Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 37
Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 37: Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 37. Manyan kuma dariya su ka yi. Su sun fi sanin baban nasu akan ƴan baya…
3,330 words
Manyan kuma dariya su ka yi. Su sun fi sanin baban nasu akan ƴan baya baya da su ka taso lokacin da ya fara fushi da Taj. Tsaurin ra'ayinsa bai hana shi kamanta mu'amalantar iyalinsa yanda addini ya tsara bakin gwargwado a lokacin ba. Dalilin da yasa ma ya sami damar iya tafiyar dasu akan ra'ayinsa kenan koda zuƙatansu basa son abu. Ya yi ƙoƙarin toshe duk wata kafa da zata sa iyalinsa su butulce masa.
Cikin jikokin wani ɗan shekara biyar zuwa ya yi jikinsa ya tsaya yana fuskantar wadda ta ce ko Alhaji ne ya kwashe kayan.
"Alhaji ba ya yin aikin mata. Shi ba ɗan daudu bane."
Tsit falon yayi. Kunya ta kama su aka rasa mai kwaɓarsa. Alhaji ya jinjina maganar musamman da ya karanci yadda kowa ya sha jinin jikinsa. Duk sai yaji babu daɗi.
Murmushi ya yi na jin kunyarsu ya dafa yaron "kwashe kaya da ninkewa ai ba aikin mata bane kaɗai Amir. Duk wanda zai iya saka kaya ya kamata ace zai iya ninke su."
"Laahhh, Uncle Taj ma ba ɗan daudu bane kenan ko?"
"Me yasa ka ce haka?" Alhaji ya tambayi yaron da sakakkiyar fuska don ya bashi amsa.
"Saboda duk wanda ya iya cin abinci shi ma ya kamata ya iya dafawa."
Mahaifiyar Amir kasa tsayuwa tayi saboda tsoron me Alhaji zai yi bayan jin amsarsa. Ta kalli yayyenta su Yaya Kubra tana neman ceto.
Matan gidan ne ƙarshen shigowa dama. Saboda haka daga baki bakin ƙofa suke tsaye. Hajiya tana kallon idon Alhaji ta yiwa Amir tambaya.
"Kai ka san waye ɗan daudu?"
"Eh mana" ya amsa da karsashi na yaron da aka yiwa tambaya mai sauƙi "sune masu yin haka..." ya ɗaga hannuwa ya tafa da iska "ahayyyeee cass, rass... ko?"
Hannuwansa Bishir ya yi saurin riƙewa ya ce "dare ya yi, ayi shirin bacci a kwanta haka nan."
Da sauri sauri su ka dinga watsewa aka bar Alhaji a tsaye cikin tunani da wata irin kunya. Yau kuma yaro ɗan shekara biyar ne ya shiga sahun masu faɗa masa gaskiya? Kuma wannan karon a gaban mutanen da yake jin ya isa dasu ta kowacce fuska!
"Alhaji na ce Allah Ya bamu alkhairi."
Da muryar Umma tunanin da ya fara ya kau ya dawo da hankalinsa ga matansa. Hajiya ma sai da safen tayi masa ta shige yayinda Mama tayi masa tambayar ko ya gama da kwanukan abincin dare da ta ajiye masa domin ta kwaso. Amsa ya bata sannan ya mayar da dubansa ga neman Inna don tunda su ka shigo ko tari bai ji tayi ba. Jiran ta ce masa sai da safe kamar ƴan uwanta yake sai yaga bata wajen.
'Fushi take? Me kuma nayi? Ba na bada izinin yin bikin ba? Sai da safen ma yau ban isa ace min ba?' Ya ayyana a zuciyarsa.
"Ba tare ku ka shigo da Abu bane?" Ya tambayi Mama.
Yanayinta yaga ya sauya sannan ta ce masa ya shiga ɗakin Innar ya sameta. Hankalinsa tashi ya yi don ko bata faɗa ba yaji a jikinsa babu lafiya. Tabbas Hajiya da Umma ma basa cikin walwalar da yayi tsammanin za su dawo da ita.
Ɗakin ya shiga kai tsaye ya tarar da ɓangarenta da ƴan kwana. Wuce na falon ya yi ya shiga ainihin ɗakin baccinta inda nan ma wasu ke ciki. Sai dai suna ganinsu su ka fita. Zai yi magana ta riga shi ta hanyar miƙa masa wannan layar.
Ya miƙa hannu zai karɓa kenan sai Inna taga ya yi baya da hannunsa da sauri yana zaro idanu.
"A'uzubillahi..."
"Ka san ko mene ne kenan?" Ta ajiye layar a wajen madubi jikinta a sanyaye.
"A ina ki ka samo ta?" Ya tambaya cikin matsanancin tashin hankali fiye da wanda tayi tsammani.
"Sal..."
Kafin ta kai ƙarshen sunan ya gane wa za ta ce. Ya ɗaga layar yaga sunan Taj. Ransa kuwa ya yi mummunan ɓaci.
"Ɗana? Me matar nan ta taka da har take tunanin zan zuba ido ta mayar min da ɗa mutum mutumi?"
Inna na jin haka nata hankalin ya sake tashi.
"Mugun tsafi ne ko? Innalillahi. Tun a wajen naga ya fara runtse idanu."
Maganarta sake tunzura zuciyar Alhaji tayi. Sirrin da ya sakayawa Mami albarkacin Ahmad ya dawo masa tar cikin ransa. Haƙiƙa kamar sauran matansa ita ma so ya saka shi aurenta. Ta zo da fitina da neman rigima. Kullum cikin takalar Hajiya da Mama faɗa dake gidan a lokacin take. Aka mayar masa da gida filin kai ƙara. Wani abin idan tayi shi kan shi sai ya yi mamakin mene ne abin tashin hankali a ciki da har za ta nemi faɗa. Abin mamakin ma shi ne kasancewar shi ɗin jajirtaccen namiji ne amma ko zai ari baki wajen yi mata faɗa da nasiha anjima ko gobe ma sai ta ƙara. Sannu a hankali ya shiga karantarta inda ya fahimci ashe asiri take yi masa, kuma yawan rigimarta tana yi ne domin aunawa taga ko sihirin ya ci. Bai gama tsinkewa da lamarin ba sai da yaga wannan layar da yaji da kunnuwansa ranar da Zabba'u ta kawo mata tana cewa sunanta Raƙumi da akala. Har tana yi mata rantsuwar idan ta tauna ko me ta umarce shi zai aikata. Burinta a lokacin tunda ta haifi Ahmad yana ƙarami ta fitar da su Hajiya.
Ƙin nuna musu ya gani ya yi. Ya kuma bari tayi amfani da ita. Ranar ta yiwa Hajiya ɗiban albarka ajin ƙarshe duk yana jinsu daga ɗaki. Zuciyarsa kamar ta fito ta baki amma ya kasa fitowa saboda a kan idonsa ta saka a bakin ba tare da ta san yana gani ba. Ta tauna ta umarce shi da ya zauna a ɗaki kada ya fito ko me zai faru.
Haka kuwa aka yi. Rigima ta kaure amma duk yadda yaso haka ya zauna a ɗaki. Don baƙinciki har hawaye sai da ya yi. Sai kuma ya shiga karanto addu'o'in tsari tunda ya gama gano illar layar. Lallai idan ya zauna da ita rayuwarsa za ta zama mara amfani.
Shigowa Mami tayi da aka gama faɗan tana kumbure kumbure.
"So nake ka saki Haj. Gambo yanzu yanzun nan."
Ko ɗaga kai ya kalleta bai yi ba ta sake maimaita umarnin amma shiru. Dama layar na hannunta sai ta ɗaga ta juya masa baya za ta mayar cikin bakin. Bata yi aune ba taji ya damƙe hannun ya zare layar.
"Ki je gida na sake ki saki uku."
Farat ɗaya ya faɗi maganar don kada a sami matsala. Ta kuwa dafe ƙirji a gigice.
"Haj. Gambo nace..."
Ƙarfin gwiwarsa ya dawo gare shi ya ce "ni kuma ke nace."
"Wallahi baka isa ba...wayyo Allah. Na shiga uku. Alhaji ina zani? Ina kake so nayi da Ahmad bayan ka san ni marainiya ce?"
Gabaɗaya kamanninta sauyawa suka yi a take. Tana wannan hargagin ya kira Mama ya ce ta ɗauko Ahmad duk inda yake a gidan ta goya shi.
"Idan ba ni ba kada ki bawa kowa har uwar da ta haife shi."
Mafarin da goyon Ahmad ya koma hannun Mama kenan. Ba a raba ɗa da uwa amma bai san sunan da za a kira shi ba idan ya bari jininsa ya tashi a gidan shirka. Haka ya nunawa iyalinsa cewa faɗan da ta takali Hajiya ne yasa shi sallamarta. Ya kuma yi ne don kyautata ƙimar ɗansa a gidan. Daga lokacin bai sake shiga harkarta ba sai da ta fara ɗorawa Ahmad ɗin buƙatun da su ka fi ƙarfinsa yaje ya samawa mijinta aiki. Baya son haɗa inuwa da mushiriki kuma wanda yake tu'ammali da tsibbu. Shi yasa ya nesanta kansa daga gareta. Baya bari komai ya haɗasu. To amma yau dai tura ta kai bango. Idan tana cin ƙasa lallai ta kiyayi ta shuri. Ƴarta ko ita ce autar mata kuma masoyiya ga Taj ba zai taɓa sahale masa aurenta ba.
Wayarsa ya ɗaga da sauri ya kira Taj...abin da rabonsa da yi har ya manta.
***
Ƙirjin Anti Zahra dukan tara tara ya kama yi da ganin wannan rashin hankali da ake yi mata a gida. Inda su ka sami ƙarfin halin iya shigar mata kitchen su ka yi binciken kayan abinci da girki shi ne babban abin mamaki. Gashi an zuzzubar da shinkafa akan kafet. Yaran babbar ƴar Anti Zabba'u sun tattake wata a wurin. Ƙarnin kifi kuwa ba a magana. Maiƙon duk an shafe a kujeru da centre table don ƙeta. Wata ma remote ne a hannunta na daman. A hagu kuma tana riƙe da kofin da aka keɓe domin maigidan ta cika shi da juice.
Shi kuwa Ahmad Anti Zabba'u da Salwa yake kallo yana neman wadda za ta yi masa bayani. Saboda yadda ransa ya ɓaci kuwa Adam's apple ɗinsa hawa da sauka kawai yake yi ya kasa magana. Gani yake duk kalmar da za ta fito bata da ƙarfin nuna yadda yake ji a zuciyarsa.
Anti Zabba'u ko a jikinta domin da shirinta ta fito. Ta saki rai tayi musu maraba kuma bata damu ba da basu amsa ba. Sai ma kaɗa baki da tayi ta ƙwalawa ƴarta da ta tafi kitchen ƙaro musu juice tayi. Ita ce ake so Ahmad ya aura yanzu.
"Habitti (Habibty take kiranta saboda tafi ƴan uwanta kyau, sunan sai ya bita) fito ga yayan naki ya dawo." Ta kalle shi "tun ɗazu take damunmu da mitar ka ƙi dawowa."
Daga cikin kitchen ɗin aka ƙwala ihu duk wai na murna sannan wata ƴar tsumburburar budurwa ta fito da sassarfa cikin farinciki. Sanye take da matsatsen wando skin tight wanda daga gani a can ƙasan dilar gwanjo aka samo shi. Ta ɗora masa wata yarbatsulan riga mai rawa a jiki da wasu irin igiyoyi. Sai da ta tabbatar ta haɗa ido da Anti Zahra sannan ta buɗe hannuwa.
"Yaya Ahmet oyoyo."
Saurin shiga tsakaninsu Anti Zahra tayi don ta kula Ahmad bashi da niyar kaucewa.
"A gabana? Baki da hankali da alama." Cewar Anti Zahra cikin fushi "nayi miki kama da matan da za su ɗauki wannan ɗabi'ar ta wasan banza tsakanin cousins?"
Da wani salon shagwaɓa Habitti ta ce "Ya Ahmet kana jin matarka ko?"
Ko kallonta bai yi ba balle tasa ran yaji ƙorafinta. Hankalinsa ya tattara ya dubi matarsa.
"Me yasa ki ka shiga tsakaninmu Zahra? Da kin barta ta ƙarasa abin da tayi niyya."
Anti Zahra taji wani abu ya soki zuciyarta. Ita kuwa Anti Zabba'u har ta fara murmushin ƙeta sai taji ya cigaba da magana.
"...ni kuma sai na nuna mata idan tana taƙama ta sha nonon hauka to nima na tsotsa tunda duk tushenmu ɗaya."
Siɗe hannu Anti Zabba'u tayi da sauri ta miƙe tana taro zanin da ta kwance domin taji daɗin yin lodi.
"Ahmad ni ce mahaukaciya?"
"Kin ji na ambaci sunanki?!" Yayi magana muryarsa a sama. Yau da yarinya ce tayi masa haka da wahala idan bai zane ta ba.
Ita da ƴan matan duka jikinsa sanyi ya yi don ba haka su ka zata ba. "Rashin kunya za ka yi min don na zo gidanka jinyar mahaifiyarka?"
"Jinya ki ka zo? Wa ya kira ki?" Ya buɗe mata wuta.
Anti Zahra sai da taji babu daɗi ta ɗan taɓa hannunsa "ƙanwar Mami ce fa. Ka sassauta harshenka a kanta."
"Kin fini saninta ne?" Ta girgiza kai da sauri don bata taɓa ganin fushinsa irin wannan ba. Anti Zabba'un ya sake kallo "cikin wađannan ƴaƴan naki babu wadda za ki je gidan aurenta ki yi wannan abin ba tare da mijinta ya yi muku kallon rashin nutsuwa ba. Kin kuma sani amma shi ne ni ki ka yi min saboda ga karkatacciyar kuka mai daɗin hawa ko?"
Hankalinta sake tashi ya yi don yau tv ta sayar daga lokacin da Salwa ta kirata ta haɗa kuɗin aikin da aka yiwa Habitti. "Saboda uwarka tana kwance shi ne za ka ci min mutumci?"
"Idan da ƙalau take ba ki isa ki shigo gidan nan ba wallahi. Yau nayi aure? Ƴaƴana biyu fa! amma ko sau ɗaya babu ke babu waɗannan abubuwan..." ya nuna matan da jikinsu ya gama laƙwas sama da ƙasa.
Babbar ce ma Hansatu ta ɗan taɓuka abin kirki ta tashi tsaye "idan ka cigaba da faɗawa mamanmu magana fa ba za mu yarda ba."
Da wutsiyar ido ya kalleta sai gata tayi tsit ita ma. Ya juya ga Salwa da ko tari bata yi ba tun shigowarsu. Babu shiri tayi ƙasa da kanta ta kama hanyar ɗaki za ta wuce sumsum.
"Idan kin wuce ciki wane mahaukacin ne zai yi min bayanin me yake faruwa da gidana? Ban soke batun zuwan nasu kafin na fita ba?"
"Yaya..."
"Ina raga miki ne kawai saboda ke mace ce, ba don haka ba da tuni na sauke miki abin da yake damun ƙwaƙwalwarki. Shashasha wadda bata san ciwon kanta ba."
Rasa da me za ta ji tayi. Da ɓacin ran Ahmad wanda bata saba gani ba, ko kuwa da ganin da Innar Taj tayi mata dumu-dumu a wajen dinner akan abin da take shirin yi? Haƙuri ta buɗe baki za ta bashi ya ɗaga hannu ya dakatar da ita.
"Ku haɗu ke da su ku kwana a ɗakin da ki ke. Gobe da safe..." ya ciro dubu goma daga aljihunsa ya ajiye akan centre table yana kallon su Anti Zabba'u "ku ɗauki wannan ku yi kuɗin mota kuma a gyara min gida kafin a fita." Ita kuma Salwa ya ce "ke kuma zan kira babanki ya turo mai ɗaukarki ki koma gida. Kuma wallahi kin ji na rantse idan ki ka fita daga gidan nan kafin lokacin tafiyarki sai na baki mamaki."
Yana gama magana ya shige ɗakin Salwan ya ɗauko Mami kamar jinjira don duk ta zuge. Kai tsaye ɗakin Zahra ya wuce da ita kowa yana ganin hawaye shaɓe shaɓe da su ka jiƙa fuskarta. Duk abin da aka yi tana ji. Tafi kowa sanin dole ƙanwarta ta zo da wata manufa. Takaicinta da ko magana bata iyawa sosai yanzu sai dalalar yawu. Da ko zama a gidan Zabba'u bata isa tayi ba. Sai kuma murnar Ahmad ya nunawa duniya ya haifu. Wannan sauƙin kan nasa da take ganin za a iya cutarsa yasa ƙafa ya ture. Ya nuna mata shi ɗin jinin Alh. Hayatu ne babu ƙarya.
Sai da ya kwantar da ita sannan ya ce da Anti Zahra ta ɗauko duk abin buƙatarta da na yaran su koma ɗakinsa.
"Idan tana buƙatar wani abu fa?"
"Zan dinga leƙawa."
Bai amince ta kwana ba don ya sani akwai cin zali ma idan yace sai ta kula da Mamin da ta ɗora mata karan tsana tun kafin aurensu.
*
Mummunar shaƙa Salwa taji a wuyanta. Gashi bata san ko wace ce ba domin ta bada baya tana shirin cire kaya.
"Sakar min wuya" ta ce da riƙon ya yi ƙarfi ta tabbatar ba na wasa bane.
"Mu za ki yiwa shigo-shigo ba zurfi ki sa a ci mana mutumci?"
Da mamakin muryar ta ce "Anti ni za ki shaƙewa wuya?"
"Haifarki nayi da ba zan shaƙe ki ba?"
Da zafin nama Salwa ta juyo ta doke hannun nata. Ganin ta buɗe baki tana shirin yi mata magana yasa ta ce "tunda baki haife ni ba nima ba zan kasa doke miki hannu ba."
"Wato na kula shiri ku ka yi da Ahmet ki ka taso mu don ku wulaƙanta mu." Cewar Habitti tana hura hanci.
Ba su san ran Salwa yafi nasu ɓaci ba saboda disappointments ɗin da ta kwasa. Shi yasa bata ji nauyin ramawa ba.
"Kwaɗayi dai ya kawo ku tunda uwarku na kira ba ku ba..."
Kiffff, taji saukar marin da yafi kama da gwaɓe baki don sai da laɓɓanta su ka amsa. A take kuma idanunta su ka kaɗa da ƙwallar azaba. A makance ta kai hannu domin ramawa akan Hansatu da tayi marin sai hannun ya sauka a kuncin Anti Zabba'u.
Ita kanta Salwa sai da gabanta ya faɗi da taga wa ta mara, sai dai kafin ta gama sanin me za ta yi ƴaƴan gwaggon tasu su ka yi mata rubdugu. Kowa na kai hannu aka lillisa mata jiki. Ihun ma da za ta yi don Ahmad yaji ya kawo mata ɗauki an toshe bakin. Sai da su ka tabbatar tayi laushi su ka barta da ta daina ƙoƙarin kare kanta. Abinka da waɗanda su ka saba da damben gidan haya.
Kukan da take fitarwa a hankali ga jini yana ta zuba daga hancinta ne ya sanya Anti Zabba'u cewa "Yanzu idan Ahmad ya ganta ya zamu yi?"
"Ba ma zai ganta ba. Kafin su tashi zamu kama gabanmu. Banda dare ai da babu abin da zai sa mu kwana" Habitti ta faɗi tana sake dungure mata kai.
***
Shiru motar ba ka jin komai sai hawa da saukar numfashin Hamdi dake baccin gajiya. Musu su ke da Taj yana tsokanarta da cewa yau shi ya haskata tana cewa ita ta haska shi. Can sai ji ya yi ta koma uhm da uhm-uhm idan yayi magana. Yana juyawa yaga ɗaurinta ya karkace saboda yadda ta kwantar da kai a jikin kujera. Mamaki da haushin ta rusa masa plans ɗinsa su ka kama shi.
"Lallai ma yarinyar nan. Bacci ma kike yi a irin wannan lokacin?"
Kafaɗarta ya girgiza a hankali ta ɗan buɗe ido ta kuma rufewa.
"Ko ki tashi ko in wuce gidanmu dake" ya faɗi yana karantar fuskarta.
Ko gezau bata yi ba wanda yasa shi tunanin tabbas bacci take yi. Don da ido biyu take ba za ta yi shiru ba. Ƙwafa ya yi ya kaɗa kai.
"Allah Ya kaimu gobe nima sai na rama. Idan an kawo ki a kwance ina bacci za a ganni akan gadon amarya."
Nauyin baccin da ya rufeta bai hanata jin abin da ya ce ba. Murmushi tayi a ɓoye ta gyara kwanciyarta. Baccin kwanakin nan da bata samu ne ya yi mata kamun kazar kuku.
Taj cigaba ya yi da tuƙin yana yi yana kallonta. A baccin ma tayi masa kyau. Sai da ya kusa shiga unguwarsu ciwon kan da ya soma ji bayan Salwa ta taɓa shi ya dawo masa da ƙarfi. Abu kamar wasa sai gashi yana gumi. Da ƙyar ya iya ƙarasawa ya tsayar da motar amma bai kashe ba. Sai da ciwon ya lafa ya fita ya zagaya gefenta ya buɗe sannan ya ranƙwafa yana kallonta sosai.
Ƙamshin turarensa da numfashin da yake yi daf da ita ne yasa tsigar jikinta tashi tun kafin ta buɗe ido. Yunƙurawar da za ta yi yayi daidai da sake matsowar Taj. Kawunansu su ka haɗu da ƙarfi.
"Ya Salam" Taj ya dafa kansa da hannu ɗaya, ya kuma ɗora ɗayan a goshinta inda yake tunanin ta nan su ka buge.
"Fasa min kai za ka...." Hamdi ta fara cewa sai ta kula idanunsa sun yi ja da taimakon fitilar waje ta gidansu.
"Kuka kake yi? Kan nawa da zafi ne?" Ta tambaye shi ganin yana runtse ido. Bata san fami ta yiwa ciwon kan nasa ba.
Yadda tayi tambayar sai da yasa shi yin murmushi. "Abu kamar auduga ina zafi a nan?"
"Awwnnnn" ta ce tana yi masa murmushi da fari da idanu "wai irin abin nan ace tsabar soyayya ka buge ma baka ji zafi ba."
Taj kasa jira ta gama magana ya yi. Tunda ta rangwaɗa kai ta ce awwnnn ɗinnan ya daina gane komai. Ɗan yatsansa ya ɗora akan bakinta yana zana leɓen wanda ya sanyata shirun dole. Sannan ya zame hannun a hankali ya kawo kansa daidai fuskarta.
" I realy tried to be a gentleman tonight Mrs Happy amma kin hana."
"Me kuma nayi?" Hamdi tayi tambayar cikin faɗuwar gaba don ta fara tsorata. So take ta ganta a cikin gida kawai.
"Baki yi komai ba sai taɓa zuciyar Tajuddin."
Wayancewa tayi saboda take takensa da take gani ta ce "Wai ka san ma'anar sunanka kuwa?"
Shi ma da gatse ya bata amsa "Ta yaya zan sani baki faɗa min ba?"
"Taj yana nufin crown, kaga Tajuddin yana nufin..." ta fara cewa ya katseta.
"Ina son ki Hamdiyya Habib Umar"