami goyon bayansa da wuri ba.

Taj ne ya yi magana bayan dogon shirun da su ka yi. "Happiness, ba fa zan bari ya wulaƙanta Abba ba. Ni ban ga dalilin da zai sa mu dinga kasa yiwa mai tsohon laifi uzuri ba. Hakan zai iya sawa su koma ga laifin."

Tausayinsa Kamal yake ji. Sai dai kuma yana ganin kamar harda taurin kan Taj. Da zai sauke nasa kambun ya yiwa Alhaji biyayya da tuni an jima da wuce wannan wajen.

"Na sani. Amma akwai hanyoyin samun lada da yawa sama da zaɓar wanin mahaifinka."

Idanun Taj sai da su ka yi ja kafin ya bashi amsa. "Baka ji me nace bane? Happiness, Alhaji bai taɓa bani zaɓi ba. He just pushes me away and gets angry when I comply (ingiza ni yake yi kuma ya yi fushi idan nayi yadda yake so). Auren nan ina faɗa bai wani ja ba ya amince min. In baka manta ba certificate kawai naje na nunawa Yaya Babba shi kenan ya koreni. Da cewa ya yi in zaɓi girki ko zaman gidansa kaima ka san ba zan taɓa barinku ba. Ba don Amma..."

Zaro idanu ya yi waje ya shiga karanto Innalillahi hankalinsa a tashe. Ya kai hannu ya damƙi hannun daman Kamal dake riƙe da sitiyari tunda yafi kusa da shi.

"Kamal...ya zan yi? Amma. Ya Rabbi." Ya faɗi cikin tashin hankali.

"Me ya same ta?" Kamal ɗin ma duk ya gama ruɗewa.

"Ya za ta ɗauki zancen nan? Ga maganar Anisa. Kada hakan ya janyo mata matsala da Daddy." Ya kuma faɗi, damuwarsa na ƙaruwa.

Har su ka ƙarasa gidan Ahmad suna jimamin yadda za su tunkari Amma da zancen nan. Kamal ya ƙara tayar masa da hankali da ya ce ya tabbata cikin kawunnansu ba za a rasa wanda zai faɗa mata ba.

"Kenan ba a bakina za ta fara ji ba? Shinenan. Na gama yawo."

Yadda ya marairaice Kamal dariya ya yi masa.

***

Falon gidan Ahmad ya cika ya tumbatsa da ƴaƴan Alh. Hayatu. Duk wadda take cikin garin Kano ta na zaune a wurin.

Yaya Zulaiha ce ƴa ta biyu a gidan. Ita ta karɓe girman daga hannun Hajiyayye don ta fi ta zafi. Ta yiwa Taj faɗa sosai.

"Don kana son taimako bai dace ka dinga yin abin da zai cigaba da ɓata masa rai ba. Mahaifi ne fa."

Haƙuri ya bata da alƙawarin zai yi ƙoƙari a nasa ɓangaren yaga al'amura sun daidaita. Ya ƙara da nanata musu cewa abin ne ya zo akan gaɓa. Yana son Hamdi tun farkon haɗuwarsu. Ya yi haka ne saboda sanin halin mata tunda cikinsu ya tashi. Idan ta kuskure musu, tsaf za a goranta mata wata rana.

Babbar yaya Hajiyayye tana jin an kashe wancan zance sai cewa tayi,

"Ya maganar lefe? Ya kamata kafin a soma zancen tariya mu haɗa wanda zai fiddo darajar gidanmu."

"Kai jama'a, Ya Hajiyayye ana ga yaƙi kina ga ƙura. Wa yake ta lefe alhalin uwayen ango basu san anyi auren ba?" Wata yayar tasu ta ce.

Duk sai su ka kama dariya. Hajiyayye dai ta fuske abinta ta ce a samo takarda tayi list. Tunda dai an riga an ɗaura auren sannan bata fatan ace saki ya biyo baya ai kuwa zancen lefe ya zama tilas. Ƴan son biki irinta su ka goya mata baya. Daɗi ya isheta domin ƙannen nata wani sa'in tamkar ƴaƴanta ta ɗaukesu.

"Sai ka tambayar min ita size ɗin takalmi da undies. In su Mama sun bamu goyon baya da wuri kaga ba sai an yi wani jinkiri ba."

"Ya Hajiyayye ki bar min sayen undies ɗin. Jibi tafiyarmu UK da Abban Farouq. Kin san na ce miki sati biyu kawai za mu yi." Wata ƙanwar tasu ta faɗi da zumuɗi.

Taj ya rasa me ya kawo wannan zance a cikin mutane haka. Kunya sosai ta kama shi don bai taɓa tunanin yin irin wannan maganar da Hamdi ba. Da su ka farga da discomfort ɗinsa kuwa su ka dinga yi masa shaƙiyanci.

***

Kamar kullum idan magana tana da mahimmanci a wajen Alhaji, ɗakinsa yake kiran matansa ya sanar dasu. A yanzu gidan nasa ya sha gyara mai kyau irin wanda ba a taɓa yi masa ba. Idan ka jima baka shigo ba sai ka kasa gane shi. Duk da cewa fasalin shi ne dai na da, amma an sabunta tsari da kaya yadda zai shiga sahun farko na kowanne maikuɗi. Saboda yanayi na girma, ya fitarwa kansa da wani ɓangaren ta baya inda ya yi sabon sashensa manne da babban falon ƙasan gidan. Saman ya barwa ƴan matan da basu yi aure ba da jikokinsa matasan mata dake yawan zuwa su kwana.

Haka kawai Inna ta dinga jin faɗuwar gaba akan wannan kiran. Jikinta ya bata ba zai wuce akan Taj ba tunda ya zo jiya. Tana son sanya ranta yayi murnar ƙila an shirya tsakanin uban da ɗansa, amma kuma duhun fuskar Alhajin ya sare mata gwiwa.

Haka su ka zazzauna har ya gama tsakurar abincinsa na rana sannan ya dube su.

"Yau bayan sallar juma'a na ɗaurawa Taj aure da ƴar gidan Habibu Simagade."

Isashshen lokaci ya basu zancen ya zauna musu. Cike da fargaba da tashin hankali su ke dubansa. Mama tayi ƙarfin halin tambayar ko wani laifi ya sake yi.

"Da farko dai yana aiki tare da Habibu saboda ya nuna min ban isa ba. Banda haka ko masu girki nawa ne a garin nan da har sai ya nemo Habibu?"

"Alhaji ina ganin ire iren matakan da kake ɗaukarwa Taj ba za su samar da biyan buƙata ba. Shi fa ɗa komai shekarunsa indai yana da iyaye to fa yana buƙatar laluma da ja a jiki." Cewar Hajiya.

Cikin fushi da faɗa Alhaji ya ce "an ƙi a lallaɓa shi ɗin." Sannan ya faɗa musu abubuwan da ya binciko da dalilin auren.

"Yaron da yake da hankalin son fitar da wani kunya ne zai kasa gane dacewar ya kiyaye ɓacin ran mahaifinsa?"

Umma ta ce "Kayi haƙuri. In sha Allahu za mu yi masa magana."

"Bakin alƙalami ya riga ya bushe tunda an ɗaura auren."

Sai da kowacce ta gama rarrashin Alhaji akan ya yafewa Taj shi kuma yana botsarewa sannan Inna ta dube shi ido cikin ido.

"Yanzu da ka tara mu wane hukunci ka yanke masa."

Dukkaninsu sun girgiza da kalamanta da ma yanayin fitarsu. Babu wannan ladabin da kiyaye harshe da kowacce cikinsu bata isa ta ƙetare ba.

"Abu? Da ni kike?"

Ko gezau bata yi ba ta ce "Alhaji na gaji ne. Ina son sanin matsayarka ta uba kafin na sanar da kai tawa ta uwa."

Hajiya sai ta ɗan taɓata don tayi shiru. Ita kuwa ta kafe Alhaji da ido. Mamakinta ya hana shi motsin kirki. Da yaga da gaske take ne ya iya yin magana.

"Faɗa min naki hukuncin. Ai kema kin isa da shi. Wata tara ai ba kwana tara bane."

Gyara zama tayi ta hakimce abinta domin a yau Alhaji ya gama kaita maƙura.

"Tunda ka aurar dashi ni kuma in sha Allahu zan yi masa biki irin na ɗan da mahaifiyarsa take so kuma take alfahari da shi."

"Da kyau Inna Abu." Umma ta faɗi cikin farinciki tana tafa hannuwa. Da Hajiya ta kalleta ta kaɗa kai tana dariya. Yau ji take kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha.

"Biki? Yanzu ke sai ki yi bikin ɗanki ya auri ƴar ɗan daudu? Auren da baki ma san da shi ba sai yanzu?"

"Aure ka ce, halattacciyar alaƙa. Kuma da kake zancen ban san dashi ba ai ba laifinsa bane. Na yarda da tarbiyar da mu ka bawa ƴaƴanmu. Yaron nan bai taɓa yin wani abu gaba gaɗi kamar mara mafaɗi ba. Tunda har kai ne ka jagoranci ɗaurin auren na tabbata ba a hanya ka tsinci zancen ba."

"Haka ne" ya ce da wani irin disbelief. Wai yau Abu ce take kallon idanunsa tana faɗa masa maganganu irin waɗannan.

"Na kuma jima da sanin cewa duk abin da zai yi yana turo maka saƙo ya sanar da kai."

Bai yi mamakin yadda aka yi ta sani ba "Shi ya faɗa miki ko?"

"A wayarka na gani."

"Bincike kike min?" Ya ɗaga murya.

"Ni na nuna mata" Mama ta bashi amsa ita ma yau da nata ƙwarin gwiwar.

Inna ta dube shi bayan ya gama yiwa Mama nata kallon za ki gamu dani ɗin.

"Abu guda nake nema daga gareka. IZINI. Duk wani abu da ya kama na bikin nan wanda zai fitar dani ko ƴan uwana..." ta nuna su Hajiya "daga gida ina roƙon ka sahale mana. Sannan ranakun taron su ma ka barmu mu je. A gidan nan kai amarya ne kaɗai uwa bata zuwa. Amma komai tare muke yi ka sani. Ko sisi ba na nema a wajenka. Alhamdulillah ina da abin hannuna na fitar da ɗana kunya."

"Ɗanki? Wai yau Abu kin sha wani abu ne?" Alhaji ya ma kasa yi mata faɗa saboda ta shayar dashi mamakin da bai taɓa zato ba.

"Ɗana Tajuddin ba. Wanda a kansa na fara sanin daɗin zama uwa. Yaron da tsabar taurin kai irin nasa ya laƙaba min suna Inna tun da sauran ƙuruciyata." ta faɗi cikin tuna baya da tasowar zazzafar ƙwalla "a wajen yi maka biyayya da son kyautatawa na dinga danne haƙƙinsa dake wuyana. To amma daga yau in sha Allahu an gama. Ba zan bari wata aƙida mara tushe tasa ya rayu da fushin iyaye biyu har ma rayuwar tasa ta kasa albarka ba."

Tana gama magana ta tashi za ta fita don hawayen da take yi ya hanata cigaba da faɗa masa irin damuwar da ta jima tana dannewa a zuciyarta.

"Zainab."

Dakatawa tayi ta juyo su ka haɗa ido da Alhaji.

"Ban yi miki izinin fita yin duka buƙatun da ki ka nema ba. Haka ma ku" ya kalli inda su Hajiya ke zaune suna murmushin jindaɗin wannan abu.

Inna ta goge hawayenta ta kalle shi.

"Samun izinin shi ne kaɗai abin da zai sa na yafe maka rabani da ɗana da kayi sama da shekara goma alhalin ba Allah Ya saɓawa ba."

Ficewa tayi ko kallon inda yake bata sake yi ba. Umma da Mama su ka bi ta. Hajiya da ta ɗan jinkirta tashi kallonsa tayi.

"Tura ce ta kai bango Alhaji. Kuma ina mai tabbatar maka da cewa idan baka sassautawa Abu ba to wannan fito na fito ɗin yana nufin ta gaji da aurenka. Muma kuma ƙofa ta buɗe mana na daina shanye mulkin mallakar da kake mana. Ah to."

"Wai ni Gambo anya ba sauya ku aka yi ba?" Ya faɗi da gaske.

Hajiya tayi dariya "ai na faɗa maka tura ce ta kai bango. Ka bar gani na shiru shiru. Wallahi da Kamal ka yiwa abin da kake yiwa Taj da gidan nan ba zai ɗaukemu ba. Ita kanta Abu har gulmar yakana irin tata muke yi da su A'i. Akan korar Taj da kayi kuma ta cigaba da zaman gidan nan akwai yayunta biyu da su ka fita harkarta. Kafi kowa sanin tana da gata. Mace tilo cikin maza shida! Babu yadda su Alh. Lurwanu basu yi ba akan za su ɗauko Taj daga wajen Jamila taƙi. Kawai don ta faranta maka. Amma kullum sakayyar da kake yi mata ba mai daɗi bace."

Ita ma ficewarta tayi ta barshi da tulin tunani da fargaba. Ba zai yaudari kansa ba. Tsoro ya mamaye shi da abin da ya faru yanzu. Idan ya matsa matansa za su iya barinsa babu waige. Idan kuma yayi sakaci gidan zai fi ƙarfinsa. Abu ɗaya ya rage. Ya dinga cizawa yana busawa. A yau dai dole ya busa don yana cizawar Abunsa za ta ɓalle. Matar da zuciya ta kasa tsufa daga yi mata soyayya tamkar yau ya aurota. RAYUWA DA GIƁI 18

Batul Mamman💖

***

Snacks lodi guda jere akan trays Zahra da Salwa su ka dinga shiga dasu falo. Komai da zafinsa saboda yanzu aka soya. Sai sassanyan zoɓo da kunun aya sun sha ƙanƙara a cikin jugs.

"Zahra mun tayar dake tsaye ba notice ko? Da ba ki wahalar da kan ki ba. Yanzu mu ke shirin watsewa." Cewar Ya Zulaiha.

Zahra tayi murmushi "ko yaya dai ya kamata ku ci. Abinci na so ɗorawa sai Salwa ta bani shawarar sayen frozen snacks daga Happy Taj."

Zahra ta nuna Salwa ta sha mayafi "kin ganta nan tana dawowa ko zama bata yi ba ta hau suya. Da kun tafi ma sai an bi ku dashi har gida."

Kowa dariya ya yi banda Ahmad da ya maka mata harara. Sai kuma Kamal da Taj da su ka kalli juna. Kamal ya yi dariyar tsokana don ya san ran Taj bai so ba.

Ya Hajiyayye tana shan zoɓo ta ce "Mungode sosai. Sai ku fara shiri ku ma. Baƙon gidanku ya yi aure yau."

Kallon neman ba'asi Zahra ta yiwa Ahmad. Shi kuwa Salwa da ta tsaya cak yake kallo. Rawar kanta da baya so tayi yawa. Amma duk da haka sai yaji tausayinta ya tsirgs masa kafin ya iya bawa matarsa amsa.

"Taj aka ɗaurawa aure bayan sallar juma'a."

Ita ma Zahran da yake ta gama harbo jirgin Salwa sai da gabanta ya faɗi. Ta waiga gefenta da sauri amma bata ga Salwan ba.

Ashe Ahmad na ambaton auren Taj ta bar wajen a guje.

"Me ya sami Salwa?" Wajen mutum uku su ka tambaya a tare.

Zahra sai ta faɗi abin da ya fara zuwa bakinta "ai kuwa samosa ta bari akan wuta."

Da sauri tabi bayanta har ɗaki. Da shigar Salwan ta banko ƙofar da sauri ta murɗa muƙulli. Kan gado ta faɗa ta riƙe ƙirji. Kukan da take tunanin yi yaƙi zuwa. Sai ajiyar zuciya kawai da wani irin zafi a ƙirji.

"Ana wata ga wata" Zahra ta faɗi tana juyawa.

Ahmad ta gani a bayanta. Fuskar nan tasa babu salama. Tare gabansa tayi kafin ya fara buga ƙofar.

"Don Allah ka barta taji da abu ɗaya."

"Wane irin rashin aji ne wannan Zahra? Ke haka kika yi?"

Bayansa ta kalla "Rage muryarka don Allah kada a ji."

Kamar bai ji me ta ce ba ya cigaba da faɗa. "Duk ta bi ta dami kanta akan wanda bai ma san tana yi ba. Da ta san da yadda yayi wannan auren ma sai ta godewa Allah. Na riga na faɗa mata da wuya Alhaji ya yarda ɗansa ya auri ƴar Mami."

Tura shi Zahra tayi don maganganun ta tabbata za su ƙarawa Salwa zafi akan abin da take ji. Duk soyayyar da bata sami haɗin kan zuciyar da take muradi ba, abar a tausayawa ce. Lokacin da tayi ta dakon son Ahmad ta sha wuya. Allah ne Ya taimaketa ashe shima yana sonta. Ranar da ya faɗa mata sai da tayi sadaka mai kyau saboda farinciki.

Ƙanana cikin matan ne su ka wanke duk abin da su ka ɓata sannan aka gyara falon kafin su tafi. Zahra ta so su bari domin dai ƴan uwan mijin nata in baka yi bani wuri ne. Kowacce tana ji da boko da gayu. Don ko kina gama secondary aka aurar dake to fa Alhaji zai yi da wajewa da mijin. Ƴarsa dole tayi karatu kamar yadda ya yi. Aiki ko kasuwanci ko zaman gida kuma zaɓin mijin ne idan ta gama.

Yadda su ka zo haka su ka tattara su ka tafi gida domin ganawa da iyayensu. Taj kawai aka bari ya shige ɗakinsa ya kwanta. Addu'a kawai yake yi Allah Ya basu ikon yi masa uzuri kada laifinsa ya yi yawa. Zuwa Abuja already ya kama shi. Ya ma ƙudurce a ransa ba zai ɗauki wayar Amma ba ko ta kira. Gara su haɗu kawai ayi ta ido da ido.

Abin farinciki shi ne irin tarbar da iyayen su ka yiwa zancen.

"Nan da ku ka taho a ayari kun zo yi mana kwarjini ne? Alhaji ya riga ku fasa ƙwan. Har mun fara shirin biki." Umma ta faɗi tana dariya.

Kamal ya ce "Tunda baku yi fushi ba mu ai Alhamdulillah."

Kafin su watse Hajiyayye ta sake tado maganar lefe bayan iyayen sun tashi.

"Bishir kai zan bawa aikin buɗe mana sabon group a whatsapp. Sai a sake maganar a gaban waɗanda basu zo yau ba. Kada ka sako mana Taj dai kaji ko?"

Murmushi ya yi akan maganarta taƙarshe "Zan kiyaye. Yanzu mece ce shawararki yadda idan na buɗe kawai zan rubuta inda aka kwana sai kowa ya faɗi ra'ayinsa." Kowa ya yi na'am suna saurarenta.

"A nawa ganin ko sisi kada Taj ya kashe da sunan lefe. Na sani cikin gidan nan babu wanda bai mori arziƙin Taj ba tun baya gari. Mu da ƴaƴanmu kullum cikin hidima yake damu. To lokaci ya yi da za a ramawa kura aniyarta. So nake ayi lefe na kece raini amma babu kuɗin ango. Ya ji da muhalli da sauran abubuwan da su ka sauwaƙa kawai."

Abinka da gidan yawa. Amincewar tasu kaɗai sai da ta kawo amsa kuwwa a falon. Wai a haka ma don mata sun fi yawa. Sun tsayar da shawarar yadda Bishir zai tsara jawabin. Sai kuma a bawa kowa damar faɗin me zai kawo daidai ƙarfi.

Wasu don zumuɗi tun kafin a tashi su ka fara faɗin nasu. Haɗin kansu gwanin ban sha'awa. Ɗakin Mama yafi kusa da inda suke zaune saboda haka taji duk abin da su ke cewa. A zuciyarta ta raya lallai wannan zaman lafiya da ƙullewar zumunci tsakanin matan gida da ƴaƴa shi ne mafi girman arziƙin Alhaji. Ba don haka ba da tuni gidan yafi ƙarfin duk wani zafin rai da tsare girarsa.

***

Yawan mutane ƴan Allah Ya sanya alkhairi a gidan ya mantar da Abba damuwar da ya tsinci kansa ɗazu a dalilin Alhaji. Murna ake taya shi da zuciya ɗaya. Cikin hikima ta Allah ya aurar da duka ƴaƴansa ba tare da tsumi ko dabararsa ba.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull