Kenza eBookz

Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 46

Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 46

Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 46: Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 46. "Rufe bakin ki" Yaya Hajiyayye ta daka mata tsawar da Hamdi ma sai da…

3,350 words

"Rufe bakin ki" Yaya Hajiyayye ta daka mata tsawar da Hamdi ma sai da zuciyarta ta kaɗa. Firdaus kuwa ta san halin mahaifiyarta dama. Akwai ban dariya da iya zolaya amma kada ka shiga huruminta. Yanzun nan za ta birkice.

"Kana ji na Ahmad? Albarkacin ka zan sassauta mata. Amma lallai ka ja mata kunne. Idan ma hauka ne to tayi a wani wajen."

Bai ji daɗi ba amma kuma bai ji haushin yayar tasa ba saboda ya san gaskiya ce take faɗa. Kuma Salwa ce ta jawo wa kanta "Ƙalau take wallahi. Tsabar son zuciya ne da rashin tawakkali. Idan tana da zuciya ko aurenta ya ce zai yi ai ta ce bata so a yanzu. Saka ni a speaker"

Yaya Hajiyayye ta saka. Ahmad ya kalli inda Kamal yake kwance ya ƙara jin nauyi a zuciyarsa. Ga damuwar gaske amma haka kawai Salwa tana tayar masa da hankali.

"Idan kin fita ki koma asibiti ko ki wuce gidan ubanki kin ji ko. Na gaji. Ba ni na haife ki ba saboda haka ba za ki saka min hawan jini ba. Duk abin da ki ka zaɓarwa kan ki daga yau ya rage naki. Kada ki yarda ki koma gidana."

Bai jira jin ta bakin kowa ba ya katse call ɗin. Salwa ta bi su da kallo ɗaiɗai. Ta muzanta ajin ƙarshe. Haka ta miƙe ta yi ƙwafa da ƙarfi ta fita.

"Ƴar banzar yarinya. A dalilin ki yau har rungume rungumen ango da amarya sai da na gani." Yaya Hajiyayye ta cigaba da mita.

Taj ya kama dariya. Hamdi kuwa hanyar ɗaki ta nufa, Firdaus na yi mata dariya. A lokaci guda falon ya mamaye da ƙaurin girkin da ya rasa kulawar waɗanda su ka ɗora shi. Su huɗun dake falo a tare su ka yi hanyar kitchen ɗin.

***

Tsinuwa da zagi da mummunar addu'a babu irin wanda Salwa bata yiwa Ummi ba da ta fito. Ta tari adaidaita sahu amma ta rasa ina za ta ce ya kaita. Sai da ya yi shirin tafiya tayi saurin faɗin sunan unguwar da za ta. Suna tafe a hanya tayi mamaki ƙwarai da ta gane gidan. Sau ɗaya ta taɓa biyo Ummi a baya bayan sun tashi daga wata haɗuwa da su ka yi kafin bikin su Hamdi.

Zuciya tana ta ingiza ta. Baƙinciki da ɓacin ran da take ciki ya yi yawa. Da ta ƙwanƙwasa ƙofa Siyama ce ta buɗe.

"Ummi nake nema."

"Wa zan ce mata?" Siyama ta tambaya a tsorace. Fuskar Salwa abin tsoro. Kana ganinta ka san ba da alkhairi ta zo ba.

Daga tambayar Salwa ta gane Ummi tana ciki. Bata ɓata lokaci ba ta hankaɗe Siyama gefe ta faɗa cikin gidan tana ƙwala kira.

"Ummi. Ummi. Ummi..."

A firgice Ummi ta fito daga ɗakin Iyaa inda aka saka ta gyaran wardrobe. Gabanta ya faɗi da ta tabbatar Salwa ce ba muryar ke mata gizo ba.

"Me ya kawo ki gidan mu? Wa ma ya nuna miki?" Ummi ta ja hannunta su ka koma ƙofar gida.

Iyaa da Baba Maje fitowa su ka yi daga ɗakinsa da Baballe inda su ke tattaunawa akan ginin gidansa inda Zee za ta tare. Wajen su ka je amma Ummi da Salwa basu ankare da su ba.

Salwa ta cakumi wuyan Ummi "Ni za ki ha'inta? Turaren da ku ka bani dama ba wanda zai sa Ya Taj ya saki wannan ƴar ɗan daudun bane ya aure ni?"

Tsohuwar bully an saba dambe. Ummi mantawa tayi da inda take ta doke hannun Salwa ita ma ta riƙe mata wuyan riga.

"Banza a banza...duk soyayyar da za a siya da asiri wallahi na raina ta. Turare kuma ba na kashe aure bane."

Don baƙin ciki Salwa harda kuka ta ce "Na mene ne? Me ku ka sa nayi?"

"Ummi..."

Iyaa ta fara kiranta horrified da jin abin da su ke cewa. Sai dai da wuri Baba Maje ya yi mata nuni da tayi shiru. Abin kunya har mutane sun fara taruwa.

"Ki jira ki gani amma tabbas soyayyarsa ba ta ciki."

"Wani aikin ku ka saka ni?"

"Alh. Usaini dai ya saka ki. Ni mene ne nawa a ciki?"

Cikin karaji Salwa ta ce "Waye Alh. Usaini? Me nayi Ummi? Turaren mene ne?"

"Turaren kassara sana'ar mijin Hamdi." Ta amsa mata da yanayin tsokana.

Ai tana rufe baki Salwa ta daddage ta kai mata wawura. Kan kace meye wannan dambe ya kacame a tsakaninsu. Duka harda yaga riguna a gaban mutane. Iyaa hawaye kawai take zubarwa. Baba Maje kuwa cikin gida ya koma yana mai jin kunyar abin da ƴarsa tayi na zubar musu da mutumci. Baballe duk zafinsa akan Ummi shi ma komawa yayi yana mai jan hannun Siyama. Ƴan unguwa su ka yi ƙoƙarin rabasu abu yaci tura. Wani kawai sai ya kira ƴan sanda. Daga cikin gidan su ka ji jiniyar motar. Baba Maje ya ce kada wanda ya fita.

Aka tattara su sai Police station. Nambar Baba Maje Ummi ta bayar. Da aka kira shi akan case ɗin ya ce zai zo. Suna gama magana ya kashe wayarsa gabaɗaya. Ya kuma ce da su iyalinsa kada wanda ya amsa kiran baƙuwar namba. Ummi ta zauna ta koyi hankali.

Salwa ta fi Ummi tsurewa. Kwana a nan abu ne da ba za ta iya ba. Gashi ita ɗin mai laifi ce. Ta kasa bada numbar Zahra saboda gudun tashin hankalin da za su yi da Ahmad. Garin Kano cike yake da dangin Mami, yau ga ranarsu amma babu wanda za ta iya kira kai tsaye saboda ba ayi mu'amalar arziƙi ba. Ƙarshe nambar babanta ta bayar. Aka kira shi sau biyar baya kusa bai ɗauka ba.

"Tunda baku da kowa mu bamu rasa masaukin baƙi. A wuce dasu su shiga su huta." Cewar DPO ya na barin inda su ke.

Hankali a tashe Salwa ta ce "Don Allah ka sa a sake kiran Babana. Ni wallahi ba zan iya kwana a nan ba."

Ummi kuwa ko gezau. Bata shaida ta shiga one chance ba sai da aka haɗa su cell ɗaya da wasu yan daban mata. Ashe damben su da Salwa wasa ne. Irin dukan da aka yi musu a cell đin ya ƙazanta. Babu wadda jikinta bai amsa ba. Kafin wani lokaci kowacce fa kama kukan gaske.

***

Saboda yawan kiran waya sai da kunnen Ahmad ya yi zafi. Duk wasu ƴan uwa Mami na kusa da na nesa ya dinga kira yana neman taimakonsu akan kula da itaa asibiti. Duk wanda ya kira suna yabon yadda ya kiyaye zumunci amma kowa da irin labarin cin kashin da Mami tayi masa a baya. Bottom line dai babu mai zuwa. Ya shiga damuwa sosai. Kamar ya faɗawa Alhaji sai dai yana tsoron me zai faru. Daɗin daɗawa ga Kamal a kwance sai na'u'rori. Kansa ya ƙulle.

Lokaci guda wata shawara ta zo masa. Ya kira likitan Mami ya ce a bashi Nos guda da za ta zauna da Mami tsahon sati ɗaya kafin ya dawo. Zai biya ko nawa ne. Aka tsadance ya tura kuɗin a take su kuma su ka tura wadda za ta iya ɗakin. Sai lokacin ya sami nutsuwa ya kira Baban Salwa ya tambayi ko ta koma.

"Bata dawo ba amma zan kira ta. Ina so ka zare hannunka a kanta. Zan yi maganin abin da kaina."

***

Kwanaki huɗu bayan nan Taj ya shirya zai koma Happy Taj. Hamdi ta dasa masa rigima kala kala. Rarrashi iri daban daban yayi mata. Ƙarshe ba shi ya fita ba sai ƙarfe goma da minti kusan arba'in. Ya fara kaita gida saboda suna sa ran tafiyar Yaya ta samu nan da kwana biyar. Yana zuwa yaran kitchen ɗinsa su ka ce yau gwaji za su yi masa su tabbatar aure bai mantar dashi girki ba.

"Kada daɗin abincin amarya yasa ka manta naka."

Kowa yayi dariya kuwa. Shi kuma ya ƙarɓi ragamar dafa chicken kabsa. A lokacin ne kuma aikin su Alh. Usaini ya yi tasirin gaske. Ya haɗa spices ɗinsa tunda abin da zai dafa dama spices ne sinadarin sa. Komai ya ajiye a gefe yayi marinating kazar. Bai ḍanɗana ba tunda hannu ya gama sabawa. Cikin ƙwarewarsa ya gama hađa komai saura jiran dahuwar abinci. Yana duba list ɗin abubuwan da aka ƙaro da baya nan yaga wasu cikin ma'aikatansa sun shigo kitchen ɗin a guje.

"Sir baka ji ƙauri ba?" Wani ya tambaye shi da ya ce me ya faru.

Ya juya ya buḍe tukunyar. Ƙauri ya sake cika kitchen ɗin. Kowa na tari banda shi. Shinkfar tayi ɓaki ta ƙone babu abin mora a ciki. Abin ya ɗaure masa kai. Ya faki idonsu ya da dangwali gishiri ya lasa. Ko ɗigo bai ji ɗanɗanon sa ba. Ya sake ɗora wata shinkafar ita kuma da ya gama aka yi serving ga masu saye babu wanda yaci rabi. Haka aka dinga dawo da plates ɗin cike da abinci. Bakinsa still babu taste. Yasa yaran kitchen ɗin ɗanɗawa. Kowa ya kai baki sai ya gumtse abinsa ya dangana bakin shara ya tofar. Akwai wanda ya soma amai a gabansa ma.

"Me kuke ji?" Yayi tambayar calmly.

"Gishiri da garlic sun yi yawa sosai. Yawan daido duk dauriya mutum ba zai iya rufe ya ci ba."

Hankalinsa sayiwani irin tashi yayi. Bai yiwa kowa sallama ba ya fita. Yana zuwa gida ya buɗe fridge ya ɗauki mixed fruit juice ɗin da ya haɗa da hannunsa jiya. Nan ma shiru baki da hanci bai ji komai ba.

***

Abba Habibu da iyalinsa suna tattaunawa game da waɗanda Yaya za ta bi saboda ta sami muharrami.

"Abba dama dai ka jira ka samu wasu kuɗin kun tafi tare." Cewar Zee

"Yanzu Allah Ya kirata. Ku dai ku yi mata addu'a. Banda abin ku mijin Labiba ai ya zama ɗan gida. Yan uwan nasa da zai yi tafiyar dasu jiya har kirana su ka yi mu ka gaisa."

"To kun gani ko..." Abba ya ce da murna.

Suna wannan hirar Halifa ya buɗe passport ɗin Yaya yana gani.

"Laah Yaya wane irin blood group ne wannan O minus?"

Hamdi ta karɓe ta kalla " ya kamata in ɗan yi studying bambancin blood group ɗinnan. Nima anyi min test ɗinsa amma ban duba ba da shi da geno type."

"Da aka yi min sai da mutumin ya ce min wai jinina na musamman ne don yana wahala."

Zee da Halifa sai cewa su ka yi su ma ɗin za su je ayi musu. Daga wannan hirar Abba ya ce,

"Hamdi ki bamu numbar Kamal ta can, idan ta isa sai ta kira shi su gaisa."

"Idan bamu da nisa in je dai mu gaisa zai fi." Yaya ta faɗi tana murmushi. RAYUWA DA GIƁI 35

Batul Mamman💖

***

Kwana biyu a ƙirgen Hamdi tana lura da duk wani motsin Taj. Ta riga taji a jikinta tun randa ya koma Happy Taj bai dawo gidan da irin jovial spirit ɗin da ya fita dashi ba. Aura ɗinsa gabaɗaya is down amma a zahiri babu wata alama ta ciwo. Ta tambaye shi me ya faru tun a lokacin ya nuna babu komai. Da dare kafin su kwanta ta sake maimaita tambayar sai ya shashantar da zancen.

Jiya ma haka aka yi, domin da ya dawo bai sake fita daga ɗaki ba. Ya ce mata mura yake ji tana neman kama shi. Tayi iya yinta ta rabu dashi. Haka su ka kwana kowa ya juyawa ɗan uwansa baya. Sai da asuba da farka ne ta ganta tayi matashi da ƙirjinsa ya rungumeta sosai. Shi kenan aka cigaba da ranar lafiya ƙalau kafin ya fita. Da ya dawo

Yau dai yana fita ta kira Abba Habibu. Kunya ta so hanata tambaya. Tana ta juya zancen a zuci. Kamar ya sani sai ya ɗauko maganar komawar Taj ɗin aiki.

"Ance maigidan naki ya soma fita ko?"

"Eh, ashe ba ku haɗu ba." Ta amsa da sauri.

"Satin nan ban fita ba. Kin san yana ta matsa min da na ajiye aikin. Ni kuma ban saba zaman haka kawai ba. Na fahimci saboda yana aurenki kamar zai takura idan ina ƙarƙashinsa...duk da tun a baya bai taɓa ci min fuska ba. Na rasa shawarar yankewa Hamdi."

Hamdi tayi murmushi "Abba indai ka san wani aikin za ka nema idan ka bar Happy Taj ɗin gara kayi zamanka."

"Ba za ki ji komai ba?"

Numfasawa tayi da rawar murya "ba zan ji ba. Wanda nayi a baya ma don Allah ka yafe min Abba."

Kafin ta karyar masa da zuciya har ya kai ga kasa ɓoye rauninsa ya ce "ba ki min komai ba. Har abada babu riƙo tsakani na daku in sha Allah. Allah Ya yi muku albarka."

"Amin Abbana" tayi maganar cikin farinciki.

Hira ce ta kankama tsakaninsu wadda duk akan tafiyar Yaya ce. Kafin su yi sallama ne ta daure tayi masa tambayar duk da gudun kada yaga rashin kunyarta.

"Abba wani abu yana faruwa a Happy Taj ne?"

"Me ki ka gani? Me ya faru?" Ya tambayeta da sauri kuma cikin tashin hankali. Ba komai ya janyo hakan ba sai lura da yayi yanzu kullum Baba Maje sai ya yi masa tambayar da ta shafi Happy Taj da kuma lafiyar Hamdi da Taj ɗin.

Amsar tasa ta ishe ta samun gamsuwa "Kullum idan ya dawo yanayinsa babu daɗi. Na fahimci kamar daga can ne matsalar."

Wayancewa Abba Habibu yayi tunda bai san mene ne manufar tambayoyin Baba Maje ba. Shi yasa bai sanar da ita ba.

"Anya kuwa? Da wani abu ya faru zan ji. Amma ki bari zan tambaya."

Taƙaita zancen yayi cikin sauri da su ka gama wayar ya kira ɗaya daga cikin ma'aikatan kitchen ɗin Happy Taj. Babu wani ɓoye ɓoye ya ce ya fađa masa abin da yake son ji. Yaron bai musu ba. Don ya ce dama sun yi niyar kiransa da kansu ma.

Labarin da yaji bai yi masa daɗi ba. Kwana uku a jere girkin Taj ba ya ciwuwa. Duk abin da zai ɗora sai an sami matsala. Haka nan indai ya taimaka musu da nasu aikin su ma ba ya tafiya daidai.

"Yau bai saka mana hannu a girki ba. Da za ayi serving wasu baƙi sake yin taro a ƙaramin conference room wallahi Abba Habibu baka ga ɓarin da yayi ba. Trolley (food trolley) ɗin gabaɗaya ya kifar a gabansu."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Yanzu yana ina?"

"Ya ce kwastoman ƙarshe na fita mu tashi. Idan akwai sauran abinci a bayar."

Jiki a sanyaye Abba Habibu ya ce "Nagode."

Allah Ya taimake shi Yaya bata nan. Ita da bata da son fita yau ta nemi Zee ta rakata unguwa...gidan Baba Maje ta tafi yi musu bangajiya na musamman duk da an riga anyi a waya. Ta sayi atamfa da shadda masu kyau da tsada za ta basu na kyautatawa.

***

"Wai ni ina Ummi ne? Ba za ta fito mu gaisa ba?"

Cewar Yaya bayan an sami kimanin awa gida suna hira da Iyaa. A ƙofar gidan daga cikin adaidaita su ka rabu da Zee don ta ce ba za ta shiga ba. Cikin gari gidan ƙanwar kakansu ta gudu. Idan Yayan ta gama za ta dawo su tafi.

Iyaa ta numfasa "tun ɗazu nake ta addu'ar kada ki yi cigiyarta."

"Allah Yasa lafiya. Indai ƙalau take ba sai kin yi min bayani ba." Yaya ta faɗi tana murmushi.

"Jinjin kenan. Kina da kawaici sosai. Yanzu idan naƙi faɗa miki ba za ki ji haushi ba?"

"Banda abin ki ai ba ayi ciki domin tuwo ba kaɗai. Kuma idan bamu zama murfin sirrin ƴaƴanmu na farko ba to wa zai zama? Kada ki ji komai. Allah Ya dafa mana akan yaran nan kawai."

Daga bayansu su ka muryar Baba Maje "sirrin Ummi ba zai rufu ba saboda lokacin bankaɗo shi ya yi."

Kallonsa Iyaa tayi tana girgiza kai. Duk lalacewar Ummi ba za ta so hakan ba. Ba kuma don tana goyon bayan abin da tayi ba. Ko kusa! Duk duniya ko Baba Maje bai kai ta son shiryuwar Ummi ba. Kuma ta yarda da Yaya ɗari bisa ɗari amma dole tayi kwaɗayin sakayawa indai ba ya zama dole ba.

"Sakaya kan ki Habibu zai shigo."

Jin haka Yaya ta juya ba shiri ta kalle shi. Murmushi ya yi kawai mai tarin ma'anoni ya fita.

Me zai kawo Abba a wannan lokacin? Wannan ita ce tambayar da ta yiwa kanta kafin su shigo tare da Baba Maje.

Babu zancen gaishe gaishe. Kai tsaye Baba Maje ya soma magana.

"A waya kayi min tambayar me yasa kwanakin nan kullum sai na tuntuɓeka game da lafiyar Hamdi da mijinta."

"Shi ne kuma za ka ce in zo gida na same ka?" Abba ya tambaye shi domin shi ma ɗin ya shiga duhu.

"Inda zamu je yafi kusa da nan shi yasa. Kafin mu tafi amma zan so sanin me ya ankarar da kai har kayi min tambayar. Na san don ina yawan tambayar lafiyarsu ba zai zama abin tuhuma ba."

"Ƙwarai kuwa. Sai dai keɓe Hamdi ba tare da yawan bibiyar lafiyar su Sajida ba shi ne yasa da naji wata magana game da Taj na neme ka. Amma ka sani ban yi da wata mamufa ba sai son jin ko kana ɓoye min wani abu ne don kada na shiga damuwa."

Hankalin Iyaa sai yafi na Baba Maje tashi. So kawai take taji me yake faruwa da Taj ɗin. Abba Habibu ya faɗa musu abin da yaji daga Hamdi da ma'aikacin Happy Taj.

Da yake Yaya akwai dauriya idan ka kalli fuskarta ba za ka fahimci yadda wannan zance ya kaɗa ta ba. Iyaa kuwa kukan baƙinciki take yi. Wannan abin da yake faruwa akwai hannun Ummi. Wace uwa ce za ta yi alfahari da haka?

Baba Maje ya labarta musu rigimar da ta faru tsakanin Ummi da Salwa. "Tun ranar babu wanda yaje a cikinmu. Rayuwar da ta zaɓa ce take yi mata horo tun yanzu. Gara a barta da duniya ta koya mata hankali."

"Kada ka ce haka. Babu ɗan da aka taba barwa duniya aka ga daidai. Kuma ita ma yanzu da ka ƙyaleta idan ta haɗu da waɗanda su ka fita fitina fa?"

"Ummi ce fa! Babu wanda ya lalata ta sama da biyewa ruɗin zuciyarta. Indai bata ɓata ɗan wani ba, to kuwa babu wanda zai ɓata ta. Da kanta ta mayar da halayenta irin wanda mutane ke gudun yaransu su yi abota da ita."

Su huɗu su ka rankaya police station ɗin da aka rufe su Ummi. Wani tsamurmurin Kofur ya fara yi musu surutu akan rashin zuwa tun ranar da aka kawo su. Baba Maje ya ce barinta yayi a ladabtar da ita. Kuma ko yanzu ba beli ya zo yi ba.

"Ɗakin da muke tsaron nasu fa a cunkushe yake. Tunda rigima ce kawai ta mata za a iya baku su."

Ɗauke kai daga gare shi Baba Maje yayi. Ya ce yana son ganin wanda ya dace domin a fito da Ummi su yi magana. Aka dangana su da ofishin DPO inda a nan ne aka fito musu da Ummi.

Kwanaki uku kacal! Ummi ta zuge ta fita hayyacinta. Babu wanka babu wanki. Kayan jikinta kamar tsummokara. Kumatunta sun yi shatin hawaye dabbara dabbara. Gabaɗayanta babu kyawun gani. Haka ta ƙaraso gabansu tana ɗingishi. Wanđanda su ka tarar a cell ɗinsu sun yi musu duka ita da Salwa.

Kamar haɗin baki. Babu wanda ya nuna damuwa akan ciwukanta. A gaban DPO ɗin dai Baba Maje ya ɗauko zancen Taj.

"Ki faɗa min gaskiya Ummi. Me ki ka yiwa mijin Hamdi har ya fara fuskantar irin waɗannan matsaloli daga komawa aiki?"

Allah Ya sani ta gaji da wajen nan don haka ba za ta wahalar da kanta wurin ɓoye ɓoye ba. Abin gudun ya riga ya faru. Kwana uku babu baccin kirki, ta fannin abinci ma sai addu'a. Wurin zagayawa kuwa tun tana amai har ta daina. Gashi don bala'i cikinta ya rasa lokacin lalacewa sai a nan. Bugu da ƙari ƴan cell ɗin nasu sun ɗora mata karan tsana. Daga ita har Salwa sun daku amma nata yafi yawa saboda ita ce mai ramawa da farko.

"Salwa ce ba ni ba."

"Wace ce Salwa?"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull