Kenza eBookz

Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 32

Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 32

Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 32: Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 32. "Babu wanda ya taɓa kawowa zai amince da auren nan amma gashi anyi.…

3,367 words

"Babu wanda ya taɓa kawowa zai amince da auren nan amma gashi anyi. Mu duka nan muna tsoron kada jinkiri yasa ya ɓullo da wani abin. Tunda ko me Taj ya yi baya burge shi. Don Allah ku barmu mu bawa duk maraɗa da mahassada kunya."

Ita dai Yaya jikinta ya soma sanyi. Anya ba wani abin su ka ji ba wanda yasa su ke so a gaggauta bikin nan? Kada fa azo a mayar mata da ƴa ƙaramar bazawara idan Alhaji ya canja ra'ayi.

Bata yi nauyin baki ba kuwa ta faɗa musu. "Ni dai idan kun san da matsala don Allah ku faɗa mana sai a yiwa tufkar hanci tun wuri."

"Ko ɗaya. In sha Allahu alkhairi zamu ƙulla. Mu dai fatanmu ku bamu haɗin kai. Zancen shiri kuma wallahi Innar Taj da ƴan uwanta sun ce ko tsinke kada ku damu da saye. Komai na biki su za su yi." Cewar Umma don ta kwantar musu da hankali.

"Ayi haka?"

Amma ta ce "An ma yi. Ba don abubuwan da su ka gabata ba ina da yaƙinin da Yaya Hayatu ne zai aurar da ƴaƴan gidan nan. Haka nan Allah Ya haɗa jininsu wanda a yanzu idan ina kallon Taj da Kamal su suke tuna min. Bambancin shekaru bai hana su ƙulla kyakkyawar mu'amala ba."

Yaya da Anti Zinatu sun yi ta ja amma babu yadda su ka iya da waɗannan gogaggun matan. Ƙarshe Yaya ta ce bari ta sansanar da Abba. Ɗaki ta koma ta kira shi a waya. Ya tuna yadda su ka yi da Taj yace ta amince. Zai san yadda ya yi tunda anyi aure Hamdi ba ikonsu bace. Idan su ka cigaba da ja'inja ba zai amfanesu ba. Yau ko ƙofa Taj ya ƙwanƙwasa yace a bashi matarsa basu da hurumin hanawa a shari'a. Balle kuma bidi'o'in biki da ko babu su aure ya ɗauro.

Sun nuna jindaɗinsu da amsar da ta kawo. Cikin farinciki Mama ta zayyane musu yadda su ka yi nasu tsarin bikin. Idan akwai abin da su Yaya su ke so sai su faɗa. Alhamis mai kamawa za ayi kamu. Ranar Juma'a kuma dinner. Asabar ana la'asar za su zo su ɗauki amarya. A kaita gidan Alh. Hayatu. Daga nan Taj zai ɗauketa (wannan shirin Amma ne. Tayi rantsuwar Taj ba zai fara rayuwar aure ba sai ya taka gidan mahaifinsa. Kuma da izinin uban.)

Iyaa ta ce hakan ya yi musu. Ranar asabar za su yi yininsu a gida. Kuma tana roƙon a barsu su ɗauki nauyin abinsu. Dariya ta bawa su Hajiya. Kowa ya yi na'am da yadda zaman ya kasance. Aka rabu cikin mutumci. Bayan an cika musu ciki da daddaɗan abinci.

***

"Ba za ka ci ba?"

Hamdi ta tambayi Taj bayan ya ajiye mata wani faffaɗan plate mai kyau da haɗaɗɗiyar shinkafar da sabo yasa bai jima ba ya gama dafawa. Asalinta girkin mutanen Afghanistan ne amma ya ta sami karɓuwa a wasu sassa na ƙasashen Asia. Afghani Pulao dafaffiyar shinkafar basmati ce wadda cikin kayan ƙamshin dafata harda sinadarin cumin da cardamom. Sai kuma naman ƙaramar dabba wanda ake marinating ɗinsa da kayan ƙamshi kafin a dafa shi ya yi laushi luguf. Ita kuma shinkafar ana haɗata da caras da aka yayyanka sirara kuma ƙanana. A haɗa shi da raisin (bushasshen inibi) wanda ake soyawa sama sama da sugar sannan a haɗa da nuts.

Kansa da ya soma juyawa tun baysn ya sake arba da ita yake matsawa da hannu ɗaya.

"Ki ci kawai. Bana jin yunwa."

Ba shiri ta ture plate ɗin.

"Meye haka?" Ya ɓata rai. Zuciyar tana kuma ciwo shi.

Ita ma baki ba linzami yau ta turo shi "na san me ka zuba tunda na shiga tsakaninka da Salawaitu."

Dariyar dole ta sa Taj "Salwa ce ta koma Salawaitu?"

"Gaskiya dai na faɗa. Gashi nan ranka ya ɓaci don na canja mata suna."

"Ke za ki ji daɗi a ɓata naki?" Ya tambaya yana ƙarewa yadda take murguɗe murguɗen baki kallo.

"Mutum ya daɗe bai ɓata ba. Kuma na faɗa ɗin. Salawaitu, Salwanatu, Sal..."

Hannunsa da yake jin kamar ƙwaƙwalwar kansa gareshi, yana marmarin sake dukanta ya damƙe a da ɗan uwansa ta baya. Dukanta yake so ya ƙara yi. Rashin kunyarta da a mizanin masu tunani ma wani ko kallonta ba zai yi ba idan tana yi shi ne yake jin kamar ya kama ta da duka.

"Ki ci abincin nan kafin na dawo."

Ya kama ƙofa zai fita yana ji tayi siririn tsaki. Innalillahi...har tafin ƙafarsa yake jin ɓacin rai. Garam haka ya buga ƙofa ya sake rufeta a ciki.

Ta zauna tana ta faman girgiza ƙafa. Bata so ya fita ba tare da rigimar ta girmi haka ba. Ya saketa kawai ta huta. Ta kalli abincin ta janyo plate ɗin a fusace.

"Idan ban ci ba ma waccan Salonin zai bawa." Ta faɗawa kanta domin ta sami nutsuwar ci.

*

Mota Taj ya koma. Idanunsa jawur kawai don yaƙi biyewa zuciyarsa. Shi ya tabbatar da zai taɓa lafiyarta tabbas zai ji dama a ransa. Kamal ya kira ta whtsapp.

Bawan Allah sauƙi ya samu tunda aka fara sabon treatment. Kusan babu sauran kumburi. Sai duhu da yayi wanda a da ya ɗara Taj haske. Fari ne sosai kamar duka ƴaƴan Hajiya.

"Happiness"

Ya kira shi da wata irin murya mai rauni. Abin da yake faruwa tsakaninsa da Hamdi a ƙasa da awa biyu is not normal. Ta yaya zai dinga jin son dukanta kamar ba matar aurensa ba? Yarinyar da ɗazun nan yake jin zai iya keta bille ya aikata kowacce irin rashin kunya yau ɗinnan akanta.

Da tsokana ya ce "Happy nawa na gargajiya. Ka kai Mrs Happy gidan Sajidan ko kuwa naka gidan?"

Taj ya ɗan yi murmushi "I'm in trouble Happiness. Yaushe za ka dawo?"

Salati Kamal ya yi kafin ya hau shi da faɗa "wane irin rashin haƙuri ne da kai ne Happy? Kwana nawa ya rage ta tare? Yanzu tana ina? Allah Yasa ba hotel ka kai musu ƴa ba."

"Ba shi bane. Kai ma ka san ɗazu wasa nake maka..wata matsalar ce daban."

Hankalin Kamal kwanciya ya yi. Da safe da su ka yi waya ne Taj yace masa zai je kai Hamdi gidan Sajida. Amma fa har gidan da za su zauna sai sun je. Kamal ya dinga yi masa magiyar kada ya kunyata su amma ya dage sai sun je saboda kawai jindaɗin tsokanar ɗan uwan nasa.

"Ina jin ka to. Me ya faru? Ba dai sakin ta kayi ba?"

Kamar zai yi kuka ya ce "Marinta nayi Kamal. I slapped Hamdi har hannuna ya fito a kumatunta."

Tashi tsaye Kamal ya yi. Ya koma ya zauna sannan ya kuma tashi.

"Mari? Hamdin? Me tayi?"

Yadda ta kasance daga shigowar Salwa har fitarta Taj ya faɗa masa.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil."

"Sai rashin kunya take min. Ni kuma ina jin kamar na shaƙeta na huta."

"Daina faɗa Happy. In sha Allah zan yi booking next flight na taho."

"Ana haka dama? Kana son mutum kuma kaji kana son inflicting pain a jikinsa? Happiness indai haka ake aure wallahi kada kayi. It hurts...so much."

"Kuka kake yi? Happy?" Shiru bai amsa ba "Tajuddin?"

Katse wayar Taj yayi. Ya shafa idonsa yaji shi a jiƙe.

"What is wrong with me?"

Ɗazu ma sun kallon juna da Hamdi ya yi hawayen nan. Shi yasa ya juya mata baya kafin ta gani.

Bai yarda ya sake komawa saman ba sai da su ka yi jam'in la'asar yaga fitar Abba. Ya koma ya sameta tayi sallah ita ma. Kanta a ƙasa tana ta avoiding kallonsa. Hakan ya fiye masa komai.

"Zo mu tafi."

Kamar jira take ta miƙe. Ta hanyar da su ka zo su ka koma.

Salwa baƙin naci sai da taga fitar motarsa sannan ta tashi ta tafi gida. Yau yadda zuciyarta take wasai har girkin dare ta yiwa Gwaggonta.

***

Abu ya ƙara taɓarɓarewa tsakanin Hamdi da Taj amma babu wanda ya sani. Yanzu ko a waya su ke magana sai anyi faɗa. A kwana na uku wanda ranar ne Kamal ya dawo ya sanya Taj a gaba ya kira Hamdi. Irin faɗan da suke yi ya tayar masa da hankali sosai.

"Ni wannan abu ya ishe ni. Kaje ka auri Salwa. Ka cinyeta. Ka haɗiyeta ma duka. Amma don Allah ka rabu dani. Bana sonka. Bana son auren."

Guntun tsaki ya yi "matsalata dake bakinki baya shiru. Just keep quite for once. Maybe zamu iya komawa daidai idan kina kama bakinki."

"Anƙi ɗin."

"Kin san zan iya zuwa har gidan in hukunta ki ko?" Ya gargaɗeta. Kafin ya kira kuma kamar ana azalzalar zuciyarsa. Kewarta kawai ke damunsa.

"Kuma aka ce maka iyayena za su zuba ido kayi yadda kake so?" Tana wani irin cije baki ta ce " Bar ganin Abbana yana yi maka aiki. Wallahi kana kuma taɓani idan na sanar dashi zai rama min."

"Me ya kawo zancen iyaye kuma?"

"Naga ƴaƴan masu kuɗi sun raina iyayen irinmu ne."

"Allah ki kiyayeni."

Ya soma magana Kamal ya karɓe wayar. Sallama ya yi wadda Hamdi tana ji nutsuwarta ta dawo harda gaishe shi.

"Me yake faruwa Hamdiyya?"

Kuka ta saka masa. Duk tambayar duniya ta kasa bashi amsa sai "shi ne" kawai da take ta faɗi. Da ƙyar ya rarrasheta sannan ya yi mata tambaya.

"Kina son sa?"

"Shi ma ba sona yake ba." Ta amsa da kuka.

Kamal ya kwantar da murya "wa yake ta tashi? Ƙanwata nake tambaya. Kina son Taj?"

Hamdi ta kalli ɗakinsu da babu kowa ta ƙara tabbatarwa ita kaɗai ce sannan tayi magana.

"A da ba."

"Yanzu fa?"

"Nima ban sani ba. Salawaitu yake so. Ni kuma sai in yi ta son shi? Haka ake yi?"

Murmushi ya yi. Ya sami amsarsa koda ba kai tsaye bane. "A'a gaskiya. Abin da nake so dake dai don Allah ki bar abubuwan nan tsakaninmu. In ki ka bari wani yaji har aka raba auren ina mai tabbatar miki Salawaitun zai aura."

Wawan duka Taj ya kai masa a baya. Baya ƙaunar zancen Salwa tuntuni balle yanzu da yake cikin damuwa shi da amaryarsa.

Ajiyar zuciya tayi "Ba zan faɗa ba"

A ransa yake auno yadda zai tsokanesu duk su biyun idan komai ya daidaita. Yana gama wayar ya koma kan Taj.

"Happy ina ganin wannan maganar fa ba tamu bace mu biyu."

"Me kake nufi? In faɗawa wani? In aka ce na sake ta fa?" Ya soma magana cikin tashin hankali.

Nutsuwa Kamal ya yi wanda yasa Taj ya gyara zama. "Me ka ke tunani?"

"Ka faɗawa Inna."

"Inna kuma? Me za tayi?"

"Duk matsalar duniya Happy uwa ce ƙarshenta. Ko bata magance ba in sha Allahu za ta faɗa maka yadda za ka yi. Sannan ga addu'arta da bata da shamaki. Abin naku kamar asiri."

Kallonsa Taj ya yi "kai duka matsalolinka kake faɗawa Hajiya?"

"Wanda ya dace lallai ta sani ba."

Kallon tuhuma Taj ya yi masa "Me yasa ka ɓoye mata ciwonka bayan ka san idan tayi addu'a za ta karɓu?"

Gaban Kamal faɗuwa yayi. Cikin sarƙewar harshe ya ce "ai...dama. hhhh. Saboda gudun tashin hankalinsu ne."

"I see" kawai Taj ya ce.

Kamal duk ya ruɗe "Kayi haƙuri don Allah. Ban ɓoye da wata manufa ba."

A nutse Taj ya karance shi. Inda ya dosa daban da inda yake tunanin Kamal ya dosa. Kenan akwai abin da Happiness yake ɓoyewa wanda bai sani ba? Shi ne mai dogon bakin faɗa masa komai wato.

"Akwai abin da ka ke ɓoye mana ne banda allergy da asirinka ya tonu?"

Wani gwauron numfashi da Kamal yaja sai da Taj yaji hantar cikinsa ta kaɗa. Babu shakka akwai sirrin da bai sani ba. Zai kuma sani ne don Kamal bai isa ya ninke shi baibai ba tunda ya gano da matsala.

"Shi ne. Allergy ɗin ne. A China ma ya tashi. Ba ka ga har wani duhu nayi ba?"

"Na gani. Yanzu nake shirin cewa ko man bleaching ɗin naka ne ya ƙare a can?"

Kamal ya taso ya yi kansa. Su ka gama zolayar juna sannan Taj ya koma cikin Happy Taj.

*** Shiru shiru Salwa tana jiran wayar Taj amma ko flashing babu. Hankalinta ya soma tashi. Kwanakin da aka ɗiba domin aurensu sun kusa. Ta kira Mami tana ta kuka. Mamin ta ce mata ta taho gida.

"Idan na ƙara nesa dashi ai babu lallai ya tuna dani ma."

"Ki taho nace miki. Zan sake shiri."

Ta samu Salwan ta amince za ta dawo. Sai dai bata san ta ina za ta fara ba. Alh. Mukhtar ya sake kiran Alhaji akan maganar ranar da za su je wajen kawunsa amma ƙememe yaƙi ɗauka. Baya son yi masa ƙarya sannan kuma baya son faɗa masa gaskiya. Idan ya faɗi gaskiyar girmansa da kullum yake tattali ne zai zube. Daga baya ne ya tausaya masa da yawan wayar ya ɗauka ya ce ya ƙara wata guda. Saboda wasu uzurirrika da su ka taso masa. Alh. Mukhtar dai tunda ya sami amsar bawa Mami hankalinsa ya kwanta.

"Nufinsa sai waccan yarinyar ta tare sannan zai auri Salwa?"

"Ina laifi?"

"Ai kuwa akwai shi tunda nima ban zauna da kishiya ba. Ƴata ma daga ita sai miji."

***

Girki ya faɗo kan Inna ranar Juma'a. Da ta haɗa abincin Alhaji Bishir na shigowa ta ce ya kai masa. Kuma bata leƙa ɓangaren ba kamar yadda su ka saba. Mai girki za ta je ta zuba masa abinci su yi hira. Idan ya gama ta aikawa sauran matan cewa ya dawo. Duk za su zo a ɗan taɓa hira sannan su tashi.

Abinci ya yi kusan awa guda Alhaji yana kallonsa. Ga yunwa ga gajiya amma yaƙi zubawa. So yake yaga iya gudun ruwan Zainabu Abu. To dai tun bayan masallaci har la'asar bata shigo ba. Da ya dawo daga masallaci cikin gidan ya shiga ya wuce ɗakinta. Jallabiya ce a jikinsa yana danna counter mai fasalin carbi ta sama. Babu kowa a falo. Ya shige uwar ɗakin. Yana sanya ƙafa ita kuma tana ɗora waya a kunne. Don ya san da wa take magana ta kira Taj da sabon suna.

"Angon Hamdi"

A tunanin Alhaji ko da gangan ta ɗauki wayar. Hannu yasa ya karɓe. Ganin sunan Taj da gaske sai ya miƙa mata. Ita kuwa ta saka speaker yadda ta saba idan ita kaɗai ce a ɗakin saboda wayarsu bata ƙarewa da wuri.

"Inna kina ji na kuwa?"

"Me ka ce?"

Bai san yadda za ta ɗauki maganar ba amma dole ya đauki shawarar Kamal yau. Faɗan da su ka yi da Hamdi a motarsa Allah ne kawai ya bashi ikon mallakar kansa ya buɗe mata ƙofa ya ce ta fita. Daga zuwa kai mata kati cibi ya zama ƙari. Saboda yau ta iya bakinta bata ce komai ba shi ne ya ce ba a yi mata tarbiyar godiya ba. Ai kamar jira take. Tunda ta buɗe baki ta fara surfa rashin kunya sai da yaji inama bai je gidan ba.

Gyaran murya ya yi "na ce ko za a fasa bikin?"

Alhaji da ya kama hanyar fita sai gashi ya dawo. Inna tayi sauri za ta mayar da wayar iya kunnenta ya harɗe fuska. Taɓe baki tayi a ranta ta ce ana so ana kaiwa kasuwa. Dama taji yadda ya rikice da yaji bashi da lafiya.

"Kai da ka san baka son biki ne yasa ka bari mu ka zazzage asusunmu? Haƙuri za ka yi kawai."

"Uhmmm, Inna ba bikin ba. Auren nake nufi."

Bata san lokacin da ta gyara zama ba. "Ka fara shaye shaye ne? Auren? Saki fa kenan."

Baya son yawan tada maganar don ransa ƙara ɓaci yake. Amma dolensa ya faɗa mata gaskiya.

"Matsaloli muke ta samu. Kullum sai mun yi faɗa."

"Wannan shaiɗan ne kawai. Ku dage da addu'a." Ta ce, hankalinta ya soma kwanciya.

"Inna har marinta nayi."

Shiru ya yi yana jiran yaji me za ta ce. Ta kalli Alhaji shi ma ya kalleta.

"Taj ka sameni a gidan Yaya Malam (yayanta na biyu.)"

Ta miƙe ta dubi Alhaji da ya yi tsaye kamar an dasa shi.

"Ka yi min izinin fita?"

"Jeki."

Hijabi kawai ta ɗauka ta fita ta shiga ɗakunan su Hajiya ta ce musu ga inda za ta je. Duk su ka bata saƙon gaisuwa ga iyalin gidan. Direba ta kira su ka tafi. Aka bar Alhaji da tunani. Yadda hankalinsa ya tashi sai da yaji kamar ya ce Taj din yazo gida. Abin da mamaki ace wai shi ne da marin mace. Wace irin tarbiyya Habibu ya yiwa ƴaƴansa?

*

Ƙasa da awa guda uwa da ɗa su ka keɓe a falon maigidan. Taj ya zayyane mata abubuwan da su ka faru. Bata ko tambaye shi me ya kai shi tafiya da Hamdi wurin sana'arsa ba.

"Idan na fahimta da kyau tun daga zuwan Salwa ku ka fara faɗan?"

"Haka ne. Na so yi mata bayanin babu komai a tsakaninmu amma ta rufe ido tana gaya min maganganu."

Inna tayi salati sannan ta ce "ya maganar azkar? Kana yi?"

Kai ya sunkuyar "ina yi."

"Ni da kai ne Taj. Ka faɗa min gaskiya."

"Allah ina ƙoƙartawa Inna." Ya kuma faɗa don ta yarda da shi.

Aikin gama ya riga ya gama. Ko yana yi dama ba zai hana ƙaddara da ikon Allah faruwa ba. Sai dai ya sauƙaƙa. Gargaɗinsa tayi akan kada ya yarda su sake haɗuwa. Wayar ma ko ita ta kira kada ya ɗauka. Sannan mafi mahimmanci ya tabbatar kalmar saki bata shiga tsakaninsu ba.

"Ka tashi ka tafi. Za ka ji ni in sha Allah idan mun gama magana da Yaya Malam. In ma sihiri ne to in sha Allah zai koma ya ci mai shi. Addu'a, sadaka, qiyamul laili da hanyoyin neman kusanci da Allah nake so ka runguma kaji ko?"

Ya gyaɗa mata kai kamar yaro. "Ki yi haƙuri na tayar miki da hankali. Alhaji ya kamata na nema..."

Wani irin tausayinsa ne ya kama ta. Ta dafa kansa tayi masa addu'o'in neman tsari wanda Ayatul Kursiyyu ke kan gaba. Sai da ya tafi ta fashe da kuka. Duk ya wani rame. Kana ganinsa ka san hankalinsa ne ba a kwance ba. A gidan ta zauna har yayan nata ya dawo ta faɗa masa. Ya kwantar mata da hankali.

"Kada ki ƙulla sharri akan wanda ki ke zargi. Shi zargi dama bashi da kyau a addini. Zan kira shi ya zo gobe in sha Allah."

"Yaya har zasu yi lafiya kafin bikin?" Ta tambaye shi da damuwa.

"Ke ta biki ma kike wato?"

"A'a, tsorona kada ta tare yadda yake cewa yana jin kamar yayi ta dukanta yaje ya lahanta ƴar mutane."

Kwantar mata da hankali ya yi. "Allah zamu roƙa ba mutum ba. Shi kuma ba ayi maSa gaggawa. Tunda ya ce idan mun roƙa zai bamu to ki saka ranki a inuwa. Ko daga ina matsalar take bata wuce Qulhuwallahu, Falaqi da Nasi ba."

Da ƙwarin gwiwarta ta fita daga gidan. A ranar yadda ta hana idonta bacci haka ta tada Taj. Shi kuma ya sami kansa da turawa Hamdi saƙo.

(Idan Allah Yasa kin gani kafin safiya ki tashi ki yi sallah da addu'a. Idan akwai alkhairi cikin aurenmu Allah Ya warware mana matsala.)

Sai uku da rabi ta gani da ta tashi fitsari. Ta ɗauro alwala ta zauna tana ta kuka. Zee na jinta amma ta ƙyale. Yaya ce ta bata aikin sanya mata ido saboda kwanakin nan kowa ya san ta canja.

A ɓangaren Alh. Hayatu kuwa, yana ganin shigowar Inna ya kira Yaya Malam.

"Ka biyo sahun ɗanka ne?" Malam ya faɗi kai tsaye domin duka gidansu dai haushinsa su ke ji.

Murje ido ya yi tunda in ba a nan ba babu wanda zai tambaya kuma "A gabana ta fara wayar shi yasa. Da gaske ya mari matarsa?"

"Ƙwarai kuwa."

"Kaga abin da nake faɗa ai. Namiji mai irin sana'arsa fa ji yake kamar shi ma mace ne. Shi yasa yake daidaita tunaninsa da nata. Cikakken namiji ba zai fara kai hannu daga aure ko wata ba ayi ba."

Yaya Malam dai dariya kawai ya yi. Ya shaida duk wata rigima da yake yi bata yi tasirin hana shi son ɗansa ba. Abin da yaji ya faɗa masa. Ya yi godiya su ka yi sallama.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull