Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 31
Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 31: Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 31. Shi ne fa yau ya shirya yau cikin nishaɗi. Happy Taj ya fara zuwa.…
3,362 words
Shi ne fa yau ya shirya yau cikin nishaɗi. Happy Taj ya fara zuwa. Akan idon Alh. Usaini ya wuce. Nan da nan ya kira Ummi ya ce aikinsu zai iya yiwuwa yau. Da alama Taj ya dawo aiki. Tunda suna ta kula da shige da ficensa tun bayan sun gama shirinsu. Sai dai bai ƙara zuwa ba sai yau ɗin.
Kai tsaye Salwa Ummi ta kira. Don dama Alh. Usaini bai yarda Salwan ta san shi ba. Ko ta kwaɓe sai dai su ƙare tsakaninsu da Ummi. Tana zuwa Ummin ta bata turarukan da Alh. Usaini ya bayar. Guda biyu ne masu wani irin ɗan karen ƙamshi. Ɗaya a yadda Ummin ta faɗa mata zai haddasa faɗa tsakanin Hamdi da Taj. Ɗayan kuma zai haɗa ƙaƙƙarfar soyayya tsakaninta da shi.
"Amma me yasa ki ke taimaka min Ummi?" Salwa ta tambayeta bayan ta karɓi turarukan.
"Saboda ba zan taɓa sanya ido Hamdi ta zauna a gidan miji alhali ni ta hana ni aure ba."
Da farinciki Salwa ta ce "Allah Ya bani ikon taimaka miki nima a duk lokacin da kike buƙata."
"Amin"
Bayanin yadda zata saka turaren Ummi tayi mata. Ta fito za ta tsallaka ta shiga Happy Taj sai taga motar Taj ɗin yana fitowa. Hankalinta ya tashi. Ummi ta ce kada ta damu. Su jira zuwa la'asar domin indai ya shigo ko ya fita da wahala a rufe wurin baya nan. Jin haka sai ta sami wuri ta zauna su ka cigaba da ƙulla yadda za ayi bikin Salwa da Taj bayan sun yi nasara.
***
Zee ce ta yiwa Hamdi light make up sannan ta shirya. Doguwar rigar atampa ta saka wadda take fitted daga sama. Sai kuma aka buɗeta daga ciki har ƙasa. Turarukanta na scentmania tabi ta shafe jikinta dasu.
"Don Allah Ya Hamdi a dinga ragawa Salman Khan."
"Wallahi zan miki rashin mutunci akan kiransa Salman Khan."
Zee ta dinga dariya. Suna gama ɗaurin ɗankwali ya kirata. Yaya tana son yi mata ɗan gargaɗin manya amma kuma ta rasa me ya dace ta ce. Miji da mata wane gargaɗi kuma za ayi musu wanda ba zai shiga hurumin shari'a ba? Ƙarshe dai sai cewa tayi,
"A kula da kai dai. Banda yin abin da bai dace ba."
Tunda ta fito ya kasa ɗauke ido daga kanta. Yana mamakin yadda ya mallaki wannan yarinyar da ya taɓa gani tana practicing speech. Ganin farko ta kanainaye masa zuciya. Ita ce first true love ɗinsa. Ya kuma yi sa'ar zama mijinta.
Daga ciki ya buɗe mata ƙofa. Sai da ta zo shiga ta fara jin faɗuwar gaba. Ta kasa gane ta murnar ganinsa ce ko ta tsoron fitinarsa, ko kuwa ta wani abin daban da bata sani ba?
Zama tayi ta rufe ƙofar sannan ta gaishe shi. Tana yi tana kawar da kai daga kallon fuskarsa. Ta san yanzu yana ganin kwalliyarta zai ce kama tsokanarta.
"Mrs Happy yau kuma ƴar ɓoye fuska ce? Irin yanayin nan da Indians..."
A gaggauce ta ɗaga fuska su ka haɗa ido.
"Kada ka ƙarasa. Ka bar Indiyawa su sarara don Allah."
Lumshe ido ya yi ya buɗesu akan fuskarta. "Na barsu. Yau ko su basu da kalaman da zan yabawa Hamdina." Yatsa ɗaya ya ɗaga a gaban fuskarsa "In ce awwnnn sau ɗaya don Allah?"
Riga shi tayi harda fari da idanu "awwnnnnn"
Taj ya sanya hannayensa duka a saitin zuciyarsa "yarinyar nan za ki kashe ni. That was just too cute."
"Tunda kaga ba kai kaɗai ka iya ba don Allah ka daina."
"Ban yi alƙawari ba. Atleast zan cigaba kafin na samu wani abin tsokanar taki."
Tuƙi ya fara a hankali suna tafiya Hamdi ta sake yi masa sannu da jiki.
"Ka rame da gaske fa."
"Sauron garin nan wasa ne? Jiya na kira mai kula da gidanmu na ce su duba duk wata ƙofa ko window a saka net." Don jin me za ta ce ya ƙara da cewa "ko mu je ki gani?"
"Allah Ya baka haƙuri. So kake Yaya ta ce a biyoni da kayana kada na dawo gida yau?"
"To ba shikenan ba. Kowa ya huta."
Cewa tayi bata yarda ba. Ya ce sai ya kaita. Dama ya kamata su gaisa da Amma. Tunda tana can da su Umma kafin su je wajen Yaya sai su haɗu. Hamdi ta rikice sosai don ya đauke hanya daga inda ta kwatanta masa gidan Sajida. Ya gama janta sannan ya ce Happy Taj za su fara zuwa.
Narke masa fuska tayi "so dai kake dole yau nayi laifi ko?"
"Ba zama zamuyi ba. I just realllyyy need to show you that peck."
Zazzaro masa idanu tayi "da ka bari ma kawai..."
Taj ya kama dariya "yau wata za ta yiwa Abba bayani. Ki ka ce min baki sani ba."
"Muna gama waya na duba a google." Ta bashi amsa da ƙaramar murya.
"Wannan fassarar google ce. Ni dai sai na nuna miki."
"Don..."
"Shhhhh. Ba a faɗa miki babu kyau roƙo ba?"
Wanda baya jin magiya biye masa kawai ake yi. Daina zancen tayi ta karkata zamanta ta zuba masa idanu yana tuƙi.
"Mene ne?"
"Jira nake muje ka nuna min peck ɗin nan."
"Haaa, shi yasa nace kalarmu ɗaya. Ni dake duk fitinannu ne. Allah dai Ya shiryemu."
Juyo da abin kanta ya yi ya dinga tsokanarta har su ka isa akan idon Salwa don ta riga Ummi ganin motar tasa. Nan gabanta ya cigaba da faɗuwa kada su haɗu da Abba. Taj ya buɗe mata wata ƙofa ta baya wadda directly office ɗinsa za ta kai mutum.
"Emergency exit ce for naughty people like us."
"Banda ni."
"Kin ganki fa." Ya janyota ya rungumeta a jikinsa gabaɗayanta "ke da aka ce ki tafi gidan yayarki kin biyo miji office."
"Laifin wa don Allah?"
"Naki mana" ya soma magana a hankali. Ƙamshin jikinta ya tayar masa da kewar sati guda "I miss you so much."
Idanunta sun soma raina fata don akwaita da tsoro ta ce "ka zo mu tafi."
"Uhm uhmm" peck ɗin da ta ce bata sani ba ya soma sauke mata a fuska.
"Happy" ta daure ta kira shi. Tsoro ne fal a zuciyarta. Na zuwa wajen da kuma na shi kan shi mijin nata.
"Mrs Happy"
Daidai lokacin su ka ji an ƙwanƙwasa ƙofar. Hamdi ta ƙwace daga hannunsa a firgice. Shikenan, idan Abba ne ta gama yawo a wurin Yaya ba shi ba.
Muryar wani yaronsa yake ji yana rantsuwar baya nan. Sai kuma ta mace da ya tabbatar Salwa ce tana cewa taga shigowarsa. A buɗe mata ta jira shi. To da yake yaron ya santa sai ya ce ta bari ya ɗauko spare key.
Ita Hamdi ko maganganun bata ji da kyau. Ƙofar kawai da taji an riƙe yasa ta neman toilet.
"Stay with me please. Ba Abba bane."
Ta girgiza kai ta gudu. Idan ba Abba bane ai dai zai iya samun labari.
Tana shigewa Taj ya buɗe ƙofar. Salwa ya gani a tsaye yau ita ce da mayafi a kafaɗa ɗaya ɗan mitsitsi haka?
"Ya Taj" ta kira sunan shi tana murmushi.
Baya ya yi don ta samu ta shigo saboda kada ta faɗi abin da zai kunyata shi. Tana sanya ƙafarta a ciki ta rufe ƙofar.
"Salwa me ya kawo..."
Faɗo masa tayi a jiki kafin ya gama tambayarta. Hannunta hagu da dama kowanne da turaren da Ummi ta bata. Wuyansa ta riƙe da hannayen saboda ance lallai ta taɓa fatarsa da turaren ba kaya ba.
Ya sanya hannuwansa zai cire nata sai dai kuma duka hannuwan ta shafesu suma. Saboda haka yana taɓawa abin ya sake shigarsa.
"Sake ni Salwa" ya ce yana jin wani irin abu na shigarsa.
"My Taj..." ta sake yunƙurin rungumarsa.
Fincikota taji anyi ta baya don bata ji lokacin da aka buɗe ƙofar banɗakin ba. Ta juya za ta yi magana Hamdi ta tsinketa da mari.
"Ke! Ni za ki..."
Rai a matuƙar ɓace Hamdi ta sake marinta sannan ta saka hannu ta rabata da Taj.
"Fita."
"Nace ki fita ko na tara miki mutane. Banza kwartuwa."
"Ya Taj warn this girl." Salwa ta ce tana ƴar dariya "ko na kashe maka jiki ne?"
Shi fa jiri ne ma yake ɗaukarsa. Amma idanun Hamdi sun rufe da ganin da tayi musu. Me zai sa ya bari Salwa ta rungume shi na tsayin lokaci har ta fito.
Ƙofar office ɗin Hamdi ta buɗe ta kamo hannun Salwa ta janyota. Inda ta sami ƙarfin hali da na jiki ma bata sani ba.
Ita kuwa dariya ma take yi ta ce "Baki ga komai ba ƴar ɗan daudu. Sai na zo har gida." Ta yi murmushi ta fita.
Idanu a birkice Hamdi ta juyo ta kalli Taj. Kan da yake riƙewa ma a wajenta ba komai bane illa pretense.
"Abin da ka kawoni ka nuna min kenan?" Tayi magana tana hawaye masu zafi.
"Hamdi ba haka bane."
"Dama ku maza munafukai ne."
"Ni ne munafukin? Ni?" Zuciyarsa ta harzuƙo da wani irin ɓacin rai.
"To ko ɗayan zan kira ka? Wanda ya dace da mazan dake neman matan da ba nasu ba?" Ta faɗa kai tsaye.
Rufe bakinta ke da wuya kuwa ya ɗaga hannu zai mareta.
"Bismillah. In baka mareni ba baka haifu cikin uwa da uba ba."
Tassss.
Shi da yayi marin da ita da ya mara su ka kama zubar da hawaye lokaci guda. Komai na jikinsu da zuƙata yana nuna musu illar kalamansu ga juna da abin da su ke yi. Amma kuma wani abu daga gefe yana ingiza su da jin haushin juna na ban mamaki. RAYUWA DA GIƁI 25
Batul Mamman💖
Taurin zuciya ya hana Hamdi kukan da sauti. Sai hawaye kawai da ajiyar zuciya. Ji take kamar ta buɗe ido ta ganta a gaban Yaya. Auren za ta ce ta fasa da gaske. Gashi dai zuciyarta tana ƙaunarsa. Ƙauna da son da har yanzu bata taɓa faɗa masa ba saboda kunya da jan aji na mata. Sai dai tayi abin da zai gane shi ɗin mai matsayi ne babba. Tana tanadin kalmominta masu tsada zuwa lokacin da za su kasance a muhalli guda. Abin da ya gagareta fahimta bai wuce yadda ta rufe ido ta iya kiran shi munafuki ba. Haƙiƙa duk wanda ya santa zai yi mata shaidar tsiwa. Amma rashin kunya irin wannan kuma ga mijin aure, abu ne da ita kanta bata taɓa kawowa zata yi ba. Kuma har yanzu yadda take jin son nasa haka kuma wani irin haushinsa yake cin zuciyarta. So take kawai ya sake yin wani abin ita kuma ta cigaba da faɗa masa abin da zai ji haushi.
Shi kuwa Taj ya ma rasa me yake yi masa daɗi a duniya. Juya mata baya ya yi ya runtse idanunsa. Sai ya yi yunƙurin juyawa yaga halin da take ciki, sai yaji zuciyarsa tana tuna masa kalamanta a gare shi. Ransa ya ƙara ɓaci har wani tafasa zuciyarsa take yi. Muddin za ta cigaba da yi masa rashin kunya yana kyautata zaton zai iya yi mata dukan da sai an ɗagata....Duka??? Ai ko ƙannensa mata ba za su yi masa wannan shaidar ba yayi saurin kwaɓar kansa. Me ya kai shi marinta?
A hankali ya juya su ka fuskanci juna. Kumatunta ya yi shatin yatsunsa raɗau. Gabansa ya faɗi da ganin aika aikar da ya yi a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. Wayarsa ya ɗauko ya kira Sajida don tabbas ba zai iya kai Hamdi gidan a haka ba.
Hamdi na cikin yanayin ɓacin ran nan taji yana cewa ba zai sami damar kaita ba. Da haka ta gane da wa yake wayar. Bata san me Sajidan ta ce ba ya bata wannan amsar.
"Lafiyarta ƙalau, kawai dai tana cikin yanayin da bai kamata taje ko ina ba. So please ki min alfarma kada ki faɗa a gida cewa bata zo ba."
Kallon mamaki Hamdi ta fara yi masa. Kafin kuma cikin fushi ta fara neman karɓe wayar. Za ta soma ɗaga murya ya danne wayar da kafaɗarsa ita kuma ya sanya hannu guda ya rufe mata baki. Ɗayan kuma matseta ya yi a jikinsa da shi. Ya yi ɗan murmushi da Sajidan ta soma cewa ta gane duk da muryarta ta bada ita.
"Ba fa abin da kike tunani bane wallahi. Fitowar ce dai kawai ba zan iya ba."
"Ko dai bata da lafiya ne?"
"She is fine. Bari tayi miki magana."
Kallon gargaɗi ya yi mata kafin ya cire hannunsa daga bakinta a hankali ya kara mata wayar a kunne. Ta ɗaga jajayen idanuwanta ta dube shi. Kalmar 'please' ta karanta a laɓɓansa. Ranta sosai yake ƙuna.
"Ya Sajida."
"Alhamdulillah" hankali kwance tunda taji muryarta ta ƙara da cewa "asha soyayya lafiya."
Da sauri Hamdi ta yanke shawarar fađa mata me ya faru. "Mar..."
Bai bari ta ƙarasa ba ya cire wayar. Ta buɗe baki za ta yi magana da ƙarfi yadda zata ji ya zauna tare da ita a jikinsa ya turata ƙuryar kujera yana girgiza kai. Dolenta tayi shiru kawai sai harare harare bayan ta tattare ƙafafunta ta cure jiki waje guda.
Sam ba zai yarda a ganta da shatin nan har a fara tambayoyi ba. Muryarsa ya gyara ya ce "Don Allah Sajida. I realy need this favour from you. Kin san dai ba zan cutar da ita ba. Duk da tana ta rigimar sai na kawota."
"Subhanallahi. Ya Taj me ya kawo wannan maganar? In sha Allah babu mai ji. Ita kuma kada ma ka biye mata."
"To nagode."
Akan centre table ɗin wurin cushion chairs ɗin mai kyau na gilas ya ajiye wayar ya fuskanceta. Zuciyarsa tana ta kai komo wurin faɗa masa ƙarya da gaskiya. Ya rasa tudun dafawa guda ɗaya. Hannunsa ya kai kumatunta zai taɓa tayi saurin karewa da nata,tana mai sadda kai ƙasa. Bai kulata ba ya riƙe hannun nata ya kai ya taɓa inda ya yi marin. Baya jin za ta kai shi jin ciwon wannan abu.
"Am sorry" ya ce muryarsa a shaƙe.
Ai kamar ya kunna famfo. Sabbin hawaye su ka sauko mata. Muryarta har ta soma dashewa ta ce, "Mari na fa kayi."
"You hurt me with your words Hamdi. Munafuki, kuma ki ce ban haifu ba?"
Cikin kuka tana ajiyar zuciya ta bashi amsa "Allah maganar da kanta ta fito. Ban yi niyya ba."
Muryarta ta sake karyar masa da zuciya. "Duka ba halina bane. Ki yi haƙuri."
Da ka ta amsa. Ya sanya hannayensa duka ya rungumota. A lokaci guda kuma zuƙatansu su ka dinga harbawa da faɗuwar gaba. Kamar hakan laifi ne gagarumi. Kusan a tare su ka saki juna.
"Mu yi sallah sai na samo miki abinci. Me za ki ci?"
Zumɓura masa baki tayi "ni bana cin girkin maza."
Ya ɗage gira yana ɗan murmushi "da gaske?"
Ta san manufarsa shi yasa ta ce "sai na Abbana kaɗai."
"Za ki ci nawa nima." Ya ɗauko copy ɗin menu ɗinsu daga kan table ɗinsa ya bata.
Ko buɗewa bata yi ba ta ce " abin da babu a nan zan ci."
"No problem."
Sallar azahar su ka yi. Ya ce ta jira shi zai iya kaiwa awa ɗaya kafin ya dawo. Tana ji ya rufeta da muƙulli ta waje. Ta koma kan kujerar da ta taɓa yin bacci ta kwanta ta rufe ido. Ƙamshin turaren Salwa da ya kama office ɗin yana cigaba da shigarta a hankali. Shi ma kuma da ya shiga kitchen ɗin, ƙamshin da ya rage a wuyansa tunda ya wanke hannayen a wajen alwala ne ya dinga bugarsa. Yaransa suna son zuwa ganin sabon girkin da babu a menu ɗinsu amma a karon farko ubangidan nasu bai bada wannan fuskar ba. Ya gama dafa Afghani pulao ɗinsa yana kaucewa haɗuwa da Abba. Saboda gani yake suna ganin juna zau gane me ya yiwa ƴarsa.
***
Ummi da Salwa rungume juna su ka yi cikin farinciki bayan ta koma. Alh. Usaini yana daga cikin mota yana kallonsu. Murmushi ya saki na samun nasara. Malamin tsibbun da ya bashi turarukan ya tabbatar masa da cewa babu abin da zai hana shi samun biyan ɓukata. Duk abin da zasu yi basu isa su kara dashi ba. Turaren farko na raba Taj da matarsa wanda shi ba abu bane dake gabansa, ya dai karɓa ne saboda Ummi da Salwa da za ta yi musu aikin. Sanin halin mata na barbaɗa da surutu, idan Ummi taji shiru tunda ta san inda yake za ta iya tona masa asiri. Ba dai tsoronta yake ji ba. Wani ƙuduri ya ɗora akanta wanda baya son a sami tangarɗa a gaba. Babban aikin yana ga turare na biyu wanda Taj da Hamdi basu ma ji ƙamshinsa ba. Shi ne mai muguwar tsadar wanda a sannu zai kassara Happy Taj sai dai a dinga faɗinsa kawai a labari.
"Baki ga idonta ba da ta ganni a jikinsa." Cewar Salwa tana ƴar dariya. Magana ta gaskiya ita ce yau tayi abin da bata taɓa ba. Shigarta da rungumar Taj babu guda da ta saba dashi bisa tarbiyar mahaifinta da Ahmad. Son zuciya da rashin haƙuri yasa ta tsallaka titin da Mami taso tayi amfani da kyanta taje gareshi tuntuni.
Ummi ta bata hannu su ka tafa "Muna nan dake za ki ji anyi saki nan da ƴan kwanaki"
"Banda rashin kamun kai ma ba ayi bikinsu ba amma take binsa har office? Me kike tunanin zai faru da ban je ba? Kuma fa babanta a wajen yake."
"Ɗan daudu har wani uba ne? Ƙila ma shi zai kitsa mata ya ce ta dinga zuwa. Kin san fa su sana'arsu tambaɗewa tayi yawa. Da ba ƴarsa ya aura ba ma zai iya kawo masa wata."
Salwa ta jinjina kai "ai kuwa dole ma su rabu. Ba zan ma yi zaman kishi da ƙazamai irinsu ba."
"Turaren nan ƙarshe ne. Kuma ko asiri tayi ta same shi to wanda ya bani wannan ya ce min babu wanda ya kaishi iya sihiri."
"Idan anyi aurenmu za ki kaini wajen Ummi. Ko don gudun matsala a gaba. A bani shi a hannu in dinga juyawa."
Wata uwar shewa su ka sake yi. Ummi tana ta son Salwa tayi ta tafi amma taƙi motsi. Ita kuwa ba don ta matsu ayi aikin ba da ba za ta fito ba. Ɗan jarabar gidansu Baballe yana hanya. Idan Iyaa ta faɗa masa yawonta da ya ƙaru a kwanakin nan bata san me zai yi mata ba. Wata zuciyar har tana raya mata ko su ma ƴan gidan ta samu a rufe musu baki. Kuma a kautar da idanunsu daga kanta.
***
Irin mutumci da karamcin da Yaya take gani a wajen bayin Allahn nan dake gabanta sai hamdala. Mata huɗu ne. Ɗaya ance mata ƙanwar Alhaji ce Amma. Sunan ba baƙonta bane a wurin Taj. Matar ta haɗu iya haɗuwa amma she is so down to earth in ji bature. Girman kai da nuna isa duka babu su a tare da ita. Mata ukun kuma Hajiya ce da Mama da Umma. Su kam ko cikinsu ɗaya iyakar abin da ido zai gani kenan. Allah Yasa ita ma bata yi ƙasa a gwiwa ba. Ta kira Iyaa da kuma su Anti Zinatu saboda bata san me za su tattauna ba. An dai ce mata akan maganar biki ne.
"Ranar Asabar in Allah Ya yarda maza za su kawo lefe. Sati mai zuwa muke son ayi biki ta tare." Hajiya ce take wannan bayani.
Amma kuma ta ce "ayi mana haƙuri mun zo da maganar a taƙaitaccen lokaci. Mun ga babu amfanin ayi aure kuma duka ba wani uzuri ne a gabansu ba ace tana gida har yanzu"
Anti Zinatu ta nuna musu hakan ba zai yiwu ba "Wannan gaskiya ne. To amma Hajiya kun san shiri irin namu yana buƙatar lokaci. Ina laifin wata guda ko biyu? Mai ƴaƴa mata baya rasa ɗan tanadinsa. To amma ba zai isa ace mun rufeta mun kai ɗakin miji ba gaskiya."
Jin haka Amma ta ce mata "Hajiya Zinatu mu ba baƙin juna bane. Wuri guda muka tashi. Babu zancen ɓoye ɓoye. Na tabbata kun san akan girki Yaya Hayatu ya kori ɗansa daga gida. Haka nan ba za mu manta yadda ya juyawa kyakkyawar zumuntarsa da Yaya Habibu baya akan ƙaddarar da ta same shi ba."
"Haka ne."