Kenza eBookz

Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 3

Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 3

Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 3: Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 3. Za a iya cewa Taj da Kamal wasu manyan jigo ne na farincikin gidan…

3,331 words

Za a iya cewa Taj da Kamal wasu manyan jigo ne na farincikin gidan Alhaji. Indai suna gida to in sha Allahu dariya da nishaɗi baya yankewa. Zolaya da wasa duk halinsu ne. Har suna su ka sanyawa juna. Kamal ya kira Taj Happy, shi kuma Taj ya kira shi Happiness. Irin faɗan nan na sakonni da wuya kaga sun yi. Sannan daga yayyensu har ƙanne ba za ka ji wanda ya kai ƙararsu akan sun masa ba daidai ba. Duk kuwa da kasancewar Taj mai tsokana lamba ɗaya. To amma yana da tsoron yin laifin da za a hukunta shi. Shi kuwa Kamal dama green snake ne. Sai ya yi abu ya koma gefe kamar ba shi ba.

Tun tasowarsu akwai wata irin shaƙuwa ta musamman tsakanin Alhaji da Taj. Shi dai da zarar mahaifinsu ya dawo to ya gama wasu wasanni. Yana daga cikin lokutan da akan gansu wuri daban daban shi da Kamal. A gefensa yake zama yana yi masa tambayoyi musamman akan kasuwanci. Nan da nan ya zama sunansa abokan harkokin Alhajin su ka fi sani. Kowa ya buɗe baki sai ya ce Taj. Har dai aka fara hannunka mai sanda a gidan ana cewa da alama shi zai gaji Alhajin. Yawan maganar yasa Inna ta fara jin abin yana damunta. Bata son rigima ta ɓullo daga ɓangarenta. Shi yasa wata rana su na zaune su biyu da Alhajin ta tayar masa da zancen.

"To ke banda abin ki mene ne a ciki? Duk uba ai yana son magaji a fannin da ya yi zarra musamman idan halattacce ne."

Wasa taga ya mayar da zancen ta girgiza kai.

"Kaga yana da yayye. Idan ana cewa magajinka wani zai yi zaton irin abin nan ne na son ture wasu don wata manufa."

Kallonta ya yi yaga sosai ta shiga damuwa.

"Ku mata sai a barku. Tunaninku kullum babu nisa. Musulunci dai ya riga ya gama mana komai. Yau ko dama na kwanta yadda shari'a ta tsara haka za a raba abin da na bari a bawa ƴaƴana. Babu wani fifiko."

"Na sani"

"Amma duk da haka kina damuwa saboda kada a ce Hayatu ya fifita ɗanki akan na sauran. Ƙila ma kina ƙarawa da cewa za a zargi ko don mahaifiyarki ƙanwar mahaifina ce."

"A'a wallahi" ta ce da sauri.

Ya sake yin murmushi sannan ya ɗan tuna mata baya. A gidansu cikin maza su goma sha uku shi kaɗai ne ɗan kasuwa kamar baban su. Sauran duk aikin gwamnati su ke yi. Shi kuwa ya ajiye kwalin tun daga degree na farko ya rungumi sana'ar gidan ba tare da an tauye ƴan uwansa da komai ba. Duk abin da ya tara yanzu arziƙinsa ne na guminsa. Ya ma zamana duka ƴan uwan nasa duk wanda ɗansa namiji ya gama sakandire sai ya tura masa shi kasuwa na shekara ɗaya. A haka yanzu akwai mutum bakwai cikin ƴaƴansu da su ke jikinsa.

"Zan yi maganin damuwar nan anjima idan an zo cin abincin dare."

Bai manta ba kuwa. Dama al'adar gidan idan ba baƙi gare shi ba duka tare ake cin abinci a babban falo. Ƴan shekaru kusa da juna ake haɗawa a kwano guda. Matansa ma yawanci tare su ke ci. Ana gamawa yaran za su nufe shi da buƙatunsu. Ko fensir ne ya karye sun fi gane su sanar dashi. Yana daga zaune zai sa a bashi reza don yafi gane mata ya fiƙe. Wasu ya koya musu homework. Masu buƙatar kuɗi ko wani abu makamancin haka duk a wannan zaman ake yi. Ana gamawa zai ja su sallar Isha sannan ya tashi. Su kuma daga nan za su ɓalle da hira. Ƙananun da duk mai ra'ayi su tarkata su koma wurin Hajiya indai ba girkinta bane domin jin daɗaɗan tatsuniyoyi.

"Mal. Bishir wai me ka ke son zama ne idan ka girma?"

Bishir ya ɗago kai daga rubutun da yake yi na homework ya kalli baban nasu.

"Shoe shiner."

Falon gabaɗaya aka bushe da dariya harda Alhajin. Shekarar Bishir bakwai a lokacin.

Kuka ya soma yi yana cewa "Alhaji kaga suna yi min dariya ko?"

"Rabu dasu. Tambayar ma ta saraya a kanka sai ka ƙara girma. Duk wanda ya sake dariya kuma bana bashi da takalmin sallah. Dama kai zan bawa ka raba."

Da haka ya kawo ƙarshen kukan nasa. Ya mayar da tambayar ka ga Abba.

"Babana fa?"

Murmushi ya yi "Alhaji ni police zan zama."

"Ni dai bana son khaki Abba. Don Allah ka zaɓi aikin da ba zai dinga hana ni bacci mai daɗi ba" cewar Mama.

Alh. Hayatu ya ce a ƙyale yara a bisu da addu'a.

"Taj kuma fa?"

Abin nema ya samu. Kowa ya zuba masa ido ana jiran a ji ya ce kasuwanci irin na baban nasa sai ya basu mugun mamaki.

"Chef! Mai girki." Ya ce hankali kwance yana murmushi.

Da yake yafi kusa da Umma a inda yake zaune bata san ma lokacin da ta buge bakinsa ba saboda wani hargitsatsen kallo da Alhaji ya watsa masa.

"Bar dukansa Jamila. Barshi ya maimaita."

Ko ɗar bai ji ba ya sake faɗin abin da ya ce da ƙwarin gwiwa.

"Chef. Mai dafa abinci a restau..."

"TAJUDDIN!!!"

Tsawar ta gigita kowa. Ƴar autarsu ma kuka ta saka harda zubar da abincin da aka ajiye a gabanta tana ci da kanta.

"Ku tashi ku bani wuri." Ya faɗa a fusace.

Da yake a lokacin sun kai shekara sha huɗu shi da Kamal duk da hankalinsu. Shi yasa Taj ya gane abin da ya faɗa bai sami karɓuwa ba. Bin sahun ƴan uwansa ya yi ya tashi.

"Ina za ka? Zama zaka yi ka faɗa min me ya burge ka da daudanci har kake tunanin kawo min wannan shaiɗancin cikin gida."

A tsorace ya zauna yana kallo kowa ya tashi har iyayensu mata. Alhaji ya ɗan sausauta murya don ji yake kamar ya fara duka akan ɗan da yake matuƙar danne soyayyarsa. Ya tambaye shi ko ya taɓa yin girki a rayuwarsa.

"Abincin da aka gama ci yanzu ma ni nayi miya. Wallahi Alhaji na iya girki sosai. Indai babu islamiyya ni nake na dare."

Sai da ya cije leɓe don wani irin sarawa kansa ya yi sannan ya ce "kirawo min uwayenka ka ce su same ni a ɗaki."

***

A ɗakin Hajiya su ka tare su huɗu ashe suna ta caccakar Mama. Musamman Umma wadda ta jima da hango ɓacin rana a dalilin wannan abu.

"Na sha faɗa miki ki hana yaron nan shiga kitchen ki ka ƙi. Tun ana ɓare maggi har ta kai yana ɗora sanwar gidan nan."

Mama da karayar murya ta ce "saboda Allah yanzu a ce mutum yana da yaro amma ba zai koya masa ayyukan cikin gida ba? Girki ai ba lallai sai mace ba. Kuma ra'ayinsa ne tunda duk yadda su ke da Kamal shi ko magin baya ɓarewa."

Hajiya ta ce "Amma tun farko kin san Alhaji yaƙi jinin ganin mazan gidan nan da tsintsiya ma balle girki. Yana gani yake cewa a daina saka su kada su zama ƴan daudu. Ko kin manta tashin hankalin da aka taɓa yi akan gugar kuɓewa?"

Wata rana ne kusan shekara uku da su ka wuce mai aikinsu ta fita bata dawo da wuri ba. Girkin Hajiya ne ita ma sun fita dubiya dukkansu. Suna dawowa taga ba'ayi tuwon dare ba. Shi ne ta rabawa Ahmad, Kamal da Taj gugar kuɓewa ita kuma da taimakon yan matan gidan ta ɗora tuwo. Alhaji da ya shigo yaga suna aikin nan a falo ya dinga faɗa ba ji ba gani. Sai da ya yi sati baya cin abincin gidan yana kuma gargadi da tuna musu aikin namiji da mace a gida ba ɗaya bane.

Mama ta ɗan kalli Inna da tayi shiru kawai tana kallonsu. "Ki ce wani abu mana. Ko kema laifina kike gani?"

"Laifi kamar yaya? Neman mafita kawai zamu yi kafin ya tasa mu a gaba don na san..."

Laluben ɗakin da Taj ya ɗaga da sallama ya katse mata magana.

"Alhaji yana kiranku a samansa."

Hajiya kiransa tayi ganin jikinsa duk ya yi sanyi.

"Girki ko a gidanka kana da damar yi Taj amma kada ka sake cewa za ka zama mai abinci ko daɗin ji babu. Duk wani namiji mai sana'ar abinci ɗan daudu ne. Su kuwa Allah baya son su tunda sun zaɓi jinsi kishiyar wanda ya basu."

Kai ya gyaɗa kawai ya fice. Sanin cewa zai haɗu da Ahmad da Kamal kuma lallai ba za su goyi bayansa ba sai ya gudu ɗakin Inna. Wuri ya samu ya kwanta ya rufe idanunsa yana tunani.

Kasuwanci da yake nacin koyo a wurin Alhaji ba don komai bane sai don yana da muradin buɗe gidan abincin da yake son ya yi suna. A rayuwarsa babu inda yake shiga yaji kamar an sabunta masa duniya kamar kitchen. Kuma a iya saninsa maza da yawa su na girki. Suna da shekara goma Alhaji ke kai yara Umra. Idan mutum ya yi shabiyar a kai shi Hajji. A Saudiyya in ka cire Takaru babu inda ya ga mata suna sayar da wani abu na ci. Maza ke girkawa su sayar. Maza musulmai magidanta waɗanda basu da wata siffa da duk hangen mutum zai danganta su da mata. Idan sana'ar haramtacciya ce ga namiji da waɗannan basu kai labari ba. Shi kam yana son girki kuma in Allah Ya so ita ce sana'ar da zai yi.

A ɗakin Alhaji kuwa faɗansa har falon ƙasa. Don ma ƴaƴan kowa ya shige ɗaki. Manyan sun haɗe kawunansu da ƙananan a ɗakunan iyayensu a ƙasa.

Ya fusata sosai don ko da su ka shiga ɗakin maganinsa na hawan jini yake sha.

"Ni za ku ha'inta? Girkin nan ba yau ya fara ba tunda ya ce shi ya yi miyar dare. Ace ko sau ɗaya idanuna basu taɓa gani ba. Abin da mamaki."

Mama ce ta fara bada haƙuri "na bari ne kawai saboda ganin yawanci gidajen da su ke da yara maza duk ana koya musu girki. Hakan bai sa sun yi koyi da ɗabi'un mata ba."

Cikin faɗa ya ce mata gidansa babu maza da yawa. A cikin mata ashirin da uku a rasa me yin girki sai maza? Shi yasa yake sanya ido sosai saboda idan ya yi sake tabbas mazan za su iya jin cewa kwaikwayon yayyensu mata ba laifi bane. Ko ɗankwali ya gani a hannun ɗansa ya dinga faɗa kenan.

"Da irin wannan sakacin wani yaro a unguwarmu ana ji ana gani wallahi ya zama cikakken ɗan daudu. Gidansu akwai mazan ma amma daga sai ga Habibu ya koma Simagade a unguwa."

Gashi dai faɗa yake yi amma faɗin wannan suna sai da ya sanya Hajiya da Mama yin ƴar dariya. Umma da Inna dai a murmushi su ka tsaya. Ai kuwa sun janyowa kawunansu sabon faɗa. Ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Musamman Mama da a yau tayi nadamar amsa sunan uwar maza a gidan.

"Dole ki yi dariya mana tunda ba ɗanki bane. Da alamu da gangan ma ki ka nemi ɓata min rayuwar yaro saboda baki san daɗin haihuwar namiji ba."

Ba ita da ya yiwa gori ba, dukkaninsu hankulansu tashi su ka yi. Mama ta saka kuka, Umma da Inna su na taya ta. Hajiya kuwa fiƙe idanu tayi ta ɗauki ragamar girmanta.

"A'a fa Alhaji. Akan ƴaƴanka ba za mu lamunci irin wannan ba. Kai ka koya mana zama da juna. Tunda mu ka kai yanzu kuwa wallahi ba za mu yarda ka haddasa mana rigimar da bamu yi da ƙuruciya ba."

"Ba akan ƴaƴana za ki ce ba. Ki fito fili ki faɗa min cewa akan Taj ba za ku yi min biyayya ba." Ya dubi Inna ya cigaba da sababi "wato sai da ki ka ga lamari ya lalace sannan ki ka ankarar dani riƙon sakainar kashin da ake yiwa ɗana don kawai ana ƙyashin kusanci na da shi."

"Na shiga uku. Alhaji yaushe mu ka yi haka?" Ta faɗi a ɗimauce ganin ƴan uwanta sun zuba mata ido.

Shi a ganinsa babu dalilin da zai sa taji wani ɗar a zuciyarta. Ya riga ya santa da kawaici saboda haka don ana yabon ɗanta a tunaninsa bai isa dalilin maganarsu ta ɗazu ba. Tabbas ganin rayuwarsa ta ɗauko hanyar gurɓacewa a hannun uwar riƙonsa shi yasa tayi magana.

Su Hajiya ficewa su ka yi aka rasa mai tambayarta abin da ya faru ma. Tana kuka ta tashi za ta bisu domin kwance wannan ɗauri da maigidan ya yi mata ya hanata fita. Dama girkinta ne. Sai kawai ya ce idan ta fita daga ɗakin ba da yawunsa ba. RAYUWA DA GIƁI 4

Batul Mamman💖

***

Manyan gidan a wannan rana basu ga bambancin dare da wuni ba. Kusan babu wanda ya runtsa tsakanin maigidan da matansa. Abin da yake faruwa baƙo ne a wurinsu. Basu saba da rigima ba sai gashi dare ɗaya ana gab da samun gagarumar ɓaraka.

Ita dai Inna daga sallar asuba ta fake da ɗora kunun karin kumallo ta sauko. Bata zame ko ina ba sai ɗakin Mama. Akan sallaya ta sameta idanu sun kumbure. Jikinta a mace ta fita ta kira Umma da Hajiya su ka dawo ɗakin tare. Kai a ƙasa ta labarta musu ainihin yadda su ka yi da Alhaji jiya.

"Ni wallahi ba da wata manufa nayi maganar ba. Na tashi gidanmu babu ƴan uba amma tsakanin yayyena sai babba ya kau ta hanyar aure ko barin gari sannan mai bi masa yake ɗaukar ragamar gidan. Ban san gudun kada a gaba yaran nan su sami raunin zumunci a dalilin haka ni zai jawowa matsala ba."

Umma ta kalleta babu wannan fara'ar ta kodayaushe "To amma me ki ka gani a gidan nan da yasa ki tunkarar Alhaji da zancen? Cikinmu wata ta canja miki ne kuma ta nuna saboda kusancin Alhaji da Taj tayi haka?"

"Ko kusa. Nayi masa magana ne kawai akan ya dinga nuna sauran ƴaƴan musamman Ahmad da Kamal da su ke manya kamar yadda ya nuna shi."

"Maganar girkin fa?" Umma ta sake tambaya don ita so take a warware komai.

"Yadda ba ku ɗauke shi laifi ba nima ban ɗauka ba. Wallahi ko kusa ni ban yi masa zancen da ya shafi haka ba. Ba gashi a ranar girkina ya yi miyar ba?"

Wata tambayar Umma ta so yi Mama ta katseta.

"Ni ban sakawa raina komai ba. Jiya Hajiya ta ƙara min nasiha akan idan muka bari wannan maganar ta girmi haka to zaman gidan nan zai daina yiwa kowaccenmu daɗi. Saboda haka zance ya wuce."

Inna sai godiya da farinciki. Bata fita daga ɗakin ba sai da su ka koma wata hirar ana ta dariya. Da rana su ka kira Taj cikin lumana su ka rarrashe shi akan ya yar da wannan buri don ba mai yiwuwa bane. Mama tayi masa nasiha sosai akan yiwa iyaye biyayya.

"Ka cigaba da bin Alhaji kasuwa ranakun da babu makaranta amma daga yanzu tsakaninka da kitchen sai hange. Don Allah kada ka bari zancen nan ya koma tasowa a gidan nan."

Nuna musu ya yi kamar maganar ta mutu, ashe suma tayi.

Shi da Kamal sun kammala sakandire suna da shekara goma sha shida da sakamako mai kyau. Alhaji kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha ranar da su ka kawo takardunsu. Dama tuni ya tura Ahmad ƙasar India inda yake haɗa degree ɗinsa a fannin Computer Science. Zaɓi ya basu tsakanin Dubai, India ko China. Burinsa su zaɓa cikin ƙasashen da su ke cibiyar kasuwanci.

"Alhaji mun fi son zuwa wurin Yaya." Cewar Taj.

Kamal ya yi Taj wani irin kallo sannan ya ce "ni dai Dubai."

Kallonsu ya yi a tsanake. Da wuya zaɓinsu yake bambanta. Bai kuma saka ran samun haka ba ta ɓangaren karatun da zai rabasu na ƴan shekaru.

"Anya kuwa Happy da Happiness za su iya rabuwa na shekara huɗu? Ku dai sake shawara ku zaɓi waje ɗaya."

Kamal ya kalli Taj da sanyin jiki. Ya ɗauka sun gama magana akan za su zaɓi Dubai. Burinsa ya koyo larabci banda karatun da za su yi. Sannan idan da faraga ya sami wani balaraben malamin ya danɗaƙi haddarsa da kyau ta ƙara zama. Kuma lafiya ƙalau Taj ɗin ya amince har da cewa shi ma zai yi. To me ya kawo wannan sauyi?

Alhaji bai ce musu komai ba amma ya fahimci akwai matsala tsakanin yaran. Sai bayan kwana biyu ya kira kowannensu gefe don jin me yake faruwa. A yadda ya fahimta zaɓinsu bai zo ɗaya ba. Kuma kowanne yana so ɗan uwansa ya bi ra'ayinsa. Kamal sai daɗa kwaɗaitawa Taj koyon larabci yake. Shi kuma duk da yana so amma haka kawai zuciyarsa tafi kwantawa da India. Sulhu ya yi musu da alƙawarin kowa zai sami inda yake so.

Harka ta kuɗi cikin ɗan ƙanƙanin lokaci an gama yiwa kowa cuku-cukun samun gurbin karatu har ana shirin tafiya. Iyayensu mata su ka sha kuka kamar lokacin tafiyar Ahmad. Ƴan uwansu hatta na gidan miji don an fara aurarwa a gidan duka aka haɗu a filin jirgi wurin rakiya.

Alhaji da kansa zai kaisu makaranta. Dubai su ka fara zuwa saboda karatun Kamal saura kwanaki a fara. Ya biya komai ya tabbatar ya yi settling sannan su ka wuce India. Ahmad ya taho Mumbai ya tarbesu su ka rankaya Hyderabad tare. Gari daban za su zauna da Taj amma haka ya zauna da shi aka gama komai. Bayan sun raka Alhaji filin jirgi ya sake bin Taj har hostel ɗin makarantarsu, Osmania University ya tabbatar babu matsala sannan ya wuce makaranta.

***

Washegari Taj ya fita ganin gari. Karatunsu sai nan da kwana goma masu zuwa. Yana cikin yawo ya ci karo da wani katafaren ginin gidan abinci na alfarma. Mutanen dake shige da fice a wajen ba za su ƙirgu ba. Murmushin takaici ya yi. Ina ma iyayensa sun bashi goyon baya. Da watarana idan Allah Ya albarkaci nemansa zai iya mallakar wuri irin wannan.

Baya tare da yunwa amma yana son ganin wurin. Musamman kitchen da masu girki. Wurin shiga ya lura layi ake bi. Gashi ginin hawa biyar ne amma ko ina ka kalla tunda zagaye yake da gilas kana hango cikowar mutane. Da kansa ya haƙura da shigar ya kama zagayen ƙayataccen ginin yana mai son ganin iya faɗinsa. Ƙamshin girki mai tada kwantacciyar yunwa gami da muryoyi da ƙarar kayan kitchen yaji yana cikin tafiya. Da sauri kuwa ya manna goshinsa da gilas ɗin wajen yana ganin yadda ake kai kawo a wani makeken kitchen cikin tsari duk a ƙoƙarin ciyar da kwastomomi. Zuciyarsa a take ta soma harbawa. Yaji saukar nishaɗi da farinciki a ransa. Bai san minti nawa ya kwasa yana bawa idonsa abinci ba sai da yaji an taɓa kafaɗarsa an yi magana da yaren punjabi, guda cikin yarukan ƙasar.

Da sauri ya juya yaga wani ɗan dattijo sanye da t-shirt da wando ya ɗaure ƙugunsa da apron mai tambari da sunan gidan abincin. Kansa wata irin hula ce kamar ta wanka amma ita mai laushi ce. Ana amfani da ita domin hana zubar gashi cikin abinci. A shekaru a ƙiyasin idonsa zai yi sa'an Alhajinsa.

Daburcewa Taj ya yi ya matsa baya a tsorace yana cewa "I'm sorry. Sorry. Sorry."

Hanyar komawa yake nema don tsoronsa ɗaya kada mutumin ya haɗa shi da security a ce me ya kawo shi nan.

Murmushi mutumin ya yi ya ce "hungry?" Don dama ita ce tambayar da ya yi masa da farko.

"Come inside" ya umarce shi da yaga yana neman guduwa.

"Am sorry Sir. Please. I won't come again." Ya ce zuciyarsa na faman lugude a ƙirjinsa.

Ko sauraronsa mutumin bai yi ba ya riƙe hannun ƙofar da ya biyo ya fito zai koma. Buɗewarsa ke da wuya wani jibgegen mutumi ya tare ƙofar ya yi magana da yarensu yana kallonsa.

Dattijon sai ya amsa da turanci yana yiwa Taj kallon in kuma ka musa babu ruwana. Nunawa ya yi ciki za su shigo da shi sannan ba laifi ya yi masa ba.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull