Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 47
Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 47: Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 47. Kofur ɗin ɗazu ya ce "ita ce aka kawo su nan tare. Ace ƴar mutum tana…
3,326 words
Kofur ɗin ɗazu ya ce "ita ce aka kawo su nan tare. Ace ƴar mutum tana sakaye amma bai san ma ita da waye ba sannan babu waiwaye."
Fuska a haɗe DPO ya kalle shi ya ce "Kofur Ɗanliti yaya haka ne? Me ma kake yi a nan?"
"Yallaɓai wasu iyayen ne sam ba sa gane illar barin ƴaƴansu mata a station."
"Kai dai naka ƴaƴan suna gida ko?" DPO ya ce a harzuƙe.
"La shakka."
"To jeka ka kawo Salwa ɗin ka kama gabanka."
Wani sassanyan murmushi Kofur Ɗanliti ya yiwa Ummi da zai fita. Harda cewa ta kwantar da hankalinta. Yanzu gaskiya za ta yi halinta. Ƙila ma a yau ta sami damar tafiya.
Tsawar da DPO ya daka masa ce tasa shi gaggawar fita yana ƙananun surutai akan ƙulle mutane ba bisa haƙƙi ba. Ita kuwa Ummi wata muguwar harara ta galla masa da ya juya. Tun zuwansu yake ta rawar ƙafa a kanta. Matan da suka yi mata duka ma ya so basu horo irin yadda ake yiwa masu laifi saidai yana ganin shugabarsu ya fita yana Allah Ya isa. Matar regular ce kuma tantiriya. A tsaye ta fishi nesa ba kusa ba.
Ba a jima ba su ka shigo da Salwa. Ta tsaya musu ƙerere tana harararsu. Ta gane iyayen Hamdi ta kuma gane iyayen Ummi daga kamanninsu.
"Durƙusa" Kofur Ɗanladi ya ce da tsawa saboda haushinta da yake ji.
DPO kai ya girgiza kawai don ya ɗago shi ya ce Ummi ta maimaita abin da ta ce. Nan kuwa ta nuna sam bata san komai akan Taj ba. Salwa ke son shi kuma ita ce tayi masa asiri.
"Lallai ma. To a ina na samo turaren? Ba ke bace ki ka bani?" Salwa ta kalli DPO "Wallahi cewa tayi idan na shafa masa zai saki Hamdi ya aure ni."
"To yanzu me ya haɗa ku faɗa?"
Salwa ta ce tayi amfani da turaren yadda aka ce amma Taj wulaƙanta ta ma yayi fiye da yadda yake yi a baya.
"Ummi har kin san bin bokaye kuma?" Iyaa ta fashe da kuka.
"Nima bani aka yi Iyaa. Don Allah ku tafi dani gida."
Ba a wani sha wahala ba ta faɗi cewa Alh. Usaini ne ya bata. Kuma a zahiri ga abin da ya ce mata zai faru da Taj saɓanin yadda su ka faɗawa Salwa.
"Aikin ku nayi muku kenan? Kin san mutanen da na rabu dasu saboda tunanin zan sami Taj?" Salwa tayi kan Ummi cikin ɓacin rai.
Kofur Ɗanliti yayi saurin anjige ta kafin ta cakumi Ummi ta faɗi a ƙasa. Abba Habibu da Yaya sun ga ikon Allah. Bayan Ummi ta kwatanta inda za a sami Alh. Usaini. Ta tabbatar musu da cewa akwai chats ɗinsu harma da recording ɗin wayoyinsu a wayarta.
"Damma kin shiryawa rana irin wannan ne?"
"A'a, na dai kula idan muka gama chatting yana bin duka abin da ya turo ya goge. Shi yasa na soma yin screenshot saboda kada a gaba wani abu ya faru ya zame ya barni."
"Allah ma Ya sa kina da wayonki. Irinsu haka su ke amfani da marasa wayo su cuce su."
Ayyanawa Ummi tayi a ranta cewa indai Kofur Ɗanliti yayi gigin cewa yana sonta, za ta nuna masa rashin mutumcin da zai jima yana yi masa ciwo. Idan ba karambani ba ai shi ma daga gani ya san su ba sa'annin juna ba. Duka duka bai fi rabinta ba a faɗi. Tsayi kuwa ba zai wuceta ba.
Gida Abba Habibu ya buƙaci Yaya ta koma tunda kawo Alh. Usaini zai ɗauki lokaci. Babu musu ta tashi. Jikinta yayi matuƙar sanyi. Ka haifi đa ya zama silar zubar mutumcin mutum babu ruwansa da gazawar tarbiyya. Wani duk ƙoƙarin iyayensa sai ya janyo musu magana hankalinsa yake kwanciya.
Baba Maje ma ya ce Iyaa ta tafi ta nuna zama za ta yi. So take taji ƙarshen wannan abu da Ummi ta zama sakarya wajen jagosarsa.
Minti ashirin bayan tafiyar Yaya sannan aka zo da Alh. Usaini. Tun a waje yake ta bala'i da zage zage. Da yaga Ummi sai ya taɓe baki.
"Kina da shaidar nunawa kice da hannuna?" Ya kalli Salwa "ke kin sanni ne?"
"Kaga ka ajiye wannan surutun zai amfane ka a kotu."in ji DPO
"Kotu??" Salwa da Ummi su ka maimaita cikin tashin hankali.
"Ƙwarai kuwa. Kafin lokacin muna buƙatar shi Taj ɗin a nan."
Ranar har dare suna station dai. Taj da Hamdi su ka zo aka maimaita komai. Ya dubi Alh. Usaini ya ce masa da shi da su Salwa duk ya yafe musu ya juya ya fita. Fitarsu ke da wuya mahaifin Alh. Usaini ya je. Bayan ya gama zagi da ci masa mutumci a gaban mutane yace ba zai bashi shugabancin komai cikin kadarorinsa ba. Gado ma ba don Allah ne Yayi da Kansa ba tabbas da ya ce ba zai gaje shi ba. A ƙarshe ya fice. Su Baba Maje ma su ka kama gabansu. Abba Habibu ne ya karɓi Ummi albarkacin iyayenta. Salwa ma an saketa amma ko da ta fito ta rasa inda za ta tafi.
***
Da Hamdi ta shiga ɗaki a kwance ta sami Taj amma ya juya mata baya. A hankali ta lallaɓa ta hau gadon ta kwanta a bayansa. Hannunta ɗaya ta zura ta ƙarƙashin jikinsa, ɗayan kuma ta gaba ta haɗe su ta rungume shi.
"Kuka kake yi ne?"
"Tsokana ta ma kike yi?" Ya yi maganar ba tare da ya juyo ba.
"Ƙorafi dai na zo yi. Ta yaya zan aureka kuma ace safe, rana da dare duk ni ce a kitchen. Gaskiya da sake."
Tashin da bai yi niyya ba yayi. "Kin manta halin da nake ciki ko kuwa da gaske tsokanar ce?"
Hamdi ta ce "Ka faɗa min damuwarka ne? Ba da kaina na nemo amsar ba?"
"Da ki ka nemo ba ki ji tausayina ba?"
"Girkin ne ba za ka tayani ba kake tada zancen?" Ta kyaɓe fuska.
Taj ya riƙe baki da yaga da gaske idanunta suna neman zubo da ƙwalla "Abu ya same ni amma saboda ƙarfin hali ke ce da ɓata rai da shirin kuka?"
"Na fi ka shiga tashin hankali. Ka da aka mana aure hancin ka da baki duk suna aiki. Yanzu da haka ta faru sai anyi min cikon sadaki." Tayi kicin kicin da fuska.
Taj bai san lokacin da ya soma dariya ba "cikon sadaki fa kika ce?"
Ta goge ƙwallar ƙarya "Eh mana. Na baka tausayi ko?"
"Haƙƙun."
"Zan iya yafewa in za ka yarda ka fito daga ɗakin nan mu shiga kitchen."
"Hamdi..."
"I'll be your nose" ta tsaya akan gwiyoyinta akan gadon ta goga hancinta da nasa "and your tongue." Ta rataya hannuwanta a wuyansa ta sumbace shi "I'll be you har ka sami lafiya."
Ƙanƙameta Taj yayi. Ta dage ta ƙi barin raunin zuciyarta ya bayyana balle tayi kukan da take ta dannewa.
"I love you."
"Me too" ta faɗi har lokacin wuyanta na kafaɗarsa.
A ranar bata yarda sun sake komawa wannan zancen ba. Sai ma mitar da take yi wai ta rasa sunan da za ta dinga kiransa. Ya Taj ɗin da take jindaɗin faɗa shi taji Salwa na kiransa dashi. Yana dariya ya ce
"Ki kirani Malam kawai?"
Ita ma dariyar tayi ta ce "Happy ya ishe ni. "
***
Washegari Taj yaje gida ya faɗawa su Inna abin da ya faru. Da Salwa ta san illar baki da bata janyowa kanta abin da zai sa ta shiga bakin mutane ba. Hajiya bata yi ƙasa a gwiwa ba ta kira Alhaji ta faɗa masa. Hankalinsa ya sake tashi fiye da baya. Bayan sun gama jajantawa juna ya kira sauran matansa. Sun jima suna magana da Inna yana kwantar mata da hankali. Ya ce su dage da yin addu'a. Shi kuma zai san yadda yayi da Alh. Usaini. Yadda su ka ƙulla abin su za su kwance in sha Allah.
"Kun sa ranar dawowa ne?"
"A'a. Za mu yi magana daga baya."
Ajiye wayar yayi yana ta juyayin abubuwa. Case ɗin Taj da Kamal ba ɗaya bane amma a ƙalla mahaifiyar Taj ta san abin da ya shafi ɗanta. Addu'arta tana kai masa. Hajiya fa? Ta ina zai fara? Duk da haka dole ta sani zuciyarsa ta faɗa masa.
Kamar haɗin baki a daren ranar Yaya Hajiyayye ta kira shi tana tambayar saura kwana nawa su dawo.
"Mene ne?"
"Alfarma zan roƙa ku ƙara lokaci. Nan da kwana shida zamu taho in sha Allah."
"Ba na ce Taj ya bari Hamdiyya ta sami visa ba?"
Yaya Hajiyayye tayi dariya "ai ta samu. Surprise mu ka so yi muku. Yanzun nan nayi tunanin kada fa garin surprise mu yi saɓani."
Farincikinsa ya nuna. Ya ajiye wayar sai yaji sanyi yana ratsa shi. Yaya zsi yi da matansa? Dama yana kusa ne da sauƙi.
Haka nan ya yi ta maza ya kira Hajiya. Tunda taji ya ce ta keɓe za su yi magana gabanta ya faɗi. Ya fara da wa'azi ds tunatarwa akan sharuɗan imani.
"Na yarda da ƙaddara. Ka faɗa min kawai me na rasa." Ta ce da rawar murya.
"Baki rasa ba amma duk wani hope yana neman ƙare min."
Jikinta taji yayi nauyi ta sami waje ta zauna. Duk yadda Alhaji ya so rage mata raɗaɗin da za ta ji ta hanyar amfani da kalmomi masu kwantar da hankali abu ya faskara. Kamal yana dab da rasa rayuwarsa saboda rashin dacen mai bashi ƙoda.
Yayi zaton za ta yi kuka sai yaji shiru. Can ta numfasa.
"Yaushe ne akwai jirgi kurkusa?"
"Zan bincika..."
"Ka duba ka biya mana. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." Sai ta katse kiran.
Alhaji ya yi ta kiranta taƙi ɗauka. Mama ya nema yace su haɗu da su Inna yana da magana. Su ukun nan kuka suke yi babu mai rarrashin wani. Su ka shiga ɗakin Hajiya su ka sameta tana haɗa kaya.
"Ku ma ku gaggauta haɗawa domin ko gobe aka sami jirgi zamu tafi tare ko?"
Cikin kuka Umma ta ce "dolenmu Hajiya." Inna da Mama kuwa ko bakin magana babu.
Basu bari yaran sun sani ba. A kwana uku aka gama yi musu komai. Yaran nasu suna ta mitar me yasa basu jira su tafi tare ba. Mama tayi ƙarfin halin cewa mijinsu ke nemansu. Aka mayar da abin shaƙiyanci ana dariya.
* Tafiyarsu da kwana biyu shi ne lokacin tafiyar Yaya. A airport su ka haɗu da abokan tafiyarta. Su Hamdi su ka yi mata rakiya da mazajensu. Abin da ya bawa Taj mamaki da kuma tayar masa da hankali bai wuce ganin Dr. Mubina tana fitowa daga wajen check in ba. Ta rame sosai kamar wadda ta jima tana ciwo. Duk wasu alamun rashin kwanciyar hankali sun bayyana gareta. Da ta gan shi da farko gabanta ya faɗi kuma ya gani. Ta basar shi ma ya nuna bai gane komai ba. Hamdi ya kira su ka gaisa ya ce
"Ku fara ƙawance don da alama ita ce Mrs Happiness."
Hamdi sai murna ta zolayeta
"Umra za ki ko Ya Kamal za ki bi?"
Dr. Mubina tayi murmushi kawai. Taj ya nuna mata Yaya ya ce ga ƙarin abokan tafiya ta samu tunda yaga kamar ita kaɗai ce.
"Na gode kuwa."
Da aka kira su Hamdi da Taj na kallo Dr. Mubina ta haɗa akwatin ta da na Yaya tana ja. Sun ji daɗin hakan kuwa. A ƙofar jirgi inda ake nuna boarding pass Yaya za ta ɗauko nata ta haɗa da ƴar takardar da su Hamdi su ka gani wadda aka saka cikin passport ɗinta. Ita ce mai ɗauke da bayanin lalurarta da su blood group ko da wani abu na emergency zai sameta. Bata san ta yar ba tayi gaba. Mubina ce ta ɗauko mata. Tana shirin bata ta kula da bayanin da yake jiki. Zuciyarta sai da ta girgiza. Ta miƙa mata da rawar hannu. RAYUWA DA GIƁI 36
Batul Mamman💖
***
A dalilin ba lokaci ɗaya aka saya musu ticket ba, wurin zaman Yaya da na abokan tafiyarta daban daban ne. Ɗan saurayin cikinsu Yaya tayi niyar bawa boarding pass ɗinta domin ya duba mata wurin zamanta, haka Abba Habibu ya sanar da ita tayi. Ya ceba inda mutum yake so zai je ya zauna ba. Ta ɗaga hannu za ta bashi Mubina ta riga karɓa. Ta kaita har wurin kujerar ta taimaka mata da ɗora hand luggage a sama sannan ta ɗaura mata belt. Ko ba a faɗa ba ta riga ta gane Yaya bata raɓa shiga jirgi ba.
Yaya tayi ta godiya da sanya mata albarka. Ita kuwa Allah Ya sani da biyu take yi. Kafin jirgi ya tashi bayan kowa ya zauna ta zo ta roƙi wadda take kusa da Yaya da cewa mamanta ce su ka yi musanyen seat. Wannan abu yasa Yaya jindaɗi matuƙa. Ta saki jiki da Mubina suna ta hira. Da jirgin zai tashi duk wani tsoronta Mubina ce ta dinga kwantar mata da hankali. Har aman da ta dinga ji Mubina leda ta bata sannan ta dinga shafa mata baya tana cewa ta hura iskar bakinta a ledar. A haka har su ka daidaita a iska.
"Allah Ya yi miki albarka Ya raya miki zuri'a. Ya jiƙan mahaifa."
"Amin Mama."
"Yaya yaran su ke kirana. Kema in babu damuwa ki dinga kirana da hakan."
Da murmushi Mubina ta ce "to Yaya."
Lokacin da aka kawo abinci Yaya bacci take yi. Mubina ta tasheta ta ci sannan da dabara ta sako zancen da ta zauna dominsa.
"Takardar nan ta passport ɗin ki naga jininki O- ne ko?"
"Ban dai riƙe ba amma tun a gida yara ke cewa O. Wani abin ne?"
Da sauri Mubina ta girgiza kai tana mai son ɓoye zallar farincikinta sai dai Yaya ta fi ta wayo.
"Babu wata matsala. Jinin naki mai kyau ne domin babu wata lalurar da za a buƙaci wani abu na sassan jiki da ba za ki iya taimakawa ba."
"Ikon Allah. Ki ce idan na koma in nemi ƙarin sadaki a wajen Abban su Hamdi."
Dariya Mubina tayi kawai sannan ta kuma tambayarta ƴaƴanta nawa.
"Huɗu ne."
"Kin taɓa yin ɓari?"
"Wai, sosai kuwa. Biyu nayi kafin babbar. A tsakaninsu kuma yaran na ƙara uku. Wani lokacin sai na sa rai da cikin sai ya zube."
Mubina bayani gamsashshe tayi wa Yaya game da rhesus da irin rawar da yake takawa idan aka sami saɓaninsa a tsakanin mata da miji wurin haihuwa.
"Ilimi kogi. Dole ake cewa tafiya mabuɗin ilimi. Kinga zaman abin da bai kai wuni ba amma na ƙaru." Da yake ita ɗin akwai zurfafa tunani sai ta tambayi Mubina me yaja hankalinta har take ganin farinciki a tattare da ita game da jinin.
Kunya ta kama Mubina. "Allah ni likita ce. Yana ƙayatar da mu ganin masu abin da wasu su ke buƙata ido rufe." Tayi dariya "kada ki ce yau kin gamu da mayya."
Yaya ma dariya tayi. Sai dai kuma daga lokacin ta dinga karantar Mubina. Akwai abin da take ganin ta ɓoye mata. Kai gani ma take tana son faɗa mata amma kamar tana jin tsoro. A zuciyarta ta ce 'Allah Yasa alkhairi ne'.
***
Yau sun tashi jikin na Kamal kwata kwata babu daɗi. Anyi alluran, an saka ruwa amma duk da haka ciwo yaƙi sauka. Su Umma ke kuka Hajiya na rarrashinsu. Tun zuwansu ko sau ɗaya bata zubar da hawaye ba. Halin da ta riski Kamal a kullum gani take ba zai shiga wata sa'ar ba. Sai dare take zuwa asibitin. Kullum tana hanya daga Jeddah inda asibitin yake zuwa Makka ta wuni a Harami tana ibada. Ta zabge sosai kamar ba ita ba. Masu rarrashin nata kuma sun fita nuna rauni. Suna tausayin Kamal suna tausayinta.
"Yanzu Alhaji ace Kamal yana cikin wannan yanayi amma Taj bai sani ba? Anya kun yi musu adalci kuwa? Ka yiwa sauran ƴan uwansa adalci? Yau ko addu'a su ke yi masa ai zai sami rangwamen ciwo." Cewar Mama tana zubar da hawaye.
"Kin fi kowa sanin cewa dukkaninsu sai sun taho. Ina gudun su zo a yanzu su haɗu wajen kashe masa ƙarfin gwiwarsa da koke kokensu."
"Ka yi haƙuri amma wannan magana fa ba hujja bace. Yaron da ya tashi a gidan gandu irin namu ace yana jinya da jama'ar da ko rabin gidan basu kai ba ai zai ji babu daɗi."
"Hajiyayye bata faɗa muku za su taho ba?"
"Ta faɗa. Kayi haƙuri. Na rasa me ya dace ayi ne." Ta cigaba da kukanta "ko sake auna jinin nasa za ayi a tabbatar? Ko kuma..."
"Mama ki yi haƙuri"
Kamal ne ya yi maganar yana mai runtse idanuwansa. Komai a jikinsa ciwo yake yi. Magana ma da ƙyar yake cijewa ya yi.
Muryarsa da su ka ji ce tasa su duka matsowa kusa da gadon nasa suna yi masa sannu. A lokacin Bishir ya shigo da waya a hannu yana kallon Alhaji.
"Ya Taj ne wai yake ta neman Ya Kamal. Ya tayar da hankalinsa wai tun jiya basu yi magana ba. Me zan ..."
"Kira min shi."
Inna ta hana "Kamal yanzu ba lokacin da za ka biye masa kuna hira bane."
"Bai sani ba Inna. Ki ka sani ma ko bamu da rabon sake ga.."
Umma bata bari ya gama magana ba ta ce "Ya isa. Kira masa shi Bishir."
Kiran yayi amma Kamal ba zai iya karɓa ba sai Bishir ne ya kara masa a kunne.
"In ka fara neman mutum kamar tsohuwar bazawara ta fito neman miji." Kamal ya faɗi yana murmushi da ƙyar.
Taj ya yi murmushi "Ba zan ji haushi ba balle buƙata ta taƙi biya."
"Me ka ke so?"
"Tambaya zan yi maka. Please ka matsa daga inda su Alhaji su ke."
"Na matsa. Mene ne?"
"Me Alhaji yake ɓoye mana ne Happiness? Tun tafiyarku hankalina ya kasa kwanciya. Amarcin ma na kasa sakin jiki nayi abuna yadda ya dace."
"In na yarda da kai in tafi a tsaye. Akwai damuwar da zata sa ka kasa amarci?" Yana maganar ne ido a rufe don baya son haɗa ido da iyayensa.
Ai kuwa hatta Alhaji sai da duka su ka yi dariya. Kamal ya nuna wa Taj lallai komai lafiya ƙalau. Ba yadda ya iya dole ya yarda.
"Mun haɗu da Mubina a airport da mu ka raka Yaya. Anya ibada ku ka je yi kuwa?"
Nan ma Kamal dariya yayi. Shi da Alhaji sun san da zuwanta. An kuma faɗawa su Hajiya. Ta ce duba shi za ta zo yi amma kowa ya san zuwan nata na sallama ne. Bakunan su ne dai ba za su iya faɗin abin da yake zuci ba. Sun cire hope.
"Happiness amana..."
"Me?" Kamal ya dawo daga tunani. Bai ji me Taj yace ba.
Taj ya sake maimaita cewa zai bashi amana. Ya sanar dashi lalurar da ta same shi da abin da su Salwa su ka yi. Shi ya so fara faɗawa amma ya gagara samunsa a waya. Hankalin Kamal ya tashi sosai.
"Ka yi min addua kafin na zo. Idan ban warke ba to ka shirya. Ni yara 12 za a haifa min kuma cin mu da sha duka wuyanka zai dawo."
"Har wasa kake yi da abu mai mahimmanci irin wannan?"
"Ina da kai Happiness mene ne zai dame ni? Amma nayi tunanin za ku j8 zancen a wajen su Alhaji fa. Sai naga da kai da su Bishir shiru. Ya Ahmad kuma kunyar nemansa nake yi."
"Da gaskiyarka. Amma na san ba zai riƙe ka a rai ba. Yana masallaci."
Suna gama wayar, Hamdi dake zaune kusa da shi tana shirya akwatin tafiyarta ya fuskanta.
"Kin san Allah, akwai abin da yake faruwa mai girma da su Alhaji. Yau kwana nawa a ce babu wanda ya faɗawa su Happiness abin da ya faru?"
"Maybe don kada su tashi hankalinsu tunda ibada su ka je" ta faɗa domin kwantar masa da hankali.
"Allah Ya kai mu gobe. Idan ma akwai wani abu zan gani."
"Me yasa ba za ka yi tunanin komai lafiya ba?" Hamdi ta sake faɗi.