Kenza eBookz

Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 44

Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 44

Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 44: Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 44. Kwanciya tayi ta rufe jikinta. Bata ji motsin Taj ba. Ta dai yi…

3,364 words

Kwanciya tayi ta rufe jikinta. Bata ji motsin Taj ba. Ta dai yi tunanin ƙila yana nasa ɗakin. Gara ya yi zamansa a can. Bata son abin da zai sake janyowa su haɗa ido. Tashinta da yayi da asuba ma don babu yadda za ta yi ne. Zancen zuci ta cigaba da yi wanda gabaɗaya ya ƙare akan baƙuwar rayuwar da ta tsinci kanta a ciki jiya. Taj ya nuna mata so da ƙauna kamar ya haɗiyeta. Wata zuciyar ta ce mata ya kuma saka ki kuka kamar zai ƙarar miki da hawaye ba.

Tunaninta na kaiwa daidai nan ya buɗe ƙofar da sallama ya shigo. Da sauri kuwa ta sake yin ƙasa da kanta ta rufe ko ina.

Taj murmushi ya yi ya je bakin gadon ya soma buɗe lulluɓin da tayi. Bata bari ya gama ba ta kama duvet ɗin da nata ƙarfin. Sai ya saki, ya hau gadon daga gefenta ya turata ciki ta hanyar matsawa yana rufa shima.

"Matsa min, matsa min" ya dinga faɗi har su ka koma tsakiyar gadon sannan ya daina turata.

"Me ya hana ki bacci? Ko jirana kike yi?" Ya yi maganar yana rungumota gabaɗaya a ɓangaren damansa.

Hamdi ga tsoro ga tsiwa, ta haɗa biyun ta ce, "In jira ka kayi min me?" Da rawar murya.

Taj ya yi dariya "Hamdiyya matar Malam Tajo. Maida wuƙar ni ba wani abu nake nufi ba."

"Waye kuma Tajo? Ɗan uwanku ne?" Ta harare shi.

"Ni ne shi, shi ne ni." Ya nuna kansa.

Hamdi ta yamutsa fuska "A'a gaskiya."

"To ke ce shi, shi ne ke?"

"A'a fa." Ta ƙara da tura baki.

Abin ya burge shi ya kwanta a jikinta "To ya abin yake?"

Murmushi tayi na kunya "Ni ce kai, kai ne ni...shi kuma Tajo bamu san shi ba."

"Taj ɗin ma in kin ce baki san shi ba sai a siyo rago a saka min sabo." Ya faɗi maganar da wani shauƙi dake kwasarsa saboda shagwaɓar Hamdi "duk yadda kike so haka za a yi Mrs Happy."

Wani sabon shafin ya so a buɗe ta ce sam bata san zance ba indai ba sumar da ita zai kuma yi ba. Ya dinga yi mata dariya. Su na ƴar hirarsu har bacci ya sake kwashe su. Ba su su ka farka ba sai da aka kira Taj.

Ƙanwarsa ce wadda a jerin haihuwarsu bayan Kamal sai shi sai kuma ita Rawda. Abincin amarya da ango na sati guda ta ɗauki nauyi saboda gidanta yafi na kowa yin kusa da na Taj. Kullum safe, rana da dare take turo yaron gidanta ya kawo a babur. Amarya da ango su ka sake samun lokacin shaƙuwa da sabo da juna.

Taj ya bar Happy Taj a hannun yaransa. Sai Abba Habibu dake zuwa amma ba kullum ba. Taj yayi yayi ya ɗauki hutu amma yaƙi.

Wata irin soyayya Taj da Hamdi suke yiwa juna wadda bata da shamaki ko basaja. Sak su ka fitowa juna tun farko, shiyasa alaƙar tasu tayi saurin ƙulluwa. Jin junansu suke yi tamkar tare da soyayyar juna su ka tashi. Ga Taj gwanin zolaya wadda a sati gudan nan Hamdi ta koya. Duk baƙon da ya shigo gidan sai ya fita da murmushi saboda nishaɗin da zai samu daga masoyan.

Abu biyu ne su ka so damun Taj amma dalilai sun sa basu yi tasiri ba. Na farko tafiyar su Kamal Umra bagatatan ko haɗuwa basu yi ba. Yayi mita kuwa kamar ya ari baki. A ranar da su ka tafi wadda ta kasance kwana biyu da tarewar Hamdi, da yamma ya tafi gida bayan wayar sallamar da Kamal ya yi masa daga cikin jirgi.

Cikin farinciki su ka gaisa da su Umma kafin ya hau sama da aka yi masa iso wajen Alhaji. Gaishe shi ya duƙa yayi Alhaji ya miƙa masa hannu yana girgiza kai.

"Kai ka san ba haka nake gaisawa da ƴaƴana ba."

Da sauri Taj ya tashi ya ƙarasa gaban Alhaji ya miƙa masa hannu. Alhaji yayi murmushi sannan su ka zauna.

"Ina matar taka?"

Kai a ƙasa yana susar ƙeya Taj ya ce "tana gida. Ta ce na gaishe ku."

"Ina amsawa idan da gaske kake."

Rantsuwa Taj ya fara sai yaga Alhaji yana murmushi. Da alama dai yayi furucinsa da zolaya ne. Sannan babu shakka yana sane da abin da ya yiwa Abba Habibu ya ɓata ran Hamdi. Ba dai zai ɗauko zancen ba saboda ba shi ya kawo shi ba. Yana da mahimmancin da shi ma zuwa da zama na musamman ya dace da shi.

"Alhaji maganar Kamal ce ta kawo ni."

"Kayi aure Taj. Bai kamata ka zauna kana ƙunƙuni don ya tafi ba tare da kai ba. Ya dace ka fara sanin ragamar rayuwarka da ta ƴar mutane ce a wuyanka yanzu. Ba dole bane Kamal ya daidaita tafiya da kai ba."

"Ba haka nake nufi ba" cewar Taj

Tausayi ya bawa Alhaji yadda ya yi maganar. Shi kuma ya katse shi ne kawai saboda baya son hankalin Taj ɗin ya kai ga abin da ake ɓoye masa.

"To ina jinka."

Shiru Taj yayi. Alhaji ya sami kansa da yin murmushi. Yayi matuƙar kewar Taj da halayansa. Idan kayi masa faɗa alhali bai yi laifi ba, haka zai yi ta marairaicewa sai ka koma rarrashinsa ko babu niyya.

"Ashe baka canja hali ba har yau? Mijin aure fa kake."

"To ai ba maganar tafiyar nazo yi ba. Duk da dai naji haushi. Ko ba a je dani ba da sai a faɗa min. Ɗan Adam ba ya rasa buƙatu a wajen Allah."

"To ka roƙa mana a inda kake. Allah Yana ko'ina."

"Amma dai ba kamar idan ana shafa Ka'aba ana ambaton suna na da buƙatuna ba ko Alhaji."

Sake faɗaɗa murmushi Alhaji ya yi. Ya dubi Taj ya ce "welcome home."

Tsabar daɗin da Taj yaji bai san lokacin da koma kusa da Alhaji ya rungume shi ba. Alhaji ya gama basarwa amma a ransa daɗi yake ji.

Da ya nutsu ne ya faɗa masa ainihin abin da yake tunani. Yana magana Alhaji shiru kawai yayi. Daga dawowa gida, bayan kwana biyu da tarewar matarsa ya zai yi idan yaji ciwon da yake damun ɗan uwa mafi soyuwa a gare shi?

"Baka yarda da ilimin Dr. Mubina ɗin bane har kake tunanin wani ciwon ne yake damunsa?"

"Ba haka bane Alhaji. Ban sani ba ko idanuna ne amma har wani kumburi naga yayi rannan. Yanayin bai yi kama da ƙiba ba."

Shi da baya son ɓoye abu bai san dalilinsa na son bawa Taj ɗan lokacin samun farincikin aurensa ba kafin ƙwai ya fashe.

"Yanzu mece ce shawararka?"

"Idan kun tafi don Allah ka tilasta masa zuwa asibiti. Idan da kai ne dole zai je ayi masa thorough check up."

Alhaji ya yi murmushi don ya ɓoye halin da yake ciki. "In sha Allahu zamu je."

"Nagode." Ya dinga faɗi har ya fita. A zuciyarsa yana mai fatan Allah Yasa babu komai.

To tafiyarsu Alhajin ne kuma sau biyu ya sake samun kansa a yanayi na ɗaukewar jin ƙamshi da ɗanɗano. A na biyun da ƙyar ya iya ɓoyewa Hamdi ya shiga ɗaki yayi ta bulbula turare kafin daga baya abin ya daidaita. Ranar da ya tasar masa na ukun kuwa ana gobe za su yi sati ne. Saboda tsabar tashin hankali, yadda yaga rana haka yaga dare. Cikin tsananin kiɗima ya zame jiki daga wajen Hamdi ya koma falo ya kira Kamal a waya. RAYUWA DA GIƁI 33

Batul Mamman💖

This page is sponsored by spicesbyMrsghaleetk....yep, MRS GHALEE TK. Nace ba, wai kina cikin masu cewa girki da spices baya daɗi? Ko kuwa kin saba saya kina bari ya siƙe a kitchen saboda baki gane ɗanɗanon da yake bayarwa ba?

Albishirinki, Mrs Ghalee TK dai za ta yi Ramadan promo. Dama ce ta samu gareki wajen sayen ingantattun kayan girki masu tallafawa cefane musamman a wannan marra ta tsadar kayan abinci. Ke dai ƴar uwa, harma da ɗan uwan da ya saba taimakawa iyayensa ko matarsa, ko kuma mai son burge iyali, ku yi tanadi don Mrs Ghalee TK ta zo da rangwame domin gyara tukwanenku. Ku sai ku garzaya ku nemeta akan wannan layin ta manhajar whatsapp ko kiran waya 08032834178.

Taku ce Batul Mamman, ganau akan kayayyakin da nake tallata muku.

***

A cikin yanayin ciwo da gajiyar jiki Kamal ya buɗe idanu ya miƙa hannu zai ɗauki wayarsa. A gadon asibiti yake inda yake samun kulawa ta musamman. Da yake dokar asibitin ba a zaman jinya, shi kaɗai ne a ɗakin. Alhaji da su Ahmad suna hotel kusa da asibitin. Tafiyar just ƙafa ke kawo su. Tare dashi su ke wuni sai takwas na dare idan an buƙaci duka baƙi da masu ziyara su fita sannan su ke tafiya. Kwanaki goma aka bashi ya gama shan magani da allurai kafin a fara dialysis.

"Happy lafiya dai ko?" Ya ce cikin bacci da firgici domin kuwa ukun dare harda kwata lokacin.

Kamar an tsunkuli Taj ya ɗaga kai ya kalli kyakkyawan agogon bangon falon. Baki ya buɗe gami da girgiza kai.

"Don Allah Happiness kayi haƙuri. Kasan Allah ban duba time ba. Ashe past one. A nan uku ta wuce ko?"

Kamal ya gyara zama ya ce "Eh...mene ne ya faru? Haka kawai ba za ka manta lokaci ba."

"Gobe sai muyi magana in sha Allah. Am very sorry." Taj ya ce har zuciyarsa.

"Taj" Kamal ya kira shi da ɗan ƙarfi "me ya faru?"

Roƙonsa Taj ya fara yi akan ya jira safiya don har ya katse kiran amma ya sake kiransa. Su ka ɗan yi ja'inja ɗinsu sannan Taj ya faɗa masa abin da yake faruwa dashi game da ɗaukewar ɗanɗano da jin ƙamshi ko wari wasu lokutan.

"Zuciyata tana bani Covid ce. Nayi browsing naga ɗaukewar sense of smell da taste suna cikin symptoms ɗinta. Ni bana mura amma bayan magrib ina ƙirgawa sau bakwai Hamdi tayi atishawa."

Kamal yayi ƴar dariya "sannu Doctor."

Taj ya ɓata rai "Happiness its not funny."

"Na sani. Shi yasa nake mamaki da kana zaune a gida ka yankewa kanka cutar dake damunka."

Murmushi ne ya kama shi. Tabbas asibiti ya kamata yaje amma fargaba ta hana. Ba kuma kansa yake jiyewa tsoro ba. Idan ta tabbata yana da corona shikenan Hamdi ma ta samu. Daga tarewa ya haɗata da ciwo.

"Gobe zan je in sha Allah. Thank you and sorry."

Sai da safe suka yiwa juna. Kamal ya ce yana jiran jin sakamakon idan ya dawo daga asibitin. Da ya koma ɗakin a dunƙule waje guda ya sami Hamdi. Ta dawo tsakiyar gadon tana baccinta hankali kwance. Sama ya kalla ya sake yin addu'ar da ya wuni yana yi. Allah Yasa ba covid bace. Idan kuma ita ce yana fatan Hamdi bata samu ba. Sai dai abin da kamar wuya. Yadda su ke manne da juna ana amarci ai taimakon Allah ne kawai zai hanata kamuwa. Kwanciya yayi a can gefe. Ko minti biyu bai yi ba yaji Hamdi a jikinsa ta ɗora rabin kanta a ƙirjinsa. Wani ɗan murmushi yayi ya sake shige mata har yayi bacci.

***

Yawan kallon wayar da Kamal yake yi ne yasa Alhaji tambayarsa kira ko saƙon wa yake jira. Shi kuwa ya faɗa masa yadda suka yi da Taj a waya.

"Result ɗin nake dubawa ko ya turo."

Shiru Alhaji yayi na wani lokaci yana tunani kafin daga bisani yace idan ya faɗa masa yana son ji shi ma. Zuwa la'asar kuwa bayan Taj ya turo ya faɗawa Alhajin cewa ba corona bace.

"To Alhamdulillah. Ince dai bai hanaka faɗawa kowa ba? Zan kira shi nayi masa ya jiki." Da jindaɗi Kamal ya ce Taj bai hana ba.

Alhaji bai tashi kiran Taj ba sai bayan sun koma masaukinsu ya shiga ɗakinsa. Bayanin yadda yake ji ya buƙaci ya yi masa.

"An baka magani?"

"Eh Alhaji. Sun ce stress ne kawai"

"To Allah Ya ƙara lafiya. Ciwon da ya shafi harshe da hanci a wajenka ba abin ɗauka da wasa bane duba da irin sana'arka. Ka mayar da hankali wajen shan magani."

Taj ya yi godiya yana cike da murnar wannan kulawa ta Alhaji.

* Wando ne tight ruwan zuma a jikin Hamdi. Jikinsa yana da wani irin laushi ga rashin nauyi. Ta ɗora shirt ɗin Taj baƙa mai maɓallai a gaba da dogon hannu. Maɓallan gaban guda huɗu ne kaɗai a ɓalle ta bar na farkon. Hannuwan kuwa tsayawa tayi naɗe su har dantsen hannu. Ga gashinta da bata taje ba ta tattara tayi packing bai shige sosai ba. Fuskarta ko ɗigon kwalliya babu. Sai ƙamshi kamar a ɗauketa a gudu don daɗinsa.

Duka wannan saurin shirin saboda sun gama sati yau za ta fara shiga kitchen ne. Ta kwana tana tsara me za ta dafa saboda baƙin da zasu yi daga gidansu Taj. Shi kuma kawai yana tashi ya ce ta faɗa masa me take son dafawa.

"Ki kwanta ki huta in dafa."

"Ka dafa?" Ta juya tana kallonsa "ni ce fa amaryar."

"Ni kuma angon amarya ba."

"Girkin nawa ne baka son ci ko baka yarda dashi ba?"

"Taimako ne fa kawai. Besides na gaji da zaman nan. I miss my kitchen."

Wata uwar harara ya samu wadda ta sanya shi tuntsirewa da dariya.

"Me kuma nayi? To ki bar min aikin duka idan rabawa ne ba kya so mu yi."

"Yanzu don Allah baka san kowacce amarya jiran wannan ranar take yi ba? Ranar da za ta fara yiwa mijinta girki. Sai kawai kace in bar maka kayi?"

"Nayi zaton murna za ki yi fa. Ki ce yau ga ranar auren Taj" ya ɗage gira.

"Ni kuma to da me zan burgeka? Girki a wajen mace ni dai a wajena abin alfahari ne." Hamdi ta ce idanunta a kan shi.

Hannunta ya kama su ka shiga kitchen ɗin.

"Ke ce sarauniya a nan. Ni kuma bafade mai neman suna a wajen uwarɗakinsa."

Murmushi Hamdi tayi. Ta buɗe store Taj yana kallonta shi ma yana murmushi.

Juyawa tayi ta kalle shi "kada in yi shinkafa da miya ko? Its too common."

"Dafa shinkafar ki bar min miyar. Sai in yi chicken curry maimakon stew da potato salad."

Abin da take ta gudu da alama dai shi zai faru a gidan nan nasu. Girke girken ƙwalisar da ta koyo a wajen Abbanta ƙarshenta duk ba za su burge shi ba.

"Na fasa ma. Kullum shinkafa ake ci. Naga akwai macaroni shape daban daban..."

Don tsokana kawai Taj ya ce "ni yanzu ba abin in ce miki pasta ake cewa ba ki ji haushi. Macaroni is just a type of pasta."

Hamdi ta sha kunu shi kuwa ya ɓoye dariyarsa.

"Ka gama faɗa ai, wato ko fashewa zan yi babu ruwanka?"

Laɓɓansa ya ɓame gami da alamar yiwa bakinsa zip. Ita kuma da yake tana son yin shawara dashi don kada tayi gaban kanta sai ta sake yi masa tambaya.

"In dafa ita pasta đin?"

Allah Ya sani ya ma manta, bai san lokacin da ya ce "Ki zauna in yi musu creamy chicken pasta kawai."

"Na fasa."

Rarrashinta ya kama yi "dafa abin ki, ba zan saka miki hannu ba."

"Naƙi wayon. Ban ma iya ba."

Fushin nata da ture turen baki dariya su ke bashi. Ya dai bata haƙuri ya ce kuma ba zai kuma magana ba.

"Tuwon shinkafa ma zan yi." Ta faɗi da murna don tana tunanin baya cikin abin da ya ƙware.

Store ɗin ta shiga da wuƙarta a hannu za ta buɗe buhun shinkafar tuwo. Shiru Taj bai ce komai ba har ta soma farke buhun sai ta ɗaga kai ta kalle shi.

"Don Allah baka iya tuwo ba ai ko?"

"Uhmm" ya faɗi yana rufe baki.

Ga mamakinsa kawai sai Hamdi ta ajiye wuƙar a kan buhun ta fito ta zauna akan wata kujerar kitchen a gefen sink mai ɗan tsayi ta kama kukan shagwaɓa.

"Ban iya tuwo ba. Don Allah ki yi shiru. Da gaske ban iya ba." Taj ya ce a rikice.

Da dai ta san ta kunna shi da kukan sai taƙi dainawa. Yana lallaɓata tana mita.

"To ni da me zan burgeka? Me yasa ka iya komai? Mene ne baka iya ba?"

"Ban iya ɗan wake ba" ya faɗi da sauri don ta daina kukan.

"Ahaaa...ashe ka iya tuwon" tayi maganar tana jinjina kai.

Sai lokacin ya fahimci me tayi. Dole ace mata daban suke. Ƴar ƙaramar yarinya tayi masa wayo.

"Ai ba sosai na iya ba. Ɗaki ma zan tafi har ki gama." Ya saketa zai fita.

Hannunsa ta kamo ya tsaya suna kallon juna.

"Allah so nake na dafa maka abin da baka iya ba. Wanda in kaci za ka yaba min da zuciya ɗaya."

"Come on Love, ko me ki ka dafa kin san zan yaba." Ya rungumeta yana shafa mata kai.

"Honest review nake so. Ka yaba har zuciyarka ba don naji daɗi ba kawai."

"To shikenan. Maganar gaskiya na iya tuwo amma ban fiye yi ba."

"Da gaske don Allah."

"Da gaske."

Da murnarta ta nuna masa ƙofa "To ka tafi falo ko ɗaki ka huta."

"Ranki ya daɗe duba fridge ɗinki dai ki tabbatar babu abin da ki ke buƙata."

Da wani rangaji duk na jindaɗin cewa bai iya tuwo ba sosai ta tafi ta buɗe freezer. Nama kala-kala akwai. Ga kayan miya da aka wanke aka ɗaɗɗaura a ledoji. Ɗaurayewa kawai zata yi tayi blending.

"To idan babu takura don Allah ina da saƙo."

"Yes Ma. Me kike so?" Ya tashi yana sauraronta.

Ganyen ugu da alayyahu ta buƙata daidai yadda take jin zai isheta yiwa mutum biyar da za su zo da kuma su na gidan abinci.

Bayan fitar Taj a bincikenta na store taga kwali na kayan annurfoods. Ta buɗe ta ɗauko garin tsaftatacciyar niƙaƙƙiyar farar shinkafa. Ta fito ta ɗora ruwan tuwo sannan a wata tukunyar ta ɗora nama. A ruwan tafasar bayan ta saka maggi da gishiri, sai ta sanya paste ɗin citta da tafarnuwa. Ta kawo mixed spices, da garin lawashi duka na Mrs Ghalee TK ta zuba. Ya kusa dahuwa ta zuba yankakkiyar ganda ƙanana da aka zuzzuba a zip lock aka ajiye mata. Sannan ta kawo albasa ta yanka da girma ta zuba. A gefe kuma ta tafasa kifi sama-sama a wata tukunyar ta ciccire ƙayar ba tare da ta fasa tsokar sosai ba. Tana yi tana azkar cikin kwanciyar hankali.

Tana tuƙin tuwo Taj ya dawo. Tayi masa sannu da zuwa ya sami wuri ya zauna.

"Kada ki koreni please."

"To kada ka taɓa komai."

"No problem."

"Kuma kada kayi magana"

Alamar yiwa baki zip yayi. Ya zauna yana kallon yadda take komai cikin ƙwarewa da kazar kazar. Duk motsinta burge shi kawai yake yi. Ta dami kanta akan iya girkinsa da tsoron kada ta gaza ta wannan fannin a idonsa. Bata san shi kuma cikar buri yake gani ba a tare da ita. Samun matar da ko bata iya girki ba za ta ƙoƙarta tayi masa a matsayinsa na mijinta ba ƙwararren mai sana'ar girki ba. Shi ma yaji shi isasshen namiji a cikin gidansa.

A flask mai kyau ta jera tuwon da ta ƙulle a farar leda. Taj ya ɗaga hannu tamkar a aji. Hamdi ta yi murmushi. Dama ta san ba shirun zai yi ba.

"Ina jin ka."

"Tuwon mene ne wannan don Allah?"

Ta faɗa masa. Yace bai san ana yi ba. Sai ya kuma wata tambayar. Yana so ta faɗa masa miyar me za ta yi.

"Miyar ganye."

Bai ƙara magana ba sai da yaga ta gama yanka ganyen daban daban ta wankesu da kyau sannan kowanne ta ɗora a tukunya daban da ruwa kaɗan. Za ta kunna wutar taga alamun zai yi magana sai ta dawo gabansa ta tsaya ta duƙar da kanta. Yayi zaton magana za ta yi. Sai ta shammace shi tayi kissing ɗinsa.

"Na rufe maka bakin nan. Don Allah kayi shiru. I want to surprise you."

"Surprise ya wuce wannan?" Ya taɓa bakinsa "ai kawai ki kashe wutar ki zo in baki tukwici."

Guje guje su ka gama har falo tana zille masa. Da ta gaji ta jingina da bango ta dafe ƙirji tana mayar da numfashi.

"Don Allah ka barni haka."

"Kin san me?" Ya faɗi yana zama "wallahi na fi ki gajiya."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull