Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 30
Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 30: Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 30. Godiya Yaya Kubra tayi mata har ta rasa kalmar faɗa. Mubina ta shige…
3,340 words
Godiya Yaya Kubra tayi mata har ta rasa kalmar faɗa. Mubina ta shige gaba zuwa ɗakin da Kamal yake. A hanya tayi ta nanata mata don Allah ta daure zuciyarta idan ta ganshi. Wannan yasa zuciyar Yaya Kubra ga tsinke tun kafin su shiga.
Mubina ce ta fara shiga da sallama. Yana kwance gaɓoɓi da fuskarsa sun kumburo sosai. Shi kaɗai ya san irin azabar ciwon da yake ji. Amsa sallamar ya fara da muryarsa can ƙasa kawai sai ya yi tozali da Yaya Kubra. Ya yunƙura ya tashi zaune kafin ta ƙaraso.
Hannu ta ɗora akan bakinta don kada tayi kuka mai haɗe da ihu da taga yadda ya koma.
"Kamal?" Ta kira shi da rawar murya.
Ya miƙa mata hannu, kwarmin idanunsa yana ziraro hawaye ta riƙe. A gefen gadon ta zauna su ka rungume juna. For the first time tun bayan ciwon nan ya same shi ya fashe da kuka mai ban tausayi. Duk wani ciwo, ƙunci da damuwa da yake ɓoyewa ya bari ya nuna kansa a wannan lokacin. Shi ɗan dangi yana ta fama da damuwa shi kaɗai. Abin da gidansu basu saba ba.
Yaya Kubra tana kuka tana shafa bayansa da lallashi. Mubina kuwa ficewa tayi don bata son karyar masa da zuciya fiye da halin da yake ciki. Mara lafiya baya son ganin rauni a tattare da likitansa.
Tsahon minti goma zuwa shabiyar kafin yaji sanyi a ransa ya daina kukan.
"Kiranki tayi ko?" Ya tambayeta yana nufin Mubina.
Faɗa ta soma yi masa "Me yasa ka zaɓi wannan rayuwar Kamal? Bamu da mahimmanci a wurinka? Ko kana ganin ba za mu damu da lalurarka ba?"
"Irin wannan kallon kamar kina yi min sallama shi ne bana son gani. Wannan kukan zamu dinga yi kullum har lokaci..."
"In sha Allahu za a dace. Ina nan ina bincike."
"Bata faɗa miki cewa ko dialysis ba zai iya riƙeni na tsayin lokaci ba?"
"Na sani Kamal. You need a new kidney. And we'll find one in sha Allah" ta share masa hawaye da hannunta.
Alƙawarin riƙe masa sirri ya roƙeta har zuwa lokacin da za ayi bikin Taj. Sannan ƙanwarsu mai shirin haihuwa ko yau ko gobe ita ma ta sauke.
"Me yasa? Wallahi ka san ba za ka burge Taj ba. Infact ni ba zan so ganin ranar da zai sani ba. Za ku yi faɗa Kamal. Za ku yi faɗa sosai. Ko jiya da naje duba shi sai da yayi ta zancen wai ina duba maka magungunan allergy kuwa."
Jingina ya yi da pillow don ya gaji da zaman. Ya yi ajiyar zuciya.
"Na sani. Amma Happy zai tsayar da duka uzurin rayuwarsa ne. Zuwa yanzu kin san mutum ne mai sanya abu a rai. Amma kina gani saboda mu ya mayar da komai ba komai ba tsakaninsa da Alhaji. Kuma hakan fa ba ƙaramin ciwo yake yi masa ba."
"Tsakanin uba da ɗa ne wannan. Ina maganar Happy da Happiness. Sai ka shiryawa duk abin da zai biyo baya."
"In ya ganni a haka kina tunanin zai iya yi min mita? Kuka kawai za mu zauna mu sha abinmu."
Yadda yake maganar kai ka san akwai tsantsar tawakkali. Yaya Kubra a nan ta wuni har tara na dare sannan ta tafi. Ta amince za ta yi shiru amma ba don Kamal ba. So take ta samu cikin dangin wanda idan ta bijiro da buƙatar ba zai ƙi ba. Maganar neman donor ta hanyar gwamnati ba zai yiwu ba. Waɗanda su ke kan list sun yi yawa sosai.
Tsakanin Kamal da Taj a waya sai ta whtsapp. Kamal ya cire simcard da sunan baya ƙasar. Wai ya tafi China odar takalma. Taj harda mitar me yasa bai faɗa masa shirin tafiyar ba. Ya ce wanda ya bawa sautu ne ya sami matsala. Gashi kuma komai ya kammala. Ana buƙatar mai kaya. Abinka da rashin sabo da yi. Taj bai kawo komai ba ya yarda. Iyaka dai in suna waya ya dinga kiran wash wash kenan don kawai yaji Kamal yana sannu kamar ya ari baki. Bai san ciwon Kamal ɗin ya ninka nashi ba.
***
Kamar yadda Anti Zahra tayi hasashe, Salwa gidan ƙanwar babanta ta tafi. Gidan da tun farkon karatunta baban ya so taje amma saboda Mami ta raina arziƙinsu ta rufe ido ta ce bata san zance ba. Wannan tafiya da tayi sai ta sami lasisin fita yadda take so tana haɗuwa da Ummi. Gwaggonta kuma bata iya yi mata magana saboda tsoron jarabar Mami.
Bayan bugun cikin da Ummi tayi mata sai ta nuna mata cewa tana jajanta mata rashin samun soyayyar Taj. Ta kuma yi mata alƙawarin za ta taimaka mata ta sami biyan buƙata indai tana so.
"Mamina ma ta gama komai har an fara maganar aurenmu" ta faɗawa Ummi da farinciki.
Taɓe baki Ummin tayi "in an ɗaura muku auren kina tunanin kin yi nasara ko me? Mutumin da baya sonki kuma igiyar auren tana hannunsa."
A tsorace Salwa ta ce "kuma fa haka ne. Amma ba sona bane baya yi. Haɗuwarsa da matar da aka aura masa ƴar ɗan daudu duk shi ya lalata komai. Da muna waya normal."
A zuci Ummi tayi tsaki. Wannan Salwan irin matan nan ne da sakarci ya rinjayi tunaninsu. Gashi dai ta san cewa ta girmeta amma irin shirmen da take yi da sunan soyayya ita ko da wasa ba za ta yi ba.
"Ni naga sharrin ƴar ɗan daudu. Akanta aka koreni daga makaranta sannan aka fasa bikina. Gidanmu kowa ya tsaneni akansu. Wallahi da zan haɗu da Hamdiyya Habib sai na rama abin da tayi min ko yaya ne."
Idanu Salwa ta zaro tana kallonta "Hamdiyya? Ai kuwa ita ma sunanta kenan. Babanta yana aiki a Happy Taj."
"Ni ban san a ina yake ba. Amma dai shi ma sana'ar girki yake yi. Kin ganta. A yadda suke matsiyata bana jin ko iskar da mai Happy Taj yake shaƙa ita ma za ta shaƙa wataran."
Hoton Hamdi ta nuna mata wanda ta samu ta ɗauka daga wayar Siyama na ranar aurensu. Salwa ta dinga sallallami gami da rantsuwar ita ce. Ita ma Ummi ta nuna nata mamakin ƙwarai.
"Indai Hamdi ce nayi miki alƙawarin zan bada nawa taimakon na raba su da masoyinki."
"Nagode. Ni kam alkhairi ne ashe ya kai ni Glory mall rannan."
Ummi sai dariyar yaƙe kawai take yi. Ita kanta duk fitinarta abin da Alh. Usaini ya tanadarwa Taj ya yi mata hatsabibanci da yawa. Ta riga ta nuna masa tana tare dashi bata da hanyar guduwa. Haka kawai take tsoron mutane irinsa waɗanda za su iya yin komai domin biyan buƙatarsu. Rashin kunyarta bata kai nan ba. Domin kuwa duk iya shegenta akwai abubuwan da take tsoron yi don kada su koma kunnen iyayenta. Tunda Allah Ya kawo Salwa sai ta bashi shawarar amfani da ita don ya cimma burinsa.
*** Jinyar sati guda Taj ya yi kafin ya farfaɗo sosai. Har ya faɗa kuwa. Abba yaje duba shi har gidan Ahmad. Kuma ya sami tarba ta mutumci daga gare shi. Wannan ya sake daɗaɗa ransa akan halin ƴaƴan Yaya Hayatu. Da zai tafi ne Taj ya yi masa maganar Hamdi.
"Abba don Allah ina neman alfarma a gareka."
"Indai zan iya in sha Allahu zan maka."
"Maganar rabani da Hamdi. Don Allah ka cire komai a ranka ka bimu da addu'a."
"Innalillahi..." Abba ya riƙe kai "faɗa maka tayi? Ban san Hamdi da surutu ba wallahi."
Taj ya yi murmushi "ba ita ta faɗa min ba." Ya tuna maganar da Salwa tayi ya ce "Yaya Ahmad ne ya faɗa. Amma ya ce kada na damu in sha Allah su Inna ba za su bari ba."
"Lamari na iyaye..."
"Allah bai bawa iyayenmu damar kashe mana aure ba. Musamman idan raba auren cutarwa ne ba hanyar samun maslaha ba."
"Ina jiye maka yawan saɓanin da kuke samu dashi. Hakan ba zai haifar da alkairi ba."
"Abba ina ƙoƙarin tsayuwa akan iyakar addini kan abin da ya shafi Alhaji. Duka abubuwan da yake fushu dani a kai shi yake nuna amincewarsa sannan ya zargeni da rashin kyautawa."
Shi dai Abba gani ya yi zai shiga tsaka mai wuya. Ya yi ta nunawa Taj illar dake tattare da zama cikin fushin iyaye.
"Don Allah ka nemi sulhu dashi kafin lokaci ya ƙure."
Muryar Taj a raunane ya ce "na jima ina wannan amma yaƙi bani dama. Zan cigaba da ƙoƙari amma Abba kada ka kuma sako aurena a ciki don Allah."
Tausayi ya bawa Abban "na daina. Allah Ya kiyaye mana ɓacin rana."
"A sunnar Annabi SAW? Inaaa, Abba ai sai dai lada."
Nauyi Abba ya fara ji tun kafin Taj ɗin ya je inda bai dace ba ya ce "naga ka fara jin sauƙi. Bari na tashi."
Taj ya dinga dariya kamar ba shi ne yake kwance kafin zuwan Abban ba.
***
Inna tana falonta ana yi mata kitso aka yi mata waya. Baƙuwar lamba ta gani. Ta ɗauka da sallama su ka gaisa da matar da ta kira.
"Na san ba ki gane ni ba tunda bamu zauna tare ba. Mahaifiyar Ahmad ce. Ahmad babban ɗa namiji wajen Alh. Hayatu nake nufi."
Murmushi Inna tayi. Wannan ƙalau take kuwa? A take ta cire wayar daga kunnenta ta karanto Ayatul Kursiyyu. Ɗabi'arta ce haka. Duk abin da bata gamsu dashi ba koda bata aka yi sai ta tofe shi da Ayatul Kursiyyu kafin tayi amfani dashi. Yadda Mami ta gabatar da kanta sam bai yi mata ba.
Sai da ta gama sannan su ka gaisa da ita.
"Dama naji shiru ne ina ta sa rai da wayarki amma baki kira ba. Nace bari ni na neme ki naji me ake ciki."
"Wace magana kenan?" Tashi tayi daga wurin kitson ta koma ɗaki.
"Auren Taj da Salwa. Alhaji ya ce baya son a wuce wata guda. Naga har an cinye sati."
Azkar ɗin tunkarar shugaban da kake tsoron cutarwa daga gare shi Inna ta karanto wannan karon kafin tayi magana.
(Allahummak finihin bima shi'ta)
"Wane Taj ɗin wai? Nawa dai sati biyu kenan da aurensa. Bani kuma da labarin zai ƙara wani."
Mami tayi kwafa a hankali tana raya duk za su zo hannu ne. Da ta san haka za ta yi mata tun farko ma da ta karɓo laya.
"To ki tambayi maigidan naki. Sai mu yi magana daga nan."
Inna ce ta fara kashe wayar. Ta dinga karanto addu'o'i. Me yasa duk wata rigimar gidan akan Taj take kunno kai? Istigfari tayi da sauri sannan ta fita ta tafi ɓangaren Alhajin. Dama yana gida. Girkin Umma ne. Inna tayi sallama ta shiga falon bayan Umma ta amsa ta iske shi yana cin abinci.
"Alhaji me nake ji daga bakin tsohuwar matarka?"
Karo na biyu kenan da Inna tayi masa magana babu kyautata kafazi. Yana namiji sai da yaji wanibabu a ransa. Maganar Hajiya na neman tabbata da ta ce masa kada ya ƙure haƙurin Abu don mai haƙuri bai iya fushi ba.
"Wani abin ne ya faru?" Ya tambayeta kamar bai sani ba.
"Ka fini sani Alhaji. To amma ina so ka sani ka gama yi min hawan karkatacciyar kuka. Wannan juya min yaro da kake yi ya isa haka."
"Haba Inna. In ranki ya ɓaci kada ki bari hankalinki ya gushe mana. Da mijinki fa kike magana." Umma ta ankarar da ita don muryarta tashi take sosai.
"Me ya rage min? Yau ko agola ne Tajuddin ai iyakar abin da mijin uwa da baya sonsa zai yi masa kenan. Wai ni matar nan za ta kira ta ce ya maganar auren Taj da Salwa?"
"Me?" Umma ma ta ɗaga murya ba tare da tunani ba.
"Ah to, kema kya faɗa. Wai da Alhaji su ka yi magana."
Ya fa manta da maganar nan. Duk a zatonsa idan Ahmad ya faɗa mata yadda su ka yi za taji haushi ta ce basa so. Daga ranar da su ka yi maganar ko tunawa bai sake yi ba saboda rashin mahimmancin zancen a wajensa.
Umma ta dube shi "Alhaji wai haka?"
"Eh. Mun yi magana da mijinta ya bawa Taj Salwa. Sharaɗina kenan idan ba zai saki ƴar gidan Habibu ba. In ba haka ba kuwa..."
"Kana son ya saketa kafin auren ya wuce wata uku ko? Ahmad, ɗan halak ya faɗa mana" Inna ta ƙarashe masa.
"Tunda kun sani sai ku sa ya zaɓi ɗaya. Na gama magana."
"Ahaf. Ai babban kuskurenka da ka bari aka yi auren nan Alhaji. Shi ne mai wuyar. Ko yanzu ba abin mamaki bane ace Hamdi tana da juna biyu."
Ba Alhaji da ya kusa ƙwarewa da ruwan da yake sha ba, Inna ma zaro idanu tayi.
"Kai Umma?"
"Auren yanzu da ake yiwa yara bayan duk sun ƙosa. Ko mu nan nawa ne ƴaƴanmu su ka haihu wata tara ko goma da aure? Indai an bada sadaki ai magana ta ƙare. Don ma ba lafiya gare shi ba."
"Ai kuwa sati mai zuwa za ta tare." Inna ta faɗi sannan ta dubi Alhaji "ka faɗawa tsohuwar matarka ta nemarwa ƴarta miji tun wuri."
Inna na fita Alhaji ya tsare Umma da tambaya. Shi fa daina gane komai ya yi daga inda ta ce bashi da lafiya.
"Ciwo ne da Taj ɗin?"
"Typhoid yake da maleriya. Satinsa guda ko aiki baya zuwa."
Ransa a ɓace ya ce "Kuma shi ne aka rasa wanda zai faɗa min?"
"Taj ne fa. Ka damu da ciwonsa ne dama?"
"Me kike nufi?"
"Wai abin da ido ya gani baki ke faɗa."
Ta jima da fita daga ɗakin ta bar Alhaji da tunani. Me yasa sai akan Taj iyalinsa su ke yi masa irin wannan? Sai kuma maganar Salwa. Bai san har yanzu Mami bata da cikakken hankali ba. Ai da maimakon hannunka mai sanda sai ya fito musu a mutum kawai.
Yana wannan lissafin tuni Mami ta garzaya wajen toshe ɓarakar da take hangowa. Magana ta yiwa Alh. Mukhtar. Ya kuma aiwatar duk da baya so.
Alhaji sai waya kawai yaji. Ganin sunan mai kiran ya hanzarta ɗauka domin ya kashe maganar Salwa. Sai dai kafin ya ce komai Alh. Mukhtar ya yi masa dabaibayi.
"Akwai wasu ƴan uwana mazauna Kano da muka yi magana mutum biyar. Ɗaya ma ƙanin mahaifina ne uwa ɗaya uba ɗaya."
"Wani abu ne ya same su?" Alhaji ya ƙosa yaji ƙarshen zancen ko ya sami damar yin nasa.
"Lafiya ƙalau. Dama don a sama muku sauƙi ba sai kun taho har nan ba. Shi Baffan namu na sanar dashi za ku zo neman aure da biyan sadaki. In kun saka rana sai ka sanar dani. Na tura musu lambarka ma dai."
Alh. Hayatu mai baki sai yaji yawun bakinsa ya ƙafe. Ta ina zai fara cewa ya fasa? Abin da kamar wuya. Girmansa zubewa zai yi. Idan matansa su ka san halin da yake ciki ya tabbata dariya za su yi masa.
"Idan na saka ranar zan sanar da kai."
"Yauwa to nagode." Ya đan numfasa "don Allah kada a ja lokacin. Nima na gama shiri."
"To"
Alhaji ya gyaɗa kai. Kuma har zuciyarsa sai yaji yana tausayin Alh. Mukhtar ɗin. Shi da zai iya dafa littafi mai tsarki ya yi rantsuwar matansa basa biye biyen tsibbu ashe a aljanna yake. Gudun faɗuwar girma ya janyo ya kasa kyautata musu akan abu guda da su ke buƙata daga gare shi.
*
Inna na dawowa daga ɓangarensa taci karo da wasu rantsattsun akwatuna manya manya guda huɗu a tsakiyar falo. Ƴan gidan an haɗu ana ta murnar yaushe gamo da Amma. Rabonta da shigowa gidan yayan nata an jima.
"Takwara oyoyo" Umma ta ce daga bayan Inna da ta kasa magana.
"Yauwa Takwara" Amma ta ce, ita da su Mama su ka bi Inna da kallo.
Murmushin dole tayi musu gami da yiwa Amma sannu da zuwa sai ta shige ɗaki. Ta manta da mai kitson sai da ta ganta zaune tana jiranta. Kuɗin kitson ta bata sannan ta ce ta tafi za ta nemeta daga baya. Matar bata matsa ba don ta lura Inna bata cikin nutsuwa. Uwar ɗaka ma ta shige ta rufo ƙofa. Wayarta ta ɗauka ta kira babban wanta. Tana jin muryarsa ta fashe da kuka.
"Me yake son ya mayar da rayuwar yaron nan? Shi ba fasiƙi ba, ba ɓarawo ko ɗan fashi ba. Amma ace duk wani abu dake nuni da ba a son mutum akansa yake ƙarewa?"
Rarrashinta ya yi sannan cikin kuka ta labarta masa abin da ya tunkaro su kuma.
"Ina jin lokaci ya yi da zan nunawa Hayatu bai fi ni zafin kai ba. Turo min lambar baban ita matar Taj ɗin. Sati na sama in sha Allahu za ta tare. Idan ya kuma barazanar rabasu kuma ni da kaina zan ɗauki mataki."
"Yaya ita kuma tsohuwar matar tasa fa?"
Dariya ya yi ta manyan dattijai "kinsan Allah, barazana ce kawai. Hayatu da wuya yake yar da abu ya waiwaye shi. Abin da ya raba shi da Habibu kenan tun farko. A yanzu kuwa ban hango zai taɓa yarda babar Ahmad ta zama surukarsa ba. Rabuwarsu ba ta daɗi bace."
Nutsuwa ta samu da wannan wayar. Ta fito falonta don zuwa wajen Amma ta gansu duka zaune. Umma ta faɗa musu abin da ya faru. Su ka haɗu suna bata baki. Tun bata son nuna ai ɗan cikinta Alhaji yake yiwa haka har ya kai ta fito tana faɗa da bakinta.
Su ka haɗu da Amma su ka bata baki. Auren ƴar Mami kuma ko Taj ne ya kwaso da kansa ba za su yarda ba. Suna wannan tattaunawar Alhaji ya shigo ɓangaren nasu. Ganin babu kowa ya tambayi ina su ke. Aka ce su na ɗakin Inna. Juyawa ya yi bakinsa alekum ya fice, musamman da yaji cewa Amma ta zo. Sake hargitsasu za ta yi ta zuge su tas. Ƙarshenta in bai yi da gaske ba sai anyi sa'in'sa a gaban mutane idan ya ce zai nemasu yanzu.
***
Sai washegari Taj ya sami ƙwarin fita sosai. Jiya da su ka yi waya da Hamdi ya ce zai je Happy Taj ta ce ya bari ya ƙara hutawa.
"Kin isa matar Happy. Dama tunda Happiness ya yi tafiya na san ba wani daɗin wajen zan ji ba sosai. Da ni ɗan gata ne dai sai ki zo ki tayani zama." Yayi maganar a hankali.
"Naƙi wayon. So ka ke Abba ya tsireni? Yana wajen sai na zo na wuce."
Marairaicewa ya yi "A misali da ba zai yi faɗa ba za ki zo? Uhmm? Allah naji jiki fa. Ga rama."
"Kullum fa ina kiranka."
"Kira daban, gani da ido daban. Kin san fa babu jinya mai daɗi kamar kayi a gaban matarka."
Hamdi tayi dariya. Da alama Taj kallon yarinya yake yi mata. Shi ne zai yi mata wayo.
"Allah ko? Saboda me?"
"Ana yi ana petting ɗin mutum. Ga pecks here and there. Sai ka manta ma da ciwon." Ya bata amsa yana jin dama so samu ne.
Baƙuwar kalmar da taji ta tambaye shi. "Meye kuma pecks?"
Taj na jin haka ya tashi zaune yana ƴar dariya. Ashe ma wayon da take ta zillewa zai yiwu.
"Peck ɗin ne baki sani ba? Ko dai kin faɗa ne?"
"Allah ban san shi ba. Pecks naji ka ce."
Da fatan kada ta ɗago shi ya ce "Da yawa ne pecks. Gashi akwai nauyi da na ɗauko miki."
"Idan da rabo sai na gani watarana."
Duk a zatonta wani abu ne da ido zai iya gani kuma hannu zai ɗauka.
Dama ce ta zo wa Taj bayan sun gama wayar da yamma. Mama ta kira Yaya ta sanar da ita za su zo washegari ita da su Amma. Wasu daliliai sun janyo suna son ayi biki sati mai zuwa. To dama su ma suna ta ɗan shirinsu don ba a zauna haka ba.
Yaya sai ta kira Hamdi ta ce ta tambayi Taj ko gidan Sajida ne gobe ta tafi.
"Idan baki je yanzu ba aka fara biki za ku kwana biyu baku haɗu ba."
Daɗi ya kama Hamdi. Tana ta murna ta kira shi. Sai ya ce ta shirya shi zai zo ya kaita.