Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 29
Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 29: Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 29. "A nan matsalar take. Ya ce min shi kaɗai ne mai rhesus negative…
3,339 words
"A nan matsalar take. Ya ce min shi kaɗai ne mai rhesus negative blood group a gidan. Dalilin da yasa yaƙi sanar da kowa kenan."
"Wannan ai ba dalili bane. Ya ma aka yi shi kaɗai yake da negative? Wane blood group ne?"
Yaya Kubra tayi maganar cikin hawayen da bata san ya sauko ba. Ita da ta zo da niyyar jin ko kidney stone ko wani infection. Bata zata abin ya kai haka ba. Kamal, Happiness ɗinsu da ciwon ƙoda wadda take gab da daina aiki gabaɗaya.
Kukan da ita Mubina tayi a lokacin da ta hanga taga kamar mafita ta ƙarewa masoyinta, shi yayarsa take yi.
Abin da yake faruwa babba ne. Ƙoda ba abar sayarwa bace. Sannan ko a cikin gidan su mutum ba fa kowa ne zai iya yarda a cire tasa a bawa wani ba. Duk da tana da yaƙinin da wuya aje da maganar gida ba a sami kaso fiye da saba'in a shirye da su bayar ba. A ina za su sami ƙoda? A dangi?...abin da kamar wuya. Sannan zancen cigiya ma bai taso ba. Hukumomin tsaro da na lafiya basu yarda wani ya saka kuɗi ya sayi wani ɓangare na jiki ba. Faruwar haka zai sa mutane su dinga sayar da organs ɗinsu da zarar sun shiga matsala da ma abubuwa daban daban marasa daɗi da za su iya biyo baya.
"Ki kwantar da hankalinki mu yi magana doctor."
A gigice Yaya Kubra ta ce "ta ina hankalina zai kwanta? Iyayenmu duka na tabbata jininsu positive ne. A ina ya sami negative don Allah?"
Bayanin wannan ruɗani Mubina tayi mata kamar ba likita ba don hankalinta na neman gushewa. Da gaske likitoci kamar kowa in lalura ta waji nasu ce su ma ba sa ji, basa gani. Group ɗin jini daban kamar yadda ta sani guda huɗu. A, B, AB da O. Sannan yana ɗauke da wani sinadari da ake kira rhesus. Idan akwai sai wannan blood group ɗin ya zama positive (+), idan kuma babu sai ace negative (-). Abin mamakin shi ne da group ɗin jinin da rhesus ɗin duka a wajen iyaye ake gada. Uwa za ta iya zama A+, uba kuma O-, sai su haifi ɗa O+. Ya gaji group a wajen uba, rhesus a wajen uwa. Wannan shi ne normal. To a case ɗin Kamal an wayi gari shi kaɗai ne yake ɗauke da jini rhesus negative. Wannan yana nufin ɗaya daga cikin iyayensa yana ɗauke da alamun rhesus negative ɗin a ɓoye. Tunda kowanne abu na jikin ɗan Adam ana samu daga uwa da uba a tare, wanda yafi ƙarfi ya nuna kansa (domimant gene). Ɗayan kuma ya zama a ɓoye (recessive gene). To wannan ɓoyayyen zai iya bayyana a jikin ƴaƴan da za su haifa a matsayin mai ƙarfi. A taƙaice dai ɗaya daga cikin iyayen Alhaji ko Hajiya suna ɗauke da rhesus negative gene. (Batul ba likita bace. Wannan bayani na samu shi ne bisa bincike da nayi. Idan yaci ƙaro da ƙa'idar likitanci don Allah ayi min uzuri. Littafin fiction ne dama.)
"Allah Sarki Kamal. Nagode Doctor. In sha Allah zan yi cigiya a family ɗin Hajiya. Don da ace daga ɓangaren Alhaji ne tabbas Kamal ba zai kasance shi kaɗai ne mai wannan blood group ɗin ba."
"Cigiya kuma? Doctor Kubra please ki duba abin a matsayin likita. Anya ya kamata ki fara bin dangi kina neman mai bashi ƙoda?"
"Zuba ido zan yi ciwo ya cinye shi? Me yasa ki ka faɗa min in ba don haka ba?"
"Saboda mu nemi mafita amma ba da garaje ba. Cigiya zata iya zama laifi a shari'ance. Musamman idan mai bayarwar ya nemi a biya shi."
Duk ta inda Yaya Kubra ta ɓullo sai Mubina tayi mata nuni da illar hakan. Iyayensa ya kamata su sani. Shi kuma Kamal yaƙi amincewa saboda a ganinsa tayar musu da hankali zai yi. Ga ciwo, ga kuɗi amma babu mai iya taimakawa. Damuwar da za su shiga sai ta ninka ciwon nasa.
"Da na sani Taj na faɗawa." Mubina ta ce da taga Yaya Kubra ta manta da dokokin aikin nasu. Yadda zai sami lafiya kawai take nema.
"Rufa mana asiri. Gara kowa yaji akan Taj. Ina miki rantsuwa da sai yafi Kamal jinya. Those two are like one soul in two bodies."
Da ƙyar Mubina ta sami kan Yaya Kubra. Sun tsayar da magana akan cewa za ta zo ranar next appointnent ɗinsa. Daga nan sai su san abin yi kuma.
***
Yadda Mami ta so ko ana muzuru ana shaho haka Alh. Mukhtar maigidanta kuma uba ga Salwa yake yi. Ta zauna ta kalallame shi da ƙarya da gaskiya aka son da Salwa take yiwa Taj.
"Mu ne da alhakin sama mata farincikinta. Idan ba haka ba Allah muna gab da rasata."
"Ni uban mace ki ke so in kira tsohon mijinki in roƙi ya sa ɗansa auren ƴata? Da hankalina fa."
Ɗaure fuska tayi "to sai ka barta ciwon so ya kasheta ai."
"Ki gaggauta kiranta ta dawo gida kafin ranta ya ɓaci wallahi." Har wani haki yake don ɓacin rai. Rainin hankalin Mami ya yi yawa.
Juyawa ya yi zai fita tayi saurin jefa layarta ta biyan buƙata a baki ta tauna. Kamar an tsayar da ƙafafunsa ya tsaya cak.
"Nace ka kira Alh. Hayatu ka san yadda za ka yi dashi ya amince a aurawa ɗansa Taj Salwa." Ta faɗi da izza.
"To. Yanzu ko yaushe?"
"Zauna ka kira yanzu."
Zaman ya yi ya ɗauko waya. Ta miƙa masa wayarta mai ɗauke da numbar Alh. Hayatu ya kwafa ya yi dialing.
"Assalamu alaikum"
Ta jiyo muryar tsohon masoyinta abin begenta har yau. Sake tauna layar tayi ta zarewa Alh. Mukhtar idanu. Jiki na rawa ya amsa sallamar tare da gabatar da kansa. RAYUWA DA GIƁI 24
Batul Mamman💖
Lallai Alh. Mukhtar ɗinnan ya gamu da sharrin Mami shi ne abin da Alhaji ya fara rayawa a ransa bayan sun gama waya. Yadda ya dinga koro bayani akan irin son da ƴarsa take yiwa Taj da fatan amincewar Alhajin don ayi aurensu kai ka san kan ba ƙalau ba. Shi dai yana son ƴaƴansa, amma fa yana ganin babu ƴar da ta isa ta saka shi zubar da mutumci haka a gaban tsohon mijin matarsa. Irin waɗannan abubuwan ya fara gani da burinta na fin kowacce mace matsayi ta kowacce hanya yasa shi sakinta. Yana da labarin yadda matan Alh. Mukhtar biyu su ka fita bayan an aurota. Kuma duk wadda ya ƙaro bata jimawa za ta yi waje ita ma.
Zama ya gyara da ya tuna yadda ya ce masa ya amince kai tsaye. Fakewa zai yi da guzuma ya harbi karsana. Ya san a taurin kai irin na Taj akan ya auri Salwa ya faranta masa gara ya saki Hamdi. Ana yin sakin da kansa zai ce masa ya janye batun auren. Duk da a iya saninsa Salwa yarinya ce mai saukin hali. Babu mamaki sirrin zuciyarta ta sanar da Mamin ita kuma tayi amfani da raunin ƴar ta ɗorata akan hanya mara ɓullewa irin wannan. Tsigar jikinsa har wanu tashi tayi da ya yi addu'ar Allah Ya tsare shi surukuta da Mami da lusarin mijinta kamar yadda ya laƙaba masa suna.
Bai ga alamun Habibu Simagade zai iya wani kataɓus wurin raba yaran ba. Yanzu da ya sami dama shine zai yi amfani da ita. Ɗansa yake muradi ya dawo gida. Amma ba tare da iri ko jinin ɗan daudu a tare dashi ba. Saboda rashin son ganin Hamdi ranar da aka ce za ta zo gidan zamansa ya yi a kasuwa har ƙarfe tara. Shi ba abin ya ce kada ta zo ba matan gidan su soma tijara. Ya fahimci yanzu kamar ma jira suke ya ce kule su ce masa cass.
Ahmad ya nema da yazo gida yana son ganinsa da daddare. Bayan ya taso daga office kai tsaye can ya wuce. Alhaji ya keɓe dashi yana tambayarsa alaƙar Taj da Salwa tunda duka a gidansa su ke.
Tsoro ne ya bayyana a fuskar Ahmad. "Alhaji wata maganar ka ji?"
"Ya zan yi maka tambaya ka amsa min da tambaya?"
Da sauri ya bashi haƙuri tare da amsa tambayar da ya yi masa. "Babu komai a tsakaninsu amma kuma ba faɗa su ke yi ba. Shi Taj ma bai fiye zaman gida ba ai saboda kullum su ke buɗewa."
"Babanta, Alh. Mukhtar sunansa ko?" Alhaji ya faɗi da irin rashin damuwar nan.
Ahmad baya jindaɗin yadda ake magana akan Salwa yanzu. Rannan ƴan uwansa ne su ka yi ana ta dariya. Yau kuma Alhaji ke tambayar sunan babanta kamar wani abin gudu.
"Sunansa kenan."
"Ya kirani yana roƙon na amince Taj ya aureta."
Maganar ta dake shi sosai "Roƙo kuma Alhaji?"
"Roƙo mana. Ya tabbatar min ita take son sa. Kaima yanzu ka ce babu komai tsakaninsu. To me zai sa ita babar taku ta amince harma mijinta ya kirani?"
"Zan yi mata magana Alhaji." Ya girgiza kai "Gobe in sha Allah zan mayar da ita Bauchin. Idan ma mijin ne su sama mata a can." Tashi ya yi zai tafi. Alhaji ya ce ya dawo.
"Babu daɗi mutum ya nemeka akan wata alfarma ka nuna masa baka so. Saboda haka na faɗa masa na amince. Saƙon da nake son baka shi ne ka sanar dasu cewa bana so komai ya wuce wata ɗaya indai da gaske su ke."
Yana magana ne yana kallon yanayin Ahmad. A ransa kuma yana addu'ar Allah Yasa ɗan nasa ya yafe masa. Da gangan yake maganar a haka saboda yana so idan Ahmad ya tashi kai saƙon ya nuna musu shi fa bai ɗauki maganar da mahimmanci ba. Sannan baya ɗokin haɗa zuri'a da ƴarsu. Ya sami wannan canjin ra'ayin ne bayan wani nazari da ya yi. A matsayinsa na uba sai hankalinsa bai kwanta da ya yi amfani da ƴar wani domin biyan buƙatarsa ba. Idan komai ya tafi yadda yake so ya dawo ya ce da Taj kada ya auri Salwa me kenan ya yi? Shi mai ƴaƴa da jikoki mata ya dace ya tozarta ƴar wani haka? Gashi saboda sanin halin babarta ya tabbatar idan ya yi sake ta auri Taj sai sun mayar masa ɗa abin wasan yara.
Ba a raba hanta da jini. Hakan da yake yi ya san duka Ahmad zai faɗawa Mami. Kuma tunda yaro ne hankali zai yi ƙoƙarin nusar da ita illar bari a yiwa ƴarta irin wannan auren. Da bakinsa ne dai akwai nauyi bayan ya aminci ɗazu ya dawo ya ce ya fasa. Abin zai zama cin fuska sosai. Fatansa yanzu dai Allah Yasa iyayen suna da hankalin gane manufarsa.
Da wannan damuwar Anti Zahra ta tarbi Ahmad. Juyin duniya tayi ta tambayarsa amma yaƙi faɗa mata abin da yake faruwa. Abinci ma kasa ci ya yi saboda baƙincikin yadda Salwa take zubar da darajarta ta ƴa mace. Gashi yanzu ta sa iyayenta biye mata. Don ma su Hajiya akwai kawaici. Babu mai zancen Mami a gidan ko a aibata ta. Amma yanzu da sun ji maganar auren nan babu abin da zai hanasu fitowa ƙiriƙiri su ƙi.
Salwan ya kira tana ɗaki tana chatting da Ummi. Cikin sigar wayon da Alh. Usaini ya koya mata take ta jan Salwa tana dukan cikinta. Rai bai so ba ta katse hirar ta fita wajen Ahmad. Ɗakinsa ya kirata ba ma falo ba.
"Kun yi maganar Taj ne da Mami?"
"Eh" ta amsa masa babu wannan girmamawar da ya santa da ita.
Yadda su ka yi da Alhaji ya faɗa mata. Babu kunya ta kama murmushi. Baki har kunne.
"Da ni ne ke Salwa da na haƙura da mutumin da bai damu dani ba. Wane irin aure za ku yi yanzu? Shi baya so kuma na tabbata da wahala ƴan gidanmu su so."
"Ai ba da su zan zauna ba." Ta ce da tsiwar da bai santa da ita ba. Wai duk so ne ya canjata ko kuwa dama can halinta ne da bai sani ba?
"Shikenan. Zan kira Mami na faɗa mata. Duk abin da ya biyo baya kada ki ce ban yi warning ɗin ki ba."
Da ƙunƙuni ta tashi tana cewa "alkhairi zan gani."
Daina bashi mamaki tayi. Ya ce mata ta haɗa kayanta gobe za ta koma gida. Ƙarfe tara za su kama hanya. Tana fita ya kira Mami ta rangaɗa uwar shewa. Mantawa tayi da wa take magana ta ce,
"In ya san wata ai bai san wata ba. Har ni zai wulaƙantawa ƴa saboda yaci sa'a tana son shi?"
"Mami ana dole ne? Aurensa duka-duka sati ne fa da ƴan kwanaki. Ni dai da za ku ɗauki shawarata da kin ce mata ta haƙura."
Da faɗa Mami ta ce "to mai halin ubansa. Wanda baya kishina da na ƴaƴana. Idan ta haƙura kai za ka aureta?"
"Allah Ya baki haƙuri." Kawai ya ce.
"Amin. Kuma ka tanadi abin da za ka bani don a wata guda ko babanta ba zai iya haɗa abin da ya dace ba."
Allah Ya sani bashi da irin kuɗin da ya san idan ya bata ba za ta raina ba a yanzu. Sabon wata ne kuma farkon term an koma makaranta. Ɗa ɗaya amma ɗawainiyar karatu sai dai kawai a dinga yiwa iyaye addu'a. A bisa tsarin gidansu kuma tunda su ka soma kawo ƙarfi sun ɗaukewa Alhaji abubuwa da dama. Ba kuma don bashi da kuɗin ba. Ko a danginsa babu kamar shi har yanzu. Suna yi ne don neman albarka. Kayan abinci, kayan buƙata na gida irin su sabulu da kuɗin kashewa ga iyayensu. Duk masu aiki da masu kasuwanci suna contributing. A matsayinsa na babban namiji duk da cikin matan akwai waɗanda samunsu yafi nashi, amma yana ƙoƙarin ganin ya yi bajinta. A haka kuma yake bawa Mamin dubu talatin duk wata.
"Kai, Ahmad. Baka ce komai ba."
Ya ma manta waya yake. "Allah Ya hore. Sai da safe."
Ko minti goma basu yi da gama wayar ba ta sake kira. Ya san zancen ba zai wuce na kada ya dawo da Salwa ba. Shi yasa yaƙi ɗauka. Zai kaita gida gobe in sha Allahu.
Ƙarfe bakwai da rabi Anti Zahra ta same shi a ɗaki wai Salwa ta fita.
"Bangane ba. Ina ta tafi?"
"Ina ta tambayarta tana kuka. Da alama bata son tafiyar. Da ka ƙyaleta."
A harzuƙe ya tashi yana ta faɗa. Sai a lokacin Anti Zahra taji me yake faruwa. Ta ma kasa comprehending wannan al'amari.
"Don Allah kayi shiru kada Taj ya ji. Kwanansa biyu yana fama da zazzaɓin nan mai zafi. Sannan ko babu komai ka haɗa uwa da ita. Mutumcinta abin karewa ne a wajenka komai rashin daɗin da abin ya yi maka."
"Gidan wa zata da safiyar nan? Idan tana tunanin zan bita ne wallahi tayi kuskure."
"Naji. Ka san ba za ta wuce gidan ƙanwar babanta ba ta Sheka. In ba nan ba kuma ƙila ta wuce Bauchin."
"Ita ta sani."
Sai dare ya ɗauki wayar Mami. Ta ƙare masa tanadi kuwa. Shi kuma ya tsaya akan bakansa na cewa indai Salwa ta dawo gidansa to Bauchi zai maidota. Ba zai zauna da mara kunyar da bai isa ya faɗa mata taji ba. Mami da taga yaƙi tanƙwaruwa ta haƙura.
"Shegen yaro mai halin ubansa."
***
A kwana biyun nan kullum Hamdi sai ta kira Taj. Zazzaɓi ne irin wanda ya kan zo gama gari mai shiga gida gida. Ita kanta tana mamakin yadda ta damu da ciwon nasa da kuma rashin ganinsa. Da Zee ta tsegumtawa Sajida halin da take ciki haɗuwa su ka yi suna tsokanarta.
Zee ta ce "Salman Khan ya sallame zuciyar Hamdi."
Ita kuma Sajida tana dariya ta tuna mata tsohon ƙudurinta.
"Ta dai gama cika bakin bata son namiji mai girki. Yanzu gashi nan mai gidan abinci ya hanata sukuni."
Da yake a wayar Zee ake ta bidirin, gajiya tayi da kare kanta ta tsuke bakin nan. "Aljannar mace dai tana ƙarƙashin ƙafar mijinta. In kuma kuna baƙincikin kada na samu ne sai in ji."
Sajida da Zee me za su yi kuwa banda dariya. Ashe rana irin wannan za ta zo musu a kurkusa haka basu sani ba.
Ƙyalesu tayi ta koma kitchen wajen girkinta. Tana aiki tana tunaninsa. Yau ce rana ta uku tun zuwan da ya yi ta kira masa Kamal. Wayar ma idan sun yi ba wani jimawa su ke ba. Gaisuwa ce da jin yaya jikin nasa. Ɗan wasan nan duk ya daina.
"Ke!"
A firgice ta kalli Yaya. Bata san tun yaushe take tsaye tana yi mata magana ba.
"Jikin nasa ne har yanzu?"
Wayancewa tayi kamar bata gane ba "wa?"
"Garinku in kin san shi. Wa ma za ki ce min?"
Ƙasa ta kalla a kunyace. Fuskarta babu walwala. Yaya ta fahimci har yanzu a kwance yake.
"Jiya dama Abbanku yake zancen zuwa a dubo shi. Zan sake yi masa magana yanzu in sha Allah a waya."
Fuska mai tona asirin zuciya. A take fuskar Hamdi ta washe. Yaya ta kama baki tana salati.
"Anya dama ba shirya maganar auren nan ku ka yi da Taj ba? Cikin ƴan kwanaki kin zurma haka?"
"Ni ban zurma ba Yaya"
"Tsiwar ma ai naga ta ragu. Allah Ya yiwa aure albarka. Amma ki rage murna don ba dake zai je ba. Halifa zai ɗauka."
"Kai Yaya, ni yaushe na ce zan je?"
Dariya tayi "nima wasa nake miki. Ai na san ko tayi aka yi miki za ki ce a'a."
Bata ƙara magana ba tunda ta gane Yayan ma tsokanarta take yi. To ita har me tayi da ake mata wannan fassara?
*
A ɓangaren Taj abin da ya zata zazzaɓin gajiya ne ashe combo ne na typhoid da maleriya. Ciwon da ya manta rabonsa da yi. Shi ne ya yi masa rubdugu irin wannan. Kuma da yake zafi ake yi sai ya haɗu goma da ashirin. Dalilin zazzaɓin ne ma su Mama su ka tsahirta da sanya lokacin biki. Shirye shirye dai sai abin da ba a rasa ba. So su ke amarya ta shiga ɗakinta nan da sati uku ko wata guda. A nasu shirin idan ta tare da wuri za su ɓata shirin Alhaji. A ganinsu dama wata ukun nan da ya bayar ya yi ne saboda sanin cewa da wahala ace Abba Habibu yana da abin da zai yi bikin wata ƴar nan kusa.
Sosai Ahmad yake bashi kulawa. Musamman bayan tafiyar Salwa. Fushin da ya fara akan yadda aka yi mata dole ya kau da ya gaskata ita ce ta janyowa kanta.
Kamal ne dai tun ranar da ya kai shi asibiti ya ƙirƙiri tafiya washegari. Ciwo ke neman kayar dashi kuma baya son kowa ya sani. Haka ya tattara ya tafi asibiti. Mubina ta kwantar dashi. Magunguna tana iya bakin ƙoƙarinta. Bata so su fara dialysis domin ana kaiwa wannan matakin, transplant (dashe) shi ne best option ɗin da zai rage.
Ranar da ta kwantar dashi bayan ya zama stable ta kira Yaya Kubra. Dama kullum jiran wayarta take yi. Tana gani kuwa ta bar ayyukan gabanta ta tafi asibitin.
"Akwai shirin da ki ka fara yi ne Doctor saboda in san next course of action?"
Yaya Kubra ta gyaɗa kai "na fara bincike ta bayan gida. Wata questionnaire na ƙirƙira a google form nace ta research ɗina ce. Ita na tura a groups na family ake ta cike min. Harda families ɗin duka matan gidan mu. Kuma da yake da suna so far na sami mutum huɗu that are rhesus negative."
Idanun Mubina harda ƙwalla ta ce "Masha Allah. Amma dangin kusa ne?"
"Surprisingly daga dangin Hajiya na sami uku. Ɗaya ne a dangin Umma. Ai jinsi baya hana bayarwa ko? Duka huɗun mata ne."
Mubina ta ce gender baya hanawa. "Amma fa Kamal A negative ne. Indai ba irin nasa ba kinsan sai dai O ko AB negative ko?"
"Dukkaninsu O negative ne. Yanzu su Alhaji ya rage su sani sai a tuntuɓe su."
"Muje ki ganshi. Akwai Nephrologist da na fara magana dashi daga Port Harcourt. Idan an sami nasarar samun mai bayarwa sai naji yaushe zai iya zuwa."