Kenza eBookz

Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 45

Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 45

Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 45: Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 45. Dariya suka yi sannan ya barta ta koma bakin aikinta. Kowanne ganye…

3,336 words

Dariya suka yi sannan ya barta ta koma bakin aikinta. Kowanne ganye ta kunna shi ya soma tafasa kaɗan sai ta kashe ta tsane ruwansa tas. Ta haka ne miyar ba za ta yi ruwa ba yadda take so. Sannan kalar za ta fi kyau. Manja ta zuba a tukunya ta kawo garin daddawarta na annurfoods ta zuba a ciki. Ta zuba tumatir, albasa da attaruhu da tayi blending sama-sama. Ya fara suyowa ta ƙara da wata albasar da ta yayyanka mai ɗan dama. Ita ma tana yi mata daidai ta juye ruwan naman nan a kai ta ɗanɗana. Abin da bai ji ba ta ƙara ta bari ya haɗe jikinsa sannan ta fara zuba ganyen ugu da shuwaka ƴar kaɗan wadda Yaya da kanta ta wanke masu a gida ta busar. Jiķata kawai tayi da ruwan zafi ta taso. Ƙamshin girkin har falo. Ta zuba alayyahun da ugun yayi yadda take so sannan ta ƙara da kifin da ta riga ta gyara. Ta zuba garin crayfish ta rufe tukunya. Bayan minti biyar ta kashe ta saɓa murfin tukunyar.

"Zuba min nawa yanzu." Firgigit ta juya don bata ji shigowarsa ba.

"Ka bari su iso mana tunda sun ce a nan za su yi azahar."

"Ko ki bani ta laluma ko in miki ɓarna a tukunya."

Hannunsa ta ja har bakin tukunyar ta ce ya ɗanɗana miyar. Ya zuba a plate ya ɗeɓi zallar miyar da bata yi ruwa ba ga kyau a ido ya ci.

"Mrs Happy..."

"Yes" Hamdi ta amsa da ɗoki.

"Kin sami 100/100"

Mamaki ta kuma bashi da ta kama rawa tana juya ƙugu. Ya kuwa dangwarar da plate ɗin ya kwasheta. Abincin da basu ci ba kenan sai da baƙinsu su ka zo. Suma kuwa su ka yi ta santin girkin amarya.

***

Jiki na rawa Yaya ta kira Inna Luba a waya tana kuka. Innarta ta tada hankali tana ta tambayarta me ya faru.

"Ke kaɗai Allah Ya bani Jinjin. Idan kika ɓoye min damuwarki waye zai faɗa min tasa? Ko ba kya son addu'ata?"

Mijinta da kishiyarta suna tsakar gidan take wannan wayar. Su ka tsayar da hirar da suke wadda har yau basu sakata a sabgarsu suna sauraronta.

"Hmmm, ƙarshenta ɗan daudun mijinta ko ƴaƴanta ne wani ya kwaso abin kunya." Cewar kishiyar Inna Sarai.

"Ko kuma ta cangala ƙafarta a inda bai kamata ba" Malam ya faɗi yana zungura baki irin shi dai babu ruwansa ɗinnan.

Inna Luba ko ta kansu bata bi ba ta cigaba da cewa Yaya ta faɗa mata me ya faru. To dama Abba Habibu yana gefe yana dariya. Da yaji kukanta yaƙi yankewa bayan ta kira wayar shi ne ya karɓe wayar.

"Inna kada ta tayar miki da hankali. Makka za ta je shi ne take kukan murna."

"Allahu Akbar kabiran" Inna Luba ta faɗi da dariyarta "Habibu wa ya biya mata?"

"Ni ne Inna" Abba ya bata amsa yana murmushi.

Yaya sai ta karɓe wayar "Inna ashe yana ta tarin kuɗi ban sani ba. Yaje domin ya biya mana kuɗin sun ƙaru akan yadds ya sani. Shi ne ya ce shi ya taɓa yi ni na tafi. Inna tarinsa na tsayin lokaci amma ya zaɓi ya tura miskiniyar matarsa akan yaje" ta sake fashewa da kuka.

Inna Luba ma sai da tayi kuka. Ta dinga yiwa yayarta da mijinta Mal. Umaru addu'a. Sun ƙaunaceta, sun ƙaunaci gudan jininta. Yau gashi da ranta da lafiyarta take jin Jinjin za ta keta hazo taje ƙasa mai tsarki.

Da ta gama wayar Malam dawowa yayi gabanta ya tsaya.

"Naji kina zancen zuwa Saudiyya. Waye zai je?"

"Yarinyar nan ce mijinta ya biya mata." Ta bashi amsa tana miƙewa tsaye.

"Wai Jinjin ɗin ko guda cikin ƴaƴanta?" Malam ya kasa ɓoye son abin duniyar da ya taso masa haiƙan. Idan ƴar cikinsa taje Makka tabbas ya sami abin cika baki da fankama cikin abokansa a ƙauyen. Bugu da ƙari yadda bata da rowa yasa rai da jallabiya, ɗan madina da tashi-ka-fiye-naci. Ƴar bagaruwan nan a gaban su Mal. Ya'u zai dinga ɓantara yana korawa da zamzam.

Zuciyarsa ta luluƙa birnin tunani da yaji ita ce dai mai zuwa, Inna Sarai ta katse masa daddaɗan mafarkinsa.

"Daga ji an fara biye biye kenan. Dama naji labarin auren jari aka yiwa yaran nata. Shi ne za ku fara kai mazajen ana mallakesu. To dai a dinga jin tsoron Allah."

Inna Luba ta dubeta da kallon baki ishe ni kallo ba ta kawar da kai.

"An faɗa miki kowa irinku ne? Da mallakar namiji tana gabana ke kin isa Malam ya kalle ki? Ku da malaman tsibbu ku ka dogara. Ni kuwa kin san gidan Qur'ani da hadisi na fito. Har yanzu akwai irin ɗaliban babana da ko ƙwandala ba zan bayar ba za su ban mijin naki a tafin hannu."

"Ai wallahi ƙaryarki. Malam nan gani nan bari daga ke har musakar ƴarki."

Lokaci guda ga mamakin matan nasa ya daka tsawa.

"Ba na son sakarci Sarai. Duk abin da za ku yi na kishi a daina haɗawa da ƴata."

"Jinjin ɗin? Mai shan inna" cewar Inna Sarai don tana ganin kamar bai gane ba.

"Shan inna kika ce ai ko? Kowa ya san lalura ce ba ita ta ɗorawa kanta ba."

Wannan furucin nasa ya sanya duka matan kallonsa da mamakin da yafi na farko. Shin mafarki suke yi ko gaske ne. Inna Sarai haɓa ta riƙe daga baya ta koma tafa hannuwa. Inna Luba kuwa ƙare masa kallo tayi ta kama hanya ta wuce ɗaki. Tana jiyo shewar Inna Sarai tana kiran Malam mai kwaɗayi.

***

Kamar kullum Ahmad yau ma da ya kira Zahra sai da ya nemi Salwa. Baya kiran wayarta saboda ya san yanzu yi masa ƙaryar taja gida ba zai bata wahala ba.

Ta gaishe shi da ladabin kura ta saurari jawabinsa. Wai ya samo asibiti sun gama komai za a kwantar da Mami.

"Ke za ki zauna da ita. Akwai wani yaron office ɗinmu da nayi making arrangement dashi akan kawo muku abinci idan Zahra ta gama"

"To Yaya. Allah Ya dawo daku lafiya."

Babu wata ƙofa da Salwa ta bari a buɗe wadda Ahmad zai yi zargin wani abu. Zahra ma da su ke gida ɗaya bata ga komai ba. Duka su biyun har suna addu'ar Allah Yasa shiriya ce ta zo. Ta dawo hayyacinta. Salwan da su ka sani ce a gabansu.

Ashe kwantan ɓauna tayi musu. A ranar da yamma su ka koma asibiti ita da Mami. Bayan tafiyar Zahra rufe ƙofa tayi tayi juyin murna son rai. A nan dai Ahmad bai isa ya ce ta bawa Mami su yi magana don ya tabbatar tana asibiti. Dama ce ta samu da za ta bi kadin aikin da tayi don ayi a wuce wajen.

Bari tayi sai wuraren shabiyun rana washegari ta silla wanka ta ci ado tamkar a gidan biki take ba asibiti ba. Tayi nan tayi can tana ta shiri, Mami na aikin binta da ido. Sarai Salwa ta san tuhuma ce take mata da irin kallon da take binta dashi. Ita kuwa yanzu wannan kallon ya bar yi mata kwarjini. Mamin kanta ta jima da rasa martabarta ta uwa daga ranar da ta buɗewa Salwa sirrinta na biye biyen malaman tsibbu. Gajiya tayi da kallon da ake mata ta dubi Mamin tana mai taɓe baki.

"Naga kina ta kallona. Unguwa zanje. Ga nurses nan za su kula dake kafin na dawo."

Mami ta girgiza kai. Tana takaicin yadda ta koma babu magana kuma babu damar yi da gaɓɓai. Da ƙyar ta iya girgiza kai ta kafe Salwa da ido da kallon gargaɗi. Ita kuwa tayi mirsisi tamkar bata san me Mamin take nufi ba.

Su kansu ma'aikatan asibitin sun yi mamaki sosai da ta fito zata tafi. Wata mai shara ta kasa ɓoyewa har sai da ta magantu da Salwan ta ce su dinga leƙa daƙin kafin ta dawo.

"Baiwar Allah wace irin unguwa ce wannan da ba za ki iya jiran wani a ƴan uwa ya canjeki ba sai ki tafi?"

"Au..." Salwa ta faɗi cikin murmushi sannan ta buɗe jakarta ta fito da wallet. Dubu biyar ta miƙawa ta kusa da wadda tayi maganar "gashi ku raba da duk wadda ta tayaki dubata. Ba wani jimawa zan yi ba."

Suna ji suna gani ta fita abinta. Wadda aka bawa kuɗin kamar ta karɓi wuta sai sannan tunaninta ya dawo. Zubar da kuɗin tayi ba shiri domin ta san dokar asibitinsu. Zuwa duba mara lafiya indai ba shara ce ta kaisu ba ba huruminsu ba. Sauran ma kowacce neman zillewa tayi. Sai a ƙarshe su ka yanke shawarar kai kuɗin wurin wata babbar metiron kafin ya janyo musu matsala. Ai kuwa tayi ta fađa da su ka je.

"Mahaifiya babu lafiya ai ko jarabawa ce da ita ta haƙura tunda babu kowa."

Su dai sub-staff ɗin babu wadda ta sake magana. Suna kallo ta tashi da kuɗin a hannu ta tafi ofishin daraktan asibitin. Shi tashi yayi yaje yaga halin da Mami take ciki. Tayi fitsari har ya gangaro kan kafet. Idanun jajir tasha kukan baƙinciki. Ƴar cikinta ce ta banzatar da ita saboda nata muradin kamar yadda ta dinga yiwa nata ƴan uwan. Barewa ba tayi gudu ɗanta yayi rarrafe ba. Ko ma mene ne laifinta ne!

Darakta ya bincika yaji likitan da yake kula da case ɗinta wanda aka haɗa da Ahmad ta waya har su ka yi magana kafin a kwantar dasu.

A matsayin wurin na asibiti, fitsarin ba shi bane damuwarsu kamar fitar Salwa wadda ita ya dace ta neme su idan wani abu ya faru. Bai ɓata lokaci ba kuwa ya kira numbar Ahmad ta Saudiyya wadda su ke magana.

"Laifi ne babba wani daga waje ya biya ma'aikatanmu su yi masa personal aiki kuma a cikin asibitin. In asibitin ne bai yi muku ba kuna iya ɗauke patient ɗin. Amma ba za mu yarda da negligence daga gareku ba tunda patient ɗinku mai buƙatar kulawa ce 24/7 sannan daga baya azo ana kuka damu."

Ran Ahmad yayi matuƙar ɓaci. Ya bawa likitan haƙuri da alƙawarin za a gyara. Wayar Salwa ya shiga nema ba ji ba gani.

Lokacin bata jima da sauka daga adaidaita sahu a bakin gate ɗin gidan Taj ba. Ta fiddo wayar taga sunan mai kiran sai kawai ta mayar cikin jaka ta buga gate ɗin. Zuciyarta wani irin zillo tayi da maigadi ya buɗe mata ta shiga bayan ta tabbatar masa da cewa ita ƙanwar maigidan ce.

"Allah Sarki. Gaskiya kuna da yawa Masha Allah. Jiya wasu sun zo. Yau ma kinga mota can..." ya nuna mata motar gidan Yaya Hajiyayye "ta ƴan uwanku da su ka riga ki isowa."

Wani abu Salwa taji a ranta. Kamar ta juya ta koma. Sai ta tuna da aikin da aka tabbatar mata da zai kama shi. Ta saki murmushi. A gaban ƴan uwansa shi ne wuri mafi dacewa da ya kamata ya nuna soyayyarsa gareta. Da wannan tunanin ta shiga gidan gaba gaɗi. RAYUWA DA GIƁI 34

Batul Mamman💖

* Saɓanin baƙin jiya da bata gama sabawa dasu ba, yau da yake Yaya Hajiyye da Firdaus ta zo sai Hamdi tayi saurin sakewa. Ga albishir ɗin tafiyar Yaya da ya sake faranta mata rai. Kitchen su ka shige da Firdaus suna ƙusƙus. A falo kuma Taj ne da Yaya Hajiyayye su ke tasu hirar.

"Wai ka san Kubra tare su ka tafi da Alhaji? Ko ni kaɗai ce ban san da tafiyar ba?"

"Bana son jin kowa na faɗin bai sani ba. Sai nayi ta wasu irin tunani." Taj ya faɗa da damuwa a tare da shi "kamar wani abu ake ɓoyewa."

"Kai ka san Alhaji bashi da wannan. To ma me zai ɓoye? Kawai maybe taji maganar ne ta ce ita ma zata sai ya barta."

"Amma ta kasa faɗa a Home group?"

Waya Yaya Hajiyayye ta ɗauko ta dubi Taj "zan yi sanarwa yanzu. Duk mai ƴan matsabbai da lokaci da kuma niyya ta shirya sayen ticket mu bi su."

"Ayi min alfarma. Jiya na kai Hamdi anyi passport. A jira ya fito a sami visa."

"Gaskiya za a iya jimawa. Mu tafi za ku taho?" Ta ce don akwaita da wutar ciki. Bata son ɓata lokaci idan aka ce za ayi abu.

Taj ya bata amsa da cewa "Alfarma na nema" yana sa ran komai zai samu da wuri in sha Allahu.

Basu gama hirar ba Salwa ta ƙwanƙwasa ƙofa. Taj ya tashi zai buɗe sai ga Firdaus ta fito daga kitchen. Maimakon ya koma wajen zamansa sai yayi kitchen.

Ita kuwa Firdaus hannun ƙofar ta kama da murnarta tana cewa "Ko ƴan gidanmu ne?"

Wani irin kallo na rashin fahimta ta yiwa Salwa da ta gani a tsaye taci kwalliya irin wadda bata taɓa ganinta da ita ba.

"Anti Salwa ke kaɗai? Ina Anti Zahra da su Hayat?"

"Ni kaɗai ce. Ya Taj yana nan?"

"Eh, shigo ciki."

Ƙamshin turarukan da Salwa ta yiwa fesawar Allah tsine saboda yawa ya doki hancin Yaya Hajiyayye da Taj. Ta dinga taku ta shigo ciki da kwarkwasa. Ta kuma rasa inda za ta zauna sai kusa da Taj dake zaune akam two-sitter. Shi da yayarsa tsayuwa ganin ikon Allah da tana nufo shi suka yi. Shi yasa babu wanda ya iya dakatar da ita.

"Ya Taj ina wuni?" Tayi magana da wata zuƙaƙƙiyar murya.

"Lafiya ƙalau."

"Ka ganni sai yau ko?"

Tashi ya yi tsaye da yaji me ta ce ya ce "mun yi dake za ki zo ne?"

Ko a jikinta ta sake kashe murya ta ce "Noooo, I thought you want to see me. Miss me?"

"Ba sai kin canja harshe ba Salwa, gidanmu babu wanda bai yi karatu ba." Yaya Hajiyayye ta ce tana jifan Taj da wata muguwar harara "akwai wani abu a tsakaninku ne?"

Duk da ya gane tambayar domin abin da Salwa take yi da kalamanta kowa zai harbo jirginta da wuri. "Me ki ka gani?"

"Me ta zo yi gidanka a haka?" Yaya Hajiyayye ta nuna ta sama da ƙasa.

Danne ɓacin ranta tayi ta ɗauke kai ta dubi Taj.

"Ya Taj a ina za mu yi magana?"

Gajiya da sauraronsu Hamdi tayi ta baro ƙofar kitchen ɗin inda take tsaye ita da Firdaus tun bayan ta faɗa mata baƙuwar da aka yi.

"Ga hanyar ɗakinsa can ku je can ku yi."

"Ba laifi, gara na san yadda yake tun yanzu kafin na dawo cikinsa." Ko shakka bata ji ba ta bada wannan amsar tana murmushin cin nasara.

Zuciyar Hamdi kamar ta fashe ta juya za ta bar wajen Taj ya damƙo hannunta. Ta ja za ta fizge ya janyota gabaɗaya jikinsa yayi mata wata irin kyakkyawar runguma a gabansu. Ta kuwa fashe da kukan da Anti Labiba ta faɗa mata a gida ana yiwa miji. Da gatanki da tarin soyayya a zuciyarsa ake yinsa don kawai an isa. Kissa adon mata! Da aka faɗa tayi zaton shegantaka ce za ta sa mace kuka babu duka ba zagi daga miji. Ashe ba haka bane. Shi ma kukan yana sanin lokacin zuwansa yayi.

Tayi nasara fiye da tunani. Taj ya shiga tashin hankali sosai. Bayanta kawai yake shafawa yana faɗa mata kalaman kwantar da hankali.

Wannan abu ya tayar da hankalin Salwa fiye da ƙima. Me yake faruwa ne? Ya dace zuwa yanzu hankalin Taj ya koma gareta. Ko zuwan nan, tayi ne don son ganin rigimar da take sa ran sun fara.

"Ya Taj..." shiru bai waigo ba, yadda ka san Hamdi ce kaɗai a duniya. Ƙirjinta ya kama hawa da sauka cikin kiɗima ta ce "magana nake fa."

"Kana ji tana kiranka. Ni gidanmu zani. Da na sani ban..." Hamdi ta soma faɗi cikin kuka.

Yaya Hajiyayye ta hanata ƙarasawa da cewa "Hamdiyya ki yi haƙuri kinji ko. Taj ya ci albarkacina kada ki yarda ki ɗaga masa hankali akan Salwa. Ƴa na ɗauke ki ba matar ƙani ba. In har na isa to don Allah ki barni da ita."

Hamdi ta ɗaga kai ta ture Taj da ta farga da yadda su ke ta ce "Kin isa Yaya. Wallahi kin isa."

"Salwa baki da lafiya ne ko me? Haka kike dama ko kuwa wani abu ne ya same ki?" Yaya Hajiyayye tayi tambayar tana kallon ta.

Kasa magana tayi. Idanunta na bin Hamdi da kallon tsana. At the same time tana jifan Taj da nasa salon kallon na bege. Ta kasa gane ya aka haihu a ragaya. Yardar da tayi da aikin yasa bata kawo haka zai iya faruwa ba. A karo na uku dai ta sake gwada sa'arta ta gani ko akwai dama.

"Ka bani minti biyar mu yi magana Ya Taj. Wurinka na zo don Allah."

Haɓa Yaya Hajiyayye ta kama tsabar mamakin wannan ƙarfin hali. Muryarta a kausashe kuwa ta ce,

"Wuce ciki da matarka yanzun nan." Ta dubi Firdaus "koma kitchen ki kula da girkin." Sannan ta dawo da dubanta ga Salwa "ke kuma kama gabanki yanzun nan kafin in gwada miki ni wace ce."

"Allah na tuba sani kuma na nawa zan yi miki Yaya Hajiyayye? Kishiya ta hanaki zama a gidanki na farko. Alhajinku ya ƙaƙaba wa yaronsa ke aka haifi waɗannan" Salwa ta nuna Firdaus tana yatsina fuska.

Wani kukan kura Firdaus tayi, tayi kan Salwa. Kafin ta kai mata duka Hamdi ta riƙeta da iya ƙarfinta. Firdaus na ƙoƙarin ƙwacewa Taj ya ɗaga hannu zai kai mata mari shi ma Yaya Hajiyayye ta riƙe nasa hannun.

"Jinin Alh. Hayatu da dukan mace? Allah Ya kiyaye."

Maganarta ta farko yaji ta jan hannun Hamdi domin su bar falon. Zamansa tabbas zai janyowa gidansu abin faɗa. Da Firdaus ya haɗa su ka shiga ɗakin Hamdi ya ce su zauna shi kuma ya sake fitowa. Daidai lokacin Yaya Hajiyayye tana yiwa Salwa magana.

"Ki tafi gida Salwa. Wannan abin da kike yi ba zai taɓa baki abin da ki ke nema a mutumce ba."

Taj gaban Salwa ya ƙarasa ya tsaya fuskarsa a murtuke "Salwa na taɓa cewa ina son ki?"

Shiru tayi. Zuciyarta cike taf da uwar kunya sai dai son zuciya ya riga yaci ƙarfinta. Sunanta kawai da ya kira sau da ya saukar mata da kasala da ƙarin son sa.

"Tunda baki da amsa to ina roƙonki this should realy be the last time. Ina raga miki ne kawai saboda Yaya Ahmad."

'Ko dai shafa masa turaren zan yi in kuma yi masa magana a lokacin?' Salwa ta raya a ranta. Wanda yake hannunta da ta shafa a bakin ƙofar falon ta duba ta hanyar mitstsika yatsunta. Tana ɗaga hannuwa ita kuma Yaya Hajiyayye tayi tunanin rungumarsa za ta yi shi yasa tayi saurin shiga tsakani ta tsinketa da mari tasss. Kunnuwan Salwa sai da su ka ɗauke wuta na wucin gadi.

"Ke jakar ina ce kike ƙoƙarin rungumar baligin namiji mai aure?"

Caraf maganar a kunnuwan Hamdi. Ta yunƙura za ta tashi Firdaus ta ce ko ta fita kada ta saka baki.

"Ki barta da Mama. Wallahi yau ko me take ji dashi ta tara ta samu."

Hannuwa duka biyu riƙe da kumatu su ka sameta. Taj ya kasa kallonta. Zama kawai yayi ya dafe kansa.

"Bata da lafiya Yaya Hajiyayye. Wannan ba abin da mai lafiyayyar ƙwaƙwalwa zai yi bane."

"Babu wani hauka a tare da ita. A nono ta zuƙa kuma in sha Allahu gidanmu nan gani nan bari."

Tana rufe bakinta ta dannawa Ahmad kira.

"Yaya please zan kira ki anjima kaɗan..." rashin samun Salwa a waya ne ya kiɗima shi. Ya rasa wa zai kira ya tafi asibitin. Mami da danginta amma tamkar wadda ta faɗo ita kaɗai saboda baƙin halinta ya kori kowa.

"Ai koma mene ne uzurin indai ba sallah bace to ka saurare ni. Batun wannan yarinyar ne Salwa..."

Katse ta yayi da saurin sa "gidan ki ta zo?"

"Ina fa. Gata a gidan Taj."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Yaya Hajiyayye tun ɗazu nake kiranta ina nemanta." Ya ce a sanyaye gwanin ban tausayi.

"Ta ina za ta ɗauka bayan ta fito yawon zubar da mutumci?"

A tsiwace Salwa ta ce "ni da aure nake son shi ba..."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull